Breaking News

DUDUWA 12

          _12_

"Wannan dalilin yasa dayawan jama'a suka fito ƙofar gida dan shan iska"A chan kuma ƙofar gidan mai gari jama'a sun hallara kowa yayi zukuɗi yana jiran mai gayya mai aikin ya ƙaraso,malam barau ya dubi liman da tun zuwansa yake mis mis da baki ya ce"".


""Allah gafarta malam wai taron me za ayi ne naga imu imu ne a wajan ba sauran jama'a nifa yasin gabana sai dukan 3-3,yake kar SURUN BUHANI nan tazo ta iske mu kwaf ɗaya zatayi damu tunda ba auki garemu ba, kafin liman ya numfasa"sai da ya tofa addu'o'i bila adadin ya shafe dukka jikin sa ya dubi malam barau daya zuba masa ido ya ce""...


"Malam barau ni ma a yanda ka san labarin zaman da za'ayi haka kai tsaye naji shi ban san taƙameman abinda za atattauna a kai ba,batun bugun zuciya kam ba kai ɗaya ba kusan dukkan jama'ar dake nan wajan haka ke faruwa dasu,amma taimako ɗaya da zan iya bamu shi ne ko wane ya tofa FALAƘI DA NASI ya rufe da AYYATUL KURSIYU,,,'insha Allahu babu abinda zai wakana a wajan nan.....


""Allah ya amince..........,gaba ɗaya suka ɗauka da amin,ana cikin karatun mai gari ya fito,fitowar da kowa yayi kasa ƙe yana kallon sa,wato wata iri yar shiga yayo gaba ɗaya ya nannaɗe kansa tun daga wandon jikin sa har rigar sa ya naɗe su ya tattare a saman bujen wandon sa kamar me shirin yin dambe ya nufi kujera ya zauna yana mis mis da bakin sa,hankalin kowa ya dawo kan mai gari ban da me unguwa dake kalle kallen hanya har suka fara tattaunawa aka ƙare da neman shawarar kowa akayi addu'a daga ƙarshe aka shafa taro ya watse kowa ya kama hanyar gidan sa Duduwa shiru bata hallara ba....


_DARE MA HUTAR BAWA_



"DIJE!!!!!!!,"na am malam me kuma zan yi maka yanzu na gama duk shimfiɗar na aje ma charbin da sallayar akan katifar,ina kika aje min sanda ta na duba ban ganta ba,ita ma tana nan a gefan katifar ka daga ɓarin hagu,to ai shikenan yau ba guna zaki kwana ba,,,gaskiya malam ba zan iya ba munsharin ka kaɗai ke hanani barci ga burgima ka dinga makan ƙafa a fuska kamar a filin dambe,to uwar tonan siriri ba cewa nayi ki kwarma tani kowa yaji ina munshari da burgima ba, je ki cikin yaran ki kwana ni na kwan ni kaɗai tunda ni ba mace bace,,ka dai faɗi gaskiya liman da tsoro ko waya ce kaje kiran da mai garin yayi maka duk buguwa da tsima maka jikin da akayi aradu ban kwana a gunka ɗakin yara zan kwan duk abinda ka ibo ya ƙare maka kai kaɗai..


'Yo ya ƙare ɗin mana,ko an ce miki haka nake zaune babu abinda na taka,bari kiji duk faɗin garin nan banga abinda ya isa ya saman ba sai dai kallo aradu.


Au haka ka ce ko.....


Ƙwarai da gaske haka na faɗi.


Allah ya haɗaka da Duduwa muga ƙarshen cika baki.


Amin aminnn ince duduwar banza duduwar wofi.........,""na shiga tara ni Dijee malam duduwar kake zagi.


sai kuma kiyi ni duk kin ishe ni da zanchan banza, zaki zo ɗakin ko kuwa na rufe.



Wallahi babu inda zan zo ka rufe abinka hmmmm haka fa naga ranan ka rin tumo a guje har rawanin ka na faɗuwa......



Dijeee,dijeee hmmmmm ........



      liman ya furta yana mai faɗawa ɗakin sa ya bonko ƙofa har da saƙala kuba ya rufe,liman na shiga ɗakin yaji wani mugun bacci ya ziyarce shi nan da nan yafara kai hamma ba ƙaƙƙautawa a haka ya janyo sallayar ya shinfiɗa ya aje charbin sa ke nan akan sallayar wani bacci me ɗan karan daɗi ya kwashe shi habawa liman na lumshe ido aka wanke shi da mari me zafi ya hantsila kan katifar yana..




""Dijeeee""dijeeee ......aka kuma ƙara masa a karo na biyu,ya miƙe a fusace zai buɗe ƙofar yaji an dawo dashi kan katifar nan da nan ya kwaɓe baki yana.



Wayyo,wayyo dijeee.



"Dijen uwaka liman ka ƙi halin malam,"yau mu da kai shege ka fasa..........aka saukewa liman bulala akai rawanin ya kwance.........




.........A chan ƙofar gida samari duk sun baje suna shan rake lawwali ya juya da zumar jefa raken daya tsotse kenan ya hango abu duƙul na dashe masa baki duk wawulo,raken da lawwali zai zubda shi ya mai da bakinsa da sauri yana taunawa jikin sa na ɓari...........







_*By*_

_*Maman Dr*_

No comments