AJALI COMPLETE
Page 1
.
BABI NA FARKO
.
"A gaskiya Nazifi sai
dai ka yi haquri da
abinda zan fada maka ni dai
shawarar da zan
ba ka ita ce, ka yi haquri ka
manta da
al'amarin wannan yarinyar
domin kuwa a
gaskiya ba abokiyar tafiya ba
ce"
Nazifi ya dubi abokin hirar
tashi cikin
mamaki da kaduwa, "Kamar
yaya in yi haquri
Jamilu, ban gane abinda kake
nufi ba."
Jamilu ya muskuta a kan dogon
bencin da
suke zaune,
"Ka gane ko Nazifi, ba
wai ina
nufin yarinyar ba ta da kyawawan
halaye ba ne,
a'a tana da halaye nagari. To
amma, ni dai
halayen babanta nake hango
maka Nazifi.
Na san halin mutumin domin
kuwa tunda ka yi
mini kwatancen yarinyar, na
fara zulumin ka
yi zaben tumun dare."
.
Nazifi ya sake duban sa cikin
rudani.
"Haba Jamilu wannan wace
irin magana ce?
Yaya ma za a ce in ga yarinya
jiya-jiyan nan,
sannan kuma in ji ina son ta
a raina, har mu
gama tattaunawa mu yi
alqawari ni da ita,
amma kuma ina fada maka ka ce
da ni in
rabu da ita. Kai ma kanka ka
san cewa
wannan magana taka Jamilu ba
mai amsuwa
ba ce."
.
"Ba ina qoqarin raba ka
da yarinyar ba ne
Nazifi. Abinda nake qoqarin
nuna maka a nan
shi ne wannan yarinyar ba
baquwa ba ce a
wurina. Na san gidansu domin
kuwa mun
taba zama a unguwar. Hakan
shi ya sa na
fahimci cewar ba za ka iya
jurewa da halayen
mahaifinta ba."
.
Samarin biyu suka qurawa juna
idanu. Nazifi
ya ce da shi, " To ai ni
ban gane matsalar da
kake so ka nuna mini na
rabuwa da ita din ba
ne, kuma ka qi ka sanar da ko
wane ne
mahaifinta, domin kuwa ni
gidansu kawai ta
kwatanta mini ba ta fada mini
sunan
mahaifinta ba."
.
Jamilu ya dan saurara sannan
ya ce da shi,
"Mahaifinta ba wai
voyayye ba ne, sunansa
Alhaji Dage, wataqila ma dai
ba za ka rasa jin
labarinsa ba."
"Ban san shi ba, Jamilu,
to amma dai tunda
ka sanar da ni a halin yanzu,
ina ganin kana
iya ba ni taqaitaccen bayani
game da halayen
nasa don in fahimci irin
matsalolinsa da kake
magana a kai."
.
Jamilu ya kai ganinsa dama da
hagun harabar
qofar gidan, ya tabbatar babu
wanda yake
sauraron hirar tasu, sannan
ne to ya dawo da
hankalinsa kan Nazifi, wanda
ya yi fakare
yana sauraronsa.
.
"Ka gafarce ni Nazifi,
zan fada maka
halayensa gaba daya. A
gaskiya Alhaji Dage
ba ya baiwa talaka auren `ya`yansa, domin
kuwa ya aurar da `ya`yansa
aqalla guda
biyar, amma kuma na ji an ce
duk a cikin
wadannan `ya`yan nasa, babu
wacce ta auri
talaka irinka Nazifi. Kuma a
wata majiyar ma
an ce wai idan har ka auri
'yar gidan Alhaji
Dage, dole ne ka riqa samar
masa da albashi
kowanne wata. Ka ga dai kai
talaka ne Nazifi,
don Allah ka yi wa kanka
qiyamul laili, kada
ka jawowa kanka abin tsiya
kana zaune lafiya.
Kawai ka mance da zancenta,
ka nemi wata
budurwar daidai
qarfinka."
.
Nazifi ya yi shiru yana
tunanin maganar, zuwa
can sai ya ce, "Amma fa
al'amarin nan ya
daure min kai Jamilu, domin
kuwa jiya a
wurin fatin nan kada ka so ka
ga yadda
yarinyar nan ta manne mini,
duk inda na
nufa tana liqe da ni kamar
cingam. Kuma har
ma mun yi alqawari da ita
cewar zan kai mata
ziyara a yau din nan."
.
Jamilu ya fashe da dariya.
"To daga haduwar fari
kuma kawai sai ka
tsaya kana damun kanka
Nazifi? Sai ka ce za
ta kai ka qara idan ka ce ka
fasa yin soyayyar?
Ni dai ka ji shawarar da zan
ba ka. Idan ka
dauka ta yi maka amfani. Idan
kuma ka yi
kunnen uwar shegu da wannan
shawara tawa,
to wannan kuma ya rage naka.
Ni dai na fita
haqqinka a matsayina na
abokinka, tunda dai
ka tambaye ni gaskiya na gaya
maka."
.
Koda ya kammala sanar da shi
sai ya juyar da
fuskarsa wani bangaren don ba
shi damar yin
tunanin maganganun.
.
Nazifi ya yi tagumi
yana tunanin wadannan
maganganu na
wannan aboki nasa Jamilu.
Sannan ya sake
dawo da farkon haduwarsu da
yarinyar a
daren jiya sanda ake fatin
wani abokinsa.
.
Tana daya daga cikin manyan
qawayen
amarya. Tana sanye da shudin
gwaggwaro.
dan saurayin ya yafito ta tun
daga nesa cikin
qwarewa da sabo da kiran
kyawawan 'yan
mata a wurin fati na yau da
kullum.
.
Kyakkyawar yarinyar ta taso
daga cikin
qawayenta ta same shi, suka
dan kebe,
sauran jama'a kowa nata
harkarsa.
"Idan ba za ki damu ba
'yan mata, zan so ki
ba ni 'yan mintuna koda biyar
ne haka,
domin kuwa ina da wata 'yar
magana da ke."
.
Yarinyar ta yi masa fari, ga
alamar wayayyiya
ce, ta ce "In ban da
abinka malam, ka taba
ganin wanda zai damu da
sauraron baqon
shi? Ba komai kai dai yi bayaninka
ina
sauraron ka."
.
Nazifi ya yi mata murmushin
farin ciki.
"Na yi farin ciki da
kika nuna mini yarda
kuma na ji dadi sasai da
sakin fuskar da kika
nuna mini."
.
Ya dan saurara sannan ya ci
gaba da cewa da
ita.
"Ni dai sunana Nazifi
kuma dan asalin garin
nan ne ni, domin kuwa iyayena
ma a nan aka
haife su. A zahirin gaskiya
ni ba wani mai
wadata ba ne, domin kuwa
sana'ar kafinta
nake yi, a nan nake ci in
sha, sannan kuma in
yin wasu 'yan buqatuna.
Wannan shi ne dan
taqaitaccen tarihina da zan
sanar da ke. Na
fada miki ne don ki san ko ni
wane ne kafin ki
ba ni amsar tambayoyin da zan
yi miki."
.
"Wacce tambaya ce Malam
Nazifi?"
Ya yi mata murmushi,
"Mhm! Tambayar ba
wata boyayyiya ba ce. Da ma
so nake yi na ji
ko kina so na, sannan kuma za
ki iya aure na?
Ni dai gaskiya ina masifar
qaunar ki malama,
domin kuwa ba ki lura ba ne
tunda aka fara
wannan fati ke nake ta
kallo?"
.
Zan cigaba Abokai
AJALI
Marubuci
Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 2
.
Ta yi dariya, "Na ji
bayaninka Malam Nazifi
kuma ina yi maka albishir da
cewar ka sami
karbuwa a zuciyata, domin
kuwa ni kaina ina
matuqar sha'awar namiji
irinka mai ban
dariya."
.
Suka tintsire da dariya a
lokaci guda.
"Kada kuma ki ziga ni
mana, in riqa fasa kaina
a wurin 'yan mata."
"Ba maganar ziga Nazifi,
gaskiya nake fada."
Ya sunkuyar da kansa sannan
ya ce da ita
yana murmushi.
.
"Ban san iyakar godiyar
da zan yi miki ba
wallahi, ga shi kuma ban san
sunanki ba."
Ta dan yi farin cikin kissa,
sanna ta ce da shi.
.
"Kada ka damu Nazifi,
kana iya kira na da
A'isha."
"Mhm! sunan naki akwai
dadi wallahi, da ma
wata rana na tava mafarkin
zan auri wata
kyakkyawar mace mai suna
A'isha."
