YAU DA GOBE 5 & 6
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🌹YAU DA GOBE 🌹
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾Story & writing by mmn fareesa
🅿️5&6
Wannan shafin na y'an tead'in MUSTY ne😜🏃♀️
......Da sauri hjy jamilah tasaki fuskarta tana musu sannu da zuwa...jidda kuwa Baki yak'i rufuwa sbd murna"kafe Yaya Aliyu tayi da idanunta tana kallo"sbd ganin yadda yyi wata irin canzawa "lumshe ido tayi tana hasko yadda zata d'agawa k'awayen ta Kai in har ta mallakesa amatsayin mijinta...fatarsa tayi frash alamar hutu dajin dad'i ga wata wayewa da yyi na ilimi na ratsashi"uwa uba Kuma kyawun daya k'ara..shikuwa tamke fuska yyi sbd y'an miskilancin sun motsa had'e da shan k'amshi"zama sukayi kan kujeru"yyinda Sadiq yazo yarungume Yaya Aliyu yace well come back b
roth! murmushi yasaki "yyi hugging nasa back" hade da cewa thanks!Suka zauna kan 2 seeter"hjy jamilah tayiwa jidda signal da ido..da sauri cikin yauk'i da Jan hankali tace Yaya Aliyu sannu da zuwa ya hanya?"batare d'aya kalletaba yace alhmdllh! atakaice yanata latsa waya...yyinda safeenah ta gaidashi amsawar yyi cikin ko in kula"kafin yakkali hjy jamilah yace umma Ina wuni?"jiki na kirma ta amsa ta juya suna gaisawa da ummi"nan safeena ta nufi fridge sbd kamusu drinks "yyinda Sadiq yasha mamakin ganin zarah da musty kayansu iri d'aya"gashi musty yyi Kane kane ga k'ugunsa gana zarah...kallo d'aya Sadiq yyimusu ya d'auke kansa Yana kallon SUMAYYA wacce ke tsaye...sumayya kuwa dake kallonsu mamaki ranta fal"sbd kallo d'aya tayiwa Yaya Aliyu tagane yanada izza da gadara"sannan gabanta sai fad'uwa yakeyi...acikin zuciyar ta take gulmarsu..inbacin rashin kunya ji yadda yagaida hjy jamilah"dakuma yadda su jidda kemishi mgn Yana wannan basarwa...duk yadda su jiddar ke d'okin zuwansa !ita wlh ta zata mugun so da kulawa yake bawa jiddar....Yaya Sadiq Ina wuni?"muryar zarah ta katsewa sumayya tunanin ta"Sadiq yyi murmushi yace lfy qlau zarah"bakisan zumunci ko?lah wlh ba haka bane Yaya"ak'ule musty yace Yaya Sadiq barka da dare! Sbd kallon da ummi ta Masa yasan mitake nufi,inbacin ita wlh bbu ruwanshi dashi ji yadda yaketa wani hura hanci...cewar musty azuciyar sa...
Yauwa"Sadiq ya amsa atakaice...kafin yadubi sumayya yace sumayya jeki Kira abba kice gasu ummi sunzo...gaba d'aya banda Yaya Aliyu suka kalli sumayya"sumayya ta russuna ta gaida ummi"ummi tayi murmushi"aranta tana yaba hankalin yarinyar"gasu safeenah nan dg zaune suka gaida ita "dukda jidda da akeso aturawa Aliyu"sbd tasan wannan rawar kan da hjy jamilah keyi sbd jidda ta auri ALIYU ne"shiyasa take sake Mata fuska"shekaru28 dasuka wuce hjy jamilah na daga cikin manyan mak'iyanta.....
Sumayya na k'ok'arin barin parlourn"abba da mama suka yo sallama"tuni fuskar hjy jamilah ta sauya"yyinda Abba ya fad'ad'a fara'arshi sbd ganin family d'in yayansa..... sumayya kuwa k'ok'arin fita takeyi abba yace ah ah dawo cikin y'an uwanki... bbu yadda ta iya dole ta nufi cikin parlourn.. da sauri Yaya Aliyu yataso cikin nutsuwa ya rungume abba"Abba yyi murmushi yace my lovely son nayi kewarka wlh"yafad'a cike da k'aunar d'an d'an uwanshi...sakinsa Abba yyi"nan Yaya Aliyu yaduk'a yagaida Abba "da mama dake tsaye kusada abban tana kallonsa tana murmushi"hakan yatabbatar Masa itace amaryar abban kenan...isowa suka idayi parlourn.. sumayya kuwa tayi mamakin yadda yagaida mamanta cikin girmamawa"wata zuciyar tace sbd Abba na Gurin...
