DUDUWA 15
""Kee kulu gani nan,a kusa bakida ido ne,"mudi mudi bunsuru na magana mu kam yau tamu ta ƙare daga duka sai ganin jinsi kalla kalla mai gari dan Allah ka ƙaraso kar ya haɗiye ni,ummm,kulu ta diro daga kan gadon tayi waje da gudu tana kwarmawa mudi kira"a guje mudi ya fito daga ɗakin sa na soro yayo cikin gidan da saura kaɗan yarage suyi gware da kulu taja burki ta tsaya tana mai da numfashi dafe da ƙirjin ta.
"Lahiya uwar ɗaki na,me yake faruwa?.
"Bunsuru na gani a ɗaka mudi har magana yake yi, kashiga ka ganewa idanun ka ni dai daga nan sai gidan mu aradun Allah.
Aa,Uwar ɗakina kar kiyi saurin tafiya kin tsaya kin duba da kyau kuwa,ina yallaɓan yake.
Su Duduwa sun tafi dashi tun daran jiya bakaji an kawo amarya ba.
Ina zanji jiya dana kwashi gajiya takalmi na ma ƙarewa dashi na kwana tsabar na gaji ban iya cire shi ba,yanzu dai bari naje na duba inaga firgita kikayi matar mai gari.
Ko ma dai menene babu inda zan koma tunda na samu ƙafata tabar ɗakin wallahi gidan mu na nufa.
Kiyiwa Allah ki tsaya naje na duba karki tafi uwar ɗaki na daga baya mai gari yayi mun faɗa,kin san ku sarakai sai ana adana ku.
Zan chan kake so mudi kaga tafiya ta,kulu tayi hanyar soro ta miƙa hannu zata tura ƙyauran ƙofar gidan kenan aka turo daga waje har ɗan buge hannun kulu akayi,,da baya kulu ta koma da guda tana...
"Mudi gasu nan sun dawo,kulu na shigowa gidan tayi turus haɗe da sakin sallati ta ce"""
"Mee zan gani ni kulu jikar Abashe,dama kai ne a ɗakin mai gari,,,,,"ko kuma ɗan bunsurun da kika faɗa ba,ashe kulu ke ba me rufa mini asiri bace duk halin da zan shiga sai dai ki nemi ki tona mun tooooo..............bakin mai gari ya maƙale shi bai rufe ba,be kuma ƙarasa abinda ya ke son faɗa ba ganin Dije da Adamu sun shigo ɗauke da malam liman a wilbaro fuskar liman ta haɗe da ido da hanci ga leɓan duk sun kumbura duk uban gashin da Dije tayi masa a banza kamar ƙara tashi fuskar take,mai gari ne ya tako a duƙe gemun daya cika masa fuska har ja yake da ƙasa yazo daf da wilbaron da liman ke ciki ya ce.
""Liman kokawa da ƙyanwa kayi ko hatsari kayi,wannan fuska taka da ƙyar wallahi na shaida ka,Dije meyake faru????
A tsorace dije ta ce.
"Gamo yayi yallaɓai jiya kwanan zaune mukayi ni kai na sai da na samu rabo na kaga muƙamuƙina duk a dauje suke............kaji abinda nake faɗa maka yau gashi ka gani da idon ka,wayyo ni kulu na shiga uku malam ka sauwake mun dan Allah ko na huta,waya san a inda namu tsautsayin yake,kuka sosai kulu ta saki sai zagaye tsakar gidan take da taga babu abinda kukan zaiyi mata ta faɗa ɗaki,ƴan tsumokaran kayan ta ta haɗo ta ɗora akai ta fito waje jiki ba ƙwari ta dubi mai gari daya fara fidda ƙwalla tace""
""Ka sallame ni ko kar ka sallaman ni kam na barka har abada, idan mun ɓatawa juna rai a zaman mu to mu yafi junna sai mun haɗu a darissalam idan da rabo,daga mai garin har mudi dasu Dije babu wanda ya tanka sai ido da suka bi kulu dashi har tafita tabar gidan Dije ta ce.
"To ni ma kam bin ta zanyi abinda ya kai ku kuka jajiɓowa kan ku ya saura akan ku duk gashi an sauya muku kamani har mu da muke kusa daku bamu tsira ba neman nakasta mu ake,dan haka ni ma na tafi kuyi jinyar tare iyayena na sona,liman kuka mai gari kuka mudi ma na matsa kwallah haka shima Adamu ya juya yabi gatumarsa malam liman nata ƙoƙarin kiransa da miƙowa adamu hannu ya share yabi bayan Dije,gari yayiwa mai gari zafi gashi babu damar fita bare ya haɗa gungin jama'ah asan me za'ayi an sauya musu kamani ta dole...
-----------A hankali jama'ar gari suka fara fitowa nasu safgar,kowa yana hurumun gabansa daka ga ƙungin jama'a waje ɗaya tofa labari ake na sauyawar mai gari da malam liman ga kuma ganin su Talatu da hansai kusan kullum cika gidajen su yake da ƴan kallo zuwa ganinsu kamar a gidan zoo.
Mai unguwa kuwa sai karansa yake ci babu babbaka gaba ɗaya mulki da isa sun koma hannunsa shi yake cewa ayi yake sawa a bari,har Rabi bai ragawa akan rashin mutunci tunda yana da ƙafa,ya kwashi ƙarya da gaskiya yaje ya zayyanewa duduwa musamman ta ɓangaran me gari abinda bai sani ba duk wani motsi da tashin sa ɗan dunƙule na biye dashi kallonsa Duduwa takeyi kawai kafin burin ta na mallakar mai gari ya cika.
"Yau ma kam tunda ta tashi ta kumbura tayi santim ita a dolle sai Inna taje nema mata aure wajan mai gari gashi inna tace ita babu mai sakata a safgar tunda tana sonshi ta mai dashi abin gudu ga jama'a,idan kinga tasaka hannunta to kin saka an aske uban gashin dakika turawa mai gari a gemun sa ba ƙaramin firgita nayi ba ranar danayi tozali da wannan abu,ya ilahi gashi har ja yake da ƙasa ina bayani,,wannan magana yasa duduwa kiran ƙawayenta,SAILUƁAT da SAISHURAT,suka tattauna akan idan har mai gari ya amice da Auran DUDUWA,za a tattara gashin a kwashe masa shi har abadah,idan ko yayi gardama bai ma fara ganin rikici da tashin hankali ba har garin kanwa da jama'ar ci kinsa,da wannan sharaɗi Duduwa tajewa da inna,inna ta amince zata shige gaba,bayan kwana biyu kuwa suka shirya suka garzaya gidan Ango mai gari😂😂😂😂
_*By*_
_*Maman Dr*_
No comments