.
Suka sake yin dariya, ta ce
da shi.
"Kai dai Malam ba ka
rabo da abin dariya
wallahi."
Abu kamar wasa a cikin 'yan
mintoci biyar din
da suka yi suka saba da juna
sai ka ce sun
shekara biyar da fara
soyayya.
Bayan ta yi masa kwatancen
gidansu, shi ma
ya sanar da ita inda gidansu
yake. Sai ya ce da
ita.
.
"Ina fatan dai daga
wannan bikin ba mun
rabu kenan ba, A'isha?"
Ta sake duban shi ta ce.
"Ni dai a bangarena ba
mu rabu ba, amma
idan kai ma haka abin yake a
zuciyarka, me
zai hana kai ka fara kawo min
ziyara don in
tabbatar da gaske kake
yi."
.
Nazifi ya ce da ita.
"Yaushe to zan zo in
same ki, A'isha?"
Ta jefe shi da wani sabon
murmushin.
"Ko gobe ma kana iya
zuwa Nazifi, kowanne
lokaci ina nan a gida ba inda
nake zuwa."
"Ki saurare ni da yamma
A'isha, in Allah ya
so za ki ganni."
.
Ta sake cewa da shi.
"Don Allah ka zo Nazifi,
wallahi ka shiga
raina. Ba na gajiya da
sauraron maganarka,
kamar kada mu rabu."
Suka yi dariya cikin farin
ciki
.
Wannnan shi ne mafarin wannan
al'amari.
Har aka tashi fatin ya koma
gida, bai daina
tunanin 'yar budurwar ba. Duk
ya qosa gari
ya waye don yamma ta yi ya je
ya same ta.
.
To amma ko a cikin ranshi,
dama ya yi
alqawarin kafin ya je wurinta
sai ya shaida wa
abokin sana'arsa Jamilu.
Domin kuwa har
suka bar wurin fatin a daren
jiya bai sanar da
shi abinda ya wakana a
tsakaninsa da yarinyar
ba
.
Tunanin Nazifi ya katse a
yayin da ya ji
Jamilu ya girgiza kafadarshi.
Ya dube shi cikin
tsananin kidimewa.
.
"Wanne irin tunani ne
wannan Nazifi? Daga
na dan ba ka mintoci biyu ka
yi nazari amma
ka share wajen mintoci
goma?"
.
Nazifi ya yi ajiyar zuciya,
sannan ya ce da shi.
"Wallahi tunaninta nake
yi Jamilu."
"Tunanin wacce
kuma?" Jamilu ya tambaye
shi.
"Maganar me muke yi da
kai, Jamilu?
Tunanin masoyiyata A'isha
mana, ko ka
mance ne"
.
Jamilu ya dube shi cikin
rudani.
"Au Wai da ma duk
shawarar da na ba ka, ba
ka dauka ba Nazifi? Ai ni na
yi tsammanin ka
mance da al'amarin. Ni
wallahi da na ga ka yi shiru na dauka tunanin wani abun kuma
kake."
.
Nazifi ya kawar da kansa
cikin wani yanayi
mai kama da damuwa, sannan ya
dubi abokinsa
Jamilu.
.
"A gaskiya ba zan boye
maka ba Jamilu, ba na
jin zan iya rabuwa da A'isha,
tunda dai tana
so na. Na san dai duk tsiyar
baban nata ba dai
zai kashe ni ba don na ce ina
son 'yarsa."
*************
Ya fito daga cikin dakinsa, a
lokacin da ya ji
Burarin 'yarsa A'isha, riqe
da jarida a
hannunsa, sanye da qaton
farin tabarau a kan
ramammiyar fuskarsa. A daidai
wannan
lokaci ne mafadaciyar matar
ta ci wa
kyakkyawar yarinyar kwalar
riga ta girgiza da
Karfi, sannan ta daka mata tsawa.
"Don ubanki wane ne
saurayin da kika canza,
fada min?"
.
Yarinyar ta sake fashewa da
kuka, ta dora
hannayenta bisa kanta.
"Lallai A'isha kin zama
'yar iska, ni zaki dubi
tsabar idanuna ki sanar da ni
cewar wai ba
kya son Gali, kin samu wani
sabon saurayin
To ki fada mini ko dan gidan
uban wane ne a
garin nan ko in ci
ubanki."
.
Ta sake cukuikuyarta ta kayar
da ita a kan
lallausan kujerun da ke
zagaye da tsararren
falon.
,
"Ya isa haka nan."
Tsamurarren mutumin ya fada a
sanyaye.
Babu alamar damuwa ko farin
ciki a fuskarsa.
To amma dai da ganin
guru-gurun idanunsa
da ke cikin faskeken tabaran
ka san cewar ba
a son ranshi matarsa take
dukan 'yar tasa
Kwallin kwal da ya fi kauna a
duniya ba, duk
da yake dai bai san laifin da
yarinyar ta yi ba.
.
Matar tasa mai suna Juma ta
dago kai ta dube
shi tana numfashi sama-sama
kamar ranta
zai fita, kwata-kwata ba ma
ta san lokacin da
Alhaji Dage ya shigo falon
ba, sai dai kawai
maganarsa da ta ji.
"Laifin me ta yi miki
kuma Juma, kike yi
mata irin wannan mahaukacin duka?
Irin
wannan in tsautsayi ya ratsa
ai sai ki karya ta
a banza."
.
Ta sakar mata wuyan riga,
A'isha ta miqe tana
sharbar kuka. Ta nufi dakinta
da gudu-gudu.
Alhaji Dage ya bi ta da
kallo, duk da yake
idan yana sanye da farin
tabaronsa ba kasafai
mutum zai iya karanto wani
yanayi a fuskarsa
ba, to amma dai a wannan
karon duk da
wannan uban tabaron da ya
tsare harabar
kusan ramammiyar fuskarsa
gaba dayanta,
hakan bai hana bayyanar da
alamomin
damuwa ba a kan fuskar tasa.
.
"Wai laifin me ta yi
miki ne, iye?"
Juma ta dube shi cikin
tsananin damuwa.
"Ba ka ji magana da muke
ba ne da ita a
lokacin da ka shigo?"
"Ba wannan na tambaye ki
ba. Ko na ji ko ban
ji wannan ni ta shafa, ke dai
ki fada mini
abinda na tambaye ki."
Mafadaciyar matar ta sake
numfasawa, duk
fuskarta ta yi sharkaf da
zufa sai ka ce ta ci
uban aiki.
.
"Wai Alhaji, wannan 'yar
banzar yarinyar
saura kwana takwas kenan fa a
daura aurensu
da Gali, shi ne don rashin
albarka ta same ni
har daki ta shaida mini cewar
wai ba ta son
shi, ta samu wano sabon
saurayi wanda take
so."
.
Alhaji Dage ya cire qaton
tabaron cikin
tsananin kaduwa da jin zancen
matarsa Juma,
saura qiris jaridar ta
sullube daga hannunsa
ta fadi qasa. Ya tambaye ta a
tsorace.
"Ta canza wani saurayi
fa kika ce...?
"Qwarai kuwa, idan kuma
ka tababa sai in
kira maka ita ka tambaye ta
ta fada maka kai
ma ka ji."
.
Ramammen mutumin ya ja
doguwar ajiyar
zuciya. Abu na farko da ya
fara darsuwa a
zuciyarsa shi ne, yanzu dai
idan wannan 'ya
tasa ta bijire har maganar
auren nan ta
lalace, a ina zai lalubo
dubbban daruruwan
kudin da suka cinye wa wannan
saurayi da zai
aure ta? wanda akalla ba
akasara ba, in dai
lissafi za a yi dalla-dalla
to sun ci wa saurayin
kudi ya kai miliyan guda, duk
don kawai za su
aurar masa da 'yarsu daya,
sai kace 'yar
zinare. Shi kuma da yake
Allah ya jarrabe shi
da son ta, haka nan yake ta
bayarwa, tunda
dai ya san in dai aka riga
aka yi auren duk
masifa dai kuma ba za a ce ya
riqa ba da
albashi duk wata ba.
.
"Amma fa wannan yarinyar
tana neman
dama mana lissafi, domin kuwa
idan zancen
auren nan ya lalace ban san
yadda zan yi da
wannan yaro ba."
.
Ya yi ta sambatu shi kadai
matar tana tsaye
tana kallon sa.
.
Abokai kuyi mani afuwa kwana
biyu ina skul shi yasa kuka jini shiru
Shuraih usman
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 3
.
