MADADI COMPLETE
*🗯️MADADI!!💍*
*NA*
*BINTA UMAR
ABBALE🍒*
*'Kir'kirarren
labari ne kuma ba'ayi dan aci zarafin wani ko wata ba. Wanda yaga yayi dai-dai
da yanayi na labarinsa to a rashin sani ne*
*Ban yarda a
sauya min salon labari ta kowace siga ba, wanda ya sanja min labari na ta wata
hanya daban to ban yafe ba*
*NASIHA*
```A wasu
lokotan sauyi na rayuwa yakan zowa mutum. misali da farko kana cikin
'kunci sai Allah ya saukar maka da farin
ciki wanda zai sa ka manta ba'kin cikin ka na baya. Idan kaga haka ya kasance
da kai/ki to tabbas ka/ki ji'banta dukkanin al'amuranka ga Allah. Na biyu kuma
kana cikin farin ciki katsaham! Ubangiji sai ya saukar maka da ibtila'i na
rayuwa gabad'aya al'amuran ka su dagule! To idan irin haka ta kasance da kai
sai ka nutsu kayi tunanin shin wane laifi kayi wanda Allah ya saukar maka da
ibtila'in rayuwa, kada ka/ki ce bari kaje gurin
malaman duba su duba maka ko wani ne yayi maka asiri daga ka/kin aikata
hakan shikkenan ta'bewa da lalacewa ta tattara a kanka ko a kanki, idan ka/ki
fad'a ko wane irin bala'i na duniya Ubangiji kad'ai zaka/zaki fuskanta da
matsalarka lokaci guda zai magance maka/miki, Allah ba'a had'ashi da abokin
tarayya! Idan ka kuskura ka had'a Ubangiji da wani to zaka/zaki dawwama cikin
'kunci da lalacewa har 'karshen rayuwar ka/ki.```
*SADAUKARWA
GARE KU*
'Yan Uwa
Rabin Jiki♥️
*SADDIQA
UMAR ABBALE*
*HALIMATU
UMAR ABBALE*
*NAJA'ATU
UMAR ABBALE*
~~~~~~~~~~~~~
*1*
"Innalillahi
wa'ina ilaihi rajiun."! Abinda Baba Talatu tafad'a kenan ta kalli Saddiqa
dake gefe a tsaye tana hawaye tace" Yi sauri ki d'ebo ruwa suma
tayi." Saddiqa ta futa daga d'akin da sauri, karo suka ci da Baba Malam da
Babban d'ansa Alhaji Magaji."
Baba Malam yace." wato dai har
yanzu Kuka kuke yi ko da alama dai kuna so
ku hana Halima ta kwanta lafiya a
kabarin ta." Tana girgiza kai had'e da 'kokarin mayar da hawayen idonta
tace"Baba Malam mun daina kuka Yaya Naja'atu ce tafad'i ta suma
shine Baba Talatu tace na d'ebo ruwa." Da sauri Baba Malam da
Alhaji Magaji suka shiga d'akin. ita kuma ta futa da saurin gaske, ruwa ta
d'ebo cikin kofi ta shigo d'akin dashi.
Baba Malam
dake tsugune kusa da Naja'atu yana mata addua ya kar'bi ruwa ya shiga yayyafa
mata a fuska, Baba Talatu hawaye kawai take sharewa tana girgixa kanta.
Baba malam
sai da ya yayyafa mata ruwan sau uku sannan ta saki wata ajiyar zuciya mai
kar'fi! idanunta ta shiga kiftawa, sai ta mi'ke zaune da sauri ta shiga rarraba
idanunta a kansu.
Baba Talatu
ta ri'ke hannunta tana fad'in "Naja'atu
kiyi hakuri kada ki jazawa kanki lalura." Ihu! ta zumduma! tasa
hannu ta toshe kunnuwanta jikinta na wata iriyar kyarma! tace"Baba Talatu kunnuwa ba zasu iya
d'aukar wannan maganar taki ba! a ina aka ta'ba haka *Uba ya Auri 'Yarsa* ashe
dama dake da Baba malam dashi kansa Abban nawa
dukkanin ku maguzawa ne ku baku san addin........Kafin ta 'karasa Alhaji
Magaji ya kwad'a mata mari! yace."Ke ki nutsu ki shiga hankalin ki bama
son shirme da shashanci ki saurara ayi miki bayanin yanda al'amura suke."
A zabure! ta
mi'ke tsaye! kamar wacce zata tada iska tace"Baba Magaji ni bazan fuskanci
komai ba ba kuma zan nutsu ba, saboda ni
ba kafura bace wallahi sai na kashe kaina idan kuka d'aura min aure da Ubana,
wai baku ji sunansa bane Abban Naja'atu fa sunansa amma shine zaku daura mun
aure dashi! to dukkaninku sai na kaiku *Hizbah!.* Ta'karashe maganar tana wani
irin kuka mai cin rai.
Baba Malam
ya goge guntin hawayen idonsa ya ri'ke hannunta da fad'in "Auta zauna ni
da kaina zan warware miki abunda baki sani ba." Fuzge hannunta tayi tana
'kokarin tsallakeshi ta wuce! Alhaji Magaji yayi sauri tare mata hanya
Yace."Naja bakya jin magana ko? To shikkenan idan baki kaimu *Hizbah* bakya 'kaunar Allah."
Yafad'a babu wasa a tare dashi.
Hannunsa ta
ri'ke jikinta sai mazari yake tace"Abba Magaji ka duba maganar nan da kyau
fa! Kayi duba na tsanaki! ya za'ayi dan
kawai Mamanmu ta mutu sai suce zasu d'aura min aure da Ubana wace irin rayuwa
ce wannan."!!! Tafada cikin wani irin sauti!! Shima a fusace!
Yace."Wai ke waye ya fad'a miki Alhaji Abbas Ubanki ne."!? Shuru tayi
tana binsa da wani irin kallo! bakinta sai rawa yake yi. da kyar ta iya bud'e bakinta tayi
magana....."Baba Magaji bangane maganar ka ba."! murya na rawa tayi
maganar, Baba Malam ya zaunar da ita kusa dashi hannunsa cikin nata ya rike
sosai yana kallonta, tausayi take bashi sosai, tabbas yasan dole ne ta shiga
rud'ani da tashin hankali sakamakon bayyanuwar abinda yake rufe tsayin shekaru
goma sha shida! da suka wuce. Wanda ta d'auka a matsayin mahaifinta dashi
ake maganar d'aurin aure a tsakaninsu, babu shakka duk wanda ko
yaji wannan lamarin dole ya
shiga halin d'imuwa da tashin hankali
'Dakin ne
yayi shuru na tsayin mintina uku kowa jikinsa yayi sanyi mussaman Naja'atu
wacce take jin wata irin fargaba da fad'uwar gaba, tunda Abba Magaji yayi
furucin cewar ba Abba Abbas ne mahaifinta ba
take wata zabura tana rarraba idonta a kansu bakinta motsi kawai yake
tana so tayi magana amma ta rasa me za tace! fashewa tayi da wani kukan tana
kallon Baba Malam da kansa yake sunkuye sai zufa yake gogewa, tace"Baba
malam kuna so nima na mutu ko? kuna so kamar yanda kuka rasa mamana nima ku
rasa ni ko ? zuciyata daf take data daina aiki sakamakon bala'in da kuka jefata
a ciki! Baba Magaji yace wai Abbana bashi ne Ubana to shikkenan sai ku fad'a
min wanene ya haifeni."? Murya na rawa ta 'karasa maganar.
Baba Malam
ya d'ago kansa a nutse yace."Naja'atu Nine Ubanki ni na haife ki Alhaji
Abbas Uban ri'kon ki ne kuma miji ga 'yar uwarki Halimatu." wani irin
kallo ta shiga yi masa tana girgixa kanta sai hawaye ya wanke mata fuska! murya
a sanyaye tace"Baba malam ya akayi haka? ya kuka yi mun wasa da hankalina?
ni ban yarda kaine mahaifina ba, Abba Abbas shine Ubana shi na sani tunda na
taso shine yaci dani yasha dani ya tufartar dani ya tsaya a kaina nayi karatu
kuma shi nake so ya aurar dani ga mijin dana za'bawa kaina."! Ta'karasa
maganar cikin yarda da abinda take fad'a.
Abba Magaji
ya fusata! sosai ya bud'e baki zaiyi magana Baba malam ya d'aga masa hannu
yace."Kada kayi mata tsawa ko ka hantare ta, dole ne dama haka ta kasance
da ita damu bakid'aya, ha'kika mutuwa itace ta janyo mana wannan tashin
hankalin dan da Halimatu na raye to babu shakka Naja'atu zata cigaba da zama a
matsayin 'yar data haifa alhalin kuma 'kanwa take a gareta, Yanzu zamu bari ta
nutsu tukkuna zuwa dare sai mu sake wani zaman domin mu sanar da ita abinda ya
faru a baya wanda bata sani ba." Abba Magaji ya sauke ajiyar zuciya a
nutse yace."Shikeenan Allah ya za'ba abinda yafi alkairi." Baba Malam
ya amsa da amin kana ya mi'ke suka futa a tare.
Suna futa,
Naja'atu ta kalli Baba Talatu tace"Baba dan Allah dan annabi kada ki bari
al'amarin nan ya tabbata, ke macace ce mai hankali da sanin ya kamata kuma kina
zuwa isilamiyya kin san dai haramun ne Uba ya auri 'yar sa ko."? A zauce!
take maganar.
Baba Talatu
tace"Naja'atu Alhaji Abbas ba Ubanki bane an fad'a miki Mijin Yayar ki ne
Halimatu Allah ya ji'kanta, Alhaji Abbas kinga wacce ya haifa nan ita da 'yan
uwanta su Mussadiq.'' Ta nuna mata Saddiqa dake zaune a kusa da ita.
Wani irin
kallo ta shiga binsu dashi tana girgiza kanta, ta rasa a'ina zata ajiye wannan
babban al'amari a cikin zuciyarta, *Abbah Abbas* ba shine ya haife ta ba *Baba
malam* ya haife ta? anya kuwa da gaske suke wannan maganar ko dai kawai suna so
bukatarsu ta biya ne gurin ganin sun d'aura mata aure da *Ubanta* tabbas dole
ne ta nemawa kanta mafita dan ita kam bata yarda da wannan maganar da suke ba.
Tana kallon
Baba Talatu da Saddiqa suka suka futa daga d'akin, ta shiga girgiza kanta tana
masifar mamakin a'lamarin, kwanciya tayi kan tabarmar dake shimfid'e a dakin ta
shiga tunano rayuwar ta ta baya tare da mutanan data dauka a matsayin iyayenta.
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA
#400 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA
KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI
MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA
BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN
WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU
NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN
NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
[10/15, 1:05
PM] Gagarabadau👺: a
*🗯️MADADI!!!💍*
_(Ba Haram Bane!!!)_
*NA*
*BINTA UMAR
ABBALE🍒*
~~~~~~~~
*MANAZARTA
WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar
Masu Nazari da Aiki da Ilimi._
~~~~~~~~
~~~~~~~~
*SADAUKARWA
GA DUK WANI A HALINA DAKE CIKIN WANNAN UNGUWA♥️*
*2*
*'Kofar
Na'isa* Unguwa ce mai cike da d'umbun tarihi, duk wanda ya kwana ya tashi a
cikin birnin kano ya san da zaman unguwar. 'kofar na isa unguwa ce ta malamai
masana addini da kuma 'yan boko masu aiki da iliminsu, duk wanda yake mu'amula da d'an cikin unguwar
zai gane cewar suna da wani irin quality wanda Allah yayi musu, saboda sun iya mu'amula da mutane sosai!
akwai masu kudi a unguwar akwai marasa karfi a ciki, dai-dai gwargwado masu
rufin asirin dake cikin unguwar suna taimakawa marasa shi mussaman da azimi
suna hidima sosai da sosai da wuya kaji ance maka ga wata hatsaniya ta tashi a
unguwar irin ta *Daba!* ko kuma *Sace-sace* dai-dai gwargwado suna bawa yaransu
tarbiya had'e da ilimin addini dana
boko!
Alhaji
Sama'ila mai kwano wani attajirin mai kudi ne a cikin unguwar wanda yayi suna
sosai dan idan kana neman gidansa daga bakin titi ka ambaci sunansa za'a nuna
maka Alhaji Sama'ila mai kwano mutum ne mara ganin 'kyashi mai kaunar dan
uwansa da ma'kotansa, Yana da 'yaya Uku kacal
wanda matarsa Hajiya Abu ta haifa masa su, Biyu maza mace d'aya, amaryarsa mai suna Hajia Rabi bata ta'ba
haihuwa ba tsayin shekarun da sukayi a tare! Yana zaune da ita haka dan shi
mutum ne mai mi'ka al'amuransa ga Allah
yasan tabbas Allah ne ke bada haihuwa kuma shine yake hanawa.
*Ramlatu*
itace babba a cikin 'yayansa sai wanda yake bin ta, Abbas sai Alhasan shine na
karshe! tunda su Abbas suka taso a cikin unguwar nan suka ga yanda mahaifinsu
ke mu'amula arziki da makotansa sai suma suka fara kwantantawa, hakan yayi wa
mahaifin nasu dadi sosai ya kuma 'kara nuna musu cewar hakan da sukeyi shine
dai-dai dan cikin jinsin mutunan da Allah ya hallita a duniya babu wanda yafi
wani a gurinsa sai wanda yafi bauta masa, kada su nuna sunfi karfin yin
mu'amula da wanda suka fi rufin asiri,
to babu shakka watarana Allah zai iya 'kwace damar dake hannunsu ya
mi'kawa wanda suke ganin bai isa ba......Wannan dalilin ya sanya suka saki
jikinsu da kowa suke mu'amula a cikin unguwar tamkar sauran mutane.
'Karamin
gida ne madaidaici mai kofa gami da dakalin siminti a kofar gidan, gidan na kallon gate din gidan Alhaji
Sama'ila hanya ce kawai ta raba tsakaninsu!
Malam Baba shine mai wannan gidan, kamilin mutum nitsatstse mai kamala
da dattako, malam baba mutum ne shi mai yawan ibadah da karatun al'kur'ani
kusan duk azimin yana zaman tafsiri a kofar gidansa, inda Alhaji Sama'ila ke
sawa ana fito da sadaka daga gidansa, akwai jituwa mai kyau a tsakaninsu dan sai
nace halinsu ne yazo daya na gudun duniya shiyasa suke zaune lafiya da kowa,
Alhaji Sama'ila ya dauki ragamar gidan Malam Baba a hannunsa ba wai dan shi
malam din ya gaza ba Malam na futa sana'arsa kuma sa'i da lokaci al'amajiransa
na kawo masa abun arziki gidansa babu yunwa ko kad'an! malam nada 'Yaya Uku
wanda suka haifa tare da matarsa Baba Talatu
Babban cikinsu shine Adamu wanda yaci sunan mahaifinsa sai suke kiransa
da Magaji, Halimatu itace ta biyu sai kuma Naja'atu da tazo a karshe! Lokacin
da suka haifeta har sun cire tsammani da sake haihuwa sai kuma Allah ya kawo
cikinta, lokacin Halimatu na daf da kammala secondary skuul lokacin tana da
shekara goma sha shida a duniya.
Tsakanin
Abbas da Magaji akwai jituwa sosai suna abota mai kyau da tsabta komai nasu
tare sukeyi karatu tare su d'inka kaya iri daya hula iri d'aya takalmi iri daya
kai hatta da agogo iri daya suke daurawa! Sai kuma Allah yasa shekarunsu suka
zo daya da juna yanzu haka suna matakin shekaru talatin da d'aya koda biyu
Lokacin ne kuma iyayensu suka fara yi musu maganar aure dan sun riga sun
mallaki hankalin kansu! kuma suna zuwa kasuwa suna harkokinsu, Alhaji Sama'ila
yanzu ba ya fita kasuwa sosai su ya d'ora kan harkokinsa na yau da gobe! Alhaji
Sama'ila nada shaguna sama da talatin a cikin kasuwar sabon gari kuma dukkanin
rumfunan sa harkar siye da siyarwa akeyi a ciki, suna harkar kayan rufin gida
da kofofi da ta gogi sannan kuma yana da gidajen bulo suna buga bulo da harhad'a intar lock da ties, mutane da yawa naci da sha a karkashin wannan
bawan Allahn, to ganin 'Yayansa sun kai munzali ne yasa ya d'ora su kan
harkokinsa na kasuwa kwata-kwata baya nuna bambanci tsakanin Abbas da Magaji
Abinda zaiyi wa d'ansa Abbas shi yake wa Magaji, har jama'ar unguwa na surutu kan cewar ba haka
kawai Baba Malam ya barshi ba wasu suna gani kamar yayi masa asiri ne domin ya
mallake shi shida dukiyarsa, wannan cece kucen da mutane keyi bai dameshi ba, dan saboda yasan Malam baba ba zai ta'ba
cutar dashi da zuriarsa ba.
Mama Ramlatu
babbar Yaya gasu Abbas tayi aure a cikin unguwar dan gaba dasu kadan cikin
unguwar Tudun wuzurci! wanda ta aura yana da rufin asiri dai-dai gwargwado amma
tana da kishiya, Ramlatu wata irin mata ce mai izzah da ta'kama! bata da hali
mai kyau! Tayi ta wulakanta kishiyarta kasancewar ta yar talaka gorin yau daban
na gobe daban! a duk sanda Alhaji Sama'ila zaiyi mata aiken kud'i ko kuma
tufafi sai ya had'a da kishiyarta kafin ta bawa kishiyarta sai ta gama yi mata
gori sannan! Ita kuwa da yake mai hakuri
ce sai dai kawai ta girgiza kai ta kyaleta, gabadaya Ramlatu bata dauko halin
mahaifinta da 'yan uwanta ba.
Lokacin data
haifi 'Danta na fari! sosai Mahaifinta ya gatantata daki guda aka cika mata da
kayan barka, shi kuwa maigidan mota guda ta kayan abinci ya sauke masa, aikuwa
Ramtalu ta samu abunda take so shiga take tana fita tana sakin habaici da gori!
Cewar da abincin ubanta mutum ke rayuwa sannan kuma da tufafin ubanta mutum ke
tun'kaho! Allah Sarki Sakina kishiyarta tasan da ita take, sai ta shiga daki
taci kunanta ta koshi kuma ta dauki aniya kan cewar idan mijin nasu ya dawo
zata fada masa abinda ke faruwa a gidan dan gaskiya ita ta gaji da wulakancin
da matarsa keyi mata, gabadaya ta lura Ramlatu bata san mutunci ba ba kuma
tasan mai kyautata mata ba, tunda ta haihu take hidima da ita ta kasa zama ta
hutu kullum a tsaye take amma babu sannu bare nagode kullum cikin fada mata
bakar magana take to gaskiya ta gaji hakurinta yazo karshe kudi ai ba hauka
bane.
Maigidansu
na dawowa bayan yaci a binci ya huta sai ta shiga fada masa abubuwan da suke ta
faruwa a gidan wanda shi bai san dasu ba, tabbas ransa ya 'baci sosai kuma ya
sheda halin matarsa Sakina tana da hakuri sosai da kawaici ba zata takali Ramla
da rigima ba duk da cewar itace Uwargida amma ta hakura da komai burinta ta
kawo zaman lafiya da daidaito a gidin! Yace."Kiyi hakuri insha Allahu zan
sameta nayi mata fad'a amma kada irin haka ta sake faruwa kiyi shuru da bakin
ki duk abinda ke faruwa tsakanin ki Ramla ki sameni ki fada mun zanyiwa tufkar
hanci." Tace."To insha Allah."
Lokacin da
ya shiga dakin Ramlatu tana zaune gefan gado taci uwar kwaliya da less an turo
dauri gaban goshi kana kallonta zaka fahimci 'Yar Alaji ce hannunta da kunnata
gami da wuyanta duk Gold ne sai walwali take...Zama yayi kusa da ita ya mika
hannu ya kar'bi yaron dake hannunta da ta gama bashi nono ya tofa masa addua
kana ya kwantar dashi ya fuskanceta.......Babu cikakkiyar walwala a tare dashi
yace."Yanzu Ramlatu abinda kikewa Sakina a gidan nan ya dace."!? Wani
irin shan kunu tayi ta kumbura fuska tace"Me nayi mata ashe! zaunar da kai
tayi tana fad'a maka karya da gaskiya ko."? Yace."Abinda Sakina za
tayi nasa ni haka kuma abinda Ramla za tayi nasa ni dukkanin ku nasan halin ko
wacce ba wai ina so nace Sakina tafi ki a gurina ba A'a dik matsayin ku d'aya a
zuciyata, amma ki sani abinda kikewa abokiyar zamanki bai dace ba! wace iri ce
ke mai manta alkairi? menene Sakina ba tayi miki ba, ina cewa gabadaya sai da
kika daina girki sai dai ta dafa ta kawo miki har d'aki kuma hakan bai hanaki
kwana da miji ba! idan muguwa ce ai zata hanaki ki kwana dani ba tunda itace
take girki amma ta dafa ta baki kici kina kwance kuma ki rasa sakayya da zaki
mata sai irin wannan."!! Fashewa tayi da kuka tace"Shikkenan to ai ba
sai ka futo fili ka nuna kafi kaunarta a kaina ba, amma meye haka daga zuwa
babu tambayar ba'asi sai ka kama wasu maganganu ai bani ce nace tayi min girki
ba ita taga zata iya ta dauka tayi ni ba burgeni tayi ba, kuma koda ba tayi min
girki ba zansa a turo mai aiki daga gidanmu tazo ta kula dani har na
haihu."
Yace."Ni
dai na fad'a miki wallahi duk sanda kika 'kara ci mata fuska ko kikayi mata
gori kan wani abu da aka kawo shi gidan nan sai ranki ya 'baci!! Cikin 'bacin
rai tace"To ai shikkenan tunda uwata ce ita sai na kwanta ta takani saboda
tana da daurin gindi a gurinka, akan me? kai da ita kuna cin arzikina amma kuma
kuce sai nayi muku biyayya wallahi ba zai yuwu ba.""! Takarasa
maganar tana buga cinya."! Cikin fusata yace."Zanyi maganin ki
ai shashasha mara tunani meye abinci da
kike gori a kansa, meye kuma tufafi wanda zasu lalace su barki da mutum! to
zanje na samu Alajin da kaina zan fad'a masa bana bukatar k'wayar abincinsa a
gidana ko ya aiko dashi na dawo sai an mayar." A fusace ya mike ya futa
daga dakin....Shuru tayi tana tunani addua take kada Allah yasa yaje gurin
mahaifinta da wannan maganar tabbas tasan idan yaji matsalar daga gurinta ne to
babu shakka ranta sai ya 'baci.
Aikuwa
misalin karfe biyar da rabi na yamma ta fito daga wanka kenan wani yaro ya
shigo gidan yana fadin "Wai Ramlatu tazo soro mahaifinta ne yazo.
Gabanta ya
fadi da sauri tasa kayanta ta futa da tabarma a hannunta, tana zuwa soron sai
taga Sakina a durkushe suna gaisawa da Alhajin, shuru tayi tana jinsa yana bata
hakuri dangane da abubuwan da suke faruwa, koda ta gaishe shi 'kin amsawa yayi
ya rufe ta da fad'a sosai yace kuma ta bawa abokiyar zamanta hakuri! tana kuka
ta shiga bawa Sakina hakuri! Tace " Babu komai ta mike ta shiga gidan, Alhaji ya kalleta da
fad'in "Wallahi Sakina duk sanda mijinki ya sake kai 'karar ki gurina to
babu ni babu ke! dama ashe mugun hali ne dake ko? to na kara jin na kawo muku
wani abu gidan nan kiyiwa wani gori ranar sai na 'bata miki rai! Hakuri take
bashi tana share hawaye, ransa ya a 'bace! ya futa daga soron ya barta a tsaye
hannunta ri'ke da tabarma.......To tun daga
ranar Sakina ta samu lafiya a gidan Yanzu Ramlatu ta daina yi mata gori
da kallon banza amma dai duk da haka idan 'yan wulakancin na kusa tana ta'bawa
sai dai kawai ta kau da kanta domin dai a zauna lafiya.
****
Irin kulawar
da Abbas keyi kan Halimatu ya sanya iyayensu suka ga kamar sonta yake yi, shi
kuma ba haka bane a zuciyarsa kawai yana tausaya mata ne a matsayinta na mace
kuma mai nakasa, Halima bata da lafiyar k'afa sosai kafarta ta dama ta samu
tawaya tun tana yarinya anyi magani na
hausa dana Asibiti tafiyarta bata dai-dai ta ba, sai kawai suka hakura suka bar
mata hallitarta da alama haka Ubangiji ya hallice ta, kafarta ta dama itace
take da nakasa ta inda in tana tafiya take jefata, Amma a fuska Halima bata da
muni kyakkyawa ce sosai mai madaidaicin
tsayi! komai nata cikin nutsuwa take gudanar dashi.
Magaji ya
fitar da matar aure A lokacin da iyayensu suka bukata, shi kuma Abbas din har
yanzu ya rasa wacce zai tsayar a matsayin uwar 'yayansa! Mutum ne mai ruwan
idon tsiya ko wace mace ba tayi masa ba! Da kyar da ya tsayar da Halisa a
matsayin matar da zai aura gidansu na bayan layi! kuma Halisa kawar Halima ce
tare ma suke tafiya makaranta, Allah sarki Halima tunda Taji labarin Abbas zai
auri kawarta sai ta rasa nutsuwa komai nata ya tsaya cak! bata san tana sonsa
ba sai da taji zaiyi aure! damuwa ta shiga sosai ta rage walwala har sai da
iyayenta suka gane!
Da yake Baba
Talatu macece mai saurin fahimtar abu nan da nan ta fahimci abinda ke damun
'yar tata! Ta sameta tayi mata fada da nasiha sosai tace"Kada ta janyowa
kanta lalura mutum baya ta'ba auran mijin da bana sa ba, dan haka ta cigaba da
addua Allah itama ya za'ba mata miji nagari." Duk da wannan nasihar da mahaifiyar ta tayi
ma bai sanya ta daina damuwa ba, ita gani take waye zai aureta tana da nakasa
(gurguwa) tana ganin watakila ma haka zata 'kare rayuwarta ba tayi aure ba.
Ita kuwa
Halisa tunda ta fahimci Halima na shiga
damuwa a duk sanda taje mata da maganar Abbas sai ta dauki d'amarar muzguna mata
kullum kan hanyarsu ta zuwa isilamiyya
sai tayi mata zancensa da irin soyayyar da sukeyi, Halima tayi shuru bata tanka
mata, ita kuwa Halisa tai tayi mata dariya...........Akwai lokacin da Abbas
yaje zance gurin Halisa ta tsare shi wai dole sai ya fad'a mata tsakaninsa da
Halimatu! mamaki sosai ya kamashi Yace."Halimatu kanwata ce amma babu wata
soyayya a tsakanina da ita." Halisa tace"To idan kai baka sonta ita
tana sonka dan ba kaga halin damuwar da ta shiga ba lokacin da ta samu labarin
abinda yake tsakanina da kai, dan haka gaskiya gwara kayi wa tufkar hanci tun
kafin tafiyar tayi nisa duk da take kawata bana tunanin zan iya zaman kishi da
ita."
Mamaki ya
rufe shi da yake mutum ne mai tsare gida sai yace."Okey yanzu kina so ki
nuna min ga yanda zanyi kenan? Idan na fahimce ki kina so kice ke ba zaki zauna
da Halimatu ba a matsayin kishiya ko me."? Da sauri tace"Kwarai kuwa
ai naga kusancin dake tsakanin gidanku da gidansu ne ina tunanin idan iyayenta suka fahimci halin
da take ciki a kanka zasu ce ka aure ni kuma bana so gaskiya shiyasa nake so
tun kafin tafiya tayi nisa kayi wa tufkar hanci." Ya girgiza kansa yana
kallonta yace."Bari kiji Halisa ni ba irin mazan da mata zasu zauna suna
tsarawa magana bane! abinda nasa kaina shi nake yi ke baki isa kice ga yanda
zanyi ba, bani da ra'ayin zama da mace d'aya ki rubuta wannan ki ajiye bayan na
aureki zan sake auran uku mutukar Allah
ya bani iko saboda haka sai ki daura d'amarar zama da kishiya Halimatu kuma da
kike magana na jawa kunne a kan tana sona to kin sanya ma naji sha'awar auranta
zan aureku rana d'aya tunda dama 'kawayen juna ne." Da jin abinda ya fada
sai ta mike a fusace! tace"Wallahi sai dai ka za'ba ko ni ko ita dan na
rantse da girman Allah ba zanyi kishi da gurguwa ba."!!! Ya bude bakinsa
yana kallonta cikin tsananin mamaki! lallai
Halisa muguwar jahila ce yanxu me bambamcin muskini da mai lafiya?
saboda jahilci da hauka kishi ma sai ta za'bi da wanda za tayi! Ya mike tsaye
fuskarsa a murtuke yace." Tunda kin rantse ba zakiyi kishi da Halimatu ba
to nima kuma ba zan janye 'kudirin dana dauka a kan auranta ba, saboda haka sai
kije ki r'ike duk wani abu da nasa aka kawo miki da niyyar auranki na bar miki,
ki samu wani mijin ki aura ni kuma zanje na auri muskiniya sai naga abinda zai
cinye ni." Yana 'kare maganarsa ya futa daga soron gidan nasu. durkushewa
tayi kasan soron ta fashe da kuka tana data sanin abinda ta aikata, tun farko
ta lura Abbas din ba irin lusaran mazan da mace ke tursasawa bane yana da wani
irin baud'addan hali tabbas kamar yanda ya fad'a din babu me sashi yayi abinda
baiyi niyya ba mutukar ba iyayansa ba.
Tofa
al'amarin yayi tsanani dan Abbas yaja tunga ya tsaya kan maganarsa kan cewar ya
janye maganar auransa da Halisa saboda wasu dalilai saboda haka Halimatu itace
matar da ya za'ba a matsayin uwar 'yayansa, Baba malam da Alhajinsa suka dinga
bashi hakuri suna rarrashinsa, kan yayi hakuri ya auresu gabadaya, nan ya futo
ya fada musu abunda ke faruwa! Yace."Halisa tayi mummunan furuci ga Halima
kuma tayi izgili ga hallitar da Ubangiji yayi mata, dan haka to shi ba zai auri
macan da zata dinga kokarin nuna masa yanda zaiyi ba, saboda haka shi ya janye maganar auranta
Halimatu yake so. Baba Malam da Alhaji Sama'ila ba suji dadin faruwar al'amarin
ba kasancewar mahaifin Halisa din mutumin kirki ne duk tare suke zama bakin titi ranar juma'a da yamma, dan haka
sai suka yanke shawarar fada masa halin da ake ciki, suna kuma fatan Allah yasa
hakan shi yafi alkairi. Koda mahaifin Halisa yaji yanda al'amarun suka kasance
sai hankalinsa ya tashi sosai! babu shakka yarinyarsa tayi wa kanta wauta ba
kad'an ba ta cutar da kanta kuma shi sam baiga laifin Abbas ba, da irin
hukuncin da ya yanke yana bala'in son yaga jajurtaccen namiji mai tsayuwa kan
magana daya.............Halisa tasha fada sosai gurin mahaifinta
yace."Tunda ba zata auri mai mata ba to taje ta nemo wanda bashi da mata
wanda kuma yayi mata alkawarin da ita kadai zai zauna, mutukar ta kawo masa
komai illarsa da rashin nagartarsa to shi kuma zai daura mata aure dashi tunda
itace taji ta gani.
Hankalinta a
tashe ta nufi gidan Ramlatu, tana kuka ta zayyane mata abinda ke faruwa, a
ganinta tinda Itace take gaba da Abbas din zata fada masa yaji tace dan Allah
ta bashi hakuri yanzu ta yarda zata zauna da Halimatun a matsayin kishiyarta.......Ramlatu
ta fusata ta dinga surutai tana aibata Halimatu da iyayenta a cewarta sam Abbas
bai dace da auran muskiniya ba, saurayi dashi mai kyau da kudi da Ilimi yama
za'ayi ya auri nakashshiya wacce take ci take sha a 'karkashin alfarmarsa dan
haka sai ta shiga bawa Halisa hakuri tace ta kwantar da hankalinta za taje ta
same shi, insha Allahu zai aure ta.........Da safe da wurwuri ta sauka a gidan
kowa yayi mamakin zuwanta, ko gaisawa ba suyi da mutanan gidan ba ta nufi
dakinsa, lokacin yana kokarin fitowa da shirin fita kasuwa! Yace."A'a barka da safiya kece a gidan."
Tace."Eh gurinka nazo." Cike
da mamaki yace."Gurina."? Tace"Eh yace."To Kinga ni yanzu
sauri nake zan fita ki bari na dawo ko kuma ki koma gida da yamma idan na dawo
zan shigo gidan naki sai naji abinda yake faruwa.
Cikin d'aga
murya kamar wata uwarsa tace"Yanzu kai Abbas ka rasa wacce zaka aura sai
Halima muskiniya nakashshiya ashe dama anan ruwan idonka zai 'kare gaskiya ka
bani mamaki wallahi! Ga Yarinya mai hankali da nutsuwa 'yar gidan mutunci mai
kaunarka amma kace ka fasa auranta ka koma gurin wata banza wacce take ci da
sha a 'karkashin mahaifin.......'Daga mata hannunsa yayi fuskarsa a murtuke
yace."Wallahi ban san sanda zakiyi hankali ba! kullum kina girma kina cin
'kasa! Yanzu ke ko kunya baki ji ba ki
shigo har dakina kina daka min tsawa da nuna min yanda zanyi, haifata kikayi da
zaki dinga yi min haka? ina ruwanki da aurena da Halimatu idan ba zaki saka
albarka ba to kiyi shuru da bakin ki dan ni wallahi duk abin nan da kuke yi
'kara mun 'karfin gwiwa kukeyi babu gudu babu ja da baya sai na auri Halimatu
in yaso ku kasheta saboda 'kiyayyya." Fashewa tayi da kuka tana nuna shi
da hannu tace"Ni kake zagi ko Abbas dama ai baka da mutunci baka dauke ni
a bakin komai ba kuma kai dama ba'a fada maka magana kaji." Yace."Da
kinzo min da lisilama zan fahimce ki amma kinzo kina yi mun hayagaga! a kunne
ai kin san halina ni ba'a haka dani." ratse ta yayi ya futa dada dakin, kallo ta bishi dashi tana
jijjiga kanta, dama tun yana yaro bata iya lankwasa shi gwara Alhasan shi tana
fada masa magana yaji amma banda Abbas futo na futo yake da ita girgiza kanta
tayi ta futa daga dakin.
To haka
al'amura sukayi ta kasancewa kowa na fadar albarkacin bakinsa kan wannan auran
yayin da Abbas ya shafawa idonsa toka ya tsaya kai da fata sai da yaga auransa
da Halimatu ya tabbata sannan hankalinsa ya kwanta.
Gida gudu
biyu iri d'aya Alhaji Sama'ila ya mallakawa Abbas da Magaji Gidajen nasu na cikin unguwar *Gwangwazo*
wajejen gidan Sarki.
kowanne ya
tare da matarsa a ciki, Maryam matar Magaji 'yar cikin gari ce dai-dai
gwargwado tana da hankali da nutsuwa shiyasa tasu tazo d'aya da Halimatu suke
zamansu lafiya, kamar yanda mazajensu ke
zaune da juna lafiya suma haka suke mutunta junansu...
*GA MASU
BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #400
SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA
KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI
MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA
BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN
WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU
NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN
NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
_*Bata sati
da gama book zata fara wani kan san kud'inta za'a daina san book dinta ni DA
WATA A 'KASA Ma dana siya ko pege d'aya ban karanta ba, bata nazari gurin
rubutu sai tazo tana rubuta 'karya bata ganin yanda su Billyn Abdul suke ita da
Hugama suna Nazari kafin su fara littafi amma ita san kudinta yayi mata yawa😅😅😅*_
*KAJI!! UWAR IYA MAI ZANI BA 'DAN CIKI 🥱INA RUWAN KI ME YA DAME KI? BINTA
TANA SON KU'DI💵💵 🥱KUMA BA ZATA DAINA RUBUTU BA SAI SANDA BASIRAR TA TA'KARE
'KARYA DA RASHIN NAZARI DA TUNANI YANZU TA FARA RUBUTAWA IN DAI ZA'A SIYA
MAGANA TA MA'KARE🤣🤣🤣 ALLAH KA TAIMAKI BINTA TA CIGABA DA SHIRYA 'KARYA DA RASHIN
NAZARI DA TUNANI, A SIYA A CIKA MATA ASUSUNTA😇 MY REAL FANS A CIGABA DA KARANTA 'KARYA DA RASHIN NAZARI IN DAI ZAKU
KARANTA KU NISHAD'ANTU NI KUMA BA ZAN GAJI DA TSARA MUKU 'KARYA BA🤗🤗*
*RUBUTU
BAYAYI WA BINTA WUYA SABODA TANA DA MATAYA👺*
_Banyi
niyyar typing ba yau amma saboda na
mayar da martani yasa na dau'ki al'kalamina🖊️_
*3*
Halisa
hankalinta yayi masifar tashi ganin irin uban gidan da'a kai Halimatu ga uban
lefen da Abbas yayi mata atampopi da lesuka masu tsada kuka ta yini tana yi ta
rasa nutsuwarta, mahaifiyar ma ba'kin ciki ne fal a cikinta zuciyarta tana
aikace-aikacen ta na yau da kullum ta nayi wa 'yar tata fad'an wautar da tayi,
in banda rashin tunani da kuma jahilci ina kai ina kushe hallitar Allah alhalin kaima baka wuce Allah ya mayar da kai
wata hallitar ba, gashinan lokaci guda Allah ya juya al'amarinsa, tayi kuka tayi
nadama gami da dana sani wanda hausawa suke kira da 'keya ce.
Zama mai
tsafta ne yake wanzuwa a tsakanin Abbas da Halimatu! tawayarta bata hanata
sauke hak'kokin mijinta dake kanta ba, Tana kula dashi sosai dan wani sa'in
idan yaga tana hidima dashi har tausayi take bashi dalili yanayin tafiyarta da
rashin kuzarinta ma abin tausayi ne, amma abin na bashi mamaki sosai! kafin ya
dawo daga kasuwa ta gama komai na gida tayi masa kwalliya mai burgewa. duk
sanda ya shigo gidan yayi tozali da ita wani farin ciki ne yake rufeshi, wai
shin meye aibunta ne? Halimatu bata da wani abu ko nakasu a gurinsa tinda duk
wasu hakkokinsa tana saukewa kwata-kwata nakasarta bata dameshi ba zahirinta
yake so ba wani abu na jikinta ba, zaman lafiyar da suke da juna ya sanya yake
ji a cikin ransa zai iya zama da ita har'karshen rayuwarsa.
*****
Wata goma
cif da auransu Maryam matar Yayanta magaji ta haifi d'a namiji, murna da farin
ciki a gurinta tamkar ita ta haihu kullum tana gidan tare da mai jego tayi ta
hidima da ita da jinjirin 'Yan uwan Maryam suyi ta tausaya mata idan sunga ta
wani abun na wahala sai suce ta zauna,
murmushi kawai take musu ta rabu dasu
idan kuma sun matsa mata takan ce dasu itafa babu abunda ba zata iya ba
saboda haka su daina yi mata kallon mara lafiya da rashin kuzari! To suma ganin ranta ya 'baci
yasa suka daina cewa da ita komai! kafin ma suzo ta shiga gidan ta gyara tsaf
ta gyara yaron sannan ta had'awa maijego abun kari, sannan ta dawo gidanta tayi
wanka ta shirya ta sake komawa, haka ta dinga zurga zurga har sai da akayi suna
inda yaron yaci sunan Maigidanta Abbas sai take kiransa da
Amir...................KullumAmir a hannunta yake wuni sai dare take mayar
dashi ko kuma idan ya bukaci nono sannan,
gabadaya dai ita Maryam haihuwar yaron tayi amma raino yana gurin
Halimatu, idan ta dauki yaron tun safe to sai dare ita dashi.
Abbas bashi
da matsala ta 'bangaran wannan dan shima mutum ne mai son yara duk sanda ya
dawo ya tarar da ita tana fama da takwaransa yakan ji dadi yayi ta addua Allah
suma ya basu nasu mai albarka.
Shakaru uku
da auransu Halima bata ta'ba 'batan wata ba,
gashi har anyiwa Amiri 'kanwa Ilham, Abbas tun yana daurewa dai har ya
kasa hakuri yace ta shirya suje asibiti a dubasu, koda sukaje likita ya dubaso
gabadayansu babu abunda ke damunsu kawai dai lokacin haihuwarsu ne baiyi ba,
likita ya rubutu musu magani mai kyau yace suje suyi amfani dashi insha Allahu
za'a dace.....Dukkaninsu a sanyaye suka koma gida, kuma ba suyi 'kasa a gwiwa
ba suna amfani da maganin kuma suna sake kula da kansu.
Ramlatu kuwa
a duk sanda suka had'u da Halimatu a taro sai ta zage ta tayi mata gorin rashin
haihuwa, duk taro na family dinsu sai ta tara mata mutane tayi ta nuna ta tana
fad'in mugwayen kalamai a kanta, wata irin tsana Ramlatu keyi wa Halima ko ta
mece oho! dan akwai ranar da tazo har gida taci mata zarafi da fad'in sun gaji
da jiran gawon shanu dan su duk irinsu babu mara haihuwa saboda haka sun gaji
da daci da ita idan ba zata haihu ba to zasu kawo wacce zata cika musu gida da
'ya'ya.'
Wannan cin
zarafin ya 'bata marai rai sosai ta yini tana kuka dan ki girki ba tayi ba
ballanta tayi wanka ta shirya kamar yanda ta saba, koda maigidan ya dawo rasa
gane kanta yayi, tambayar duniya tayi masa shuru sai kuka take yi, tsayin
shekaru uku da auransu bai ta'ba fuskantar irin wannan matsalar daga gurinta
ba, da kyar ya samu yayi wanka ya futo palon tana dai zaune a inda take tana
kukan da take, zama yayi kusa da ita yana sake rarrashinta kan ta fada masa
abinda ke faruwa, da kyar tayi masa
magana tana hawaye gwanin tausayi tace ita taga ji tunda bata haihuwa ya 'kara aure ko kuma ya
saketa dan cin zarafin da Yayarsa take mata ya isheta.
Ransa idan
yayi dubu ya 'baci! shin wai me yake damun Ramlatu ne? ina ruwanta da matarsa
ina kuma ruwanta da rashin haihuwarsa, idan zai mutu bai haihu ba bai dameta ba
shine yaga zai iya zama da matarsa a haka, shi kam ya rasa wace irin 'kiyayya
Ramla keyi wa Halimatu, hakuri ya bata sosai yace zai same ta yaja mata kunne
kan kada ta sake zuwar masa gida.
