DUDUWA 13
_13_
"Hannu liman ya kai cikin hanzari ya rarimi rawanin sa ya mai dashi kansa yana hange hange ko zai ido biyu da wanda yayi maganar wayam yaga babu kowa a cikin ɗakin,ya koma chan ƙarshen katifarsa ya takure kansa yana duban ƙofar dake kallonsa bacci ɓarawo yai awon gaba dashi ko nisa bai yi ba aka kuma wanke shi da mari dama da hagu,,tsabar zafin da liman ya ji kukan ma kasawa yayi ya fara wani irin gurnani shi a dole magana yake son yi,har raɗaɗin ya dishashe,chan wani bacci me ɗan karan daɗi ya kuma ibar sa,ko gama rufe idon bai yi ba aka ƙara masa,da rarrafe ya ƙaraso bakin ƙofar ya miƙa hannu da zumar cire kubar kenan,aka dako shi ta baya ya hantsila dashi da hannun nasa suka daki
bangon ɗaƙin da fuska nan take ya baje a ƙasa yana mai da numfashin wahala,sai da liman yaga ya fara hango turɓar saman ɗakin ya dashe baki yana ihu majina da hawaye suka taru sukayi baje baje a kumatun yana ihu yana hamma da idanuwansa sun kwashe shi sai ya miƙa hannu da sauri ya gwale idanuwan yana kuka da ihu azo a taimake shi kar ya mutu,,daga saman ya sake ji ance.""A haka nan zamu kwana mu da kai yau ba baci har garin Allah ya waye,liman naji haka ya kuma runtuma ihu yana.
"Natuba,nabi Allah kuyi haƙuri kuyi mun rai...........
"Idan baka haɗa leɓan sama da na ƙasa kayi mana shiru ba,fishin mu zai tabbata akan ka me muni,zamu chanja maka kamanni daga siffar bil Adama zuwa shekararran ɗan bun suru wanda a haka zaka zauna har tsawon rayuwarka ba tare da kowa ya shina ba,ƙarshe wani ya kamaka ya danne ya yanka ai sanwa da naman ka.......,liman najin haka ya damƙe bakinsa cikin sauri yana,"""ƙ ƙ ƙ ƙ................
.........lawwali na tsaye ya kasa gaba ya kasa baya sai ma ƙafafuwan sa dake karkarwa yana sakin fitsarin da ɗimin ya taɓa Idirisu dake kusa dashi,cikin faɗa idirisu ya juyo zai balbale lawwali ya hangi abu duƙul na doso inda suke ai ko uffan bai tanka ba ya rarrafa a hankali zai fece,Harun yayi charfa ya damƙo ƙafafuwan duka biyun a firgice Idirisu ya waigo yana.
""Wayyo Uwani ƙafafuwa na""kai Idirisu wai meye haka kamar wani ɗan rarrafe,"Ubanka ya daki hancin uwatar Haruna sakarni na shiga uku.......
Wallahi ban sakin ka tunda ka zagan naga gidan uban wa zaka tafi............haruna ya maƙale a nan sakamakon hango abinda idanuwansa saka gano.
Sai a yanzu lawwali ya dawo daga duniyar firgiciwar da yayi ya kwarma uban ihu haɗe da furta."""
""Aljanin dare jama'a,ko wanne ya fara ƙoƙarin fecewa daga me fitsari sai me zawo da adungure gaba ɗaya suka ɗuru cikin shagwan me shayi daya bari abuɗe dan shan iska ta kansa suka dinga bi suna shigewa ciki da ƙyar ya samu ya miƙe yana zazzaga bala'i yaji haruna ya saki wani danƙareran kuka yana nuna bayan shi,cike da mamaki me shayi ya juyo dan ganin me gardi haruna kewa wannan kuka kamar yaga mutuwa,ai a hankali me shayi yayi ƙasa yana ƙoƙarin shigewa babbar rigar lawwali dake wani irin fusga yana makyarkyata kamar me shirin tada farfaɗiya ɗaki ya ɗauki ihun garada aljani dunƙul kuwa na bakin ƙofar yana ɓalbala musu dariya da guntayen hannunsa har da tafawa da tsale suna ihu da kiraye kirayen iyayen su.
Kusan ko wane gida sun tashi tsabar ihun da suke jiyowa kowa cikin sa ya ɗuru ruwa da fargaba an rasa wanda zai fito waje ya duba lafiya ga ihun na ƙara yawai ta,inna na baci ta farka a furgice ta kuna ƴar fitilar da tasiya ta dolle ta haska gadon ƙarfan Duduwa datake kwana akai,abin mamaki daya saka inna miƙewa zaune ba shiri Duduwa taga babu ita babu dalilin ta a gadon daga katifa sai fulon ta da bargon datake rufa dashi,inna na son fitowa ta duba ko Duduwa na tsakar gida ihun dake tashi a garin na ƙara tsorata ta nan take ina ta tsula fitsarin dolle ta rarimi charbi tana ja tana hawaye da shara majina daga ƙarshe ma rintse idon ta tayi a cewar zuciyar ta abe baɗan na duduwa na nan kusa da ita,murus ɓera ya daki kwanan tuwon da inna ta ajiye,inna ta wage baki tana....