Duk da yake da ita ma irinsa
ce, ba wai auki gare ta ba,
to amma dai ta fi
shi cika fuska, domin kuwa
duk da tambarin
da sunanshi ya yi a gari,
wajen masifa da
rashin hakuri, to idan ya
dawo cikin gidansa
kuma sai ya yi lagwaf kamar
tsumma.
.
Domin kuwa matarsa Juma ta fi
shi masifa nesa ba kusa ba. Kuma ko tsiyar tasu ta taso shi da
ita, ba ya wani cin riba, don
kuwa ta fi shi
baki. Shi ya sa yake lallaba
ta tunda dai ya san
cewar jiya ba yau ba ce.
.
Da ace sanda yake da dukiya
ne, kafin ya samu karayar arziki, ai itama ta san cewar ba abokiyar takawarsa
ba ce.
To amma tunda ta ga cewar dan
abinda yake
takamar ya kare, sai dai 'yan
dabaru a gari,
ita ma ta daina raga masa a
cikin gida
.
"To wai a ina ma ta samu
wani saurayin,
kuma ma dan gidan wane ne a
garin nan?"
Alhaji Dage ya tambaye ta
cikin karaya.
.
Juma ta turo baki a fusace ta
ce da shi.
"Ni fa ba ta fada mini
ko wane ne ba. ta dai
ce da ni ba za ta auri Gali
ba. Kuma ni ina
tsammanin duk yadda aka yi a
wajen wannan
tsinannen fatin bikin kawarta
da ta je jiya, ta
hadu da saurayin domin kuwa
ba ta dawo nan
gidan ba sai da talatanin
dare."
.
Alhaji Dage ya warware
jaridar ya soma
fifita, domin kuwa a halin
yanzu shi ma zufa-
zufa yake ji.
.
"To in ban da abinki
Juma me ya sa kike
barin yarinyar nan tana zuwa
wani fati? Kin
san fa yanzu zamani ya canza.
A wurin
wannan fate-faten na
alatsine, a nan 'yan
mata suke lalacewa, su
kangare a yi ta fama
da su, ko kuma ma su je su
kunsowa mutane
abin kunya."
.
"To yanzu dai aikin gama
ya gama." Juma ta
ce da shi. "In dai
kangarewar ne ita dai A'isha
ta riga ta yi tunda har ta
dube ni ido da ido ta
ce a canza mijin aure, don
haka yanzu ya
rage namu mu nemi mafita,
amma wannan
cacar bakin da muke yi ba za
ta fisshe mu
ba."
.
Alhaji Dage ya sake jan
doguwar zuciya,
sannan ya ce da matar tasa.
"Eh to ke ma a nan kin
kawo shawara mai kyau
Juma, domin kuwa ko da a ce
al'amura sun
lalace ita yarinyar ba
ruwanta, mu za a tsare
don haka lallai dabara ta
rage tamu."
.
Ya sake numfasawa, zuwa can
ya tattara
hankalinsa wuri guda, ya ce
da matar tasa a
sanyaye.
"Ina ganin abinda za mu
yi shi ne mu zuba
idanu mu ga sabon saurayin
nan, babu
mamaki yana da maiko-maiko.
Idan zai iya
ba mu naira miliyan guda mu
biya Gali
kudadensa da ya kashe, ina
jin ai ba wata
matsala ba ce, miliyan guda
kawai zai ba mu
sai a sallami Gali a daura
auren da shi."
**********
.
Ta sami kimanin awa daya cur
a kwance a
dakinta, tana ta faman
sharbar kuka ita kadai.
Tunda take a duniya ba ta
taba samun kanta a
cikin matsanancin halin
damuwa irin wannan
ba.
.
(Shuraih 99% daga
hausaebooks.cf)
A'isha ta tsayar da kukan, ta
mike ta
zauna a kan gadonta, ta
kurawa bangon dakin
idanu, ko kiftawa ba ta yi.
To amma a zahiri
ba bangon dakin take nazari
ba, hankalinta da
kuma wani tunaninta kai gaba
dayan zuciyarta
ma ba ta kan komai sai a kan
wannan dan
saurayin da suka hadu a wurin
fatin kawarta a
daren jiya
.
Tun rabuwarsu bayan ta dawo gida, ta yanke
shawarar ko dafa ta za a yi a tukunya ba za ta taba yarda a yi wannan aure nata
da wannan saurayi mai suna Gali ba.
.
Domin kuwa har ga Allah matsa
mata ake yi, amma ba ta kaunar sa ko miskala zarratin, to
amma a yanzu tunda dai har
Allah ya hada ta
da Nazifi, to ta kwana gidan
sauki.
.
A'isha ta dade da sanin
wannan al'ada ta
mahaifinta, domin kuwa ba
akana ta ya fara yiwa
`ya`yansa auren dole da,
attajirai masu
hannu da shuni ba. Duk
yayyenta da aka aurar
su kimanin biyar duk auran
dole akayi musu,
to amma ita lallai akwai
alamar daga kanta
za`ayita ta kare,
.
domin kuwa komai tsiya baza
ta bada goyon baya ba, duk da yake kuwa ta san mahaifinta ya ciwa saurayin
makudan kudi, duk kuwa da cewa saurayin
nata Gali soja ne, da shi aka
je kasar Saliyo.
.
Ita kanta wannan dukiyar da
yake facaka ita, a
dalilin wannan yaki ya same
ta, domin kuwa
an ce gwamnati ta basu
miliyoyin kudi,
wadansu kuma suna cewa daga
can kasar ya
samo wannan dukiya. To amma
dai koma
mene ne sanin kowa ne cewar saurayin ya
samu kudi,
,
wadanda kuma ba su yi masa amfani wajen
mallakar masa zuciyar `yar budurwa A`isha ba, domin kuwa ko da wurinta ya zo
sai dai ya kari surutunsa shi kadai, amma ba za ta ce masa ci kanka ba
.
To amma kuma duk da wannan
durama da suke
yi wai a zahiri saura kwanaki
kalilan a daura
musu aurensu. A`isha ta share
hawayen da ke gangarowa
daga cikin idanunta, sannan
ta yunkura
gwuiwoyinta babu karfi
.
Ta sauka daga kan gadon,
domin kuwa ta san cewar a kowane
lokaci bayan yanzu, Nazifi
zai iya zuwa ya
same ta a cikin wannan hali.
Don haka gara ta
gaggauta ta kimtsa kafin ya
zo. Nan da nan ta
nufi bandaki,
.
ta yi wanka ta fito fes kamar
babu wani abu da yake damun ta. Ta fiddo kayan kwalliyarta ta soma caba ado.
Har kawo wannan lokaci zuciyarta ba ta daina tunanin masoyinta Nazifi ba.
.
Ta yi tunanin cewar duk don
saboda ta ce tana kaunarsa aka lallasa
mata shegen duka, ta yi wa
kanta murmushi
sannan ta ce a bayyane.
"Ka da ki damu A`isha ba ki fadi kasa ba, in
dai don soyayya za a yi miki
wannan uban
duka na kawo wuka. Ba ki fadi
a banza ba
A'isha, 'yar autar mata,
soyayya ai ta fi gaban
wasa."
.
Ta kammala shiryawa, ta dubi
madubi, ta gamsu da abinda ta gani. Ta yi wa kanta murmushi domin kuwa ta san
cewar wannan kwalliyar za ta biya kudin sabulu, tunda dai masoyinta na gaskiya
ne zai ga kwalliyar.
.
Dadai a ce wannan wahalallen
ne zai zo, to ba za
ta tsaya bata lokacin inganta
wata kwalliya ba. Domin kuwa ita da a ce ma akwai abinda za
ta shafa, ko ta sanya a jiki,
ya gani ya daina
kaunar ta, to da tuni ma ta
aikata sun rabu, don ta hutawa rayuwarta da wannan naci nasa.
.
Haryanzu dai kuna tare da
Shuraih 99% cikin littafin AJALI na shafi'u dauda giwa
Muje zuwa
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 4
.
Tunda take ba ta taba ganin
mutum da
shegen nacin tsiya irin
wannan saurayi da aka
sa ranar bikinta da shi ba
.
Babu irin cin mutuncin da ba ta yi masa ba,
amma kullum yana nan like da ita don tsabar masifar naci.
.
Don ma ta yi sa'a ne a halin
yanzu ba ya nan,ya yi tafiya kafin ranar daurin aure ta zo Amma ba don haka ba
da tuni har ya zo ya dame ta da surutun tsiya.