Jin abinda
ya fad'a yasa hankalinta ya tashi sai ta dinga bashi hakuri tana nuna masa
illar abinda zai aikata, mutukar ya tunkari Ramlatu da wannan maganar to babu
shakka ya sake rura wutar gaba mai zafi a tsakaninsu, kuma ita ba zata so su
samu matsala da 'yar uwarsa ba, Nuna mata yayi ya hakura ba zaije gidan
Ramlatun ba........Washe garin ranar kafin ya tafi kasuwa sai da ya tsaya gidan
Ramlatun sukayi ta babu kyau babu dad'i a tsakaninsu, dan ya nuna mata
mahimanci da matsayin Halima a gurinsa kuma ya nuna mata cewar itama ta tsaya a
matsayinta na 'yar uwarsa mutukar tasan wata fitina ce zata kaita gidansa to
kada ta sake zuwar masa gida, dan tuntuni shi ya riga yasan Allah ne ke bada
haihuwa ba wani mahaluki ba! Ramlatu kuka taci ta 'koshi 'dan uwanta da take
alfahari dashi shine yazo ya ci kata mutumci a gaban kishiryata lallai babu
shakka dole sai ta tashi tsaye kan Halima dan da alama Iyayenta suna tsaye a
kanta gurin ganin ta mallake mata d'an uwa.
*Kaji rigima
ta Ramlatu ke ba uwar Abbas ba komai ba amma kina kishi da matarsa, Uwar miji
aka sani da kishi da matar d'anta Uwar mijin ma irin wacce bata san abinda take
ba.*
Abbas
zuciyarsa wasai yaje kasuwa yayi harkokinsa......koda suka tashi daga kasuwar
kai tsaya 'Kofar Na'isa suka nufa dan ji yake idan bai fad'awa mahaifiyarsu
abunda Ramla ke masa ba za'a iya samun matsala nan gana gwara ya fada mata ta
kira ta ta ja mata kunne.
Hajiya Abu
ranta ya 'baci sosai tace"Ni dik abinda ke faruwa a tsakaninsu ban sani ba
wallahi amma Wannan yarinya anyi babbar kwabo wallahi dan taga matar taka mai
saukin hali ce shiyasa take mata cin kashi a ko'ina amma kayi hakuri ka kuma
bawa Halimatun hakuri insha Allah zan aika yara har gidanta su kira min ita zan
mata tsakani da matarka duk sanda ta sake zuwa gidanka domin ta kuntatawa
matarka to babu shakka na samu labari da Alhaji maihifinku zan had'ata....
To tun daga
wannan rana Halimatu ta samu lafiya Ramlatu ta saurara mata da gorin haihuwa
ammafa sa'i da lokaci suka had'u a wata sabgar sai ta yar mata da habaici
al'amarin Ramlatu sai addua.
*****
Halisa ce ta
shiga kara kaina a gidan, mussaman ranaku guda biyu Juma'a da Lahadi ranakun da
ta tabbatar da cewar maigidan nan bai futa sai taci uwar kwalliya ta sanyo
turare mai 'kamshi tazo ta yini a gidan! idan sun had'u dashi tana nuna masa
kamar babu wani abu a ranta, ta hakura dashi
kawai ta zuwa ziyara ne gurin 'kawarta!
Sai dai ya girgixa kansa kawai ya shareta dan shi ba yaro bane ballanta
ta raina masa hankali.........Ita kuwa Halima zuciyarta ce ta shiga sa'ka mata
wani abu! tana ganin tunda dai har yanzu Halisan bata da tsayayye mai zai hana
ya aureta ya had'asu tunda ta lura da Halinsa tayi hankali kuma duk wasu alamu
da take nunawa a kan mijin nata ta gane sabida shi take zuwa gidan........Koda
ta sameshi da maganar cewa yayi zaiyi shawara zai fada mata kome ya yanke!
Kwana biyu
ta sake tuntu'barsa da maganar ya dinga kallonta yana mamakinta yace."Ke
kina ganin idan na auri Halisa na had'aku babu matsala kuma zaki iya zama da
ita."?
Cikin farin
ciki tace"Zan zauna da ita tsakani da Allah nasan ko ta nufe ni da sharri
zai koma kanta tunda ban cuce ta ba, sannan kuma ina so ka aureta kaga tanan
za'a tabbatar da rashin haihuwar mu shin
waye yake da matsala tsakanina da
kai."! Wannan magana da tayi sai ta sake sa masa 'kwarin gwiwa shima yana
so ya tantance waye mara lafiya a cikinsu, kai tsaye ya tunkari Halisa sa
maganar, ranar kamar ta zuba ruwa a 'kasa tasha dan farin ciki! ta dinga murna
da godewa Allah! Yace."Ina so ki zauna lafiya da Halimatu dan da yawun
bakinta nazo nan neman auraki kada ki shiga gidana ki tayar mana da hankali mun
gina rayuwarmu cikin mai kyau da
inganci" Halisa taji wani irin d'aci a ma'kogwaronta! wato ma ba'a karan
kansa yazo neman auranta ba sai da izinin matarsa! 'kwafa tayi a cikin ranta! a
zahiri kuwa cewa tayi" Haba Alhajina kada ka damu zan zauna lafiya da ita
ai ko lokacin baya ma kuruciya ce ta janyo nayi wannan furucin amma ka daina
kokwanto da shakku a kaina."
Yaji farin
ciki ya kamashi dama can yana son Halisa halinta ne baya si to tunda dai yanzu
tayi hankali zai aureta su zauna tare cikin inuwa daya.
Ba'a wani ja
dogon lokaci ba aka d'aura aure Halisa ta tare a dakinta, da yake gidane mai
dauke da bangare uku sai kowa ya dauki d'aya, kasancewar babu yara a gidan yasa
maigidan ke bin 'Dakunan matayen nasa bai tare a nasa part ba din sai ranar da
ya tara iyali tukkuna.
*Rubuta
'karya sakaka! babu tushe ballanta makama ba za tayi armashi ba! My Fans ku
cigaba da karanta tushen labari domin shine makamar zance Labari na gaba.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram
Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR
ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA
WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar
Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
_*Allah
Sarki My real Fans♥️ kuyi hakuri ban san maganar da nayi
zata 'bata muku rai ba, nagode kwarai da kulawa, kamar yanda bakwa so mutumcina
ya zube nima bana so naku ya zube, ammafa kusa ni sun d'auke ni sun sani a
gruop dinsu dan su samu damar cin mutumcina, To ina ro'kon Allah ya mutuntani
wanda yake da tunanin tozarta ni ko yaci mutuncina Allah gaka nan gashi
nan........Ke kuma my Aminiya kiyi hakuri kinfi kowa sanin halina yanzu ma
raina ne ya 'baci! to amma insha Allah kome zai biyo baya na sharri zan had'a mutum da Ubangijin da ya hallice
shi.🤗*_
*Wallahu
galibun Ala amrihi👏🏻*
*4*
Sati biyu da
shigowar Halisa gidan al'amura suka sauya, Halimatu ta kasa gane kan mijin nata
gabad'aya Halisa ta ri'ke masa wuya ko yana kasuwa bashi da nutsuwar kirki
mutukar bai dawo gida yayi tozali da ita ba, ranar girkin Halimatu sam bai da
wani kuzari da walwala yakan dad'e ma a waje bai shigo ba, idan ma ya shigo
d'in babu wani abun arziki da yake tsinana mata ba kwanciyarsa yake yi yai bacci! Halima ta shiga damuwa
matsananciya ta rasa wanda zata samu ta fad'awa damuwarta gabakidaya Abbas ya
sanja mata baya kula da ita sannan ba ya zama yaci abincinta kamar da idan tayi
masa magana sai yace."A koshe yake shine dalili, Ita kuwa Halisa data
fahimci rashin jituwa a tsakaninsu sai ta sake zage damtse gurin ganin ta sake
mallakarsa, kissar yau daban ta gobe daban, duk abincin da zata bashi sai ta
bad'e shi da magani abun mamaki kuma Yayarsa Ramlatu itace ke kawo mata maganin
mata dana mallakar zuciyarsa, ita dai burinta Halimatu ta wulakanta a gidan.
Ranar Asabar
har ya futa kasuwa da jaraba ta ciwo shi ya
dawo gida, a maimakon ya nufi 'bangaran Halimatu tunda Girkinta ne sai
kawai ya nufi bangaran Halisa, domin a yanda yake jin kansa yana ganin kamar
Halimatu ba zata iya dashi ba, sai yanzu ya gane cewar Halisa ce dai-dai dashi
dan tana iyawa da fitinarsa ita kuwa Halimatu rashin kuzarinta a ko'ina ma
gwadawa take, ada hakan bai dame shi ba sai da ya auri Halisa ya gane cewar
itace zata iya dashi, dan jaraba irin tashi baya tsayawa kan hallitar da Allah
yayi masa duk karfi da kuzarinsa sai ya had'a da maganin 'karfin maza, kullum
akwai wanda yake kawo musu magani kasuwa suyi ta siya suzo suna gallabar
matansu da daddare.
Halisa duk
da tasan ba girkinta bane bai hanata nuna masa kulawa ba kar'barsa tayi hannu
biyu suka shiga d'aki suka shafe awa kusan hud'u suna abu
daya............Halimatu ce ta shiga sashin tana sallama a palon taji shuru
idanunta ne ya sauka kan hular maigidan da key dinsa na mota da kuma rigarsa
kan kujera.
Tabbas kayan
daya sa ya futa dashi ne a dakinta ya
shirya kuma asali ma itace ta dauko masa kayan dole kuma tayi mamaki! kafin ta
dawo daga tunaninta suka fito daga dakin a tare dashi da halisan daga shi sai
gajeran wando, ji tayi yana fad'in "Zo ki bani abinci naci a gurguje na
koma kasuwa na bar mutane na jirana."
Had'a ido sukayi ita dashi! sai
ya wani dake! kamar ba mara gaskiya ba, ya bude baki zaiyi magana kawai sai ta
juya ta fita daga palon.
Jikinsa ne
yayi sanyi ya zauna kan kujera yana kokarin mayar da kayansa, tabbas yasan wani abun da yake a gidan baya
kyautawa sam be san meya sa ba yanzu kwata kwata baya damun cikakken
satisfaction da Halimatu! bata da ni'ima kuma bata gamsar dashi kamar yanda
Halisa ke gamsar dashi, gashi Halisa ta iya salo-salo shi kuma haki'kanin
gaskiya yana so a dinga kula dashi kan shimfida.
Halisa ta
fito daga kicin da abinci a hannunta, mikewa yayi da fad'in" Bana jin zan
tsaya cin abincin nan zan koma kasuwa yanzu.''
"Haba
dai don Allah ka zauna kaci gashi da zafinsa dama ban jima da gamawa
ba." Girgiza kansa yayi ya nufi
hanyar fita yana kallon agogon hannunsa da fad'in "Biyu da rabi yanzu na fada miki akwai mutanan dake jirana."
Sakin
bakinta tayi ta bishi da kallo tana girgiza kai, da sauri kuma ta ajiye plate
din abincin taje bakin window ta d'aga labule tana le'kensa, gani tayi ya nufi gurin Halimatu, shi da yace
sauri yake yi to mai kuma ya kai shi gurin ta........Takaici kamar ya kasheta
ta zauna kan kujera tana cizar yatsa.
Koda ya
shiga palon samunta yayi zaune a kan kujera ta tsirawa guri guda ido tana kuka!
yaji wani irin tausayinta ya kama shi, yana sonta baya son ganinta cikin damuwa
shiyasa yaji wani irin rashin kuzari a jikinsa.
Kafin ya
karasa inda take sai da ya tanadi kalaman da zai wanke kansa a gurinta.
Cikin wata
mayaudariyar murya ya kira sunanta had'e da kamo hannunta, shuru tayi bata amsa
ba, yace."Ki gafarce ni hakika nasan ni mai laifi ne a gurinki, kin san
dan adam ajizi ne, ina tausaya miki ne shiyasa bana so na dinga d'ora miki
lalurata."
Hannunta ta
cire a cikin nasa tace"Wallahi ban ta'ba tsammanin haka daga gurinka ba,
ashe dama duk wani abu da kake fad'a a baki ne? Halisa ko wata uku cikakku ba
tayi ba ka sauya gabadaya ka daina kula dani baka sauke hakkina dake kanka,
yausha rabon daka hada shimfida dani? ina tunanin tunda Halisa ta shigo gidan
nan tsayin wata uku sai biyu ka kwanta dani shima sai dana nema sannan kuma
abun har ya kai ka dinga satar kwanana kana kai mata, ina hankali da tunaninka suka tafi? idan ni
bana ganinku ai Allah yana kallonku kuma kasan sai ya saka mun." Jiki na
kyarma yace"Na sani wallahi kiyi hakuri
ki dauki hakan a matsayin tsautsayi! na fada miki ajizanci ne irin na
d'an adam amma ba zan sake ba kuma inaso kice kin yafe mun."
Tace"
Sai ka fad'a mun sau nawa kana satar kwanana kana kai mata." Da sauri yace."Yau ne kawai shima kuma
akashi aka samu." Ta goge hawayenta a hankali tace"Na yafe maka amma
dan Allah ka dinga kiyayewa kana kokarin sauke hakkina dake kanka.
Yace."Insha
Allah ki tayani addua nima cikin 'yan kwanakin nan wani iri nake jina."
Tace."Insha Allah zan cigaba dayi maka addua harkarshen numfashina."
Mikewa yayi yana fadin." Muje ki rakani ko." Ta mike tana mirmushi
tamkar baiyi mata laifi ba suka jera tare suka futa har inda motarsa take.
Halisa har
yanzu na tsaye bakin window tana kallonsu suka futo suka tsaya a bakin mota
suna magana! gani tayi Halimatun na dariya tana kallonsa shi kuma ya kamo
fuskarta ya sumbuta, ya shiga mota hade da daga mata hannu.......Zaman da'baro
tayi kan kujera tana hargitsa gashin kanta, kai jama'a!! wai shin Halimatu wace
irin macace ne? wacce bata da zuciya bata kishin kanta! ai idan itace mijinta
ya saci kwananta ya kaiwa kishiyarta ranar sai ta kusa kashe shi da tashin
hankali, amma ita duba dariya ma take harda rakoshi bakin mota.
Wayarta ta
dauka ta kira Yaya Ramlatu! ta daga
wayar suka gaisa, Murya na rawa tace"Yaya al'amura fa sun dagule wallahi!
ban san wane irin so Abbas kewa Halimatu ba! daga aiki ya fara sai kuma ya karye! gashi itama kamar mayya duk abinda za'ayi
mata bata fushi, 'karewa ma kwananta ya kawo min a maimakon taji haushi sai ma
take dariya harda rakoshi bakin mota." Yaya Ramlatu ta shiga girgiza kanta
tace" Nasha fad'a miki Uwarta da Ubanta ba'a zaune suke ba dan ita bata da
kuzari da 'kafar yawon gidajen malamai Ubanta 'kasurgumin dan tsubbu ne duk wasu
asararai yana dasu, ina kyautata zaton yayi aiki mai zafi akan Abbas din, amma
duk yanda zanyi sai nayi na wargatsa shirinsu." Halisa tace"Ni
wallahi yanzu babban burina ta fita ta bar min gidana sannan naga na samu ciki
na haihu." Ramlatu tace'' Kada ki damu zaki haihu ita kuma zata fita ta
bar miki gidanki zaki zauna tare da 'yayanki insha Allah zanyi miki kokari akan
wannan lamarin." Tace"Nagode Yaya Ramlatu! Sallama sukayi Ramlatu
tace"Yauwa dama inaso kiyi dubara a gurin mijin naki ki samu 'yan kudi
masu kauri sai ki kawo min dasu nake so naje a taimaka miki."
Tace"Insha Allah zanyi kokari kamar nawa ." Tace"Dubu hamsin ma
ta isa."
Ajiyar
zuciya ta sauke tace" Zan duba inda yake ajiyar kudinsa idan ya bar key
din a jiki zan dauko zan kawo miki anjima dan nafi so ayi komai da
zafi-zafi."
Ramlatu
tace"A'a kada ki daukar masa kudi ya gane fa." Tace"Ai suna da
yawa ba zai gane ba tunda kusan kullum sai ya shigo dasu kafin ya kai
banki." Tace"To shikkenan ina sauraranki idan kin kawo min ni kuma
nayi miki al'kawari komai yamma zan tafi
gidan *Yar Sa'adu."*
Halimatu kuwa zuciyarta fes ta futo daga
bangaranta ta nufi na Halisa domin yi mata sallama tana so taje su gaisa da
iyayenta sannan kuma ta shiga gidan Dan uwanta su gaisa da matarsa Maryam,
abinda yasa Maryam ta rage shigowa gidan saboda zuwan Halisa dan bata so wata
hatsaniya ta tashi a tsakaninsu sunanta ya fito, dama kuma ta lura da irin
wulakantaccen kallon da Halisa ke mata, shiyasa gabadaya ta dauke kafarta daga
gidan, sai dai sa'i da lokaci ita Halimatun ta shiga su gaisa.
Halisa na
kokarin zaro kudi cikin drowar taji sallamar Halimatu a palonta, da sauri ta
zabura ta futo palon tana kallonta, Halimatu ta fahimci rashin gaskiya a tare
da ita, girgiza kanta tayi tace"Halisa zan je gida mu gaisa dasu Baba
Malam sai nadawo." Cikin ya'ke tace"To sai kin dawo dan Allah ki
mi'ka min gaisuwata gurinsu."
Tace"Zasuji
insha Allah." Juyawa tayi ta fita, Halisan ta rakata da wulakantaccan
kallo tana cin laya a kanta.....Tsaki taja ta koma dakin ta cigaba da
ciku-cikun dauko kudin daga drowar da take a kulle dan ba taga key din ba amma
dan jaraba sai da tasan yanda tayi ta zura hannunta ta zaro kudin duk sun ya
mutse, da kyar ta samu ta ciro dubu talatin da biyar ta hakura haka, kaya ta
sanja ta zuba kudin a jaka tasa kai ta fita daga gidan ba tare da maigidan ya
sani ba.
Baba Malam
da Baba Talatu sunji dadin zuwan 'yar tasu duk sanda ta kai musu ziyara sukan
yi murna da farin ciki ganinta cikin nutsuwa da wadata!
Bayan taci
abinci sai suka shiga hira da mahaifiyarta Na'ajatu ce ta shigo gidan hannunta
rike da buhun kayan wasanta duk tayi bud'u-bud'u da jikinta, Baba Talatu ta
harareta da fadin" Kin gama yawon wasan naki yunwar cikin ki ta koro ki
ko."'? Zum'bura bakinta tayi tana kokarin yin kuka. Baba Talatu
tace"Ai sai ki nemi me baki abinci dan banyi dake ba dama na fada miki
tunda baki zuwa makaranta to zakiyi ta zama da yunwa." Kuka ta fashe dashi
ta jefar fa buhun kayan wasan nata tana kallon Yayar tata. Halima ta riko
hannunta tana rarrashinta, kwanciya tayi a jikinta tana kuka cikin rashin iya
magana sosai tace"Ni ba zani makaranta malam ya dakeni ba kuma sai an bani
abincina." Halimatu ta dinga dariya tana kallonsu suna drama Baba Talatu
tace"To sai naga wanda zai baki abinci a gidan nan." Kuka take sosai
tana fad'in "Ni sai an bani abinci yunwa nake ji."
Halimatu
tace"Yi shuru autar Baba Ni da kaina zan baki abinci ki fad'a min ma me
kike so na siya miki kici ki kyalewa Baba abincinta."
Hawaye
tagoge tana kallonta tace"Zan biki gidanki ki dinga bani shayi da bredi
ita Baba Talatu kullum koko da kosai take bani, sannan bata bani na siyo alawa
da biscuit. " Baba Talatu ta ri'ke ha'ba! tana fad'in "Ikon Allah!
Wato Naja'atu abinda zakiyi mana kenan! kullum fa sai na dafa miki shayi malam
ya siyi miki bredi da madara ga kwai amma kice koko da kosai nake baki."
? Halimatu tace"Gaskiya Baba bakya
ji da wannan autar taki! dubeta dan Allah yanda kika barta tayi daud'a dubi
kitson kanta duk ya tsufa, gashi bakya bata ta siyi sweet da biscuit saboda
haka ni zan tafi da ita gidana, zaki bini ko Auta."!? tafada tana kallonta,
Da sauri ta daga kanta tana dariya.....Baba Talatu ta gyara zamanta tana ta'be
baki tace"Ai sai kuje dama nima na gaji da bari bari yarinya kullum nakan
layi tana yawo ta'ki zama a makaranta malam na kaita kafin ya dawo gida ta
rigashi, ki tafi da ita ku sata a makaranta tayi karatu watakila idan taga babu
idanmu zata zauna a makarantar.
Halima
tace"Aikuwa dai bari Baba Malam ya shigo na fada masa.......To koda Baba
malam yaji kudirin Halima na tafiya da Naja'atu gidanta, be'ki ba yace dai idan
taga da akwai matsala to ta dawo da ita." Baba Talatu ta hada mata kayanta
tsaf suka tafi.
*Wannan
shine mafarin dawowar Naja'atu hannun 'Yar uwarta, a lokacin tana da shekaru
hud'u a duniya dalili kenan da yasa ta girma da tunanin cewar Abba Abbas da
Halimatu sune suka haifeta.*
Ita kuwa
Halisa koda ta fita kai tsaye tudun wuzurci ta nufa gidan Yaya Ramlatu! basu ja
dogon lokaci ba suka dauki hanyar gidan *'Yar Sa'adu* abin mamaki mata ne
dan'kam! a gidan! d'aki guda idan waccan ta shiga ta fito sai waccan ma ta
shiga ta fito har akazo kansu! koda suka
shiga dakin *'Yar Sa'adu* na zaune kan wata kujera katuwar macace mai ki'ba
taci uwar kwalliya ga hancinta da wani abu mai kyalli a jiki, hannu da wuyanta
duk gold ne! taci ubab bleecig kana ganinta kaga 'yar duniya, suka gaisa da
juna, Halisa sai kallon dakin takeyi ganin ko ina manne da hotonan mace da
namiji tsirara! sannan ga wasu manya manyan drowars ko wanne kayan mata ne a
cike a gurin kala-kala! Yaya Ramlatu ta ciro
kudin jakarta dubu talatin da biyar ta zube gaban *'Yar sa'adu* tace" Uwar
dakina wannan itace matar 'kanina da nake baki labari gata nan na kawo miki ita
don Allah ki san maganin da zaki bata wanda zai sanya ta mallaki mijinta ita
kad'ai."
*'Yar
Sa'adu* tasa dariya ta bata hannu suka tafa tace"Lallai 'kawata kina ji da
matar 'kanin nan naki! Allah yasa idan ta samu duniya ta tuna dake, akwai wata
mallaka da zan bata! Amma gaskiya tana da tsada kuma naga kudin da kuka ajiye
bashi da yawa! Wannan mallakar tana da sirri dan da yawa mutane sunyi amfani da
ita sun tabbatar da gaskiyar maganata, ina zaune ake zuwa anayi min tukwuci da
kujerar makka had'e da gida da filaye, dan haka idan kuna da bukatar na baku
ita to gaskiya zaku ajiye min dubu dari biyu."
Halisa tayi
saurin kallonta tana marairaice fuska tace"Dan Allah ki bani wallahi nayi
miki al'kawarin idan bukata tabiya zanzo
na kawo miki kudinki har inda kike." Ramlatu tace"Eh kwarai kuwa ni
zan zama sheda a tsakaninku tunda dai kin tabbatar da ingantuwar maganinki to
ki amince ki bamu insha Allah cikin sati guda za'a kawo miki sauran
kudinki."
*'Yar
Sa'adu* tayi shuru tana tunani! Wani littafi ta dauko ta mikawa Halisa da biro
tace"To na amince zan baki amma kisa hannu! sannan ki rubuta abinda kika
bani da farko."
Halisa ta
kar'ba da sauri tasa hannu! sannan ta rubuta kudin data bayar dubu talatin da
biyar! *'Yar Sa'adu* ta kar'ba ta ajiye, sannan ta mike taje ta dauko mata wata
'yar mitsitsiyar kwalbar fiya-fiya! wani abu mai mai'ko da yau'ki! ne a ciki
tace"Gashinan duk sanda zakuyi auratayya da mijinki to sai ki lakata
kad'an a d'an yatsan ki! sai ki tofa maliki yaumin dini 'kafa takwas a jiki sai
ki lakata maganin a gabanki, kafin kwana biyu zaki bani labari." Halisa ta
dinga washe bakinta tana godiya, *'Yar Sa'adu* tace''Mijin ki zai zame miki
kaska sannan ba'kin ciki zai kashe kishiyarki wannan shine la'kanin
maganin." Wani sanyi ya sauka a zuciyoyinsu jin abinda 'Yar Sa'adu ta
fada, godiya sukayi mata sosai tare da
al'kawarin insha Allahu cikin satin nan zasu kawo mata kud'inta........
*Ayar Allah
da ita ake wasa, wai kuma mutum yace yana so yaga dai-dai a rayuwarsa, Ubangiji
Allah ka karemu daga fad'awa halaka*
*GA MASU
BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #400
SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA
UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN
NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA
DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU
NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN
NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram
Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR
ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA
WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar
Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*5*
Kamar dai
yanda 'Yar Sa'adu tafad'a musu hakane ya kasance, kwana biyu zamantakewar gidan
ta samu tangard'a! Abbas hankalinsa ya dauke gabad'aya baya ganin kowa a
gabansa sai Halisa! Komai ta tambayeshi baya yi mata musu da gardama, kuma koda
ya duba gurin da yake ajiyar kudinsa yaga ba yanda yake ba, da yayi mata magana
kai tsaye tace"Ita ta dauka tayi ba'ki ta sallamesu! shuru yayi mata baice
komai ba, tana ganin ya shiga toilet ta bude drowr ta dauki dauri d'aya ta
mayar ta rufe! Sai da ya fita sannan ta lissafa kudin dubu dari ne, kai tsaye
ta yafa mayafinta ta nufi gidan Yaya Ramlatu da kudin, Gidan 'Yar Sa'adu suka
nufa, nan Halisa ta zauna tayi ta basu labarin yanda al'amura suka kasance ta dinga
basu labarin irin abun da Abbas din yake mata idan suna kwance da daddare! 'Yar
Sa'adu da Ramlatu suka dinga dariya suna tafawa! ita kuwa Halisa tace"Ai gaskiya maganin
nan karshene kuma yaci kudinsa, dan a tsakanin kwanaki bakwai d'in nan sai da
na samu kudi a gurin sa sama da dubu dari! kullum in zai futa sai na tambayeshi
kudi kuma sai ya bani! baya tambaya me
zanyi na lura yana tsoron kada dare yayi yazo da wata magana nace masa wani abu
daban." 'Yar Sa'adu ta gyara zamanta kan kujera tana dariya had'e da
'kas-'kas! da cingum din bakinta,
tace"Ke waye ya fad'a miki dama mata na zama yanzu! ai yanzu dama
na hannuki kiyi kiyi ki samu abunda kika samu kuma ba zama zakiyi ba idan
maganin ya kare ki sake zuwa ki siyi wani."
Halisa
tace"Insha Allahu ai na gane hanya kuma." Cike da farin ciki sukayi
sallama da 'yar Sa'adu suka nufo gida.
****
Bayan wata
uku kullum jiya iya yau a gidan, Halisa ta k'wace miji gabadaya Halimatu ita
dashi sai ido da gaisuwa, Kullum kafin ya futa zai shigo su gaisawa ya zauna
suyi ta wasa da Naja'atu! yana kaunar yarinyar sosai kasancewar sa mutum mai
son 'yaya gashi har yanzu Allah bai bashi ba! Itama Naja'atu d'an zamanta a
gidan ta saba dashi sosai idan ya shigo zuwa take ta zauna a cinyarsa tayi tai
masa labarin makaranta da kawayenta shi kuma ya dinga biye mata, dan wataran
gurin tsayawa sauraran shirmenta har makara yake a kasuwa, Idan kuwa zai futa
sai ya tambaye ta me take so ya siyo mata, sautu iri-iri take masa na kayan
wasa dasu biscuit da chocolate, aikuwa duk abinda tace ya siyo mata baya
mancewa sai ya tsaya a danja ya siya mata ya shiga ya kai mata, wannan abinda
yake yana masifar 'batawa Halisa rai! ta
tsani taga yana nuna kulawarsa kan yarinyar ko kadan tana so kamar yanda ya
banzatar da Halimatun to ya kasance itama yarinyar itama ya daina kulawa da
ita, Idan tana fushi kan abinda yake wa Naja'atun har mamaki take bashi, rabuwa
yake da ita idan tayi ta gaji sai ta hakura.
Ita kuwa
Halimatu ganin yanda yake kula da kanwarta yasa ta rage jin zafinsa a zuciyarta,
addua takeyi kullum Allah ya karkato da hankalinsa kanta tabbas tasan abinda
yake yi ba a hayyacinsa yake ba, tunda tasan irin kauna da son da yake mata,
babu shakka Halisa ba'a haka ta barshi ba.
To Haka dai
Halimatu ta cigaba da zaman hakuri a gidan, tana ji tana gani mijinta yafi
karfinta dan sai yayi wata biyu uku bai kwanta da ita gabadaya an cire masa
sha'awarta a cikin zuciyarsa.
*IDAN RABO
YA RANTSE*
Ranar Juma'a
bayan an sauko daga massalaci ya dawo gida a gajiya ga kuma sha'awar dake damunsa tun daran jiya
dan kwana sukayi rigima da Halisa ta yanko masa uban kudi wai sai ya bata
sannan zata amince ya biya bukatarsa, shi kuma yace ba zai bayar ba sai ta fada
masa abinda za tayi dasu, nan ta shiga inda-inda! ya fahimci bata da hujja sai
yace ba zai bayar ba, shine tayi fushi tace itama ba zata bashi kanta ba, da
yake mutum ne mai zuciya kawai sai ya kyaleta ammafa daurewa kawai yake dan
baida hakuri ta wannan 'bangaran......Washe garin ranar Halisa naganin ya futa
itama ta shirya ta futa itama ta nufi gidan Yaya Ramla domin tafada mata abinda
yake faruwa.......koda ya shigo gidan kai tsaye gurin Halisa ya nufa gabadaya
idonsa a rufe yake bukatarsa kawai yake so ta biya yanzu ya amince zai bata
kudin mutukar dai zata biya masa bukata.
Ya dubata
ciki da waje bata gurin, rai a 'bace ya nufi gurin Halimatu, suna Tare! Da
Naja'atu a palo tana koya mata karatu ya shigo bakinsa dauke da sallama!
Naja'atu ta
mike a guje taje ta d'ane jikinsa tana fad'in "Oyoyo Abbana."! Dariya
yasa ya mi'ka mata kumatunsa kamar yanda suka saba! aikuwa ta manna masa kiss a
gurin! shima yayi mata sannan ya sauketa kasa, yana d'an ya mutsa fuska ya
kalli Halimatu dake ta faman yi musu dariya! hannunsa ya mi'ka mata da fad'in
" Ranki ya dad'e zo muje daki ina da magana." Halimatu ta tsira masa
ido tana kallonsa da mamaki a tare da ita!
Gira ya daga
mata yana yi mata wani irin kallo. Girgiza kanta tayi ta sunkuyar da kanta
'kasa, lallai wato sai yau take da amfani a gurinsa kenan! duk sanda yake cikin halin sha'awa tana ganewa.
Ji tayi ya
kamo hannunta ya mikar da ita tsaye, gudun kada yayi abun kunya a gaban Yarinya
yasa tayi saurin cire hannunta tace"Kaje ganin nan zan shigo." Babu
kunya ya nufi bedroom dinta yana wata irin tafiya.
Zama tayi
kan kujera tana kallon Naja'atu na rubutunta sai da ta tabbatar abinda take ya
dauke mata hankali sannan ta mike a nutse ta bishi dakin.
Wannan
had'uwar tasu ta firgita Halimatu gabad'aya mijin nata ya sanja mata hallitarsa
ma kamar ta sauya, ya zage karfi a kanta yana bugunta babu tausayi da jin 'kai
irin wanda yake mata, sosai yake sarrafata salo-salo duk ya fice daga
hayyacinsa itama sai wuya yake bata, kukan wahala take masa tana bashi hakuri
ya saurara mata haka, sam ba haka ya saba yin mu'amula da ita ba, da kyar ya
saurara mata ya kwanta gefanta yana maida numfashi........To tun daga wannan
had'uwar Ubangiji ya zartar da ikonsa ciki ya shiga ya zauna daram a mahaifar
Halimatu, cikin kuma da bai bayyana kansa ba sai da yayi wata hudu tukkuna
sannan Allah ya bayyana shi, saboda ita kanta Halimatu bata san da ciki a
jikinta ba kasancewar ba ko wane wata take al'ada ba shiyasa duk ta rikirkice,
ta dinga kokwanto a kan ciki.......Kai tsaye asibiti ya dauketa sukaje, likita
ta dubata sosai dan har scanning akayi mata ciki wata hudu kuma yana cikin
koshin lafiya. Abbas ya rasa inda zai saka kansa saboda farin ciki, tun a mota
ya kira wayar mahaifiyarsa ya sheda mata abinda ke faruwa, Hajiya Abu tayi
murna da farin ciki sosai ta kuma yi addua kan Allah ya sauke ta
lafiya........Halisa kwanan kuka tayi da taji labari wai Halimatu nada ciki, ya
akayi haka ta faru? wai dama mijin nata ashe yana lallabawa gurin Haliman yana
biya bukatarsa bata sani ba, lallai zai shigo ya sameta.......Shi kuwa da farin
ciki a tare dashi yake sake jaddada mata k'aruwar da ya samu! ta hasala! sosai
ta dinga zazzaga masa rashin kunya kamar zata zage shi! aikuwa ta fuskanci
'bacin rai! dan lafiyayyun marika tasha wanda hakan bai ta'ba faruwa ba tsayin
shekarun auransu, Yayi mata gargadi sosai kan tsaurin idon da take masa kana
kuma ya dauke mata wuta gabadaya ya daina kulata, ya tare sashen Halimatu!!
Halisa ta
zama tamkar mahaukaciya gashi *'Yar
Sa'adu* bata gari ta tafi Nijar dama 'Yar can ce kullum ita kenan a tafe gurin
zuwa gidan Yaya Ramlatu, suna tattauna yanda zasu 'bulluwa al'amarin, Ramlatu
tsoron zuwa gidan takeyi saboda tasan halin 'Kanin nata zai iya kunyatata
shiyasa ta zauna a gida, Halisan na zuwa inda take................Sau uku yana
dawowa gida ya tarar bata nan a'lamarin da ya fusata shi sosai, ya tsaya
harabar gidan nashi yana kai kawo kana ganinsa kasan ransa a 'bace yake, Tana
shigowa ya buga mata tsawa da fad'in "Ta koma inda ta fito! gabanta ne ya
fad'i baki na rawa tace''Wallahi naj.......Hannu ya daga mata yace." Bana
bukatar naji komai daga bakinki sau uku ina dawowa gida bakya nan ina kike zuwa
ba tare da na sani ba? saboda haka ki fuce min daga gida sai nazo gidanku inaso
kafin nazo ki fada musu inda kike zuwa."
Halisa ganin
yayi fushin mai tsanani yasa ta juya jiki a sanyaye ta futa daga gidan, kai
tsaye gidansu ta nufa tana kuka.
A takaice dai sai da Halisa tayi sati biyu a
gidansu sannan Yaje yayi bikon ta iyayenta ran su ya 'baci sosai jin irin
abinda take aikatawa na fita yawo ba tare da izinin mijinta ba mahaifinta yace
da Abbas duk sanda ta sake futa bata fada masa ba to ya sanar masa sai ranta ya
'baci sosai! Halisa ta tsorata sosai d'a zaman
da tayi a gidansu har jikinta ya
soma sanyi tsayin sati biyu da tayi a gidan nasu ji take tamkar shekara biyu
tayi, ganin ya shere ta da ita al'amarinta yasa jikinta yayi sanyi tana addua
kada Allah yasa yace zai saketa.....To tunda ta samu yanzu ya mayar da ita sai
ta dauki aniyar gyara kuskuranta a gurinsa amma dai duk da haka ba zata fasa
yiwa Halima zagon 'kasa ba.
Koda ta
dawo gidan d kafin ya sakar mata fuska
sai da ta dade tukkuna sannan ya warware gabadaya, tun daga sannan ta kiyaye
abinda zai dugunzuma masa zuciya wanda zai haifar da sa'bani tsakaninsu har ta
kaishi ga korata gidansu.
***
Cikin
Halimatu nada wata bakwai Allah ya bawa Halisa nata, Halisa aka dinga murna da
zumudi ana iyayi! shi kuwa maigidan ya dinga biye mata da duk abinda take so
burinsa kawai yaga matayen nasa sun
haihu lafiya shima ya shiga sahun
mutanan da ake kira da Abbah, duk da sunan da Naja'atu ke kiransa dashi kenan
Abbana, ko Abban Naja, a duk lokacin da zata kirashi da sunan yakan ji wani iri
dan saboda yasan ba shine ya haifeta shi dai yafi bukatar 'yayansa na cikinsa
su kirashi da wannan suna.
*****
Lafiya lau
Halimatu ta haihu inda ta haifi 'yar ta mace ta d'an d'ebo kammanin mahaifinta
gurin hasken fata gami da siririn hanci, Abbas mai kyau ne sosai irin namijin
da mata keso yana da haske da cikin zati
dogo ne amma ba sosai ba, yana da manya ido da dogon hanci wanda ya
kyata masa fuskarsa, amma kuma bashi da fara'a
da saurin sabo! Mutum daya ya amince dashi cikin abokansa shine
Magaji Yayan matarsa kenan Abba magaji
yasan sirrinsa kamar yanda shima yasan nasa...........Halisa ganin Halima ta
haifi mace sai ta dinga addua Allah yasa ita ta haifi namiji dan tasan farin cikin da mijin nasu zaiyi sai
yafi wanda yake yi a yanzu, hankalinta na masifar tashi a dik sanda taga ya
shiga gurin Haliman ya jima bai fito takan shiga tashin hankali da damuwa
saboda tasan yana can yana shiriritar
da ya saba da shegiyar yarinyar nan
Naja'atu da Babynsa wacce ya sanyawa suna Fatima amma sai suke kiranta da
*Saddiqa* dalili kenan da ya sanya take Allah Allah itama ta haihu itama taga
yana nuna kulawarsa a kan d'anta.
Haihuwar
*Saddiqa* ta janyo masa bud'i da alkairai da yawa, harkokin kasuwancinsa suka
bude sosai yake harkar gwangila na gina gidaje da ma'aikatu da sauransu........Wani 'katon gida yake ginawa a cikin unguwar
*Danbare* sabuwar unguwa ce da masu kudi suka siyeta suke ta gasar gidana gida
a gurin, gaskiya gidan da yake idan aka gama aikinsa babu shakka zai zama abun kallo a gurin
jama'a.
Halisa ta
haihu lafiya lau ta haifi namiji kamar
yanda Scanning ya nuna mata, sai dai kuma cikin ikon Allah kwanan yaron d'aya a
duniya ya koma.....Ihu! ta dinga zabgawa tana kuka dan rashin tawakkali cewa
take wallahi Halima ce tayi mata asiri d'anta ya mutu saboda tana bakin cikin
ita bata haifi d'a namiji ba.
Abba Abbas
tun yana rarrashinta har ta si'ke shi haushinta ya rufeshi, ya shiga nuna mata
illar abinda takeyi, Allah ne ya bata kuma ya kar'bi abinsa dan me zata d'orawa
wani! sai da yayi mata kaca-kaca! sannan ta daina ikirarin cewar Halima ce tayi
mata asiri.
***
Bayan
shekaru uku Halimatu ta sake haihuwa inda ta haifi 'Da namiji! Wanda wannan
haihuwar ta janyo tashin hankali sosai a gidan dan iskokai Halisa ta dinga
tayarwa na 'karya dana gaskiya tana yun'kurin kashe maijego da
jaririnta......Babu arziki ya tarkata ta ya kaita gidansu dan al'amarin yafi karfinsa haka kawai yana
ji yana gani ta illata masa d'ansa.
Ashe iskanci
ne Halisa na ganinta a gidansu, sai ta dawo hayyacinta mussaman da mahaifinta
ya samo malamai, masu ru'kiya suka dinga jibgarta, babu arziki ta dai-dai ta
nutsuwarta ta dinga kiransa a waya yazo ya
dauketa taji sauki!
Shi kuwa
dama tuntuni ya yanke shawara kan cewar zai raba musu gurin zama, dan gudun
aikata mummanan aiki idan baya nan shima ya fahimci duk wani abu da Halinsan
keyi sharri ne da ba'kin kishi da ganin kyashi!
Gidansa dake
*'Dan bare* suka tare shida Halimatu da 'yayansa kana yasa aka gyarawa Halisan
wanda suka bari ta zauna a ciki yana ganin hakan shine yafi alkairi a tare
dasu baki daya...
Wannan
al'amari ya sanya zuciyar Halisa kusan bugawa, gidan da take kulafucin zama a
cikinsa shine zai ce ba zai je da itaba, kuka taci ta koshi tana tunanin mafita
babu shakka ta ko'ina Halima tayi mata zarra! ta haihu har sau biyu kuma ta tare a sabon gida. tabbas dole ne ta
nemawa kanta mafita yanzu ne ta sake gazgata maganar Yaya Ramlatu inda take
cewa mugun sihiri iyayen Halimatu sukayi akan Mijin nata, itama idan hakane to
tabbas zama bai kama ta ba.
To da yake
yanzu bata da matsalar kudi yasa ta d'auki d'amarar shiga malamai domin bukatarta ta biya, duk ranar da ya
kasance ba a gidanta yake ba to idan ta fita tun safe sai yamma zata dawo gida
tare suke yawace yawacen malamansu da Yayar mijin nata.....Yaya Ramlatu bata da
matsala saboda mijinta matafiyi ne shiyasa takeyin abinda take so a gidan, haka
zata fuce ta watsar da 'yayanta a tsakar
gida, kishiyarta Sakina mutuniyar kirki ita ke mata dawainiya da 'yayanta tayi
da nata, tabbas albasa ba tayi halin ruwa ba, dan da Ramlatu ta gado halin
iyayen nata to ba zata aikata abinda take ba.
