GOBE NA 2
Sai da na jika mata kanwar ta sha na shiga dakina nai sallah isha'i, ina sallamewa nai saurin mikewa tsaye na nufi inda wayata take tana ringing na duba na yi zaton ko Abban Namra ne da farko sai dai ganin bakuwar number yasa ni aje wayar har sai na koma saman carpet har sai da na gama tasbihina nai addu'a ma mijina nai ma kaina da iyayena sannan na nemawa yara na shiriya. Daga bisani na mike tsaye na nufi inda wayar take aje na dauka na sake kiran layin da aka kirani da shi.
“Assalamu Alaikum”
Ni na fara mika
sallamar kamin wanda na kiran ya fara min sallamar.
“Wa'alaikissalam
Halimatu”
“Na'am Ranka ya dade”
Na gane cewar ogana ne
na gurin aiki wato oga Dahiru.
“Ki yi kokarin hada
document dinka kamin gobe ina da bukatarsu”
“To ranka ya dade”
“Kuma ki yi saving din
wannan number ita ma number ta ce”
“To ranka ya dade”
Daga haka ya kashe
wayar be sake ce min komai ba, ni ma kuma ban ce ba, daman kuma me zan ce masa,
bayan kiran da yake min ma yana damuna balle kuma har nai wata magana da shi,
zauna nai bakin gadon ina ta mamakin dalilin kiran da oga Dahiru yake yawan min
a duk lokacin da yake bukatar wani abun, shin yana manta cewar ni ma ina da
aure da iyali kamar shi, ban san miyasa yake son kira akan abunda be kai ya
kawo ba, ba kira kadai ba har wasu abubuwna da yake min bana jindadinsu, domin
duk abunda na ke ina kokarin kare mutuncin aure da kuma na yayana da mijina.
“Momy ni dai gobe idan
mun dawo daga scul gidan zan dawo ba zan je gidan Baba Sadi ba”
Namra ce ta shigo tana
wannan maganar tana wani bata fuska kamar zata fashe da kuka.
“Saboda me?”
“Bana son zawa can
Momy dan Allah”
“Ki yi hakuri Mamana,
idan kun dawo nan gidan ba wani abun za ku yi ba, kuma kin ga ba girki balle ku
ci, amman can Momy Hassana tana girkawa, za ku samu ku ci”
“Momy to ki daina zuwa
aikin nan pls ko kuma mu rika zama a gida a haka muna jiranki ki dawo”
“Mamana akwai abunda
ake miki a gidan ne da baki so?”
Ta girgiza kai alamar
aa sannan ta kwantar da kanta jikina.
“Cikin ya daina ciwo?”
“Eh amman yana min
kadan-kadan ba sosai ba”
“Zai daina
In-Sha-Allah, na zubo miki abinci za ki ci?”
“Za mu ci tare Momy zan
wanke hannuna ba zan saka miki datti ba”
Murmushi nai mata
sannan na mike tsaye na fito daga dakin na sauko downstairs. Ban samun Abban
Namra a falon ba, daman kuma ban saka rai ba domin ba kasafai yake dawowa da
wuri ba, idan kuma har ya dawo to sai idan wani abun zai yi ko zai dauka amman
dai ba haka nan kawai zai dawo gida da wuri ba ko kuma ya wuni ba. Tuwon da na
girka dazun kamin na fita na zubo miyar kuka sannan na fito bakin kofar kitchen
rike da abincin ina kiran Adnan domin bana son sai na zauna ya zo yace min zai
ci abincin.
“Adnan Aiman za ku ci
abinci yanzu?”
Babu wanda ya amsa ni
a cikinsu balle kuma har su sauko kasan da sunan cin abincin, sai Amal da ban
kora ba.
“Ommy Ommy zan ci
abinci”
“To zo ki ci yar
autana”
Na fada ina karasa
fitowa falon sannan na zauna kasan carpet din na zaunar da ita saman kafafuwana
na soma bata.