.
Tunanin A'isha ya yanke a
yayin data ji sallamar wani karamin yaro, ta amsa sallamar yayin da yaron ya
turo kofar dakin ya shigo
.
"Wani mutum ne ya ce in
kira masa ke, yana can waje."
A'isha ta ji gabanta ya fadi,
ta ce da yaron.
"Bai fada maka sunansa
ba?"
Yaron ya dan yi jim, sannan
ya ce da ita.
"Ya fada min, ya ce in
fada maki Nazifi ne ke
son ganin ki."
A'isha ta rike numfashinta,
ta yi murmushi
sannan ta ce da yaron.
"Don Allah ka je ka ce
da shi ga ni nan zuwa yanzun
nan."
"To." Yaron ya fada
cikin ladabi, ya fita. Ficewarsa ke da wuya ta bazama zuwa inda kayan sawanta
suke, ta zabo wani uban leshi mai ruwan hoda, ta fara hanzarin sanyawa.
.
Duk Allah-Allah take yi ta je ta same shi,
domin kuwa da tunaninsa ta kwana a zuciyarta
.
To sai dai kuma abinda 'yar budurwar ba ta
sani ba shi ne ba ita kadai ce ke murna da zuwan saurayin ba, bayan ita hatta
mahaifinta ma shi ma yana matukar murna da ganin saurayin, domin kuwa ya yi
bakam a daki,
.
duk ya kosa su yi magana da
sabon saurayin ya shaida masa kaulinsa na zunzurutun kudi naira miliyan daya,
idan yana son a aurar masa da kyakkyawar A'isha.
.
BABI NA BIYU
Ta fito daga cikin gida
fuskarta wasai, sai
sheki take yi, tana murmushin
farin ciki. Kai
da gani ka san cewar a boye,
a bayan wannan
kyakkyawar fuskar tata, akwai
wani
muhimmin albishir, wanda ga
dukkan alamu
kuma idan har ta furta shi
daga bakinta,
.
To dole ne ma ya dadada wa
wanda take shaidawa, tabbas zai dadada zuciyarsa. A'isha
ta tsaya wuri guda, tana waige-waigen
inda ya
tsaya a cikin harabar gidan,
wadda ke cike da
shuke-shuke na alfarma da
kuma tsirarun
dawisu dake zirga-zirga nan
da can
$
jikinsu sai kyalkyali yake
yi, a cikin dan abinda ya yi saura na hasken ranar da ke kokarin isa ga
mafadarta.
Duk da karayar arzikin da
mahaifinta ya yi,
da ganin dankareren gidansa,
ka san cewar a
wani zamani da ya wuce an yi
tabara da naira.
.
Ba kasafai za ka samu wani
mahaluki a harabar gidan ba, kullum wurin yana nan tsit kamar makabarta. Wani
lokacin kuma idan Alhaji Dage ya bushi iska, yakan fito da
kujera wajen harabar ya zauna
ya yi ta
karanta jarida. Mafi yawan
lokuta samarin
unguwar suna bakin ciki da
wannan al'ada
tasa, ta zama a waje, domin
yana matukar
takura masu wajen ganawa da
'yar
kyakkyawar yarinya A'isha.
.
Bayan A'isha ta gama waigen
kowanne
bangare na harabar, sai ta
hango Nazifi a can
rakabe a jikin wata bishiyar
dorawar turawa
da ke kusa da babbar kofar
shigowa cikin
gidan. Yana tsaye a jikin
bishiyar, ya jingine
akwalar kekensa a gefe guda.
Hannayensa a
harde a kan kirjinsa, ya sako
wani farin yadi
boyel, wanda ya dan fara
zazzagawa
.
A'isha ta isa gare shi tana
murmushi. Tun daga nesa da ya hango ta shi ma yake murmushi, har ta
kawo inda yake.
"Wallahi har na cire
tsammanin zuwanka,
Nazifi."
.
Soyayya da dadi jama'a
Saide daga karshe.......
Its shuraih 99%
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 5
.
"Wallahi har na cire
tsammanin zuwanka,
Nazifi."
Ya ci gaba da murmushi, ya ce
da ita.
"Haba A'isha, ai ke ma
kin san cewar tunda
dai har na daukar maki
alkawarin cewar zan
zo, ai ba zan karya ba."
.
Suka sake yi wa juna wadansu
sabbin
murmushi.
"Gaskiya na ji dadi
wallahi Nazifi, ka san
yadda soyayyar ta koma yanzu.
Wani lokacin
sai ka ga an kulla alkawura
sama da dari,
amma da wahala ka ga an cika
ko da goma ne
a cikin darin. Kai dai ka san
cewar da a ce
yadda ake kulla alkawarin
soyayya a duniyar
nan, haka ake cikawa, to da
yanzu babu
sauran wani mutum wanda ba
shi da
masoyinsa."
.
Nazifi ya yi dariya.
"Duk da haka dai A'isha,
ai dole ne a samu
nagari, kin san ba zai yiwu a
ce duk an zama
daya ba, duk da lalacewar da
soyayya ta yi za
a samu mutane nagari da ke
cika
alkawarinsu."
"To za ki fara ke ma
ko...?"
Ta yi dariya.
"Ba haka ba ne, wannan
ai gaskiya ce Nazifi,
domin kuwa ba wani zolaya don
ka fadi
halayen masoyinka
nagari."
.
Suka sake tuntsirewa da
dariya a lokaci guda.
Nazifi ya fara cewa bayan sun
gama dariyar.
"A'isha akwai abun
da ke tattare da zuciyata, wanda
duk na kosa da ma in zo in
amayar maki da
shi. Wallahi A'isha jiya ban
yi wani barcin
kirki ba, domin kuwa ina
komawa gida,
tunaninki ya dabaibaye mini
zuciya, sannan
kuma ko da na samu damar yin
barcin,
mafarkinki ne ya buwayi
kyakkyawan barcin
nawa. Don haka nake so idan
ba za ki damu
ba, ina son mu yi maganar
aure in dai har da
gaske ne kina so na."
.
A'isha ta yi ajiyar zuciya
sannan ta ce da
Nazifi, "Na ji duk
bayaninka Nazifi kuma na
matukar farin ciki, to amma
ina son ka yarda
har zuciyarka. Nazifi wallahi
ni ma duk
duniyar nan babu wanda nake
so sai kai. To
amma da akwai wata 'yar
matsala guda daya
da ke tattare da ni. Ina son
idan na fada maka
kada ka karaya, domin kuwa
wannan matsala
ba za ta hana mu gudanar da
soyayyarmu ba.
Ta dan saurara sannan ta ce da
shi.
.
"Nazifi saura kwana
takwas kenan a daura aurena."
Saurayin ya rike numfashinsa
cikin kaduwa,
sannan ya dafe kirjinsa,
"Aurenki!! A'isha...ban fahimce ki ba."
.
Ta girgiza kanta "kwarai
kuwa aurena Nazifi.
To amma ina son ka sha
kuruminka, domin
kuwa ni da ma ba na son
saurayin da za a
daura mana aure da shi, kawai
mahaifina ne
ya takura min a kan
al'amarin. To amma a
halin yanzu, tunda har Allah
ya hada
soyayyarmu da kai, wannan
zancen aure babu
shi, ya lalace, in Allah ya
so kai ne mijina
Nazifi."
.
Nazifi ya yi ajiyar zuciya
sannan ya ce da ita.
"To amma kuma iyayenki
kuma fa A'isha,
kina jin za su amince?"
"Sun riga sun san komai
Nazifi, domin kuwa
na fadawa mahaifiyata
gaskiyar abinda ke
zuciyata, to amma ban samu
goyon baya ba.
Domin kuwa a dalilin na ce
ina kaunar ka
Nazifi sai da ta lakada min
dukan tsaiya, da
kyar mahaifina ya yi mata
magana ta rabu da
ni."
.
Suka kurawa juna idanu cikin
jimami. Nazifi
ya ce "To amma kuma
A'isha kina jin
al'amarin nan zai yiwu? Tun
yanzun fa kenan
har kin fara fuskantar
matsaloli, to ina kuma
a ce tafiya ta yi nisa a
tsakanina da ke?"
"Me zai hana al'amarin
yiwuwa Nazifi?" A'isha
ta ce da shi.
.
"Ni dai na daukar maka
alkawari, duk rigimar
da za a yi ba zan amince a
daura mini aure da
wannan wahalallen ba, don
haka na riga na
gama tunanin komai a halin
yanzu, kai kawai
nake jira, don in ji ta
bakinka. In kana jin za
ka iya jurewa, kamar yadda ni
ma zan jure,
komai wahala mu rike
juna."