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA
#300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA
KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI
MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA
BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN
WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU
NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN
NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram
Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR
ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA
WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar
Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*PEGEN YAU NAKU NE*
*My Son
Najib Sa'id*
*Abue Sale
alqurami*
*Bashir
Saleh*
*Umar Abbas
Yusif*
*Muhammad
Karim*
Ina mutukar
godiya da kulawarku a kaina da 'kokarin yi min sharing ina rokon Allah ya
sadaku da alkairin duniya dana lahira Allah ya za'ba muku abinda yafi alkairi a
rayuwarku👏🏻
~~~~~~~~~~~~~~~
*6*
A takaice
dai duk wannan fad'in tashin dasu Halisa sukeyi a kan Halimatu ba suyi tasiri a
kanta ba, saboda halimatu ta kasance mace mai ibada kuma dukkaninsu bata nufe
su da sharri ba shiyasa kullum Ubangiji ke kara kareta daga sharrin su da
makircin su, duk wani asiri da sukeyi baya tasiri idan ma yayi baya dadewa yake
karyewa, ta inda Halisa take samun galaba akan Abbas din shine ta gurin
shaye-shayen magungunan mata to tana d'an janye hankalinsa watarana dan gaskiya
irin magungunan da Halisa take sha suna da tsada har dana turawa sha take ita
dai burinta ta janye hankalin Abbas din ya wulakanta matarsa uwar 'yayansa,
abinda Halisa bata sani ba kuwa shine irinsu Abbas asiri baya saurin kama su
idan ma ya kama su to baya wani tasiri a jikinsu zai karye! saboda Abbas mutum ne me yawan azkar da
karatun al'akurani mai girma gashi sallahr asubah bata wuce shi, shiyasa duk wani asirin da suke masa baya zama a
jikinsa.
Halisa tun
haihuwarta ta farko take samun matsala daga zarar ta samu ciki baya yin kwari
zai zube, ta shiga tsananin damuwa da tashin hankali! ganin 'Ya'yan Halimatu sunyi wayo har sun
soma zuwa makaranta gashi mahaifinsu naji dasu yana yi musu hidima kamar hauka,
ai babu shiri ta bazama yawon gidajen masu magani har gurin 'Yan bori zuwa take
su bata magani tazo ta jika tasha, ta yini tana amai, da murkukusu, amma taki
ta gane hanya madaidaiciya ta fawwalawa Allah domin shine mai bayarwa da
hanawa, Kullum kokarinta ya za'ayi ta haihu ko ta halin 'kaka. Abbas ganin ta
tashi hankalinta dan har ramewa tayi sai yayi musu viza domin zuwa 'kasa mai
tsarki su roki ubangiji hakan be mata dadi ba taso ita ya kaita kasar waje
likitoci su dubata idan ma dashe za'ayi mata zata amince ita gani take idan
sukaje saudian ba zata sanja zani ba! Gabadayan su dashi da iyalinsa suka nufi
kasa mai tsarki, Halisa ta dinga wani iyayi tana shige masa gani takeyi ai
saboda ita aka zo kasar! Halima dai sai
dai tayi mata dariya kawai dan ita wataran idan Halisa na wani abu har dariya
take bata, tana kallonsu zasu shirya su fita ita da Abbas wai zasuje asibiti
sai dai tayi musu fatan dawowa lafiya, ta lura shima mijin nasu na biyewa
Halisan ne dan kawai a zauna lafiya.
Ita kuwa
Naja'atu mugun haushin Halisan take ji dan ta soma hankali a lokacin, idan taga
tanayi wa mamanta wani abu ranta 'baci yake sai tayi yun'kurin magana sai Halimatun
ta hanata, sai dai tayi 'kwafa kawai!
ita hakurin mamanta ta har mamaki yake bata, kuma a duk sanda za taga Abban nasu yana magana da Halisa sai taji
haushinsa, tashi ma take ta bar gurin, wani lokacin kuma idan taga sun shiga
daki da Halisan sun dade kuka take zuwa taci ta koshi! ta fito tana kumbura
fuska, Halimatu ta gane yarinyar na kishinta shiyasa takejin ciwon abinda ake
mata, ta kuma fahimci yarinyar za tayi
kishi sosai dalilin da ya sanya take yi
mata 'yar nasiha a fakaice! Naja'atu kam jinta kawai take yi tana ganin kamar
wani abun ma itace take bada goyon bayan Halisan nayi mata, 'kiri-kiri sai suna
zaune a guri daya Halisa zata tsiri wasu abubuwa wanda suke sawa ta janye hankalin Abban nasu! duk
sanda haka ta faru taga ya tashi yabi bayan halinsa ji take kamar zuciyarta
zata babbake! ko ya fito bata kulashi idan yazo yana musu magana banza take
dashi sai dai yai ta tambayar Halimatu ko wani abun ne yake damunta Halimatu tasan abinda take fad'a masa maganar ta wuce! Naja'atu gabadaya daina
walwala tayi ta daina sakin fuskarta, rashin kunya takeyi wa Halisa a duk sanda tasa mata baki a
cikin maganarta dan Halisa akwai katsalandan daga zarar tazo taga suna hira da
wasa da 'yan uwanta su Saddiqa da Mussadiq sai tazo ta dinga buga musu tsawa
tana hantararsu, aikuwa dama a ciki take da ita, tace watarana suna wasa tazo
tana yi musu tsawa! Tace"Mu dan Allah ki daina zuwa kina takura mana muna
maganarmu ke waye ya takura miki eye? ina cewa abinda kike so shi kikeyi saboda
haka ki daina zuwa kina mana tsawa mtwsss!." Takarasa maganar tana jan
tsaki.
Halisa ta
fusata sosai hannu ta fitar ta tsinka mata mari tana d'ura mata ashar! sai
ambato sunanan Baba malam take tana
zagi! Naja'atu ta dinga kuka tana fad'in "Allah ya isa ba kakana kike zagi
ba naki kike zagi!
Halimatu
tazo tana doke bakinta cikin 'bacin rai tace" Ashe baki da kunya
Naja'atu." Tana kuka tace"Mamma kina ji fa tana zagin Baba Malam me
yayi mata? wallahi sai na fad'awa Abbanmu." Kai tsaye ta nufi dakin da
yake kwance yana bacci! Halisa da Halimat suka bita da kallo cike da mamaki!
Halisa mamakin yarinyar take na mayar da uban wasu nata komai akayi sai tace
Abbanta ko a gidan ubanwa ya zama Ubanta oho.
Yana tsaka
da bacci yaji kukanta a kansa, ya bude idonsa da sauri! yana kallonta a tsaye a
kansa tana goge fuska hawaye wani na sake zubowa, mikewa yayi zaune ya kamo
hannunta ya zaunar kusa dashi.
Cikin
tausasawa yace."Waye ya saki kuka." ? Cikin shashsheka tace"Gata
can Anti Halisa muna wasa da dariyarmu tazo tana hantarar mu wai sai mun tashi
mu bata guri zatayi kallo, shine dan nayi magana ta mareni har da zagin Baba
Malam."
Ransa ya
'baci! Yace." Kan wane dalili zata tashe ku a guri kuna wasa? saboda za
tayi kallo sai ta hantareku! hannunta ya ri'ke suka mike a tare suka fita palon
Halisa da
Halima na tsaye sai musayar yawu suke Halisa na fad'in "Wannan iskancin da
'kanwar taki take yayi yawa haka kawai saboda samun guri ta mayar da uban wasu
nata to tun wuri ki fada mata ba ubanta bane kada ma ta dauka tanada
gadonsa."
Halimatu ta
bude baki kenan za tayi magana ta hango fitowarsu yana rike da hannunta, Halisa
ta kallesu ranta idan yayi dubu ya 'baci! Hura hanci ta shigayi tace"Au!
zuwa tayi ta taso ka daga baccin."?
Ya 'bata
fuska sosai yace."Koda bata tasheni ba dama dai-dai wannan lokacin nayi
niyyar tashi, shin me yaran nan suke miki kullum kike matsa musu bakya barin su
su huta."!
Halisa ta
rik'e bakinta cikin mamaki take dubansa! Yace."Magana nake miki."
Ganin yanda yasha kunu ne yasa ta sassauta murya saboda tasan halinsa sai
tace"Kawai dan nace su tashi su bani guri zanyi kallo shine fa yarinyar
nan ta hau yi min rashin kunya harda zagina."
Da sauri
tace"Ni wallahi sharri tayi min ban zageta ba." Halisa tace"To
nayi miki karya ko." Zumbura mata baki tayi ta murguda mata shi! Halisa ta
shiga jijjiga kanta tana mamakin saken da yarinyar ta samu a gurin maigidan,
kauna da son da yakewa yarinyar ta lura ko 'yayansa bayayi wa."
Yace."Kawai
saboda zaki zauna kiyi kallo sai ki tashesu mai suka tsare miki! bana so ki
sake hantarar min 'yaya duk wani abu da nake nema a duniya saboda su nake
nemansa, kafin Allah ya bani sai da na cire tsammani dan haka dole ne na
kyautata musu dan bana son abinda zai 'bata musu rai! duk abinda suke su zasuyi
cikin nutsuwa da kwanciyar hankali kamar yanda kema kikeyin abinda kike
so."
Halisa
takaici kamar ya kasheta, har ta bud'e bakinta zata ce "Ai ita wannan d'in
da kake magana a kanta ba 'yar ka bace.......Sai kuma ta sanja shawara,
tace" Shikkenan me 'yaya nima Allah ya bani." Tana 'kare maganarta
sai ta fashe da kuka ta nufi daki....Jikinsa ne yayi sanyi kuma, Halimatu ta
kalleshi murya na rawa tace"Haba Abban Naja'atu ba haka ya kamata ka yanke
hukunci ba! kasan kowaye akayi wa haka dole yaji rashin dadi, yarinyar nan
Naja'atu itace tayi mata rashin kunya kamata yayi ka fara hukuntata
tukkuna."
'Dan ya
mutsa fuskarsa yayi kamar zaiyi magana kuma sai ya fasa, hannun Naja'atu dake
cikin nasa ya saki ya juya ya nufi dakin da Halisan ta nufa
Ita kuwa
Naja'atu bata so hakan da yayi ba taso ya kyaleta taje tayi kuka taji ciwon a
ranta kamar yanda take yini tana 'kuntatawa mamanta rai to itama yau ta
d'and'ana taji.
Halima ta
rufeta da fad'a kan abinda tayi tace"Wallahi duk sanda na sake ganin Kinyi
mata tsaki sai ranki ya 'baci ko an fada miki sa'arki ce." ? Kuka tasa ta
nemi guri ta zauna tana fad'in "Mama kina ji fa tana zagin mahaifinki Baba
malam Kinyi shuru dan nayi magana sai kice nayi laifi ."
Jikinta a
sanyaye tace"Dan ta zage shi sai me? ni nasan ba Ubana ta zaga ba nata
take zagi saboda haka na fada miki babu ruwanki da ita har mu bar 'kasar
nan." Shiru tayi kawai ba tace komai dan gaskiya ita ba zata dauki cin
kashi da wulakancin da Halisan keyi mata ba
haka suka cigaba da zaman doya da manja
tsakanin Halisa da Naja'atu babu sassauci kowa najin haushin dan uwansa,
Naja'atu taci alwashi kan cewar duk sanda Halisa ta sake kuntatawa mamanta rai
to itama sai ta 'kir'kiri abinda zai janyo musu fad'a a tsakaninta da Abbansu,
Halisa tunda taga take-taken Naja'atu da irin iskancin da take mata sai ta
shiga taitayinta ta rage yiwa Halima wasu abubuwan na rashin arziki badan komai
ba sai dan sanin matsayin Naja'atu da tayi a zuciyar maigidan nasu, tasan idan
ta tsananta ranta ne kawai zai 'baci a banza.
Sati biyu
sukayi a kasa mai tsarki suka dawo gida, Likita ya d'orasu Akan magani, kan
cewar in dai Allah ya nufa da akwai sauran rabo a junansu to zasu
haihu.............Wata uku da dawowarsu Halisa ta samu ciki murna ta dinga yi
tana adduar Allah ya zaunar mata dashi, to shima maigidan yayi farin cikin
ganin cikin yayi wata hudu bai samu matsala ba, sai ya umarce data zauna ta
daina aikace aikacen gida, mai aiki yace zai dauko mata, tace ya bari zata
dauko 'yar yarta sai ta dinga taimaka mata, aikuwa hakane ya kasance Unguwar
Aisami
ya kaita da kansa taje ta dauko Shamsiyya 'Yar
yarta budurwa ce 'yar kimanin shakara goma sha hida ta girmi Naja'atu da
shekaru biyu, Shamsiyya irin masu shegen iyayi ne gata mummuna amma saboda
tsabar shafa mai tayi fari da haske! murna
sosai Shamsiyya tayi da zuwanta gidan Halisan tasan kafin ta dawo
gidansu sai ta sauya tayi ki'ba dan
gaskiya ko zuwa gidan sukayi da ziyara basa dawowa ranar da sukaje sai sun
kwana dan har daukar kawayenta takeyi ta
kaisu gidan tana musu iyayi kanwar mamanta na auran *Alhaji Abbas Dan
kwagila*........To cikin ikon Allah Halisa ta haihu kalau ta samu 'ya mace sai
dai ba haka taso ba taso ta haifi d'a
namiji dan gaskiya Mussadiq ya tsone mata ido. Ita kuwa Yaya Ramlatu har akayi
suna cikin yada habaici take mussaman idan taga
Halimatu tazo gidan sai ta tsiri shige da fice tana sakin maganar da duk
tazo bakinta........"Duk cikin da ya haifi mace watarana shi zai haifi
namiji Halisa ki kwantar da hankali gabadaya dangi munfi bukatar mu samu zuria
dake dan haka tunda kin fara dasa 'kwan ki a gidan Abbas to kiyi abinda kike so
babu me ce miki don me.!! Ire-iren maganganun da Yaya Ramlatu keyi kenan
Shamsiyya na taya ta, Halima bata ta'ba tanka musu ba abinda ya kawota takeyi
ta tafi.
Ranar suna
da kyar Abbah Abbas ya lalla'ba Naja'atu ta shirya ya kaisu, dan cewa tayi ita
ba zataje ba bata da lafiya wanda shi da Halima duk sun san 'karya take yi
kawai rashin jituwar dake tsakinta da Halisan yasa tace ba zataje
ba.......kwalliya sukayi sosai gabadayan su harshi angon 'karni suna sanye
cikin dakakkiyar shaddar galila mai kalar sararin samaniya(sky blue) sun yi iri
daya da juna Halima da Naja'atu da Saddiqa! dinki iri daya ne a jikinsu doguwar
riga ce wacce tasha uban stone work da aka kashe kudi gurin yin sa
Abbah Abbas
shida Mussadiq sunyi iri daya cikin babbar riga da 'yar ciki hularsu iri daya
hakanan takalman su iri daya, agogo iri d'aya, sunyi kyau sosai dan kafin su
fita sai da sukayi hotona sannan ya kira Salim dan Yayarsa Ramlatu a waya ce yazo ya daukesu.......Salim dan
kimanin shekaru ashirin da biyar a duniya matashin saurayi mai jini a jiki d'an
kwalisa ne sosai kuma yana kan lokacinsa dan babu abinda Abbah Abbas baya yi
masa na rayuwa ya dauki yaron tamkar d'an cikinsa, shine ya tsaya masa kan
karatunsa har yayi degree kuma ya d'ora shi kan harkokin kasuwancinsa Salim
yasan wasu daga cikin sirrinkan Abbah
Abbas amma kuma bai san wasu ba, Salim tun kafin Naja'atu ta kai girman haka
yake sonta yana so su kammala secondary
tukkuna ya tunkari Kawunsa da maganar tabbas yasan shi zai shige masa gaba
gurin ganin ya mallaketa, amma dai duk da hakan yana ta kokarin kafa gwamnatinsa
a gurin Naja'atun, itace take nuna masa bata gane me yake nufi ba.
Koda Salim
yayi tozali da Naja'atu kasa nutsuwa yayi ya dinga kallonta yana sosa kansa ga
wani shegan mirmushi a fuskarsa, Naja'atu ta 'bata ranta tana kallon Abban nasu
dake gyara babbar rigarsa domin shiga mota, murya na rawa tace"Abbah kace
ya daina kallona." Abba Abbas na gyara zamansa a motar ya kalli Salim yana
d'an 'bata fuska yace."Kai bana son shashanci ka shigo mota mutafi na lura
da kai tun d'azu ka damu yarinyar nan da kallo sai wani sosa kai kakeyi na fad'a
maka ba zan baka itaba sai da amincewarta." Salim yasa dariya yana
kallonsa Yace."Haba Kawu dube ni fa kaga ni da kyau! ni ba irin mazan da
mata zasu ce basa so bane, ni nasan nan gaba kadan Ita dakanta zata furta maka
ni take so." Abbah Abbas na murmushi yace."Ni dai na fada maka malam
ka nemi yardar ta dan cikin 'yayana babu wacce zanyiwa auran dole." Salim
yace."Insha Allahu Naja'atu tawa ce."
Mussadiq ya rike hannunsa da fadin"Nima ina so ka auri
Yayarmu." Rank'washin sa Naja tayi ya shiga motar yana kuka, Halima ta
d'auka Abban nasu zaiyi mata fada mai yasa ta dakeshi sai taji yana
cewa"Kai Mussadiq bana son rashin kunya ka tsokane ta ta hukuntaka kuma
sai ka kama kuka." Mamaki sosai ya rufe Halima! Girgiza kanta kawai tayi
dan bata da bakin magana tana iya yiwa Naja'atu fad'a yace dan me shiyasa tayi
shuru da bakinta, hakika kulawar da yake nunawa a kan 'kanwartata tana burgeta
haka nan suma su Baba malam suna jin dadi yanda Abbas din ya r'ike musu 'yarsu
tamkar shi ya haifeta, duk abinda zaiyi wa 'yayansa shi yake mata wani sa'in ma
har yana bambamta ta dasu gurin wani abun.
Gabad'aya
Naja'atu kasa sakewa tayi a gidan sunan ganin yanda jama'a ke musu wani irin
kallo wasu ma sai nuna su sukeyi, dalilin da yasa kenan ta zauna guri guda tana
kalle kalle.......Halima kam kasa zama tayi ta mike ta shiga cikin mutane ana
hidima da ita duk da irin kallon banzan da suke mata hakan bai sa ta koma ta
zauna ba, ta kau da kai tana ta shiga jama'a cikin fara'a ana gaisawa da ita.
Tana zaune a
palo wasu 'yan uwan Halisa suka shigo suna she'ka dariya d'aya daga cikinsu
tana fad'in "Ku tsaya kuga yanda kishiyar Anti Halisa take tafiya."
duk sai su katsaya suna kallonta, sai ta shiga cangala 'kafarta d'aya tana
cillata kamar yanda Halima keyi idan tana tafiya! Dariya suka kwashe da ita
suna tafawa! Shamsiyya tace"Kuma wai a haka a nakashe take matar so a
gurin miji." Duk sai suka ri'ke bakinsu suna kallonta 'karin bayani suke
jira tayi musu! Shamsiyya ta bud'e bakinta za tayi magana taji saukar mari a fuskarta!
Naja'atu ce
tsaye a tsakiyarsu tana zubar da hawaye itace kuma ta mari fuskar Shamsiyya!
Wacce take gwada tafiyar Halimatu ta nuna murya na rawa tace."Yanzu
hallitar Allah kike gwadawa? Ke baki ji kunyar abinda kika yi ba Allah yayi
hallitarsa yanda yake so kina gwada kuna dariya kema fa baki wuce Allah ya
mayar dake haka ba."!! Afusace Shamsiyya tace"Dan kutumar Ubanki ta gwada d'in! shegiya yar karoro! har ni zaki tsinkawa
mari! lallai zan nuna miki nafi ki zafin kai!! kafin Naja ta ankara ta rufeta
da duka! Sai sauran ma suka shiga taya ta suka rufar wa Naja'atu da duka har
sai da ta durkushe a gurin!! Ihu! takeyi tana kokarin kwatar kanta....
Halisa ta
fito daga daki a guje! jama'ar dake waje suka shigo palon suna tambayar abinda
ke faruwa.
Shamsiyya
tana hura huci! ta shiga fada musu karya da gaskiya. Yaya Ramlatu tazo ta tsaya
a kan Naja'atu tana zaginta ta uwa ta uba! Naja'atu kasa motsi tayi dan ta daku
sosai! Halima ce tazo ta kama hannunta ta mikar da ita, tana kuka itama tana
kuka su Saddiqa da Mussadiq na kuka! abin gwanin ban tausayi! Ita kuwa Yaya
Ramlatu kamar kara zugata akeyi ta tara mutane sosai sai aibata Halima da
Naja'atu take da iyayensu kowa na tofin ala tsine a kansu! Halisa ganin abin ya
kwa'be! yasa tazo tana bawa Ramlatu hakuri saboda tasan idan maigidan ya samu
labarin abinda ya faru to babu shakka al'amura zasu 'baci! dan rayukan kowa sai
ya 'baci! da kyar ta rarrashin Yaya Ramlatu tayi shuru taja tawagarta suka fita
harabar gidan domin cigaba da rabon abinci.........Halisa ta dinga yiwa su
Shamsiya fada kan abinda suke kokarin janyo mata, dukan Naja'atu da sukayi yana
nufin abubuwa da yawa a gareta hakan na iya barazana ga auranta, shiyasa bayan
ta shiga dakin tasa Mussadiq ya kira mata Naja'atun! K'in zuwa tayi sai da Halima
ta rarrasheta sannan ta shiga dakin.
Halisa ta
kwantar da kanta tana fadin "Naja'atu kiyi hakuri kinji ko abinda su
Shamsiyya sukayi miki kinga dai a gabanki na hukunta su kuma nayi musu fada dan
Allah kada ki fadawa Abbanku." Zum'bura bakinta tayi tace"To me yasa
baki rama mun dukan da sukayi min ba! Ni wallahi bazan yarda ba sai na fada
masa sun zageshi sun zagi Baba malam sun dake ni kuma sun kushe hallitar
Allah."
tana k'are
maganar ta ta fita daga dakin, Halisa rakata tayi da kallo baki a sake.
Tana fita
daga dakin ta dauki wayar Mamanta wani guri ta 'buya ta kira numbarsa, ganin
numbar Halimatu yasa ya dauka da sauri yace"Ranki ya dade yaya ina fatan
komai lafiya."? ai kawai sai yaji fashewar kukan Naja'atu a kunnansa! Ya
mike tsaye da sauri! Yace''Naja'atu
lafiya kike kuka yi shuru ki fada mun abinda akayi miki?" cikin sar'kewa
tana jawo numfashi irin na sharri ta shiga wassafa masa abinda ke faruwa a
gidan sunan." Ranshi idan yayi dubu ya 'baci! Yace."Daina kuka kinji
ko? zan dauki mataki wato Halisa ta tara mutane ne dan ta tozarta ni! babu
laifi ki bawa maman taki wayar zamuyi
magana." Tana shashsheka da goge fuska tace"To." Zuwa tayi ta
kaiwa Halima wayar da fadin "Gashi Abbanmu zaiyi magana dake." Halima
ta fita daga cikin mutane ta samu guri tana amsa wayar, Jinsa a fusace! yasa ta sassauta mirya tana so ta
fahimtar dashi yaki sauraranta yace."Zai turo Salim yanzu yazo ya daukesu
ya mayar dasu gida ita kuma Halisa zata gamu dashi." Kafin ma tace wani
abu ya kashe wayarsa.....Kasa'ke tayi da waya a hannunta tana mamakin wannan
al'amari! gabadaya idan Naja'atu zata fada masa magana baya tsayawa yayi nazari
zai hau kai ya zauna, tabbas ba sune suke da laifi kan faruwar hatsaniyar ba,
to amma yana da kyau yabi komai a sannu tasan halinsa da mugun zafin zuciya zai
iya aikata abinda ba shikkenan ba.
Aikuwa dai
bayan watsewar taron suna da ya shigo gidan Halisa sai da ta fuskanci 'bacin
rai sosai dan cewa yayi ta ajiye masa 'yarsa ta fice masa a gida tunda dama
abinda ta shirya yi kenan shiyasa ta damu sai tayi taron suna dan haka ta ajiye
masa 'yarsa ta bar masa gida, kuka wurjan-wurjan ta dinga yi tana bashi hakuri
tana kuma gaya masa yanda al'amarin ya kasance cewar ita sanda abun ya faru ma
tana daki bata da laifi.
Jin tana
ambatar sunan Shamsiyya a maganar yasa ya 'kwala mata kira tana zaune a palo
tayi tsuru tsoronta Allah tsoronta annabi kada yace ta bar masa gida, Da sauri
ta shiga dakin, yace"Kece mai gwada yanda matata Halima take tafiya
ko."? Girgiza kanta ta shiga yi tana rantse-rantse! Yace."Duk abinda
kukayi wa Ubangiji ku dashi ne dan haka bana bukatar ganin ki a gida nan ki
dauki kayanki ki tafi." ai ta haihu babu wani sauran aiki yanzu."
Hannu ya zira cikin aljihu ya dauko dubu daya ya mika mata da fadin"Ki shiga
mota." Kar'ba tayi jiki a sanyaye ta fita daga dakin, zuwa tayi ta shiga
hada kayanta tana kukan takaici taso ta
zauna a gidan har sai ranar da Antin nata tayi ar'bain sai ta tafi amma
mutsiyaciyar Yarinyar nan Naja'atu tasa an koreta......Abba Abbas bai bar gidan
ba sai da ya tabbatar da cewar Shamsiyya ta bar gidan sannan hankalinsa ya
kwanta ko sallama baiyi da Halisan ba yayi tafiyarsa.
Gidan Yaya
Ramlatu ya nufa koda taga yanayin da yazo mata dashi sai tasha jin jikinta, ta
shiga yi masa rawar jiki, ya dinga kallonta takaici kamar ya kashe shi, Ramlatu
ta girma amma bata san ta girma kullum abubuwa take irin na marasa tunani,
ganin yanda take rawar jiki a kansa ne yasa ya sassaura zuciyarsa ya shiga nuna
mata illahr abinda takeyi take kuma tara mutane na wulakanta masa matarsa
hakuri ta bashi kamar gaske tace insha Allahu ta daina........Yaji dadi sosai
hakan yasa ya zauna sukayi hira irin ta 'yan uwantaka.
Fushi sosai
ya shiga yi da Halisa duk domin ya nuna mata kuskuranta a ganinsa idan da bata
bada goyan baya ba to babu wanda ya isa yaci zarafin matarsa da iyayanta,
Halima ba tayi musu laifin komai ba amma sun dauki karan tsana da tsangwama sun
dora mata.
*BAYAN
SHEKARU UKU*
Lokacin
Naja'atu nada shekara goma sha shida a duniya komai nata ya fito a zahiri
macace doguwa mai fadin 'kugu da cikar kirji
bata da haske sosai amma ba za'a sata a layin bakake ba fatar ta mai
kyau ce mai kuma wahalar samu, tana da kyau a fuska da jikinta wannan dalilin
yasa bata fiye yin kwalliyar fuska ba, kuma bata sanya mayafi sosai tafi amfani
fa hijabai saboda ta tsani kallon da maza ke mata a duk sanda zata fita babu
hijab a jikinta takan fuskanci 'bacin rai sosai! maza sun dinga kallonta kenan
har da masu tsayr da ita, shima Abban nasu ya fahimci yarinyar nada wani irin
jiki mai daukar hankali duk wani lafiyayyan namiji, wannan dalilin yasa kullum
idan yana gida zasuje wani gurin idonsa a kai! idan sun saka hijabin da be rufe
musu jiki sosai ba sai yace suje su sanja wani, sosai yake kula dasu da
takatsantsan a kansu. mussaman ita Naja'atun da ya lura tana kan lokacin
balagar ta....to a dai dai lokacin ne
kuma suka gama secondary ita da Ilham 'Yar gidan Baba Magaji ita kuma Saddiqa
na aji ss1 aji hudu kenan....... Lokacin
kuma Halimatu nada tsohon ciki haihuwa ko ya yau ko gobe........ a wannan
lokacin ne kuma sha'kuwa gami da soyayya mai kar'fin gaske ta shiga tsakanin
Salim da Naja'atu, hatta da manya sun san da maganar! mahaifiyar Salim wato
Yaya Ramlatu kwata kwata bata kaunar al'amarin ta zuba musu ido ne kawai tana
kallonsu! Ita kuwa Naja'atu soyayyar da takewa Salim din tasa ta manta wacece
mahaifiyarsa tana gani ita in dai Salim din zai aureta babu ruwanta da masifar
Mahafiyarsa, Abbah Abbas kuwa ganin yanda suke kaunar junansu sai al'amarin
yayi masa dadi sosai yana fatan Allah ya tabbatar da alkairi a tsakaninsu,
kenan shi ya kasance waliyyin mutum biyu Salim din da ita Naja'atun.
A dai-dai
lokacin da suke kokarin tafiya babbar makaranta, Allah ya saukar da ikonsa kan
Halimatu gurin haihuwar cikin dake jikinta Ubangiji ya dauki ranta! bata tare data haife abinda ke cikin nata ba,
mutuwar data girgixa zukatan al'umma da dama! mussaman Yaya Ramlatu da Halisa
kwana sukayi suna sambatu da zabure zabure! Halima ta mutu da kalmar shahada a
bakinta kuma ta mutu sanadiyar haihuwa babu shakka abun alfaharin ko wane
musulmi kenan, duk wani mai kaunar Halimatu zai taya ta farin cikin samun
rahamar Allah da tayi dalili kenan da ya sanya mijinta da iyayenta ke jin
sassauci a cikin zuciyoyinsu idan suka
tuna da cewar fa Halima tuntuni ta manta da rayuwar duniya domin ta riga ta
gama dacewa, duk wanda zai budi baki alharin ta zai fad'a! Tabbas Annabi yayi
gaskiya da yake cewa mutuwar mumini itace ke sawa mutane su girgiza kuma duk
wanda ya mutu jama'a na fadar alherinsa babu shakka Allah yaso shi da
rahamarsa.
*Ubangiji
Allah kasa muyi kyakkyawan karshe ameen*
To
Bayan kwana bakwai ne da rasuwar
Halimatu al'amarin ya kasance.......
Inda su Baba
Malam Alhaji Samaila Abba Magaji dashi kansa Uban gayyar suka zauna suka
tattauna maganar yin *MADADI* da Naja'atu wato Naja'atu ta maye gurbin 'Yar
uwarta Halimatu data dauka a matsayin mahaifiyarta.
*A Pege na
gaba zamu dawo ainihin labarin da muka fara da farko*
*NAGODE
'KWARAI DA ADDUARKU A GARE NI NAGODE👏🏻*
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA
#300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA
KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI
MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA
BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN
WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU
NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN
NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram
Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR
ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA
WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar
Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
_*Na gaishe
daku 'Yan 'Kungiyata ta Manazarta Writers Association, Hakika ina jin dad'i
had'in kanku, kuma ina alfahari daku mutu'ka! gabad'ayan ku ina rokon Allah ya
d'aukaka min ku d'aukaka mai amfani Ubangiji Allah ya baku ikon rubuta abinda
al'umma zasu amfana dashi*_
*PEGEN YAU
NAKI NE*
*UMMU
HANIFA*
Marubuciyar
littafin
*ANYA MUTUM
CE?🤔*
Ina mutukar
alfahari dake 'Yar d'akina Allah ya 'kara miki
basira da haza'ka, ki cigaba da rubuta littafai masu dadi da ma'ana♥️
*7*
Kanta a
tsakanin cinyoyinta ta d'ora duka hannuwanta saman kanta ta takure kanta guri
guda sai kuka take tana girgiza kanta, Baba Talatu ta dafa bayanta a sanyaye
tace"Naja'atu yanzu kinji komai daga bakin malam ko? Alhaji Abbas bashi ne
ya haife ki ba kamar yanda kike tunani,
A'a ba haka bane shi d'in ya
kasance miji ga 'yar uwarki Halimatu Allah ya ji'kanta da rahama, wannan
dalilin ne yasa su malam suka yanke wannan hukuncin a kanki babu laifi dan kin
auri mijin 'yar uwarki kuma dukkanin mu bamu aikata haramci ba kamar yanda kike
tunani da farko, idan kin auri Alhaji Abbas hankalin mu zai kwanta saboda mun
san zai ri'ke mana ke da kyau da amana
kuma su Saddiqa da d'an uwanta Mussadiq zasuji dad'in kasancewar ki a matsayin
matar babansu zasu dinga kallonki tamkar mahaifiyar su."
............Fuskarta jage-jage da hawaye ta d'ago kanta tana kallon mahaifiyar
tata, girgiza kanta ta shiga yi kana
tace"Ni wallahi bazan iya zaman aure dashi ba, a Uba fa na daukeshi kuma
ya za'ayi kuce zaku daura min aure dashi, bayan dukkanin ku kusan da maganar
Salim wannan ai abun kunya ne a gurunsa ace ya aure ni bayan shine ya raine ni
ya rike ni a matsayin 'yarsa, kawai kuma saboda mutuwa ta ratsa tsakaninsa da
matarsa sai kuce zakuyi masa *MADADI* dani ni wallahi bana sonsa."
Ta'karashe
maganar cikin gursheken kuka mai karfi.
Baba Malam
yace."Ai dama ba cewa muka yi dole sai kin so shi ba, cancanta muka duba
shiyasa muka yanke wannan hukuncin saboda haka ina so ki cire maganar ko wane
namiji a cikin ranki domun kuwa mutukar ni ne na haifeki to baki da miji sama
da Mijin 'yar uwarki wato Alhaji Abbas, zaki aure shi ko bakya sonsa nan gaba
idan kinyi hankali zaki gane abinda muke nufi dayin hakan."
Da rarrafe
ta isa inda yake ta ri'ke hannunsa jikinta sai kyarma yake tace"Wallahi
Baba malam zaku jefa rayuwa ta cikin garari saboda na fada muku iya gaskiya
shine ni ba zan iya zaman aure dashi ba, na farko yayi min tsufa kuma abun
kunya ne ace ya aure ni alhalin Ni 'yarsa ce bayan haka kuma yasan shine waliyi
na gurin daurin aurena da Sali.......Abba Magaji ya fusata! ya kai mata mari da
bayan hannu! jikinsa na tsuma! yace."Dan ubanki har wata cancanta kike
nema? dame kika fi Alhaji Abbas din ? da har kike kiransa tsoho! ana nuna miki
abinda ya dace dake kina maganar abin
kunya, kina nufin dukkaninmu bamu san abinda ya dace ba kenan? to wallahi
tallahi na 'kara ji kin bud'e baki kinyi wata magana anan gurin sai na futar
miki da jini shashashar banza da wofi."
Shuru tayi
jikinta sai rawa yake hawaye kuwa kamar an bude famfo! sai famar girgiza kanta
take tana toshe bakinta tamkar wata zautacciya.
Tausayi ta
bawa Baba malam ya kalli Alhaji Magajin a nutse yace."Yarinyar nan taurin
kaine da ita ina ganin zamu sake zama mu tattuna kan maganar, bana so ayi abu
daga baya kuma azo ana dana sani.
Alhaji
Magaji yace."Malam babu wani zama da za'a sakeyi idan wata magana ta fito
daga 'bangaran mu ba zasuji dadi ba, tunda kaga sune suka zo mana da
maganar yana da kyau mu basu goyon baya
kan abinda suka zo mana dashi duk mutumin da ya nuna yana kaunar had'a zuria da
kai to ka tabbata ba 'karamin so yake maka, hakika nasan abokina Abbas yaji
dadin zama da Halimatu shiyasa ya bukaci a bashi Naja'atu ta zame masa *MADADIN
TA* dan haka tunda mun riga mun gama magana
babu dadi kuma aje ace musu wani abu daban."
Baba Malam
yace."Yarinyar ce take bani tausayi bana son wannan kukan da take yi yana
d'aga mun hankali amma tunda kace haka shikkenan Allah ya sanya alkairi cikin
al'amarin ya kauda kowace irin fitina da zata biyo baya.
Baba Talatu
dashi Magajin suka amsa da "ameen" Mikewa yayi yai musu sallama da
niyar tafiya gida dan lokacin goma na dare ma ta wuce! Fatan sauka lafiya
sukayi masa ya dauki hularsa da key dinsa ya fita daga gidan.
Cikin
tausawa ya kalleta da fad'in"Ki tashi kije ki kwanta komai yayi tsanani
maganinsa Allah kuma ina so ki zauna kiyi tunani kan wannan hukuncin da muka
yanke a kanki, mune muka haife ki ba zamu cutar dake ba, da mutumin nan da ba
nagartacce bane to da baza mu amince da bukatarsa ba to mun tabbatar da cewar
idan muka dauke ki muka bashi muna da tabbacin zai kula dake kamar yanda ya
kula dake a lokacin da baki san kanki ba."
Mikewa yayi
ya shiga da'ki bayan ya gama maganarsa, Baba Talatu ta jima tana rarrashinta
kafin ta mike itama tabi bayan Malam din suka barta ita kadai a tsakar gidan
tana kukan zucci.
Mamaki take
sosai! wai ashe dama Abban Abbas din ne
ya bukaci auranta ita duk a
tunaninta su Baba malam ne, girgiza
kanta kurrum take tana mamakinsa, to ta aureshi tayi yaya dashi? ta yaya za ta iya rayuwar aure dashi? lallai ma! ita abun ma
mamaki yake bata ko kunya bai ji ba yace zai aureta bayan yana amsa sunan Uba a
gurinta, gashi kuma yasan da maganar Salim hummm! aikam ba zata yarda ba duk
yanda za tayi sai ta rushe wannan auran, sam ba zata auri tsoho dan shekara
hamsin ba haka kawai sun gina soyayyarsu
da masoyinta yazo yayi musu kutse a rayuwarsu ko kunya baya ji zai zo da wannan
maganar! 'Kwafa tayi ta mike ta shiga
d'aki!
Tana shiga
dakin taji shashshekar kukan Saddiqa suna kwance ita da Mussadiq a katifa ta
rungume shi sai kuka take!
A gigice ta
kunna haske wayarta, tana haske su! Saddiqa ta rufe idonta tana sake takure
jikinta guri guda......"Ke Saddiqa menene? dama ba kiyi bacci ba."?
Saddiqa ta mike zaune tana goge fuskarta, 'Karasawa tayi ta zauna gefan katifar
tana kallonta, a sanyaye tace"Meye kika kuka? nafada miki ki dainawa Mamma
kuka idan kina so ta dinga samun rahamar ubangiji."
Saddiqa ta
goge fuskarta tana kallonta tace"Ni ba Mamma nakewa kuka ba, nasan abinda nake yi a halin yanzu Mamma babu
abinda take da bukata a gurinmu sai addua ba kuka ba."
A d'an
sanyaye tace"To me kikewa kuka."? Saddiqa ta kalleta wasu hawayen na
sake zubo mata tace"Yaya Naja'atu me yasa kike nuna 'kiyayyar ki 'karara a
kan Abbanmu."!? Gabanta ne ya fad'i! sai tasha kunu! tace"Wace irin
magana ce wannan Saddiqa? kada kice min kema kina goyon bayan na aureshi."
Saddiqa taja
majina tana goge hancinta tace"To menene aibu a ciki? dan kin auri Abbanmu
ai ba wani abun bane kuma ba ke kad'ai ce kika ta'ba auran *MADADI* ba Yaya
Naja'atu idan kika maye gurbin mahaifiyarmu zamu ji dad'i sosai dan Allah kiyi
mana wannan alfarmar ki daina nuna 'kiyayyar ki a fili."
Shuru tayi
tana nazarin maganar yarinyar! Wai shin da suke ta wannan maganar ta yaya zata
fara ne? wane matsayi zata ajiye shi miji ko mahaifi? bafa zai yiwu ba.! Ta
kalli Saddiqan data kura mata ido tana jiran amsarta tace"Saddiqa nayi wa Abbanku 'kan'kanta kuma shima yayi
mun girma bayan nan kuma ni matsayin mahaifi
yake a gurina bazan iya rayuwar aure dashi ba, kuma ki daina tunanin ina 'kinsa
wallahi bana 'kinsa saboda Abba Abbas yayi min abinda ba zan ta'ba mancewa
dashi ba, kawai dai bana tunanin zan iya
rayuwar aure dashi."
Saddiqa
tace"To idan baki aureshi ba kin san dole yayi aure kuma
gabadayan mu bamu san matar da zai aura ba, kinga zamu shiga halin 'kaka
na kayi tunda dai kin san ba 'kaunar mu Anti Halisa take ba, kinga rayuwarmu na
cikin 'kalubale nida Mussadiq."
"Eh
gaskiya ne duk maganar da kika fad'a to ai ba dole sai kun zauna tare da
matansa ba, sai ku dawo gidan Alhaji da zama ko kuma ku dawo gidanan nan nasan
Baba Talatu zata ri'ke ku to meye abun tashin hankali.
Saddiqa ta
shiga girgiza kanta zuciyarta na wani irin d'aci! tace" Yaya Naja'atu kin
manta maganar Abbanmu kenan kin san fa
yasha fad'a cewar mutuwa ce kawai zata rabashi da 'yayansa bana tunanin zai
amince ya kawo mu nan mu zauna ke ko gidan Alhajin da kike magana ba zai barmu
muje ba duk da cewa gidansu ne."
Naja'atu
shuru tayi tana tunanin al'amarin Babu shakka zaman Saddiqa da Mussadiq hannun
Halisa gagarimun had'ari ne zata iya cutar dasu ta ko wace siga! Itace zata
rike su tamkar uwarsu, to ita kuwa ko a mafarki bata tunanin zata koma gidansu
a matsayin matar mahaifinsu, insha Allahu ta bar gidan har abada.
Ganin
Saddiqan ta tsura mata ido yasa tace"To ki kwanta kiyi bacci zanyi tunani
kan maganar ki." Saddiqa taji farin ciki ya rufe ta tace"To shikkenan
Yaya Naja'atu nagode Yaushe zaki gama tunanin."? Kallonta tayi na minti
biyu tace"Ke dai tunda nace zanyi to zanyi duk hukuncin dana yanke zan
fada miki."
Saddiqa
tace"To Ubangiji Allah yasa naji alkairi." Amin tace a takaice,
Saddiqa ta juya ta kwanta tana adduar Allah yasa ta amince da maganar
ta.........
Tsuru tayi
ta tsirawa guri guda ido tana tunanin yanda za tayi ta rusa wannan gagarimin
al'amarin daya tunkaro ta, kira ne ya
shigo Wayarta dake gefanta, ta dauka hannu na rawa, a kunne tasa wayar, ta
fashe da kuka 'kasa-'kasa tace"My prince kaji abunda Abbah Abbas ya 'bullo
dashi ko.''
