YAU DA GOBE 13&14
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🌹YAU DA GOBE 🌹
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & writing by mmn farees
🅿️13&14
.....Wata irin zabura hjy jamilah tayi"Afusace tace danaga wannan ranar gara naga mutuwar Sadiq!natsani Maryam da y'arta"sbd kaf zuriyarmu bbu wacce akama kishiya sai ni"ta mallakeka shima d'ana ya auri y'arta su mallake munshi ko?"hakan bazai tab'a faruwa ba ko byn raina.. tafad'a tana kallonshi ido cikin ido"Abba yyi murmushi me ciwo. kafin yace banyi mamakinkin jin wa an nan maganganun dg bakinkiba"inaso kisani Sadiq nine mahaifin sa dake dashi duk Kuna a k'arkashin ikona! sannan kicigaba da nunawa Maryam k'iyayya karki fasa....katsesa tayi da cewa wlh !wlh!!wlh!!! Muddin ka kafe akan ya aureta to Zan tsine Masa albarka"Koda kuwa aurena ayanzun zai mutu...cike da mamaki Abba kedubar umma"sbd beyi zaton wannan kalmar dg bakinta ba...tashi yyi tsaye fuska asake yace duka abinda kika lissafa bazai faruba!Zaki zauna gdn aurenki sbd y'ayanki"Sadiq Kuma bazai auri sumayya ba"saidai inaso kisani hassada gamai rabo takice! sumayya zata mallaki mijin dayafi Sadiq insha ALLAH Kuma saikin ciji yatsa inhar kikaga Wanda zata aura....hmmmm Allah ko?"yo saime tunda anraba d'ana da jaraba Allah natuba"tunda tayi kwantai dole atura mishi ita... murmushi Abba yyi yace sumayya shekaran ta 20" jidda 23 acikin su wayayi
kwantai?"jamilah sai yaushe Zaki canzane?"to Bari bari kiji Sadiq shiyazo dakansa yace sumayya yakeso"na b'oye mikine sbd nasan halinki" amma ba cusa Masa ita nayiba koki yarda ko karki yarda"inbacin wasu dalilai dasai ta kammala karatunta za'ayi aurenta...tabe Baki hjy jamilah tayi had'e da cewa can matsalar suce "d'ana yamata nisa wlh....girgiza Kai kawai Abba yyi yafice parlourn yabar Mata abincin ta data kamishi...Yana fitowa "hjy jamilah ta nufi part d'in su sumayya sbd akan idonta Abba yahau mota suka fita da driver..."""Babu ko sallama hjy jamilah ta kutsa Kai cikin parlourn"sumayya da Sadiq na zaune Yana koya Mata yadda zatayi amfani da wayarta"ba shakka wlh!hjy jamilah tafad'a tana watsa musu mugun kallo dg Sadiq d'in har sumayya"
Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un... sumayya ta fad'a aranta"Sadiq kuwa gabansa yyi mugun fad'uwa"munafiki Ashe kana nan dama ko?"nan kake zuwa Koda yaushe ni Ina zaton kafita"to wlh Kama sani kasake zuwa part d'in nan dasunan Kai ka aiko kanka ba mahaifin ka ya aikokaba banyafe maka ba?"
Tafada tana kallon sumayya tace ke Kuma algunguma keda uwarki dangin matsiyata kinyi kwantai za'a likama d'ana ko ?"to yafi karfinki"bazan had'a zuri'a da matsiyata irinku ba"wadanda talauci yyima kanta...ko kunzata bansan har wankau da dakau uwarki tayiba sbd talauci...Dan ALLAH umma kiyi hakuri bazan koma shigowa ba muje Kar Abba yazo Dan ALLAH"bazan tafiba sai minafikar uwarta ta fito namata kashedi... sumayya na kuka ta tashi tashige bedroom d'in mama sbd tasan maman najin duk rashin mutun cin da hjy jamilah ke musu...tsaki hjy jamilah tayi cikin d'aga murya tace ai wlh Allah yataimake ku ba part d'aya mukeba dako ruwa bazaku shaba"y'an iska matsiyata"Kuma gd gaku gashi"badai kinyi ciki ba sbd gado zanyi maganinku daga ke har alh..Sadiq rufe idonsa yyi cikin b'acin Rai da wani yanayi"aransa Yana jin da ana canza uwa da yacanza wlh...zaka wuce muje ko kuwa inma asiri suka maka wlh dg yau ya karye.. tafad'a tana kallonshi suka fice dg part d'in...
