Breaking News

DUDUWA 10

         _10_

'''Hamshaƙiya Duduwa ta mai da murfin tukunyar ta rufe ta juyo inda Rabi ke zaune,"Amaryar me unguwa ya zaki kawo farfesu babu kwanon da za'a zubawa Bil'Adama rabon su,ko rowar taki ce yau ta diro akan mu gaba ɗaya ne,"Aa wallahi naji baki ce na taho dashi bane shi isa ban haɗo dashi ba,"to yanzu dai na furta ki kawo har da naki kwanon da na me unguwa sai nasu Lamiru da Ɗan habu suma...."Aa duduwa nifa yasin na yafe a rabawa jama'a kowa ya samu wata ƙil idan aka zuba mini ba lallai ya isa kowa ba,"waya faɗa maka ba zai ishi kowa ba yo ma dan wa akayi farfesun ba kai kace

kana biɗar cin naman kasuwa da lemon ɓawo ba,,ƙwarai kuwa anyi haka amma yanzu a bar naman lemon dai nake sha'awa kin san abinka da mara lafiya gaba ɗaya bakin ne duk bubu daɗi musamman da ƙamshin farfesun nan ya cika min ciki dam,sai naji uwa ma naci na gatse har na rage saura,me unguwa ya ƙarashe maganar yana mai sakin murmushin dolle,shiru duduwa tayi bata ƙara cewa ƙala ba har Rabi ta kawo kwani kan ta zube su gaban duduwa,duduwa ta ɗauki kwani guda ɗaya ta ibo romo ludayi goma sha ɗaya ta zuba cikin kwanan ta waigo tabarmar maza tace"""


"Malam bisimillah ga naka rabon ya sauka.


  Malam Sammani yace,""


"Na gode amma da an baiwa wani saboda yau a masallaci wa'azin malam akan, *IN ZAKA SOWA KAN KA ABU TO KASOWA ƊAN UWANKA SHIMA* to naga ranki shi daɗe idan naƙwashi romon nan na sha har ludayi ɗai ɗai har goma sha ɗaya tofa ba lallai sauran masu *KALLABI,DA RAWANI* su samu ba shi isa nayi tawakkali na ƙara da haƙuri kamar yanda malam dai ya faɗa ariƙa yi.....


Hmmmmmm, Sanƙami kake ko Sammani babu wanda ba zai samu rabon sa ba har da kai a ciki,kuma nan ai ba masallaci bane dazaka kawo mana ƙauli da ba'adi muma ma fa karatun Alon nan damu aka buga a chan daular BANATO dake sanssanin manyan malaman junnu duk wanda na kira ya kuma katse mun hanzari na rantse da gemun kakana sai nasa anyi ƙulun,ƙuliƙuita dashi kun fini sanin abinda nake yi ne ko me kuke nufi kazo ka amshi rabon ka kaci kawai kaba masu ɗayi dama kana ɓata mana lokaci kuma ko ɗigo ɗaya kar ka sake ka rage idan ka rage yasin sai ka shanye romo zallah cikin tukunya goma sha tara a daran nan,,,da sauri Mlm sammani ya karɓi kwanon ya kai bakinsa yana salati,kafin ya kai ga ɗora kwanan a bakin sa yayi atishawa tayi hamsin da biyar yana hawaye yana kurɓar romo idonsa ya kaɗa yai jajir harya kureɓe shi gaba ɗaya ya miƙe tsaye zumbur ya koma ya zauna yasake miƙewa ya nufi ƙofa a guje yana kwara Ashariya duduwa ta kwashe da dariya tace.



"Kaga su mlm sammani ashe faɗin Allah a baki ne bai garzawa ciki ba,ai sai ka durfafi masallacin yanzo.



     Cikin kowa ya shiga ƙugi gaban su na faɗuwa duduwa ta juya ɓarin mata tace.