Salim dake
kwance kan katifar sa yace." Menene ya faru ni banji komai ba."
Juyawa tayi tana kallon bayanta, dan bata so tayi wata magana ya kasance
Saddiqa taji, sai da ta tabbatar da bacci takeyi sannan ta sake sassauta murya
ta shiga fada masa abinda ke faruwa.......Mi'kewa zaune yayi da sauri! lokaci
guda gumi ya tsatstsafo masa, yace."Da gaske kike wannan maganar ko kuma
dai tsokanata kikeyi."?
"Humm!
wane irin tsokana wallahi tallahi da gaske nake wai Abba Abbas
shine ya bude bakinsa yake fadawa su Baba malam yana so ayi masa
*MADADI* dani!!!
Katifar da
yake kai ya doka! da hannunsa da 'karfi! Yace." Kai kaji wata tatsuniya!
shi yanzu dan girman Allah baiji kunyar fad'ar wannan maganar ba!!? To shin
wai ko ya manta abinda yake tsakanina
dake ne da har zai bijiro da wannan tatsuniyar."
Tace"Oho!
ni gani nake kawai san zuciya ne yama za'ayi yace haka bayan shi da bakinsa ne
yace."Mu daidaita kanmu zai daura mana aure kuma saboda mutuwa ta ratsa
tsakaninsa da matarsa sai yace a mayar masa dani a *MADADINTA."*
Salim yayi wani murmushi na takaici yace."Ke
nifa na daina mamaki! wallahi zai aikata dama yanda yake wani kula dake da wani
takatsantsan a kanki akwai alamun tambaya dama so yake matarsa ta mutu ya aure
ki! saboda haka ni kuma wallahi bazan bar masa ba, to in banda ma rigima ina ke
ina shi! shekara hamsin har yake tunanin auran yarinya 'yar 'karama kamar ki
16years fa to idan ya aure ki yayi yaya dake? mtwwss."!!
"Humm!
ni wallahi Salim mamaki ma ya hana ni nace komai ba kaga yanda su Baba malam
suke murna ba, wannan ai tauyewa mutum
hakki ne. Ni duk na rasa ma yanda zanyi."
Yace."Kece
kuwa kike da yanda za kayi, tun kafin yafiya tayi nisa ki kokarin ganin kin
rusa maganar ni kuma gobe idan Allah ya kaimu
idan naje daukarshi domin zuwa kasuwa zanyi masa magana akan inaso yazo
gurin Baba malam kan maganar auramu sai naji me zaice."
Tace"To
yauwa kayi masa hakan nasan dole kunya tasa ya kasa magana ni wallahi duk
mutuncin sa ma ya zube a idona mtssssw!!! Takarashe maganar tana jan tsaki!
Yace."Baby
ki daina wani damuwa ki kwanta kiyi bacci bazan bari wannan al'amari ya tabbata
ba, duk yanda zanyi to zanyi na rusa
al'amarin.
A sanyaye
tace"Tom shikkenan my Prince kayi bacci mai dad'i kaji ko."
Yace."Ke ina wani maganar bacci mai dadi a gurina Wannan dattijon na nema
yasa zuciyata ta buga."!!
"Hummm!
kawai tace dan ta rasa ma abin cewa, kashe wayar tayi ta zurfafa cikin tunani
da nazari! gabad'aya bata so tayi masa rashin kunya saboda shi mutum ne mai
muhimanci a gurinta to amma tunda ya 'bullo
da wannan maganar kashi hamsin na 'kima da mutuncinsa suka zube a
gurinta.
Numbarsa ta
laluba ta dinga kallon numbar kamar shi take kallo, shawara take da zuciyarta
shin ta tura masa text ko kuwa, wata zuciyar tace" Idan kika tsaya
lako-lako kan wannan al'amarin to za kiyi kuka da idonki.......Da sauri ta
shiga rubuta masa text kamar haka.
_Assalamu
alaikum Abba nmu barka da dare ina tafan kana nan lafiya? Abbah wata magana
naji daga bakinsu Baba malam kuma sun ce kaine kazo musu da maganar shine nake
so naji daga bakin ka._
Tana tura
masa text din ta kashe wayar! kwanciya tayi tana takure jikinta hawaye ne ke kokarin 'kwace mata tana kokarin hana shi fita.
Sai bayan da
ya dawo daga sallahr asubahi ne ya kunna wayar tasa, aikuwa text din ne ya
shigo yayi saurin bud'ewa yana dubawa............Ya karanta ya kai sau biyar ya
girgiza kanshi! lallai To bata yarda ba kenan tana so taji daga bakinsa, shi
kam bai san abinda zaice mata ba, kawai
sai ya share bai mayar mata da amsa ba, ya cire jallabiyar jikinsa, ya kwanta
rigingine kan bed din yana tunanin rayuwa, Halisa ce ta shigo dakin jikinta
sanye da hijab kamar wata mutuniyar arziki, tun bayan mutuwar Halimatu wata
shiriya tazo mata takeyi komai
cikin rashin kuzari.
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA
#300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA
KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI
MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA
BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN
WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU
NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN
NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram
Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR
ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA
WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar
Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*8*
Tana tashi
da asubah ko sallah ba tayi ba ta dauki wayarta ta kunna ta shiga dubawa wai ko
ya turo mata da amsa, wayar ta kai minti goma a hannunta tana jiran shigowar
replay dinshi bai shigo ba, a sanyaye ta mike ta fita domun daura alwala, tana
shigowa dakin ta sake daukar wayar tana dubawa, ganin alamun shigowar sa'ko
yasa hannu na rawa ta bud'e! tsaki! mai 'karfi taja ganin messege din daga
*Mtn* ne, jefar da wayar tayi kan katifa, idanunta na kokarin kawo ruwa ta
shiga tayar dasu Saddiqa daga baccin da
suke.........Suna bude ido tace"Ku tashi kuyi alwala kuyi sallah."
Saddiqa ta sauko da sauri ta bude akwatin kayansu makilin da brush ta dauka ta
fita domin daura alwala.....Cikin tsawa
ta kalli Mussadiq kamar shi yayi mata laifin tace"Kai ba zaka tashi ba sai
na gaggaura maka mari ko."! Yaron ya tashi a furgice yana kallonta! da
hannu ta nuna masa 'kofar fita tace"Kaje kayi alwala gari ya waye."
sakkowa yayi daga katifar shima ya dauki abun wanke baki ya fita.
Hijab ta
zura ta gyara dadduma ta tayar da sallah, Tana idarwa ba tayi wata adduar kirki
ba ta sake daukar wayar tana dubawa, har yanzu dai babu amsa! Tsaki ta dinga ja
zuciyarta na wani irin tafarfasa! babu shakka Abbah Abbas da gaske yake! tasan
yaga text d'inta kunya ta hana shi bata amsa
shiyasa ya shareta.
Numbar Salim
ta laluba ta shiga kira. sai dai wayar a kashe take dan bai tashi ba ballanta ya kunna
wayar......Mi'kewa tayi ta koma bakin katifar ta zauna had'e da cire hijab din
jikinta, Numbar Abbah Abbas din ta sake nema ta 'kara tura masa wani text in
kamar haka.
_Abba ina
jiran amsa nasan dai kaga text d'ina dan Allah ka bani amsa shin kaine ka nemi
aure na? ko kuma su Baba malam ne suka baka ni."?_
Tura masa
tayi ta tsirawa wayar ido tana adduar Allah yasa yayi mata
magana.............Shi kuwa Abbah Abbas yana kwance Halisa na matsa masa a jikinsa yana lumshe ido baccin
da ya tara kwana da kwanaki ne yake damunsa, tinda Halimatu ta rasu bacci da
nutsuwa suka 'kaurace masa, mutuwar Halimatu babban gi'bi tayiwa rayuwarsa,
gani yake ma ba zai ta'ba samun mace tagari kamar ta ba, Yayi yun'kurin auran Naja'atu ne ba dan
komai ba sai dan yasan ita d'in tarbiyyar Halimatu ce yana kwadayin ta zama
matarsa domin hausawa suna cewa gida bai 'koshi ba to ba za'a bawa dawa ba, bayan haka kuma yana
tausayawa 'yan 'ya'yansa sosai saboda yanxu suna bukatar mai kula dasu sun saba
da mamansu sosai dole idan suka dawo gidan suka ga babu ita su shiga damuwa,
amma duk rintsi idan suna kallon Naja'atu a gidan kuma a matsayin matarsa
to zasu samu sassauci a tare dasu.
Babban
abinda yake d'aga masa hankali acikin al'amarin shine! yanda zai tunkare su da
maganar! Salim da Naja'atu gabadayan su
bai san abinda zai ce musu ba, Salim bashi da Uban da yafi shi, hakan
nan itama Naja'atu bata da uban da yafi shi, tabbas da zai iya hakura da ya
hakura ya kyalesu sunyi auransu, amma ba yajin zai iya janye kudirinsa ba dan
komai ba sai dan samun walwala da farin cikin 'yayansa guda biyu, saboda ya riga ya sani cewar babu wata mace
da zai aura ta ri'ke masa su tsakani da Allah! shiyasa yake ganin auran
Naja'atun shine yafi alkairi a garesu baki daya.
'Dan juyawa
yayi ya d'auki wayarsa ya bud'e text din ya sake bud'awa domin ya sake karanta
sai yaga wani ya sake shigowa, Ya bude idonsa sosai yana karantawa! Murmushi
yayi wanda yasa Halisa kallonsa da sauri tace"Allah yasa alkairi ne naga
kana murmushi." Kallonta yayi yana kokarin rufe wayar dan ganin tana le'ko
da kanta tana so ta ga abinda yakewa murmushin,
a hankali yace."Alkairi ne insha Allahu." Tace"To Allah
ya tabbatar mana dashi, mikewa tayi ta fita daga dakin tana fad'in "Bari
na shiga kicin na shirya abin karin kummalo." Ya bita da kallo Ba tare da
yace mata komai ba, ajiyar zuciya ya sauke bayan fitar ta daga d'akin, tabbas
idan Halisa taji wannan babban al'amarin akwai tashin hankali! ya riga yasan
halinta da mugun kishin tsiya! uwa uba
kuma tsakaninta da Yarinyar basa jituwa
ko kadan yanzu yanda zai tunkareta da maganar yake tunani.......Kira ya shigo
wayar dake hannunsa, koda ya duba numbar Naja'atun ce yayi serving da My
doghtar! kamar kada ya daga sai kawai yayi 'kundumbala ya d'aga wayar yana d'an
gyaran murya, kafin ma yace wani abu yaji shashshekar kunanta a kunnasa.
Jikinsa ne
yayi sanyi ya sassauta murya irin yanda yake mata idan tana irin wannan kukan
yace."Dota ya akayi kuka da sassafe kiyi shuru muyi magana ko."!!
hanci ta sha'ka! zuciyarta sai tafarfasa take tace"Abba tun jiya na turo
maka da text baka bani amsa ba kuma nasan ka gani dan girman Allah ka bani
amsar abinda na tambayeka ko na samu zuciyata tayi
sanyi."""" Jim yayi kafin yace."Kinga ni ban ga text
d'inki ba ballanta na baki amsa amma kome kika rubuta min a text din ina
sauraranki yanzu ki fad'a min."
Cikin rawar
baki tace"Jiya bayan kasa Salim ya kawo mu gidan Baba Malam shine naji
suna wata magana wacce tasa raina ya kusa futa daga jikina, ashe wai kai ba
kaine ka haifeni ba , sannan babban abinda ya furgita ni yasa na shiga cikin
halin damuwa da tashin hankali wai kaine da bakin ka kace musu su baka ni na
zama *MADADIN* matarka da ta rasu, shine nake ganin kamar sune suke so suyi
wannan had'in da bai dace ba! ai abun kunya ne ace wanda nake amfani da sunansa
ako ina a matsayin mahaifina aji shine kuma zai aureni ina zan saka raina idan
hakan ya tabbata."!! Cikin sar'kewar murya ta 'karasa maganar........Shuru
yayi kawai yana jin saukar numfashinta a kunnansa bakinsa yayi masa nauyi
gabad'aya ma ya rasa me zai ce mata.
Murya na
rawa tace"Abbah wannan shurun da
kayi yana nuna min cewar da gaske ne
maganar daga bakin ka ta fito!!! Innalilihi wa'ina ilahi raji'un! kaico da wannan furucin naka! Abbah! dan girman Allah ka janye wannan
maganar da kayi, na rantse da Allah ba
zan iya zaman aure da kai ba ni a matsayin Uba na dauke ka."
Tana wani
irin kuka take masa maganar, Yaji jikinsa duk ya mutu! Gumi ne ma yake
tsatstsafo masa kamar ba safiya ba, da kyar ya iya cewa" To naji maganar
ki zanyi shawara a kai idan da akwai yuwuwar na hakura dake zan samu su malam
d'in na fad'a musu duk shawarar dana yake, ki daina kuka haka kada ki janyowa
kanki wani ciwon na daban." Tace"To Abbah ni da daina kuka ai sai
naji maganar wannan auran ta rushe sannan zan daina kuka."!! Mamaki ya
kama shi, da jin maganarta sai ma ta
bashi dariya yayi kad'an kafin yace."Naja'atu me yasa bakya son na zama abokin rayuwarki."? Taji wani irin
fad'uwar gaba jin abinda yace. Tace."Abbah Please ba girman ka bane dan
Allah kada ka 'kara yi min wannan maganar kai ubana ne *Salim* kuma shine
abokin rayuwata." Kishi ne ya kama
shi jin abinda tace kawai sai ya kashe wayar ba tare da ya sake cewa komai ba.
Ajiyar
zuciya ta sauke bayan kashe wayar tasa, ta juya tana kallon Bayanta, Saddiqa da
Mussadiq sun futa daga dakin tun d'azu! taji dad'in hakan, sai ta mike itama
tabi bayansu dakin Baba Talatu.
Suna zaune a
kusa da Baba Malam suna karyawa da kunu da kosai ta shiga da sallama a bakinta,
a hankali ta tsuguna kusa da Baba Malam tana gaishe shi ya amsa cike da kulawa
yana d'an nazarinta ganin idanunta sunyi jawur! yasa yace."Ya kwanan
kuka."?
'Kasa tayi
da kanta! Baba Talatu tace"Kina so ki janyowa kanki damuwa da ciwo da
kinyi halin Halimatu da ba kiyi mana gardama ba, Halimatu komai muka umarceta
dashi tana mana biyayya dai-dai gwargwado amma ke tun jiya ake magana daya
dake, idan kika bujirewa umarninmu baki kyauta mana ba kuma baki kyautawa 'Yar
uwarki ba, a yanzu babu abinda za kayi kisa ta farin ciki illah ki zama
*MADADIN TA* Ki tallafi abinda ta bari gasu nan suna kallonki." Ta nuna su
Saddiqa dake zaune.
Shuru tayi
ta kasa magana ba wai dan bata da abin cewa ba kawai dai bata son suyi ta
sa'insa da iyayenta.....Baba Malam dai shuru yayi ya dauki kofin kununsa yana
sha yana had'awa da kosan sa dake cikin wata silba dake gabansa.
Saddiqa ce
ta zuba mata kunun ta ajiye mata a gabanta sannan ta mi'ka mata abun da 'kosan
ke ciki tace"Yaya Naja'atu gashi nan ki karya kema." Kallonta tayi
sai taji zuciyarta ta tsinke! sosai yaran suke bata tausayi Saddiqa ta damu da
ita sosai koda can bata son taga 'bacin
ranta, tabbas a wannan lokacin ne ya
kamata tayi mata sakayyar abun alherin data dad'e ta nayi mata.
Domin
Saddiqar taji dadi yasa ta dauki kofin kunun tana kur'ba a hankali tana had'awa
da kosan dake gabanta, Baba malam na gama karyawa sai ya dauki redion sa ya
mike yana kallonta yace."Idan kun gama kun kintsa ku shiga gidan Alhaji
dake dasu Saddiqa ku gaishe dasu." A sanyaye tace"Inasha Allah."
takalmansa dake bakin kofa yasa ya fita daga gidan hannunsa ri'ke da redionsa.
Suna gama karyawa
sai sukayi wanka suka shirya tsaf! Naja'atu da Saddiqa suka shirya cikin kaya
iri daya hatta da d'inkin jikin atamfar
iri daya ne komai iri daya Abbah Abbas ke musu baya bambamta su sai da gurin
d'inki na Naja'atu yana d'ara na Saddiqa da wani abun, milk din hijabi toyobo
ne a jikinsu ya sauka har 'kasa! Suna kokarin fita daga gidan da nufin shiga
gidan Alhaji Sama'ila, Shi da Salim suna
kokarin shigowa cikin gidan.
'Kamshin
turaransa ne ya tabbatar mata da cewar
shine Kafin ma tayi wani yunkuri sun
shigo Shine a gaba Salim na take masa baya, Yana sanye da farar shadda kar
'Dinkin tazarce har kasa, da adon surfani a wuyan rigar da hannunta kansa sanye
da farar hula mai ratsin 'baki! a zahiri
idan ka kalleshi ba zaka ce ya kai shekarun da yake dasu ba, za'afi tunanin
shekarunsa ba sufi 43 zuwa 45 ba, Abbah Abbas mutum ne dan gayu mai
yawan ado da kwalliya, kuma ma'abocin kamshi
shiyasa kullum baka ganin
tsufasa, dan idan yace ya kai matakin
shekara 50 a duniya da yawa wasu ba zasu yarda ba, sai dai kuma masu nazari da
tunani idan sukayi masa kallon tsanaki a zasu fahimci cewar ya kai shekarun da
ya fad'a d'in.........Da gudu Mussadiq yaje ya rungumeshi yana fad'in ''Oyoyo
Abba." Yana d'an murmushi ya bashi hannunsa tare da fadin"Barka da
Asuba magajin Abbah." Mussadiq na dariya ya rike hannun mahaifin nasa suka gaisa
sosai........Saddiqa na murmushi tace"Abba ina kwana ka tashi
lafiya."? A nutse ya d'aga kansa yana kallonsu ita da Naja'atun
Yace."Lafiya lau na tashi Ina zakuje da sassafe haka."? Yana kallon
Naja'atu yayi maganar."!
A kanta a kasa ta gaishe kafin tace"Zamu
shiga gidan Alhaji ne mu gaisa." Yace."To babu damuwa nima yanzu zan
shigo gidan.'' Kokarin ratse ta yake ya
shiga cikin gidan, tayi saurin bashi hanya, tana sunkuyar da kanta, gani tayi
yau fuskar sa babu walwalar da ya saba yi mata koda yake ai dole dama ya kasa
sakin jiki da ita saboda yasan abinda yayi.
Ta kalli
Saddiqa tace"Kuje gani nan zan biyo bayanku." Saddiqa ta kalleta tana
kallon Salim da yayi wani kici-kici da fuska yana kallonta ya wani zuba
hannuwansa a cikin aljihun jins din dake jikinsa.....Saddiqa jikinta sanyi yayi
ganin yanda Naja'atun ta wani d'aure mata fuska! sai taja hannun Mussadiq suka
fita daga gidan
Salim ya
tsira mata ido bayan fitar su Saddiqa yace."Me kike fahimta ne daga gurin
wannan Dattijon."? Cikin sanyin jiki da sarewa da al'amarin tace"Ni
wallahi har yanxu na kasa gane inda ya dosa, dazu dai munyi waya dashi na ro'ke
shi akan ya janye kudirinsa yace."zai yi shawara idan ya yanke magana zai fad'awa
Baba malam abinda ake ciki."
Cikin 'kunar
zuciya Salim yace."Jikina baya bani cewar Mutumin nan zai hakura dake My
Princess shin idan ya kasance shine ya samu damar mallakar ki ya zanyi da raina watakila ma ina jin
shikkenan 'karshen rayuwata ne yazo." Cikin wata iriyar siga yayi maganar
yana matsawa kusa da ita.
Hawaye ne
suka 'kwace mata tace"My Prince ka
daina wannan maganar dan Allah insha
Allah Allah ba zai bashi nasara ba, Ni bani da wani miji sai k..........Maganar
ce ta ma'kale a bakinta sakamakon zuwansa gurin! Ya kallesu sunyi wani daf da
junansu kamar zasu rungume junansu, kana kuma kallon yanayin su zaka fahimci
suna cikin mayen son junansu a lokacin kome zasu iya aikatawa! Tsawa ya buga
musu yana kallon Salim din Yace.
"Kai meye haka ka tsaya daf da ita rungumeta zakayi ko me."?
Salim yayi
gaggawar barin kusa da ita yana sosa kansa irin na kunya yace."Kawu kasan
sau tari nakan shiga wani yanayi idan yarinyar nan na kusa dani, dan Allah Kawu
kayi wani abu akan al'amarin aurena da ita."
Kallon
shashasha yake masa kafin yayi 'kwafa ya kalleta tana ra'be a jikin bango tana
goge fuska! Kamar zai ce wani abu sai kuma ya fasa, ya kalli Salim din rai a
'bace! yace"Shige muje." Salim ya shiga sosa kansa yana d'an kallonta
ta 'kasan ido ya fita daga gidan, shima ba tare da ya sake kallon inda take ba
ya fita ranshi a 'bace! wani irin kishi ne yake damunsa a zuciyarsa ganin
abinda ya wanzu tsakaninta da Salim..
*GA MASU
BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #300 SINGLE,
VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA
ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI
TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN
SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO
KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU
NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN
NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram
Bane!!))_
*NA*
*BINTA UMAR
ABBALE🍒*
*MANAZARTA
WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_Kungiyar
Masu Nazari Da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~~~~~~~
Na baki
kyautar wannan pege d'in *JAMILA JAMY 'YAR MUTAN KANKIA*
Marubuciyar
littafin.....
*'BARAWO NE*
Ina rokon Allah ya d'aukaka ki daukaka mafi alkairi Allah ya 'kara miki basira
ki cigaba da rubuta littatafai masu dad'i da ma'ana♥️
*9*
Cikin sanyi
jiki da mutuwar jiki ta fita daga gidan, koda ta fita kai tsaye gidan Alhajin
ta nufa tana tafiya kanta a kasa ga wani irin fad'uwa da gabanta yake, tana
tunanin idan ta shiga gidan da wane irin ido zata kalli mahaifiyar Abbannasu matar
data dauka a matsayin kakarta suke wasan jika da kaka da ita, yau an wayi gari
wai itace take nema ta zama surukarta akwai kauna da fahimta a tsakaninta da
Hajiyar tana ganin idan Abba Abbas din
bai janye 'kudirin sa ba zata nemi taimakon matar tunda mahaifiyarsa ce
watakila idan tayi masa magana ya janye.
Tana shiga
gate din gidan, ta hangi Abba Abbas din da Abba Alhassan 'kaninsa da kuma Salim
d'in a tsaye a jikin wata mota suna magana, Tun daga nesa take kallonsu Abba
Abbas din! Tsaki! taja a zuciyarta ta kalli Salim dake kusa dashi, humm yaushe ma za'a had'a!
Salim saurayi mai tashe mai jini a jika gashi dan gayu dan kwalisa, babu abinda
yake burgeta a dashi sai 'kayatacciyar fuskarsa mai dauke da siririn saje wanda
yayi masa kyau sosai tana bala'in son Salim saboda kyawunsa kuma ya iya
kwalliya mai burgewa, shi kuwa Abba Abbas
ya wani bar gashin fuska (gemu ) ya cika masa fuska duk da cewa a gyare yake hakan bai burgeta
ba, babban abinda yake 'kara sawa ta sake jin tsanar auransa, shine tsali-tsalin furfurar data fara fito
masa a gashin fuskarsa(gemu) Ai abin
dariya ne ma ta nunawa kawayenta shine mijinta, gaskiya ita kam ba zata iya
auransa ba, a tsarinta tafi son ta auri Saurayi wanda zasu mori 'kuruciyarsu
amma auran Abbah Abbas babban nak'asu ne a tattare da ita
*(Humm! Waye
ya fad'a miki haka Naja'atu.")*
A nutse ta
iske inda suke tsaye kamar munafuka ta dinga 'boye fuskarta tana gaishe da
Abbah Alhassan ya amsa fuska a sake yana
d'an kallonta a fakaice hakika yarinyar na burgeshi mutuka tana da hankali da
nutsuwa kuma babu shakka idan d'an uwansa ya aureta yayi dace da samun mace
tagari.
Abbah Abbas
kuwa kokarin shiga mota yake yi bai ko kalleta ba dan har yanzu haushinsu yake
ji ita da Salim d'in.......Simi-simi ta wuce cikin gidan, Abbah Alhassan ya
shiga motar ya zauna kusa da d'an uwansa, Salim yaja motar suka nufi kasuwa.
Hajiya Abu
na zaune a 'kasan kafet Saddiqa da Mussadiq na gefanta suna mata wasa kamar
yanda suka saba idan sunxo gidan ita kuma sai biye musu takeyi ta ri'ke hannun
Mussadiq tamau! wai sai ya bata kud'in shara na shekara biyu! Yaron sai dariya
yake mata yana cewa ta sake shi zai tambayi Abbansu ko nawa take so za'a bata.
Ita kuwa tayi kici-kici da fuska kamar gaske tace ita sai ya bata zata cika
masa hannu idan kuma bai bata ba sai ta cire masa kayan jikinsa a bakacin kudinta......Saddiqa
sai dariya take musu, Mussadiq na ganin Naja'atu ta shigo yace."Yawwa Yaya
Naja'atu kizo ki cece ni a gurin tsohuwar nan tana so ta karya min hannu."
Hjy Abu tace'' Kina zuwa nan sai na murd'e miki hannunki dan dukkanin ku zan iya daku."
Naja'atu
tasa dariya tana k'arasawa gurin tace"Lallai Hajiya 'karfi ne dake haka
duba kin murd'ewa yaro hannu ki fad'i nawa ne kudin sai a biya ki."
Tace."Ai ba zaku iya biya na ba." Tace"To dan Allah sakar masa
hannu ya tuba." Tana dariya ta sake shi tace"Ja'iri ashe ba wani
karfi ne dashi ba." Yace."Hajiya aike tsohon 'kashi ne dake ni kuwa
sabo ne shiyasa da kika ri'ke ni na kasa kwacewa." Gabadayan su suka sa
dariya har da ita.
Naja'atu ta
zauna a nutse tana gaisheta! Ta amsa cikin kulawa tana kallonta tace"Dama
kuwa ina neman ki amma ki fara zuwa ku gaisa da Alhaji yana sama sai kizo mu
tattuna magana kinji 'kawata." Naja'atu ji tayi gabanta ya fad'i !!! to
wace magana zasu tattauna da hajiyan? tabbas ta tsuniyar gizo bata wuce ta
'koki! sai
Tayi kokarin
kauda damuwar fuskarta tana kokarin mikewa tace to shikkenan bari naje mu gaisa
da Alhjin."
Sama ta hau
inda dakin Alhaji Sama'ila yake, nan ta tarar da Hajiya Rabi a dakin tana
gyare-gyare suka gaisa cikin mutunci kafin ta shiga dakin da yake ciki............Tayi kusan minti goma a
ciki kafin ta sauko 'kasa suna zaune a inda suke suna hira koda ganin zuwanta
gurin sai sukayi shuru Saddiqa ta dinga bin fuskarta da kallo ganin kamar ta
sauko da damuwa a tare da ita............zama tayi kusa da Hajiyan cikin tunanin mafita tace"Hajiya gani to na
dawo." Hajiya Abu ta gyara zamanta sosai ta bude bakinta kenan za tayi
magana, Yaya Ramlatu ta shigo bakinta dauke da sallama. Amsawa sukayi gabadayan
su, Ramlatu na ganin Naja'atu kusa da Hajiya sai ta 'bata rai! tayi kici-kici
da fuska dan koda Naja'atun ma ta gaisheta bata amsa ba sai gaisuwar su
Mussadiq ta amsa! Naja'atu jikinta yayi sanyi ta sunkuyar da kanta kasa tana
jinta tana tambayar su Saddiqa ina Abbansu suka ce ya tafi kasuwa!
Yaya Ramlatu
ta kalli Mahaifiyar ta tace"Hajiya wata magana naji daga bakin Salim dazu
da safe yake fada min shine nace to bari nazo naji shin da gaske ne abinda ya fad'a wai Abbas zai auri waccan
yarinyar ta zaune." Tana nuna Naja'atu da hannu tayi maganar.
Hajiya Abu a
nutse tace"Eh kwarai kuwa hakane Salim bai miki karya ba! Abbas zai auri Naja'atu insha Allah sai ta
zama *Madadin* 'Yar uwarta ko babu komai wad'annan yaran zasu samu walwala da
farin ciki."tafada tana nuna su Saddiqa.
Yaya Ramlatu
ta zabga salati tana tafa hannu tace"Haba Hajiya da hankalinku da komai
zaku bari wannan al'amarin ya faru? Yanzu shi Abbas din ko kunya baiji ba zai
auri yarinyar da ya ri'ke ta a matsayin 'yar sa, yarinyar da kuma ya san Salim ne ke neman
auranta shine kuma zai had'a takara
dashi! a gaskiya wannan abu bai tsarantu ba! gwara tun wuri yayi wa kansa fad'a
dan wallahi idan ya sake ya auri wannan yarinyar to duniya sai ta zage shi
saboda ya aikata abun kunya, kuma baiyi wa Salim adalci ba."
Hajiya Abu
tace"Kece kike ganin kamar hakan bai dace ba amma *MADADI BA HARAM BANE*
Dan ya ta mutu a mayar da kanwa d'akinta ba laifi bane! Kuma naji kina cewa
duniya zata zagi Abbas a kan me? duniya zata zageshi? naga ke da kanki kika
nuna bakye so 'Danki ya auri yarinyar to me yasa kuma yanzu zaki zo da wata
magana, idan Salim mai hankali da tunani
ne ya dace yayi wa Kawunsa adalci ya hakura da yarinyar ya bar masa kodan
marayun 'yayan dake gabansa."
Yaya Ramlatu
tace"A'ah!! ni ban hana Salim auran yarinyar nan ba wallahi a duk lokacin
da zamuyi maganar auransa yakan ce dani Abbas din ne yake cewa ya dakata
tukkuna zaiyi magana da iyayenta, sai kuma yanzu kawai daga ya rasa matarsa ya
'kwace masa budurwa ai hakan sam bai
dace ba."
Hajiya Abu
tace"To ai sai kiyi tayi dan tuntuni an riga an gama magana insha Allahu
kafin nan kafin sati uku za'a daura auran Abbas da Naja'atu insha Allah."
Wani irin
kuka ne ya kufcewa Naja'atu! da sauri duk suka juya suna kallonta! had'a kanta
tayi da gwiwa tana kuka sosai da sosai! Yaya Ramlatu tace"To hajiya gashi
nan dai kin gani zahiri yarinyar nan bata son wannan al'amari dan dai ba zata
iya fitowa ta fada muku bane! a wannan zamanin ba'a yiwa yaran yanzu auran dole
kada ku tauyewa yara hakkinsu, ni a ganina Abbas ya hakura kawai ya barwa Salim
shine maslaha."
Hajiya
jikinta ne yayi sanyi ganin irin gursheken kukan da Naja'atu keyi tana kokarin tayi magana Alhaji Sama'ila ya
sauko daga sama!
Ganin
Naja'atu na kuka sai hankalinsa ya tashi ya zauna kan kujera yana tambayar
abinda ke faruwa, Yaya Ramlatu ta shiga warware masa duk abinda yake tsakin
Salim da Naja'atun da irin soyayyar da suke.
Alhaji
Sama'ila yayi shuru yana nazarin maganar, shi duk abinda akeyi bai san da
maganar Salim a ciki ba, to gaskiya idan hakane shi Abbas din shine ya dace ya
hakura da yarinyar duba da cewar maganar
Salim din ta dad'e kuma shi ya san da ita bai fad'a ba saboda biyan bukatarsa,
wannan ba adalci bane, a matsayin sa na wanda suka dauka a matsayin uba a
garesu to bai dace yayi musu haka ba, dole ya janye maganar auran yarinyar ya
kyale yara suyi auransu.
Ya kalli
Naja'atu a nutse yace."Daina kuka Naja'atu
ki kwantar da hankalin ki insha Allah ba
zaki auri Abbas ba tunda bakya sonsa zamu baki wanda kike so insha
Allahu."
Jin abinda
Alhajin yace yasa Saddiqa ta fashe da kuka!! ta had'a kanta da gwiwa tana
shashsheka! tofa gida ya zama na makoki mutuwa ta dawo sabuwa dan Saddiqa
rungume Mussadiq tayi tana fad'in "Mussadiq mutuwa tayi mana tonan silili
kowa sai gudun mu yake ana neman kai damu! meye laifin Ubanmu da ba'a sonsa!
Ubangiji Allah ya zama gatanmu." Hajiya Abu ta rikice da kuka ta kama
yaran ta rungume a jikinta tana fad'in "Babu wanda ya isa yayi neman kai
daku! Kuma insha Allahu Naja'atu zata tare a gidan ubanku."
Yaya Ramlatu
jikinta ne yayi sanyi ganin mahaifiyar tata na kuka.........Bayan alhajin ya
fita Hajiya Abu ta goge fuskarta tana kallon Ramlatu tace"Kin kyauta kan
abinda kikeyi kullum burin ki ki tayar min da hankali bakya kaunar na zauna
lafiya yanzu meye amfanin wannan abun da kika zo kikayi ashe kinfi kaunar
d'anki a kan d'an uwanki? meye Abbas beyiwa d'anki ba amma da abunda zaki saka
masa kenan! kinzo kin saka marayu kuka da damuwa suna cikin damuwa a maimakon
ki taya su alhini sai kizo ki sake saka musu wata damuwar to sun gode da abunda
kikai musu."
Yaya Ramlatu
ta share guntin hawayen fuskarta a sanyaye tace"Hajiya ban san al'amarin
zaiyi miki zafi haka ba dan Allah kiyi hakuri idan ranki ya 'baci kuma insha
Allahu zan umarci Salim ya janye maganar auransa da yarinyar Allah yasa haka shi yafi alkairi."
Jin abinda
tace ne yasa Naja saurin kallonta hawaye na tsere a fuskarta shikkenan magana
ta 'kare! jiki a sanyaye ta mike ta fita daga palon.
Salim na
driving maganar dake damusa nata cin zuciyarsa,
ya dan kalli Kawun nasa dake bayan mota shi da 'Kaninsa suna magana,
Yace."Kawu ina da magana da kai."! Babu walwala a tare dashi
yace."Ina sauraranka." Da kyar iya cewa "Dama kan maganarmu ta
kwanaki ce." Kamar be san komai ba yace."Wace irin magana
kenan."? Salim cikin dakewar zuciya yace."Maganar Naja'atu mana a
cikin 'yan kwanakin nan gabadaya zuciyata ta kasa daurewa sai nake ganin kamar
akwai wani abu da zai faru dan Allah ina so kaje ka nema min auranta kamar
yanda kayi min al'kawari a kwanakin baya."
Shiru motar
tayi babu wanda yayi magana, Abbah Alhassan mamakin maganar da Salim din yayi
yake ashe dama soyayya ce a tsakanin Salim da Yarinyar? to me yasa dan uwan nasa yasan da soyayyar
dake tsakaninsu ya bijiro da bukatarsa.
Shuru Abba
Abbas yayi ba wai dan bashi da abin cewa ba, sai dan ganin cewar shi a gurinsa
a bin kunya ne ace yana maganar aurensa da Salim d'in, yafi so yaron yaji
maganar a bakin wani idan yaso ya gane ruwa ba'a sa'an kwando bane....
Shurun da
yayi tasa jikin Salim yin sanyi, tabbas yanzu ya gazgata maganar Naja'atu cewa
Abba Abbas din da gaske yake ba gudu babu ja da baya.
Yaji wani
irin d'aci! a ma'kogwaronsa! dishi-dishi! yake gani a idonsa tsabar bakin ciki
da 'bacin rai! Ga wani masifar kishin Kawun nasa dake sasakar zuciyarsa! Wai
yau an wayi gari wanda yake tunanin shi zaiyi masa wakilcin aure shine yake
kassaya dashi.........Shi kuwa Abbah Alhassan ganin 'Dan uwan nasa bai ce komai
ba yasa yaja bakinsa yayi shuru haka
suka isa kasuwar kowa na sa'ke-sa'ke a zuciyarsa mussaman Salim da yake jin
shigar zazzafan zazzabi a jikinsa.
Yaya Ramlatu
na fita daga gidan Alhaji Kai tsaye unguwar gwangwazo ta nufa gidan d'an uwan
nata........Halisa na zaune a palo tana kallo Yaya Ramlatu ta shiga da sallama
a bakinta......Halisa ta mike tana mata barka da zuwa taje ta kawo mata abinci da ruwa da lemo kana
ta zauna suna gaisawa.
Yaya Ramlatu
sai da ta cika cikinta ta 'koshi tukkuna, ta kalli Halisan tace"Kin san
gagarimar maganar da nake tafe da ita kuwa."
Halisa taji
gabanta ya fadi! a sanyaye tace"Ban sani ba Yaya sai kin fad'a."
Murmushin
takaici Yaya Ramlatu tayi kafin tace"Kina zaune da baki a bud'e har kin
samu damar zama kiyi kallo ana can ana shirya miki kasassa'ba."!! Halisa
miyau ya dauke daga bakinta tace"Yaya Ramlatu dan Allah fad'a min abinda
ke faruwa."
Ajiyar
zuciya ta sauke kafin tace"Mijinki Abbas nacan yana neman auran budurwa
'yar cikinsa, auran cuta da ha'inci Auran
da duniya za tayi turr! dashi."!
Halisa ta
zabura! ta dafe kirjinta gabanta na wani irin buguwa tace"Aure kika
ce Yaya Ramlatu.""? Tace"Kwarai
kuwa." Tafada tana tabbatar mata da gaskiyar magana
Wani irin
gumi ne ya shiga tsiyaya daga jikin Halisa! "Aure!aure! kalmar ma ba babu
dadin ji a kunnanta, wato duk ladabi da biyayyar da take masa da nuna masa
kulawar da Halimatu take masa bai sa yaji sha'awar aure ya fita daga ransa ba?
ashe duk abinda takeyi masa na kulawa a
banza take mutuwar Halima ko sati biyu
ba'ayi ba amma har ya fara kokarin aure, shin wai dame ta gaza ne a
gurinsa......wasu hawayen takaici da bakin ciki ne suka shiga sauka a
kumatunta.....Yaya Ramlatu tace." Ai ba kiyi kuka ba ma tukkuna sai kinji
yarinyar da zai aure."! Bakinta na rawa tace."Wacece."? Kai
tsaye Yaya Ramlatu tace"Naja'atu ce.'' Sai tayi kasa'ke tana kallonta
tunani takeyi wacece ma Naja'atu! dan a lokacin gabadaya kwakwalwarta ce ta
toshe ta mance a inda tasan mai irin sunan."
Yaya Ramlatu
tace''Kina mamaki! ko da jin wacce mijinki zai aura bari na 'kara tabbatar miki
da maganar, Abbas zai auri Naja'atu kanwar matarsa Halimatu yarinyar da ya
ri'keta tun tana 'karama yayi mata komai tamkar 'yar cikinsa! shine yanzu zai
maye gurbin 'yar uwarta da ita." Halisa ta dinga jin hajijiya tana daga
xaune! rintse idonta tayi tana tunano siffofin Naja'atu a idonta!!! a gigice ta bude idonta ta zabura ta mike tsaye tare da
cewar "Wallahi ba zaiyi wuba !! ba zan yarda da wannan cin amanar ba! Ni
Abbas zaiyi wa haka? me nayi masa a duniya zai had'ani kishi da yarinya 'karama
'yar cikina! kutumar uban nan kayyasa!!
sai ta zube kasan kafet ta fashe da wani mahaucin kuka tare d'ora dukkanin hannuwata a kanta.
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA
#300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA
KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI
MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA
BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN
WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU
NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN
NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram
Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR
ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA
WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar
Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*10*
Wani irin
kuka Halisa takeyi tamkar wacce aka aiko mata da mutuwar iyayenta, ta d'ago
kanta tana kallon Yaya Ramlatun fuskarta gaje-gaja da hawaye tace"Yaya
Ramlatu ina zan saka kaina da wannan abun kunyar! shin wai me yake damun d'an
uwanki ne? Ya rasa wacce zai aura sai 'yar cikinsa yarinyar da ya ri'ke tamkar
shi ya haifeta amma saboda tsabar abun kunya yace zai aureta tsofai-tsofai
dashi zai auri 'yar 'karamar yarinya babu shakka wannan karon komai zai faru
tsakanina dashi sai dai ya faru dan na rantse da Allah ba zan bari ya tozartani
ya had'ani kishi da matsiyaciyar yarinyar
nan da na riga nasan matsayinta a zuciyarsa ba."
Ya Ramlatu
ta sauke ajiyar zuciya tana fad'in "Ai shiyasa nima dana ji labarin
hankalina ya tashi sosai! Kishi da irin jinin Malam Baba ai bala'i ne wane irin daurin gindi ne Halimatu bata samu
ba a gurin Abbas din, ai wallahi kece abar tausayi mutukar kika bari ya auri
yarinyar nan to ki rubuta ki ajiye auran ki ya 'kare tsakaninki da mijinki."
Yaya Ramlatu
ta 'kare maganarta cikin karfafa maganar ta gami da 'kokarin 'kara ingiza
zuciyarta.
Goge
fuskarta tayi tace"Yaya Ramlatu ai na fad'a miki wallahi tallahi sai dai
ya za'ba ko ni ko yarinyar nan dan ni ba zanyi kishi da Yayarta ba itama nazo
nayi da ita ba, wannan karon duk abinda yake ji dashi dai-dai nake dashi zai
dawo gidan ya same ni.''
Yaya Ramlatu
ta dauki lemo ta kur'ba tace"To ai dik da haka ba zama za kiyi ba dole ki
d'an nemi taimako dan baki san irin shirin da iyayen yarinyar suke a kan
al'amarin ba, dan wannan tsinannan Malam Baba mugun mutumi ne babu irin
surkullan da bayayi." Halisa tace"Yaya Ramlatu ni yanzu gabadaya ma
banda kuzarin zuwa gurin wani malami da sunan taimako nifa gabad'aya auran
Abbas ya fice min daga rai ya dawo ya sake ni." Ta'karasa maganar cikin rawar murya. Yaya Ramlatu tace"A'a
ba za'ayi hakaba ke yanzu idan kika kashe auranki saboda wannan yarinyar ai kin
cutar da kanki! kada kice ya sake ki kawai idan ya dawo ki daga masa hankali ke
macece kin san hanyoyin da zaka hanashi nutsuwa da kwanciyar hankali gefe guda
kuma zamu sa malamai su taimaka miki insha Allah sai zuciyarsa ta karye yaji
sha'awar auran ya fita daga ransa da kansa zaice ya fasa."