Mama kuwa duk abinda hjy jamilah tayi tsab taji"bakuma tsoronta yasakata k'yaletaba"tabarta Kiran lokaci"da Kuma jikin dake cikinta"sannan ta fahimci tabbas da Sadiq Abba keson had'a sumayya"inkuma har yasanar Mata gsky bazata aminceba sbd halin uwarsa"amma bazata Masa maganar ba"kallon sumayya dake kuka tayi tace kiyi hakuri kiyi shiru komai na duniya yanada lokaci"YAU DA GOBE in ance tamana hakan bazatayi ba"d'anta kuwa koshine autan maza bazaki auresa"komai yafaru da bawa sumayya Yana cikin k'addararsa!
Share hawayenta Sumayya tayi tana tunanin yaushe zasuyi farin ciki itada mamanta?"sannan tana tunanin kodai Abba aura Mata Sadiq zaiyi sbd gudun karta auri muttala...mama ta katse Mata tunani Gurin cewa kije ki d'auki alk'ur'ani Mai girma ki k'aranta Zaki samu nutsuwa insha ALLAH.
da to sumayya ta amsa tana tashi...
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
Abba kuwa suna fita yace wa driver yakaishi gdn hjy Aysha...byn sun iso angama gaisawa Abba yyi guran murya had'e da cewa hjy nazo da wata mgn dakuma neman shawarar ki amatsayin ki na uwa ga Aliyu!ummi ta gyara Zama had'e da cewa to alh inajinka"Abba yace inaso na had'a Aliyu da sumayya y'ar amaryata aure"sbd wasu manyan matsaloli dasuka taso tsakanin yarinyar da dangin ubanta"har suna k'ok'arin zuwa su karb'e ta dg gun mamanta"sannan nayi tunani yarinyar nan dasuke tare da Aliyu ubanta yacika izzah tamkar bayasan bashi"yanzun Aliyu yakamata ace yanada iyali ,Amma sai yawo da hankali suke Mana"inhar Aliyu zaimun biyayya ya auri sumayya kodaga baya sai ya auri ita waccan din"amma wlh banison ganinsa hakan bbu iyali...ajiyar zuciya ummi tayi tace Masha Allah!alh Ina bayanka d'ari bisa d'ari"sbd wlh tunda na aza idona akan yarinyar nan naji tamun yarinyar ta"saimuyita adduar abinda yafi alkhairi...baki washe Abba yyi murmushi had'e da cewa ameen hjy"sbd dama yasan hjy Aysha nada sauk'in Kai"ummi tace to amma alh ga shawara"dama babana baya gdn bejimaba da fita kazo"in yadawo zance kazo kace yaje kanason ganinsa"inyazo saika fad'a Masa"banason yaji ta bakina"zai iya musawa "amma inyazomun da maganar Zan nuna hakan nada kyau yyi hakuri yamaka biyayya"
Abba yace hakan yyi insha Allah inyazo aturo munshi"ummi tace to alh amma yarinyar baza'a Sami matsala agunta ba ko?"eh gsky sbd insha Allah zatayi biyayya tanada hankali sosai...to shikenan Allah yashige Mana gaba.nan sukayi sallama...
************
Fitowa yyi dg bath room d'aure da towel sai wani rataye awuyansa Yana goge ruwan jikinsa"yanufi gurin mirror"agaggauce ya shirya cikin jallabiya milk yanufi masjid !sbd inyadawo zaije gdnsu rukky kwana2 su gaisa sbd bayason tana zuwa asibiti gurinsa Yana aiki..Koda yadawo shiryawa yyi cikin wata dakakkiyar shadda Fara k'ar ,riga iya gwiwa amma aiki da bakin zare"ya aza hula baka da takalmi sawu ciki... hmmmm Masha Allah duk budurwar data ganshi dole yaburgeta kota k'yasa...lolx sai k'amshi ketaji ajikinsa "SAFANA badai iya wanka ba"kyansa yafito sak abaka nensa...agogon dake daure atsintsiyar hannunsa yaduba yaga 8:12 pm yasaka "yafito yarufe parlourn sa"yanufi cikin gdn...zarah naganinsa dukda tana cikin damuwa saita tuna da musty"murmushi tayi had'e da cewa Kai Yaya wannan zazzafan wankanfa?"murmushi yyi yace kin rainani ko baby?"hmm Yaya Gurin anty rukky zakaje ko?"kafin yace wani abu ummi dake kalonsu tace "tun d'azun nike jiran shigowarka "nazata byn magarib zaka shigo! Dr safana yace eh ummi nagajine sai kawai na wuce ciki"Zan fita adafamun shayi innadawo zansha...
