TSANGAYAR MALAM 7-8
_*👳♂️👳♂️👳♂️TSANGAYAR👳♂️👳♂️👳♂️*_
_(Malam)_
_Maman Dr_
7️⃣-8️⃣
A ƙofar gida ya iske motar asibiti ƙatuwar nan wace ake iban marasa lafiya da ita," ga ƙofar gidan cike da mata da maza har da Baƙiru daya ji labarin abinda ke faruwa ya garzayo da sauri dan ya taimaki abokin nasa ganin motar asibiti a wajan yaja gefe guda ya tsaya yana kallon duk abinda ke faruwa,kurar Nafi'u ya saki ya ƙarasa bakin motar a guje zai shiga wani daga cikin ma'aikatan asibitin ya tare gaban shi duk jikin sa da wasu irin kaya da suka lalluɓe ko inan sa har kan sa da hannayen sa ya ce"
""Dakata malam ina zaka shige.
Dan Allah ku barni naga babana da Addah karku tafar mun da su ku bar ni na kai su asibitin da kai na dan Allah ku ƙyale mun iyaye na.
Kaga samari ba wani guri zamu tafi dasu ba illah inda za'a kulla dasu da lafiyar su kayi haƙuri ka kwantar da hankalin ka da ƙafarsu zaka ga sun dawo insha Allahu gwaji za'ayi musu kuma a ɗora su akan magani.
Naji amma ku bar ni na biku idan ma bazaku bani su ba wallahi su kaɗai ne gata na gaba da bayaaaaa dan Allah ku barni........kuka nafi'u ya saka yana riƙe da jikin motar gam kamar za'a kamoshi,ɗaya daga cikin ma'aikatan ya nufo inda su nafi'un sake lura da yanda nafi'u ke kuka kashirɓan yana magiya,da zuwan sa ya dafa kafaɗar nafi'u haɗe da janyo shi gaban motar ya shiga rarrashin sa da bashi baki a haka har nafi'u ya share hawayensa yana gani ma'aikatan suka ja mota suka tafi da malam musa da Addah asma'u da yadikko babu yanda ya iya har motar tayi masa ni sa sosai nan da nan kallo ya dawo kan sa,juyawa nafi'u yayi ya janyo kurar ya nufi inda ya karɓo ta yana zuwa ya ce"
"Na abu ga kurar taka na dawo maka da ita ban ma saka ko mai aciki ba an tafi da su asibiti a mota.
'Ni ba ruwa na da tafiyar su asibiti yanda nabaka kurata muka yi magana akan kuɗi na to fa haka za'ayi ina ruwana da ka saka su ko baka saka su ba malam ka miƙo mun rabin kuɗina ka ware.
Haba ɗan Abu bakaji abinda na faɗa maka ba ne na ce ban mori kurar ba.
Taɓɗi wallahi Nafi'u sai ka bani rabin kuɗin kurar nan afuwa ɗaya zan iya yi maka na haƙura ba sai ka wanke ta ba amma fa kuɗi sai am bani wallahi.
ajiyar zuciya nafi'u ya sauke ya zaro kuɗi a aljihun sa ya miƙawa ɗan abu,ɗan abu ya saka hannu ya karɓa yana ƙirgawa,nan da nan ɗan habu ya haɗe fuska haɗe da furta""
"Sauran ka jaka ɗaya ka miƙo min ko na maka rashin mutunci.
In dai akan jaka ɗaya ne, gata ba xa aji kai na da kai ba ni ba matsiyaci bane mara imani,nafi'u ya zaro ɗari biyu daga aljihun wandon sa ya miƙawa ɗan abu,ɗan abu ya warta yana murmushi haɗe da faɗin.
"Naji dai tunda ka bani da kaga ɗanyan aiki wallahi.
"Hmmm lokaci ɗan abu kasan bana barin raini bare arai na ni yanzun ma ba a hayyaci na nake ba da wallahi sai na murza maka ga kurar kanan kowa da ranar sa,nafi'u ya juya yayi hanyar layin gidan su,nafi'u na barin wajan ɗan malam ya fito daga cikin langa-langa suka chafke da ɗan abu haɗe da cewa.
"Hmmm bari ba shegiya bace da uban ta mu za'a gunawa a sha damu haka siddan haba ashe bamu haifu ba,kaga mutumin naka ɗan abu duk ya furgice daga ɗan taɓashin da nayi,dariya suka saka gaba ɗaya ɗan abu ya ce.
"Kai baka ga har wata rama lokaci ɗaya yaja ba gaskiya ɗan malam kasaka ɓawon nan a tukunya me zurfi,wai yama akai ka burkitawa tsofaffin nasa ƴaƴan hanji ne?
Kafin ɗan malam ya magantu sai da yaci dariyar sa son ransa ya gama ya dubi ɗan abu ya ce""
Diran musu nayi kawai akan wata romon miyar kakar sa koriya shar da ita kasan tsoffin nan akwai su da jan aaaa miyar yauƙi musamman ta kuka ko gidan santsi kuɓewa nake gaya maka Allah cikin ikon sa ya bani dama na yi wuf a cikin kukar tini labari ya sha ban ban dana da kai kaga yadda aka kwaso su kamar wasu tsunmokara a hannu wallahi sunyi laushi sun daku ɗan abu
Ɗan malam ho aji tsoron Allah,aji tsoron sheɗancin ka yanzu nawa zan baka.
