Breaking News

DUDUWA 9

 _*🧟‍♀️DÛDÛWÂ🧟‍♀️*_

          _9_

Ko kawar fitowa daga cikin motar jama'a suka fara yi,tsabar furgici da tashin hankali wasu ma daga ciki ta windo suka zoro jikin su jama'ar dake waje suka dinga janyo su,har aka samu nasarar fito da kowa amma mota na ci da wuta ba ƙaƙƙautawa,da mutanan cikin motar da masu wucewa haka aka taru ana bul bulawa motar ƙasa da ruwa dan a samu ta mutu direban hannu kawai ya ɗora aka yana salati da zagaya motar dan ita kadai ta rage masa yake samun na cin yau da gobe gashi yanzu motar ta kama da wuta duk agajin da ake bata dan ta mutu kamar ƙara mata maka mashi ake lamarin daya ta azara fitowar mutane daga sassa daban daban an haka wani me mashin ya ƙaraso wajan yana.."""


""Sallamu Alaikum,jam'a me ya haddasa wanga wuta haka a motar nan,budar bakin direba sai cewa yayi....


Wallahi lafiya ƙalau muka taho tun daga tashar fulani mun tsaya a nan dan ɗaukar wannan matar,direba ya nuna Rabi da ke zara ido tana duban cikin motar, ita gaba ɗaya ma ta jakar ta da ta bari a cikin motar take gashi jakar har wuta ta kamo ta sai ci take duk wasu kuɗaɗan ta da take adani suna ciki da kayan amfanin ta dayawa,direban ya nuna Rabi yana mai ƙarasa zan chan sa,"ta shiga motar ta zauna kenan direban mu ya taka mota zamu tafi wallahi sai ji mukai ana wuta wuta jama"a bamu san ta ina wutar ta faro ba.


Subhanallahi,ku me ya kai ku ɗaukar wannan matar me baƙar ƙafa ai yasin ko kaffara bazan ba ita ta janyo muku ta dalilin ta hakan ta faru.


Haba malam kai ya akai kasan baƙar ƙafa gare ta yanzu yanzu naga kazo wajan.


To bari kaji kafin ta hau wannan motar ta hau mashin ɗina kuma ga ƴan uwa ƴan achaɓa ku tambaye su wlhy kusan rabin mu sai da ta hau mashi nan mu duk suka ƙi tashi da ta sauka sai kaga sun tashi Allah yasa tsautsayi da asaran ba akan daya daga cikin mu zai faɗa ba,,nan da nan kallo ya koma kan Rabi datayi tsuru tana kallon kowa gaban ta na faduwa,ai kan kace me wa ƴanda kayan su ya kama da wuta cikin motar suka yi kanta suna duka da zagi kan kace me sun tarawa Rabi jini da majina sai ihu take su ƙyaleta zasu kashe ta direba ma cewa yake yi sai fa ta biyashi motar ta ko zata mutu, daƙyar wani dattijo ya shige gaban ta yana.


Haba bayin Allah bai kama ta mu ɗauki doka a hannun lokaci ɗaya ba,yanzu idan ta mutu dole akamo mu gaba ɗaya dan mune sanadi akan abinda bamu da tan tamar ita ce sillar wannan iftila'in  ƙarfen nasara bashi da tabbas bare Allah ya rubuta hakan zai afku mu godewa Allah ma da badamu abin ya faru ba mu kuma dinga auna hankali da tunani kafin muzar tar da hukunci..........,gaskiya kafaɗa baba ba a kyauta ba ƙwata ƙwata,wani magidan ci ya firta yana duban yadda aka tashi kumatu da leman Rabi suka kumbura kamar burodi ɗan dari biyu ƙaton nan na da.

        Da taimakon Allah da na mutane aka samu wanga wutar motar ta mutu,anan fa direba yace ko kowa ya haƙura to fa shi bai da wannan tunani dole Rabi ta sai da gonar gado ta biya shi ko da da rabin kudin motarsa ne ya ɗauki a sara,Rabi tasake rushewa da kuka tana faɗin,"ko sile wallahi bana magani ƙunzugun nawa shima ya babbake a cikin motar,kukan da take ya ƙara bawa dattijon tausayi matuƙa gaya yace shi yaji yagani zai bawa direban rabin kudin sa amma akan ya rabu da Rabi taji da dukkan kawo wuƙar da akayi mata,diraban ya amsa da,"


TO.