       


""Ta kan layi ta iso,gadan gadan Salame ta nufo duduwa ta amshi nata romon ta kurɓeshi lokaci ɗaya irin abin nan wai ita dauriya,bata dauki daƙiƙa ɗaya zuwa biyu ba Salame tayi wurgi da gyale da takalmin ta chan gefe ta wage bakin ta tayi kan sauran matan tana faɗin"""



"Ku yiwa Allah ku gano mun da kwai haƙora ko kuwa duk na haɗa na haɗiye dasu,sai kuka tayi nan tayi chan taga dai babu sarki sai Allah ta ruga waje da gudu tana haƙori naaa jama'a,,,,,,ashe ƙofar gidan cike yake da jama'a kowa yazo tarbar ɗan uwansa da malam sammani ya keto shima tini yaransa suka auna gida dashi a guje aka shiga bashi taimakon gaggawa kusan ɗan ƙaramin hauka yayi yana zabura ana kamoshi,haka Salame ma na wargatsowa wajan ƴan gidan su suka jata tana haƙoran......,ɗaya bayan ɗaya suka dinga fitowa jama'a na jan nasu suna barin wajan har suka ƙare gari ya ɗauka gaba ɗaya nan da nan sahu ya ɗauke daga ko wace unguwa da saƙo har inna taji abinda ke wakana.

       Ko da duduwan ka ta waigo kan me unguwa dake kuka kashirɓan da sallati yatasa naman a gaba sai risga kuka yake dan shi yasamu muƙami an haɗashi da tsoka manya manya har guda biyar,ya rarimi tsoka uku a haɗe ya danna a baka,abin mamaki sai ga me unguwa na tauna nama yana lashe baki, ashe shi ko tashin tsedigun bai jiba har yaci nama ya ƙoshi ya fara kwara godiya yana kirarin ban girma wa duduwatun har yasa ka duduwa dariya ta dubi Rabi da bakin nan ya ƙara hauwa tana tsugune.

"Amaryar me unguwa ga wannnan,duduwa ta tura mata tukunyar nama,""ki tsami nama biyu kachal ki ɗan ɗana ladan ganin ido sauran kuma ki baiwa su lamiru da ɗan habu saura ki haɗa ki cinye kiga aikin banza akan ki,ke kar kiji tsoro fa wannan dahuwar taki ce bata dangin Ashhritu ba ki bararraje ki kwashi nama da romo kin ji.



To to mun gode Allah ya biya ya ƙara nisan kiwo......



""kut wa ziyi nisan kiwon,ni kike nufi ko ƙa ƙa amaryar me unguwa?



Nisan ƙwana nake nufi bakina ne yayi tuntuɓan harshe.



Allah ya soki tuntuɓan harshe kika yi dakin gane shayi ruwa ne,Bance kuma ki mun godiya ba,sannan kar na kuma ji kinwa me unguwa maganar da zata ɓata masa rai ki dinga lallaɓashi kamar ɗanyan ƙwai kina masa duk abinda yake so har dasu lamiru tun da ke kika ƙula tsiyar dakika kori gyatumar su yanzu kuma ki dawo kan su ,ahir wallahi idan na dawo naji labari mar daɗi hmmmm ko da yake ina daga gida ina kallon duk kitimur murar da zaki ƙulla me unguwa ni nayi nan,duduwa tayi hanyar da zata kai ta waje cikin sauri me unguwa yace""".



"Hamshaƙiya a sauka lafiya ya dallawa Rabi harara datayi laɓo tana duban sa babu bakin magana.



..............


       


""Zaune Talatu ke a tsakar gidan su ta duƙufa sai tsife gashin kan ta take daya taru ya cika har kusan kafaɗar ta dayake innar ta ba fulatana ce usul haka ma baffan ta,gama tsefe kitson daya saura kenan taji sauti daga gefan ta ana.



"eh ita zakayi wa sol sol din ko silin gashi ɗaya kar ka kus kura ka bari ya saura ka haɗa da girar dukka biyun ki aske su sannan ka taho da it..........talatu bata jira jin ƙarshen zan chan ba ta ƙwasa a guje saura taku ɗaya ta shige ɗakin innar ta,taji anyi sama da ita bata tsinci kanta a ko ina ba sai a wata _*HAMSHAƘIYAR*_ fadda wace ke cike da wasu irin halutu mara sa ƙyan gani talatu dai na cikin wani keji da yayi kama da tafin hannun mutum ƙato nan da nan aka sake jefo abu cikin inda talatu ke takure tana kuka jin maganar datayi yasa tayi saurin ɗagowa tana.


"Hansai ke ce kuwa?



    "Ni ce talatu kema kawo kin aka yi.????????????





_*By*_

_*Maman Dr @ff@n*_

No comments