.
Nazifi ya sake yin doguwar
ajiyar zuciya,
sannna ya ce da ita,
"Kada ki damu A'isha, na
daukar maki alkawari, komai
wahala ni ma
ina nan tare da ke, sai dai
mutuwa za raba
mu."
.
A daidai wannan lokacin ne da
suke ta
wannan doguwar hirar tasu ta
masoya, kamar
an jeho shi, sai Alhaji Dage
ya fito daga cikin
gida. Tun dazu yake zaman
jira, yana
tsammanin jin sautin
dankareriyar mota ta yi
fakin a kofar gidan, domin
kuwa shi har
yanzu tsammani yake yi, sabon
saurayin da
A'isha ta ce ta sake, wani
hamshakin attajiri
ne wanda ya rude ta da
zunzurutun kudi.
Fitowarsa ke da wuya, ya kai
ganinsa inda
A'isha ke tsaye tare da
saurayin a gindin
bishiyar. Alhaji Dage ya yi
raunanannen
murmushi da ya hango wanda ke
tare da ita,
domin kuwa ya dauka cewar
masinjan
masoyin 'yar tasa ne, ya zo
fadawa 'yarsa
A'isha cewar Alhajin ba zai
samu zuwa ba.
.
Alhaji Dage ya nufi inda suke
a tsaye. Ya
hango tsohuwar akwalar keken
saurayin a
jingine da bishiyar, kamar
dokin kara, nan da
nan sai ya ji tausayin
saurayin ya kama shi,
domin kuwa yana matukar
takaicin yadda
attajirai da manyan ma'aikata
ba sa kulawa
da masinjojinsu, haka dai ya
iske su suna
cikin hirar
.
Nazifi ya rage tsawo ya
gaishe da
Alhaji Dage. Ya amsa cikin
fara'a-fara'a akaici-takaici, kana ya ce da saurayin.
"Allah sarki! Kai ya
turo kenan, bai samu
zuwa ba. In ka je ka ce da
shi na yi zaman
jiransa, domin ina son mu yi
wata 'yar
ganawa da shi a kan lamarin
'yata A'isha da ya
ce yana so"
.
dan saurayin da 'yar budurwar
suka kalli juna
cikin tsananin mamaki. Ba su
san me siririn
mutumin yake nufi ba, to amma
shi bai
damu ba, sai ma ya ci gaba da
zancensa kai-
tsaye.
"Idan ka gama fada mata
sakon da ya aiko ka,
don Allah ka yi saurin janye
akwalar keken ka
tafi malam, domin ina jin
tsoron kada ka
tsorata mini agwagi da dawisu
da wannan
tsohon keken mai shegen rakin
tsiya."
A'isha ta dubi mahaifinta
cikin damuwa, ta ce
da shi cike da kaduwa.
.
"Baba shi ne, ba aiko
shi aka yi ba."
"Ban fahimta ba, shi ne
wa?" Ya zazzaro
kwala-kwalan idanunsa da ke
boye a cikin
kwafcecen-tabaron.
.
A'isha ta ce da shi cikin
ladabi.
"Baba shi ne ai saurayin
da nake so dama, shi
ne masoyin nawa." Tuni
jikinta ya soma
kyarmar kaduwa.
.
Alhaji Dage ya kai hannu
cikin razana, ya
ciccibo katon tabaronsa kaya
guda, ya rike a
hannusa, ya kalli saurayin
sama da kasa
sannan ya ce a sanyaye.
.
"Lallai A'isha
tubarkalla na ga saurayin, ya
sunanka malam?" Nazifi
ya sunkuyar da kansa
kasa, domin kuwa ya tabbatar
akwai matsala
babba da ke shirin faruwa. To
amma dai duk
da haka, sai ya kokarta ya
bude baki ya baiwa
mutumin amsa.
"Sunana Nazifi"
Alhaji Dage ya dubi A'isha ya
daka mata tsawa.
"Shige cikin gida kafin
in zo in same ki `yar
banzar yarinya kawai"
.
A'isha ta juya cikin tsananin
karaya, ta nufi
cikin gidan. lokaci-lokaci ta
kan waigo don
ganin abin da zai wakana ga
masoyinta. Nan
da nan ta soma addu'ar Allah
ya sa dai kada
mafadacin baban nata ya buge
shi, domin
kuwa ta san shi wajen saurin
hannu.
.
Wannan na daga cikin abin da
ya sa shi yin kaurin
suna a unguwar, domin kuwa ya
sha marin
samarin da ke zuwa wurin
`ya`yansa,
musamman ma idan a kasa mutum
ya zo ba
a mota ba
.
Shigewar A'isha ke da wuya,
sai ya tattara
hankalinsa gaba daya ya ce da
dan saurayi
Nazifi.
"Ina son in yi maka
gargadi na farko, kuma na
karshe, wannan yarinya `yata
ce, ni na haife
ta, kuma saura kwana takwas
kenan a daura
aurenta, ka rufawa kanka asiri
ka fita daga
cikin harkokinta, domin kuwa
A'isha a halin
yanzu ko kai aka sayar ba za
ka biya abinda za
kai aurenta ba. Domin kuwa na
san dai ba za
ka kai naira miliyan guda ba,
don haka kar ka
jawo wa kanka bala'i dan
saurayi."
.
Nazifi ya girgiza kai cikin
gamsuwa bayan da
ya ji mafadacin mutumin ya
kai aya. Ya jawo
akwalar kekensa cikin hanzari
domin kuwa in
ma tsautsayi ya ratsa ya ga
alamar cewar jiki
zai yi tsami, to ba zai bar
akwalar keken a
wurin ba, wacce ita kadai ya
mallaka a duniya
.
Malam Nazifi abun tausayi
Talakan masoyi ya hadu da ma
kwadaicin siriki
Its shuraih 99%AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 6
.
Nazifi ya girgiza kai cikin
gamsuwa bayan da
ya ji mafadacin mutumin ya
kai aya. Ya jawo
akwalar kekensa cikin hanzari
domin kuwa in
ma tsautsayi ya ratsa ya ga
alamar cewar jiki
zai yi tsami, to ba zai bar
akwalar keken a
wurin ba, wacce ita kadai ya
mallaka, a duniya.
.
Alhaji Dage ya sake cewa da
shi a fusace,kafin ya tafi.
"Ka rike a zuciyarka dan
saurayi ba na magana biyu, haduwar mu da kai ta biyu babu dadin gani. Idan na
sake ganin ko da inuwarka a nan gidan,kai ko sawunka na gani wallahi sai na
aika polisteshan, an kulle min kai, shege beran masallaci."
________________________________
Wata dankareriyar mota mai
tudun baya, ta garzayo a guje kamar kibiya, tana sheki a cikin hasken
kwaleliyar ranar wacce ke ta faman gasa naman bil'adam. Jama'ar da ke zazzaune
a bakin titin, suka bi motar da kallo, domin kuwa lokaci-lokaci sukan ga motar ta shigo cikin unguwar tasu, to amma kuma har
yanzu babu wanda ya san takamaiman abin da ke kawo motar a kai- akai ba
.
Kamar kullum sai motar ta
rage gudu sannan ta fara sigina, cikin abin da bai fi dakika biyar ba,har ta
tsallako titi.
.
Saurayin da ke tuka motar ya
daga musu hannu, wannan al'adarsa ce koda yaushe, da ma ya kan dago musu hannu
in ya same su a zazzaune. Yawanci idan haka ta faru, su mutanen ba sa wani kula
shi, ko a yanzun ma da ya dago hannu da kyar aka sami mutane uku da suka kula
da shi, su ma kuma ba hannu suka daga masa ba, kai kawai suka gyada masa kamar
kadangaru.
.
Me yiwuwa idan aka tona
zuciyar mutanen unguwar watakila suna da gaskiya, domin kuwa tun ganin farko da
suka yi wa saurayin ya shigo unguwarsu, duk da yake a cikin mota yake, ta
gilashi suke hango shi, a matsayin suna kwararrun zauna gari-banza, sannan kuma
masana akan ilimin sa-ido, sun fahimci cewar wannan saurayi duk inda ya fito ba
mutumin kirki ba ne
.
Akwai wani mutum da ya taba
cewa ma da ganin saurayin ya san cewar dan fashi da makami ne, shi yasa da zarar ya shigo unguwar
suke hade masa fuska, kamar sun ga mutuwa.
.