Kowa ya watse dayawa wata motar suka hau suka tafi Rabi kuwa da sayyadar ta ta taka ta dawo ƙauyen KANWA,da shi garta gida ta iske Duduwa zaune a kan turmi ga uban nama jibge a gaban ta me unguwa kuwa taɓo yayi kamar wani sha tara,sai da Duduwan ka ta ƙarewa Rabi ido fuska ta cika tayi ɓam da kumburar ran leɓe wajan ya bala'in tashi kamanin ta gaba ɗaya ya sauwa Duduwa ta ɓarke da wata iri yar dariya tana nuna leɓan Rabi har me unguwa sai da ya razana daga baya shima yasaka dariyar dole gudun uwar zugar kar tace bai yi ba,Duduwa ta jima tana ɓaɓɓaka dariyar mugunta daka chan ta haɗe fuska tace.""""


Rabi iyayen daka yaji gashi ke baki dakashi ba shi yajin ya dakoki har kinyi laushi kinga maza wuce ki ɗora mana sanwa yau dabge zamu sha romo mu ƙoshi amma ko ɗan ɗanawa ki kai hmmmm ba sai na faɗa ba wallahi bakin ki tsayi zai kuma ya ƙara tashi kamar cinyar nan tawa kuma fa haka zai zauna har abada..


Kiyiwa Allah ki barni naji da raunin dake jiki na wallahi ko moruwa bazan iya ba.


Kutmelesi mu muka aike ki dakon yajin,mai unguwa kaji fa wai rauni ka ajikinta yo ko duk jikin ki rauni ne na rantse yau sai kin mana dafge munsha mun more ko mai unguwa,,"haka ne kam ke Rabi maza tashi yawuna sai tsinkewa yakeyi yo ma wayayi bikon ki har kika dawo mani gida eyyi.


Kaji fa mai unguwa an samu waje har wani fi'ili ake.


Ai ranki shi dade zama da madaukin kanwa shi yake kawo farin kai,wannan duk daga cikin karatukan dana ɗiba daga taskar ilimin ki ce Allah dai yabar mana *HAMSHAƘIYA,TAURARUWA,FASA TARON MASU TARO,DODAN MAZA DA MATA*,Duduwa kenan ta mai gari bada kanki asare idan kinje gida kice da inna ya faɗi Allah dai ya kaimu bikin nan muci musha ranar ni kaɗai nasan irin farin cikin da zanji.


Allah, kuwa me unguwa,Duduwa ta washe bakin nan tana ta ɓaɓɓaka dariyar jin dadi,me unguwa ya dube ta yace.


Allah kuwa fatana dai Allah yasa na warke kafin wannan rana me ɗumbun tarihi tazo lar ayi biki ina changal changal.


Ai sha kuri munka me unguwa da kai na zan amso maka magani kasanya a ƙafar gobe da katashi ka miƙe tsaye zumbur,wallahi garau zaka jika kana gudu chan da nan kamar ɗan biri.


Wayyo Duduwa ta mai gari kayya kayya huhuhu ina mata ga gwanar ku cikin dubu ke guda daya kin ishi garin masu gari gaba ɗaya,ke ɗin ta daban ce gayyar masu gayya Duduwan mai gari..


Hahahahahahhaha,kai na baka akuyar inna kyauta aradu yau kam me unguwa kasani nishaɗi dana san haka kake da ba'aci ƙaniyar ka ba, amma babu komai kai kajanyo ma kan ka ko yanzu ka sake yasin na lahira sai ya fika jin daɗi,ɓam me unguwa yaja bakinsa yai shiru jin furucin da duduwa tayi ganin me unguwa bai kuma tankawa ba duduwa ta mai do da duban ga Rabi dake raɓe jikin bango a zaune.



