Breaking News

ZAN FASA KWAI 12


 *ZAN FASA KWAI*

                    *Page 12*

.........Ta faka motar me kololuwar daraja a farfajiyar Asibitin national hospital dake babban birnin tarayya Abuja inda ta fito fuskarta sanye da Derk spes ta soma takawa sannu ahankali tamkar me tausayin kasa hannunta sabe da jakar LV kafar ta sanye da takalmin LV mahadin jakar sai wani matsiyacin leshe Wanda ya lashe kudi ba kadan ba kamshin turaren ta ya bulale wurin ta kara daukar kanta yayin da ta ga wasu manyan Mata suna binta da kallo don gaskiyar magana shigarta Babu karya don ta samu Kabir mashi yadda take so Kuma ya rike Mata Kan macijin inda har take Jin kanta ame jinin arziki 

Ta iso ofis din sister mero wadda aiki yayiwa sauki suka gaisa inda meron ke kallon ta cikin Sha awa 


"Jiya kin Kira bana Asibiti naje gwarunfa duba wata abokiyar aikina da bataji Dadi ba Ina fatan dai ba kwayar pills din da Kika Saba karba Zaki karba don gaskiya lokaci yayi da ya kamata ace kin haihu ai kin Sha Miya haka Nan,


"Uhum mero ai ba Zan kuma yarda insha wani Abu yanzu da sunan Hana daukar ciki don nayi nadama ba kadan ba......


"Gara dai Kam don abin in ya kazanta Babu kyau. To yanzu me za ayi Miki?

Ta sauke ajiyar zuciya


"Mero na rabu da mijina sanadin Rashin haihuwa inda ayanzu nayi wani auren Wanda bana fatan sake gamuwa da wani tarnakin irin na gidan AK shine nake son samun mafita daga gareki.....

Mero ta tareta 

"Kin samu matsala ne halan?

"Na samu matsala kuwa gagaruma wadda silar Shan maganin Hana daukar ciki ya haifar min har na samu bakin sakamakon ba Zan haihu ba shine nake gudun haduwa da irin waccan matsalar ta gidan AK shine nake so ki taimakeni da mafita.


Sister mero ta sauke ajiyar zuciya

"Gaskiya izzatu Babu wani taimakon da Zan iya yi Miki illa ki rungumi kaddara Kuma hakan ya zamo izna da Jan kunne gareki da masu irin abinda kikayi

Shi Allah ba ayi mishi Dole ana yin tsari Amma sai an fara haihuwa anga yadda haihuwar ta faro  misali yinta Kai da Kai ko Kuma inke da mijinki zaku iya haifar me cutar sikila idan kunyi tsari ba laifi bane don ku hutar da yaran daga wahala Amma da yawan ku Kuna SHIGA hurumin Ubangiji da son kuci gyaran wahayi........


"Kinga mero ban baro gida don inzo kiyi min wa azi ba in wa azi nake sonji zanje ne in siyi kaset ko in bude Sunnah TV ban kumayo wanka don inzo ki shaki kamshin turarena ba, A a nayo kwalliya ne don ina so ta biyani kudin sabulu......


"To naji hajiya izzatu me kike so nayi Miki yanzu?

"Shine abinda ya kamata kiyi ba Wai ki saki baki kina neman shiga rigar malunta ba.

"Ina so ne na mallaki Da ko Diya ta yadda Zan fita daga matsalar bana haihuwa shine kawai nake so ki taimakeni


"Wannan me sauki ne inaga gidan marayu kawai ya kamata kije ki darzo duk kalar Wanda yayi Miki mace ko namiji sai kin zaba....


"Idan naje gidan marayu na dauko ai kowa yasan ba nawa bane Kuma bana son na gidan marayu gaskiya Kuma ai kowa zai kalle shi da sanin asalin sa,


"To yanzu ya kike so ayi ?

"Mijina na yanzu baisan bana haihuwa ba shiyasa nake so yin kauda bara da hankalin shi abinda nake so mero ke Nike so muyi magana ta fahimta don Zan biyaki kudi tundaga naira milyan daya zuwa goma akan bukatata idan har Zaki iya shiyasa ma na taho gareki don nasan aikin da Zan Baki akwai mutane fin dubu da in na Kai  musu da gudu zasuyi min


Sister mero da taji yawan kudin da izzatu ta ambato zata Bata akan aikin da bataji komeye ba sai ta rude ta kidime  har take Jin ita ko ma Arayuwar ta ta taba Kama milyon guda ahannun ta? Yau sai ace za ta samu goma me take jira?..............

No comments