Halisa tayi
shuru tana tunani! Yaya Ramlatu tace"Dole ki futo da kudi aje a taimaka
miki ni gaskiya bazan so ki bar dakin ki
ba, ki zauna kici ubansu daga shi har yarinyar idan Allah ma ya kaddara sai ta
shigo gidan sharri kad'ai ya isheta.
Halisa taja
ajiyar zuciya tare dayin 'kwafa,
tace"Maganar ki haka take Yaya Ramlatu bari na kawo miki dan abinda ke
hannuna dan Allah kiyi min kokari akan al'amarin." Yaya Ramlatu
tace"Kada ki damu zan shiga na fita insha Allahu maganar auran zata rushe
ke idan ma Allah ya kaddara auran to wallahi ba zamu k'yalesu suji dad'in
rayuwa ba." Halisa ta gyada kanta tana dan jin sassauci acikin zuciyarta,
bedroom dinta ta nufa, minti biyar ta fito hannunta rike da kudi 'yan dubu
dubu. Ta mikawa Yaya Ramalatun da fadin "Dubu ashirin ne zuwa gobe sai ki
aiko a kar'bi dubu talatin din zanyi duk yanda zanyi na dauki key din gurin da
yake ajiyar kudi na dauka."
Yaya Ramlatu
ta mike tana gyara yafan mayafinta tace"Nima daga nan zan wuce gidan *'Yar shagamu* (wata hatsabibiyar 'kawar Ramlatun ce)Ta
cigaba da cewa......"akwai wani malami da mukayi hirarsa kwanaki da ita
tace ya iya aiki idan dare baiyi ba zamuje idan kuma dare yayi to da sassafe
zamu buga sammako dan kada muje mu tarar da mutane." Halisa taji wani
sanyi a ranta tace"Yaya Ramlatu nagode kawarai da kaunar da kike nuna min
hakika ina alfahari dake a cikin 'yan uwan Abbas kina nuna min kaunar da
mahaifiyarku ma bata nuna min."
Yaya Ramlatu
ta dafa kafadarta tace"Kada ki damu
cikin ko wane irin hali ina tare dake, maganar Hajiyarmu kuwa dama can tafi
kaunar Halima a kanki saboda gidan Malam Baba sun riga sun gama dasu daga ita
har Alhajin, dan baki ga yanda suke murna da wannan al'amarin ba, Hajiya har da
kuka tana 'kokarin yi min baki akan nace auran Abbas da yarinyar bai dace ba,
shine fa take kuka har dayi min gorin abinda Abbas din keyi wa Salim."
Halisa ta
shiga girgiza kanta, cikin 'kunar zuciya tace"Ai ba sai kin fad'a mun ba
dama tuntuni na san Hajiyarku bata sona ko lokacin Halimatu tafi nuna kulawarta
a kanta, to kinga kuwa dole taso wannan al'amarin ni na rasa me nayi mata ta
tsaneni."
Yaya Ramlatu
tace"Wallahi duk sharrin daga gidan Malam Baba yake gabadaya fa sun gama
da zuciyoyin jama'ar gidanmu nice kadai na gagaresu." Halisa na jin d'aci
a ma'kogwaronta tace"Insha Allahu sai mun karya alkadarinsu."
To sallama
sukayi da juna inda Yaya Ramlatu take sake tabbatar mata da cewar yanzu idan ta fita gidan *'Yar Shagamu* zata
nufa domin su tattauna yanda al'amarin tafiya gidan malam zai kasance.
Koda
Naja'atu ta koma gidan Malam kai tsaye dakinsu ta shige taje ta kwanta kan
katifa, ta dinga kuka tana birgima kan katifar! sai sambatun surutai take da
kiran sunan Halimatu wai ta mutu ta bar baya da 'kura mutuwarta tana nema ta
zame mata barazana ga rayuwarta...........Sautin kukan tane ya cikawa Baba
Talatu kunne da sauri ta fito daga kicin ta nufi dakin, nan ta tarar da ita sai
burgima take kan katifa tana dukan kanta da kanta kamar wata mahaukaciya sai
surutai takeyi da fad'in in dai aka
daura mata aure da wani ba Salim ba to sai ta kashe kanta ta kashe wanda aka aura mata......Baba Talatu ta shiga
dakin hankalinta a tashe ta birkitota
wani wawan mari ta kifa mata a fuskarta tana wani irin huci!! Rintse idonta tayi ta mike zaune hannunta kan
kuncinta idanunta a rufe amma hawaye ne kawai yake zurara.
Murya na
rawa Baba Talatu tace"Naja'atu idan baki kashe kanki kin kashe Alhaji
Abbas ba bakya kaunar Allah! Wai shin ke d'in wace irin yarinya ce butulu mai
manta alkairi! yanzu da abinda zaki sakawa da wannan bawan Allahn kenan? wannan
wace irin 'kiyayyace kike nuna masa 'karara? meye bai miki ba? ki sani idan da mutuwa bata ratsa tsakaninsa da matarsa ba ke
baki isa ya kalleki ba ballanta yace zai aure ki dan saboda baki dace daki auri
nagartaccen namiji kamar wannan ba! meye laifinsa? meye kuma illarsa!? Muna
tsaka da alhani gami da rad'ad'in mutuwar 'yar mu mai biyayya kina nema ki
d'ora mana ciwo! ashe bamu isa dake ba? ashe kuma Halima bata cancanci sakayya
al'kairi a gurinki ba? Idan kin auri mijin Halimatu babu wanda zai kai ki Jin
dad'i itama kuma zata samu farin ciki alkairin da kikayi mata kin auri mijinta bayan
babu ranta kin tallafi 'yayanta! to wallahi duk sanda na kara jin kinyi wani
mummunan furuci kan wannan bawan Allahn sai ranki ya 'baci! sai na fad'awa
Magaji duk abinda kike yi tunda ni da
malam kin raina mu bakya ganin mutuncin mu."!! Baba Talatu ta kare
maganarta cikin tsantsar 'bacin rai gami da jin takaicin abinda 'yar tata
takeyi.
Baba Talatu fita tayi daga dakin ranta a
'bace! hakika yarinyar bata ta'ba 'bata
mata rai ba irin yau! ita rasa gane meye abin gudu a game da wannan auran da
suke kokarin had'awa, a iya tunaninta da tsinkayen ta tana ganin kamar gata
sukayi wa yarinyar har indai sun had'ata
aure da mijin 'yar uwartata dan hausawa na cewa Naji dad'i shine gari ba nasa
baba........Baba Talatu na fita daga d'akin ta zame a hankali ta kwanta kasan
ledar dakin tana takure jikinta ta cigaba da kukan rashin mafita, a lokacin ji
take yi dama Allah zai dauki ranta ta huta daganin wannan masifar..........
Koda Saddiqa da Mussadiq suka shiga dakin suka sameta a kwance tana kuka! Mussadiq ne kawai ya tsaya a kanta yana mata
magana ita kuwa Saddiqa saboda tasan ko kukan me takeyi yasa ta juya ta fita daga d'akinta ranta a
'bace! hakika tana jin ba'kin ciki da takaicin irin 'kiyayyar da take nunawa
mahaifinta, shiyasa itama ta soma jin haushinta akan irin abinda takeyi kan
al'amarin.
Mussadiq ya
'karaci maganarsa ko kallonsa ba tayi ba haka ya fita daga dakin jikinsa duk a
sanyaye! haka suke shiga damuwa koda can idan sun ganta tana kuka ko rashin
lafiya daga su har mamansu da Abbansu duk su damu duk da bashi da wayo sosai shima ya fahimci
cewar Antin tasu bata 'kaunar zaman aure da babansu........Zama yayi kusa da
Saddiqa tana gyarawa Baba Talatu wake suna hira jefi-jefi ya kalli Baba talatu
da fad'in "Baba me akayiwa Yaya Naja'atu take kuka."? Baba Talatu
tace." Kyaleta Mussadiq ka fita daga sabgarta kaji ko." Mussadiq yayi
shuru jikinsa duk yayi sanyi.........To Har aka idar da sallahar azuhur
Naja'atu na kwance a daki tana juye-juye zazza'bi me zafi ne ya rufe ta wanda ya hanata mikewa taje tayi alwala tai
sallah.
Saddiqa ta
shiga dakin domin yin sallah ta kalleta
itama ta kalleta babu wanda yace komai a tsakaninsu, Saddiqa ta gyara dadduma
ta tayar da sallaharta, koda ta idar mikewa tayi ta fita daga dakin ba tare da
tace komai ba, to sai hakan da tayi ya
bata mamaki sosai! kuma ya nuna mata cewar yarinyar fushi take da ita, jikinta
ne yayi sanyi sosai ta rinste idonta murya na rawa tace"Ba laifi na bane
laifin zuciyata ne Saddiqa bana 'kin mahaifinku sai dan zuciyata ta riga ta
gama makancewa da kaunar Salim, a dai-dai lokacin da muke sanya rai da
bukatarmu zata biya a dai-dai lokacin kuma za'a kawo mana cikas a rayuwarmu
ha'kika rayuwarmu nida Salim na cikin kalubale mai girma mutukar akace baza'a
daura mana aure da juna ba."
Muryar Mussadiq taji a kanta, tayi saurin bude
idonta tana kallonsa......Mussadiq duk yaji abinda take fad'a ya fahimci wata
maganar wata maganar bai fahimce ta ba, Yace."Yaya Naja'atu ki tashi kiyi
sallah kici abinci mu tuntuni munyi sallah munci abincinmu.
Hannunsa ta
ri'ke ya zauna kusa da ita murya na rawa tace"Mussadiq bani da lafiya
zuciyata na daf da tarwatsewa."!! Da sauri yaron ya d'ora hannunsa saman
goshinta yana fad'in "Yaya Naja'atu kanki ne yake ciwo ? sannu bari na
kira Abbanmu a waya ya kawo miki magani." Girgiza kanta tayi tana kokarin
mikewa zaune tace"Mussadiq wannan ciwon nawa Abbanmu shine ya haddasa mun
shi dan Allah kace dashi yayi hakuri ya k'yaleni." Mussadiq ya dinga
kallonta cikin mamaki yace."Yaya Naja'atu
Abbanmu ba zai cutar dake ba kiyi
hakuri ki aureshi ki zauna dashi."! Taji wasu hawaye na kokarin kufce
mata, wai kowa sai yace tayi hakuri ta zauna dashi to wai ta yaya zata iya zama
dashi alhalin bata sonsa kuma a matsayin Uba take kallonsa, abunfa da wahala
wai (gurguwa da auran nesa) mikewa tsaye tayi a hankali ta fita daga
dakin, Shi kuma Mussadiq din ya dauki
wayarta ya nemi numbar Abban nasu ya shiga kira.
Koda yaga
Numbar Naja'atu na kiransa bai 'ki dauka ba, sai dai babu walwala a tare dashi
yayi sallama! sai kawai yaji muryar Mussadiq yana fad'in "Abbanmu nine
Mussadiq na kira ka da wayar Yaya Naja'atu." Murmushi yayi yana jin wani
farin ciki yace."Na gane ka Magajin Abbah Ina fatan lafiya ina Naja'atun
take."? Mussadiq yace."Yanzu taje yin sallah bama ta da lafiya sai
kuka takeyi tana cewa wai dan Allah ka 'kyaleta."!! Shuru yayi yana
nazarin maganar yaron daga bisani yace."To shikkenan kace mata na kyaleta
tunda bata son Allura ba zan kawo likita yayi mata ba." Mussadiq
yace."Ba wannan ba Abba naji tana cewa kada ka aure ta ita tafi so ta auri
ancle Salim Abbanmu tunda bata so ta zauna tare da kai ka kyaleta ta auri wanda
take so."!! Abbah Abbas ya jima yana mamakin maganar yaron, kuma yana
mamakin abinda yarinyar take yi na rashin kyautawa! wato yaran take zaunawa
dasu tana nuna musu a zahiri bata kaunar Ubansu har tana bawa 'Dansa sa'ko ya
bashi! ranshi ya 'baci sosai da sosai! sai kawai yayi 'kokarin bagarar da
maganar ta hanyar fad'in "Ina Saddiqa take kace mata nace ku shirya gobe
zan aiko Salim ya dauke ku xaku koma makaranta ranar Monday."
Yace."Tom zan fad'a mata Abbah." Yace." Yawwa ka gaishe min da
Baba Talatu da kyau." Yace." Za taji Abbah." Kashe wayar yayi ya
shiga nazarin irin iskanci da wulakancin da yarinyar ke masa, zai iya hakura da
duk irin cin fuskar da za tayi masa amma kuma ba zai lamunci ta dinga cin
fuskar 'yayansa ba, hakan da take yi zai sanya ransu ya 'baci! su shiga halin
damuwa da maraicin mahaifiyarsu.
To da wannan
'bacin ran ya shiga gidansa......In da yaje ya tarar da tashin hankalin Halisa
dan ko zama bata bari yayi ba tabi shi d'aki! ta shiga zazzaga masa rashin
kunya gami da farfad'a masa duk maganar da tazo bakinta kana kuma tace"
Sai dai ya za'ba ita ko Naja'atu dan wallahi ba za tayi kishi da Ya tayi da
kanwa ba.
Babu Abinda
yace mata ya shiga bandaki domin yin wanka zuciyarsa tamkar zata tsaga kirjinsa
ta fito dan tsananin 'bacin rai!!!! Koda ya fito samunta yayi a kwance 'kasan
ties tana kuka had'e da wata iriyar fuffuka tana burgima 'kasan ties kamar mai
iskokai! Ya shirya tsaf ya tsallaketa ya fita ya barta a dak'in! Bin hanyar da
yabi tayi da kallo hawaye na sharara ta mi'ke zaune tana cizon tsaya wato Abbas
ko gani yayi zata mutu ba zai tanka mata ba kenan ballanta ya fada mata magana
mai dad'i! aikuwa a zuciye ta mi'ke tsaye! tana rangaji! da had'a hanya, ta
nufi kicin d'inta.
Yana zaune
gurin cin abinci yaga fitowarta kallo ya bita dashi yana jan tsaki a fili ya
shiga bude kwanonin abincin da ta jera kamar gaske! wayam! babu komai a ciki
amma saboda tsabar iskanci da iya shega na Halisa ta shirya tevur kamar ta
shirya lafiyayyan abinci......Takaici ne ya kamashi ya tsirawa hanyar data bi
ido, kawai sai ya hangota ta fito daga kicin d'in hannunta ri'ke da
shar'be'biyar wu'ka sabuwa dal da alama daga cikin kwalinta ta cire, kai tsaye
ta durfafo inda yake jikinta na tsuma da rangaji! take fad'in "Wallahi yau
koni ko kai a gidan nan Abbas na gaji da wannan abun da kake min ni ka sake ni
ma na huta da ganin wannan takaicin auran wannan yarinyar da zakayi masifa ne a
gare ni da kai baka sani ba sai sanda nayi maka illah a rayuwarka sannan zaga
gazgata maganata." ..........Mufida ta shigo palon tana sanye da uniform
na makaranta ta hango abinda ke faruwa, a guje ta jefar da jakarta tayi kan
mahaifiyar tata dake dumfarar mahaifinta da dalleliyar wu'ka! tana nema ta caka
masa! " Cikin karaji!! tace" Mommy meye haka? me za kiyi? Wayyo Abbanmu ka gudu."!! Tafad'a tare
da zuwa ta rungumeshi tana jansa wai ya gudu. Shi kuwa yana tsaye turmin danya
bai razana ba, wato wai-wai d'in da yake ji a gari a na cewar mata na kashe
mazajen su idan za'ai musu kishiya abun yazo kansa, jira kawai yake ta 'karaso
da wukar yaci ubanta! Halisa ido a rufe
ta 'karasa inda suke Mufida na kuka tana jansa da fadin "Abbah mu gudu
kada ta caka maka wu'ka Abba me kayi mata n...........Gani tayi ya kama duka
hannuwan Mahaifiyar tata ya murd'e da iyakacin karfinsa Wu'kar ta su'buce ta
fad'i 'kasan gurin! Ya kai mata wani lafiyayyan mari! da bayan hannunsa, wani
'karamin jini ne ya fito daga hancinta, kafin ma ta dawo hayyacinta ya sake
kifa mata wani a d'aya gefan, sai kawai yaga ta yanke jiki ta fad'i ta shiga
turje turje tana taune harshenta..........Aljanunta ne suke ka da ita a gurin
ta dinga turje-turje tana taune harshenta farar kumfa nata fitowa daga bakinta,
Halisa na 'karyar aljanu ashe dama tana dasu da gaske! sosai take burgima a
gurin tana ta wasu gwalantu wanda ba wanda yake ganewa a cikinsu, Mufida ta
nufe ta tana kuka zata ta'ba ta, ya
hanata Yace." Je ki cire uniform din'ki idan ta gaji da iskancin da
take zata tashi."
Tsakanin Uwa
da D'a sai Allah tace"Abbah duba fa kaga abinda take wannan abun ba 'karya
bane dan Allah kayi wani abu kai."
Tsayawa yayi
tsai yana nazarin Halisan da abinda takeyi Eh kwarai kuwa wannan abun da take
yasha bambam dana ko yaushe dan haka sai ya umarci Mufidan ta kawo masa ruwa a
kofi, da sauri ta taje ta dauko masa, ya kar'ba ya shiga tofa ayatul'kursiyu da
fala'ki da nasi 'kafa bakwai bakwai kana ya iske inda take, ruwan tofin ya
guntsa a bakinsa ya shiga fesa mata a jiki, sai da yayi haka sai uku tukkuna
sannan ta daina burgimar da take yi ta daina gwalantun surutan da take yi jikinta ya shika sosai tayi lakaf gumi duk ya
jika mata jiki, Mufida na kuka taje ta rungumeta tana kiran
sunanta................
_*Ana samu
mata marasa hankali da tunani irinsu Halisa wanda suka maida kishiya abokiyar
gaba suke ganin zasu iya jefa kansu ako wace irin masifa saboda namiji da
kishiya, Allah ya sawa'ke wa duk macan da take haukan kishi kan mijinta zai
'kara aure! Wallahi garin tsabar haukan ki zaki je ki jefa kanki cikin masifar
rayuwa gami da nadama.*_
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA
#300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA
KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI
MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA
BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN
WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU
NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN
NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram
Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR
ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA
WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar
Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*11*
Mufida
sai tatta'ba jikin mahaifiyar tata take
tana kuka had'e da kiran sunanta, Halisa na kwance tamkar gawa wani irin bacci
take yi mara dadi...........Ya fito daga daki Cikin shirin fita nan yaga Mufida sai kuka take ta takure
kanta a guri guda, tausayi ta bashi sosai kasancewarsa mutum mai son 'ya'ya
yasa kwata-kwata baya 'kaunar abinda zai 'batawa d'ansa rai dalili suma yaran
nasa dai-dai gwargwado suna masa biyayyar da ta kamata, a nutse ya tsuguna kusa
da yarinyar yana kiran sunanta.
A firgice ta
d'ago kanta tana kallonsa sai ta sake rurucewa da kuka tana nuna masa Mommynta
dake kwance, baki na rawa tace"Abbanmu mommy ta'ki tashi sai tashinta nake
yi gashi babu kyau baccin yamma." Yace."Insha Allahu za tashi ki
kwantar da hankali yanxu tashi kije ki sanja kaya kizo ki rakani na siyo mana
abinda zamu ci." Jiki a sanyaye ta kalleshi kafin tace"Abbah mommy
tayi girki gashi can ta jera kan tevur." murmushin takaici yayi
yace."Babu komai a cikin kwanukan dake jere a tevur kawai tayi hakane dan
ta 'bata min rai." shuru yarinyar tayi tana nazarin maganarsa, babu shakka
akwai abinda ke faruwa wanda bata sani ba
Yace."Maza
tashi ki sanjo kaya mu tafi kada magariba tayi." mi'kewa tayi ta dauki
jakarta ta nufi dakinta, A nutse ya juya
yana kallon Halisa dake sheme 'kasan kafet idanunta duk sun zurma ciki lokaci
guda duk ta furgice ta rame, tausayi ta bashi kad'an! ya shiga girgiza kansa
mamaki yake sosai Halisa ta kai matakin shekaru talatin da biyar a duniya amma
har yanxu ba tayi hankali ba, wai wu'ka ta d'auko zata yi masa rauni kawai
saboda zai raya sinnar ma'aiki, to meye a ciki kuma meye abun damuwa dan ya
auri Naja'atu, sam bai aikata haram ba sai ma sinna daya 'karfafawa kansa dan ya auri Naja'atu
tana da shekaru 16 a duniya a ganinsa ba aibu bane, tunda Annabi Muhammad
(s.a.w) ya auri Nana Aysha tana da shekara tara, to kuwa idan hakane ai babu
laifi gurin auransa da Naja'atu, wani
sa'in mutane sunfi girmama al'ada akan addini shiyasa su suke ganin kamar ya
aikata haramci! auransa da Naja'atu kuwa yana tunanin babu wani mahalukin da ya
isa ya hana, idan ba'ayi ba to babu
shakka Allah ne bai so ba
Mufida ta
fito a kintse itama tasha hijab dinta har'kasa, haka yake sawa ana d'inka musu
hijab manya manya, kasancewar sa mabiyin sinna kai idan kaga yanda yake
mu'amula da mutane da yanda ya tsayar da (gemu) zaka fahimci cewar bai yarda da
wata bidi'a ba, abokanshi wataran har tsokanarsa suke idan yana kawo musu
'kauli da ba'adi, koda yake irin wannan dama ya saba faruwa a tsakanin mutane kowa da d'ari'kar da tayi masa shi dai Abbah
Abbas 'Dan izala ne sosai dan gabad'aya bai yarda da bidia ba shiyasa bai fiye
sakin jikinsa da mutane ba.
Da kansa
yake draving din yana tunanin rayuwa da abubuwan da suke
faruwa dashi da 'yayansa, babu shakka mutuwar Halimatu babban gi'bi tayiwa
rayuwarsa data 'ya'yansa da Halimatu na raye babu wanda zai samu dama a kansa,
Kira ne ya shigo Wayarsa dake gefansa ya
d'an kalli wayar sai yaga My dota na yawo kan screen din
wayar......Dauke kansa yayi ya cigaba da draving d'insa, hakika abinda yarinyar
nan keyi masa yana mugun 'bata masa rai!
Ita kuwa
Naja'atu cigaba tayi da kiran wayar so take ya d'aga ta fad'a masa magana mai
zafi dan yanzu suka gama waya da Salim ya sake tunzura mata zuciyarta, ya
fad'a mata duk yanda sukayi da Abba Abbas din dazu da safe da zai kaisu kasuwa,
shine ya kira wayarta ya fad'a mata komai ya ingizata kan tayi fito na fito
dashi tunda shine ya zubda mutuncinsa, lokacin itama zuciyarta ta gama
'ke'kashewa tana ganin zata iya fito na fito dashi tinda hausawa na cewa idan babban ya zubar da girmansa to shi
'karami sai ya hau ya taka............Kiran wayar take yi jikinta sai kyarma
yake tana had'a gumi, shi kuma yana kallon wayar nayi tana katsewa bai dauka ba
kamar yasan abinda zai faru.
Mufida tace"Abba
ana ta kiran wayarka fa." hankali
yace."Mufida bana so ina draving ina amsa waya idan muka sauka zan kira ko
waye." Shuru tayi na minti biyu kafin tace"Abbah dan Allah me ya
had'aku da Mommyna ta d'auko wu'ka zata caka maka."
Yayi jim
kafin yace."Mufida babu abinda ya had'a mu kawai tayi ra'ayin kasheni
ne."! Yarinyar tayi shuru na minti biyu kafin tace"Abbah dan Allah
kayi hakuri kaji ko." Murmurs yayi
yana kallonta yace."Nayi hakuri saboda ke Mufida da mahaifiyar ki nada
hankali irin naki da naji dadin zama da ita." Murmushi tayi tana rufe
fuskarta tace"Abba nagode Yana farin ciki yace."Ubangiji Allah ya
raya min ku tafarkin addini musulunci." Ta amsa da ameen
Abbah............Naja'atu kuwa wani 'katon abu ne yazo ya tokare mata a
ma'kogwaronta ta jefar da wayar kan katifa ta kwanta rigingine had'e da 'kurawa rufin dakin ido! Abba Abbas
ya'ki daga wayarta saboda yasan bashi da gaskiya eh ai dama dole da ya'ki d'aga
wayarta saboda ya kasance munafikin mutum kuma azzalimi! Hawaye suka kwaranyo daga
idonta.
Muryar
Mussadiq taji a kanta yana fad'in "Yaya Naja'atu ya jiki ki tashi kiyi
sallah magariba tay.......A fusace! ta mike zaune tana nuna masa 'kofar futa da
fad'in " Fita ka bani guri munafikin yaro babu dama na shigo daki na
kwanta zai shigo ya dame ni."!
Yaron ya
dinga kallonta a tsorace! dan tunda suke bata ta'ba yi masa tsawa irin ta yau
ba.
Baba Talatu
da Saddiqa sun jiyo abinda ke faruwa ransu ya 'baci sosai Saddiqa ta d'aga
labulan d'akin tana kallon Mussadiq din
cikin rawar murya tace"Kai Mussadiq fito ka bata guri."!
Cikin sanyi
jikin ya juya da niyar fita daga d'akin, gabad'ayansu tabi su da wani irin
kallo wanda na kasa tantance ko na meye......Baba Talatu ta kalleshi a nutse
cikin tausasawa tace"Mussadiq kada ka 'kara zuwa kace tazo taci abinci ko
tayi wani abu Yunwa dai ba 'kanwar uwarta bace da kanta zata nemi abinda za
taci , kada ka kara zuwa inda take ballanta ta hantareka ko ta zageka duk
abinda take ganin shine dai-dai da Rayuwarta sai taje tayi, tunda Ita ba tajin
magana."
Mussadiq da
Saddiqa suka zauna tsuru cikin sanyi jiki, sai da malam ya shigo sannan suka
samu sakewa suka ci abinci tare dashi yana jansu da wasa da dariya.
Take away
yayi musu na abinci mai rai da lafiya ya
siya musu lemuka da yught masu sanyi da dad'i! Kowa da nasa ledar, Yana draving
ya kalli Mufida yace."Kafin mu koma gida zamu je ki gaisa da 'yan uwanki
sai na basu na yught d'in ko." Tace."Yawwa Abba dama nayi kewarsu da
Yaya Naja'atu ma." Yace."Zan kai ki yanzu ku gaisa sai mu shiga gidan
Alhaji ma ku gaisa dasu Hajiya ko." Tana ta murna tace"Abbah nagode
sosai kuma naji dad'i." murmushi
kawai yake yi a kaso d'ari na damuwar da yake ciki kaso hamsin ya zube
sakamakon nutsuwa da nagartar 'yarsa Mufida, a duk sanda zai kalleta wani farin ciki ne yake lullu'beshi dama haka
Ubangiji yake sai ya fitar da shiryayye daga jikin mara hankali, yanzu yanda
Mufida take mu'amula waye zai ce Halisa ce ta haifeta, Yarinya 'karama tafi
uwarta hankali.........Ana kiraye kirayen sallah magariba suka shiga unguwar 'kofar
Na'isa, a bakin gidan Alhaji yayi parking din motarsa, ya umarci Mufida ta
shiga gidan Alhajin shi zai shiga massalaci...........tare suka fito daga motar
Mufida ta nufi gidan Alhajin shi kuma ya
nufi masjid din dake jikin gidan...........Baba Malam ne da Mussadiq suka fito
daga gida da niyyar shiga massalaci Mussadiq na ganin Abbansa na daura alwala
yayi murmushi cikin farin ciki yace."Baba Malam ga Abbanmu can yazo."
Baba malam na fara'a yace."Eh kwarai kuwa watakila zuwansa kenan."
Abba Abbas
na ganin zuwansu gurin sai ya mi'ke cikin fara'a ya mi'kawa Baba Malam hannu
suka gaisa cikin mutunci Mussadiq ya mika masa hannu yana dariya
yace."Abba barka da zuwa."Ya amsa da barka dai Mussadiq." Alhaji
Sama'ila ne ya fito daga cikin gida dai-dai lokacin da limami ke kokarin tayar
da sallah dan haka gabad'ayan su sai suka shiga cikin massalacin domin gabatar
da sallahr magariba.
Koda suka fito daga masjid din sai da suka
sake gaisawa, Mussadiq ya ri'ke hannun mahaifinsa sai walwala yake, shi kuwa
Baba malam sai tsokanarsa yake ganin ya manta
dashi dan yaga babansa, Baba malam na kallo Mussadiq yabi bayan
mahaifinsa zuwa cikin gidan Alhaji, sai kawai yayi murmushi ya juya domin shiga
cikin gidansa, yana mamakin halin
'kuruciya.
A nutse suka
gaisa da mahaifiyarsa tana tambayarsa Halisa yace."Tana nan lafiya kalau
alhamdullhi." gurin yayi shuru na minti biyu kafin Alhaji Sama'ila dake
zaune kan kujera yayi gyaran murya, a nutse yace."Naji dadin zuwan nan
naka kwarai da gaske, domin ina so mu tattauna magana da kai mai
muhimanci." Gyara zamansa yayi a nutse yace."To Alhaji inajin
ka." Alhaji Sama'ila yace."Dazu Ramlatu tazo da wata magana wacce ni
ban san da ita ba wai ashe Salim d'an
wajenta ya d'ade yana son ya auri yarinyar nan Naja'atu wacce ake maganar aure
a tsakaninku, tace tun tana yarinya yake sonta kuma kai kasan da maganar domin
har al'kawari kayi masa kan cewar zaka shige masa gaba ya aureta ya akayi kuma
kasan da wannan magana a tsakani ka bijiro da bukatarka." ? Abbah Abbas
yayi shuru yana nazari maganar mahaifin nasa,
a nutse yace."Eh kwarai kuwa Salim ya dad'e da fada min cewar yana
son Naja'atu kuma ni da kaina nine nayi masa al'kawari kan zan bashi auranta,
kuma ina nan zan shige masa gaba akan lamarin mutukar Allah ya kaddara yarinyar
matarsa ce."
Alhaji
Sama'ila yace."To alhmdullhi wannan magana da kayi tana nuna mana cewar ka
janye kudirinka na auran yarinyar ma'ana ka barwa Salim din ya aureta."?
Kai tsaye yace."Eh idan hakan shine alkairi a gare mu baki daya." Alhaji Sama'ila
yace."Masha Allah to Allah ya tabbatar mana da alkairi yanzu idan mun fito
daga sallahr isha'i zan shedawa malam din abinda ake ciki.
Yace."A'a
Alhaji kada kayi masa magana ka kyaleni da kaine xan masa maganar yanda zai
fahimta." Alhaji Sama'ila yace."To babu damuwa duk dai yanda ake ciki
nasan zaiyi min bayani Allah ya tabbatar da alkairi."
Ya amsa yana
kokarin danne damuwa dake taso masa.........Mi'kewa yayi yace."Bari na
shiga gidan malam din mu gaisa zan d'an duba yara ina tunanin daga can zan mu
wuce gida."
Ya kalli
Mufida data kurawa tv ido yace."Mufida tashi mu tafi ko zaki zauna tare da
hajiya ne." Mikewa tayi tana murmushi, Hajiya Talatu tace"Nima ban
nema ba, kai da baka so 'ya'yanka na
zuwa ko'ina yanzu ma ka fad'i hakane dan kaji dad'in bakin ka." Dariya
yasa, ya rike hannun Mufida yana musu sallama.............Mussadiq na jikin
motarsa a tsaye suka fito suka same shi, ya bude motar ya fito da tsarabar da
yayi musu leda uku ya mika masa da fad'in "Ka dauki naka ka bawa Naja'atu
da Saddiqa nasu." Ya kar'bi ledojin yana murna suka shiga gidan malam din
shida Mufida.
Malam na
zaune kan dadduma a kan dakalin gidansa yana kallon zuwansu, yayi murmushi yana
kallon Mussadiq din cikin tsokana yace."Zo ka bani nawa." Mussadiq
yasa dariya yana fad'in "Baba Malam ai kai baka shan za'ki baka shan Ice
cream." Yace."In dai ka bani to zan sha yanzu." Mufida ta mi'ka
masa ledar hannunta tace"Ni ga nawa na baka." Baba malam yayi
murmushi yace."To godiya nake yi Mufida wasa nake ni ban iya shan kaye kayen za'ki ba wannan
sai ku yara." Abbah Abbas ya karaso gurin yana murmushi yana jin dadin
yanda mutumin ke wasa da dariya da 'yayansa shi duk mutumin da zai kula da
d'ansa to yana da daraja da martaba a idonsa.
Mufida da
Mussadiq suka shiga cikin gidan baba malam din, shi kuma ya nemi gefan daddumar
malam din ya zauna a nutse ya sake bashi hannu sukayi musahaba kafin
yace."Malam naji dadin samun ka kai kad'ai , dan saboda dama ina so muyi
magana da kai mai muhimanci."
Baba malam
ya gyara zamansa yana kallonsa a nutse yace."Ina sauraranka." Shuru
yayi na minti biyu kafin yace."Magana ce kan Yarinyar nan Naja'atu kwana biyu da suka gabata nazo maka da
bukatar son ka bani auranta saboda inaso ta zama *MADADIN* halimatu a gurina,
to malam ka gafarce ni da maganar da zan fad'a maka a yanxu na janye maganata
ta farko kan yarinyar nan, inaso a bata wanda take so ta aura kuma insha Allahu
ina nan a matsayin uba a gareta zan dauki nauyin komai idan auranta ya
tashi."
Malam Ya
shiga girgiza kansa yana kallonsa yace."Abbas ni ba 'karamin mutum bane
kuma ba'a magana biyu dani! kamar yanda
ka bukaci na baka yarinyar nan ka aura na kuma ce na baka to na baka ita har
abada idan nine na haifi Naja'atu to bata da miji sai kai dan haka ka daina
kawo wata magana ta daban." Abbah Abbas ya bude baki zaiyi magana Alhaji
Magaji ya iso gurin, hannu ya mika musu su gaisa ya samu guri ya zauna yana
kallonsu ganin dukkaninsu fuskokinsu babu walwala yasa ya tambayi abinda ke
faruwa.
Baba Malam
ne ya sheda masa abinda ke da a kawai
Alhaji
Magaji ya shiga kallon abokin nasa cikin takaici yace."Banyi tsammanin
haka daga gurinka ba Alhaji Abbas! Ya zaka zo da magana mai muhimanci daga baya
kuma ka dawo da wani zance da daban. Gaskiya bamu ji dadin wannan furucin naka ba, dukkaninmu munfi
kaunar ka zama miji ga Naja'atu dan haka wannan maganar da kazo da ita ka ajiye
ta kamar yanda malam ya fad'a maka cewar Ya baka yarinyar nan har abada to bata
da miji sai kai."
Abbah Abbas
yayi shuru yana jimanta al'amarin yaso ya daurewa zuciyarsa ya hakura da
yarinyar duk domin samun daidaito da kwanciyar hankali ta kowane 'bangare to
amma ya lura dasu malam ba zasu amince masa da bukatarsa ba......Yana kokarin
yin magana, Mufida da Saddiqa da Mussadiq suka fito daga gidan malam d'in Mufida hawaye take
sharewa Mussidiq na sharewa hawaye Saddiqa ce kawai mai dauriya a cikinsu.
Abbah Magaji
ya kallesu da sauri yace."Kai kukan me kukeyi Saddiqa me ya faru."?
Shuru tayi
ta kasa magana bakin ciki kamar ya fasa mata zuciya, wai yau an wayi gari Yaya
Naja'atu itace ke zaginsu tana wasa musu yught a jiki.
Mussadiq na
goge fuskarsa da jikinsa yace.''Yaya Naja'atu ce tayi mana tsawa! ta watsa mana
Yught a jikinmu nida Mufida." Abba Abbas ya dinga bin jikin yaran nasa da
kallo Eh tabbas gashi nan duk yught a jikin hijabin Mufida da 'kasan rigar
Mussadiq."
Abbah Magaji
yace."Me kukayi mata to." Mufida tace"Abbanmu ne ya siyo mana
yught da snacks shine ya bamu kowa leda d'aya yace mu kai mata nata shine muna
shiga dakin ta zage mu ta watso mana yught nida Mussadiq."
Gurin ne
yayi shuru kowa na 'kokarin danne 'bacin ransa, mussaman shi Uban yaran da baya
so ko 'kuda ya sauka a kansu, kokarin danne fusatarsa yake gudun kada ya aikata
abun kunya yasa ya mike yana fad'in "Zamu tafi da yaran gabadaya dan
monday zasu koma makaranta.
Jikin sanyi
jiki Baba Malam yace." Alhaji Abbas ban tari hanzarin ka ba, ka koma ka
zauna ai bamu gama magana ba."
Abbah Abbas
ba yanda ya iya ya koma ya zauna yana ta ya'ki da zuciyarsa......Abbah Magaji
kuwa mikewa yayi a fusace! ya shiga cikin gidan, Tana tsugune da buta a gabanta
zata daura alwala ta kasa ta had'a tagumi sai tunani take yi, kawai taji saukar
duka a jikinta.
Abbah magaji
ne yake zabga mata igiyar shanyarsu dama yana shigowa gidan igiyar ya tsinke ya
nad'e a hannunsa ya nufe ta da ita.
Ihunta ne ya
fito da Baba Talatu daga daki hannunta rike da carbi da hijabi a jikinta, Baba
Talatu kullum ta idar da sallahar magariba sai tayi zaman lazimi kafin a kira
sallahr isha'i sai ta tashi ta gabatar da sallahar shiyasa bata san abinda ke
faruwa ba tunda tana cikin daki su Mufidan suka shigo........Da gudu taje ta
ru'kunkume Baba Talatun tana kuka da ro'konta kan ta hana Abba magajin dukanta,
Baba Talatu ta dinga kare ta tana tambayarsa abinda tayi.
Igiyar ya
jefar yana huci yace."Baba Talatu ashe yarinyar nan rashin mutuncinta har
ya kai ta zagi Alhaji Abbas kan yayi mata abun alkairi ta zageshi gaban
'yayansa ta 'bata musu jiki da Yught saboda tana jin haushin Ubansu, hakika
banta'ba ganin butulu mai manta alkairi ba kamar wannan yarinyar."
Baba Talatu
ta koma ta zaune kan dadduma tace"Magaji yini guda yau a haka muka yini ni
kaina zagina ne kawai yarinyar nan ba tayi ba hantara da kyara kuwa babu irin
wacce ba tayi wa su Saddiqa wai jinin 'yar uwarta take wulakantawa." Baba
Talatu ta'kare maganar cikin rawar murya.
Abbah Magaji
ya kalleta tana tsaye jikin bango(garu) tana rawar jiki sai kuka take, da hannu
ya nuna ta kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa yaja tsaki ya fita a fusace!!
Cikin
nutsuwa ya d'ago kansa bayan ya gama sauraran maganar da Baba Malam din keyi
yana kokarin yin magana Baba Malam yace."Kada kace komai ko ka kawo min
wata magana, na riga na gama yanke magana mutukar ni na haifi Naja'atu to na
tsayar da ranar daurin auren ka da ita Gobe Juma'a Sadakinta kawai zaka
bani, idan yaso idan ta tare a gidanka
sai ta nuna maka 'karshen 'kiyayya."
Yace."Baba
Malam anya ba'ayi gaggawa ba kuwa wannan al'amarin yana bukatar nutsuwa ni da
kunbi ta maganar da nazo da ita da ina ganin sai amfi samun maslaha ga
junanmu."
Abba Magaji
yace."Magana fa ta kare abokina insha Allahu gobe bayan an idar da Sallahr
juma'a za'a daura auran nan sai kowa ya huta itama kuma idan taga an daura
auran duk wani iya shege da take zata daina shi kuma wannan yaro Salim sai muce
Allah ya bashi wata macan wacce zata
zame masa alkairi a rayuwarsa."
Abbah Abbas
ya jima shuru yana tunanin yanda
al'amarin ya kasance sam baiyi tsammanin zasu yanke irin wannan hukuncin ba, to
alkairi kullum yake fatan Allah ya sada shi dashi idan hakan shine alkairi yana
ro'kon Allah ya tabbatar masa dashi..
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA
#300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA
KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI
MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA
BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN
WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU
NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN
NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram
Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR
ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA
WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar
Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*12* Cikin wani mawuyacin hali Halisa ta tashi
duk jikinta yayi mata mugun tsami! ga wani irin ciwo da kanta ke mata, da kayar
ta rarrafa ta shiga dakinta ta zauna bakin gado tana ri'ke kanta, a maimakon
tayi addua kawai sai ta fashe da kuka tana fad'in mugwayen kalmomi a kan mijin nata saboda kawai yace zai yi mata
kishiya shine take addua Allah yasa ya samu karayar ariki komai nasa ya lalace!
