Breaking News

ZAN FASA KWAI 17

 *ZAN FASA KWAI*

                   *page 17*

......... Izzatu ta dubi mero cikin Jin haushi da takaici . Mero ta dubeta yadda take Brest feeding din yarinyar tamkar itace asalin uwar ta ta gaskiya  


"Uhum kinganki kamar dai ace da gaske kinji yadda akeji sai kokarin feeding ya akayi ma maman yazo? "Ba damuwar ki bace Ni bansan haka kike ba mero da ban hada tafiya ta dake ba Ina amfanin tafiya da matsiyaci? 


"Na ma fi da haka matukar kikce Zaki dawo min da bara bana akan hakki na don haka tashi ki dauko min in wuce me motar da na siya ya isheni da na kawo mishi kudin shi 


Izzatu ta Mike tana Saba fulani akafada tana fadin Banga amfanin tarayya dake ba tunda Baki da mutunci

Ta shige daki ta rubuto check na milyon biyar ta Miko Mata 

"Sai abi wani sarkin ba na garin mu ba 

Mero ta dubeta tana kallon ceck din da take Miko Mata

"Ai bamuyi dake Zaki bani takarda banki ba cash kikace Zaki don haka koma ki dauko min kudi na daidai.

 "Banda su ajiye sai dai kije banki ki karba ta fada tana cillo Mata ceck din afuskar ta


Mero ta dauki cack din tana duba inda tayi arba da rubutun milyon biyar

Ta dubeta 

"Ya Naga kin rubuta min milyon biyar amaimakon goma?


"Biyar din Naga damar Baki don ko ke Kika yi cikin Kika haife iyakar ta kenan


Mero ta Mike tsaye tana kwabe gyalenta ta na cin damara a kugun ta

"Bari kiji in fada Miki izzatu bafiki iskanci don ni har takardar shaida sai da na Kama don haka bini sannu ko  yanzu in fasa kwai rubuto min cikon kudina in wuce in ko      Kuma yanzu in iske Kabir mashi in fasa mishi Kwan kigani idan Baki kwana gidan ku ba 


Da gaske kuwa ta Kada hantar cikin izzatu inda har ta rubuto mata cikon kudin ta tabata . "Ai kuwa godiya ma ya kamata in Miki don kuwa kin yi min silar farin cikin da ba Zan iya manta shi ba na gode sosai Allah ya Kara daukaka


"To ameen in da gaske kike in ma ba gaske ba ne Allah ya biye bakinki Nima na gode  da samun abinda ban taba zaton samu ba sai gani na biyu.....


"Bana bukatar ganin ki a gidana don Zaki iya Zama barazana ga Rayuwa ta mu hadu Nan mu Rabu Nan 

Sister mero tayi murmushi ta fice inda ta shige mota ta nufi banki don ta fito da kudi ta biya me mota kudin shi.


Fitar sister mero ya bawa izzatu damar kamo bakin zaren wani mugun qulli da tayi nufin zargawa mero

Da sauri ta jawo wayar ta ta Kira wani Dan ta Adda da ta sani Wanda ya taba yiwa wata kawarta aiki har ta zarga nata mugun qullin

Don haka ta Kira wayar gambo mafiyas Wanda ya kware a iya Sara suka da ta addsnci


Kara biyu gambo mafiyas ya daga "Allah ya taimaki hajjyata ta samu ne? Kwarai kuwa gambo maza kazo Ina son ganinka....


"An gama hajiya dama Babu komai ahannu na..........

"To maza garzayo kasamu kudi yanzu


Minti Sha biyar ya iso inda take fada mishi abinda take so yayi Mata

"Ka Gane ko gambo wata ce nake so ka bi min bayanta zuwa first Bank zata fiddo wasu manyan kudi shine nake son ka karbo min su ka dawo min dasu zaka ganta cikin mota 206 jar kala me lambar katsina yi maza gambo ka karbo min kudin Nan kar ka yarda asamu akasi ko sabani.........


"Babu kuskure acikin aikina hajiya Ina me tabbatar Miki da awa uku tayi yawa kisaka Ranki inuwa kudin ki sun dawo Miki sun gama 

Ya fice Yana fiyto izzatu ta zauna tana dariyar mugunta 

"Uhum mero kenan yaro yaro ne yaro Bai San wuta ba sai  ya taka mero kinci karya kin kwana da yunwa


Gambo mafiyas ya iso bakin ya labe a gefe Yana kallon mutane me SHIGA da me fita ba inda ya hango motar sister mero wadda aka kwatanta mishi Sai ya soma dakon jiran fitowar mero


Mero da ta gabatar da cek din da zata fitar su kansu sun girgiza Anna da suka duba asusun izzatu sai Basuyi mamaki ba atake suka Bata takardar da zata cike ta cike aka fitar Mata da kudin duka sai ta raba su ta saka milyon biyar cikin asusun ta ta fito da milyon biyar don taje ta biya bashi sau Kuma ta aje don bukatu


Ta SHIGA motar ta ta nufi gida don ta Kira me mota yazo gida ya amshi kudin shi saboda zai fi sirri 

Sai dai wani Al amari dake Shirin faruwa ya gigita sister mero inda wata mota ta Sha gabanta cikin azama ta taka burki don kadan ya rage ta banki motar da ta Sha gabanta


Atake gambo mafiyas ya fito ya na bude motar mero Yana kanga Mata bindiga agoshi Yana tambayar ta kudi

Bataja ba ta jawo buhun kudin ta Miko  mishi ya amsa ya koma motar sukaja  motar aguje suka bacewa ganinta inda mero take sauke ajiyar zuciya ta iso gida tana tunanin waye ya San zataje banki? Babu ko shakka izzatu na da hannu akan wannan abin da akayi Mata koma ita ta turo Mata bakaken mabiya sai Kuma ta tuna da yadda izzatun taso yi Mata dungu akan kudinta sai kawai ta gano mugun kulli ne izzatu ta kullo Mata inda Kuma wata zuciya ke Bata shawarar tashi kije kuyi ta ta Kare Babu Wanda yasan zakije banki sai ita to komai zai iya faruwa


Aikuwa ta fice zuwa gidan izzatu inda ta badda sawu da saka nikabi ta tari napep ya kawota kofar gidan izzatu inda Kuma cikin sa a ta ga motar da tayi Mata fashi ta faka har katon basamuden da ya yi Mata atakin da bindiga ya fito Yana rike da buhun kudinta inda ta tabbatar dai izzatu ce me alhakin yi Mata hakan, to yanzu meye abin yi? Anya kuwa idan tace SHIGA zatayi gidan izzatu ba zata saka katon ya illatata ba????............

No comments