Saurayin bai taba kula ta
tasu ba, don kuwa ya
san cewar wata rana ma ba za
su sake ganinsa ba, neman aure ya jawo mishi shigowa wannan unguwar mai cike
`yan sa-ido, dazarar an yi aure kuma ta kare
.
Saurayin ya yi murmushi da ya
tuno cewa nan da kwanaki hudu za a daura auren sa da A'isha rabin
ransa, Aisharsa da ya mace a
kan kauna tsawon lokaci.
.
Ko da ya tsallaka titi sai ya
shiga layin gidan
su masoyiyarsa A'isha wacce
yake ta faman
ambatar sunanta sai kace mai
bitar darasi. Ya
ci gaba da murmushinsa sannan
ya daki
sintiyarin motar cikin farin
ciki,
.
hakika komai yana da iyaka,
ya ce a zuciyarsa. Ya dauki dogon lokaci yana nunawa A'isha soyayya, amma ta ki
ta gane kullum sai dai kawai shi yake kidansa sannan kuma yake rawarsa,
amma ita ba ma ta tasa ta ke
ba. To amma
dai yanzu ai wulakanci ya
kare tunda dai ta
kusa zama matarsa, ko da a ce
ba ta
kaunarsa, ai ya zame mata
dole ne ta zauna
da shi tunda dai ya saye
iyayenta.
.
Saurayin ya ci gaba da
murmushinsa na
samun nasara, ya ce a
zuciyarsa, "Hakika kudi
suna da matukar amfani a
rayuwa," domin ya
san cewar da bai mallake su
ba to da shi da
A'isha kyakkyawa sai dai
hange daga nesa. Da
yawa daga cikin abokansa sun
sha damun shi
da surutai a kan wannan
soyayya da ya ke yi
wa A'isha domin kuwa ta sha
ta kwabsa shi ko
a gaban wanene ko da kuwa
yana tare da
abokansa ne
.
Akwai wani lokaci da wani
abokinsa ya ce da shi.
"Don Allah Gali ka rabu
da yarinyar nan tun
da dai ba ta kaunar ka, wai kai ina ma ka
taba jin inda aka yi soyayyar
dole ne? Ya
kamata ka canza sheka haka
nan, domin kuwa
akwai `yan mata kyawawa a
garin nan, ba
A'isha ba ce kadai
kyakkyawa"
Gali ya yi murmushin ya ce da
shi
.
"Abokina kada ka ga
laifina don na likewa
yarinyar nan, wani lokaci ni
kaina nakan yi
kokarin ganin cewar na cire
son ta a zuciyata,
don in huta wa rayuwata domin
kuwa A'isha ta
zame mini kamar maruru ko
sartse a cikin
zuciya, ba na minti daya a
duniya ban yi
tunaninta ba sannna kuma ba
na iya daina
son ta a zuciya ta."
.
Tun daga wannan rana mafi
yawa daga cikin
abokan Gali suka shafa masa
lafiya, wadansu
kuma suka ma bata da shi
domin kuwa su a
ganinsu ya ba da sojoji, ba
haka aka san
zuciyar soja ba. To amma kuma
abin da ba su
sani ba game da lamarin
soyayya shi ne, ta
kansa mutum ya makance ya
dukufa akan
son wani abu, wanda sauran
jama'a ko da
kudi aka hada su ba za su so
wannan abu ba,
.
domin kuwa idan ba haka ba,
babu abinda zai
sa babban ba'askare a cikin
sojoji, wanda ya
shiga har kasashen turai,
amma ya dishe da
kaunar wata yarinya `yar
cikin gida ba kirar
waje ba, har kuma ta zo tana
wulakanta shi,
lallai abin dai kam akwai
takaici.
.
Gali ya yi ajiyar zuciya da
ya tuno walhalun
da ya sha a baya na kaunar
wannan yarinya
A'isha, ya ce a bayyane cikin
rada-rada.
"Kin ba ni wahala A'isha
amma ba komai na
kusa ramawa"
A daidai wannan lokaci ne ya
karaso kofar
gidan, ya yi fakin din
dunkulalliyar motarsa
mai tudun baya, ya fito yana
sanye da
dogayen kayan shudiyar
shadda, dinkin ta-
zarce, dogo ne kakkaura baki,
yadda yake
haka zuciyarsa take
bakikkirin domin kuwa
da ran mutum da na kiyashi
duk daya suke a
wurinsa.
.
Shekarunsa za su kai talatin
da biyar koma fiye a duniya. Ya shiga zagayen gidan
kai tsaye, ya tsaya a cikin
harabar inda shuke-
shuken alfarmar suke. Bai
dade ba a wurin
wata karamar yarinya ta shigo
cikin gidan, ya
tsayar da ita, ya ce da ita.
.
"Kice wa Ai'isha Gali
yana jiran ta a waje"
Ba a jima ba yarinyar ta fito
ta ce da shi.
"Ta ce tana zuwa"
Ya zaro wazobiya sabuwa fil
ya mikawa
yarinyar. Ta amsa cikin doki
ta fice a guje.
.
Gali ya yi ajiyar zuciya ya
fara nazarin
harabar gidan. dawisu da
agwagin ruwa da
suka fi komai ba shi sha'awa
suna ta yawace-
yawace, da kuma koke-koke
abinsu. Ya yi
mamakin yadda mahaifin A'isha
rabin ransa
ke matukar kulawa da wadannan
halittu. Ba a
jima ba A'isha ta fito. Tun
daga nesa ta
murtuke fuskarta da ta hango
Gali tsaye
kamar gunki
.
Ta ce a ranta "Wannan
wahalallen banzan kuma yaushe
ya dawo?" Ta
karaso wurin da yake ta
tsaya, ko sallama ba
ta yi masa ba, ballantana
kuma ta dube shi,
to amma shi da yake ya saba
da wannan
dabi'a tata, bai damu ba sai
kawai ya fara
aikinsa na surutu.
.
"Ai'sha ya kamata yau
dai rana daya ki saki
fuskarki a gareni, domin kuwa
ni da ke mun
zama daya, kin ga fa yau
saura kwanaki hudu
kenan a daura mana aure
.
Bai kamata a ce mu yi aure
kuma ya kasance ba wata kwakkwarar jituwa a tsakaninmu ba. A'isha
ya kamata ki hakura haka nan,
bakin alkalami
ya riga ya bushe."
.
Ta juyo cikin izgili ta dube
shi a yatsine ta ce
da shi.
"Kai da wacce kuma za a
daura muku aure?"
Gali ya dube ta cikin kaduwa.
.
Ku jira part 7
_________
Yan mata kudaina wulakanta
samari
Domin kuwa zai iya yiwuwa su
zaku Aura
Izan ya kasance Saurayin da
ki ka wulakanta wajen neman aurenki ya zama mijinki sannan ki ka kamu da ciwon
sonsa a yayin da shi kuma ya fara Rama wulakancin da ki ka masa
.
Mutane masu tsananin fushi,
masu rike abu a zuciya, basa taba manta wulakanci
.
Wani mawaki yace = in aka
furta so gareka sai kai na'am a zuciya karka zagi Kauna,
= Masoyi yana da rana
= Masoyi yana da Rana
.
Sai mun hadu gobe
Its shuraih 99%
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 7
.
"Kai da wacce kuma za a
daura muku aure?"
Gali ya dube ta cikin kaduwa.
.
"A'ah! ni da ke mana
A'isha, ko ba ki gane ni ba ne? Ni ne Gali masoyinki."
.
A'isha ta yi murmushi, amma
ko da ganin
murmushin ka san cewar a boye
a bayan sa
akwai abubuwa marasa dadin ji
bila'adadin.
.
"Wani lokacin ka kan ba
ni mamaki Gal wai
kai don Allah wanne irin
mutum ne a duniyar
nan? Ba tun yau ba na nuna
maka a zahiri, na
furta maka baki da baki ba na
sonka, ba zan
taba sonka ba kuma, to amma
kai ka like
mini. Yanzu kai saboda Allah
har sha'awa
kake yi ka auri matar da ba
ta kaunarka a
duniya?"
.
Saurayin ya yi ajiyar zuciya
ya ce da ita cikin
damuwa "A'isha kin dade
kina wulakanta ni a
lokacin da ni kuma nake
ganiyar nuna miki
tsantsar soyayya tagari. To
amma kuma ke
mene ne dalilin da za ki ce
ba kya kauna ta?
.
