Breaking News

RANAR MURNA COMPLETE

          *RANAR MURNA*

                            💓💓 💓

         *💓Written by Amrah💓*

                    *💓NWA💓*

                                                      *1-end*

🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂

    A firgice na tashi dag bacci sanadiyyar tunawa da nayi cewa ina da lecture ta karfe takwas na safe. Raina a bace na tashi zaune na kasa tashi saboda ina tsananin jin dadin baccin da nake.

     Ummana dake tsaye naji tace "idan kuma kina so ki makara ne to sai ki koma baccinki kiyitayi." Ta fita ta bar dakin. Banida zabin daya wuce in tashi in fara shirin makarantar saboda malamin da zayyi lecture din ya tsani ayi late.

     Cikin lokaci kadan na shirya cikin straight skirt dina black na dora black top 'yar karama. Doguwar rigata na saka irin kimono din nan da ake yayi. Pink colour ce sai madaurinta black. Black veil na yafa sai karamar hand bag pink da takalmi ma pink. Kallon kaina nayi a mirror naga nayi kyau sosai masha Allah duk da ba wani make up nayi ba.

    Locker ta na bude na ciro dubu daya na saka a hand bag sai cajar wayata ma na sakata. Wayata kirar iphon7 na rike a hannu cikin hanzari na fita parlor. Ummah na zaune alamar tana kan yin aiki taga na fito. "Amrah ya da fita baki karya ba?"

     Cikin sauri nace mata "wallahi ummah na makara ne, gashi har bakwai da rabi ban bar gida ba." Ban ko gama maganar ba na fice bayan na dauki makullin motata."

    Parking space naje na dauki motata kai tsaye na fita na bar harabar unguwar.

     Karfe takwas da rabi na isa makarantar. Bayan nayi parking na dauko jakata na fito na nufi theatre. A bakin theatre din naga kawayena kawayen albarka tsaye suna jirana. Kallonsu nayi na sakar masu murmushi. Suma din murmushin suka sakar min tare da fadin "ya akayi kikayi late Amrah? Kuma tunda muka tambaya akace bakya ciki shine muka ki shiga muka tsaya jiranki."

    "Allah sarki! Naka sai naka. Lallai *RAZ* ku aminai ne na gaske. Fatana dai Allah ya barminku."

    "Ameen" suka fada a tare. Kofar muka shiga cike da farin ciki.

      Da shigarmu malamin yayi saurin dakatar damu. "Hey! Get out from my class, what is the time now and you are still comin g to my lecture? Abeg leave this theatre and I dont want to hear anyi beg from you."

   Cike da takaici muka bar theatre din. Ba wai haushin lecture din da zamu rasa nayi ba, no, haushin dizgin daya mana  kawai naji.

    Tsabar jin haushi yasa ko magana babu wadda tama wata a cikinmu. Mini theatre muka nufa kuma mukayi sa'a babu kowa a ciki.

     Zama mukayi sai a lokacin nace "kuyi hakuri pls, nasan ni naja maku..." da sauri Rabiatu ta dode min baki. Zarah tace "miye naki nayin wannan maganar kuma? Allah ya rigada ya tsara haka fa, koda bamu tsaya jiranki ba dole sai an koremu."

    "Hakane kawayena." Na fada tare dayi masu murmushi. Fira muka hau yi sosai take na nemi duk wani bacin raina na rasa.

      "Anyi a daidai ma wannan korar tamu da yayi, kunga sai muyi shawarar yanda birthday party na zai kasance."

    Caraf na mike tsaye cikin farin ciki nace "hakane fa. Ni kunga hakan ma sam bai fado min a rai ba. Yanzu ya kenan?"

   "Hadadde kuma kawataccen party zamu hadawa sis Z." Rabiatu ta fada cikin jin dadi.

     Kallonmu tayi tayi murmushi tace "kuce dai ni din 'yar gayu ce."

    "Kuma bama bukatar ko sisinki." Na fada ina kallonta.

     Farin ciki fal a fuskarta tace "kai godiya kuwa nake kawayena. Allah ya bar minku."

