Breaking News

ZAN FASA KWAI 2


ZAN FASA KWAI*



              *NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*



_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_



                *Page 2*



*_________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


*________________________________*




..Hawaye ya tararowa izzatu Jin abinda hajiya Mama ke Fadi wata zuciya ta kuleta taji kamar ta tashi ta rufe hajiyar da duka sai dai Babu hali hajiyar zaune take da kuturinta.


"Kukan banza ne kike kukan wofi. Yanzu Nan daga gidan saminu nake Ina shiga yara suka taho suna min oyoyo abin farin ciki duk inda na waiga Yan dugwi dugwi ne ke hawa da sauka ajikina  shi wannan haka zai lalace akan ki ba zaiyo aure ba ? To maza ki Kira min shi kice Ina jiranshi...


Ta wurgowa hajiyar harara kafin ta bude Baki cikin gadara da izza ta fara magana


"Hakan da kikayi yayi kyau hajiya  ku sama mishi mafitar da zata bulle dashi don nagaji Nima magana ce kawai banyi ba to tunda har Anzo inda Kika gaji hajiya zanso ayau koma yanzu ki tsinke igiyoyin aurena sai ki kawo mishi wadda zata Rika haihuwa duk wata .......


Hajiyar ta dago Mata hannu "kar ki sake ki zageni don na Fadi gaskiya.....

"Ba Zan zageki ba hajiya Amma Nima ba Zan yarda ki fada min maganar da zata dameni ba kija bakin Ni Kuma Zan fassara Miki kowane kalar ciwo Zan fada Miki kalar maganin tunda na kula shekawa jaki shayi aikin banza ne ba iya Sha zaiyi ba....


"Ki Fadi komai damar kice Amma na rantse Miki sai an kawo wata mace agidan Nan wadda zata haifa Mana yara wallahi na gaji da sai dai kici ki kasayar


"Ai hajiya Ni tuni na gano kece Baki gano ba kice Rabon a bankado abinda zai saka zuciya tashi Baki taba tambayar ko shi Dan naki ne ke da matasala ba sai dai Ni kuke kallo? To za ayi duk yadda kike so tunda watan da za ayi magana ya Kama wallahi za ayi magana 


Don haka yanzu sai kiyi hakuri baya gari  Yana can kasar waje neman lafiyar da zata bashi Yan dagwai dagwai din da kike magana idan ya dawo sai kizo kuyi maganar kafin lokacin Ni na Dade agidan mu tunda nayi kawaici nayi hakuri ba ku San nayi ba  to Ak ya dawo Ni kuma ya sallame Ni


Hajiyar tayi shiru tana tauna maganar izzatu kar dai matsalar daga AK din ne na Rashin haihuwar? Karfa allura ta tono garma   Kai Bata zaton hakan Kuma ko daga gareshi ne ai akwai magani sai agwada.


Da haka hajiyar ta taso inda talai tayi Mata rakiya har wurin motar ta suka tafi ita Kuma ta juyo inda Kuma izzatu tace dawa Allah ya hadata ba da talai ba?


"Kinje kun zageni ke da hajiya to in zata burgeni Mata hudu ya kamata ta aurowa ak haihuwa Kuma sun Dade basu haife mishi singa da kasuwar kurmi ba 

Haka tayi ta sababi tamkar zata aro Baki ta hada da nata talai dai ta wuce daki ta barta 


Kwana biyu tana cikin takaici da bakin cikin da hajiya Mama ta guma Mata inda take ta jiran zuwan me gidan don ayi ta ta Kare Wai ramamme ya zagi maye


Ya Kira wayarta yake sanar da ita kanwar shi asma,u ta haihu har gobe ake suna hajiya Mama ta kirashi ta sanar dashi inda ya bukaci ta dauki kudi dubu hamsin ta kaiwa asmau kudin aski

"Gaskiya ba zanje ba ak sai dai na tura talai ko harira Amma Ni dangin ku nayi wuri na aje su gaskiya saboda nagane basa kaunata........


"Babu komai tunda har Kika iya fada min kinyi wuri kin aje dangi na na gode.......

Dit ya tsinke wayar inda Kuma taji lallai Bata kyauta ba kamata yayi ta amsa mishi da to in yaso sai ta tura wani kawai don haka sai ta Kira wayar tana bashi hakuri cikin kissa da kisisuna har tana fadin tayi kuskure yayi hakuri da haka suka aje wayar t


Washe gari ta nufi gidan Asma u inda ta tabbatar ba zasu kwashe da marar arzikk ba musamman dangin shi dake da burin yada Mata bakar magana to yau Suma zata nuna musu uwar su ma dai dai take da ita bare su kanan shegu 


Da haka ta fice ta iso gidan sunan Wanda ya ciki ya batse da Yan uwa da abokan arziki ta fito mota tana shakar iska dai dai inda ta hade fuska don kar su Raina ta.......

No comments