Ummi tasaki murmushi had'e da cewa Allah yasa amarya batayi fushiba!Zama Abba yyi yace ah ah batayiba"mama na murmushi suka gaida da ummi"yyinda Abba yasake gabatar da mama da sumayya"atake zarah taji sumayya ta burgeta"yyinda sumayya ta gaida zarah da musty"shikuwa y'allab'ai be isheta kalloba"y'an cikin parlourn basu lura bata gaidashiba sai hjy jamilah da safeenah kawai"suma azatonsu tsoronsu yasaka bata Masa mgn ba"
shikuwa Yaya Aliyu bega fuskar sumayya ba "sbd Koda Abba yagabatar da ita be kalletaba!"amma aransa yaji tsanar yarinyar sbd besan raini"yakuma fahimci batada kunya da ladabi"tunda gashi tagaida musty da zarah bata gaidashiba"Kuma agabanta duka yaran gdn suka gaishesa"tsaki yaja aransa yanajin haushin kansa akan tomeye ruwansa da yadamu ma?"wayarsa tayi ringing"
dubawa yyi yaga Nasir(babban amininsa ) murmushi yyi yamik'e tsaye byn yad'aga wayar....
Shima Sadiq tashi yyi Yana kallon zarah sbd Yana son yanunawa musty yafisa iko akan zarah"yadube ta yace zarah biyoni na baki wani sak'o...wani abu musty yaji yatsaya Masa amak'ogwaro...da sauri zarah tasaci kallon musty "shikuwa yak'i yarda su had'a ido"farin ciki k'al aran hjy jamilah sbd azatonta k'ila Sadiq zecewa zarah Yana sontane...kitashi Mana ! Cewar ummi tana kallon zarah sbd talura tana tsoron tashi sbd musty...sum sum sum"tabi bayan Sadiq "musty kuwa tuni yahad'e girar sama da ta k'asa"d'agowa yyi sukayi 4 eyes da safeena yad'ank'ara Mata wata uwar harara...kwata kwata yarinyar bata masaba"shiyasa besakar mata fuska.
Wayar musty tayi ringing" Yana dubawa yaga Yaya Aliyu ne"tashi tsaye yyi yana kallon ummi yace ummi muje ga Yaya can naji ranmu..bejira cewartaba yabar parlourn sbd dama jinsa yakeyi tamkar Yana kan k'aya ne...
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
Sadiq kuwa aharabar gdn suka tsaya da zarah suna hangen Yaya Aliyu dake waya"Sadiq yamik'a Mata wayarsa yace kisamin contact naki maruk'a zumuncin ta waya tunda bakison zuwa gd ayi zumuncin... karb'a tayi tana dariya tace hmmm Yaya Sadiq ai kaima bakasan zuwa gdnmu"injiwa?"bacin sanda nike zuwa Kuna skul keda musty"hakane fa"tafad'a tana mik'o Masa wayar"
Yace y karatu ?"
tace Alhmdllh ! Sai Shirin gamawa muyi service shikenan" ok to ALLAH ya taimaka"ameen Yaya...kafin yace wani abu zarah tahango musty"da sauri tace Yaya Sadiq Saida safe gasu ummi nan zasufito!
Sadiq yace ok ! Yabar Gurin...musty ko inda suke be kallaba"yanufi parking space"girgiza Kai zarah tayi tatsaya sbd hango ummi datayi da Abba da mama sun fito musu rakkiya"shima kuwa Abba yyi zaton ko Sadiq zarah yakeso"dama yasaka Masa ido ne"Yana jiran dawowar Yaya Aliyu yahad'asu yyimusu aure yagaji da ganinsu tuzurai musammun ma Aliyu"ita Kuma zarah dama yagaya Mata dasun kammala service ta fito d mijin aure..har bakin mota su Abba suka rakasu...Saida motarsu ta fice tukum"Abba yakalli mama yace muje ciki nabaki labarin family d'in alh Umar safana...