   "Shshshs! Kar na sake jin godiya daga bakinki, inhar waninmu zaima wani abu yayi godiya to tabbas zai iya godema kansa idan yama kansa abu." Rabiatu ce tayi wannan maganar cikin natsuwa  kasantuwarta komai nata a nitse take yinsa.

       Haka dai muka sha firarmu har karfe goma tayi muka nufi wata lecture din.

             Washe gari.

   Ta kama Wednesday ne, sai karfe goma muke yin lecture a wannan ranar. Shiryawa nayi cikin bakar abaya nayi veiling da pink kashka. Purse kawai na dauka saboda joter ta tana cikin mota kuma bana son daukar hand bag yau. Bankwana nayi da ummah sannan na kama hanyar makaranta.

     Cikin lokaci na isa yau, waya mukayi dasu suka shaida min cewa suna daga bayan theatre suna jirana tunda da sauran lokaci. Binsu nayi saboda dama nasan inda muke zama din.

      Da zuwana kuwa mukaci gaba da firar yadda partyn zai kasance gobe idan Allah ya kaimu.

   Karfe goma saura minti biyar muka shiga theatre domin daukar lecture.

    Tun kafin sha biyu tayi malamin ya barmu muka tafi saboda baya so ya makara meeting din da zasu shiga.

   A motata muka tafi a hanya ma maganar birthdayn zarah kawai muke. Munci babban buri akan wannan birthdayn, mun yanke hukunci akan zamuyi dressing hot pink and black kamar yanda cake dinta zai kasance pink colour.

    Bayan na sassaukesu na kama hanyar gidanmu, munyi dasu cewa gobe tun karfe goma na safe zanje in daukesu muyi duk abunda ya dace.

 

       _Thursday 25th May 12:00am_

 

   Idona kyam akan agogon wayata yake. Wannan lokacin yana cika nayi gaggawar turawa aminiyata Zarah birthday text. Data na bude na shiga watsapp. A *RAZ FOREVER* naga Zarah ta rubuta _alhamdulillah! Am plus one today._ Ganin tana online yasa mukaci gaba da charting sosai kamar ba dare ba. Muna cikin yi ne sis Rabiatu ma ta hau, nan fa fira ta barke, mune bamu sauka ba sai kusan karfe hudu na asubah.

    Duk da rashin samun barcin kirki bai sa na makara tashi ba, sallar asubah nayi sannan na fito daga dakina. Masu decoration na samu har sun iso saboda dama munyi dasu karfe shida na safe zasu zo su fara, nafi so ayi komai a gabana kuma karfe goma zan fita.

    Ummana na samu tare dasu, har kasa na duka na gaisheta tace

   "Kai Amrah lallai kina matse da wannan birthday party, keda kullum sai nasha wahala  wurin tashinki amma wai yau kece kika taso tun yanxu."

   Murmushi kawai na mata nacewa masu decoration din "ku taso mu tafi a fara aiki." Tashi kuwa sukayi, a babbar farfajiyar gidanmu muka isa, nan fa aka fara decoration baji ba gani. Baki daya kalar hot pink and black ne, an kawata wurin da ado na musamman, daga tsakiyar rumfar decoration din aka saka wata royar chair black wadda itace wadda celebrant Zarah zata zauna. Daga hagu da dama kuma aka aje wasu kujeru inda can ne zamu zauna. Can gaba daga gefen dama gurin zaman 'yan *NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION* ne, daga gefen hagu kuma inda aka tanadar ma 'yan *ONLINE HAUSA WRITERS* ne.  Daga tsakiya kuma *RAZ NOVELLA 1&2* aka ajema wurin. Masha Allah! Wuri yayi kyau sosai abun sai wanda ya gani.

    Karfe takwas da rabi aka gama komai wuri ya fito tsaf kamar inda za'ayi wata gagarumar dinner ko kuma kamu. Umma da kanta data gani saida ta yaba da kyawun wurin.

   "Lallai Amrah kina ji da wannan kawar taki. Allah ya barku tare."

    "Ameen ummana." Na fada tare da zaro daurin yan dari biyar na sallami masu deco din.

     Goma saura kwata sis R. Ta fara kirana akan ta shirya, ina gama waya da ita celebrant Zarah ma ta kirani, nan na shaida mata cewa na shirya gani nan fitowa yanzu.