Ummi tace to shikenan! amma duk inda zakaje kafara zuwa gdn abbanku yazo d'azun da marece yanason ganinka...hakan kawai safana yaji fargaba akan Kiran"azatonsa ko kan maganar daya masane kan yabashi 3 month yafito da wacce yakeso...
"Ahankali yace to ummi bara naje d'in"saina dawo!to babana Allah yatsare"Yana murmushi yace ameen had'e da kallon zarah yace baby namiki tsaraba tunda broth d'inki bayanan?"
Eh Yaya wlh ice cream nakeso nakwan 2 bansha Shiba...ohk "yafad'a Yana ficewa..
Da kansa yyi driving d'in"Yana isowa yyi horn"get man yabude Masa get yadanna hancin motarsa ciki...Yana Gama parking yafito...yahango Abba zaune kan resting chairs dake haraban gdn.. directly yanufi gurinsa...bayan sun gaisa Abba yyi ajiyar zuciya cikeda fargaba yace ALIYU!da sauri Dr safana yakalli abba jin ya ambaci ainahin sunanshi"yasan maganar Mai mahimmanci ce"Ina neman alfarma agurinka amatsayina na k'anin mahaifin ka"Wanda ayanzun nine matsayin mahaifin ka duk duniya!cikin gamsuwa Dr safana yad'aga Kai Yana cewa hakane Abba insha Allah zanyi komeye kafi k'arfin neman alfarma guna saidai kabani umarni kawai..Abba yyi murmushi had'e da cewa Allah yayimaka albarka....nasan zakaji abinda bakayi zatoba abakina"inaso Aliyu ka auri sumayya y'ar amaryata"ba masoyi tarasaba ah ah!akwai wasu dalilai masu karfi"ko itama batasan da zancen Zan Mata aureba"inaso inbaka aminceba kamun bayani wlh bazanji haushiba.. sbd adah da Sadiq dake sonta Zan had'a su"to Amma mahaifiyar'sa sbd kishin Maryam tace muddin ya amince zata tsine Masa"kaga kuwa inbaka amince bazanji haushiba sbd d'an dana haifa da cikina an hana yamun biyayya duk da kaidashi duk d'ayane agurina...Ina saurarenka meye kagani??"
Dr safana jin maganar Abba yyi tamkar ankwad'a Masa guduma akansa "yarinyar daya tsana akeson lik'ama aurenta"Kuma suna soyayya da Sadiq? Wata zuface taketo Masa"dakuma yatuna da rukky sai yaji wani irin yanayi marar musaltuwa...Abba ya girgiza Kai Yana kallonsa "kafin yace inhar zaka amince ka aureta bbu laifi dg baya ka auri ita yarinyar dakuke tare"kobaka auri sumayya ba gsky banison ka k'ara wani lokacin bbu aure....cikin k'arfin hali had'e da b'oye halin d'aya tsintsi kansa yace bbu komai Abba Allah yasa hakan shiyafi alkhairi...
Cike da mamaki Abba yace ameen and beyi zaton zai aminceba jin yyi shiru.."tashi tsaye Dr safana yyi had'e da cewa Abba na wuce Saida safe"
baki washe abba yace to my son nagode k'warai"kaji Allah yyimaka albarka"cikin k'aka'ro murmushi Dr safana yace ameen Yana tafiya har ya iso Gurin motarsa yashiga ya ja yabar gdn...Abba yyi murmushin samun nassara...
#########
Cikin damuwa had'e da b'acin Rai"Dr safana keyin driving d'in"sai yanzun yyi nadamar ki'nyin aure da wuri"inda yanada aure bbu Wanda zai lik'a Masa wata wlh...tsaki yaja afili yace laifinkine rukky!kekika jamana"yafad'a Yana canza akalar motar zuwa gd"sbd gaba d'aya bayada kuzarin zuwa wajen rukky"Kuma itama yanzun haushinta yakeji sbd aganinsa itace sanadin komai...cikin damuwa da jin haushi yawuce part d'insu ko gun ummi be shigaba.
Da kyar yyi shafa'i da wuturi yakwanta. Yana ganin miss call din musty Dana rukky yyi burus dasu...da k'yar bacci yyi awon gaba dashi... yyinda ummi ke fargaba sbd tasan tabbas besan maganar tunda ko shayin dayace adafa Masa bezo yakarba b'a ,balle ice cream d'in daya ce zai siyama zarah..saidai ummin ta duk'ufa da adduar zabin alkhairi agurin ALLAH!