*************
Saida duk Abba yagama abinda zaiyi tukum"yazauna kusada mama yace "naga Baki d'okin sanin jin tushenmu ko?"murmushi tayi tace ah ah alh Ina jinka...gyaran murya Abba yyi kafin yafara da cewa...
Anhaifemu a safana LG"mahaifin mlm musu haifaffan canne"acan ya auri mahaifiyarmu fatima..damuke Kira da *hajjah*mu 3 ne agurin iyayenmu Umar shine babba sai ni Usman sannan k'anwar mu"zainab..bayan mun gama secondary skul muka zo Kano muka Fara neman kud'i"ni nakoma makaranta , shikuma Yayana Yana neman kud'i,cikin ikon Allah har Allah yasaka Mana albarka ni nazama barrister"shikuma yazama d'an canji"muka dawo da iyayenmu Kano "sannan mukayi aure...umar yaransa 3 da hjy Aysha na farko yarasu sai Aliyu da zarah"ALMUSTAPHA bad'an gdn bane"d'an k'anwar hjy Aysha ne tada rasu ita Kuma ta karbeshi tun Yana d'an shekara 3 alaokacin zarah nada shekara5...
Shakuwa tashiga tsakaninsu sosai"Zara tayita kuka inzata skul ita dole Saida musty"hakan yasaka aka sakashi dukda shekarunsa basukaiba dalilin dayasa suka Zama mate itadashi kenan..alh Umar Yana son musty sosai baya nuna banbanci atsakaninshi da yaranshi...atsakanina da d'an uwana akwai soyayya da hadin kai"sannan Yana kulawa da nawa yaran...ahaka mahaifin mu yarasu... zainab kuwa k'anwar mu bayan tayi aure bata tab'a haihuwa ba ,har yanxun...alh Umar zamu sakashi acikin jerin masu kud'in garin nan ,yarasu ta sanadin accident...tun Aliyu Yana yaro nake sonsa da jawosa ajikina hakan yasa nashak'u dashi har girmansa"ayanzun haka da tuni anyi aurensa"wata yarinya ce sunanta RUKAYYA! y'ar gdn commissioner of education ce "itace suke son juna da ita"ubanta yace sai ta kammala karatunta za'ayi aurensu"shikuma yace ya amince"hakan yasa yawuce Karin karatu a UK amma yanzun naso Masa mgn akan yarinyar tagama karatun ko kuwa??" sbd nagaji da ganinsu shida Sadiq bbu aure sun girma....wannan shine labarinmu atakaice... murmushi mama tayi tace Allah yajikansa da rahama...
€€€€€€€€€€€
Su musty kuwa acikin mota bbu Wanda yyi mgn har suka iso gd"saidai zuciyar musty acunku she take "anya ba gara yasanar Mata ba ?" Kada garin kallon ruwa....zarah ma aranta tana tambayar kanta Wai meyasa musty ke yin fushi ko canzawa aduk sadda wani nmj yamata mgn ko a skul ko a gida?"
Ummi kuwa duk tana lura dasu"har sula fice kowa yyi d'akin sa.....
Washe gari....Gurin karfe5:30am ummi ce ta nufi bedroom d'in musty sbd ta tadoshi 'sallar asuba tasanshi da nauyin barci...k'arar ruwa taji a toilet alamar wanka yakeyi...gabanta yafad'i"azuciyar ta tana tambayar kanta meke Shirin faruwa Wai?"ta lura da yaron na kusan kwana3 kenan indai zata zo tadashi Sallah zata samu Yana wanka"ga yawan azumi yanayi na nafila ,Kuma bawai ranar litinin da alhamis ba!
Ah ah ko wane lokaci inyakama zai iya yin azumin"Anya be kamata ba ta k'yalesa gara taji damuwarsa?...da wannan tunanin tayi maza ta fice tunda yatashi ta wuce d'akin Yaya Aliyu tasamu Yama wuce masjeed...