·
·
“Namra zo ga abincin”
Da sauri ta sauko ta
shiga kitchen ta wanke hannunta sannan ta saka min a plate, loma uku zuwa hudu
kawai tai ta cire hannunta wai ta koshi.
“Cikin ne har yanzu
Namra?”
“Eh ciwo yake min”
Ya fada tana yamutsa
fuska sannan ta kwanta a gurin ba tare da ta wanke hannunta ba, ni kuma ban
matsa ba ganin gata jindadi har sai da na gama sannan na dauke plate din na kai
kitchen na wanke hannuna da na Amal a can sannan na dawo na dauki Namra na shigar
da ita dakinsu na cire mata tufafin jikinta na nai mata wankan dare kamar yadda
na saba musu na saka mata kayan bachi sannan na kwantar da ita, Adnan nan kam
sai da nai kamar ina yi sannan ya bar gabar system din ya tafi yai wanka nai ma
Aiman suka kwanta, ni kuma na dauke system dina na fito na baro musu dakin.
Dakina na dawo na kwanta gefen gadon Amal ta haye min kafafuwa tana kokarin
fara kukanta na banza. Wayata na dauka na kunna data dama bana samun hawa
online sai da dare idan yara sun yi bachi kuma na gama komai, grps din muna na
Nothen Women's Advice na fara budewa na duba chat din sannan na shiga na Salma
pre-order na duba abubuwan da ta turo cikin har da injimin wanki wanda na fi
kowa bukatarsa a cikin gidan nan saboda wanki da nake na yaran nan gashi kwana
biyu sun lalata. Ban bar online din ba sai kusan sha daya da rabi na
dare, sannan na tashi Amal wacce a lokacin ta dade da fara bachi a take ta saka
min kuka daman ta saba ko ba ai mata komai ba tana kuka balle kuma an yi da
dalili. A haka nai mata wanka na saka mata tufafin bachinta na goyata saboda na
samu ta daina min kukan.
Dakin yaran na koma na ciro musu dayan set din uniform dinsu na dora musu a
inda na saba aje musu sannan fito na shiga kitchen din n dauko abincin Abbah
Namra na kai masa dakinsa duk kuwa da na san ba lallai ne ya ci ba domin ba ko
da yaushe yake cin abinci a gida ba. A falo na fito da laptop dina na duba
document din da oga Dahiru yace na shigo da su na fida su dabam a cikin wata
folder sannan na rufe laptop din na koma dakin yara na kwantar da Amal. Na
shiga nawa dakin nai wanka na saka kayan bachi na dawo dakin Abbah su na kwanta
a take bachi yai gaba da ni abun ka da wanda ya gaji. Can cikin bachin nawa ina
jin lokacin da Abbansu ya shigo duk yadda na so na dago nai masa sannu da
dawowa sai na kasa saboda bachin da ya ci idona.
Washe gari tun da
asuba na tashi, sallah ce farkon abunda na fara yi sannan gabatar da addu'o'ina
suma ba duka ba daman idan ba weekend ba bana samun tsayawa nai yi su gaba
daya, ina saukowa kasa na shiga kitchen na shiga shirya musu abincin makaranta
da kuma na karyawarmu, bayan na firaye dan na fasa kwai sannan na shiga dora
ruwan zafin, Amal ce farkon tashi daman haka take tafi kowa rigima ko a dare
idan ta motsa bata ji ba, indai yan rigimar suna nan sai ta saka kuka ta dawo
dakinmu ta kwana.
“Ommy Ommy”
Ta fada tana murja ido
cikin kuka.
“Minene Amal?”
“Bachi”
“Je ki dauko zane”
Sai kawai ta fashe da
kuka, haka yasa dole na cire dankwalina na goyata da shi na cigaba da aikina.