     Bayan na daukosu muka nufi just unique boutique, magana nayi akan a bamu rigunan da nayi ordering tun last two weeks, fiddosu akayi nan na kare masu kallo, biyu iri daya ne sai guda daya ta banbanta tama fi kyau wadda itace ta uwar party.

    Bayan mun bar nan muka nufi favour hair beauty, gyaran kai aka mana sosai sai karfe biyu na rana aka gama.

      Sallah mukayi sannan muka baro shagon salon din, kai tsaye muka nufi Royal bakeries inda zamu karbi cake.

    Shiga mukayi inda zamu karba, reciept na fiddo daga hand bag dita na mikama cashier din wurin, koda ya duba ya mikawa wata mata, kallo tayi sannan itama ta tashi tsaye, babu jimawa sai gata ta fito hannunta rike da katon cake three layers pink zallah sai chocolate stones da aka kawatashi dasu. Karba nayi ta sake juyawa sai gata kuma da wani one layer amma kuma babba sosai ne, sis R. Ta karba sannan muka kama hanyar tafiya.

    Tun karfe uku da rabi umma ta fara kirana cewa ga gida nan fa ya fara cika kuma shiru bamu dawo ba. Nace ta basu hakuri gamu nan mun kusa karisowa.

     Bamu isa gida ba sai gidan su sis R. Muka nufa. Acan mukayi wanka muka shirya, Zarah uwar birthday ita ta mana make up saboda ta kware da wannan.

   Bamu muka bar gidan ba sai hudu da rabi. Gidan su Zarah muka dosa, saida ta gwadawa maminta kwalliya sannan ta mana fatan alkhairi muka wuce gida a lokacin har karfe biyar tayi.

     Nayi mamaki sosai ganin yanda kofar gidanmu ya cika makil kamar ana wani daurin aure. Murmushi mukama junanmu sannan nayi horn maigadi ya wage min gate  na shiga da motata. Hatta da wurin parking rasashi nayi, sai dai nayi reverse na koma waje na samu wuri nayi parking.

     A hankali muke taku mu uku kamar wanda basa son taka kasa, da motar Abdul Mr. Smiles na fara cin karo,murmushi sis Rabiatu tayi amma bata fadi komai ba, ganin haka yasa nace "aifa sis taga motar nata ta saki murmushi." Dukan wasa ta kaimin sannan muka shige ciki.

    Raheem jega iyayen party can cikin gida ya parka motarshi ya wani hakimce daga ciki, yasha ado da suites dinshi black and white.

      Ta baya mukabi dan bama so a ganmu, ta kofar kitchen muka shiga babu kowa anan kai tsaye muka shige dakin Abbah.

    Waya nayiwa DJ akan su tada sauti gamu nan fitowa.

    Wakar broken angel suka saka saboda na fada masa cewa hot music muke son shiga da ita.

   Da kunnata kuwa muka zira high heels dinmu muka jera da taku daya bayan daya kamar wasu dawisu.

   Ta parlor muka fita inda *NAGARTATTU* suke zaune, nan fa suka hau tafi da karfi kowa ka gani cike da walwala, *NAGARTATTU* ba dai fara'ah ba.

      Jin sauti na tashi yasa 'yan *ONLINE* fitowa, dama sune a dakina, cike da jin dadi suka iso inda muke, nan fa sai gaisuwa baji ba gani, 'yan *ONLINE* ba dai surutu ba.

    Nan fa suka mara mana baya, mu uku a gaba sai su a bayanmu.

     Inda aka tanada domin zamanmu muka isa, murmushi muka saki a

 tare, nan fa masu daukar hotuna suka fara, banda hasken flash babu abunda ke fita, ga sautin dake tashi kadan kadan.

    Nan fa aka fara gudanar da sha'ani, ni nayi speech na welcoming mutane, sis Rabiatu kuma tayi na nuna farin cikinta na zuwan wannan rana.

     Casu fa ya kaure baji ba gani, can na hango Mr. Smile sai kwasar shoki yake, tun daga kasa yake kwasota ya dire bisa ido🤣.

