DUDUWA 8
_*📚 _8_
"Rabi na jin haka ta hantsila tayi cikin daki da gudu tana ƙoƙarin rufe ƙofa duduwa ta riƙe ƙofar katamau ko motsin kirki ƙofar bata kuma yi ba har duduwa ta shige dakin tana.
```fito nan muguwa azalima me mai gari na yayi miki kika ƙarawa goshin sa tsayi yasin kema naki sai ya miƙe kamar bubburutu,Duduwa tayi kan Rabi dake shirin ja da baya tana faɗin"yasin ni ban masa ko mai ba,'ki tambaye shi kiji ɓarin makauniya mu kayi dashi a dokin ƙofa amma wallahi babu abinda na yi masa..
"babu wani nan ke kika ƙarawa goshin masoyi mai gari tsayi,ki wuce muje in tambaya naji,in ko ƙarya ki kayi mun wallahi na lahira sai ya fiki jin dadi a gidan nan dan dakuwa zakiyi har sai naga kin yi laushe, ki wuce muje duk kin tsare ni da ido kamar wata Ashanty ƙawata,zungwai zungai Rabi ta shiga gaba Duduwa na bayan ta,ko da suka fito tsakar gidan babu mai gari babu da lilinsa sai me unguwa dake faman salati yana baiwa Duduwa haƙuri ko kallon sa batayi ba ta fuce daga gidan da gudu dan bin bayan mai gari,shi ko me unguwa ganin Duduwa ta fece ya dubi Rabi da tayi tsuru tana nazarin ta gudu ne ko ta tsaya ya ce.
""Maza dauke ni Rabi kisa a daka kar ta sake dawo wa bamu san dame zata zo ba,""Aa ni yasin ban iya wannan tashin hankalin bazan zauna ya shafe ni ba dama ban ajiye a gidan ka ba bare in ɗauka kaga tafiya ta gidan mu zanyi,,,""Dan girman gyatumin ki Rabi ki tsaya idan kin wuce wa zai duba ni,,"oho kai ka sani daga aure sai jinya ga kuma tashin hankali da yanzu wannan shirgegiyar ta taɓani ka ce mun me,""haƙuri zan baki...........
""Ai kaji a bugi banza kenan ko to bada Rabi jikar Ashiru ba ka gurgurɗa a haka kaje bikon tsohuwar matar ka ga jinya ga hidimawa ƴa ƴanka sam ba wannan ya kawo ni ba.
"Dan Allah kiyi haƙuri mana Rabi.
"Wallahi ban yiwa tafiya zanyi ka aiko min da takarda ta idan kuma ka ƙi wallahi bugaka ƙara zanyi dan ba'a zaman aure dole,Rabi tayafa mayafin data ɗakko daga ɗaki ta futa tana mita ita bazata iya da jinya da yara ba ga masifar duniya Duduwa.
Me unguwa na zaune a inda Rabi ta fita ta barshi kwatsam sai ga Duduwa ta shigo gidan tana hakki,duban me unguwa tayi duk ya burkice ya fita hayyacin sa ganin ta,tace dashi...........
"Masoyi mai gari ya dawo kuwaa?.
"Na rantse babu inda ya dawo, tun da ya fita ban kuma saka shi cikin ido na ba.
Har Duduwan ka ta juya zata fita daga gidan ta sake dawo wa baya ta ce""
"Ina me dakin naka tayi me unguwa?
Jikin me unguwa har ɓari yake ya ce da Duduwa ai ta taf........... dakata ta gudu gidan su ko saboda kar tayi jinyar ka ta dafa tuwo su Lamiru suci su ƙoshi kamar ita ma ba haifo ta a kayi ba.
"Haka ne kam yasin ta ce baza ta iya zama ni da yarana a haka ba wai ta gaji,me unguwa ya furta yana mai gyaɗa kan sa,murmushi Duduwa tayi ta sake cewa.