Lalalalala,"Zama ma kika koma kika yi,lallai lam kin samu dama,zaki tashi ki mana abinda ya zaunar damu ne ko kuma zaman sa ido da jin gulma zakiyi na kuma faɗa miki ban da ɗan ɗane,kika ɗan ɗana to zaki ɗan ɗanowa kan ki ɗan daka tsalle duk abinda ya meki ke kika jama kanki ba ruwana Duduwa ta mai gari,a dafe a dafe Rabi ta miƙe sai cijewa take taje ta wanko uban naman nan dayawa ta zubashi cikin tukunya ta kawo albasa ta yanka da yawa ta saka maggi da ɗan gishiri da ƴar citta da tafarnuwa ta ɗora bisa murhu nan da nan nama ya game gidan har maƙota da ƙamshi Duduwa na zaune tana kallon duk abinda Rabi keyi haka me unguwa da ƙamshin gaba ɗaya ya gigita masa lisafi ji yake kamar ya afa cikin tukunyar ya tsamo ɗaya ya mai da kwalamar sa amma ba dama magana ma tsoron yinta yake tunda yaji mai gayya mai aikin tace ƙaniyar sa zai ci.

    Tsedugu Rabi ta iba da albasa ta jajjaga su azaune ta watsa cikin tukunyar ta ɗan ƙara ruwa kaɗan dai dai romo ta rufe ta zauna sai haɗiyar yawu take tana duba farfesun jifa jifa,,"innalillahi,wani bala'in ƙwadayi taji yana fusgarta kamar ta faki ido ta ɗan ɗana koda ro mone ta kasa ganin Duduwanka na ankare ta zuba ƙwala ƙwala idanun ta chan dai suka fara jiyo ana.


""Salamu alaikum,mutanan gidan nan yau me kuke dafawa haka unguwa gaba ɗaya ta dauka,wasu mata su uku suka shigo ganin Duduwa na kallon su suka juya da sauri ta ce.


"Ku dawo kar wacce ta fita daga gidan nan.


Sim sim suka juyo suka dawo,tashi Duduwa tayi taje ta ibo tabar mi har guda uku manya tazo ta shimfoɗa ta dube su...


Ku zauna tunda ƙwaɗayi ya ibo ku daga gidajen ku ya kawo ku,Allah ka kawo wasu ƙwaɗayayyun duk mu taru mu zauna,,da wannan ta dubi wannan sai wannan ta dubi wannan,suka dai yi shiru kamar ruwa ya shanye su ana haka sai ga wata slm daga ƙofar gida,da sauri Duduwa ta miƙe ta leƙa bata jima da fita ba ta shigo da kusan mutane bakwai tayi musu nuni da izinan su zauna suma,a haka har sai da tacika tabar ma ukun,tabar ma biyu mata ne zallah,ta ukun kuma maza ne suma zallah wanda rabon ya sha wahala ya tsaga dashi.


  Tofa Rabi na dafa farfesu tana kuka saboda tsabar uban yajin dayake tashi dan yanzo tashin yajin har ya doke ƙamshin naman kuma tsidugun kadan tasaka saboda kar yai yaji amma abu kamar masifa har tari ta fara tana kuka kashirɓan ga zafin wuta ga ciwo.

        Ashe dai azabar yajin ba Rabi kaɗai ya addaba ba har da mazauna kan tabarma suma bala'in ya ishe su har wasu daga ciki sun fara ihu suna bawa Duduwa haƙuri baza su ƙara zuwa ƙwadayi ba ga uban ATISHAWA da suke ta faman jerawa kamar a gidan biki.🤣🤣🤣🤣


    Gogar kuwa ta make waje ɗaya ta dubi wannan ta dubi wanchan ita ko yajin bata ji tayi zukuɗi tana jin gardawa na kuka suna atishawa mara iya ka,me unguwa da ya gaji da atishawa da face majina hannun sa ɗaya yasaka ya toshe hancin sa dayaji numfashin sa zai ɗauke sai ya cire yashaƙi uban yajin sai dai kaji yana hahahahaciiiin,sai ya kuma kai hannun sa ya toshe a haka har Rabi ta iso da tukunyar farfesu zuwa gaban Duduwa ta ajiye,," wayyo Allah gaba daya gida ya koma gidan koke koke musamman da Duduwa ta buɗe naman tana jefawa na tabarma kallo ko da mai ɗan ɗane,nan kowa yafara ja da baya har da me unguwa da tan kafin naman ya sauka yace shi ya yafe a baiwa wanda bai samu ba kason shi da zuciya ɗaya.🤣🤣🤣🤣🤣



*Idan kin n/kaji daɗin page din nan ku Sanƙama min Comments na bazata👍*




_*By*_

_*Maman Dr @ff@n*_

No comments