Ban tashi su Adnan ba sai da na tabbatar na shirya musu komai na makaranta
sannan na tashe su nai musu wanka suka sauko kasa na hada musu tea kawai suka
sha suka hau sama suka shirya cikin uniform dinsu kasancewar yau monday. Ni
kuma na shiga cikin dakina na dauko kudin napep na saka hijab dina na fito na
saka yarana a gaba muka fito har Amal muka nufi titi ina kokarin taron napep
sai ga makocinmu kuma mijin kawata Hajara ya faka gefenmu tare da yaransa a
cikin motar ya sauke gilashin motar yana miko min gaisuwa, sai da muka gaisa
sannan ya ce da su Adnan su shigo motarsa suka shiga da saurin ganin yaransa
daman can makarantarsu daya kuma yana yawan wucewa da su idan zai kai nasa
yaran, wani lokacin ma har gida yake aikowa yace su fito zai kaisu makaranta.
Sai da suka shiga motarsa sannan na juyo na dawo ni da Amal ina yanje da
hannunta muka shigo cikin gida. Tea ta na dazun da bata karasa shanyewa ba na
mika mata sannan na nufi dakin Abbansu, tufafin daya cire na jiya na fara dauka
dan hade su da waendan kayan daudan nashi, al'adata ce duba aljihun rigarsa da
wando kamin na saka su a kayan dauda saboda cire masa duk wani abu nasa da yake
cikin aljihu. Rigar na fara dubawa sannan na saka hannuna a aljihun wandonsa,
sai na ji abu kamar kwalin wani abu ina cirowa na ga kwalin kwandon sai dai ba
cikakke ba da alama an yi amfani da shi. Ni a
Kadai na san abunda na ji a wannan lokacin a take jikina na dauki rawa kamar
dai yadda zuciyata ma take ta bugawa da karfi idanuwa na cika da hawaye. Juyawa
nai ina rike da kwandon din a hannuna na kalli Abbah Namra da yake kwance saman
gado yana ta sharar bachinsa hankalinsa kwance ni kuma nawa hankalin a tashe da
kwandon a hannu. Dayan hannuna na saka na share hawayena da suka zubo na dauke
kayan na fita da su, sai dai har nai aikin da nake na shirya Amal nai wanka nai
shirin aikina hawayen ba su daina min zuba ba, ni kuma ban fasa sharewa da
hannuna ba. Kamar yadda na saba yau ma na hada masa komai nasa na karyawa na
shigar masa da shi dakinsa na kai masa, sai dai ban same shi a kwance ba sai na
samu ya shiga bandaki da alama yana wanke baki ne, a can na baro Amal na fito
na sauko kasa na nufi dinning na hadawa kaina tea amman sai na kasa sha saboda
bacin rai da ke cikin raina, i decided na aje tea din na dawo saman cushion na
zauna na dafe kaina. Wannan karon ba hawaye na ke ba wani abun ya ke jin ya
tsaya min a zuciya marar misaltuwa daker na ke iya hadeye yawu da numfashi. Na
kai minti talatin a haka sannan na tashi na koma dakina na dauko kwalin condom
din na nufi dakinsa, kamin na kai hannu na tura kofar dakin na jiyo sautin
dariyarsa hakan ya tabbatar min ko dai yana magana da Amal da take dakin ko
kuma waya yake, ban yake dayan biyu ba na ji yana fadin.
“Na samu hutu satin
nan ina kike son muje?”
Hakan yasa ni dauke
hannuna daga jikin kofar daman can rikawa kawai nai ban tura ba.
“Kaduna? To yayi ba
matsala zan shirya mana komai, amman kamin na turo account dinki zan saka miki
wani abu sai ki yi siyayyar da kanki kin san ni ba zan iya zuwa siyayya yanzu
ba, kuma kin san idan ina fita da ke yau da gobe za a iya fara cewa wani abu”
Kadan kadan yake
maganar amman hakan be hana ni ji ba, domin mutun ne mai daga murya idan yana
magana da wani ko da kuwa kadan-kadan yake yi. Ji nai kamar ba zan iya sauraren
firarsu suka ba hakan yasa na murda kofar dakin na shiga ina kokarin maida
hawayen da suka cika min ido.
