Breaking News

ZAN FASA KWAI 13

       


           *Page 13*

......Sister mero ta zakuda tamkar wadda kunama ta sakarwa harbi jin izzatu na ambato Mata milyon goma

"Banji me kikace ba izzatu

"Yadda kikaji hakan nake nufi milyon goma na ce Zan Baki idan har aikinki ya tafi daidai.....

"Wane irin aikine zanyi Miki ki bani wannan kudin? Don Allah karki yaudare Ni izzatu ko cikin mafarki ban taba ganin milyon goma ba ......

"Zaki gansu ido biyu harma su zamo naki idan kinyi nasarar kammala aikin ki Babu kuskure ko sabani........

"To naji wane irin aikine kike ta fada haka? Fada min don Allah tun zuciya ta Bata buga ba.


Izzatu ta dubeta tayi shiru kafin tace

"So nake mu hada wata kwangila dake kwangilar da zata danka Miki milyon goma ahannu.....


"Wace irin kwangila Ni ki fito amutum kiyi min magana ba alaye da kwane kwane ba.


"Da ko Diya nake so ki samo min acikin karbar haihuwar da kike Ni Kuma Zan sanar inada ciki Wanda Dan da Zaki kawo min shine Zan batar da hankalin mutane Kan cewa nice na haifa.........


"Dakata Allah idan na fahimce ki wata ta dauki cikin ta haife sai in dauko in kawo Miki?

"Hakan nake nufi.

"To tashi ki Kai kudin ki gaban da Kika San fin dubu zasu yi Miki Ni dai Kam albarka ban siyar ba.

"Haba wannan ma ai Rainin hankali ne da son ki wulakanta min aiki kija akore Ni

Haka kawai wata zatayi wahalar daukar ciki da rainon shi ta Kuma ketare hadarin na kuda ta haifa saboda son zuciya sai in sato in kawo Miki don Allah meye sunana idan nayi Miki hakan? Yaya zakiji idan ke akayiwa hakan? To mu rufe wannan maganar muyi wata 


Izzatu ta dubeta asheke

"Dama fa ALHERI bai Faye karbar bakin mutum ba Amma ki sani kudin da kike kokarin yiwa arziki kullin da zai tarwatse har ki mutu ba Zaki taba mallakar su ba tunda Kuma ba Zaki iya ba zanje birnin gaba inda za ayi min 

Tana gama fadin haka ta Suri Jakarta  ta fice tamkar kububuwa inda sister mero ta bita da kallo inda Kuma take Jin wani lissafin me kama da na dokin Rano ya sauko Mata akan bukatunta na son ta mallaki mota da son ta siyi gida  Amma ta Yaya zata mallaki gidan da motar alhalin albashin ta ma kafin ta karbe shi bukatu sun targada shi? Amma Kuma ta Yaya zata iya wannan aiki me matukar hadari akanta da aikinta? Sannan Kuma Yaya zatayi da hakki da alhakin wadda zata sibarewa Dan? 


Ance mugun tunani shi ke abotakar shaidan sai sister mero ta ture wancen kalubalen ta hango bukatar ta inda tayi na am da aikin da zai mallaka Mata milyon goma wannan ai shine yiwa arziki kulli yaushe ne? Yaushe ne zata hada Kan wadan can kudin a wannan Nigeriar me jiya tafi yau gobe tafi jibi.


Don haka tana tashi aiki sai ta Kira wayar izzatu ta nemi kwatancen gidanta......


"Me ye na neman kwatancen gidana Kuma? In ma shawara Kika sauya kin makara don Ni magana guda nake bana maimaici.....

"Yi hakuri fada min inzo muyi magana

Izzatu taja tsaki kafin ta Bata kwatancen 

Mero ta iso gidan Wanda ita da kanta ta San lallai Dole izzatu ke rudewa da son samun mafita


Ta dubeta awatse

"Meye Kuma na biyoni gida?

"Kiyi hakuri shawara nayi Naga Bai kamata ace kizo da bukatar ki wurina ba in watsa Miki kasa a ido  haka na yarda sai mu tsara yadda abun zai kasance.


"Me yasa shi matsiyaci ko ya shiga tandun Mai yake fitowa kandas?

Yaushe ne mero Zaki Tara milyon goma?

Meye abin wuya acikin aikina?

Wannan magana tayiwa mero zafi Amma ta hadiye


"Ni dai yanzu muyi magana Yaya abin zai kasance?

"Zan sanar da Kabir nazo Asibiti ance inada ciki Zan dauki acting din masu ciki ke Kuma ba ki Nan da wata bakwai ko takwas kiyi kokarin kawo min abinda yasamu namiji ko mace duk Wanda ya samu Ina so 


"To shikenan zanyi kokarin hakan in Sha Allah sai dai maganar kudin Zaki fara bani wani Abu ne kafin cikar aikin ?


"Kare ya cijeni ne mero da zan Baki kudi Baki gama aiki ba?

Ranar da duk Kika gama aikin ki Ina me tabbatar Miki da ko minti ba za a Kara ba Zan biya ki kudin ki cash 


Da haka sukayi sallama da mero ta fice daga gidan inda Kuma a wannan Rana lamarin ya soma Wanda ya kunshi wani KWAI da fasuwar shi zai tafi da Ruhin Al umma da yawa.


Kabir ya dawo inda izzatu ke sanar dashi taje Asibiti an sanar da ita cikine da ita inda yayi murna tamkar ya mayar da ita cikin shi  inda ita Kuma ta soma fito da salo kala kala inda Kuma izzatu ke baza izza inda Kuma akayi sa a Kabir Bai Faye bawa uwarshi muhimmanci ba inda izzatu ta Kara baza komar wulakanta uwar Kabir din wadda Allah ya zubawa tsananin hakuri da alkunya inda a yau ta nuko gari tundaga birnin Zaria ta iso gidan Dan nata don ta ga shi saboda shi dai yakan iya share shekara Bai lekota ba bare ya agaza Mata duk kudin shi da shaharar shi Bai bada Kai ga lamarin mahaifiyar shi ba inda Ni Kam gidan iko nace anyi asara kuwa indai haka ne...........

No comments