""" Ahankali yake sakkowa dg matattakar benan"jikinsa sanye da suit farare da breaf case d'insa ahannunsa...fuska asake yake kallon ummi da zarah dake jera breakfast a dining table"da sauri zarah ta gaidashi had'e da cewa amma Yaya saikayi break fast ko?"
Sorry baby !atsarina bbu African time nayi signing 8am Zan Fara duba patient... yafad'a Yana duba agogan dake d'aure atsintsiyar hannunsa"yadubi ummi yace ummi sannu da aiki ni na wuce office"yanzun babana bazaka yi karinba?"eh ummi nayi a office yafad'a Yana ficewa"ummi da zarah nafasa fatan sauka lfy...byn fitarsa ummi tace jeki jiramun auta yazo muyi karya...da to zarah ta amsa kafin ta fice...
Rufe d'akin yake da alama betashiba kokuma ganin damarsa ce tasaka yarufe.knocking zarah tayi "shiru ba'a yi mgn ba"batagajiba tacigaba"Afusace yace Wai wayene?hmmm broth nice fa"kazo muyi break inji ummi"Saida yad'auki kusan second 10"harta cire Rai dajin zaiyi mgn ! kafin yace ok bake kika turo kankiba ko?"to azumi nakeyi"cike da mamaki tace azumi Kuma bacin yau Friday?"banza yyimata.
Hakan yasa ta juya"ummi na zaune ta kalli zarah tace Ina yake?"tab'e Baki zarah tayi tace Wai azumi yakeyi...shiru kawai ummi tayi batace komaiba"Amma k'asan ranta tana burin jin dalilinsa nayawan azumi...zarah kuwa musty yabata haushi"akan yadda yake Mata tamkar yayanta bacin tagirmesa Yana gaya mata mgn yadda yaga dama...
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
Zaune yake kan kujera ya aza k'afafunsa kan table d'in dake gabansa idonsa alumshe"da alama yagajine! knocking akayi yabada izinin ashigo"azatonsa inma katine na patient gsky yagama duba kowa da yyi azahar "sukayi meeting gd zai wuce yahuta... SAFANA!badai kagajiba?"da sauri yabude idonsa yaga Dr Nasir"harararsa yyi yace ya bazan gajiba tunda ga agogo sarkin aiki?"murmushi Nasir yyi yace maida wuk'ar "kaga da kanada family kahuta"amaka wanka da tausa....tsaki Dr safana yyi Yana murmushi yace eh naji"aikai ana maka ko?"yo eh Mana bbu abinda my meena batamun "tacema nagaya maka tayi fushi"anyi biki baka nan "kadawo jiya koka shigo agaisa...kafin Dr safana yace wani abu anmurd'o k'ofar...RUKY da k'awarta saady suka bayyana"tuni Nasir yyi kicin kicin da rai "Yana mamakin safana da lik'ewa yarinyar nan RUKY"abin mamaki duk inda zata da saady nabiye da ita...Dr safana kuwa fuska yatamke sbd fushi yakeyi da ruky akan yasanar Mata jiya zai dawo "amma Wai tana kaduna gun duba k'anwar mamanta bbu lfy "a yadda ta fad'a Masa...
Ruky tayi murmushi tana kallonsa"had'e da cewa haba nawan tuba nakeyi!pls abokinmu katayani bada hakuri"murmushin yak'e Nasir yyi yace ai dole nataya bada hakuri dukda bansan laifin me kikayiba! yafad'a Yana k'arewa hannuwansu da saady dake sark'e da juna"
Sanye ruky take da areviant gownt maroon colour da veil maroon "yyinda saady kesanye da riga da siket na atamfa"sunfito Mata da k'irarta...
Bud'e ido Dr safana yyi Yana hararar ruky "tayi murmushi had'e da Jan kujera ta zauna"tana gaida Nasir"itama saady dake cika tana batsewa ta gaidasu ...ruky ba wani mugun kyaune da itaba"kasancewar ta Fara tas"hakan yasa ake ganinta da mugun kyau"shikansa Dr safana harda farin yajashi sbd yanason farar mace"saidai ruky akwai wayewa da gogewa atare da ita"kasancewar ubanta yanada kud'i yakuma shagwabata sosai...Dr safana yadubeta fuska atamke yace amm ita wannan chewing gum d'in tafita tajiraki awaje"tunda yazama wajibi duk inda Zaki Saida ita... yafad'a cikin husky voice d'in sa"kasancewar baya tsoro baya shakka gakuma bayason raini...Nasir kuwa yaji Dr safana yyi mugun burgesa da yyi hakan.