“Oh Okay Faruk sai na
shigo”
Shine abunda ya fada
sannan yai hanzarin kashe wayar, ya gyara zamansa yana kokarin fara cin abinci,
ko da wasa ban bar wata alama da zata nuna cewar na fahimci da mace yake waya
ba, duk kuwa da kasancewar bana iya sauya yanayi na rashin jindadi da walwala
dake tare da ni a yanzu. Zaunawa nai gabansa.
“Ina kwana”
Na fada ba tare da na
kalleshi ba. Shi ma bana tsammani ya kalleni kamin ya amsa min sai Amal kawai
yake wasa da ita yana bata abincin shi ma yana ci.
“Jiya Hajiya ta sake
min maganar kudin ac”
“Ai sai ki ce mata kin
fada min magana, ni Wallahi na manta amman yau zanje na fada kudin
In-Sha-Allah”
“To Allah ya bada iko”
Be amsa min da amin ba
sai ya dago ya kalleni.
“Ya akai kin san bana
son ana tsare ni idan ina cin abinci akwai wani abun ne?”
Har zan mishi maganar
condom din sai kuma na hade yawu na gabatar masa da abunda na san ba lallai ne
yai min ba.
“Jiya ne naga wani
injimin wanki da ake order daga waje shine na ce ko zaka saka min wani sai na
hada da abunda yake hannuna sai na siya na huta da kai wanki”
“Ba ni da kudi yanzu,
ina albashinki? Ko aikin kawai kike ba a biyanki?”
“Ana biyana mana kai
ma ai ka sani domin da su na ke rage wasu abubuwan nawa”
“To ki siya da shi ni
ba ni da kudi yanzu, da kin ga mutun ya zauna kin fara masa maganar kudi kenan
shiyasa ko zama gidan nan bana son yi kuma baki da lokacin magana sai lokacin
da nake cin abinci”
“Irin wannan lokacin
kawai nake samun damar magana da kai Abban Namra, baka dawowa da rana sai idan
wani abun zaka yi da dare kuma sai 12 ko 1 kake dawowa”
“To ni dai ba ni da
kudi yanzu”
Ya fada yana wani kara
hade fuska. Sai na aje masa condom din da ke hannuna murya a sanyaye na ce.
“Ga wannan na gani a
cikin kayan da ka cire jiya”
“Oh jiya Bala ya bani
ajiyarshi na manta na bashi abarsa”
Ya fada kai tsaye
kamar gaske ba tare da ya kalleni ba. Idanuwana cike da kwalla na ce
“Ko dai na wanene
Allah ya sani kuma yana jiran kowa a madakata”
Ina fadar hakan na
mike tsaye sai dai kamin na kai tsayen ya rigani yana daka min tsawa.
“To me kike nufi?
Zagin kike ko kuma Allah ya isa za ki min? Wai mi yake damunki ne Halima? Daman
munanan mata kun fi komai bakin hali ku ba kyau ba sai sakawa mutum damuwa da
bakin zargin tsiya”
“Ba ni n hallici kaina
ba Abban Namra, kuma saboda bana da siffar da kake so a jikin mace ba shi yake
nufi ka bi wasu matan ba, kai kanka kasan ba haka ka aureni ba, auren shekara
goma sha biyu bana kwana biyu ba ne, dole wani abu a jikina ya canja, na haihu
har hudu dole jikina ya bude, ka dinga jin tsoron Allah Abban Namra....”
Kamar jira yake na
kare a take ya wanka min wani mahaukacin mare mai zafi kamar garwasun wuta,
kamin nai ihu Amal ta fara fashewa da kuka ta rike masa kafa damn ta saba masa
haka ida da su Namra da Adnan idan yana dukana, ni kuma ban tsaya komai ba ya
juya da sauri na fice daga dakin ina kuka.
“Dacan bana tsoron
Allah aka ce miki? Wawuya kawai”
Shine kadai abunda na
ke iya jiyo yana fada bayan na baro dakin, da gudu na dawo dakina na zauna kasa
na fashe da wani irin kuka mai ban tausayi da taba zuciya.
No comments