*Washe gari*
Dr safana be shigo gdn ba sai 7:40 am"a dining area yasami su ummi yagaida ita"zarah ma tagaishesa tana k'ok'arin masa tuni akan ice cream d'in ta "saidai ganin mood d'in sa yasa taja bakinta ta tsuk'e "aranta tace yau y'an hospital sun shiga ukku"
Ummi ta dubesa ganin be zaunaba tace kazauna kayi Karin Mana!
Cikin wani yanayi yace ah ah nak'oshi, yafad'a Yana dubar zarah fuska a'daure yace ke tashi zamuyi mgn..sum sum zarah tabar Gurin da sauri...Zama yyi kan d'aya dg cikin kujerun table d'in"murya asark'e yace pls ummi Ina cikin damuwa!Abba yabani umarnin zai auramun yarinyar nan y'ar amaryar wlh ummi bana sonta...tamkar gaske ummi tace subahanallahi"baka santafa kace?"Toni meye nawa aciki "bagara kayi aurenba "daka zauna jiran wannan yarinyar da har yanzun bata Gama karatun da ubanta yace ba... marairai ce murya yyi had'e da cewa dan ALLAH ummi kimasa mgn yajanye wlh yarinyar batamunba"zaro ido ummi tayi had'e da cewa"lallai ka isa meya hana sadda yasanar maka kace bakaso saini zaka turako?"to bari kaji tun kana k'arami alh Usman kesonka da shagwaba ka"sai Dan yanzun Yana umarni ke bazaka iya Masa biyayya"ayanzun tunda mahaifin ka yarasu kanada uban daya fishine?"ni inaji ajikina insha ALLAH auren nan alkhairi ne! na haneka da cewa baka sonta ko bata maka"sbd da yawa abinda mukeso muka k'wallafa ranmu akanshi ba alkhairi bane"Wanda Kuma bamaso shine yafi alkhairi agaremu...itama ai basonka takeba ko?"sbd haka ita wacce kakeson ubanta namaka yawo da hankali nan gaba inya gadama yabaka ka aureta...shiru kawai Dr safana yyi Yana sauraren ummi ta inda take shiga batanan take fitaba"yalura tana son auren d'ari bisa d'ari.. ahankali ummi tace ni aganina babana kayi hakuri kayi biyayya insha Allah zakaci riba"karik'e yarinyar nan da gsky inaga shiyafi maka"inkuwa ka kafe to saidai kaje da kanka kasanar Masa bakaso ,amma ni bazan iya ba"inkuma har kasanar Masa natabbata k'imar dayake kallonka da ita ta zube...ajiyar zuciya Dr safana yyi had'e da cewa shikenan! yafad'a atakaice Yana ficewa abinsaa...ummi tayi murmushi tace ai wlh gara ka aureta da ama lik'ama jidda da uwarta ke suntirin turowa"saidai nasan muddin hjy jamilah taji wannan mgn akwai aiki agaba...
Bangaren Abba kuwa yasanar ma ma "Wanda yatsaba ma sumayya amatsayin mijin aurenta"mama kuwa taji dad'i sbd ta yaba da hankalin Aliyu"sannan Abba yace karta sanarma sumayya shizai gayamata da kansa in ankwana2... sannan da kansa yaje gun baba Iliya yasanar Masa komai da Kiran da binta tayiwa mama game da zuwan su baffa habibu...
*bayan kwana5*
Musty ne zaune aroom din daya sauka "yanata aikin kallon pics d'in zarah dake awayarsa....mamaki yakeyi kusan kwanansa nawa kowa nakiransa agdnsu amma banda ita"contact yashiga ya lalibo *my heart* yyi calling d'inta...zarah na bacci ma Gurin 12 na safe" Kiran yatayar da ita!tana duba wayar taga my broth"turo baki tayi had'e da hararar wayar tace kaida ka manta dani meye na kirana?"katsewa tayi yasake Kira"d'agawa tayi"yasaki ajiyar zuciya aboye"kafin yadaidaita muryarsa yyimata sallama!ta amsa hade dayin shiru"lumshe ido yyi sbd dama muryarta kawai yakeson ji"baby dama ummi nikeson mgn da ita nakirata bata shiga"dit ta kashe wayar cikin jin haushi"wato bama ita yakira yaji lafiyarta kenan "ai ummin nada waya saika kirata "amma bada wayar zarah ba, tafad'a tana kashe wayar baki d'aya...
