Breaking News

TSANGAYAR MALAM 9-10

 _*‍👳‍♂️👳‍♂️👳‍♂️TSANGAYAR👳‍♂️👳‍♂️👳‍♂️*_

                  _(Malam)_

            _Maman Dr_

_*Haɗaka Writer's Asso, 

               9️⃣-1️⃣0️⃣

'Ya soma kiran "Malam!!,malam!!"ƴaƴan hanji na za su fato malam inna uwaila kizo dan Allah kar na wula ku taimake ni kar na mutu lokaci na bai iso ba, wayyo ciki na kashiiii taho taho ko ɗan marayan Allah zai yi ya huta wayyo Allah na malam Innalillahi, ku agaza ku taimake ni malam, wayyo Allah malam ina ka nausa ka nufa,ɗan malam ya cigaba da jan jiki yana ƙoƙarin fitowa daga ɗakin da gudu inna uwaila ta ƙaraso ƙofar ɗakin hankalin ta atashe ta shiga cewa.

"Na shiga uku Attahiru mutuwa kayi?

    "Wallahi da rai na inna,mutuwar nan tukunna ba yanzu zanyi ta ba, a dai taimake ni a miƙa ni gidan magani ciki na inna kamar zai fashe amai nake ji ga kashi ina ya tsaya ya tokare mun.........wayyo Allah na.

"Subhanallahi,ai ido na saka maka tunda kai ba a saka ka a hana ka gashi nan ka haɗawa kanka masifa ka gafza wake da wake ga tsami ai dole ka shiga wani ɗan yanayi Attahiru ka riƙa dubawa da irin cimar da kake ɗiba ba komai ake samu a dinga a fawa a ciki ba,uwaila ta ƙare batun da buɗe kofin kunun tsamiyar ta sake buɗe na wake da shinkafa chan ta hangi ledar kulele ta dubi ɗan malam ta ce.


"Ta shin hankali kaf ka shanye kunun ka cinye ƙosan attahiru har da kulele, lalai ka haɗawa kan ka gwarama ka tarowa kan ka mach kwanta kawai ka ƙara sa lokaci ka ke jira.


Ido a waje ɗan malam ya dubi uwaila da sauri ya ce"


"in ƙara sa ina?


"barzawo mana in da kowa zai tafi.


Uwaila ta bawa ɗan malam amsa a taƙaice cikin hanzari ɗan malam ya fara ƙoƙarin moƙewa zaune yana kuka kamar wani ɗan akuya.


     "A'a, "ina kuma zaka tashi ka je kai da kake jiran lokaci attahiru ka soma istigifari tun sa'i ya cimaka.


"Ɓeyeeeeee Wayyo malam ka zo ka taimake ni ko rubutu ne ka jiƙa ka bani,na rantse da Allah ko sallah banyi ba gashi na sha ruwa bare in wuce da azumi na abaki.


'tirƙashi yau attahiru da shan rubutu ni uwaila wallahi tausayi kake bani ko sallah bakayi ba zaka wuc...........,na shiga uku uwaila ki ɗauke ni ki ɗaura mun alwalar nan ko akwance ne na samu na jata.


Dani da kai wa zai kwashi wani sam bazan iya ba aradu.


To ki goyani ki kai ni rariya nayi achan ɗin.


Shima Allah bazan iya ba ka jira malam idan yazo baka tafin ba sai ya kwashe ka ya kai ka .


Innalillahi jama'atul musilmi,sai ihu da jan ciki yake yana ƙoƙarin fitowa uwaila na ta maimaita masa kalmar shahada ta na"


"Ka riƙa yi da neman gafara a haka zakaji ka a inda ba adawowa,ana haka malam ya shigo gidan jin ihu da kururuwar ɗan malam ya faɗa ɗakin da sauri yana tambaya?


"To lafiya uwala.


'ina fa lafiya malam attahiru sa'i ya matso.


   ai malam baiyi aune ba sai jin ƙafarsa yai an ƙanƙame ta,an riƙe gama ana kalmar shahada da ƙarfi,jan ƙafar malam yayi ya ce"


Kai sakar muni ƙafa waya gaya maka in lakaci yayi ƙafafuwa ake kamowa.


   "Malam kayiwa Allah da Annabi,"S'A'W,uwaila da malam suka haɗa baki suka faɗa atare,ɗan malam ya ci gaba.


"karka bari na wuce dan girman iyaye da kakanni ka taimake ni yanda Allah ya taimake ka malam.


"Ina,"wane ni attahiru nima jiran ta nake kayi haƙuri kawai ka tafi.


Wayyo malam to kayi mun rubutu na sha na miƙe.



Yau kuma,malam ya dubi uwalai,"uwaila kin ji ikon Allah.


Hmmm babu mamaki ga wanda lokacin sa ya tunkaro malam ai duk cikin bankwana ne.



"Allah sarki attahiru Allah ya bada sa'ar tafiya ga shi an kwashi haƙƙin jama'a.



