Breaking News

DIJA QAYA 21

 🌿🦋🌿🦋🌿🦋🌿🦋🌿🦋

            *DIJAH QAYA*

            *page* 2⃣1⃣

 Sani yayi kamar bai jishiba aransa yana addu'an Allah ya nunamasa randa zaikama Kabir da wannan furucin dayadad'e yanayi, Kwanciya yayi luf acikin sit d'in yana kallon motan  Mami da yake tafiya kaman bazai tafi, Don sam Mami bata yarda ayi agudu da ita, shiyasa har yau tak'i canja tsohon drivernsu,  juyawa d'ayan gefen yayi yana kallon motan seceurity sum airin tafiyan sauran motan sukeyi, yaja d'an gajeren tsaki afili yace "Wlh na matsu inganni acikin d'aki na gaskiya nayi missing Bed d'ina over, Sani ya kalli agogon Hanunsa,  ka kwantar da hankali Minti goma kacal ya rage insha Allah,



Wai Kb wani mataki zamu d'auka akan Alhaji ya'u ne?


"kafa iya ma bakinka nagaya maka banison Mami tagane cewa yana da Hanu cikin maganan har sai kungama binciken ku kun gano kome.


Sani ya d'an kalleshi "kana nufin har yanzu baka gamsu bane? Duk hujjojin dana baka basuyi bane? Najima ina zargin Alhaji ya'u cikin son ganin yaga bayanka, sai gashi zargina yazamo gaskiya yanzu da abunnan yafaru wlh ranan da suka tsare motocinmu da idona naga gayannan lokacin da yabi Motanmu yana Harbi sannan kuma da idona yanzu nake ganinsu tare da Alhaji ya'un,



Sannan naji da kunnena suna hiran bayan maganan da Nafisa tagayamin yagaya mata, 


Bai kamata azuba masa idoba Kabir yakamata ada'auki mataki,


Kabir yad'an Murmusa yana kallon waje yace "Tun kafin ka gayamin wannan magana nida Habib munsan komi, sai dai inason abi komi ahankaline, ko bakomi ubanane shi sannan kuma ina sa ran auren "yarsa don inason cikama Mami ta Burinta, don bata da Burin da yawuce haka.


 Tunda mai gadi ya wangame Gate d'in gidan, Kabir yake ta murmusawa har suka faka aka bud'e masa k'ofa yafito pert d'insa ya shige kai tsaye,  komi na part d'in agyare yake fes dashi har yanzu k'amshinsa yana nan kaman koda yaushe, afili yace "wannan aikin Mami tace, uwa ta gari Allah yabani daman cika miiki burinki koda Hakan yana nufin Bak'in cikinane, indai ke zakiyi farin ciki shikenan, 


 Yana shiga Bed room ya zube akan gado ya lumshe ido yana shak'an iskan dake shiga da fita ad'akin, photon Dijane yazo masa idonsa siraran Hawayenta da yake sintiri akan  fuskanta yake gani da sauri ua zabura yatashi ya zauna afili yaja tsaki yace "stupid girl, ya mik'e yana k'ok'arin rage kayan jikinsa aljihunsa yaji abu ya ciro zobe da Hamsind'in da Goggoji ta bashine yayi Dariya yana girgiza kai ya zubasu akan Mirrow,   ya shige toilet,



       *Bayan sati d'aya*



Zaune yake akan kujeran k'ofan shiga part d'insa ya d'ora k'afansa d'aya akn Table d'in dayake gabansa yana waya da abokan aikinsa, kan yanda tafiyansu zata kasance, nan da sati biyu,  Motoci ne guda biyu suka shigo gidan kusan ajere, d'aya nasu Abban Habib ne da uncle Musa d'aya kuma na Alhaji ya'u maida kansa yayi yaci gaba da wayansa batare da yakalli fitowansuba, 


Yana gama wayan ya tashi yashiga lambun gidan yana zagawa,  jin wani abu yakeyi aransa mai kama da kewa,  Sannan wani sashi na zuciyansa yana kamomasa photon irin shak'iyancin da Dijah takeyi yarasa meyasa hakan ke damunsa, yana cikin wannan Tunani yaji wayansa tana Ringin yana dubawa yaga Mami ya kara akunnensa, "kasameni afalo ta fad'a atak'aice sannann ta kashe batare da taji me yaceba,



Zaune suke su biyu akujera d'aya Alhaji ya'u yana fuskantansu, yayin da Mami take tsiyaya Ruwa agaban Alhaji ya'u, ta koma ta zauna shikuma ya d'auka yafarasha yana d'an mata wasan da suka saba (wasan k'anin Miji, ) dai2 Lokacin ne kuma Kabir yashigo da sallama,  har ya iso tsakiyan Falon Alhaji ya'u yana shan Ruwa, Kabir yasami guri ak'asa daf k'afan Mami yazauna, tas sukaji k'aran fashewan cup agurin gaba d'ayansu dama shi suke kallo ban da Mami da take kallon Kabir, Gaba d'aya ya dirieice har yafara tunanin ko magarki yakeyi, wani irin zufane yake ketomasa ta ko ina, jiya2 yagama narka mak'udan kud'i wajen canja takardun cpanin Kabir d'in yana mafarkin campani yazamo nashi sai gashi yayi mafarkin ganin mai campanin,  


Cikin tashin hankali yanuna Kabir "Dama kanan ataye?


