DIJA QAYA 18
🌿🦋🌿🦋🌿🦋🌿🦋🌿🦋
*DIJAH QAYA*
*page* 1⃣8⃣
Abun Duniya duk ya taru ya dami Alhaji Ya'u yarasa inda zaisa kansa har yanzu mafarkinsa yak'i yazama gaskiya, Bashi da buri aduniya daya wuce ya mallaki Dukiyan Kabir amma abun yaci tura, ada yana ganin kashe Kabir shine masalaha saidai yanzu yana ganin yayi wauta dayawa, ayanzu dai gashi ya halaka Kabir Amma Haryanzu burinsa bai cikaba, baisamu koda takarda d'ayaba na dukiyan, sannan Mamin da yakeso ya aura aikin boka yak'i tasiri akanta Ga yaranshi guda biyu dayaci burin suyi karatu Su zamo Abun kwatance abu yagagara, Aminu kam yagama lalacewa da shaye2 ga Nafisa tak'i karatun dayakashe mak'udan kud'i dantayi yanzu tazama saidai wannan samarin ya d'auketa wancan yad'auketa, wani abun Haushinma akan idonsa,
Inyace tafito da Miji tace KB take jira tunda haryanzu ba aji labarin mutuwansaba.
Wani hucin iska ya furzar, zuciyansa kaman wuta, dan takaici,
Wayansa yad'auka yayi d'an danne2 sannan yakara akunnensa, cikin fad'a yake magana, "Nacuceka ko kacuceni kai kace zaka samomin Boka yamin aiki danaje wajen Fatima duk abunda nace tayi zatayi,
kasani naje nasameta nace takawomin duk wani duccument na Kabir, sai gashi yayanta yashigo maganan har da shirin makani akotu, shiru yayi na d'an lokaci Sannan yace no yanzudai kawai so nake akashe Alhaji Musa yayanta inkungama dashi Fatima bazata gagareniba tunda angama da Kabir daga Haka ya ajiye wayan yanajin k'warin gwiwa,
🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴
Yau take Alhamis, matasa maza da Mata suna ta shirye shiryen Gobe juma'a Ranane da aka tanadar da wasannin Al'adun FULANI kala kala, Wanda k'ak'anan Rugan dasuke kewaye dasu suke zuwa ayi dasu.
Tun jiya Iro yakeba KB labarin yanda ake gudanar da wasan.
Kud'i sosai KB yabashi don yin nashi.
Tun da aka dawo daga Masallacin juma'a Kabir yake zaune akan kujeran Roba a k'ofan gida cikin kwalliyan shadda sky blue, Da Bak'ar Hula da tasha kari, bak'aramin kyau yayiba, shiyasa yawancin Masu Wucewa suke shagala da kallon sa.
Shikam Kallon yafara isansa don Haka ya mik'e da nufin shiga Gida,
Dai dai lokacin Baffa ya iso akan kekensa.
Da sauri Kabir ya matsoshi yana masa sannu.
Cike da fara'a Baffa ya amsa, yad'ora da "naji dad'in ganinka anan Likita,
Yanzu mukayi waya da Hajiya, take cemun wai ka matsa akan wai zaka koma asatinnan,
Cikin girmamawa Kabir yace "Wallahi kuwa Baffa Asibitin danake aiki Suna da buk'ata na Sosai kasancewan gaba d'ayan Asibitin babu Wanda yakaranci fannin dana karanta,
Tun barina wajen ba Wanda yamaye Gurbina Har yanzu saidai afita waje,
Shiyasa nakeson inkoma tunda naji sauk'i,
.
Baffa ya jinjina kai bank'i makaba Kabir sai dai zuwan Kawunka na kwanan nan yatabbatar min da cewa zaka d'an zauna anan dai dai agama gano masu Hanu cikin abumda aka maka,
Kayi Hak'uri kaji nasan dole kagaji kodon yanayin Rayiwanku tasha banban danamu.
Meya hana d'an'uwanka dawowane?
"Mahaifiyar shi ce bataji dad'iba, Anma da sauk'i inaga Gobe ko jibi zai zo insha Allah.
Baffah yace "Ayyah Allah yabata lafiya.
Dai dai lokacin Dijah tafito zata shiga Gidansu Jebu, Baffa yace "yauwa Ga Dijah kuje ta nuna maka Gari, inaga zaman waje d'ayane ya dameka,
Daga haka ya shige ciki yabarsu anan,
Kabir Sam baiji dad'iba aransa, Dan baya k'aunan abunda zai had'a Inuwansu da Dijah,
Itakam sosai tashagaltu da kallon kb ba k'aramin kyau yamataba, Ahankali Kabir yad'ago ya kalleta, ya maida idonsa k'asa, ga yarinya har yarinya kyau da kyan fasali, duk Allah yabata Ga sweet voice, Sai Hatsabibanci,
Sake Binta da kallo yakeyi kayan FULANI ne ajikinta dark blue fuskanta ba wani kwalliya daga powdar sai kwalli sai d'an jam bakin da tashafa.
Cikin kasallaliyan Murya tace masa "Mutafi, sake kallonta yayi jin voice d'in datayi maganan dashi,
wuce wa tayi yabi bayanta, ajere suke tafiya ahankali kaman masu niman wani abu ak'asa.