"Sha kurumin ka me unguwa kamar ta dawo an gama me da me kake so ka ci.?
"Naman kasuwa da lemon ɓawo dan na daɗe rabon dana saka su cikin ido na ba bare na kai ga ci.
"Yau din nan kuwa zaka ci har ka more,amma fa ba dan kai zanyi ba dan su Lamiru da ɗan habu zanyi kai ɗin nan ba mutunci gare ka ba surutun ka har da na tsiya a ciki,wai wani lemon ɓawo da naman kasuwa nake so kamar ya ban a jiyar kudin saura idan Rabi ta dafa kabata ta ci ko kuma ka hana su Lamiru yasin duk wanda ka haɗiye ka cinye sai ka fiddo shi kaji ni.........shiru me unguwa yayi sai raba ido yake chan ya ce da Duduwa..
Naji amma yaushe Rabi zata dawo.
Kai dai ka zuba ido ka kwashi kallo yanzu haka na aika ƴar aike ta musamman in baka labiri ma da ƙafar ta ja'ira zata dawo ba wanda ya ya riƙo ta.,me unguwa yaja dogon numfashi ya sauke shi ai baya tanka ba nashi yai zafi dan ko warkewa ban gama yi ba bana ƙara wani rauni akan rauni ba,Duduwa ta ce dashi.
"Na ware amma zan dawo da Rabi ta shigo duk abinda kake so ka furta ka wai zakaga anyi maka shi ba ɓata lokaci.
Eyee,me unguwa ya furta haɗe da zaro ido waje.
Ko baka so ne?,Duduwa ta jefa masa tambaya ta zuba masa ido ita ma,muryar sa har rawa take yace.
"So kai wane ni nace bana so....
Ayyoooo dana saka an miƙar da kai ta dole yanzu.
UHIMMMMMM,me unguwa kawai yake furta wa Duduwan ka ta fuce daga gidan abinta bata tsaya a ko ina ba sai bakin kasuwa ƴan nama ta nufi wani matashi dake yanka nama yana ware na kudi kudi,ta ce dashi.
"Malam nawa nawa naman naka.
Duban ta yayi ya kuma dubanta ya watsar kamar yaga kashi.
Na ce malam nawa wannan kashin naman............,ke dallah bar wajan nan kar ki kore mun jama'a ke a wannan teɓar jikin naki ina zaki zuba nama yai miki amfani ai sai dai kiyi ta shan ruwa daro daro kina futsarar wa ban da rashin mutunci ina ke ina tambaya ta ki wuce ki bar gurin nan kar kisa nayi kwantai.
Ni kake gayawa haka,ka wai dan na tambayi nawa kashin nama.
Abinda yafi haka ma zan faɗa miki zaki dakan ne?.
Duka ma me zafin tsiya wallahi da saya zan na baka kudin ka a hannu chas amma tun da kai ɗan marasa mutunci ne baka iya magana ba kyauta zaka bada naman ko sisin kwabo babu.
Wallahi ko gyatumar ki albarka taci allakoro bare wata buhu dake idan ma baki matsa kin bani waje ba dokeki zanyi......"Tassss,Tassss.
Me nama yaji saukar mari bai san sanda yayi taga taga zai faɗi yaji an tsayar dashi chas.
Duban inda Duduwa take yayi ya dubi in da shima yake tsaye abin mamakin har yaushe ta tsallako inda yake ta zabga masa mari haka,tambayar da babu amsa ya sake ji an wanka masa mari, da gudu ya zabura zai ruga aka riƙe shi kam kuma babu kowa a inda yake,nan da nan yafara tsorata ya kuma takewa zai ruga wannan karan babu wanda ya riƙe shi amma gudu yake a guri daya ko taku daya bai ƙara ba sai ya rushe da kuka ya tsaya.