Saiya tashi Yana cewa nima bara na wuce Kar ahad'a dani akora abar Love birds su wala... yafad'a cikin tsokana Yana ficewa...saady kuwa inbacin kwarjinin da Dr safana yyi Mata wlh daya gane kuransa"
Ruky tace haba my man disgifa?"
Kallon ido cikin ido yamata kafin yatab'e baki yace well Zaki iya tafiya in hakan be Miki ba"kinsan halinaban rik'e mgn ko boyeta"yafad'a irin ko ajikinsa...saady batace komaiba ta juya ta fice...Dr safana ya dubi ruky yace as from to day kada kikoma zuwamin da ita inzamu had'u'to kawai rukky tace sbd tasan halin mutimin nata.. k'aramin abu zai maidashi babba! murmushi tayi had'e da aza hannunta kan nashi....wani kallo daya Mata yasakata janyewa da sauri...Wai my man masifa ka koyo a UK d'in ko?"
hmmm ni yanzun inasan sanin kin shirya aurena ayanzun?"murmushi tayi tace haba sweet heart inada Wanda nakeso da aure Wanda yawuce Kai...kasan befi 6 month ba nagama service d'inaba sai ayi mgn ko"me zai Hana asaka rana bayan 6 month ayi bikin?"b'ata fuska tayi had'e da cewa ah ah daddy bazai yarda fa"ok kawai yace yashareta...marairai cewa tayi tana rarrashinsa da cewa data Ida service d'in sai asaka bikin 2 month kawai...hakan yasa yasaki fuska.suka cigaba da firan soyayya...
*3 days ago*
Kwance take kan 3 seeter tana waya da sameera k'awarta"sai yamutsa fuska take"ahankali tace pls samee in za'a dauki attendance kice bana lfy"kinsan duk month sai nayi wannan ciwon cikin" wlh yau naso nazo skul... kasancewar Abba yasakata skul gab dazai auri mama"yanzun suna 100lavel itada sameerah k'awarta Kuma course d'aya suke karanta...kashe wayar tayi tanata murk'ususu anan harda hawayenta gwanin ban tausayi... subahanallahi! sumayya lfy?"
Cewar Abba dasuka fito tare da mama dg wani dak'i...mama tayi murmushi tace wlh ciwon ciki ne tun jiya d dare...shine Baki sanarmunba?"Abba yakatseta..kayi hakuri alh wlh duk wata haka takeyinsa...bece komai ba.yaciro waya yakira Sadiq yace yazo yanxun part d'in maryam...kashe wayar Abba yyi Yana dubar sumayya Yana Mata sannu had'e da cewa shiga kisaka hijab Sadiq yakaiki asibiti gun my son yaduba minke"sumayya kuwa batasan wa Abba yake nufiba da zaa kaita gunsa "saitatashi tashiga ciki"sadda ta fito tasami Sadiq zaune a parlour Yana jiranta"suna had'a ido tayi saurin sunku yadda kanta k'asa tana cewa Yaya Ina kwana?"
K'afeta yyi da ido bbu k'akkautawa "kafin yace lfy qlau yajikin?
Tace Alhmdllh"
Yace muje parking space"yafad'a Yana ficewa sumayya tabi bayan sa.... alaokacin data iso har ya shiga motar yabude gdn gaba hakan yasa tashige kawai...hakan yafaru akan idon safeena data shigo get gdn....
Innaga comments acigaba kokuji shiru...
Share pls...
Ga link ga masu tambayar suna son shiga grps d'ina..Amma inkinsan bazakiyi comment ba karki shiga Banda maza...
👇https://chat.whatsapp.com/C7p4CLXSUZl7bJQb6ERPgF
By mmn fareesa 🖊️
No comments