Allah yasa ya taulace ya zama wanda bashi da cin yau bare na gobe insha Allahu
kuma Naja'atu sai ta zame masa masifa a rayuwarsa, tana kuka take wannan
surutan tamkar wata mahaukaciya, Cikin wannan yanayi suka shigo gidan shi da
yaran gabad'aya dan dubara yayi wa Baba malam yace zai tafi dasu Mussadiq
saboda zasu koma makaranta, baba malam baiji dadin haka ba dashi da Abba Magaji
sun fahimci cewar abinda Naja'atu tayi
musu ne yasa yaji sha'awar dauke yaransa.......Kai tsaye Dakinsa ya nufa yana
so ya samu nutsuwa sosai kafin ya tunkari Halisan dan ya fahimci dole sai ya
karyar da kansa mussaman yanzu da ya dauko nauyi 'yayansa ya d'ora
mata.........Mufida da Saddiqa Mussadiq suka nufi bedroom din Halisan nan suka
tarar da ita ba yanda take sai sambatun surutai take da alama dai har yanzu
mutanan nata basu gusa daga jikinta ba, Mufida taje ta zauna kusa da ita tare
da dafata tana kiran sunanta.........Saddiqa da Mussadiq a bakin kofa suka
tsaya saboda dama can sun san halin masifar Halisan ba kaunarsu take ba sai
taga Abbansu take yi musu magana da wasa da dariya, shiyasa suka kasa
'karasawa, Halisa ta juyo tana kallon 'Yarta Mufida ganin su Saddiqa a tsaye a
bakin kofa yasa ta mike tsaye a furgice tace"Ku dan Ubanku waye ya kawo ki
gidana maza ku fuce mun daga d'aki shegu tsinannu 'yayan asara."! Saddiqa
da Mussadiq suka zabura! a tsorace suka fita daga d'akin sukaje suka nemi
kujerar palo suka zauna jikinsu sai rawa yake dama can Saddiqa da Mussadiq suna
masifar tsoron Halisa Naja'atu ce take musu maganinta.......Mufida na goge
hawaye tace."Mommy ya kike zaginsu su
Yaya Saddiqa ne fa 'yan
uwana." Wani irin bahagon mari ta kifawa yarinyar tana huci!
tace"Zanci Kutumar ubanki wallahi shegiya munafuka ni zaki fad'awa su d'in
'Yan uwanki ne? Wallahi duk ranar da kika 'kara kiransu da sunan 'yan uwanki
sai naci ubanki." Mufida tana
kuka tace"To mommy me yasa kika tsanesu bayan mamansu ta mutu dan Allah ki
daina yi musu abinda kike musu babu
kyau."! A fusace! ta sake gaura mata wani mari tana wata irin fuffuka
tace"Tashi dan babanki mara mutunci ki bar min dakina ko kuma yanzu na
sumar dake." A gigice! yarinyar ta mike hannunta dafe da kuncinta ta fita
daga dakin tana kuka, wanda yayi dai-dai da fitowarsa daga daki yana sanye da
jallabiya ruwan toka, Ganinsu Saddiqa sunyi muzu-muzu a zaune yasa jikinsa yayi
sanyi ya kalli Mufida dake dafe da kunci tana kuka, yace."Menene? Cikin rawar
murya tace"Mommy ce ta mare ni tace na fito mata daga d'aki. Ba tare da
yace."Komai ba ya kama hanyar dakin Halisan, Har yanzu tana zaune gefan
gado ta had'a tagumi babu maganar sallah a tare da ita, cikin nutsuwa ya shiga
dakin bakinsa dauke da sallama, Kallonsa ma ba tayi ba ballanta ta amsa masa
sallamarsa, gefanta ya zauna yana kokarin ri'ke hannunta ta fizge a fusace! ta
mike tsaye tana nunashi da hannu tace"Kaga dan girman Allah ka fita ka
bani guri naji da abinda ke damuna baka da abinda zaka ce dani." Yaji
zafin maganarta amma sai ya danne ya mike ya iske inda take, Rungumeta yayi a
jikinsa yayi amfani da wata murya wacce ya tanade ta dan rarrashinta,
yace."Haba Halisa wai duk me yayi zafi ne kike nema ki zautar da kanki
akan abinda bai kai ya kawo ba! Menene abin damuwa dan nace zan auri Yarinyar
nan Naja'atu? idan kin kwantar da hankalinki kin ri'ke girmanki sai kinfi
daraja da kima da martaba a idona! Shin wai baki ga yanda Halimatu ta sadaukar
da rayuwata a kaina ba, bana shakka ko tantama Halimatu yanzu tana gidan
aljanna saboda ta rabu dani da iyayenta lafiya, kuma ta mutu hanyar haihuwa,
har na gama rayuwata ta duniya bazan ta'ba mantawa da Halimatu ba, a kwanakin baya kin soma kwaiwayon hali da
d'abi'unta amma tashi guda zaki watsar da abin da kika fara na alkairi, wallahi
auran Naja'atu da zanyi ba zai sanya ni na daina kaunarki ba, kin san dai kece
macen dana fara furtawa kalmar so, ko Halimatu ma kece kika jawo na aureta, to
itama Naja'atun ina so ki sani bani ne nace inaso ta zama *Madadin 'Yar uwarta
ba* Iyayenta ne suka nemi haka dan ko yanzu sai da na fada musu cewar maganar auran su barta suka nuna sai
anyi So inaso ki kwantar da hankali ki
samu nutsuwa ki kula dani da yarana gasu nan na kawo miki su ni kuma insha
Allahu zan baki mamaki zan nuna miki ni d'an halak ne auran Naja'atu ba zai sa
na juya miki baya ba." Shuru
tayi jikinta duk yayi sanyi da kalamansa tace"Nifa ban hanaka aure ba
wallahi ko budurwar zaka aura to kaje ka aura amma banda yarinyar nan bana
kaunarta saboda bata ganin girmana." Yace."Na fad'a miki fa cewa kece
uwargidana duk ragamar mu tana hannuki har ita Naja"atun idan tazo a
'karkashin ki take sai abinda kika tsara a gidan shi za'ayi." Jin wannan
maganar tasa yasa ta sauke ajiyar zuciya tace"Nifa wallahi nasan dadin
baki ne kake mun yarinyar nan na zuwa
zaka manta dani, dan haka gwara tun kafin tazo na san inda dare yayi min dan
bana tunanin zan zauna da ita a karkashin inuwa guda." Yace."In banda
abinki ba gidanku daya ba to me zai dame ki da ita ko wacce na gidanta idan
wannan da kike ciki bai miki ba sai na sauya miki wani." Tsaki taja
tace." bazan yarda ba wallahi sai dai ka had'amu gida daya dan bazan
amince a cutar dani ba." Yace."To shikkenan duk abinda kike so shi
za'ayi, Zan sa a gyara miki side d'inki dake gidana na *'Danbare* ina fata
hakan yayi miki." shuru tayi tana zum'bura baki, Ya saketa yaja hannunta
suka zauna a nutse yace."Ki fad'a mun duk abinda kike so na siya miki na
fad'ar kishiya komai tsadarsa zan siya miki." Tace"Sai nayi shawara tukkuna."
Dariya ta bashi amma beyi ba yace."To shikkenan inaso na baki kudi kije ki
had'o mata lefe kuma kema ki had'a naki
hakan yayi miki." Dadi ne ya rufe ta tace"To Hakan yayi amma
inaso ka sanja min mota." Yace."An gama ranki ya d'ade! amma dan Allah
daga yau sai yau kada ki sake aikata abinda kika aikata a d'azu! rashin hankali
ne kawai kije ki dauko wu'ka kina so ki kashe ni! kina tare da shed'an a
lokacin idan da tsautsayi sai ki aikata aikin dana sani ki 'kare rayuwarki
cikin uku'ba kuma ki mayar min da yara marayu." Hanci ta sha'ka! cikin
takaici tace"Haba ai wallahi idan ma nayi maka rauni ban huce bacin raina
ba, kana kallonta ina magana ka tsalleke ni ka tafi ai dole zuciya ta ta
tunzurani a kanka." Yace."Tom yanzu dai duk magana ta wuce Gobe insha
Allahu bayan sakkowar sallahr juma'a za'a daura auran amma ina tunanin ba zata
tare ba sai nan da sati biyu." Halisa gabanta ya fad'i tace"Da wuri
za'a daura auran ashe."? Yace."Baba Malam ne ya yanke hukuncin
haka." Cikin tsabar bakin ciki da takaici tace"Aikin banza aikin hofi
'kwad'ayayyen tsoho mai son abin duniya ai dama dole ya gaggauta yin abun kodan
bukatarsa ta biya." 'Bata rai yayi yace."To yanzu zamu 'bata dake
kuma bana son wannan d'abi'ar taki ta zage-zage da rashin ganin girman manya." Cikin fusata! ta mike ta nufi toilet tana
surutai da 'kananun maganganu, kallo ya bita dashi, Al'amarin Halisa dai sai gyaran Allah, yaji dadi sosai da ya shawo kanta
cikin ruwan sanyi *(Tabbas haka maza ya kamata su dinga rarrashin matansu idan
zasu 'kara aure, sau tari wasu mazan
sune suke ingiza zuciyoyin matansu ga aikata abinda ba shikkenan ba, idan ya
kasance zaka 'kara aure to yana da kyau ka dinga nuna kulawarka a kan matarka
ta gida, kuma banda kiran wayar amarya a cikin gidan dan hakan ma na iya janyo
muku samun sa'bani a tsakaninku*) Mikewa yayi ya fita daga dakin yana dan jin
sassauci a cikin zuciyarsa tunda ya gama da matsalar Halisa yana ganin duk abinda zai biyo baya mai sauki
ne.
Yana fitowa palon ya gansu a zaune duk sunyi
tsuru-tsuru Mussadiq ma gyangyadi yake, Ya kalli Saddiqa data had'a tagumi
hannu bibbiyu har yanzu zuciyarta na jin ciwon abinda Naja'atu tayi musu a
d'azu duk da take yarinya wacce bata gama mallakar hankalin kanta ba ta gane ba
'karamar 'kiyayya Naja'atu keyi wa Abbansu ba, sai ta dinga tunanin to wai meye
aibunsa da har zata dinga 'kinsa da kuma zaginsa, sam bata ta'ba tsammanin haka
daga gareta ba...... a nutse yace."Saddiqa kuje ku kwanta kinji ko,
dukkaninku ku daina damuwa ku saki jikinku a gidan nan gidanku insha Allah ba
zaku samu wata matsala ba." Saddiqa murya na rawa tace"To
Abbah." Ya sunkuya yana d'an tashin Mussidiq ya tashi yana mutsika ido,
ganin Abbansa yasa ya bude idonsa sosai, Abba Abbas d'in ya rike hannunsa ya
mike tsaye.........Shi da kansa ya rakasu d'akin dama gado uku ne mai dauke da madaidaiciyar
katifa da pillo da bargo, Mufida ta gyara nata ta kwanta, Abbah Abbas da kansa
ya shimfidawa Saddiqa da Mussadiq sabon bedshirt ya gyara musu sosai sannan suka
kwanta, Ya tsaya kansu yayi musu addua sosai kana ya fita daga dakin tare da
kulle musu kofa.............To bayan barin Abbah Abbas daga gurin Malam Baba
shima Abbah Magaji sallama yayi masa kancewar kafin ya shiga gidansa zai tsaya
ya siyi dik abinda za'a bukata gurin daurin auran, Malam yaji dadin hakan
yace."Dashi kafin ya tafi ya shiga gidan Alhaji domin ya sheda masa abinda
ke faruwa, koda Alhaji yaji bayanin da Abbah Magaji yayi masa sai ranshi ya
'baci! ya za'ayi sun riga sun gama magana da Abbah Abbas din kan cewar ya janye
maganar auran yarinyar kuma dan yaga baya gurin zai sauya magana, yaji haushin
hakan ya dauki laifi kacokan ya d'orashi kan Abbah Abbas d'in, Dan 'kin tsayawa
ma yayi ya saurari bayanin da Abbah Magaji ke masa, ya sauko daga samansa, kai
tsaye futa yayi daga gidan, Abbah Magaji na binsa a baya........Malam Baba yayi
mamakin fusatar Alhajin kasancewar yasan shi d'in mutum ne mai saurin fahintar
abu da kuma sau'ka'kawa cikin ko wane al'amari.......Da 'kyar Baba Malam da
Abbah Magaji suka fahimtar dashi ya gane cewar ba laifin Abbas din bane sune
suka tursashi......Alhaji Sama'ila yayi shuru yana ta nazarin al'amarin, daga
bisani kuma addua yayi da fatan alkairi tabbas tunda Allah yayi haka to babu
alkairi a cikin auran Naja'atu da Salim d'in,......Shine ya sake 'karfafawa
Abbah Magaji, cewar yayi 'kokarin tana dar duk abinda ake bukata a gurin daurin
aure tabbas babu makawa gobe auran Naja'atu da Abbas sai ya d'auru.........Sai
misalin goma da rabi sukayi sallama da juna kowanne ya shiga gidansa cikin
fatan alkairi ga junansu.........Baba Malam kafin ya kwanta sai da ya sanar da Baba Talatu abinda ake ciki na irin
hukuncin da suka yanke cewar Za'a daura aure gobe dan jan lokacin bashi da
amfani, Baba Talatu taji dad'in hakan sosai kuma tayi fatan alkairi dangane da
al'amarin.....Naja'atu dake takure kan shimfidarta a lokan rumfar luf!! tayi
kamar mai bacci tana sauraran maganganunsu, sai da taga sun shiga daki, da
niyar kwanciya sannan ta mike a hankali ta dauki wayarta dake kusa da ita ta mike ta fita daga
dakin ........Daya dakin ta nufa tana shararar da hawaye, xaman 'yan bori tayi
tana toshe bakinta domin kada sautin kukan da take ya fita suji, wayar ta kunna
hannunta na kyarma ta shiga laluben numbar Abbah Abbas d'in, tana jin idan bata
zageshi ba zuciyarta na iya bugawa.........Yana zaune a palo shi kadai da
Loptop a gabansa yana duba sa'konnin abokan kasuwancinsa na 'kasashen waje,
Kiran wayar ta ya shigo wayarsa dan duban wayar yake hankalinsa na kan typing
din da yake cikin loptol din, koda yaga
numbar Naja'atun baiyi gaggawar dauka ba,
ya janye idonsa ya cigaba da abinda yake Naja'atu! ta dingi kiran wayar
tamkar zata kashe masa dodon kunne dole ba yanda ya iya ya daga wayar tare da
gyaran murya babu wasa a cikin muryarsa yayi sallama....
'Dif! tayi
gabanta na wata irin fad'uwa! sakamakon jin sautin muryarsa mai cike da
kwarjini da rashin wasa yasa ta mance abinda yasa ta kiransa a wayar sai mazari jikinta yake tana sha'kar hanci
had'e da sauke ajiyar zuciya irin na wanda yaci kuka ya 'koshi........'Dan
gyaran murya yayi a karo na biyu yace."Dota ya akayi ne dare yayi baki
bacci ba."......Murya na rawa tace"Me yasa ka san ni 'yar kace kake
shirin aurena."? Shuru yayi yana nazarin maganarta, Yace."Eh abinda
yasa nake kiran ki da Wannan suna (Dota) saboda nasan a matsayin shekaruna da
Allah ya bani haihuwa da wuri dana haife ki kamar ki ko wacce ta fiki so ina
ganin babu laifi dan na kira ki da wannan suna."!A hasale! tace." To
tunda dai da bakin ka ka fad'a cewa a matsayin shekarunka da Allah ya baka
haihuwa zaka iya haifeta ko wacce ta fini me zai sanya ka zubar da k'ima da
mutunka a gurina ni da ka 'rike kamar 'yar cikin ka, ka sani ba da badan mutuwa
ta ratsa tsakanin ka da matarka ba da
kowa yana maka kallon matsayin uba a gare ni." Murmushi yayi wanda har sai da taji sautinsa a kunanta
Yace."Nifa ban haife ki ba ki daina kirana Ubanki yanzu sunan da yafi
kamata ki kirani dashi shine Mijin ki dan gobe idan Allah ya kaimu iwar haka
kin zama matata"! Taji tamkar ta d'ura masa ashar! sai dai ta daure taja
wani matsiyacin tsaki! mai 'karfi! da
fad'in "Amma dai anji kunya wallahi."!! Kit! ta kashe wayar tana wani
irin huci!!! Abbah Abbas ya dinga bin wayar da kallon mamaki! Yau shi yarinyar
nan take jawa tsaki har tana kokarin zaginsa, Kasa hakura yayi ya sake kiran
wayar! A fusace! ta d'aga ta bud'e baki za tayi magana, ya buga mata wata
masifaffiyar tsawa! da fad'in " Dan Ubanki ni kike zagi ashe baki da
mutunci dama."!? Jikinta ya shiga karkarwa domin tsawar da ya buga mata
bata ta'ba saninsa da ita ba, kashe wayar tayi gabad'aya ta kwanta tare da
takure jikinta tana kuka mai tsuma zuciya, ta kirasa a waya domin ta farfad'a
masa magana mai zafi 'karshe shi ya fad'a mata maganar data ya mutsa mata
tunani har da zagin Ubanta..........Abbah Abbas ya ajiye wayarsa a fusace! ya
rufe loptop din ya mike ya nufi bedroom d'in Halisa........... *Sorry kuyi
hakuri waya ta ta d'an samu matsala wallahi zaku ga yanayin typing din ba irin
yanda na sababa........Ina ro'kon Ubangiji Allah ya kawo mana zaman lafiya a
wannan 'kasa tamu ta Najeria Ubangiji Allah ka bamu nutsuwa da daidaito a
tsakaninmu amin.........MY FANS KADA MU MANTA DA SALATIN ANNABI A WANNAN RANA
MAI ALBARKA SANNAN KUMA MU DAURE MU KARANTA ABINDA YA SAWWA'KA DAGA CIKIN
SURATUL KHAFI.*
*************************GA
MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #400
SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA
KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI
MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA BIYAN
KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA
MAGANA TA WHASAP
*MUTANAN MU
NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN
NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram
Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR
ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA
WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar
Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*13*
Ranshi a
'bace! ya aje loptop din kan wani tevur ya nufi toilet alwala ya daura ya fito
ya hau kan dadduma ya tayar da sallahr nafila, raka biyu yayi ya daga hannunsa
sama yana rokan Allah ya za'ba masa abinda yafi alkairi a rayuwarsa,
kwata-kwata ji yayi auran yarinyar ya fice masa daga rai! a sabili da irin
iskancin da wulakancin da take masa da shida 'ya'yansa bai ta'ba tsammin
faruwar hakan daga gurinta ba yana ganin barin auranta kamar shi yafi alkairi
don baya so da girmansa da komai yarinya k'arama tazo tana fada masa maganar da
duk ta gadama, mikewa yayi daga kan dadduma yaje ya kwanta kusa da Halisa, ya
d'an janyo ta jikinsa,
Bude idonta
tayi ta wani fizge jikinta tana jan tsaki! Al'amarin sai ya bashi mamaki! ganin
cewar d'azu suka gama magana da ita kan cewar komai ya wuce amma saboda ya
ra'bi jikinta tana fizgewa, bai yi zuciya ba ya sake kai hannu zai janyota ta
mike zaune tana 'bata fuska tace"Nifa ba zan sake amincewa da bukatarka ba
sai na yankewa kaina hukunci tukkuna dan gaskiya ni maganganunka na dazu basu
shige ni ba."
Ya mike
zaune yana kallonta cikin d'umbin mamaki! yace." Wane irin hukunci zaki
yankewa kanki bayan wanda muka yanke d'azu na dauka yanzu dani dake mun zama
d'aya, ashe duk maganar da mukayi dake dazu ta banza ce." Tace."Kawai
ka rabu dani na cigaba da tunanin mafita ni ba zan sake amincewa bukatarka ba
kaje idan an daura auranka da 'karamar yarinya sai ka sauke bukatarka a
kanta." Cikin tsabar takaici yace."Halisa ban ta'ba ganin mara
hankalin mace irin ki ba wallahi kin girma amma har yanzu kin 'ki hankali 'Yar
cikin ki Mufida ta fiki nutsuwa."
Tace."Duk
dai abinda za kace a kaina kace ba zan
amince da kai ba wallahi sai yarinyar nan ta shigo gidanka naga irin zaman da
zakayi da ita."
Murmushi
takaici yayi cikin sigar 'kuntatawa yace."Zanyi zama da ita irin na
ma'aurata kuma ba zaki hana ni na ji
dad'ina da ita ba." A fusace! taja tsaki! da fad'in "Kana tare da
kunya kuwa duk ranar da 'yayanka su kaga ka kwana a d'akin wacce suka d'auka a
matsayin yaya a gurinsu, sai ka tanadi abinda zaka fada musu."
Girgiza
kansa kawai yayi ya dauki rigarsa yasa a jikinsa ya sauka daga bed din hanyar
fita ya nufa jiri naso ya kayar dashi, gabad'aya ji yayi duniyar tayi masa zafi
ko ina babu sassauci tabbas sai yanzu ne zai fara kukan rashin matarsa da yayi,
a da baiyi kukan rashin Halimatu ba sai yanzu da Halisa da Naja'atu suke gwara
kansa a bango....
'Bangaran
Naja'atu kuwa yanda taga rana haka taga
dare daga zarar ta tuna da cewar gobe za'a daura mata aure da Abba Abbas din
sai gabanta ya fad'i ta hau takure jikinta, ta jima tana sa'kawa da kwancewa da tunanin mafita a gareta, tana so gari ya
waye ta kira Salim a waya ta sheda masa hukuncin data yanke.......Aikuwa tana
idar da Sallahr asubahi ta shiga kiran wayar Salim din inda akaci sa'a yau
ya tashi da wuri, ya dauki wayar cikin
mayaudariyar miryarsa yace.."My Princess kin tashi lafiya."? Murya a
'kasa tace"Lafiya kalau my prince." Ya wani narke murya irin yanda
yake mata yana kashe mata jiki yace."My Prince jiya kwana nayi da tunanin
ki da begen ki har mafarki nayi dake muna kwance a gado d'aya kina bani
kulawa."
Ta rintse
idonta hawaye na zuba tace."My Prince Abba Abbas naso ya yanke mana jin
dad'inmu bana tunanin zan iya mallakawa wani da namiji kaina sai kai! bana
sha'awar kowa sai kai soyayyar ka kawai nake muradi! amma ina tunanin mafarkina
dakai ba zai tabbata dan ganin yanda magauta suke 'kokarin kassara mana
rayuwarmu." Mikewa zaune yayi yace."My princess ki fad'a mun yanzu a
wace matsaya aka tsaya dangane da maganar auranki da Abbah Abbas din.
Tace."Komai
yazo karshe My Prince jiya da daddare Baba Malam naji yana fad'awa Baba Talatu cewa gobe bayan
sallahr juma'a za'a daura aurena dashi, wannan dalilin yasa na yanke hukuncin
guduwa daga garin gabadaya su neme ni su rasa."
Salim ya
shiga goge gumi ma'kogwaronsa ya bushe sosai, yace."Innalilihi wa'ina
ilahi raji'un! abinda ya iya fad'a kenan, murya na rawa yace."My bani da
kuzarin yin magana yanzu saboda na shiga rud'u da tashin hankali jin wannan
maganar taki, zan kira ki anjima kafin nan nayi nazari kan hukuncin da kika
yanke."
Kashe wayar
yayi ya zauna yana tunani.......Ashe dai
dattijon nan da gaske yake sai ya dasa masa 'kunci da ba'kin ciki! to
kuwa in dai ya kasance cewar ya samu
nasara a kansa gurin auran Naja'atu to shi kuma zaiyi amfani da damar sa, a
gurin ita Naja'atu duk wani abunda yake
bukata a gurin yarinyar ba zai same shi ba sai ta zame masa mafisa wanda da
kansa zai gaji ya saketa, koda ya saketa
shi ba auranta zaiyi ba yana so ya kawai ya dasa masa 'kunci da 'bacin rai
kamar yanda ya dasa masa a zuciyarsa.
Mikewa yayi
ya shiga cikin gidan...Yaya Ramlatu na kicin tana kokarin kunna wuta, taga
shigewar d'an nata, sai da ta kunna wutar ta d'ora ruwan kunu kan murhun,
sannan ta bi bayansa, koda ta shiga dakin gani tayi ya takure kansa hade da
dafe kansa, Kafin ma tayi magana taga yana hawaye.
Tace."Salim
lafiya me yake faruwa."? Cikin tsabar bakin ciki yace."Yaya 'Dan
uwanki bashi da kirki ya kasance mutum mai son kansa, ya cuce ni ya cutar da
rayuwata kuma ya yaudare ni da yasa na amince masa na daukeshi a matsayin uba
ya ha'ince ni, yarinyar dana 'kwallafa raina a kanta yau xa'a daura masa aure
da ita, ba zan ta'ba mantawa da wannan mutumin ba."
Yaya Ramlatu
ta dinga mamakin maganar tace."Kai waye ya fad'a maka yau za'a daura
auransa da Naja'atu da har kake wannan maganar......A fusace! yace."Ita
yarinyar ce ta fad'a min yanzu ta kirani a waya tana kuka tare da sheda min
hukuncin data yanke kancewar zata gudu daga garin gabadaya."
Shuru Yaya
Ramlatu tayi takaici da bakin ciki kamar ya kasheta, lallai Abbas bai da
alkawari kamar dai yanda Salim din ya fada hakane Abbas yafi son kansa akan
kowa bai duba soyayyar dake tsakanin Salim d'in da Naja'atun ba sai da ya shiga
ya fita ya raba tsakaninsu......Tace."To shikkenan sai ka hakura ka
fawwala wa Allah tunda Allah yasa ya samu nasara a kanka, maganar Naja'atu zata gudu ta bar gari bata taso ba
dan idan hakan ya kasance to kowa zai d'ora zarginsa a kanka, dan haka kace
mata baka amince ba, dan bana son abinda zai janyo min 'bacin ran
iyayena."
Yace."Idan
ya kasance Naja'atu ta tare gidan Kawu Abbas wallahi tallahi nayi al'kawari sai
na 'kunsa masa ba'kin ciki da takaici kamar yanda ya 'kunsa min, tunda dai Naja'atu ni take so ai magana ta
'kare zuciyarta tana hannuna shi kuma yana tare da gangar jikinta."
Yaya Ramlatu
tace"Duk wani iya shege da rashin arziki da zaka yi masa ban hanaka ba,
kaje kayi domin shima yaji idan da dad'i abinda yayi maka d'aurin aure suje
suyi babu inda zanje." Yace."To dama me zaki je kiyi a gidan
gabad'aya ma da Alhajin da ita Hajiyan basa kaunarki da suna kaunar ki ba zasu
bari haka ya faru ba, sunfi kaunar Kawu
Abbas d'in saboda yana da kud'i." Yaya Ramlatu ta dinga girgiza kanta
takaicin da ba'kin ciki dik ya cika mata zuciya.
Da asubah da
kafin ya tafi massalaci sai da ya shiga ya tashi yaransa domin suyi sallah,
koda ya fito daga dakin nasu bai ko kalli dakin Halisa ba dan har yanzu
haushinta yake ji yana ganin duk wani kokari da ya kamata yayi a kanta yayi zai
dauke mata wuta gabad'aya dan ba zai cigaba da rarrashinta taba tana masa
iskancin da taga dama.
Bayan ya
dawo daga massalaci ya koma dakin nasu
nan ya tarar dasu sunyi sallah suna zaune Saddiqa da Mufida suna magana,
dukkaninsu suka shiga gaishe shi ya dinga amsawa cikin nutsuwa da kulawa, ya kalli Saddiqa a nutse yace." Saddiqa
ki shiga kicin ki dafa muku tea da abinda kike ganin zaki iya."
Tace."To Abbah." Mikewa tayi tana kokarin cire hijab d'inta shi kuma
ya fita daga d'akin, Kai tsaye d'akin Halisa ya nufa domin ya dauki loptop
dinsa.
Tana kwance
kan bed din ta tsirawa rufin dakin ido, da alama ma ba tayi sallah ba, Ko
kallon inda take baiyi ba ya dauki loptop dinshi ya kama hanya ya fita daga
dakin, Halisa tabi bayansa da kallon ba'kin ciki tamkar ya tarwatsa mata
zuciyarta..............Saddiqa na tsaka da aiki a kicin taji an buga mata uwar
tsawa! "Ke dan Ubanki waye ya baki dama ki shigo min kicin."!? Jiki na rawa tace." Abbah ne yace na
dafa mana tea da indomee." Da hannu
ta nuna mata 'kofar fita da fad'in "Fice ki bar min kicin 'yar iska
munafuka masu gadon mugun abu." Saddiqa hawaye ne suka tawo mata, tayi
saurin mayar dasu tana kokarin fita daga kicin din Halisa ta kai mata
ran'kwashi a kanta tana zaginta. Da sauri ta 'karasa ficewa daga kicin din
hawayen da take ta kokarin mayarwa suka zubo.......Ganin yarinyar ta fito a
firgice yasa ya kalleta yana tambayar ta menene."? Tana share hawaye
tace"Babu komai." Tsawa yayi mata da fad'in "Ba zaki fad'a min menene
ba."? Tace." Anti ce tace na fice mata daga kicin."
Yace."Zoki zauna anan." Kusa dashi ya nuna mata, taje ta zauna tana
goge fuska, cikin tausasawa yace."Kiyi hakuri ki daina kuka kinji
ko." 'Daga kanta tayi tana goge hawaye, laptop din dake cinyarsa ya ajiye
kan kujera ya mike ya nufi kicin din, Halisa na tsaye tana feraye doya ya shiga ya sameta......Babu
walwala a tare dashi yace."Me yasa kika hana Saddiqa ta had'a musu abun
kari."?
Juyowa tayi
dan ba tasan ya shigo kicin din ba, ganin fuskarsa a murtuke yasa itama ta
murtuke tata fuskar tace"Ai sai ka tsaya ka gani idan nayi ban basu ba sai
ka bata umarnin tayi musu meye wani zaka ce ta shigo min kicin."!! Girgiza
kansa yayi bai ce mata komai ba ya juya ya fita daga kicin d'in, sam bai dauka
Halisa za tayi abinci ta bawa yaran ba dan ganin irin rigamar da sukayi ita
dashi jiya shiyasa ya umarci Saddiqan ta shiga kicin domin ta samar musu da
abinda zasu ci........Suna zaune shida yaran Yaya Ramlatu tayi sallama ta
shigo, turus tayi ganinsa zaune a palon, shima cike da mamaki yake binta da
kallo, har ta'karaso ta zauna kan kujerar dake fuskantarsa, Yaran ne suka shiga
gaisheta ta dinga amsawa tana washe bakinta.
Cikin
nutsuwa ya gaisheta ta amsa tana ta dariya kamar wacce ta shigo gidan da abin
arziki, Tace."'Dazu Salim yake sheda min cewar anjima wai za'a daura
auranka da Naja'atu hakane ko." ? Yace."Eh insha Allah bayan an sakko
daga sallahr za'a daura anan massalacin jikin gidan Alhaji."
Tace."Allah
ya sanya alkairi yasa haka shi yafi alkairi, amma banji dadi ba da baka fad'a
min ko a waya ba sannan daga can gidan Alhajin ma babu wanda aka turo domin ya
fad'a mun sam ba'a daukeni a bakin komai ba, ace maganar daurin auren ma sai a
bakin Yarinyar mukaji dan da asussuba ta kira Salim tana kuka tana fad'a masa
cewar za'a daura auran kuma idan an d'aura to zata gudu ta bar gari a neme ta a
rasa, wannan maganar ta tayar min da hankali sosai saboda nasan yarinyar nan ta
gudu to da kai da Salim zaku shiga cikin masifa, dalilin da yasa na umarci Salim din maza ya kira ta a
waya sheda mata cewar bai amince da 'kudirin data dauka ba, Kuma nace ya fad'a
mata cewar shi tuni ya cire ta a zuciyarsa, dan haka ta daina tunanin guduwa a
kansa ta zauna a gidan mijinta tayi zaman
aure mai tsafta."
Abbah Abbas
ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Yaya Ramlatun yace."Dukkanin abinda ki
kaga yana faruwa to dama can haka Allah ya 'kaddara zai faru, ko a mafarki ban ta'ba tsammanin wai zan auri
yarinyar nan ba, sai dai kuma babu yanda Allah baya tsara al'amarinsa, mutuwar
Halimatu ta janyo min sha'awar auran yarinyar domin ina ganin yarinyar tarbiyar
tace kuma zata zame min *MADADIN TA* ta gurin kyawawan halaye da sauransu, sai
dai kuma ashe ba haka al'amarin yake ba ,
Allah shine ya hallici Halimatu ya kuma Hallice Naja'atu a bigire d'aya,
sai kuma ya bambamta musu halaye, Halin
Halimatu daban Halin Naja'at daban, A
jiya mun zauna da Alhaji mun tattauna magana kan cewa na janye bukatata tasan
auran yarinyar, zan kuma shige gaba gurin ganin Salim ya mallaketa, a lokacin
da naje wa da Baba Malam da maganar shi kuma ya nuna bai amince ba, yace
yarinyarsa bata da miji sai ni saboda ni yayi ra'ayin bawa auran 'yarsa, dik
yanda naso na fahimtar dashi ya kasa fahimta, haka nayi musu sallama na dawo
gida ina fatan Allah yasa hakan shine alkairi a gare mu baki d'aya."
*GA MASU
BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #300 SINGLE,
VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA
ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI
TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN
SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO
KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU
NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN
NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram
Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR
ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA
WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar
Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*14*
Yaya Ramlatu zagin Baba malam kawai take a
cikin zuciyarta amma a Zahiri dariyar
ya'ke tayi tace"To ai shikkenan ni a gurina da kai da Salim din duk
d'aya ne, kuma na zaunar dashi nace masa ya cire yarinyar daga cikin ransa
gabadaya domin kai ba tsaransa bane ballanta ya had'a neman aure da
kai."" Abba Abbas yayi murmushi yace."Kwana biyu ma bana
ganinshi a kasuwa ko kiransa nayi a waya baya d'auka nasan duk akan
hakane." Tace."Ai yanzu komai ya wuce na nuna masa dama can kai kafi
cancanta daka auri yarinyar." Murmushi yayi yana girgiza kansa, gaskiya
bai tsammaci zai zauna da Yaya Ramlatu haka suyi magana ta fahimta ba yaji dadi sosai da sosai data fahimce shi.
Yaya Ramlatu
a gidan ta karya kummalo suka shiga daki ita da Halisa, suna 'kulle-'kullensu, Halisa
ta fad'a mata duk yanda sukayi da mijin nata da maganar zai bata kudi ta had'o
lefe kuma zai sanja mata mota bayan haka kuma yace ta fadi duk abinda take so
zai bata kudi ta siya.....Jin haka yasa Yaya Ramlatu tace"Kinga aikin
malam ya fara yi ko ai dama na fad'a miki sai Abbas ya dawo tafin hannunki sai
yazo yana miki rawar jiki, dan haka ki daina d'aga hankalin ki kan auransa da
yarinyar nan nasan idan muka ri'ke Malam mai al'mutsutsai! a hannunmu to
bukatar mu zata biya dama kuma babban
burin ki shine ki mallaki Abbas a hannu ina ganin nan da 'kan'kanin lokaci zaki
mallake shi da duk wani abu nashi tunda har ya bud'e bakinsa yace miki dashi da
duk wani wanda yake 'kar'karshinsa a 'kasan ki suke to kinga kuwa ai sai ki
godewa Allah ki sake tanadar kudi masu kauri domin tukwici ga malam bisa ga
aikin alherin da yayi miki." Halisa tace."Nifa Yaya Ramlatu sai nake
gani kamar dan zai yi aura ne yasa yake kwantar da kansa ba wai asiri ne yayi
tasiri a kansa ba, ki duba fa ki gani tsayin shekaru nawa muka dauka muna yawan
bin malam tun Halimatu na raye asiri baya tasiri a jikinsa, sai yanzu."
Yaya Ramlatu
ta 'bara rai tace"Kada ki sake wannan maganar, wato duk kokarin da nake
miki bakya gani sai kin 'karya ta ni! kin 'karya ta aikin malam to babu ruwana wallahi
idan kika lalata a aikinki, kada ki sake cewa na taimaka miki, inaso ki sani ko
wane malami da irin kalar aikinsa, wani da ruhainai yake aiki wani kuwa da
turawan aljanu yake aiki wani kuwa da ba'ka'ken aljanu yake aikinsa, to shi mai
al'mutsutsai da ba'kaken aljanu yake aikinsa,
idan kin san ba'kar wuyar da muka sha nida 'Yar shagamu kafin mu je
zauren malam d'in sai kin tausaya mana, amma
kin samu aiki yayi shine kike 'karyata wa to wallahi babu ruwana."
Halisa ganin
ran Yaya Ramlatu ya 'baci sai ta shiga bata hakuri tace"Ba wai ina
karyatawa bane nasan kina kokarina akaina kiyi hakuri dan Allah." Yaya
Ramlatu tace"Koda can ma ba wai asirin ne baya tasiri a jikinsa ba yana
tasiri sai dai yana saurin karyewa ne saboda yawan addua da zama da alwala
dashi mijin naki yake, amma nasan wannan aikin da akayi masa zai dade kafin ya
bar jikinsa."
Halisa ta
sauke ajiyar zuciya da fad'in "To shikkenan insha Allahu zanyi kokarin
ganin na kauda duk wani abu dake raina dangane da auran, ammafa nace ban yarda
ya raba mana gida ba dan ina ganin kamar za'a cutar dani, sannan kuma wa 'yan
nan 'ya'yan nasa daya kawo min sam bana son ganinsu wallahi."
Yaya Ramlatu
tace"Eh kina da gaskiya gwara ya had'aku a gida d'aya duk da nasan ba wani
d'okin auran yarinyar yake ba amma
hausawa nace wa amarya ko mahaukaciya ce dole ayi d'okinta, dan haka tana
tarewa ya kwashe yara ya kai mata dama ai saboda ta zama *Madadin* Uwarsu ya
aureta."
Halisa
tace"Yace idan an d'aura auran sai bayan sati biyu zata tare." Yaya
Ramlatu tayi shuru tana nazarin maganar tace"To shikkenan sai ki hakura ki
ri'kesu kafin lokacin amma ban amince ki zalince su ba tunda basu ne sukayi
miki laifi ba." Cike da mamaki Halisa ke kallon Yaya Ramlatun wato idan ta
fahimta tana so ta nuna mata cewar ita tana 'kaunar 'ya'yan d'an uwanta,
Halimatu da Naja'atu ne bata kauna! To idan hakane kuwa 'kiyayyar da take musu
ba takai har zuciyarta ba tunda ba zata bari a zalinci jininsu ba.
To Duk
abinda Allah ya tsara ya hukunta sai ya kasance dama haka al'amarin yake mutum
baya ta'ba tsarawa kansa rayuwa sai irin wacce Allah ya tsara masa, Abba Abbas
da Naja'atu ko a mafarki basu ta'ba tsammanin zasu zauna a inuwar ma'aurata ba,
sai gashi Ubangiji ya zartar da ikonsa a kansu, Sai gashi a yau jama'a masu yawa suka sheda daurin auransu,
kowa sai fatan alkairi yake gami da fatan zaman lafiya, Alhaji Sama'ila da Baba
Malam da Abba Magaji bakin su ya'ki rufuwa sai gaisawa suke da jama'a Abba
Magaji na raba goro da alawa fuskarsa tamkar gonar audiga........Shi kuwa ango
fuskarsa kadaran kadahan yana ta mi'kawa abokanshi hannu suna gaisawa suna taya
shi murna da fatan alkairi yana amsawa fuska d'auke da murmushi.
Cikin gida
kuwa, Naja'atu kasa gane kanta
akayi ta rufe d'aki! da sakata, sai kuka
take tana kiran mutuwa tazo ta dauketa, Baba Talatu da 'yan uwanta da suka cika
gidan hankalinsu ya tashi suka dinga buga 'kofa suna kiran sunanta, tana jinsu
tayi shuru sai ihu! take tana birgima 'kasan d'akin.
Baba Talatu
ta fashe da kuka tana fad'in "Wannan yarinya tana so ta jawo min abin
kunya a idon jama'a innalilihi wa'ina ilahi raji'un! Daki ta shiga ta zauna gefan gado tana share
hawaye babu shakka Naja'atu ta fita zakka a cikin 'yayanta.......Abba Magaji ne
ya shigo gidan ya gansu tsaye a kofar d'akin! Gashi sai gunjin kukan Naja'atun
yake ji daga cikin d'akin, Ya karasa gurin da sauri yana tambayar
ba'asi.........Baba Larai wacce ta kasance Yaya ga Baba Talatu itace tayi masa
bayani duk abinda ke faruwa, Ya shiga
bubbuga kofar yana kiran sunanta, tana jinsa taki kulashi.
Cikin
rarrashi yace." Naja'atu bude kofa kinji ko duk kinsa hankalinmu ya tashi
yi hakuri ki bude kofar zanyi magana dake.......Cikin dashashshiyar murya
tace"Sai dai ku dau'ko gawa ta amma wallahi bazan bud'e 'kofar nan
ba."
Abba Magaji
ya kalli kofar 'kofa ce irin tada mai k'wari tabbas jijjige ta aikine babba
amma yana ganin hakan shine mafita, yana kokarin fita Baba malam na kokarin
shigowa ganinsa a fujajan! yasa ya tsaya tambayarsa, Baba malam ransa ya 'baci
sosai babu shakka Naja'atu ta shirya tsaf! domin ta tozarta shi a cikin unguwa,
nan ya umarci Abbah magajin ya samo matasa majiya karfi suzo su jijjige
'kofar......Gidan ya shiga ya tarar da jama'a sai surutai suke kowa na fad'in
albarkacin bakinsa, har da masu cewa
dama a warware auran tunda yarinyar bata so.......Baba malam ya tsaya a
bakin tagar dakin ya daga labule yana le'kanta da kiran sunanta, duk da tasan
shine bai sa ta amsa masa ba, juya baya tayi ta cigaba da
kukanta...........Abba Abbas na tare da Dan uwanshi a bakin gate din gidan alhaji
suna magana, kawai yaga abokin nashi tare da zaratan maza majiya 'karfi harda
Salim a ciki zasu shiga gidan Malam......Ya bisu da kallo cikin mamaki! Jikinsa
ya bashi da akwai abinda ke faruwa..............Sai da suka fara sassa'ke
'kasan 'kofar da (diga) sannan suka sanya mata karfi! aikuwa a take suka cire
ta.........Mi'kewa tayi tsaye! cikin firgici! tana rarraba idonta a kansu,
ganin sun shigo dakin har Baba Malam d'in yasa ta takure jikinta a bango tana
rawar jiki, Abba Magaji ya nufe ta a zafafe! da alama jibgarta zaiyi Baba Malam
ya hanashi, a fusace ya bar dakin, su kuwa jama'a 'yan zuwa taya murna sai
fad'ar albarkacin bakinsu suke a kanta........Baba Malam yace."Magana dai
duk ta 'kare kowa yaje ya cigaba da sabgarsa aure tunda an daura babu zancan a
warware shi.
Dakin ne
yayi shuru na tsayin minti biyar kafin yayi gyaran murya a nutse ya kira
sunanta."Naja'atu.'' Shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya, ya kalleta cikin
yanayi na damuwa yace."Kina so jama'a su zage ni a unguwa ko? ashe a
matsayina na mahaifinki ban isa na nemi alfarma a gurin ki kiyi min ba! kin
shirya tozartani a cikin unguwar ko, ba'a ta'ba samun labarin yarinyar data
fujirewa umarnin iyayenta a cikin unguwar nan ba sai ke! wato tun munayin abun nan a cikin gida sai ki
janyo hankalin jama'ar dake waje sun gane cewa tilas mukayi miki ki auri mijin
'yar uwarki, Kina ji da kunnan ki irin surutan da jama'a keyi a kanki, kina so
duniya ta zage tayi tur! dake kan 'kin bin iyaye meye aibun Alhaji Abbas da
kike masa wannan 'kiyayya! idan da al'kawari da amana Abbas bai cancanci haka
daga gare ki ba, to saboda haka ni wannan itace magana ta ta karshe a tsakanina
dake, an daura auraki da Alhaji Abbas to kada naji kada na gani, mutukar kin
daukeni a matsayin uba to ina so ki zauna da wannan bawan Allah zama na amana
kamar yanda 'yar uwarki ta zauna dashi, idan aka kai ki dakin mijinki aka samu
matsala ta 'bangaranki to babu shakka zan yafe wa duniya ke babu ni babu ke har
abada."!! Kallonsa kawai take tana shararar da hawaye bakinta sai rawa yake
tana so tayi magana amma ta rasa ma ta ina zata fara.......Baba malam ya mike
ya fita daga dakin ya barta cikin zullumi da tararrabi gami da neman mafita.