    Raheem Jega kuwa cin face yayi wai a dole shi ya kamata ya zauna a inda muke, amma mun masa cin karfi.😜

     Masu serving abinci suka fara aikinsu, tray daya ake ajiyewa akan table daya, wanda yake dauke da kaji guda uku sai sauce. Yayyanka kajin akayi gumduwa gunduwa daidai ci.

    Jejjera lemuna akayi sai wani dan plate karami da aka jera chocolates da sweets manya masu tsada.

     Yan kananan kwanuka ne fried rice a ciki hadadda wadda taji hanta da koda. Nan fa aka hau aikama ciki.

   Nayi mamakin ganin 'yan *RAZ NOVELLA* bil hakki suna dambe wai tray uku na kajin da aka ajiye masu sun masu kadan.😳

     'Yan *UMMEN AMRAH FANS* sun nabba'a wuri daya wai su basu saba da mutane ba sosai.

    Can cikin kwasar shoki idona ya hango min Mr. Smiles ya cika aljihunshi da kaza, dayan aljihun kuma chocolates ne ya zuba a ciki  wai a tunaninshi babu wanda ya ganshi.😂

    Haka aka karaci bama ciki hakkinshi sannan aka fara haramar yanka cake.

     Nan fa masu wayoyi suka kunna video suka fara dauka. *RAZ* suka yanka cake da kansu, a tare nida sis R. Muka sakama celebrant cake a baki tare da yaba mata cream a fuskarta.

     Diba tayi itama ta bama sis R. Ta sake diba da nufin ta bani a bakina.

     Pas! Pas! Pas "ke dillah malama ki tashi daga bacci sai wani murmushi kike kina bacci har an cinye miki dan dumamen tuwanki.

   A harzike na farka daga bacci, kanwata Rukayya ce na gani bakinta cike da irin jan bakin nan 24hours sai taunar chewing gum take cikin kauyanci da gani wayewa tayi karanci.

       Iya bacin rai yau na jishi, wai ashe duk abun nan dake faruwa mafarki nake, ni haushina ma daya da bata bari an saka min cake din a baki ba, kuma gashi wai tuwo ya kare.

   "ni ki tashi zanyi shara, na gama shiryawa zanje gidan su Barah, kin san yau zamu fiddo ashoben Fure."

    Bance mata komai ba na mike daga kan langa langar karifata, ji nayi inama ace gaske ne ba mafarki ba.

     Na mike kenan na jiyo kir kir kir din wayata, inda na ajiyeta naje na duba, nade take da robali irin tsohuwar tecno din nan ce. Habu Lado na gani a rubuce, tsaki kawai nayi dan duk a samarina na tsaneshi saboda shi a dole sai ya zama wayayye wai dan in soshi.

   Nan fa na hau tariyar mafarkina, inama ace ba mafarki nayi ba, wai ni dakeda iphon7 a mafarki amma tsohuwar tecno ce dani. A takaice dai yinin ranar haka nayishi cike da bakin ciki da kunar rai. Fatana kawai koda makamancin abunda ya faru a mafarkin ne ya faru.

 

 

********************************

  Na kirkiri wannan labarin ne kawai dan in nishadantar da duk wani masoyin RAZ tare da godiya ga duk wanda suka mata fatan alkhairi a zagayowar shekarar haihuwarta. Inda nayi kuskure Allah ya yafe min.

 

  Sadaukarwa ga aminiyata *XARAH~B~B* Allah ya karo miki shekaru masu albarka musha shagalin bikinki kawata.

 

Nagode kwarai ga duk wanda ya bada lokacinshi wurin karanta wannan gajeren labarin nawa. Ina fatan kunji dadinshi.

 

    _Tabbas RAZ *AMINNAN JUNA* ne masu kaunar junansu.  Muna kaunar junanmu sosai ba kamar yanda *HAYDAR DA HAYBAR* suka tsani junansu ba. Haduwata da RAZ *KADDARATA CE!* wadda wannan kaddarar ta zame min alkhairi a rayuwata.  *NAYI DANA SANI* daya kasance ban sanku ba tun a farkon rayuwata._

 

 

 

 

 

 

*Amrah A Mashi*

*AKA Princess Amrah*

No comments