Breaking News

DUDUWA 29

 _            _*🧞‍♂️NA DUDU🧞‍♂️*_

          _(cigaban Duduwa)_

~29~

         Da ƙyar da siɗin goshi Dije ta samu ta ƙwaci kanta tayi ɗakin su ya'u da gudu ta banko ƙofar tana kuka me ban tausayi,"wai yau ni malam ya ɗaga hannu da kansa akan kuchakar yarinyar nan ya buge ni tsawon shekara da shekaru ko tsintsiya bai taɓa nuna ni dashi ba sai a yau ya mammake ni da ludayi,"lalai kishiya masifa ce duk ƙanƙantar ta,Dije dake zan chan zuci ya fito fili tana goge hawaye wani na kuma silalowa kan kuncin ta.


       tun bayan da liman ya raraka dije ɗaki ya juyo kan ƴar chakaren sa da sauri yana"sannu sannu ina da ina ta bugar miki tashi muje bayan layi wajan lagwani likita ya duba minki kin ji sannu amarya ta,ƴar chakare ta ƙara narkewa a ƙasa riƙe da cikin ta ta ce


"Ni kam ba inda zani liman sai dai ka kira gwaggon ta zo ta ɗauke ni tunda ita ta bugeni wayyo Allah cikina ƙafata liman ka taimake ni zan mutu"kul da kiran mutuwa ana ƴar chakarr ba yanzu ba kinji amarsu daure ki miƙe ko adafe ne mu ƙarasa ya dudduba ki.

  

    shure shuren ƙafa ƴar chakare ke yi ta kuma cewa.


"wayyo zan......


"dan Allah ki dena kirawota.



to ka kirawo gwaggon tazo ta goyeni ko kuma kai kai goyeni mu je a dubani.


da sauri liman ya miƙe tsaye yana tafe yana.


"bari dai ita dijan ta zo ta goyeki ni ina zan iya keta unguwa dake a hannu ƴar chakare da rawani na akai "Dije ke dije ki buɗe ƙofar nan tun kan na ƙaraso gare ki ko kuma na kuma sassaɓa miki kamanni,liman ya doshi ɗakin su ya'u da dije ke ciki.



Dije na jiyo ihun liman akan ta fito ta goyi ƴar chakare ta kuma rushewa da kuka ta na""


"Oh ni dije na shiga uku a dokeka a hanaka kuka yanzu ni da aka make ake son nazo na goyi munafukar ƴar nan na kai ta har kyamis aduba ta bayan babu uwar da na yi mata to kuwa maga yanda za'ayi na fito na kai ta,sallamar ya"u ce tasa dije buɗe ƙofar da sauri dije ta ƙara fashewa da kuka tana ƙoƙarin shigewa bayan ya"u,da sauri liman yayo kan dije yana"



"wuce maza ki goye ta tunda ke kika jamata duk lalurar dake damunta dije ki wuce nace ki goye ta.



"wai wa za'a goya ne baba?


gyatumar ka ƙarama dije zata goya mukai a duba ta saboda rashin kai irin na gyatumarka ta mammaki ƴar mutane haka kurum.



haba baba ya za'ayi inna ta goyi wannan yarinyar kamar wata ƴar goye.



la'illaha illallahu,ya'u gyatumar taka ce wannan kuma yarinya lalai zamani mai juyi da mutane ni ka duba ido da ido kake gayan haka ya"u zakiyi albarka kuwa.




ina sha Allah zaiyi tunda ba kai ka ɗai ka haifar ba albarka kulum ina saka musu indai akan wannan ne malam kayi duk abinda zakayi wallahi ya'u na rantse da Allah ban yi mata komai ba ta kwanta tana ganin malam ya shigo ta soma ihu wai na bugeta aciki ya'u,dije ta saki kuka me ɗacin rai duban ƴar chakare ya'u yayi yaja ƙwafa ya dubi dije""


inna wuce ɗakin ki ki zauna babu inda zaki kuma babu yarinyar da zaki goya ki kai wani wuri a duba ta indai ina gidan nan.

 


ya'u ya nemi waje ya zauna,liman ya fusata ya nuna ya'u da yatsa ya ce""


to ubana nace sai dije ta goyeta ta kai ta kyamis ni da kai muga me faɗa aji a gidan mara ɗa'a.


shiru ya'u yayiwa liman dije tasa hannu ta goge hawayen ta tayi ɗaki ƴar chakare sai ihu take da ta gama jin duk abinda ya wakan a tsakaninsu tana riƙe da ciki sai ihu take,ihun ya cikawa liman kunne ya rasa yanda zai yi yayi waje ba ajima ba Rabi matar me unguwa ta shigo ta kama ƴar chakare suka fita tare da liman yana taiwa ƴar chakare sannu sannu har suka sha kwana,sai da ya'u ya tabbatar da su liman sun yi nisa da gida tukunna ya miƙe ya nufi ɗakin dije data haɗa hannu da fuska ya ce""



Dan Allah inna ki fita a harkar yarinyar nan duk abinda kika san zai haɗaku to ki barshi kinga bazamu iya jurar irin wannan abun yana wakana a tsakaninku ba baba ba zai taɓa gane makircin ta ba ki dinga kauda kai nasan da ciwo amma kiyi haƙuri inna komai zai zama labari.



kuka dije ta saki ta yayimi gefan rigarta ta goge hawayen ta na.




 "Naji ya'u insha Allahu na fita sabgarta har abada amma yanzu ma bani na shiga ba ita tamin rashin kunya.



na sani inna duk na karance ta ke ce babba kome zai je ya zo ke za'abaiwa laifi kinga hakan babu daɗi ki zuba mata ido duk rashin kunyarta sai kin dubeta kiyi kamar bata wajan.


to ya'u insha Allahu zanyi.


yauwa inna ko sun dawo baba na faɗa kiyi masa shiru kinji zaiyi yabari.



duk zanyi insha Allahu ga abincin ka a madafa.


to inna bari na ɗauka.




Bayan ya'u ya ɗauki abincin sa yaci ya kuma komawa wajan sana'arsa bai jima da fita ba liman suka dawo da ƴar chakare da ƙafarta da ledar tsire fal a hannu da kansa liman ya shimfiɗa mata tabarma ya baje mata ledar tsire sai waƙa take tana ɗaukar ɗai dai tana gutsira a hankali dan dije taji ta gani malam nata ƙwaɗata yana faman yi mata sanuu dije ta fito tayi kamar bata gansu ba girkin dare tashiga hada hadar ɗorawa ran ƴarchakare yasosu ta cika tayi ɓam dan baƙin cikin dije bata kula ta ba.





…………………




Bayan mai gari ya aika burni ɗan uwansa ya sayo madarar jariri ya kawo a ranar ya kaiwa inna da sauran kaya da yawa harda nasawa,Masha Allah Na Dudu ya amshi madara nan da nan yafara sauyawa yaro ya soma ƙiba da kumatu kamar bashi ba ga kulawa da inna ke bashi ko ƙuda bata son ya taɓa na dudu.





*Kuyi haƙuri da wannan insha Allah gobe zamu shiga labari ka'in da na'in ina yinku fan's😘*





_*By*_

_*Maman Dr*_

No comments