Kallon2 Abba sukayi shi da Uncle Musa, Mami tad'an Nisa tafara magana "kayi Hak'uri Dadinsu tun randa muka dawo da Kabir nake k'iranka awaya, dama nafidon sai kazone gaka gashi inshaida maka yanda akayi, Kabir yana raye bai mutuba dam..


Dasuri Uncle Musa ya katseta ganin zata ruguza musu plan,  "Eh tabbas Kabir yana raye Dama hatsari yayi ahanyan Abujah likitoci suka tsinteshi kasancewan sun sanshi yasa suka rik'eshi agunsu basu sanar da kowaba, kodayake sun kaffa hujjan hakan dacewa yasamu matsalane ak'wak'walwansa, 


Har saida sukaga yafara warkewa suka sanar damu, tunda aka dawo dashi aka k'ira akan kazo kaga d'anka yana raye bai mutuba, baka samu zuwaba sai yau.



Cike da mamaki Mami ta kalli d'an'uwanta dan batasan dalilinsa na b'oyema Alhaji ya'u zancenba, a ganinta ko za'a b'oye ma wani shi bai cancaci a b'oye masaba.



Shikuwa tsaban Rud'anin da yashiga daga farko bai ji abunda akecewaba, sai kalman k'arshe yaji wato Karbi nada matsalan k'wak'walwa, 


Ganin irin kallon dasuka shiga masane yasa yawayence cikin k'arfin Hali yafara fad'a ta inda yake shiga banan yake fitaba, ya tashi yana fad'in shikenan tunda kunnunamin niba kowabane awajen Kabir saidai kurik'e aranku ina da rana zaku nimeni komin jimawa, haka yafice ko gani baya yi da kyau, yana karad'e hanya ya isa Mota,



Kan Kabir nak'asa yanajin yanda Mami take complain d'in sam basu kyauta masa ba sosai suka fahimtar da ita cewa hakan duk a rarrashin kar yad'auka da zafi ne,



  Bayan sungama ne Mami tasanar dasu Waliman da take shirin shiryamasa in ya dawo daga tafiyansa,




 Da dare Kabir yana zaune afalon Mami suna Hira  Habib yashigo da sallama Mami ce ta amsa cikin fara'a tanamasa Sannu gefe ya zauna suka gaisa, ya kalli Kabir da idonsa yake kan T.v yace Wai kai har yanzu baka canzaba? Yanzu dirowana garinfa nazo dubaka kana wani shanmin k'amshi, 

 


Kabir ya harareahi yana tab'e baki, "tom ni nak'ira kane? Kona ce kazo ka dubani? 


 "kadai ji dashi gurgu kawai, yafad'a yana mai da dariyansa,  ya mik'e yana kallon Mami da take musu dariya,  "Mami yau me aka dafa agidannan?  


Kabir ya manna bayansa da jikin kujera yanata murmushi, ta wutsiyan ido Habib yake kallonshi yana cin abinci.



Ikon Allah ne kawai yakai Alhaji ya'u gida dan baimasan irin tuk'in da yakeyi ba,  ko gama perkin baiyiba ya bud'e murfin Motan ya fita   a fallo ya tarar da Matarshi tana ganinsa ta mik'e cikin damuwa take tambayansa,


Ko sauraranta baiyiba ya ciro waya bugu d'aya kila ya d'auka, 


"Kai Kila nagaji da rainin Hankalin da kakemin dama baka kashe Kabir ba kacemin ka kasheshi?, 


 "What? Meka ke nufi Alhaji?  Kodan baka gama bamu kud'inmu bane yasa kafito tanan?  Kamar yadda nagayamaka ai Kabir saidai uwarshi ta haifi wani, amma shikam yayi nisa, 


Cikin zafi ya katseshi da kai kar kawomin maganan banza zanyi maganinka, daga Haka ya katse wayan, ya zube kan kujera,


Rabi ta k'araso tazauna gefensa tana tambayansa, nan ya gayamata komi, 


Tad'an kalleshi to Alhaji ka kwantar da hankalinka mana kuyi magana na fahimta kai da Kilan wlh nikaina na matsu ayita ta k'are muci dukiya musha dukiya mu kwanta akan dukiya, 



*Oh Allah Duniya budurwan Wawa Allah yasa mufi k'arfin zuk"atanmu*


Kar kugaji kubiyoni har yanzu ba afaraba,😂..........................






*HAUSA NOVELS* 📚

*HAUSA NOVELS* 📚📚

*HAUSA NOVELS* 📚📚📚

No comments