""Ku kuke ganin mu ba mu muke ganinku ba,ni ce kakar ASAMA"U,da ake kira da Duduwa,ni ke kiran ta da wannan sunan saboda Ma'u ita tasha nono ta barwa Rakiya su biyun ga Allah yabani ita Ma'u har tayi aure tasamu albarkar aure garin haihuwa ta rasu shine aka maidawa Duduwa sunan ts,ita ko Rakiya Allahu Akhubar ko ɗakin mijin ban kai ta ba ta rigamu zuwa gidan gaskiya kunga daga ni sai Asama'u ƙarama kunga ai na ci darajar jikalle gashi ni ɗin tsohuwa ce ai mun aikin gafara............,inna na antyo tarihi tana matsa kwallar data cika mata ido,ita a dole mutanan duduwa takewa bayani dan su barta kar siyi mata komai.
Shi ko me unguwa najin ihun ya farka a firgice yana kokawa da kayan jikinsa,nan da nan ya ƙwaɓe babbar rigarsa yasaka ƴar shara da gajeran wando ya dubi inda Rabi take wayam yaga babu Rabi a gun da gudu yayi lokon da durowar su ke ajiye ya iske Rabi maƙale a cikin durowar tayi lamo sai raba ido take yayi ƙasa da murya yadda baza aji shiba ya ce""".
""fito ki bani waje na bake ake nema ba ni ake bulayin nema ruwa a jallo Rabi kiyiwa Allah ki bani maɓoyar nan kar su iso su taddani ,,"Rabi ta ƙanƙame jikin durowa tace.
"hmmmmm hmmmm innnnn hmmmmmm.
Bafa zan gane me kike nufi ba har sai kin bani waje na.
""Ummmm innnnn hmmmm.
me unguwa ya ƙulu ya sake duban Rabi ya ce,""bazaki fito ba wai ,wato kin raina ni kin mai dani shagiri girbau Allah ya kawo Duduwa duk rashin mutuncin dakike mun sai na faɗa mata tunda ni ne jagaba shugaba a cikin gidan nan,Rabi najin sa tayi uwar shegu da me unguwa yagaji da magiyi ya haƙura ya koma kan gado yai tsuru yana tunanin shi ai na hannun daman duduwa ne tunda har tsegumi yake kwasa ya kai mata babu abinda zai sameshi wataƙil ma har ds masu gadinsa a gidan da wannan tunanin me unguwa ya haɗa kai da gwiwa yana jiyo ihun su Haruna dake ɗaga masa hankali...
Ta ɓangaran mai gari kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye ga kulu dake ƙara tsoratashi daya waiga ya waigo si dai yaga wawulon Kulu ta dashe bakin tana kuka wiwi ita mai gari ya ɗauke ta a daran ya mai da ita gidan su bazata iya zama da jinsin da ba a faɗar sunan su ba a zumar kishi musamman dataji ihu,ai alan katafar ƴan kawo amarya duduwa ne suka nufo gidan da tsakar daran nan dama daran jiya tayi mafarkin an ɗaura auran mai gari da Duduwa har masu kawuna uku huɗu sun shigo gidan ƴan kawo amarya yanzu kuwa da Kulu taji ihu ta tabbatar da su ke tafe,data sanar da mai gari yace shi ƙarya ne mafarki ba gaskiya bace sai dayaji ihun nan na tashi hankalin sa gaba ɗaya ya dugun zuma ya tashi ya kasa zaune ya kasa tsaye daya dubi kulu sai yaga kamar ɗaya daga cikin ƴan kawo amarya duduwa ne nan da nan mai gari ya fara zufa,gumi duk ya tsattsafo masa ya janye rawanin kansa da zumar zai goge gumin kenan sai gogo gashin kansa yayi daya shafo shi a hannu har da biyo kan rigarsa cikin hanzari ya tube rawanin gaba ɗaya ya shafa kan yaji gashi dumus a hannu,chan yaji abu na tafiya a saman idon sa ya kai ɗaya hannun da sauri zai bige,"ashe gashin girarsa ne yake gangarowa har da girar aka haɗa aka aske wa mai gari ya saki wata iriyar ƙara ya baje wanwar a ƙasa dafe da girar tasa dukka biyun,."""
Ihun daya cika garin kanwa shi yayi sanadin tashin Dije hankali a tashe tayi ɗakin liman da zuwa ta fara,,,,
"Malam,malam,dije ta shiga bugawa liman ƙofa,liman na riƙe da bakinsa sai uban hawaye ke bin ɗaya bayan ɗaya yana ji Dije na kwara masa kira babu halin magana kai tashin ma ba hali,'Dije najin malam shiru bai amsa ba ta koma ɗakin yara ta tadosu su zo su buɗe ɗakin malam ko lafiya ga ihu daya karaɗe garin ko dai daga ɗakin yake,nan da nan suka shiga kokawar buɗewa da yara kamar wasa aka wankawa Dije mari ta kwashi ƙafafuwan ta ta runtuma a guje ta banko ɗaki yaran suka bita suna ihu ta buɗe,itama tana ɗaki tana nata ihun duk sun firgita sun ruɗe...............
_*By*_
_*Maman Dr*_
No comments