Salim kuwa
suna fita kai tsaye inda su Abba Abbas suke ya nufa, Yana so ya fara dasa masa
'bacin rai a zuciyarsa........Ba tare da wani damuwa ba ya shiga sheda masa
abinda Naja'atun tayi ta kulle kofa tana cewa sai ta kashe kanta tunda ba'a
aura mata wanda take so ba, dalilin da yasa kenan suka shiga gidan suka 'balle
'kofar har da cewa data ganshi zuwa
tayi zata rungumeshi Yayanta Magaji ne ya hanata, Salim ya wani 'kasan'kantar
da kansa yace."Wallahi ni Kawu tuntuni na hakura da yarinyar nan tunda
naji maganar auranka da ita naji ta fita daga raina saboda nasan kai ba mutumin
da zan had'a takara dashi bane, to amma kullum sai ta dame ni da kiran waya
babu dare babu rana, ko dazu sai da ta kira ni da safe tace zata gudu daga gari
nine na hanata nace idan kaunar da take min gaskiya ce to ta nuna ta a kanka, dan na nuna mata a yanzu dai
kai ka fiye min ita sau dubu, tunda ta zama mallakina ka nake daukarta a
matsayin antina."
Wannan
al'amarin yayi masifar d'aga masa hankali mussaman idan ya tuno da maganar
runguma sai yaji wani sabon 'bacin rai na taso masa bai ta'ba d'auka 'kiyayyar
da yarinyar nan ke masa ta kai haka ba, wato da tuni ta gudu da badan Salim din
ya hanata ba, babu shakka dole ya tsaurara matakan tsaro a kanta.
Baba Malam
kam yana fita ya samu Abbah Abbas din da
maganar lallai yau da daddare yake so Naja'atu ta tare a dakinta tunda an daura
aure to maganar aja wani lokaci bai taso ba........Abba Abbas din ya nuna masa
cewar ba wai ya'ki maganarsa bane yana so yayi d'an gyare-gyare a gidan,
shiyasa yace sai nan da sati biyu.....Baba malam fafur ya'ki yarda da maganarsa
Yace bai amince da wani gyara ba za'a kai Naja'atu ta zauna a d'akin 'Yar
uwarta a yanda yake.
Abbah Abbas
baya son yayi ta jayyaya dashi sai kawai ya amince da hakan.
Sai da yayi
sallahr isha'i a 'Kofar na'isan sannan ya nufi gidan nashi, Halisa ana zaune a
palo anci kwalliya cikin wani uban less tayi ado da gold hannu da wuya da
kunne, tayi kyau dai-dai gwargwado, suna zaune ita da yaran suna kallo amma
kallo daya za kayi wa su Saddiqa ka gane a tsorace sukayi ko motsin kirki sun
kasa yi, shigowar Abban nasu yasa suka sauke ajiyar zuciya suna masa sannu da
zuwa....Ya amsa musu yana kokarin shiga dakinsa.
Halisa ta
mi'ke tabi bayansa, yana tsaye yana kokarin cire babbar rigar shaddar dake
jikinsa, Halisa aka 'karasa kusa dashi kamar ba ita ba ta taimaka masa ya cire
rigar ta ninke rigar ta ajiye gefan gado aka wani kalleshi ana fari da ido
cikin kissa tace"Ango kasha
'kamshi."! Dariya ta bashi amma beyi ba yace."Nayi miki kama da ango
a haka."? Murmushi tayi tana ta'be bakinta tace"Sosai kuwa gakanan
sai 'kyallin goshi kake." Yasa dariya yana kallonta yace."Ba haka
ango yake ba ango zaki sameshi cikin walwala da farin ciki komai nasa sabo amma
ni duba ban ma sa sababbin kaya ba fa, kuma yaushe zanyi 'kyallin goshi
bayan har yanzu na kasa samun kwanciyar
hankali dake."
Wani fari
tayi da ido tace"Zaka samu kwanciyar hankali dani idan baka tauye min
hakkina ba ni kuma zan baka kulawa wacce tafi ta da." Yace."To naji
maganarki kuma ina rokan Allah ya bani ikon kwakwanta adalci a tsakaninku, nima
inaso ki dauke kanki kan dukkanin abinda zai faru a nan gaba inaso ki ri'ke
yarinyar nan bisa gaskiya da amana, kece
babba dan haka ki ri'ke girmanki ni kuma
zan baki mamaki sosai ba zan ta'ba juya miki baya." jin furucinsa yasa
taji wani farin ciki ya cika mata zuciya, Toilet ta shiga ta hada masa ruwa
yaje ya wanka ya fito ya shirya cikin
sabuwar jallabiya milk sannan suka fito tare, Halisa sai wani ririta shi take,
ta hada masa abinci da yaji magani ya zauna yaci da bisimillah a
bakinsa.....Sai bayan da ya kammala cin abincin ne ya sheda mata cewar Naja'atu
zata tare a dakinta yau dan abinda mahaifinta yace kenan....Cikin 'kokarin
danne bala'in kishin da ya taso mata tace"To yau kana nufin acan zaka
kwana kenan."? Kai tsaye yace mata "Eh." sunkuyar da kanta tayi ba'kin ciki kamar ya
kasheta, Yace."Idan kina ganin kema zaki zauna a haka ba tare da anyi miki
gyara ba gobe kina iya komawa." Tace"A'a ni bana gaggawa na fiso ka
sanja min kujeru da labulaye da kayan gado duk wani abu da babu a can inaso ka
samin kafin na tare."
Yace."Kada
ki damu insha Allah cikin satin da zamu shiga za'a kammala komai."
To sai kusan
goma da rabi ya bar gidan, Halisa ji
take kamar ta dawo dashi amma ba yanda ta iya dole ta hakura ta kyaleshi ya tafi ta nufi dakinta cikin takaici da
damuwa.
Naja'atu
taci kukanta ta 'koshi bayan 'Yan kaita sun watse! tsoro ne ya cika mata zuciya
gidan ya dinga yi mata gizo gani take kamar zata ga Yayarta, motsin kirki ta
kasa yi sai makyarkyata take ita kadai a
takure a d'aki! kamar mujiya duk
ta tsargi kanta......Mi'kewa tayi cikin tsoro taje ta murzawa 'kofar d'akin key
ta barshi a jiki dan bata so ma idan ya shigo gidan ya shigo inda take, takurewa
tayi kan bed tana kuka had'e da kiran sunan Allah, 'Yar uwarta kawai take
tunawa tana zabura!
Abbah Abbas
ya shigo gidan cikin motarsa, gurin parking ya nufa, yayi parking din motar
yana fitowa maigadi ya 'karaso ya mika masa hannu suka gaisa, maigadin
yace."Alhaji Ashe ka daura aure to ubangiji Allah ya sanya alkairi ita kuma Hajiya Allah ya jikanta da rahama.
Abba Abbas ya amsa cikin kulawa kana yayi masa sallama ya nufi cikin
gidan........Ko'ina shuru sai hasken tarwai a palon, kujera ya samu ya zaune
yayi shuru yana jin wani irin yanayi a jikinsa! Gidan da yayi rayuwa da
Halimatu yau shi zaiyi rayuwa da kanwarta Yarinyar da bai ta'ba tunanin zai
aureta ba......Ya kai minti ashirin zaune a palon kafin ya mike cikin rashin
kuzari ya nufi d'akin da yake tsammanin tana ciki.....
A hankali Ya murd'a handile d'in d'akin
yana so ya bud'e kofar sai yaji ta a rufe ya murd'a sosai nan yaji
alamun key a jiki! Dan buga 'kofar yayi da hannunsa.......A furgice! ta mike
zaune tana zare ido! Ya sake buga kofar dakin had'e da kiran sunanta! jin muryarsa yasa taja tsaki! ta koma ta
kwanta.
Cigaba yayi
da kiran sunanta yana d'an bubbuga kofar a hankali............Ta sake mi'kewa
zaune murya na rawa tace"Waye."? Ajiyar zuciya ya sauke jin
muryarta hankalinsa ya kwanta da yaji
tabbacin tana cikin gidan, Yace."Bud'e kofar ki kar'bi abinci kici.'' Kai
tsaye tace"Bana ci." ta koma ta kwanta! Tsaye yayi a bakin 'kofar d'akin yana d'an
tunani Ya sake dan buga kofar hade da kiran sunanta.
Tace"Abbah
dan Allah ka kyaleni kayi tafiyarka wai dole sai naci abinci ni bana bukatar
duk wani abu da zai fito daga hannunka."
Yace."To naji bud'e kofar ina so nayi magana dake."
Tsaki taja
tace"Ni ba zan bud'e maka 'kofa ba
kawai kayi tafiyarka.'' Ajiyar zuciya ya sauke yace."Okey shikkenan
yanzu dai kin bani dama na koma inda na fito ko? kai tsaye tace"Eh hakan
sai yafi min kwanciyar hankali." Girgiza kansa yayi ya matsa daga jikin
'kofar, ledar dake hannunsa ya ajiye kan center teble ya juya ya fita daga palon,
yana fita ya fito da key daga aljihunsa ya kulle kofar palon kai tsaye ya nufi inda motarsa take.......
*GA MASU
BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #300 SINGLE,
VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA
ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI
TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN
SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO
KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU
NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN
NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram
Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR
ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA
WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar
Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*15*
Kai tsaye da
ya fita daga gidan Naja'atu gidansa na gwangwanzo ya nufa domin bashi da inda
zaije in ba nan din ba, maigadinsa na gidan ya bude masa kofa ya shiga da
motarsa ya gyara Parking a nutse ya fito daga motar ya nufi cikin gidan, shuru
palon da alama itama Halisan ta dade dayin bacci, kai tsaye
bedroom dinsa ya nufa dan ganin kamar hakan shine maslaha koda ya shiga
dakinsa bai jira wani abu ya zare jallabiyar jikinsa, yai saura daga shi sai
singlet da gajeran wando ya kwanta kan
gadonshi tare da rufe jikinsa da bargo, cikin ikon Allah bacci mai nauyi ya
dauke shi.......Komai gajiya da dad'in bacci asubah nayi yake tashi saboda
tsabar sabo da yayi da tashin asuba jikinsa har bashi yake lokaci yayi, karfe
hudu da kwata ya tashi ya nufi toilet a
gurguje ya daura alwala ya fito ya zura jallabiyarsa, dadduma ya hau yayi
nafila(raka'atanilfijir) yana idarwa yayi addua yanda ya sawwa'ka kana ya mi'ke
ya fita.......Dakin Halisa ya nufa domin tashinta, ya tarar da ita tana sharar
bacci, tsayawa yayi a kanta yana dan bubbuga bed din da kiran sunanta, Halisa
firgigit ta tashi zaune tana kallonsa, cike da mamaki tace" Yanzu ka shigo
gidan ne."? Girgiza kansa yayi yana
kokarin fita daga dakin yace."Ai anan na kwana lokacin dana shigo kinyi
bacci ki tashi kiyi sallah.'' Ya bud'e kofar dakin ya fita.
Halisa ta
shiga mamakin maganarsa to anan ya kwana garin ya akayi haka ta faru? to ko dai
yarinyar nan tayi masa tsiya ne? murmushi tayi ta mike farin ciki kamar me a zuciyarta ta nufi toilet cikin zuciyarta tana fad'in
"Lallai wannan babbar dama ce a gurina.........Wajejen biyar da minti goma
ya shigo gidan ya nufi dakin yaransa, nan yaga suna ta bacci basu tashi ba,
tashinsu yayi yace suje suyi alwala suyi sallah. Ya fita daga d'akin, Halisa
kuwa wanka tayi sannan tayi alwala ta fito tayi sallah a gurguje ko adduar
kirki ba tayi ba ta mike daga kan daddumar, wata matsiyaciyar rigar bacci ta
dauko bata da maraba da tsirara tasa a jikinta ta fesa turare kusan kala goma a
jikinta, ta dauko maganin mata na matsi ta lakata a hannunta kafin tasa a
gabanta sai da ta tofa maliki yaumi dini (Subahanallah) sannan ta cusa maganin
a matantakar ta, ta mayar da maganin
inda take 'boye shi, hijab d'inta ta zura a jikinta ta nufi dakin
maigidan.........Abba Abbas na zaune a kan Sofa yana dan duba wayarsa ta shigo
dakin, 'kamshin turaranta ya cika dakin, fuskarsa a sake ya amsa mata
sallamarta, tazo ta zauna kusa dashi tana gaishe shi ya amsa a nutse yana
tambayarta kwanan yara Tace" Sun kwana kalau! Hijab din jikinta ta cire ta
ajiye gefe, Ya tsira mata ido yana kallonta, gani yayi ta dawo 'yar yarinya
domin rigar irin mai maida tsohuwa yarinya ce Halisa akwai breast sosai gasu
manya manya gashi bata wani shayar da yawa ba shiyasa basu zube sosai ba,
gabakidaya ji yayi hankalinsa ya tashi, dama daurewa kawai yake, idananunsa
suka kad'a sukayi jawur, Ta sake matsawa
jikinsa tana masa magana kasa-kasa, wai tambayarsa take mai yasa bai kwana
gidan amarya ba.....Abbah Abbas da ya soma fita daga nutsuwarsa kai tsaye
yace."Kulle 'kofarta tayi shine dalilin da yasa na dawo nan." Ta'be
bakinta tayi ba tace komai ba ta shiga
shashshafa jikinsa, hannunta ya ri'ke suka mike kai tsaye bed suka
nufa..........Halisa ta baje hajar ta sosai ta sakar masa jiki yayi abinda yake
so da ita tana taimaka masa da sabbabin salon data tanade su dan samun damar
mallakarsa, abinka da jarumin namiji ji
yayi Halisan ta kasa isar sa gabad'aya yaji kamar an 'kara mata ni'ima da
d'adi! gashi gabanta ya tsuke ya cika sosai sai zubar da ruwa yake, abinda
bayayi a ranar sai da yayi sambatun surutai Abbah Abbas komai dad'in sex baya
ta'ba yarda yayi wannan sambatun da iface-iface! a ganinsa duk shashancin ne
meye abin ihu! sai dai yayi ta sauke
numfashi yana sakin ajiyar zuciya........Basu saurarawa junansu ba sai kusan
tara saura na safe, yara har sunyi wanka sun shirya sun fito palo sun zauna
amma babu break fast.......
'Bangaran
Naja'atu kuwa bayan fitar Abbah Abbas din daga gidan, sai ta shige cikin bargo
ta kud'indine jikinta tana addua, daga zarar ta rufe idonta fuskar 'yar uwarta
take gani, gashi bargon dake lullube a jikinta sai kamshin turaran Halimatun
yake, cikin fitar hayyaci ta cire bargon daga jikinta ta mike da sauri ta bud'e kofa ta fita, kan kujera ta
takure jikinta tana kuka, nan ma ta dinga ganin gilmawar Halimatun tana jin
sautin muryarta a kunnanta.
Hannu ta
dora a kanta, tana kuka da fad'in "Innalilihi wa'ina ilahi raji'un! na
shiga ukuna!! ta mike a sukwane ta nufi dakin Abbah Abbas din cikin ikon Allah
tana murd'a kofar dakin ta bude shiga tayi da gudu ta kulle dakin taje ta
kwanta kan bed dinsa, ta rufe jikinta da bargonsa tana ta rawar jiki da addua
hawaye kuwa kamar an bud'e famfo, haka ta kwana tana firgita da zabure-zabure, da
asubah tayi sallah a dakin ta bude kofa ta fito kai tsaye kofar fita daga palon
ta nufa, ta dinga murdawa kofar ta'ki bud'ewa zubewa tayi bakin kofar ta had'a
kanta da gwiwa tana ihu!!
Abbah Abbas
yayi mamaki tsayin lokacin da ya dauka yana tara da Halisa dan haka a gurguje
ya samu yayi wanka ya shirya a gurguje ya fito palo ya same su suna break fast
dan Halisa data fito Umarni ta bawa Saddiqa kan ta shiga ta dafa musu ko
indomee ce...
Yaran na
ganinsa suka shiga gaishe shi ya amsa fuskarsa cike da walwala, Ya kalli Mufida
da fad'in " Ina Mommyn ki."? Tace."Ba ta dade da shiga dakinta
ba." ba tare da yace wani abuba
ya kama hanyar fita, gabadayansu suka ce
Abbah adawo lafiya.'' Ya amsa musu a lokacin da yake kokarin fita.
Lokacin da
taji kamar ana 'kokarin bud'e 'kofar dakin zabura! tayi ta mi'ke tsaye hawaye
duk ya bushe fuskarta ga jijiyoyin kanta da suka tashi alamun taci kuka ta
koshi! kofar ta tsirawa ido gabanta na dukan uku-uku......Abbah Abbas ya bud'e
kofar palon ya shigo..........Da gudu taje ta rungumeshi ta fashe da kuka tana
makyarkyata a jikinsa! hannu guda yasa ya dafe bayanta yana bin palon da kallo!
Ba yau Naja'atu ta saba ri'ke shi ko ta rungumeshi ba, a duk sanda xata r'ike
shi ko ta rungume shi a lokotan baya baya jin komai a cikin zuciyarsa da
jikinsa, amma yau ji yayi jikinsa na wani irin rawa mussaman da yaji tudun
breast d'inta a cikin kirjinsa ajiyar zuciya ya sauke mai zafi! ya d'an cire ta
daga jikinsa, yana kallon fuskarta yaga duk tayi wujiga-wujiga ga alamun
furgici nan a tare da ita! gyaran murya yayi kafin yayi magana, Yace."Dota
wato har yanzu baki daina kuka ba ko ki
fad'a min abinda ke damun rayuwarki."! Hanci ta sha'ka tana sake shigewa
jikinsa da rarraba ido a palon murya a dashe tace."Abbah Yaya Halimatu ce
tazo tana yi min magana dan Allah ka taimaka min ka rabani da wannan rayuwar da
nake cikinta ka mayar dani gida gaban iyayena wallahi ba zan iya zama a gidan
nan ba ka taimaka min Abbah rayuwata na cikin garari da tashin hankali."!
Tana rirrikeshi take wannan maganganun
Hannunta ya ri'ke ya dan sassauta muryarsa
sannan yace."Ki kwantar da hankalin
ki Dota wanda ya mutu baya dawowa kawai kinsa tsoro acikin zuciyarki shiyasa
kika kasa samun nutsuwa a gidan.....Shuru tayi tana goge fuskarta, yaja ta suka
nufi bedroom dinshi, koda suka shiga dakin sai yaga shimfidar gadonsa a
hargitse ga bargonshi a 'kasa, ya kalleta
cikin nazari yace."A dakin nan kika kwana ne."? Hawaye suka
wanke mata fuska tace."Eh ko ina tsoro ake bani shine na shigo nan na kwanta to anan din ma ban daina firgita
ba." shuru yayi yana bin dakin da kallo, kafin yace."Babu wani abin
tsoro a cikin gidan nan ke kanki kin sani lafiya lau mukayi rayuwa a ciki ina
ganin kamar kin sanya tunanin Halimatu a cikin ranki shiyasa kike furgita ina so
ki kwantar da hankalinki ki nutsu ki san da cewar wanda ya mutu baya dawowa,
fargaba da damuwar da kika sanya a ranki duk itace ta janyo miki firgita."
Girgiza kanta tayi tana ri'ke hannunsa
tace"Abbah ba zan iya zama ba dan Allah ka mayar dani gidanmu ka dubi halin
da nake ciki ka tausayawa rayuwata." Ya dinga kallonta yana mamakin
maganarta ya tausayawa rayuwarta to wane irin tausaya mata zaiyi bayan wanda
yake mata, Yace."Yanzu dai je kiyi wanka
tukkuna naga alama ma kamar baki karya ba ko."? Daga kanta tayi tace"Ba
zan iya shiga dakin ba tsoro nake ji." Kai tsaye yace."To sai kiyi a
toilet dina." Tace"To kayana na dakin ai." Yace."Bari na
dauko miki." Fita yayi daga dakin, ta dinga zazzare idonta tana bin dakin
da kallo, shi kansa dakin nasa tsoransa take ji, tana tsaye ya shigo hannunsa
rike da riga da zani na atamfa super ire-iren kayan da yake d'inka musu, ya
ajiye kan bed yace."Baki shiga wankan ba." Hanyar toilet din ta nufa salo-salo! ya bita
da kallo mai tarin ma'anoni! bayan shigarta toilet din ya dauki bargon dake
kasa ya mai dashi kan bed din ya xauna gefen bed din hade da kunna wayarsa yana
dubawa, kawai yaji ihun ta daga cikin
toilet din kafin ma yayi wani yun'kuri ta fito a guje jikinta duk kumfar sabula
ta dauro towel dinsa yana kokarin fad'uwa daga jikinta, ya mike a gigice yana
tambayarta ihu! take tana nuna masa toilet din, Ya rike hannunta yana tofa mata
addua tangadi ta shiga yi tamkar 'yar maye ta tafi luuuu! zata fad'i! ba tare
da 'bata lokaci ba ya ri'ke ta sosai a jikinsa, cikin tashin hankali da damuwa
ya nemi gefen bed ya zauna da ita rungume a jikinsa, ji yayi jikinta na wani irin kyarma! yana
rawa kamar wacce take cikin zazzabi mai zafi! babu shakka a firgice take,
adduoi ya shiga tofa mata a jikinta yana me tsirawa fuskarta ido, a fizge suna
dan kama da Halimatu kad'an, nan ya shagala da kallonta dan gani yayi tana nema
ta rikid'e ta koma masa Halimatu.......Lokacin ne kuma ta dan samu nutsuwa ta
bude idonta tana ambatar kalmar
innalillahi wa'ina ilahi raji'un! Ta mike da sauri ganinta kwance lakadan a
jikinsa ga towel din jikin ya sa'bule! brest dinta duk a waje! Da sauri shima
ya gyara yanayin sa amma dai duk da haka kana kallonshi sai gane ya hau
network, Yayi dan gyaran murya as'usul
Yace."Sannu ki dinga yawaita addua ina ganin tunda kin firgita da
zaman side din nan zan sa a gyara miki Side din da ya kasance nawa sai ki koma
can." Gyara towel din jikinta tayi ta mike daga jikinsa, kayan ta dake
kusa dashi ta dauka tana so tasa tana jin kunyarsa, Yace."Ya zaki sa kayan
bayan duk ga sabulu nan a jikinki." Cikin rawar Murya tace"Ba zan iya
komawa toilet din ba, dan ina wanka naji kamar ana kiran sunana." Ya dinga
kallonta abin na bashi mamaki! Mikewa yayi ya rike hannunta yace."Muje na
raka ki kiyi wankan." Ma'kale kafad'a tayi tana komawa baya!
Yace."Zan tsaya har ki gama fa kuma bazan kalleki ba." Hawaye ta
share tace''Na hakura da wankan."Ya girgiza kansa da fad'in "A'a ai
bai dace ba kina amarya ki zauna da datti ba zakiyi ba'ki fa." Kallonsa ta
dinga yi tana mamakin maganarsa, Tace."Abbah ni d'in amaryar waye."?
Ya nuna kansa da hannu da fad'in "Amaryata mana." Taji wani irin ciwo
da takaici a cikin zuciyarta, hawaye suka kece mata tace."Kaico da wannan
kalmar taka Abbah! Kaico da wannan maganar dake fitowa daga bakin ka, ni ba amaryarka
bace 'Yar ka ce." Tana gama maganar ta ta cire hannunta daga cikin nasa ta
fita daga dakin, gabadaya ma ji tayi ta
daina jin tsoron akan ta zauna a dakinsa yana kiranta da amaryarsa gwara ta
fito koma meye ya cutar da ita....
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA
#400 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA
KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI
MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA
BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN
WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU
NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN
NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram
Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR
ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA
WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar
Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~~~~~~~~
*16* Ya jima a dakin yana sa'kawa da kwancewa kafin ya fito palon, inda ya
sameta a takure a kan kujera har yanzu bata daina zubar da hawaye......Saboda
jin haushin maganar data fad'a masa yasa ya kama hanyar fita dan baya so ya
zauna a gidan zuciyarsa ta tunzira shi a
kanta, dan ya lura koda 'kuruciya a tare da ita to da akwai iskancin dan
iskancin ma yafi yawa a tare da ita, gabad'aya ya lura ta raina shi kuma ta
daina ganin girmansa, wannan d'abi'un da take masa na 'bata masa rai sosai da
sosai! Yana dab da fita yaji ta ri'ke
masa hannu, ya juyo fuskarsa babu walwala yana kallonta yace."Me zanyi
miki kuma."? Cikin rawar murya tace"Dan Allah zan bika dik inda
zakaje kada ka barni ni kad'ai wallahi ba zan iya zama ba." Shuru yayi
yana kallonta na minti biyu kafin yace."Jeki dauko hijab din'ki." Da
sauri ta saki hannunsa Hijab dinta dake
kan kujera ta d'auka tasa ya nuna mata 'kofar fita da hannunsa, da sauri ta
fice tana sauke ajiyar zuciya, kwana d'aya tayi a cikin gidan jin ta take
tamkar a cikin 'kaya, kulle 'kofar palon yayi yazo shigeta ya nufi
motarsa....Bin bayansa tayi da saurin
gaske, ta ma rigashi bude motar ta shiga ta zauna tana zazzare ido, sai da ya
gama magana da maigadinsa sannan ya shiga motar, yana zama tace."Jakar
kayana na manta ban dauko ba kuma tana d'akin Yaya Halimatu.'' Ya kalleta cikin
rashin walwala yace."To meye amfanin daukar jakar kaya ke a tunaninki ina
zan kai ki."? Tace."Na dauka zaka mayar dani gidan Baba Malam."
Girgiza kansa yayi yace."Ba can zan kaiki ba zan kai ki gidan Halisa ku
zauna da yara zuwa dare sai mu dawo gidan tare." Fashewa tayi da kuka
tace"Dan Allah ka daka mu dawo ni wallahi akan na zauna gidan nan gwara na
zauna a gidan Anti Halisan yafi." Yace."Kina ganin zaki iya zama a
gidan."? Da sauri tace"Eh zan iya." Ba tare da yace komai ba ya
bud'e kofar motar ya fita, cikin gidan ya koma ya shiga, jakar kayanta dake
dakin Halimatu ya dauko mata ya fito.Ganinsa dauke da jakar kayanta yasa ta
sauke ajiyar zuciya,tana ganin gwara ta zauna a gidan Halisa akan ta zauna ita
kadai a wannan uban gidan wanda ake bata tsoro, bayan mota yasa jakar, ya shiga
ya zauna ya tada motar ya fita daga
cikin gidan........Tana ganin sun hau kan titi ta sauke ajiyar zuciya wacce ta
sanya shi dan kallonta da gefan ido, ya
dauke idonsa tare da maida hankalinsa gurin draving din da
yake.............Motar tayi tsit! na kusa minti goma kafin yayi gyaran murya a
nutse ya ambaci sunanta! ta kalleshi tare da amsawa, Yace."Ina so inyi
miki wata tambaya bana son ki munafurce ni ko kuma ki 'ki fad'a min
gaskiya." Tayi shuru tana wasa da yatsun hannunta, Yace."Me yasa
bakya so kiyi rayuwar aure dani."? Kallonsa tayi ya gyada mata kansa a
nutse yace."Amsa nake so ki bani bance kuma ki bani amsar da zata 'bata
mun rai ba." Tace"Saboda na dauke ka a matsayin mahaifina shiyasa
nake ganin kamar haramun ne nayi rayuwar aure da kai." Yace."Waye ya
fad'a miki haka? shiru tayi Ya cigaba da cewa" Aure a tsakanina dake ba
haramun bane Naja'atu, dan na ri'ke ki kin girman a hannuna hakan ba zai hanani
na raya sinnar ma'aiki dake ba mutukar Allah ya kad'dara hakan a tsakanina
dake, mutane nawa ne sukayi irin wannan auran na *MADADI* kuma auran yayi
albarka, inaso ki sani da badan mutuwa ta raba tsakanina da Halimatu ba to da
babu abinda zai sanya ni naji sha'awar auranki, na kwadaitu da auranki ne dan
ina ganin kamar zaki maye min gurbin matata ta gurin kyawawan halaye gami da
sadaukarwa, ashe ba haka abin yake ba, Allah yasa kun fito ke da Halimatu ta
tsatso daya amma kuma halin kowa ya bambanta, shin meye aibuna da bakya so kiyi
rayuwar aure dani? ko kina ganin ba zan iya dauke miki dukkanin bu'katunki ba
ne? Shuru tayi kanta a kasa tana ta nazarin maganganunsa, Ya cigaba da
cewa....."Nasan babu irin sa'ke-sa'ke da zuciyar ki ba tayi miki a kaina,
kina ganin kamar nazo da son zuciya a cikin al'amarin a matsayina na babba ba
yaro ba na aure ki, kina ganin tamkar na cutar da rayuwarki ne tunda na hanaki
auran saurayi wanda ya dace da rayuwarki ko ba haka bane".? Kasa magana
tayi, Ya cigaba da cewa" Nasan kin san da cewar Annabi Muhammad (slw) ya
auri Nana Ayshatu tana 'yar shekara
tara, yayin da shi kuma yake da shekara Hamsin, to kuwa idan hakane aurena dake
babu haramci a ciki tunda wanda akayi duniya dominsa ma ya auri 'yar 'karamar
yarinya wacce bata kai matsayin shekarun da kike ba a yanzu, ina ganin ni na
aikata sinna mai kyau tunda nayi irin
abinda Annabi ya aikata."......Naja'atu duk jikinta yayi sanyi da
maganganunsa, Ya cigaba da cewa" Inaso ki san da cewar abinda kike tunanin
wani saurayi mai tashen balaga zaiyi miki a zamantakewar aure to Matashin mutum
kamata dan kimanin shekara hamsin zaiyi miki abinda yafi wanda kike
tunanin shi saurayin zaiyi miki."
ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cigaba da cewa" Mafi akasari 'yan matan
yanzu abinda ke damunsu kenan.... ((('kalubale gare ku 'yan mata masu tashe saboda ku na zauna nayi wannan littafin, dan
akwai masu 'karamar 'kwa'kwalwar da za suce su baza su auri tsoho ba sai
saurayi, toh wallahi bari na fad'a muku a wannan zamanin ba'a tsayawa za'ben
miji, idan kikace xaki tsaya za'be-za'be to zaki tsufa baki yi aure ba, idan
magidanci mai mata yazo auranki idan har anyi binkice mai kyau a kansa an gane
cewar yana tsaye a kan gidansa da kula da iyalinsa to ki lalla'ba ki shiga daga
cikin, idan kin tsaya kince ke sai saurayi to zaki iya auran saurayin kuma ki
kasa samun biyan bukatarki, Samarin
yanzu duk 'yan bana bakwai ne kuma mafi akasari auran sha'awa suke daga zarar
bukatarsu ta biya shikkenan zaki fuskanci kalubale, bance duka aka taru aka
zama daya ba amma dai abinda yake faruwa na fad'a, idan kuwa kika auri wanda ya dan kwana biyu
to shi yasan menene aure saboda ya dade a cikin inuwarsa zai ri'ke ki da kyau
kuma duk wata soyayya da kike tunanin saurayi zaiyi miki to sugar Dady d'in da
kika raina zaiyi miki wacce tafi ta saurayin domin shi tsohon hannu ne a harkar😁)))) Abba Abbas ya cigaba da cewa" Abinda yake
damun su kenan sai suce su baza su auri tsoho ba dan suna ganin kamar idan sun
auri mai shekaru baza su more kuruciyarsu ba, wanda kwata-kwata ba haka bane
sunyiwa abun mummunar fahimta ne, inaso ki zauna kiyi tunani mai kyau a kan
wannan maganganun da mukayi dake, Na farko ni ban haife ki ba, ballanta ki
dinga ganin kamar kin aikata haramci dan kinyi mu'amular aure dani! Na Na biyu
kuma wad'annnan abubuwan da kike yi sun soma isata idan baki gyara ba to zan
dauki mataki a kanki, ni ba yaro 'karami bane ballanta ki dinga yi min iskancin
da duk kika ga dama, a yanzu ni ina a matsayin mijinki ne ba Ubaba kamar yanda
kike dauka a da to yanzu ba haka bane! Wallahi! duk ranar da na sake jin kin
fad'i wata mummunar magana a kaina da aurana sai na 'bata miki rai! na dauka
kuruciya ce ke damunki sai kuma daga baya na gane rashin arziki ne, to ni ba
lusarin namiji bane ke zaki fadawa kowa hakan tunda kin taso a gidana kinga
yanda nake zamantakewar aure da mataye na, suna bani girma suna mutuntuni babu
wacce take fad'a min bakar magana ko kuma taja min tsaki! dan haka nake
gargadinki ki kiyaye aikata abinda zai janyo miki 'bacin raina."
Tun kafin ya
gama maganarsa ta rufe fuskarta cikin hijabi tana kuka, shima tunda ya gama
maganarsa bai sake cewa komai ba ya cigaba da draving dinsa, daf da zai shiga
cikin unguwar ne kira ya shigo wayarsa, koda ya duba sai yaga numbar
Halisa a nutse ya daga wayar,
Tace"Abban Mufida ya kuma ka fita baka karya ba."? Kai tsaye
yace."Naje duba Naja'atu ne yanzu ma dai ganin zuwa tare da ita ta kasa
zaman gidan." Da sauri tace."Kamar yaya."? Yace."Idan nazo
zanyi miki bayani." Kashe wayarsa yayi dan ganin kamar zata 'kara masa
wani 'bacin ran! Yana ta jin shashshekar
kunanta sai damunsa take kawai dai yayi
mata shuru ne yasan dole idan ta gaji zata daina........Halisa kuwa kasa'ke
tayi da waya a hannu shin me hakan yake nufi da zai dauko mata yarinya ya kawo
mata gida! cika tayi ta batse ta hard'e a kan kujera tana jiran
zuwansu.........
Saboda yasan zai samu matsala daga gurinta
yasa ya shiga gidan fuskarsa a murtuke dan baya so tayi masa rashin arziki ya
lura ba tayi maraba da zuwan Naja'atun ba......Mussadiq na ganin Naja'atu tare
da Abbansu ya tashi a guje yaje ya rungumeta, Allah sarki yaro kenan har ya
mance abinda tayi musu, tsugunawa tayi ta rungumeshi tana sumbatarsa a fuska,
Abba Abbas kuwa bai tsaya ba kai tsaye dakinsa ya nufa, Halisa ta mike ta bishi
tana huci!! Dama ya tsammaci shigowarta, ya tsira mata ido yana kallonta ganin
yanda idonta yayi jajawur lokaci guda, Ri'ke 'kugu tayi tace"Nifa bangane
ba meye amfanin kawo ita gidana naga
harda jakar kayanta." Yace."Eh kamar yanda na fad'a miki a waya
hakane tana jin tsoron zaman gidan ita kadai shine dalilin da yasa na daukota
na kawo ta ta zauna nan kafin na yanke hukunci." Murya na rawa
tace"To ba sai ka kai mata su Saddiqa su taya zama ba, meye sai ka kawo
min ita gida." Yace."Ina tunanin ko ta ganta tare dasu Saddiqar ba
zata samu nutsuwar da ake bukata ba." Tace"To naji a'ina kake shirin
ajiyeta." Cikin jin haushin titsiyen da take masa yace."A duk inda
nayi ra'ayi gidana ne ai." Ganin ya fusata! yasa ta dan sassauta
tace"Sai dai a gyara mata d'aya
sashen ta zauna dan ni bana jin zan iya zama tare da ita." Yace."Ai
dama ba'ace dole ki zauna da ita ba tunda ita tafi so ta zauna anan ke yanzu
zanyi duk yanda zanyi cikin satin nan a gyara miki inda zaki zauna a can
gidan." Girgiza kanta tayi tana 'kas-'kas! da cingum! din bakinta
tayi wani murmushi tace"Ba zai yiwu
ba! ai na fad'a maka ba zan amince da wannan rabe raben gidan ba, nima ina nan
babu inda zanje." Daga mata hannu
yayi yace."To magana ta 'kare kada nan gaba kice min zaki koma can dan ba
zaki koma wallahi." Tace."Ai duk inda kake ina nan idan ka tattara ka
koma can nima zan tattaro nawa nawa na biyo bayanka." Shuru yayi mata ya
zauna gefan gado, ta juya ta fita tana fadin "Bari na kawo maka kayan
break din." Tana fita ta gansu zaune a kujera sun kewaye ta har da Mufida
sai murna sukeyi tamkar sunga wata sabuwar hallita, ita kuma sai murmushi take
musu.....Halisa taja tsaki cikin tsawa tace"Ke Mufida me kike anan zo nan
ki taya ni 'aiki." Yarinyar ta mike da sauri! Halisa ta nuna mata hanyar kicin tana fad'in
"Bana son shashanci ni kun wani zauna kuna dariyar banza." Naja'atu
dasu Saddiqa suka bita da kallo tana kokarin shiga kicin tana
surutai.........Bayan shigewar Halisan, ta kalli Su Saddiq tana nazarinsu,
kwana biyu da bata gansu ba sai taga kamar sunyi rama ta rike hannun Mussadiq
tare da fad'in "Kayi rashin lafiya ne."? Girgiza kansa yayi
yace." Yaya Naja'atu kema kin dawo nan kenan na dauki akwatin kayan ki na
kai miki dakinmu."? Kanta ta d'aga masa idanunta na kawo ruwa, da sauri
yaron yaje ya shiga jan jakar kayan Saddiqa ta mike taje tana taimaka masa,
Naja'atu binsu tayi da kallo hawaye ya zubo mata tausayi yaran suka bata, tana
ganin ko dan saboda su zata dinga adduar Allah ya sanya mata dangana domin ta
zauna tare da dasu.......Halisa ce ta fito daga kicin hannunta ri'ke da tire
jere da kayan tea ko kallon inda Naja'atun take ba tayi ba tayi ba ta nufi dakin
maigidan, Naja'atu ita dai binta da kallo kawai take..........
Yana zaune 'kasan kafet ta shiga dakin, ajiye
tiren tayi ta zauna tana kokarin had'a
masa tea din yace."Ki bawa Naja'atu abinci dan bana tsammanin taci wani
abu tun jiya." Kallonsa tayi kamar
za tayi magana kuma sai ta fasa, ta hada masa tea kana ta zuba masa farfesun
kayan cikin rago wanda yaji magani! ta mike ta fita daga
dakin...........Saddiqa ta kalla tace"Ke Saddiqa ki shiga kicin ki girka
muku abinda zaku ci dan ni ba baiwar kowa bace."! tana gama maganarta ta
shiga dakinta......
Saddiqa ta mike da sauri tana kallon Naja'atun
tace."Don Allah Yaya Naja'atu kada ki kulata." Murmushin takaici tayi
tace."Jeki yi aikin ni ba'a gabana take ba ballanta na tanka mata."
Saddiqa ta sauke ajiyar zuciya ta wuce kicin din, mikewa tayi ta nufi dakin su
Saddiqar nan ta tarar da Mussadiq yana ta jera mata kayanta a cikin wardorbe
dinsu, Tace"Mussadiq daka bar kayan ma a jakar da yafi."
Yace."Ai akwai guri a wardrobe din shiyasa nake shirya miki kayanki a
ciki." Zama tayi tana bin dakin da kallo, gado uku ne kananu irin na 'yan
boarding....Mussadiq yace."Yaya Naja'atu zan baki gado na ki kwanta kafin
Abbanmu ya kawo miki naki." Tace"To nagode Mussadiq." ya mike da sauri yana fad'in "Bari ma
naje na fada masa." Kallo ta bishi dashi har ya fita daga dakin....Dakin
Abban nasu yake kokarin shiga Halisa ta hangoshi tsawa ta buga masa da fad'in
"Me zaka shiga kayi."? Yace."Zan fad'awa Abbanmu ne cewar Yaya
Naja'atu bata da gado." Cikin tsawa! tace"To sarkin iyayi da rawar
kai ai ya fika sani." Abbah Abbas din ne ya fito daga dakin nan Halisa ta gyara yanayin fuskarta
Tace."Gashinan wai yana so ya shiga yayi magana da kai shine nace masa
kana cin abinci sai ka fito tukkuna." Ya kalli Mussadiq din a nutse
yace."Menene."? Mussadiq yace."Abbah Yaya Naja'atu bata da gadon
kwanciya amma kayanta sun samu guri a wardrobe d'in mu." Murmushi yayi
yace."Gaskiya Magaji kana son Yaya Naja'atu sosai kada ka damu zansa a
kawo mata gadonta itama." Murmushi yaron yayi yace."Nagode
Abbah." Cike da farin ciki ya nufi dakin nasu yana so yaje ya fad'a mata
abinda Abban nasu yace..........Abbah Abbas fita yayi daga gidan ya tafi
sabgoginsa sai yamma likis ya shigo unguwar kuma bai shiga gidan ba sai bayan
sallahar isha'i, Halisa yau ma ta cancad'a kwalliya kamar itace amaryar tana
zaune a palo ita da yaran suna kallo kamar jiya, ita kuwa Naja'atu ta kasa zama
a palon tana d'aki ta takure kanta sai neman Salim take a waya bata
shiga.....Hannu bibbiyu Halisa ta kar'be shi, ta bashi abinci yaci kamar koda
yaushe ya dawo palon ya zauna nan yaga babu Naja'atu a gurin, Ya kalli Mussadiq
da fadin "Ina Yaya Naja'atu." Mussadiq yace."Tana dakinmu nace
ta fito muyi kallo ta'ki." Kai tsaye yace."Je ka kirata." Yaron
ya tashi da sauri! ita kuwa Halisa shan kunnu tayi ta wani tamke fuskarta....Da
hijab a jikinta suka fito ta zauna kan kujera kanta a kasa tace"Abbah
Sannu da zuwa." Ya amsa yana nazarinta yace."Me kike a daki ke kad'ai
bayan kowa na palo." Shuru tayi, Ta kalli Halisa a nutse yace."Inaso
nayi magana daku a dakina." Mikewa yayi ya nufi dakinsa." Halisa ta
mike tabi bayansa, ita kuwa Naja'atu gyara zama tayi dan bata fahimci maganarsa
ba, Minti biyar da shigar Halisa dakin nasa Kira ya shigo Wayarta koda taga
numbarsa sai gabanta ya yanke ya fad'i! ta dauki wayar Yace."Ki shigo
dakina zanyi magana daku." a
raunane tace"To." Kashe wayarsa
yayi, Halisa kam sai jijjiga kafa take ta cika ta batse sai wani
'kas-'kas take da cingum din bakinta, Ya kalleta cikin 'bacin rai
yace."Malama ki cire wannan cingum din na bakin ki." Ta daina
'kas-'kas din tayi ta dauke kanta......Da 'kyar ta iya mi'kewa ta nufi d'akin
nasa yayin da yaran suka bita da kallo, Saddiqa dai duk tafi su hankali ta gane Yanzu Yaya Naja'atu
dai-dai take da Anti Halisa a gidan to dan ta shiga dakin Abban nasu ba abun
mamaki bane.......