Sund'anyi tafiya kad'an ya zauna akan Dutsi agindin wani Bishiya, danshi sam baiyarda da Dijah ba yasan k'aramin aikintane ta cusashi wani gurin.
Saida tad'anyi nisa sannan ta lura da baya bayanta.
Can tahangonshi zaune yana Kallon masu wucewa, "Lallaima wannan gayen ya rainani wallahi badon kar yab'ata Baffa yamin fad'aba da tafiyana nayi, tafad'a tana dawowa, agabanshi ta tsaya tana mishi wani kallo, Ganin bai ko kalli inda take bane yasata matsoshi, tace "katashi mutafi wallahi ko inyi tafiyana, kab'ata ba Ruwana dondai nan ba birnibane,
ai bata rufe bakiba ta hango kuliya yana zuwa inda suke wayyo Allah na!! Tafad'a atsorace ta juya zata gudu, cikin zafi ya cafkota yadawo da ita gabanshi, jikinta na b'ari tace "Don Allah kasakeni intafi wallahi banison kule, ta juya tana kallon kullen har yanzu gun yake zuwa, ta juyo ta kalli Kabir Murmushi yakeyi alamun zai mata mugunta, tahad'a Hununta Biyu tana matsan k'olla "Don Allah d'an Birni kayi hak'uri kasakeni in tafi, wani Murmushin muguntan yakumayi
"Waye d'an Birni?
Bakisan sunana bane? Ko rashin kunya?,
Kayi Hak'uri Don Allah Likita, tajuya daf da ita taga kullen yanashirin tab'ata wani k'ara tasake tayo kanshi Ganin tana shirin Hawa jikinsane yasa yad'agata cak ya d'orata kan wani k'aton Dutse, ya matsa da baya yana kakkab'e Hanunsa yana kallonta sai b'ari takeyi tana d'angale k'afafunta, Arayuwan Dijah kokun kulle taji sai hankalinta yatashi bare taganshi ido da ido, batayi auneba kawai taga Kb yad'auki kullen ahanunsa yana nufota, ihu tasaka tana shirin fad'owa akan Dutse da sauri ya tareta da hanunsa d'aya, yagyara mata zama yana rik'e da damtsen hanunta, d'ayan Hanunkuma yana rik'e da kullen, daga ita har kullen sai zare ido sukeyi
Cike da tsoro tafara magiya
"Don Allah yaya Likita kayi Hak'uri,
Saketa yayi ya Ajiye kullen ak'asa yana Dariya mai sauti "ta ina nazama yayanki? Dani yayanki ne Khadijah dana jima da b'ab'b'alaki,
Yazaro hankachef a Aljihunsa yana goge Hannayensa yana kallonta kuka takeyi tsakaninta da Allah, hankalinta bajikin kullen da takwanta luf ajikin dutsin tana wasa da takalmin Kb da yake k'afansa,
Yaja tsaki ke ga shegen tsoro kamar farar kura ga kuma rashin kunya, yanzu duk ina wannan tsiwanki yaje?
Tasa bayan hanunta tanashare hawayen da yake ta zirya akan fuskanta tace "Kayi Hak'uri yaya Likita wallahi bazan sakeba don Allah kakoreshi intafi gida Bacci nake ji,
Yana dariya yace to goge hawayenki tas inkinason inkoreshi ba musu takama bakin Hijabinta ta goge fuskanta, ya kalli fuskanta yayi jazur yace
"Meyasa ne ke bakya kwalliya kamana na "yanmatan garinnan? Shiru tayi tana sheshshek'a,
"Inbaki ban Amsaba zan d'aukota insamiki acikin Riganki,
Da sauri tace "nikawai bani son kwalliyane bayi burgeni,
Yatab'e baki "Ok masifa da Rashin kunyane kawai yake Burgeki?
Talangab'ar da kanta tace "
Nifa bana Masifa,
"to meyasa agarinnan ake cemiki Dijah k'aya?
"Nima haka naji suna fad'amin tun ina k'ara amma ba a fad'a a idona sai abayan idona, tad'an had'e rai wallahi duk yarinyan da tacenin Dijah k'aya sai nafasa mata baki.
Don Allah yaya kakoreshi intafi bacci nake ji tafad'a cikin sanyi murya,
Ya kalleta duk takoma kalan tausayi haka kawai yaji wani iri a zuciyansa,
"Niba yayanki bane nagaya miki Sunana Kabir inbaki saniba, kuma ba gida zamu komaba can wajen wasannan zamuje inason ganin wasan da za'ayi,
Gyad'a kanta tayi da sauri tace to yaya bazan komaba, dariya Kabir yayi har yana d'an sunkuyawa, jiyake kaman su tabbata ahaka ganin yanda takoma sosai game d'in yamasa.
*Tofah 😆🤔 yau Dijah ce daba Kb hak'uri? Hardace masa yaya? Gashi tace masa bazata sakeba anya kuwa dagske yaci bulus kenan? Kubiyoni danjin yanda zasuje dandali* 😂..........................
*HAUSA NOVELS* 📚
*HAUSA NOVELS* 📚📚
*HAUSA NOVELS* 📚📚📚
No comments