YA JI TA MATA 2
Farar shadda kamar wacce ya cire ya sake sawa Dan shi kullum bakin kaya yake sawa acewar shi tafi fito da haskensa. Tunowa yayi da dalilin da yasa ya sanya farren kaya. Jiya ya shiga school market zai karbi typing da ya bayar ayi masa na test din dalibai amma a shagon photocopy din makaranta saboda kar question yayi leaking sai ya hangosu su uku tsaye a bakin wani shago. +
Da alama ruwa zasu siya fasa shiga motarsa yayi yaje shagon dake gefen inda suke ya tsaya yana kallonta cikin abayanta kamar kullum tana kyalkyala dariya tare da kawayenta.
Beeba yaji tace amma yanzu let's be serious marakis idan yanzu m. Ahmad dinki yace yanason a daura muku aure in 2 weeks zaki yarda? Marakisiyya tace two weeks? Mansura tace eh marakis tace da alamu kun karya kumallo da piya piya AI cewa zanyi da weekend ma an gama komai sake kyalkyale wa da dariya sukayi mansura tace kaji maiya.
Beeba tace nikam wai shi kullum bashida kayan sawa ne sai baki? Mansura tace toh ai yana yi masa kyau shiyasa kuma kinga ni favourite color na kenan. Marakisiyya tace nikam ko na arana daya ne in yasa favorite color na fari toh sai nayi wata ina farin ciki.
Bai tsaya jin sauran zancensu ba kamar Wanda akayi masa tsafi haka ya shige mota ya koma office take ya Kira umminsa yace a siyo masa ready made na kaftans farare guda 30 dan na wata daya cir zai saka.
Murmushi yayi bayan ya dawo daga tunanin da ya fada ya nufi gaban madubi yana girgiza kai yace marakisiyya kenan gashi nasa miki farin kaya kuma sai Kika bata min.
Fesa turare yayi ya fice tare da komawa makaranta ya nufi office dinsa. Tun daga office din take jiyo takunsa lokacin ta nannade a dungu a office din tana ta zubda hawaye.
Da sallama ya shigo bakiga kowa ba yace lallai yarinyar nan tana neman maga..... kasa karashe maganar yayi jin shesshekarta ya juya da sauri ya ganta a bayan kofa.
Yace rakisiyya dago jajayen idanunta tayi jin sunan da ya kirata dashi. Dama yasan sunanta harda yi masa wani salo kusa da ita ya karaso yama rasa abun yi yace me.. me ya sameki? Goge hawayenta tayi tace ba komai tana shirin mikewa a take ta koma saboda yadda taji kamar an zaro hanjin ta yayinda taji wani Abu nabin kafarta wadda ta tabbata ba jinin al'ada bane Dan baifi sati da gamawarta ba.
Yace ya zakice min babu komai bayan gashi kina kuka kuma da alamu baki iya tsayuwa? Kode .... sai kuma yayi shiru Dan tunowa da yayi cewa zaiyi banbarama. Dan shi ya dauka al'adanta ne ma yazo yace Bari na Kira class rep dinku ya turo min kawayenki su dauke ki su saka min ke a mota bakinsa kawai take kalla tana nazari iri iri jin wani Abu na sake fita a jikinta yasa ta kankame jikinta ta rufe ido.
Wata lecturer wacce ke mutuwar son (malam ) m. Ahmad sai bibiyarsa take tayi knocking daga marakisiyya yayi daga bayan kofar har zai ajiyeta akan kujera sai ya fasa saboda gudun zargi balle a yanayin da take sai yazaunarta gefe tare da bude kofan.
Dalilin da yasa dukda akwai larura amma bayason ya dauketa ya fitar da ita saboda halin dalibai babu Wanda zai duba larura tasa ya dauketa yanzu sai ayi gaba daku balle ga abinda ya faru. Abinda bai sani ba kuwa shine zama daki d'aya da yayi da marakisiyya ya daga Mata hankali ba kadan ba balle kuma ya dauketa kawai sai ta sume Dan ita dai taci alwashi bazata taba yin zina ba saide ta mutu.
Saboda zina guba ce.... zina masifa ce kuma bomb ce ko da mai yinta ya tuba sai ta cutar da ita musamman ma diya mace karancin abinda zai faru shine babu zumunci ko kadan da zai yanzu a cikin iyalinki Lamar yan tasha haka zasu zama danki baya daraja baya kaunar yan uwanta, baisan mutuncin danginki ko na mahaifina ba.
Kai mazinaci! Dakai nake, wallahi ka sani in ka samu yar mutane kayi zina da ita toh yarka ce zata biya ma. Ku duba mana a shekarun baya muyum bai isa yayi zina da karuwa ba sai yana da kudi. Amma yanzu fa? Ba tare da ko Kabo ba. A baya ka bata 10k kayi zina da yar mutane wallahi ko naira 10 gate bazai bawa yarka ba zaiyi zina da ita. Zakin bakin minti Goma zai Mata ya gama da ita.
Mazinata in Baku sani ba toh bari na fada muku da dumi dumin sa. A yayinda zakuyi zina komai na Allah sai ya barka, ko ka haddace kur'ani sai ya barka. Duk wani Abu dake da hadi da Allah ko manzonsa sai kun taba hanya. Akan jin dadin awa daya kun tarko wa kanku masifa ba na kwana daya ba. +
Ba na sati daya ba, wata daya ba. Ba shekara daya ba wallahi har ku mutu bazai barku ba...shiyasa Allah yace kar ma mutum ya kusanci zinan balle ya aikata.
Kallon ms madeena dake tsaye tana kallonsa yayi yace thank God ms madeena kinzo please wannan dalibai zaki kama min mukaita sick bay I think anxiety attack ta samu saboda tsoro. Murmushi ta sake masa yau wace rana bai ja tsaki ya dauke kai ba... kuma har sunanta ya Kira harda neman alfarma a wajenta.
Tace with greet pleasure malam Ahmad rike min jakana karba yayi yana tabe baki ganin shigar da tayi daga ita sai Riga da siket. 'Daga marakisiyya tayi ta nufi waje da ita idonsa ne ya fada a jurwayen dake bayan marakisiyya ya kalli wajaje biyu da ta zauna duka biyu a jike.
Zaro ido yayi kamin ya hau kiftasu da sauri ya.......
😳😳KAI JAMA'A 😂😂 NI DARIYA MA ABIN YA BANI SU MALAM AHMAD ANGA TA MATA.. NAMU BA IRIN NASU BANE IKO JALLA JALALU SAI KALLO.
WAI SHIN YAYA ZAI KAWANCE DA MARAKISIYYA NE? SHIN MALAM AHMAD KO DE YA FADA NE HAI GANE BA? INA LABARIN OGA LUDU UBAN JARUMTA😂
KU BIYONI DON JIN YADDA LAMARIN ZAI KAYA ANYA KUWA KUNA JIN DADIN WANNAN LABARI ? YANZU DE MUKA FARA KUMA KUNSAN ME NAKE CEWA KULLUM ANA KARA ZURFI LABARI YANA KARA CITTA😉
DAN ALLAH KARKU MANTA DA FOLLOWING DINA SECOND BIYAR KACAL ZAI DAUKA.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU KU TABBATA KUN ANTAYO MIN COMMENT TARE DA VOTES FA. A NA GOBE AKWAI WANI JAWABI DA ZAN ANTAYO MUKU
Miss untichlobanty 💕
No comments