Dole ne ma ki so ni A'isha,
don kuwa babu
dalilin da zaki ki so na. Me
kike bukata ki
mallaka a duniya wanda ba ni
da shi? Ke
kanki kin san cewar ina da
abinda za ki so ni a
duniya.."
.
Aisha ta tsayar da shi ta
hanyar jifan shi da
wani busashshen murmushi
"Lallai ba ka da
hankali Gali kuma ba ka san
soyayya ba,
tunda har ka iya bude baki ka
ce wai kana da
abin da zan so ka da shi dole
.
Na san cewar ba wani abu kake
takama da shi ba face dukiyarka, to bari in fada maka ni ba
dukiyarka ba ce a gaba na?
Kai a haukanka shi
kenan don kana da kudi dole
ne mace ta
soka wannan ba gaskiya ba ne
ka sake
tunani, domin kuwa kai ka
mallaki kudi
amma kuma ni ba na sonka. Ka
ga kenan
ashe ko wannan ma ya ishe ka
darasi, don ka
fahimci cewar kudi ba sa iya sayen
soyayya."
.
Gali ya dubi `yar budurwar
cikin harzuka,
tunda suke ba ta taba kule
shi irin wannan
karon ba. Ya ce da ita a
fusace "To ya isa
hakan nan mu bar wannan
zancen, yanzu
mene ne shirye-shiryenki game
da auren
mu? Na san dai ba za ki rasa
bukatar wani
abu ba."
.
Tace da shi "Ina bukatar
abubuwa da dama
amma kuma ba wurinka ba. Ina
da bukatar
ne a wajen mijina da zan aura, ko ba ka san
cewar wani zan aura ba ne
Gali?"
.
Ya dube ta a tsorace
"Wai me kike nufi ne?
A'isha ni fa ban gane ba, duk
kin ruda ni
wallahi."
.
Ta ci gaba da murmushinta
sannan ta ce da
shi.
"Abin da nake nufi shi
ne saura kwanaki hudu
a daura aurena da wani
saurayi da nake
kauna a zuciyata, amma ba kai
ba."
.
Gali ya ce da ita cikin
rudani.
"To ai ni ma saura
kwanaki hudu kenan
mahaifinki ya daura aurenki
da ni, kuma har
ma na fara raba katin
gaiyata, A'isha."
.
"Wannan matsalarka ce
Gali, ni dai
kasancewar ban taba cewa in
kaunarka ba
kuma ban taba amsar komai
naka ba don
haka idan an daura aure sai a
kai maka wata
amayar amma ba dai ni
ba."
.
Tana gama furta kalaman sai
ta juya ta shige
gida tan kunkunai hade da yin
tsaki. Saurayin
ya bi ta da kallo har ta
bace, maganganunta
na ta faman amsa kuwa da
kururuwa a
kwakwalwarsa. Tuni har ya
fara lissafo
mutanen da ke bukatar a sai
musu likkafani a
cikin jerin wadanda zai aika
barzahu, indai
har ba a kai masa amaryarsa
daki nan da
kwanaki hudu masu zuwa ba
_____________
BABI NA UKU
.
Ba kasafai Nazifi yake barcin
rana ba, domin
kuwa ko ba inda yake da
bukatar zuwa, da
wahala ka same shi a kwance
da rana tsaka
kai ko rashin lafiya yake yi
bai cika kwanciya a
daki da rana ba,
.
bar shi dai ya fito kofar
gida ya zauna a dakali ya karanta mujallun fina-
finai ko kuma littafan
soyayya. To amma
kuma sabanin wannan halayya
tasa da aka san
shi da ita shekara da
shekaru, kwanaki biyu
kenan Nazifi yana wuni a gida
a kwance, ko
lekowa waje ba ya yi
.
Mahaifiyarsa Tabawa ta yi
iyakar kokarinta
don ya fada mata dalilin
canjin wannan
halayya tasa amma kuma abin
ya faskara, ya
ki ya fada mata, sannan kuma
babban abin da
ya fi ba ta mamaki shi ne wai
a cewarsa
lafiyarsa kalau, ba inda ke
yi masa ciwo. A
cikin kwanakin biyun nan ko
wurin sana'arsa
ta kafinta bai leka ba,
.
wanda abu ne mai wahala ko ma
kuwa menene dalilin a ce
Nazifi ya ketare rana daya
bai je wurin
wannan sana'a tasa ba.
To amma kuma abinda ya
tsorata Tabawa shi
ne, wani lokacin idan yana
kwance yana barci
idan ta leka dakinsa
,
sai taji yana ta sambatu a cikin barci, yana
fadar sunan wata yarinya
wai ita A'isha. Sannan kuma
wani lokaci sai ta
same shi yana ta murmushi
.
Ko da Tabawa ta lura da wannna bakon al'amari
da ya sami danta Nazifi sai ta ce da shi a fusace a wuni na biyu
.
"Haba ai ni dama na san
a rina ai ga irin ta
nan kullum kwanan duniya
yaron nan sai na
yi fama da kai ka rika shan
maganin miyagu
da kuma na mutanen boye, amma
taurin kan
tsiyarku na `yan zamani ya
hana ka Nazifi, ga
shi nan ai ka yi gamo da
aljana za ta sabautar
da kai a banza."
.
Tun daga wannan lokaci Tabawa
ta fara
shirye-shiryen kaiwa
bokanyarta ziyara,
domin kuwa ta san cewar
wannan aljana da ta
cafi danta guda daya da take
alfahari da shi a
duniya, duk tsiyar aljanar in
dai har ta kai ta
wajen kwararriyar bokanyarta
Iya mai
dogari, to ko ba ta shirya ba
sai ta fice daga
jikin danta Nazifi
.
To amma kuma shi Nazifi ya
san cewar ko sarakan bori na duniya ne suka taru a kan shi ba za su iya maganin
wannan matsala tashi ba,
domin kuwa duk
kwarewarsu akan wannnan
sana'a ba za su iya
mallaka masa masoyiyarsa da ya kamu da
ciwon so ba, wacce saura
kwanaki biyu kacal a
daura aurenta da wani
saurayin can daban
....
CIWON SO kenan
___________
MASOYA AKIYAYE
Izan zaka so mutum to ka soshi daidai wa daida
Haka nan yan mata kada ku dauki son duniya ku daurawa
saurayi/budurwa, daga karshe kuma ku rasasu, rayuwarku ta fada cikin garari
.
Its shuraih 99%
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 8
.
Kamar kullum a cikin kwanaki
biyu yana
kwance sai mahaifiyarsa ta
shigo cikin dakin.
Ya yi tsammanin zancen neman
maganin ta
zo yi masa, to amma sabanin
haka sai ta ce
da shi.
.
"Wata yarinya ce wai ta
zo tana son ganin ka,
shi ne na ce bari in zo in
sanar da kai."
.
Nazifi ya mike zumbur cikin
mamaki, domin
kuwa inda haka nan ne banza
sai a wuni ana
fama da shi ba zai tashi ba,
kai a cikin
kwanaki biyun nan har lokacin
sallah sai ya zo
ya wuce yana kwance ba zai yi
ba.
.
Amma yanzu daga jin an ce
wata ta zo nemansa, duk da dai bai san ko wace ce ba, amma a can
cikin zuciyarsa sai ya ji ya
dokanta da ya fita
din.
.
Ya tashi da sauri kamar ba shi ne ke wuni
a nannade a gado ba, kamar
wanda ake yiwa
karin ruwa. Lallai dai
sha'anin yaran zamani
sai dai a bar su, Tabawa ta
fada a zuciyarta,
ita ma ta fice daga dakin.
.
Fitar sa ke da wuya ya cikaro
da ita a tsakar
gida tana sanye da atamfa
shudiya da kuma
dan fingilin gyale. Hakika
zatonsa ya zama
gaskiya domin kuwa wacce yake
tsammani ce
ya gani. Suka yiwa juna
murmushi, Nazifi ne
ya fara yi mata magana.
.
"A'isha da ma ashe ke
ce...?"
Ta jefe shi da murmushin
Allah kashe ni don
dadi, sannan ta ce da shi.
"Kai da wa kake
tsammani?"
"Ban yi tsammanin ki ba,
domin kuwa na
dauka cewar tuni kin mance da
ni A'isha."
Ta sake jifan shi da wani
murmushi.
.
"In ban da abinka Nazifi
ka taba ganin inda
mace ta mance da mijinta? Ko
ba ka san
cewar ni a matsayin mijina
nake daukarka ba,
ko ka mance da alkawarin da
na daukar maka
ne in dai ina da miji a
duniya ai kai ne
Nazifi."
.
