KWAI CIKIN KAYA BOOK TWO 7
Page 7
.................Mintuna kaɗan budurwar ta dawo da tire babba a hannu, wanda aka jero abubuwan da muka buƙata a kansa.
Tana ƙoƙarin ajiyewane Jay ya miƙa hannu zai ɗauki ruwan da aka fara kawo masu, a salon da babu wanda ya isa fahimtasa har bily bata kulaba ya tanƙwaɓi tiren ya suɓuce, jikake “Tarats!!! Tass! Tatass!!” kwanikan da suka zube na fashewa, abinda ke cikinsu gaba ɗaya sun koma jikinsu sun wankesu, duk jikinsu ya ɓaci daga shi har bily da bata san mafari ba, a take duk hankalin mutanen dake kusa dasu ya dawo kansu.
Na ɓata fuska saboda harga ALLAH banji daɗin yanda jikina ya ɓaciba. Cikin langwaɓe kai na kallesa kamar zanyi kuka.
Da ƙyar Jay yay ƙoƙarin haɗiye dariyar dake neman kufce masa saboda yanda Bily tayi fuska kamar zata fasa ihu, ga mai da yay tsalle harkan fuskarta sai naso yake.
A fusace na miƙe saboda ganinma dariya yake neman yimin, dan da gaske haushi naji har raina, maimakon ya mata faɗa amma kuma tsabar wulaƙanci yake neman yimin dariya a cikin mutane, bamma san sanda na fara zazzaga mata masifa akan tayi hakanne da gangan ba, yanda ta rikice ba ƙaramin tausayi ta baniba, amma kuma uwar mi take kallo da zata wankemu haka?, shima jinake kamar na juya na talle masa ƙeya yasin.
Jawaad ya tsaya kawai yana kallon bakin Bily dake masifa, babu shiri murmushi ya suɓuce masa, ganin tamkar abin nata da gaskene shima sai ya miƙe, cikin son maidota hayyacinta ya nema riƙo hannunta, amma sam taƙi yarda, dan danan wasu ma'aikatan nasu su
No comments