Dr safana ne zaune a office nasa yyi zurfi atunani"sbd ganin da gaskedai aura Masa marar kunyar yarinyar nan za'ayi(sunan dayake Kiran sumayya dashi) tunda jiya Abba yakirasa yasanar Masa ansaka ranar auren nanda wata 3"d'azun Kuma ummi tace ana gidan zasu zauna yasiyi fili dake bayan gdn yaturo ciki amusu b'angarensu sbd taga kalar zaman dasukeyi... gashi ko rukky besanar mataba "balle amininsa Nasir...sak'a da warwara kawai yakeyi....Wai kanka d'aya safana?"cewar Dr Nasir daya shigo yanata sallama amma ,yyi zurfi atunani bejishi ba...ajiyar zuciya Dr safana yasaki "had'e da cewa zauna inasan ganinka Ina cikin matsala wlh"yafad'a azuciyar sa na k'una... subahanallahi!to Ina jinka Allah yaka mana da sauk'i"cewar Dr Nasir Yana kallon SAFANA..
Cikin jin haushi Dr safana yayiwa Dr Nasir bayanin auren da Abba zai Masa "dakuma K'arin haushi da yarinyar daya tsana....wani farin ciki Dr Nasir yaji"jin Wai sumayya Dr safana zai aura"amma dayake yasan halin abokinsa saibai nuna farin cikin ba"ahankali yace to meye aciki?"kayi biyayya kawai mutumina"nasan Kuma kana buk'atar auren ai...harara Dr safana ya watsamasa had'e da cewa in Ina buk'atar auren ai yarinyar ba choice d'ina bace ko?"hmmm safana kenan watarana YAU DA GOBE zaka sota harta Zama choice d'in ka....mitsss Allah yakiyaye nasota"me akeyi da bak'ar mace?"dariya Dr Nasir yyi yace wlh ka yarda ko karka yarda sumayya tafi rukkin daka k'wallafa aranka komai"kawai banbancinsu ita ruky farace...kaikuma kanason Fara! hararar sa safana yyi had'e da cewa Ashe dai akwai banbancin"banason bak'ar mace"
Dr Nasir yace hmmm ai sumayya bata cikin bakak'en Mata"ita chacoolate colour ce"irin colour d'in dake wuyar samu acikin Mata.... sannan wlh sunfi ni'ima da wuya kasami bak'ar mace batada ni'ima saidaiko inbata kula da kanta"Kuma kasani tunda Kai likita ne...tabe Baki Dr safana yyi had'e da cewa niba fannin komai na Mata na karantaba"sabanin Kai da fannin Mata kawai ka karanta"hmmm naji kadai daina cika baki"Allah yasa alkhairi yakaimu lokacin kawai shine yafi ka hakura...
Shiru Dr safana yyi Yana yatsina fuska had'e da yin tsaki yyi kwafa yace wlh zatasan abinda tamun inta shigo hannuna... murmushi Dr Nasir yyi had'e da cewa kadai rik'e musu y'a da amana"ohni safana ka kusan shiga dg ciki... hararar sa yyi Yana tab'e baki had'e da cewa nafi k'arfin abinda kake tunani"rukky Kuma daba'aso na aura Zan aureta...hmmm abokina kenan kaida bakada tsarin mace 2"tsaki Dr safana yyi had'e da cewa to yazanyi"amma saina Mata abinda da kanta zata nemi saki bayan aurenmu na zauna da my rukky!kadaiji tsoron Allah wlh nidai shawarata"yanzun ba wannan ba yaushe zamuje zance narakaka?"Dr Nasir yafad'a cike da tsokana Yana murmushi...wani kallo Dr safana yyi Masa had'e da cewa fitarmun a office!Dr Nasir Yana dariya yace bbu damuwa insha Allah saikaso sumayya SO Mai tsanani wanda ko kwatansa bakama rukky ba..banza safana yamasa sbd yakaisa karshe...
**********
Afusace hjy jamilah ta shigo bed room d'in Abba tamkar zata tashi sama"jikinta na kirma tace alh!wani kallo Abba yajefeta dashi sbd yasan be wuce ace taji saka ranar Aliyu da sumayya ba"cikin ko inkula yace lfy?"
Inafa lafiya wani mugun labari naji shin da gaske ne kokuwa k'aryane Wai sumayya zata auri Aliyu ?"
Murmushin jin dad'i Abba yyi yace eh"kozaki hanane kamar yadda kika hana d'anki?"yafad'a atakaice sbd yasan zataji bak'in cikin dayafi Wanda yaji sadda ta nuna be isa da d'ansa ba... musammun tunda yasan burin ta jidda ta auri ALIYU....
Share
By mmn fareesa 🖊️
No comments