50/50,za'ayi kawai ɗan abu.
Kamar ya?
kamar yanda kunnuwan ka suka jiye maka kasan bana maimaita magana biyu in zaka raba malam ka raba kawai na ɗaye.
Amma kasan kurar tawa ce ko.
Ni kuma nakawo maka harkar har gidan ka idan ban kawo ba zaka samu?
Haka ne kuma gashi to,ɗan abu ya raba kuɗin kashi biyu ɗan malam ya karɓi na shi ya tafi shi kuma ɗan abu ya tattara kayan aikin sa ya mayar cikin langa langa ya rufe ya nufi kasuwa.
Ko da nafi'u ya dawo gida,gidan ya shiga gyarawa ya wanke duk inda kashin ya taɓa da ruwa da omo da gishiri yana yi hankalin sa nakan iyayen sa har kusan daf da shan ruwa ya rasa inda zai saka kansa ko waye zai bashi abun shan ruwa gashi ya bala'in gajiya,yana cikin tunanin yanda zai yi aka shiga ƙwarma sallama a zaure cikin ƙarfin hali nafi'u ya amsa dan bai taɓa tsammanin zuwan wani cikin gidan ba jiki ba ƙwari ya miƙe ya nufo zauren'cike da mamaki ya dubi yaya manu da yayi wata iriyar shiga duk jikin sa buhu ne a nannaɗe ƙafarsa da hannayen sa kuma safa ce ta kai goma hancin a toshe ga uban leder fara daya kifa a fuskar numfashin sa sai hura ledar yake yana mannewa da sauri yaya manu ya miƙawa nafi'u langar abinci da miya da kofin sulba da wani kwanon shima daban,kamar nafi'u ba zai amsa ba kuma chan ya karɓa haɗe da cewa"
"Na menene yaya manu?
"Ummmm innnn ummm,maganar kenan yaya manu ya juya da sauri ya bar gidan da garin sauri ya kusa hantsilawa ya fadi yasa hannu ya tare ya fita har murmushi nafi'u yayi dan kar ya ɗau kwarfin19 duk yake haka,"Allah sarki ni na mutu,da haka nafi'u ya koma cikin gidan ya zauna a ɗakinsa duk bai jin daɗin komai sai tunanin daya ishe shi na iyayen sa.
_*An sha ruwa ido ya buɗe*_
…………Kusan gaba ɗaya masallatan unguwar suka soma kiran sallah jama'ah kowa na ƙoƙarin Addu'ah yana kuskura bakin sa domin gaggauta shan ruwa,dabino dayawa suka fara kaiwa bakin su sai ruwan sanyi da ya biyo baya aka fara shirin yin Alwala don gabatar da sallar magarib,su ɗan malam kuwa na kan inna uwaila a tsaye yana bala'i akan ƙosan data zuba masa dole sai ta ƙara masa akan wanda ta zuba acewar sa ba isar shi zai yi ba,ya kuma cewa"
"Wai Kin ma san irin yunwar dana keji kuwa zaki kama ki zuba mun ɗan wannan abun sai kace na roƙa yasin dashi gwama babu ki ƙaran ko kuma kowa ya rasa wallahi ai tsohu na ne ya bada ba daga gidan ku aka aiko ba ko ba haka bane,inna uwaila sam bata tanka masa ba sai ma juye masa na cikin kwandon da ta tsame tayi gaba ɗaya kunun tsamiyar ma ta kuma kandama masa da yawa ya sa hannu duk da haka ya kuma ibo na cikin man ya bar wajan, madafa ya wuce kwantan abincin jiya daya sa masifa ya ɗumama yaje ya ɗauko ya shige ɗakin sa kai tsaye ya fara afa ƙosan uku uku yake jefawa cikin bakin yana kurɓar kunan tsamiyar har wani lumshe ido yake dan daɗi kan kace me babu komai a cikin kwanan sai kunan kaɗai ya rage a kwanon sha ya janyo shinkafa da waken gaban sa ya zaro kulele daya siya tun rana ya ajiye asha ruwa ya ci, nan ya fara kai shi yana ci yana shiii tsabar zafi da uban yajin daya afa.
Sai da ɗan malam ya cinye shinkafa da wake da kulelen kaf ya shanye kunan tsamiyar ya tura kwanukan gefe ya baje a ƙasa wai zai ɗan huta cikin ya sarara ya tashi yayi sallah ciki ya fara kiran curoma ya fara ƙara yana ƙugi ga kumburin da yayi suntum sai juye yake yana ƙoƙarin yin amai,aman sam yaƙi tasowa nan da nan idanuwan ɗan malam sukayi tulu tulu abinka da masha Allah ido dara dara ya soma laluban abin zai kama ya miƙr zaune,amma fafur ɗan malam ya kasa.
"Tara-tara ya fara ganin ɗakin kamar zai rufta masa ai bai san san da ya soma""""""""""
"aradu ku tara next page,😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂,alhaki kyuikuyo😂😂😂😂😂😂😂
_*A nan zan gintse in da Comments/Share*_
No comments