",Malam karka barni na tafi malam innalillahi,sai kuka da sharɓe sharɓen majina da dariya ta tahowa uwaila sai ta kau da kai ko tasaka hannayenta a fuska ta fara share hawaye tana murza ido kamar me yin kukan gaske hankalin ɗan malam ya tashi har cikin nasa ya tsagaita ciwon bai ma sani ya tsagai ta ba tsabar tsoron mutuwa,kuka yai kuka gunji maza na tashi chan dai ɗan malam ya fara""


"Allah ka yafe mun na zalinci bala na daki kamisu na babaka gonar hakimi ta albasa.............



"La'ilaha ilallahu,attahiru abun naka har da su hakimi.


"wayyo malam duk abunda ya faru jiya gidan su Nafi'u na rantse maka da Allah ni ɗin nan ni ne sila da taimakon ɗan Abu.


        "Waje malam ya samu ya zauna bakin sa a buɗe uwaila kuwa sai salallami take tana.



"Mun shigesu malam kaji wani ɗunbun zunuban daya kwasa, anya kuwa attahiru zaka shiga Aljanna?,ko daya yake ta mai rabo ce Allah ya yafe mana baki ɗaya.


Ajiyar zuciya malam ya aje ya dubi ɗan malam dake hawaye kashirɓan ya ce.


"Anya anya Attahiru alhakin mutane zai barka yanzu duk gwagwarmayar da aka sha jiya kai da kanka kai ne sila,ya ilahi ka dube ni ka shirya yaron nan kayi maza maza ka tashi mu tafi gaban hakimi achan duk ka faɗi abinda ka ƙula ko jama'ah za su ji su dena ƙyamar yaron nana Nafi'u yanzu a masallaci sai da na tausaya masa wallahi shi kaɗai yayi sallah kowa guduwa yayi daya ganshi a masallaci sai a waje aka taru aka ja sallar bawan Allah ya tafi babu wanda ya kulashi ashe kai ne silar komai attahiru,amma kam ka ɗuma as........,"A'a,a'a malam karka yi masa baki ya kuma shiga wani yanayin da yafi wannan Addu'ar ita ce makama.



"Hmmm da wannan yaron uwaila gwara bab........'dan Allah malam karka faɗi haka ku fa kukewa jamma',ah wa'azi akan mugan furucin da yake lalata tarbiyar yara sai kuma kai kayi,dan Allah ka haƙurƙurtar da zuciyar ka duk wannan abun dayake faruwa jarabawa ce kuma muna fatan Allah ya bamu ikon cinye wa.


'Amin uwaila tabbas albasa batayo halin ruwa ba,zaka miƙe mu tafi fadda ko sai na ɓata maka na rantse da Allah ka musa ko kaƙi tashi zan maka bakin da baka taɓa zata ba attahiru kuma idan munje ka faɗi duk rashin ɗa'ar da ka haɗa jiya.


Gaba ɗaya jikin ɗan malam a sanyaye yake sai alokacin yaji ashe ciwon cikin ma ya tafi sai kumburin cikin nasa da yayi saura, ya miƙe a dafe malam ma ya tashi ya saka shi a gaba sukayi gidan hakimi.




…………Qofar gidan hakimi cike take da jama'a kusan manya manyan masu faɗa a aji na garin lambu,duk an sha ruwa anje sallah an dawo ana taɗi wasu na ɗan motsa baki da kayan marmari,malam ya nufo ƙaton kafet ɗin shi da ɗan malam dake duduƙawa,waje akayi musu iso suka zauna malam yabi duk ya gaggaisa da jama'ah haɗe da yiwa junna *Barka Da Shan Ruwa* malam ya ɗora bayani,kowa yayi mamakin yanda malam da kansa ya sako ɗansa tilo ɗaya agaba ya kawo shi dan a hukuntashi dai dai da abinda ya aikata ɗan malam ya kwashe duk yanda akayi tun zuwansa karɓar magani wajan Basi likitan dabbobi har yanda yazo ya zuba maganin da taimakon ɗan abu kowa yasa salati da tafa hannuwa yana jimanta lamarin take hakimi ya badda izini aje atahu da basi likitan dabobi da dan abu a haɗo da Nafi'u kafin nan bari in ɗan kurɓi ruwan sanyi na ɗora fan's.🥰



"Jama'ah kowa yayi jugum ana jiran bayan Allah nan su ƙaraso sai ga basi likitan dabbobi an taso ƙeyar sa sai rantse rantse yake shi fa ba ruwansa bai ma san me ya faru ba,da zuwa hakimi ya bada umarni a ɗan jiƙa wa basi likitan dabobi baya kafin ma yasan me ya kawo shi,ma bada bulala ya shimfiɗar da basi da ƙyar ya kwanta dan sai da aka riƙe ƙafafun mabada bulala ya shiga aikin sa haƙƙun basi likita ya fara sambatu har da su tusar wahala me shegen wari hakimi da gudu yasa akawo turare bayan ya rufe fuskar sa dukka da babar riga ya ɗauka iya hancin ya rufe😂😂😂😂😂






*Aradu akwai chakwakiya a gaba ku dai ku biyo ni a sannu fan's ina yinku da irin ruwan commenats ɗin da kukeyi da Addu'ah a gare ni har cikin raina nake jinku Allah ya bar ƙauna haɗe da lafiyar ido ai ta sambaɗa karatu ana yi mana wuf da comments🥰😘🥰*





 _*A nan zan gimtse in da Comments/Share*_

No comments