Breaking News

DIJA QAYA 4

 🌿🦋🌿🦋🌿🦋🌿🦋🌿🦋

            *DIJAH QAYA*

  

🌿🦋

           *page* 4⃣



Abinci kal2 Nuratu k'anwar Amira ta gabatar musu;Ko ruwa basu shaba, had tafito Riga da sket ne ajikinta na atamfa, da hijab d'inta har gwiwanta, balaifi tana da kyau dai2 gwargwado,


Tunda tayi sallama tazo tazauna, batace komiba, kallon kallo sukashigayi tsakanin Kabir da Habib Kabir yad'an dunguri Habib Alamun wai yayi magana shima dungurinsan yayi wai shi yafarayi,


Kabir yasaci kallonta  da gefen idonsa ta takure gefe guda kanta ak'asa ya kalli fuskanta tasha kwalliya sosai, 


Hanunsa yasa yatab'o Habib k'asak'asa yamishi nuni da fuskanta, Habib ya d'ago ya kalleta gaba d'ayansu suka kwashe da dariya,


Amira da batasan meke faruwaba sosai ta tsorata har tafara tunanin to kodai ba dai2 sukeba 


Kabir yayi gyaran murya yana kallon ta yace "sannu "yanmata ba gaisuwane? Sai alokacin tad'an nitsu ta kallesu ina wuninku, dariya suka kuma yi yanzu kam ta fahimci rainin hankali suke mata don haka ta d'aure fuska tana kallon hanyan waje


Kabir yayi gyaran murya " mnnnh dama dai munzone wajenki da niman aure ba wasaba don gaskiya kinyi Wa Abokina, 


Shiru yakuma baya suka kalli juna sanna yace so yanzu dai munmiki? Ko ba Mu mikiba? Ma'ana kina son Abokina? 


Wani irin haushi ne Yakama Amira wannan wasu irin shashashu ne? Afuska gashj anaganinsu anga wayyayu masu aji,

Amma sumata irin wannan shirmen maganan tun yaushe akabar irin wannan  Hiran? 



D'an gajeren tsaki tayi a iya lips d'inta 

"Pls say something mana "yan mata muryan Habib ya katsemata tunani 


'Kara sunkuyar da kai kawai tayi don bataji aranta zata iya maganaba, 


Zaman kurame sukayi tsawan 5 minutes Habib yace to tunda kin kasa mgana Mu zamu tafi, ai bai k'arasaba ta mik'e tafara tafiya 

Habib. Yace "mnnm kituro mana k'anwanki da sauti tad'aga labule ta fita kicib'us sukayi da k'anwanta gefenta tabi ta wuce ta tafi ita kuma tashiga da niyan gaidasu,


Bayan sungaisa Habib yace "wai Akwai wata k'awan Amira kusa daku nan ko? tace "eh tana gidannan ma, "yauwa yimana magana da ita "OK to tafita, 


Kabir yayi fuska yace "kai karfa ka rainamin hankali wlh  ba ruwana da wata yarinya dai2 lokacin ta shigo da Sallamanta ita ma irin shigar k'awantan tayi, bayan sun gaisa ba b'ata lokaci Habib yagabatar mata da Abokin sa amatsayin manimin aurenta Asaba'in ta kallo KB jikinta har b'ari yakeyi aranta tana Ayyana irin sa'anta ita da haryanzu bata da k'wak'wk'waran saurayi Ace mutum kaman KB yazo niman aurenta? ita koyau Ina zata saka kanta Dan murna, 


Cikin rashin sa'a tad'ago kai tana murmushi sukayi  ido biyu da KB ya mata kallon baki da hankali, Habib sai dariyan mugunta yakeyi, KB ya tashi yana kallon Habib inkagma zuban naka kasameni a waje daga haka ya fita, 


Asanyaye Aliya ta kalli Habib tace "Anya kuwa dagaske  yana sona Habib ya mik'e yana fad'in karkidamu haka halinsa yake tun Muna yara, ba'a gane abun da yakeso da Wanda bayaso Amman dai kiyarda dani yana sonki bari Mu wuce zamu dawo,


Tare suka fito alokacin KB yana shirin fita Habib yayi wuf ya bud'e motan ya shige,


🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴

Shiru yayi yana sauraran muryanta duk da ba filatanci yakejiba amma ya fahimci akanshi take magana cikin nitsuwa ya k'araso inda take zaune hanusa rik'e da Bakin Allurai, ya kalli Baffa yana murmushi yace "Baffa sai Alluran ne bataso?  "Hahh Dijah da tsoro Allura daga gani a hanunka shine take magiyan kar amata Baffan yafad'i haka don bazai iya fad'amasa Abun da ta ke fad'a akansaba, 


Murmushi yayi cike da zolaya yace "wannan ba Allurankibane Amma tunda kina so zansa amiki d'aya, 


Cike da tsiwa ta murgud'a baki "nidai wlh baniso na warke ba Alluran da za'amin,


Tsayawa kawai yayi yana kallon bakinta ahankali yafara tunota yarinyannane  marar kunya Wanda suka tab'a had'uwa arugan juma ta mishi rashin mutunci, tabbas biri yayi kama da mutum tunda tafarfad'o take masa kallon kamar tasanshi, wato shine data ganeshi take masa kallon raini haka? Tuno maganan da wani saurayi yagayamasa arugan yayi   


*Dijah bukar med'ori kenan yarinyace maihankali sai dai akwaita datsiwa inkashiga hark'anta gashi bata da hak'uri, bata manta abu komi Kamata saita rama ko ta d'au fansa*  


tsaki yaja yajuyamata baya ahankali yace k'arya ne yarinya kinyi kad'an baki kai kiyi wasa daniba yaushema aka haifeki? Ko can dakikamin nabarki, gani nayi bakikai intsaya yi da ke bane; 


 

Baffa ya matso gaban Dr kB yace "likita don Allah kasallamemu  tunda taji sauk'i  murmushi yayi yanashafa k'irjinsa  "OK Baba yau d'innan za'a sallameku insha Allah, yajuyo da kallonshi ga Dijah ya na mata dariyan mugunta gami da kallon zakisani, 


Yakalli Alluran da yake hanunsa ya kuma kallonta yace "za'a k'arasa mata Alluranta "to kawai Baffa yace sannan yafita Dan yin sayyayan da yakesonyi yatafi dashi  gida Cikin takunsa na izza ya matso daf da ita yahad'e fuska Yana kallon tsakiyan idonta, ya lashi lips d'insa meye ma sunanki? *Dijah k'aya* ko? Sunan da "yan k'auyenku suke k'iranki da shi, ya jijjiga kansa "kinga ikon Allah ko? kin tuna alokacin da kikamin rashin kunya a k'auyenku? Yau gashi Allah ya kawoki hanuna, ya juya ya fita Jim kad'an ya dawo da Allura ahanunsa, ina hannunkinan da yamin B'arna mik'o shi yafad'a yana zabga mata harara,



 Dijah  tuni ido ya raina fata Sai b'ari takeyi amma idonta bai huta da hararansaba, sai b'oye hannayenta takeyi tsakanin cinyoyinta, shi kuma yana tsaye k'yam kallonta kawai yakeyi 



Ahaka Baffa ya traddasu, "yau likita anmata Alluranne ya tab'e baki tak'i amata kuma bazai yiwu asallameku ba amataba, Baffa ya matsota yadafa kanta haba mamata akamiki baunda yafi Allura zafi, bare Allura kiyi hak'uri amiki ya wuce muyi Mu tafi yau zaki ga innanki insha Allah, taso tasanar da Baffanta cewa Alluran zalunci zai mata bana gaskiya ba sai dai tasan Baffa bazai fahimcetaba don haka kawai ta fashe da kuka ya jima yana rarrashinta sannan ya kalli Dr KB da yake tsaye yana mata wani irin kallo "bismillah likita yimata mutafi matsowa yayi yana mata Alama da tabashi hanunta bayan da ta iya ta mik'o hanunta yana totson lips d'insa yace "atafin hanun za'ayi, Baffa kanshi Abun yabashi mamaki Allura a tafin hannu? 