Daya tsaya sai kaji an sake wanke shi da mari me gigita mutum nan fa me nama yashiga kwarma Ihu yana gudu a waje daya har mutane suka taro ana ganin abinda ba a taɓa gani ba wasu idan sun zo wajan sunga Duduwa baka sanin lokacin da suke zamewa su bar wajan Duduwan ka ta kwashi Nama yanda take so me nama na kallo yana karɓar mari ba damar magana har tayi nisa aka dena hango ta a wajan wani ke labar tawa mutane wace duduwa kafin ya ƙarasa silifas guda daya babu kowa ya cika wandon sa da iska sai me nama dayake ya faman ruga gudu a waje daya....
"Koda Rabi ta fito daga gidan me unguwa bata zame ko ina ba sai MARABA,inda zai fi mata sauƙin hawa achaɓa ya gangara da ita 'YAN LEMAN,ƙauyen su ta iso daf da ƴan achaɓar.
"Hajiya tafiya ce,"eh nan ƴan leman zaka kai ni nawa zan baka?.
jaka daya ne hajiya,ɗan achaɓan ya furta yana gangaro da mashin din sa inda Rabi ke tsaye,waro ido tayi tace"""
Muttala biyar zan baka nan da ƴan leman din a ƙafa ma muna zuwa yanzun ma dan dai sauri nake yi ne.
Gaskiya ki bada muttala shida in ba haka ba na juya ki latsa wani nasan su sai muttala bakwai zasu kai ki.
To muje ya na iya.
Ɗan achaɓa ya burga mashin ya tashi yace.
"bisimillah.
To Rabi ta haye kan babur tana zama babur na mutuwa.
To ya kuma ya mutu,"wallahi nima abinda nake tunani kenan kika rigani bara na kuma tayarwa nagani.......tashin duniya mashin yaƙi tashi har sauka ɗan achaɓan yayi Rabi na kai ya tura abu yaƙi tashi,ya sake hawa ya jarraba amma fafur babur yace shi sam ba zai fa tashi ba me babur yace.
Hajiya sauka na hau ƴan uwa su tura naga ko zamu dace amma lfy ƙalau yake wallahi,Rabi ta sauko tana in yalala ce kawai ta hau wani tunda suna da yawa,ɗan achaɓa yace dai,"bari mu jarraba.
Abu kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba bugu daya da Rabi ta sauka daga kan babur ya tashi,dauke da murna ɗan achaɓan ya dubi Rabi.
Maza hau mu tafi tunda ya tashi,Rabi ta hau tana dariyar jin dadi tana zama yasake mutuwa🙆♀️,kai Rabi na kai sauran ƴan achaɓan suka taru suna turasu babur dai yace bazai tashi ba daga ƙarshe Rabi ta sauka daga kai bayan sunyi da wani me babur din ciniki tana sauka babur kuwa na tashi ɗan achaɓa yaja babur dinsa ya koma kan layi dayan da sukayi ciniki ya kunno yazo ta haye...........
Shima dai a take ya mutu,kai a wajan Rabi ta hau babur ya kai biyar duk abinda ya faru a na farko shi yake faruwa a na kowa,ƴan a chaɓa suka koma gefe suna gulmar Rabi babu shakka baƙin hali gareta dayawa suka ja mashinan su suka bar wajan ace warsu Rabi masifa ce babba babur ma yaƙi tashi ina kuma mitum gwara kowa ya bar wajan daga Rabi a gun sai jakarta sai raba ido take tana hange hange chan ta hango mota na zuwa.
Hamdallah tayi ta jira har motar ta iso wajan da take ta tsaya,tako yi sa'a ta ƴan lemon din motar zatayi ta cika dam da mutane saura kujerar zaman mutum daya,da murna Rabi ta hau st din gaba ta zauna kwandas ta shima ya hau yaja ƙofa ya rufe me tuƙa mota ya kunna mota dan tafiya.......
""""""INNALILLAHI,kowa ya fuce wuta wuta a ƙasan motar jama'a kowa ya fito.....................
_*By*_
_*Maman Dr @ff@n*_
No comments