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA
#300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA
KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI
MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA
BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN
WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU
NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS.........90899076_88137740
KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram
Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR
ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA
WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar
Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
_*Aunty Binta wai dan Allah me yasa duk
littafin ki kike bawa maza Power akan mata ni dai duk na karanta novls din 'ki
ban ta'ba ganin wanda kika bawa mace power ba*😅_
_*MAFI A
KASARIN TAMBAYAR DA MUTANE KEYI MIN KENAN WAI ME YASA NAKE BAWA MAZA POWER! A
LITTAFIN NA, TO GA AMSA, BANI NA BAWA MAZA POWER (IKO)
BA ALLAH NE YA BASU, NAMIJI IN DAI SUNANSA NAMIJI TO KOMAI 'KAN'KANTARSA
SAI YA JAGORANCE KI KODA KUWA KE KIKA HAIFE SHI, TO BALLANTA NAMIJI A CIKIN
GIDANSA😅 TO AI NI KO LOKACIN DA NAKE KARATUN LITTAFIN HAUSA
DAGA NA FARA KARANTA LITTAFI NAGA AN BAWA MACE POWER A KAN MIJINTA NAKE DAINA
KARANTAWA DAN NA TSANI LUSARIN NAMIJI WANDA BAYA IYA JAGORANTAR GIDANSA, MEYE
AMFANIN POWER MACE A GIDANTA🤔 IDAN
YA KASANCE KINA JUYA MIJIN KI TO ME KENAN AKAYI? AI DUK GIDAN DA KUKA GA MACE
NA MULKI A CIKINSA TO TA KAUCE HANYA NE, NI DUK MACEN DAKE MULKI A GIDAN
AURANTA TANA JUYA MIJINTA YANDA RANTA YAKE SO WALLAHI BATA BURGENI SABODA NASAN
'KARSHEN TA NADAMA! MATA SU ZAUNA A 'KARKASHIN MAZAJEN SU KAMAR YANDA ALLAH YACE,
SU KUMA MAZAN SU KULA DA DUK WASU HAKKO'KIN MATAYEN SU, AMMA BA WAI INA FIFITA
NAMIJIN NOVEL AKAN MACEN NOVEL BA INA SO INA NUNA MUKA ABINDA YAKE FARUWA A
ZAHIRI SHINE NAMIJI KO MAI 'KAN'KANTARSA JAGORA NE😁*_
*17_18*
Kanta a
'kasa ta shiga dakin da sallama a bakinta, Shi kadai taji ya amsa sallamar dan
ko Halisa ta amsa ita dai ba taji ba.
Kusa da
Halisan ta zauna tare da sunkuyar da kanta 'kasa, dakin ne yayi shiru na tsayin
minti uku kafin yayi gyaran murya kamar yanda ya saba idan zaiyi magana yace."
Gabad'ayan ku nasan kunsan abinda yasa na tara ku anan ko."? shuru sukayi
babu wacce tayi magana.
Ya kalli
Halisa a nutse yace."Tun kafin na kawo miki Naja'atu gidan nan mun gama
magana dake ina fatan zaki kar'bi yarinyar nan hannu biyu ki dauke ta a
matsayin *'ya* ba kishiya ba, wannan kad'ai za kiyi min ki nuna min ke mai
kaunata ce." Halisa ta d'ago kanta da sauri ta kalleshi, lallai sai ta
ri'ke yarinyar a matsayin *'Ya* ba kishiya ba sannan zai gane ita mai kaunarsa
ce maganar ma mamaki ta bata sosai kuma ta 'kara tabbatar da cewar namiji bashi
da kunya, komai 'kan'kantar kishiyarta yaushe zata dauke ta a matsayin *'Ya*
wannan magana ma bai mai yiwu bace. To shima dai da ya fad'i maganar yasan
abune da ba zai ta'ba yiwu ba dan ya riga yasan yanda Halisa take da masifar
kishi ai da wuya ta ri'ke yarinyar a matsayin *'Ya* ko *'Yar
uwa*......Hankalinsa ya mayar kan Naja'atu ya dan tsira mata ido na minti biyu
kafin ya kira sunanta.
Da sauri ta
d'aga kanta tana kallonsa da idanunta da suka soma kawo ruwa.
Ganin ita
yake kallo yasa tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na fad'uwa!
Yace."Ke
ma d'azu kafin na kawo ki cikin gidan nan mun gama magana dake kuma ina fatan
dukkanin abinda na fad'a miki sun shiga kunnan ki kiji ki kuma shiga hankalin
ki, zaman aure kika shigo kiyi a gidana ba shirme da shashanci ba, wannan da
take zaune tafi kar'fin raini a gurinki." Yafada yana nuna mata Halisa,
bata kalleta ba sai sake sunkuyar da kanta 'kasa da tayi
Ya cigaba da
cewa"Duk ina sane da rashin kunyar da kike mata a lokotan baya! bakya
ganin girmanta duk irin maganar da tazo bakin ki fad'a mata kike bakya gaisheta
a duk inda zaku had'u! tsaki! harara duk babu wanda bakyayi mata, to duk nasan
da hakan nake kyale'ki koda ita Halisan zata kawo 'karar ki ina bata hakuri
saboda a samu zaman lafiya ina kuma nuna mata ke yarinya ce idan kika kara
hankali zaki daina.......Halisa tayi hakuri da halayen ki a baya, dan haka a
yanzu kada naji kada na gani kin zageta ko kin fad'a mata bakar magana ko kuma
kinyi mata tsaki! tsakaninku mutunci da
mutunta juna inaso ki dauki Halisa a matsayin Uwa abokiyar shawararki wannan
kad'ai zakiyi min nasan cewar ke d'in tarbiyar Halimatu
ce."...............Tsit dakin yayi bayan gama maganarsa Halisa tamkar ta
zuba ruwa a 'kasa tasha dan farin ciki taji dadi sosai yau da ya nunawa
yarinyar matsayinta a gurinsa, ashe duk yana sane da iskancin da yarinyar ke
mata a baya amma bai ta'ba magana ba, ji tayi duk wani haushinsa da take ji ta
daina, sai wani murmushi take tana jijjiga 'kafa.......Ita kuwa Naja'atu kanta
a kasa ta kasa dagowa dan tasan idan ta dago 'kwallar dake kokarin zubowa daga
idananunta zata tona asirin zuciyarta...........'Dan kashingid'a yayi kan bed
din yana kallon Halisa babu alamun wasa a fuskarsa yace."Yarinyar nan zata
cigaba da zama anan dakin! tunda ya kasance d'akuna uku ne to bai kamata ta
kwana cikin yara ba idan yaso ni nabi
da'ki-d'aki! kafin komai ya daidaita." Halisa ba haka taso ba amma sai
tayi kokarin danne kishinta tace"To shikkenan hakan ma yayi dai-dai ai." Yace."To tunda kece uwargida
sai ki shirya yanda al'amarin zai kasance."
Cikin ya'ke!
da danne wani mugun kishi tace"Kwana biyu zaka dinga yi kamar dai yanda
kake yi lokacin Halimatu." Gemunsa
ya shafa yana d'an murmushi yace."Ai na dauka ko zaki sanja tsari ne
shiyasa na tambaye ki."? 'Yar dariya tayi tana ta'be baki tace"Kwana
bibbiyu shine tsari mai ma'ana idan kuma kafi son kwana d'ai-d'ai to." Ya
kalli Naja'atu had'e da kiran Sunanta! A firgice! ta kalleshi dan ita bata san
wainar da suke toya ba tana can tunanin ya za'ayi ta fece daga gidan.
Yace."Ke
a ganinki kwana nawa-nawa zan dinga yi a tsakaninku."? Murya na rawa
tace"Ban gane maganar ba." Mikewa zaune yayi yana kallonta
yace."Muna maganar raba kwanan girki ne a tsakaninku shine nake tambayar
ra'ayin ki." Shuru tayi wasu lafiyayyun hawaye suka wanke mata fuska wai
yau itace Abbah Abbas ke tambayarta maganar kwanan girki.
Ganin tayi
shuru yasa ya kalli Halisa yace."Kwana bibbiyu din shi zamu dauka kamar
yanda kika ce."Mikewa tayi tana fad'in "Hakan yayi! to ni dai sai dai
nace Allah ya bamu alkairi." Hanyar fita ta nufa zuciyarta kamar ta
babbake! Kallo ya bita dashi kafin yace."To Allah ya tashe mu lafiya idan kin fita kisa yara su tashi daga kallon
da suke suje su kwanta haka." Ai fad'ar wannan magana da yayi sai ya 'kara
tunzura ta a fusace! ta bud'e kofar dakin ta fita tare da doko kofar da karfin
gaske........Tana fita palon ta raraka yaran d'akinsu sai masifa take tana
zaginsu kamar sune sukayi mata laifi......Mussadiq da Saddiqa a tsorace suka
bar gurin.
Innalilihi
wa'ina ilaiji raji'un! kawai take ta ambata bayan fitar Halisa daga dakin
gabadaya Jinin jikinta ya daskare hatta da kafafunta jinsu take sunyi mata
nauyi da sanyi tana ji kamar ba a jikinta suke ba.........Gyaran muryarsa taji
kafin taji ya kira sunanta, amsawa tayi tana kallonsa ya iya kiran sunanta
tamkar a bakinsa a ka rad'ashi.
''Kinci
abinci ko."? Yafada yana mata wani kallo na 'kasan ido! 'Daga kanta tayi tana mai dauke idonta daga
kansa, Yace." To shiga toilet ki dauro alwala kizo muyi nafila ta godiya
ga Allah." Mi'kewa tayi salo-salo ta nufi toilet d'in.........Minti biyar
ta fito daure da alwala ya mike ya shiga toilet din shima ya dauro alwala ya
fito.
Nafila
sukayi raka'a biyu kamar yanda Annabi ya koyar da sababbin ma'aurata! Abba
Abbas ya jima hannunsa a saman kanta yana addua kafin ya cire ya d'aga hannunsa
sama nan ya jima yanayi wa Allah kirari, daga bisani ya rufe adduarsa da
fatihatulkitabi suka shafa ita dashi, mikewa yayi daga kan abun sallahr ya
dauki key motarsa dake kan drowar taga
ya bude dakin ya fita.
Zukud'un!!
tayi bayan fitarsa daga d'akin, ita yanzu abun ma mamaki yake bata gami
da tsoro! da gaske dai sai tayi zaman
aure dashi, tunda gashin nan har ya zaunar dasu tare da matarsa yana kawo mata
tsare-tsarensa harda kashedi da gargadi kada ta zagi matarsa, lallai Abbah
Abbas yayi masifar bata mamaki! to ita yanzu ba wannan ne ma yake sake
furgitata ba sai kawo ta dakinsa da yayi, to me zaiyi mata? bata da mai bata
amsa! mikewa tayi da saurin gaske ta nufi kofar fita, cikin ikon Allah kuwa
tana jan kofar ta bude! palon ta fita tana zazzare ido! tv a kashe yaran duk
sunje sun kwanta.
Kujerar
data zauna a dazu nan ta nufa ta duba
wayarta zama tayi kan kujerar ta shiga lalubar numbar Salim.......Lokacin shi
yana ma can gidan kallo hayaniya ta hanashi ya daga wayar sai ihu suke shida
abokansa sunci 'kwallo.
Text ta tura
masa tana hawaye tace.
_Salim anya
kuwa kana sona kuwa? tun jiya nake kiran
wayarka baka dauka ba ashe dama duk soyayyar da kake min karya kake......Kada
fa ka manta kai kad'ai nayi wa alkwarin mallakawa kaina da komai nawa dan Allah
kada ka bari Abba Abbas ya samu nasara a kanmu dan gani nan a gidansa a cikin
dakinsa ya kulleni kasan hakan da yayi
yana nufin abubuwa da yawa, dan haka dan Allah ka daure kayi wani abu
akan wannan al'amarin."_
Tura masa
tayi tana adduar Allah yasa ya duba ya bata amsa.......Salim shida abokinsa suna
cikin mota bayan fitowarsu daga gidan kallo ya dauko wayarsa yana dubawa, ganin
Kira da text din Naja'atu yasa yaja tsaki! text din ya shiga dubawa! bayan ya gama karantawa ya
nunawa abokinsa, shima ya karanta, dariya yasa ya bashi hannu suka tafa yace."Amma
gaskiya yarinyar nan na sonka da yawa, yana da kyau ka fara gudanar da aikinka
dan na lura dattijon nan zulamamme ne! ya samu 'karamar yarinya sai 'barin jiki
yake kada ka barshi ya lashi zumar nan ta dad'in rai."
Salim yayi
wani murmushi yana shafa siririn sajensa yace."Ai wallahi sai na d'and'ana
masa d'aci! da bakin cikin daya jefa ni a ciki dan haka bari kaga ni." Sai
kawai ya shiga kiran wayar Naja'atun, da
sauri ta dauki wayar ta kara a kunnanta.
Salim ya
wani narkar da murya cikin sigar yaudara da janye hankali a kasalance yace."My Princess bani da
lafiya zuciyata ta kusa ta daina aiki yini nayi ina aman jini! soyayyarki ina
tsammanin itace ajalina! na kasa daga wayarki ne saboda ni kadai nasan irin
masifar da zan shiga idan naji sautin muryarki, to amma ganin wannan text din
naki na yanzu ya firgitani sosai har naji sha'awar na kira ki a waya na gargade
ki kan cewar komai rintsi kada ki kuskura ki mallakawa wannan tsohon jikinki
kada ki bari ya kusanci inda kike my princess ni kad'ai nasan irin yanda nake
jin fleengs a duk sanda na tuno zubin hallitarki hakika na jima ina kwadayin na ganni ina
tsotsar bakin ki! sannan babu babban abinda yake d'aga mun hankali kamar breast
dinki na jima ina mafarki gasu a hannuna ina wasa dasu ina tsotsa ina lailayasu
a hannuna! dan Allah my princess kada ki bari wani yayi amfani da damata duk
rintsi duk wuya kiyi min wannan alfarmar."
Tunda yake
maganar take 'kan'kame wayar a kunnanta tana sauke ajiyar zuciya tsigar jikinta
na tashi, ji tayi gabadaya jikinta ya rikice ta dinga jin sha'awar Salim din na
taso mata...........Murya a dushashe tace"My prince kada ka damu zan kula
maka da kaina da jikina nayi maka alkawarin babu mai mallakata sai kai kuma
insha Allahu zan fito daga gidan Abba Abbas da budurcina muyi auranmu tinda
shari'a bata rahamta mana ba."
Salim ya
sakeyin 'kasa da murya yace."Yawwa my princess nagode kwarai da soyayyarki
gareni nima insha Allahu zan cigaba da yi mana kokarin dan ganin bukatarmu ta
biya." Ajiyar zuciya ta sauke tana kokarin magana, taji alamun bude kofar
palon..........Da sauri ta mike ta nufi
dakinsu Saddiqa da wayar a kunnanta tana magana 'kasa-'kasa tace"Salim
gashinan ya dawo zan kashe wayar yanzu." Yace."To shikkenan my
Prince. " Kashe wayar yayi ya kalli abokinsa dake draving sai kawai suka
kwashe da dariya kamar wasu shashashai! Kamalu yace."Gaskiya Salim ka iya
tuggu! yarinyar nan fa gabadaya ta mato a kanka duk maganar daka fada mata da
sauri take amsawa kamar wani ubanta." Salim ya shafa sajensa yana dariyar
mugunta yace."Ai na fada maka dama gangar jikinta kawai ya aura, amma
zuciyarta na tafin hannuna." Yafadi maganar yana nuna hannunsa.
Abbah Abbas
ya shigo hannunsa ri'ke da ledoji guda uku, kulle kofar palon yayi kai tsaye ya
nufi dakinsa a hannunsa rike da ledojin dake hannunsa................Jim yayi
yana bin dakin da kallo sai kuma ya ajiye ledojin hannunsa kasan kafet ya nufi
toilet, dan kwankwasa kofar yayi yana kiran sunanta, shurun da yaji ne yasa ya
dan tura kofar toilet din yana dubawa, ganin bata ciki yasa yayi saurin fita
daga dakin, kai tsaye dakinsu Saddiqa ya nufa domin yasan tana can dan babu
wata hanya da zata samu ta fita daga gidan tunda kafin fitarsa sai da ya rufe
kofar palon da key.
Yana shiga
ya hangota kwance kusa da Mussadiq........Ya tsaya daga bakin kofa tare da yin
gyaran murya, mikewa tayi a zabure tana kallonsa, Yace."Ya zaki zo ki
takure kanki ki anan bayan kin san ko shi Mussadiq din gadon na iya yi masa
kad'an." Kasa tayi da kanta tana wasa da hannayeta, Ya juya tare da fad'in
"Ki taso daga cikinsu ki dawo dakina ki kwanta ko bakiji abinda nace d'azu
ba."?
Murya na
rawa tace" Abbah dan Allah ka kyaleni na kwanta a cikinsu sai nafi iya
bacci. girgiza mata kansa yayi yana lumshe ido yace."Ba zaki takurawa kowa
ba ki taso kawai."
Da sauri
tace"Sai na kwanta a 'kasan kafet babu damuwa.'' Yace."Idan baki taso
ba zanzo na daukeki da kaina bana son gaddama." Ganin yayi maganar cikin
rashin wasa sai ta tsorata! da sauri ta sauko daga gadon Mussadiq ta biyo
bayansa suka fita daga dakin.
Suna shiga
dakinsa ya nuna mata ledojin da ya shigo dashi yace."Ki dauki guda d'aya
akwai kazar amarcinki a ciki kada nan gaba ace ana bina bashi."
Naja'atu ta
dinga kallonsa le'banta na rawa, babu shakka mutumin nan da gaske yake abinda
ta fada kenan a zuciyarta......Tana kallonsa ya nufi toilet ta dinga girgiza
kanta tana sake takure jikinta cikin kujera wai shin me yake shirin faruwa
ne?.........Ganinsa ya fito daga toilet daure da towel iya 'kugu! faffad'an
kirjinsa mai cike da yalwar gashi a waje
sai yasa 'yan hanjinta hautsinawa! cikinta ya wani
murd'a mata! da mugun sauri ta sunkuyar kanta a 'kasa! ashe haka yake da
'kirar mazantaka gani tayi kirjinsa a cike dam!
ga jikinsa a murd'e! cikinsa a shafe tamkar wanda baya cin abinci!
Karkarwa
jikinta ya shiga yi gumi na yanko mata daga ko wace kusurwa ta jikinta....
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA
#300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA
KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI
MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA
BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN
WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU
NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN
NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram
Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR
ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA
WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar
Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*LAST FREE PEGE*
*19_20*
'Dauke kanta
tayi lokacin da taga yana kokarin sanya gajeran wando, ta tsirawa 'kasan kafet
ido gabanta sai duk uku-uku yake, muryarsa taji ta dokin kunnanta inda yake
cewa"Ta tashi taje tayi wanka tazo ta kwanta, ba tare da tayi kuskuran
kallonsa ba ta mike salo-salo ta nufi bandakin, to koda ta shiga toilet din ma
kasa yin komai tayi ta jingina jikin bango(garu) tana tunani yanzu idan Abbah
Abbas yace zai kar'bi sadakinsa ya za tayi? wani irin tsoro ne ya shige ta,
taji gabad'aya gwiwowinta sunyi sanyi! ita yanda ma za'ayi ta kwanta gado d'aya
dashi take tunani gashi ta lura dashi sai wani abu yake yi tamkar bai damu da
halin damuwar da take ciki ba.......Da kyar ta d'an sirka ruwa yayi d'umi tayi
wankan, ta wanke bakinta kamar dai koda yaushe kafin ta kwanta sai tayi brush
ta daura towel jikinta ya tsane tsaf sannan ta mayar da kayan jikinta ta fito,
kwance ta same shi saman gado babu komai a jikinsa sai gajeran wando ga fitilar
dakin a kunne! simi-simi ta nufi kan kujerar data ta bari, sunanta taji ya kira
cikin ma'koshi, tsayawa tayi ba tare data juyo ba, Yace."Ba kiyi wankan
bane."? a sanyaye tace."Nayi." Yace."To cire hijabin kizo
ki kwanta." Tace."Abbah kayi hakuri zan kwanta kan kujera."
Mikewa zaune yayi yace."Tunda nake da Halimatu bamu ta'ba raba shimfida ba
saboda haka bana so mu fara haka dake, kizo ki kwanta a makwancin ki Ni babu
abinda zanyi miki.'' yafada yana nuna kusa dashi.
Hawaye suka
zubo mata tayi tsaye tana kallosa gami da d'umbun mamakinsa.
Ganin ta'ki
zuwa yasa ya mi'ke ya nufi inda take, cikin gaggawa tayi 'kasa da kanta dan
gabadaya ji tayi ilahirin tsigar jikinta na mi'kewa sakamakon ganinsa babu kaya
a jikinsa.
Yana zuwa ya
ri'ke hannunta yaja ta suka nufi bed din, zaunar da ita yayi ya zauna yana
kokarin cire mata hijab din jikinta, ta
ri'ke hannunsa tana girgiza masa kanta bakinta sai rawa yake tana so tayi
magana amma tana gudun yayi mata fad'a.
Bai
saurareta ba sai da ya cire mata hijab din yabi jikinta da kallo, Atamfar d'azu
ce a jikinta, d'inki kuma mai nauyi ne da dogon hannu gashi garin ana zafi
dalili kenan daya sanya shima bai kwanta da riga a jikinsa ba, Yace."Ki
dan cire koda rigar jikinki ce sai kiyi daurin kirji da zanin dake jikinki zaki
fi jin dadin kwanciya."
Cikin rawar
murya da rawar baki tace"A'a ai bana kwanciya babu riga a jikina komai
zafi zan iya kwanciya a haka." Girgiza kansa yayi ya raba 'kafafunsa ya
jawo ta yasa a tsakiyar sa yana fad'in akwai cutuwa ki kwanta da riga a
jikinki. kawai sai ya shiga kokarin cire mata rigar......Rirri'ke hannunsa take
tana fad'in "Allah zan iya kwanciya da riga a jikina dan Allah kada ka
cire min riga Abba......Bai saurareta ba sai da ya cire mata rigar jikinta yayi
saura daga ita sai breziya ganin haka yasa tayi saurin sa hannayenta duk biyun
ta rufe kirjinta dasu, hawaye na zubo mata! kokarin mikewa zaune take a jikinsa
ya hanata kafafunsa ya hard'e da nata sosai ya matseta a jikinsa, ya kwanta
rigingine itama ta kwanta rigingine duk rabin jikinta na jikinsa, bargo ya janyo ya rufe musu jikinsu
ya d'ora hannunsa guda saman cikinta dai-dai cibiyarta.....Naja'atu ihu! ne
kawai bata kurma ba amma hawaye tuntuni
yake gudana a fuskarta..
Addua yake
so yayi musu amma ya gagara yi dan gabadaya hankalinsa tashi yayi jikinsa yayi
wani irin sanyi wata irin sha'awar
yarinyar ce ta taso masa, gabad'aya a yanda ya tsara shine ba zai taki yarinyar
ba sai an dan kwana biyu tukkuna yana so ya nuna mata kulawa ne ya kuma nuna
mata cewar abinda take tunanin baza ta samu ba dangane da auranta dashi to ba
haka bane dalilin da yasa kenan ya shirya tsaf! domin ya siye zuciyarta da
kalolin soyayyarsa.
Rintse
idonsa yayi yana sauke wata zazzafar ajiyar zuciya, gaskiya da wuya ya iya
daurewa dan gabadaya hankalinsa ya tashi jinta a cikin jikinsa, ba tare da yayi
tunanin komai ba kawai ya shiga wasa da hannunsa a saman fatar cikinta yana
d'an shafa ramin cibiyarta..... Hannunsa da yake yawo a jikinta tayi saurin
ri'kewa 'kam! tana wani irin kuka tace"Abbah dan Allah ka bari dan
Allah."!! Shuru yayi yana sauke ajiyar zuciya, ita kuma ta kama hannunsa
ta ri'ke kamau! tana sheshsheka! Lumshe idonsa yayi yana adduar Allah yasa
bacci ya daukeshi ya huta, amma yasan da 'kyar yau ya iya rintsawa sakamakon
azababbiyar sha'awar dake taso masa.
Ita kuwa jin
ya daina shafa jikinta yasa ta sauke ajiyar zuciya amma dai duk da haka bata
sakar masa hannu ba yana d'amke a cikin nata, a wautar ta wai so take yayi
bacci sai ta sake shi ta kuma bar masa gadon......Kawai sai taji ya mike zaune
da sauri ya burkitata 'kasan gadon, rintse idonta tayi ganinsa yayi mata rumfa
zai danneta!
"Wayyo
Allahna."! Tafada muryarta na hard'ewa, hannunsa yasa a saman fatar
le'banta yana shafawa a hankali a hankali! Tsira masa ido tayi jikinta sai
karkarwa yake.
Gani tayi
duk ya koma wata kala idanunsa sunyi jawur! duk da ya rage hasken fitilar dakin
bai hanata hango tsabar sha'awarta a cikin 'kwayoyin idonsa ba!!
Ganin tana
yi masa wani irin kallo ne yasa ya kashe dusasheshen hasken da ya bari a take d'akin yayi duhu lokacin ne kuma Allah
ya bata damar ture shi ta mike zaune da sauri tana laluben hanyar sauka,
hannunta ne ya sauka kan jikinsa, taji ta ri'ke wani abu mai tauri da kwari a
hannunta! a gigice ta saki ta dira kasan bed d'in tana makyarkyata.
Kamota yayi
da saurin gaske ya mayar da ita ya kwantar,
still ya sake yi mata rumfa da jikinsa.......Hucin numfashinsa ne ya
dinga dukan fuskarta hakan ya tabbatar mata da cewar fuskarsa na dab da tata!
ta dinga kuka tana kauda kanta!
Saukar
fuskarsa taji a tsakanin wuyanta yana sakar mata wasu zafafan kesses
(Parsonality) Wanda yayi bala'in rikirkita mata lissafi.......
A take
tsigar jikinta ta shiga tashi sakamakon jin yanda yake goga mata gashin
fuskarsa a jikinta sai tsikarinta yake
yi tana jin 'kaikaiyi!
Bud'e baki
tayi da kyar tace."Ab.....Abbah please ka bari ba girman ka bane bana jin
dadin wannan abin da kake mun."
Kamar ta
'kara tunzarashi dayin abinda yake yi ya
cigaba da goga mata gefan fuskarsa a fuskarta da wuyanta, a jiyar zuciya ta
shiga saukewa tana kauda kanta had'e da tutture fuskarsa........Cikin dubara
irin tashi ya samu nasarar had'a bakinta da nasa ba tare da tayi tsammani ba
kawai sai jin bakinta tayi a cikin nasa yana tsotsa tamkar mai tsotsar alawa!
ta dinga kokarin cire bakinta ta kasa saboda ya riga ya ri'ke da nasa! Wasu
hawayen bakin ciki da takaici ne suka shiga zubo mata, *Wai yau Abbah Abbas
shine ke kissing d'inta baki da baki kai wannan rana ba zata ta'ba mancewa da
ita ba*
Shi kuwa
wani irin sha yake wa bakinta kamar zai shanye mata ruwan bakinta tsotsa yake
yana sa harshensa a sa'ko da lokonan bakinta har wani tallafo kanta yake yana
kyarma da rawar jiki, kai!! bai ta'ba
jin baki mai sugar irin nata ba wani irin za'ki yawun bakinta ke dashi.....................Da
'kayar ya cika mata harshe aikuwa gabadaya da le'bunanta da harshen suka
d'umame da radad'in zafi sakamakon jin ba'kon abu da sukayi suka dinga yi mata
zafi da zugi! kuka take tana dukan kirjinsa had'e da turje-turje da kafafunta!
Cikin wani irin hali ya sauke daga kanta ya samu gefen gadon ya zaune had'e da
dafe kansa!
Gabad'aya
yarinyar ta tayar masa da hankali gashi yana ganin ba zai samu biyan bukatarsa
ba a gurinta.
Mi'kewa
zaune tayi tana kuka tana laluben zaninta domin ta daura a jikinta wannan karon ma a cinyarsa ta d'ora hannunta,
jin kamar gashi-gashi yasa da sauri ta cire hannunta! tana matsawa baya! can lokon gadon ta makure jikinta ta janye
bedshirt din ta rufe jikinta dashi tana hawaye.
Sautin kukanta ne ya cika masa kunne, ya dan
juyo a hankali yana kallon bayansa, duk da akwai duhu a dakin bai hanashi
hangota a can 'kuryar gado ba, ya dan shafa kansa cikin wani irin hali na damuwa gami da bukatuwa ya mike ya
nufi toilet domin ya tsarkake jikinsa....Har ya fito daga toilet din bai daina
jin sheshshakar kukanta ba, sai ya kunna
fitilar dakin a take dakin ya gauraye da haske.
Rintse
idonta tayi da saurin gaske tana sake matse jikinta guri guda, bed din ya hau,
sai ta zabura tana rawar jiki tace"Abbah dan Allah kayi hakuri kada kayi
min komai."
Ganin yanda
take ta makale jikinta a jikin bed din yasa ya dan janyo hannunta aikuwa ta
'kwala 'kara! had'e da fizge hannunta ta sauka daga bed din tana kare jikinta
da bedshirt din hannunta.
Ranshi ne ya
'baci da abinda take yi kawai sai ya rabu da ita ya kai hannu ya kashe hasken
dakin, kwanciyarsa yayi ya rufe kafafunsa da blankent.
Ita kuwa kan
Sofa ta lalla'ba taje ta zauna tana me
tsirawa bed ido gani take kamar zai biyo ta kan
kujerar................Abbah Abbas bacci
ne ya dauke shi bacci mara dad'i baccin
da ya sanya shi mafarkai barkatai. Naja'atu kuwa yanda taga dare haka taga rana
sai gefin asuba bacci ya soma fizgarta, jin motsin tashinsa yasa firgigit ta
mike zaune tana zazzare ido.
Yana kunna
hasken dakin ya mike ya nufi toilet ya daura alwala kamar dai yanda ya saba ya
gabatar da nafila kafin ya wuce massalaci.....Sai da ya fita sannan ta sauke
ajiyar zuciya ta mike da sauri taje ta duba rigarta tasa ta dauki hijabinta ta
zura da sauri ta fita daga dakin.
Dakin su
Saddiqa ta nufa koda ta shiga dakin sai
ta gansu duk a kwance basu tashi ba, taji dadin hakan da sauri ta nufi toilet
din dakin, ta tub'e kayan jikinta, ruwa ta hada tayi wanka kana tayi brush sai
ta daura alwala ta fito.....A gurguje ta shirya ta tsaya kan Saddiqa tana
tashinta, gabadayansu suka tashi tace"Ku tashi kuje kuyi alwala."
Saddiqa ce
ta fara tashi ta nufi toilet din, ita kuma ta gyara dadduma ta tayar da sallah.
Bayan ta
idar da sallar kwanciya tayi kan daddumar ta takure jikinta daga zarar ta tuno
da abinda ya faru a tsakaninta da Abbah Abbas sai gabanta ya yanke ya fad'i!
har yanzu le'bunanta zafi suke mata idan ta tuno da yanda ya dinga shan bakinta tsigar jikinta duk sai ta mike.
Mussadiq ne
yazo ya zauna kusa da ita yana gaisheta, ta mike a sanyaye tana amsawa, Saddiqa
da Mufida ma suka gaisheta a nutse ta amsa musu............'Dakin ya shigo
hannunsa ri'ke da wani maidaidaicin carbi, Naja'atu tayi saurin sunkuyar da
kanta 'kasa kwata-kwata bata so ta had'a ido dashi.
Ya tsaya
daga bakin kofa yana fadin "Ashe kun tashi." Mussadiq yace."Eh
Yaya Naja'atu ce ta tashe mu." Ya d'an kalleta da gefan idonsa, ya kauda
kansa yana amsawa gaisuwar 'yayansa, juyawa yayi zai fita yaji muryarta tana gaishe shi, ba tare da ya Juya ba ya
amsa, ya bude kofar dakin ya fita.
Gabad'ayan
su suka mike zasu fita tace"Ina zakuje."? Saddiqa tace"Zamuje mu
gaisa da Mommy ne." shuru tayi tana kallonsu suka fita daga dakin..
Lokacin da
suka shiga gaishe da Halisa yana tsaye a dakin suna magana, ya bisu da kallo
har suka fita yana mamakin ina ita Naja'atun wato ba taji maganarsa ta jiya ba
kenan? a tunaninsa zata biyo yaran suzo
gaishe da Halisan tare, Inda ita kuma sam ba tayi tunanin hakaba saboda ba
gaishe da Halisa ne a gabanta ba abinda ke gabanta shi ya dameta.........Ya
kalli Halisa a nutse yace."To yanzu
nawa kike ganin zasu isa.?
Mikewa tayi
daga kan daddumar da take zaune tana kokarin cire hijabin da tayi sallah dashi
tace"To ka zauna mana sai nayi maka lissafi." Jim yayi kafin ya
zauna! dan yana sane ya'ki zama a dakin saboda yasan halin da yake ciki na
sha'awa baya so taja ra'ayinsa ya aikata wani abun da ita a cikin hakkin wata.
Zama tayi
kusa dashi tana nanikar jikinsa, ya kalleta babu yabo babu fallasa
yace."Kiyi min bayanin nace kamar nawa ne zai isa da zaki siyo mata
sutturun da suka dace."
Fuskarsa ta
shafa da hannunta ta kai bakinta kan kuncinsa ta manna masa kiss! tana me d'ora hannunta a cinyarsa, ganin irin abinda
take masa ne yasa ya gane abinda take nufi! Yace."Kin san dai ba'a cikin
kwanakin ki kike ba ko."? Marairaicewa tayi tace"Haba ai kaima kasan
ba zab iya bari har sai nan da kwana shida ba wallahi, ni dai gaskiya a bukace
nake."
Kallonta ya
shiga yi yana mamakin maganarta, yace."To nima bani nake da kaina ba sai
kije ki tambayi mai hakki idan ta baki aro na shikkenan."
'Bata rai
tayi tana sake shigewa jikinsa tace"Allah ya kiyaye na tambayi yarinyar
nan wani abu kaine kake da iko da kanka kuma kafi kowa sanin halin da nake
shiga idan ina cikin wannan halin dan haka
ni ba zan iya sauraran komai ba sai na samu biyan bukatata."
Kallonta kawai yake dan shi ya rasa ma abinda zai ce mata, yana jinta tana ta
shashshafa jikinsa tana masa salo iri-iri to abinka da wanda dama yake a bukace
a take ya bada kai bori ya hau, suka shiga biyawa junansu bukata...
Gabad'ayansu
har ita suka fito palo suka zazzauna suna hira kar'fe takwas shuru basu ga gilmawar masu gidan
ba, tara ma tayi shuru, basu fito ba, A
hankali ta kalli Mussadiq tace"Ko Abbanku ya fita ne."? Yaron ya
girgiza kansa da fad'in "Wallahi ban sani ba dazu dai da muka shiga gaishe
da Mommy na ganshi a dakin."
Shuru tayi
tana nazarin maganar yaron, ta kalleshi cikin sanyin jiki tace"Kana jin yunwa ko."? Kai ya d'aga mata,
mi'kewa tayi ta kalli Saddiqa da Mufida tace"Kuzo ku nuna min kicin din na
had'a muku break fast." Suka mike da sauri
suna murna, tare suka shiga kicin din nan suka shiga aiki kowanne ta
bashi abinda zai taimaka mata dashi..............Halisa ta samu abinda take so
sosai ta ri'ke wuta ta'ki barinsa ya huta shi kuma jinta zam-zam! ya dinga
d'imautar dashi ya kasa hakura da ita suka dinga abu daya kamar jaraba koda
yake dama can sun saba tunda jajayen sawun su......Sai kusan goma da rabi ya
fito daga dakin, lokacin su har sunyi break dinsu suna zaune dai a palon suna hira wanda take saka musu
baki jefi-jefi......Ido suka had'a ita dashi lokacin da ya fito daga dakin
Halisan duk sai ya diririce! lokaci guda ta gane rashin gaskiyarsa kuma ta gane
abinda suka dade sunayi a dakin, wace irin magana ce za'ace an shiga daki sama
da awa uku anayi ai da akwai alamun tambaya.........'Dauke kanta tayi sam bata
wani ji ciwo ba dan ba wai sonsa take ba ballanta taji haushin abinda sukayi mata, cigaba tayi da dan dudduba wayarta dake
hannunta, Shi kuma da sauri yake kokarin shiga dakinsa.....Mussadiq
yace."Yawwa Yaya Naja'atu ga Abban namu ya fito dama nace miki bai futa
ba."
Da sauri ta
kalli yaron tana d'an hararasa! Shi kuma Abbah Abbas din tsayawa yayi yana
kallon Mussadiq din yace."Waye yazo nema na."? Shuru tayi, Mussadiq
yayi karaf yace." 'Dazu ne Yaya Naja'atu take tambaya ta wai ko ka fita
saboda munji shuru bamu ga ka fito daga dakin ka ba shine nace mata kana dakin Mommy."
Naja'atu taji
kamar ta kwad'awa yaron mari! kada fa Ya d'auka ko sonsa take shiyasa take
tambayarsa
Shi kuwa
Abbah Abbas murmushi yayi yana dan shafa gemunsa ya kalleta a nutse yace."Ina tare da
Halisa muna tattauna magana mai muhimanci insha Allah anjima zakuje tare dake
da ita ki za'bi irin kayan da kike so domin ita na wakilta ta had'a miki
lefe." Tsakaninsa da Allah ya fad'i maganar dan shi yana ganin meye a ciki
dan Halisa ta had'a mata lefe ai duk a zaman d'aya!
Ita kuwa
Naja'atu maganar ce ta girmi tunanin ta wannan ma ai rainin hankali ne da zaice
Halisa ta had'a mata lefe kuma har ya
iya fad'a mata da bakinsa, zuciyarta tace mata "To ke meye abin damuwa ai
ba sonsa kike ballanta na dan yace Halisa ta had'a miki lefe kiji haushi!!!
" Eh duk da ba sonsa nake ba amma
ai hakan bai dace ba abin kamar yazo da cin fuska a ciki, to idan ya kasance
tana sonsa kuma haka zai dinga d'ora kishiyarta kan al'amuranta abinda ba zata iya jurewa ba kenan don ita ba Yaya
Halimatu bace...........Dauk'e kanta tayi ba tare da tace masa komai ba, shi
kuma yanayin yanda yaga ta nuna sai yaji wani farin ciki ya lullu'beshi yana
addua Allah yasa yarinyar ta soma sonsa......Yana shiga daki, Ita kuma ta shiga fad'a da zuciyarta ganin kamar tana
so ta takura mata gurin ganin kamar anyi mata rashin adalci a gidan zuciyarta
sai ingizata take akan ta dauki mataki ta bishi daki ta tambaye shi me tsaya
yayi a dakin Halisa har tsayin awa uku
alhalin yasan a cikin kwanakin auranta yake, sannan kuma tace ita bata
yarda Halisa ta had'a mata lefe ba!.....Allah mai iko! abinda zuciyarta keta
sa'ka mata kenan duk ta kasa samun
nutsuwa a gurin sai kallon kofar dakin nasa take tana tununin taje ko kada
taje? Mikewa tayi ba tare da dogon nazari ba ta nufi dakin nasa har tasa hannu zata bude kofar sai kuma ta
fasa, ta juya cikin sanyi jiki ta nufi dakinsu Saddiqa kwanciya tayi ruf da
ciki kawai ta tsinci kanta da fashewa da kuka.
*Tofah!🤔 Ko kukan me Naja'atu take? Ita da take ikirarin bata kaunar
Abbah Abbas din to meye najin haushi dan ta ga ya dad'e a dakin matarsa? Lallai akwai alamun tambaya dangane da
Al'amarin.................Akwai-Akwai_Akwai!! Rikita_Rikita anan agaba! Wai
shin ya zata kaya ne a tsakanin Abbah Abbas da Amaryarsa? Shin zai samu nasarar kar'bar budurcinta ko kuwa?
Salim zai kyale Naja'atu tayi rayuwar aure da Mijinta Kuwa? Wane Babban kuskure
Naja'atu zata tafka anan gaba? Meye makomar Yaya Ramlatu da Halisa? akwai sauran labari anan gaba!!!! Ga duk
wanda yake da ikon biyan kudin littafin nan ya biya ya karanta #300 ko #600
basu isa su biya kudin littafin nan ba😅 Koda yake ai 'KARYA ce amma dai ni nasan 'karyar tawa tana Tasiri a wani
gurin dan haka da kai da ke ina so duk ku biyo ni domin a cigaba da tafiyar
daku Single #300 Vip #600 Babu tsada🤗 Kada ki nuna ganin 'kyashin biyan kudi ki karanta kice bari
ki bari idan an sato ki kiranta Allah ya isa! Idan anyi magana kice kema gani
kikayi an turo shiyasa kika karanta, to duk wanda ya'ki sharar massalaci zaiyi
ta kasuwa!🤗*
*Masu had'a
min decoment na books daga zarar na gama bazan ce komai ba sai dai na ro'ki
Allah ya tattara muku zunuban da na d'auka gurin rubuta littafin ya d'ora muku
a kanku😅Shikkenan sai a raba mana zunubin tare daku kun rage min nauyi.*
*Masu
tambayar wai ni bana littafin free ne
sai na kudi: Amsa To farkon littafina Nana Khadija Free ne zagi da 'korafi gami da rashin hakuri irin na
redars yasa na mayar dashi na kudi, tun
daga haka shikkenan na daina littafin kyauta
amma akwai book dina RUWAN DARE free ne book1 yana nan yana yawo a
groups ga duk mai bukatar karantawa sai ya tambaya a groups insha Allah idan na gama rubuta littafin
MADADI zab cigaba da typing d'insa RUWAN DARE free ne bana kudi bane! idan na
gama Madadi zan cigaba da rubuta muku shi🤗*
*Masoya masu
sahihiyar kauna Ina alfahari daku♥️*
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA
#300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA
KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI
MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA
BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN
WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU
NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN
NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
No comments