Breaking News

RAYUWAR BALKISU 4

Rayuwar Bilkisu

Part two


FREE BOOK


By

Nafeesat m.aliyu

(Feenah)


Masu neman Rayuwar Bilkisu part 1 a tuntubeni ta wannan number 07062481557


Yauwa kamar yanda na sanar a last Page zan nayin posting sau uku aduk week insha Allah Friday Saturday Sunday insha Allah sune rana kun dazanna posting acikin su nagode dafatan zaku kasance tare Dani.



♦️♦️♦️page 4


Kara maida su nayi na lumshe cike da sanyina,kamar sauqar aradu haka naji sauqar muryar sa"Mrs.khamal me yayi zafi haka da kallon ma bazan samu ba?"ko kwakkwaran motsi banyiba wanda zai bashi alamar cewa zai samu amsa daga gareni ba,jin sauqar lallausan tafun hannunsa akan goshi nane yasani saurin kara ware idanuna akan shi babu shiri.






Dariya Dr.ya tuntsire da ita ganin wannan saurin zabura na Bilkisu kamar wacce taji za'a saceta"matsoraciya kawai"ya fada tare da mikewa ya nufi kofa,jin karar rufewar kofar ne yasani sauke wani nannauyan numfashi tare da kara gyara kwanciya ta.




Cikin "yan mituna qalilan na kumajin an turo kofar dakin gudun kada naje idanuwana suyi tozali da Wanda banyi zato ba ya hanani bude su a wannan lokaci,hakan ce kuwa tafaru shine yadawo dakin hannun shi dauke da abinci da magun guna,da kanshi ya taimaka min natashi ya maidani kan kujerar dake Dakin Unman tare da vani abincin naci a nutse dukda da farko na nuna bana buqatar hakan amma ya daqe akan sai naci domin yasan tabbas baza arasa yunwa a tare daniba,hakan yasa nadan caccakala domin banason musu dashi.




Bayan nagama cin abincin yabani magani tare da fad'in idan zazzabi bai sauqa ba zuwa anjima dole ayi allura,wacce ni ko kadan bana fatan ta,hakan yasa har cikin raina nake addu'ar Allah ya taimakeni ya sauqa basai anyi allurar nanba.




Da haka yayi mun sallama tare dajan kofar ya futa,wani nannauyan numfashi na sauke yayinda zuciyata ta tafi tunani kala kala da sake sake irin na zuciya dama tunanin Rayuwar baki dayanta,da haka bacci yay nasarar saceni  batare da nayi aune ba.





Ko sallamar sa bata amsa ba saima wani kallo datake binsa dashi wanda inda sabo ya riga ya saba da halin Surayya a "yan kwanakin nan tunda maganar auren nan ta taso danne zuciyarshi kawai yake domin baya daga cikin mutane masu son hayaniya, direct bangaren sa yanufa batare daya tanka mata ba domin ya Dade da futa daga har karta domin ya fahimci shiga harkar tat babu abunda zai haifar masa sai bacin rai hakan yasa ya bata hutu har zuwa lokacin da zata sakko da kanta.



Wani qululun baqin cikine ya tokare mata makoqaro ganin irin shariyar da yake mata da yanda yake kamarin sa acikin gidan tamkar babu wani mai rai acikin gidan bayan shi....✍🏻


Pls manage.


Kada ku manata more comment more page.

No comments