Bai kawo komi aranshiba ya zauna kan kujera yana kalle2 sauran marasa lfyn da suke sauran gadaje,



Cike da mugunta da son ganin gudun ruwan ta ya cakka mata Allura a tafin hanunta har waje biyu sannan ya koma gefe yana kallonta,



Azuciyansa yace bake baki da kunyaba? Kuma wai komi akamiki sai kin ramaba? Tom ina jiranki, ya jawo foldernta yayi rubuce2 aciki yace "shikenan Baba Akula da shan magani da dokan da akamata zata warke insha Allah, daga haka yafice batare da yaji daga Bakinsa ba, 



Mama jummai ta shigo da sauri ta k'arasa wajen Dijah tadafa kafad'anta "haba Dijah keda yau zakije kiga mamanki meye naki na kuka? Kiyi shiru abinki maza zo muje kiyi wanka, tajata suka fita,




Kayanta da tazo dashi ajikinta tasaka Riga da zani farare  k'al irin na fulani Baffa yana tsaye abakin k'ofa suka iso ita da mama jummai, sallama ta musu da fatan samun k'arin sauk'i 


Baffa yace mata ta nuna ma Dijah office di'n likita ta mishi godiya, don d'azu yazo mata sallama tana wanka, taso tak'i zuwa sai dai bata saba yima Baffa musuba  don haka tabita, da hanu mama jummai ta nuna mata office d'in ta wuce abunta, 




a tsorace ta tura k'ofan ta shiga sai zaro ido takeyi yana zaune a cikin kujera yana aiki da lap top kallo d'aya yamata ya dakamata tsawa "ke "yar k'auye meya kawo ki nan wani irin harara ta bishi dashi batare da tace komiba,  a fusace yafara danna k'ararrawan k'ira wasu masu sharane guda biyu suka shigo kufitar min da wannan abar anan sercatif problem ne da ita Ku mai data can layin mahaukata inaga daga can ta k'wace tazo, ai asaba'in suka d'auketa cak suka fita da ita sai tirje2 takeyi tana kuka amma sai da suaka kaita,




Wata nurse suka samu awajen tana zaune tana ganinsu ta mik'e tazo wajen tana tambaya, dayan matan tace "daga nan tafita garin yaya kuke barinsu suna fita  office d'in Dr KB tashiga, nurse d'in ta kalleta cike da tausayi tace "gaskiya bansan da yarinyannan ananba inaga tun banzoba tafita,  juyawa sukayi suka tafi abunsu, cike da tausayi nurse ta jawota itakuma sai kuka takeyi tana tirjewa, akan wani kujera ta zaunar da ita ta jawo ruwan Allura zata mata,




Cikin matsanan cin kuka ta durk'usa ak'asa hanunta na bari tace "don Allah sister kiyi hak'uri wlh ni ba mahaukaciya bace sharri akanmin wlh niba mahaukaciya bace, cak ta tsaya tana kallonta, Dijah ta rik'o hanunta Allah dagaske niba mahaukaciya bace Baffa na yana waje yana jirana,  "kintabbata? dagaske kikeyi, wlh dagaskene sister inbaki yardaba muje kiga Baffa na zai miki bayani,



Nurse d'in tana rik'e da hanunta suka fito fuskanta sharaf da hawaye, Abunda ya bama Dijah mamki shine hango Baffa da Dr KB datayi, harshine ma yake nunama Baffa ita da alamuma yataya Baffan nimantane nurse dince tayi sallama tun kafin Su Amsa sallaman Dr KB yamata kallon don't say any thing, don haka shiru tayi batare da gane komiba, 




Baffa ya kamo hanun Dijah yace " haba mamata da baki gane office d'in likitanba bazaki dawoba? Sai kije ki shige wani wuri kisani adamuwa? Ina ta nimanki, 



Ya kalli nurse d'in yace "mungode ko, "bakomi tace sannan ta juya batare da tace komiba, tunda anyi waning nata



Dijah kan ko kallon inda KB yake batayiba ta wuce tayi gaba nan tabar Baffa sai godiya yakeyi ma Dr KB





*tofa wai kan meye tsakanin Dr KB da Dijah ne? Shin wani mataki yanzu Dijah zata dauka tunda ance ita bata barin ta kwana?* 



*ku biyoni* ..........................






*HAUSA NOVELS* 📚

*HAUSA NOVELS* 📚📚

*HAUSA NOVELS* 📚📚📚

No comments