Ya lumshe idanu don farin
ciki, a zuciyarsa ya
ce Allah ya sa haka ya zama
gaskiya A'ishata,
sannan ya ce da ita.
.
"Zo mu shiga daga ciki
A'isha nan ba wurin da
za mu tattauna matsalolinmu
ba ne."
Suka shiga cikin dakinsa,
rufin kwano doron
zabuwa amma kuma babu silin
babu komai a
ciki idan aka tsame dan
tsurkun gadonsa na
katako mai kama da makara da
kuma wata
kujera daya ita ma ta katako
mai kafa uku da
rabi. A'isha ta yi wa kujerar
kallon nutsuwa
kafin ta sami mazauni a
kanta, domin kuwa
tunda suka shigo cikin dakin
ta dubi
rubabbiyar kujerar ta fara
zullumin cewar da
wahala kujerar ta iya daukar
nauyin mutum
dukansa
.
To amma kuma cikin sa'a sai
kuma
ta dauke ta gaba daya, duk da
yake dai takan
nemi ta turgude a dalilin
nakasar da ta yi na
gutsurewar rabin kafa guda. Nazifi ya fada
kan gadon katako
. Da farko A'isha ta yi
tsammanin gadon zai baje a kasa, to amma
abin mamaki sai ta ga shi ma
gadon taurin rai
gare shi irin kujerar, bai yi
komai ba sai dai
burari da raki domin kuwa
ko'ina a jikinsa ihu
yake yi da zarar an motsa.
.
Saurayin da budurwar suka
kalli juna cikin
nutsuwa, Nazifi ya fara
magana "A'isha ina
fatan ba ki samu wata babbar
matsala ba a
wurin mahaifinki, domin kuwa
ransa ya baci
sosai a dalilin ganina da ya
yi tare dake."
.
Ta ce da shi "Kai zan
yiwa wannan tambayar
ka riga ni Nazifi, domin kuwa
tun rabuwarmu
nake faman zullumin ina fatan
bai doke ka ba
Nazifi."
Ya yi ajiyar zuciya.
.
"Bai doke ni ba amma
kuma gara ma a ce
duka na ya yi da abin da ya
sanar da ni. Ya
gargade ni kada in sake
kusantar inda kike
A'isha. Wannan kalami da ya
yi ya sosa
zuciyata, a dalilin haka ne
na sami kaina a
cikin wani hali mawuyaci. Tun
wannan lokaci
ban sake fita ko waje ba
kullum ina nan a
daki ina jimamin rabuwata da
ke domin ni
ban ma yi tsammanin zan sake
ganin ki ba
har abada, A'isha."
.
Ta yi murmushin karfin hali.
"Duk wannan bai kamata a
ce sun sa ka
tsorata ba, domin ni kaina ya
sha yi mini
wannan barazanar, don haka ka
kwantar da
hankalinka Nazifi, aski ya
riga ya zo gaban
goshi."
.
Ya dube ta cikin rashin
fahimta, "Kamar yaya
ban gane ba?"
Ta sake yin murmushin.
"Abin da nake nufi
shine wahalar mu ta zo karshe
in dai ka
shirya, kuma da gaske kana
kauna ta har cikin
zuciyarka kamar yadda ni ma
nake kaunarka"
Ta dan saurara sannan ta ce
da shi a sanyaye.
''Nazifi ka shirya gobe mu je
a daura mana
aure.''
.
Saurayin ya ji gabanshi ya
fadi ras da kalaman
suka dira a cikin dodon
kunnen shi a bazata,
kadan ya rage ya fado kasa
don tsananin
razana.
.
''A`isha aure fa kika ce?''
Ta dube shi har cikin
idanunsa ta ce da shi.
''Aure mana Nazifi ko ba ka
shirya ba ne,
dama yaudarata kawai kake son
yi ban sani
ba."
.
Saurayin ya dubi kwayoyin
idanin `yar
budurwar da ke zaune akan
kujera ta sa shi a
gaba, ya tabbatar lafiyar ta
kalau ba tabin
hankali ta samu ba, ya ce da
ita cikin mamaki.
.
"A'isha kin taba ganin
inda saurayi da
budurwa kawai suka ware kansu
suka aurar
da kansu ba wasu shaidu ko
waliyyai, sannan
kuma ya za a yi a ce
gobe-gobe ba wani
shirye-shiryen komai."
.
`Yar budurwar ta ce da shi
"Ni ba cewa na yi
ka sayo min akwatuna ba,
sadaki kawai nake
so a wurinka, shi ma don ya
zama dole ne, da
ba zan bukaci komai a wurin
ka ba kuma shi
din ma sai abinda ka kawo ka
ba ni. Malamin
da zai daura mana aure da
shaidu, kai ko ma
mene ne ake bukata ba za mu
sha wahalar
samu ba.
.
Wannan alhakin ka ne ka nemo mana malami wanda
zai daura mana aure
cikin sirri daga mu sai mu
sai shi. Daga nan
kuma sai ka samar mana wurin
zama na sirri
.
Duk wadannan abubuwan ne da
ya kamata a
ce ka shirya su a gobe domin
kuwa idan abin
ya wuce gobe, to mun rasa
juna kenan har a
bada."
.
Shiru bai ce da ita komai ba
domin kuwa
maganganun da take fada duk
sun gama sa
shi tsurewa. Zuwa can sai ya
ce da ita cikin in-
ina "To ai ni a gaskiya
A'isha wallahi abin ne
ya zo mini duk a kurarren
lokaci, kuma bayan
haka kin dai gani da idanunki
wallahi ba wani
wadata ne da ni ba kuma ba
wata
kwakkwarar sana'a nake yi ba.
sannan...."
,
Ta katse shi cikin damuwa.
.
"Duk da haka dai na
tabbatar a matsayinka na
namiji indai har ka yi niyya duk wadannan
abubuwan ba za su gagare ka
ba, in dai har
kana sona da gaske to bai ma
kamata ka tsaya
ka kawo mini wadanan
matsalolin ba,
kasancewar dai ko rance ka
nema a wurin
abokan sana'arka ba za ka
rasa samu ba. Ba
wasu kudin ba ne masu yawa za
ka tanada ba
Nazifi, sadaki kawai fa na ce
ina bukata, daga
nan kuma sai 'yan kudin da za
a baiwa
limamin da zai daura auren,
don mu rufe
bakinsa kada ya tona mana
asiri. Haba Nazifi
ka yi tunani fa ka gani,
akwai wanda ya kashe
miliyoyin kudi a kaina, amma
na ce ba na
kaunar shi sai kai Nazifi,
amma kuma kana
nema ka ba ni kunya, ka kware
mini baya."
.
Ya yi saurin cewa da ita
"Ba haka ba ne
A'isha, ke kina ganin kamar
ba na son
al'amarin ne, wallahi ina so.
To amma
matsalolin da ke tattare da
al'amarin nake
hangowa. Idan fa muka yi
auren nan a boye,
muka nemi wurin zama dole ne
a yi bincike
don a gano inda kike a garin
nan, kuma abin
duniya ba ya boyuwa, dole ne
asirin mu ya
tonu wata rana, don aure ba
abin wasa ba
ne."
.
"To sai me don an gane
daga baya in dai mun
yi auren? Ai shi kenan, ka
san dai duk duniyar
nan idan an taru ba mai raba
mu, tunda
muna son juna. Kuma wai kai
tsoron me ma
kake ji? Sai ka ce ba namiji
ba. Rigima wa ta
kashe a duniya? Mu yi auren
nan shi ne mai
wahala, komai zai biyo baya
ya ma biyo. Ni fa
mace ce Nazifi amma har in ce
na ji na gani a
kan soyayyar mu, amma kai
kana namiji ka
tsaya kana fargaba. Ni
wallahi ka fara ba ni
kunya Nazifi."
.
Ta kura mishi idanu a yayin
da ya yi shiru
yana mis-mis da baki, yana
kokarin fitar da
tunani daya tsakanin amincewa
da kuma
sabanin haka, daga nan sai ta
cigaba da ta ga
bai ce komai ba.
.
"Idan kuma kana ganin ba
zai yiwu ba, shi
kenan ba matsala sai in tashi
in yi tafiyata, ka
nuna mini kenan da ma ba
kauna ta kake yi
ba, sai in je in rungumi
kaddara in auri
wancan saurayin da ba na
kauna a zuciyata,
wanda shi kuma yake sona
kamar ya hadiye
ni. Ba komai Nazifi, dama an
ce son maso
wani koshin wahala."Ta
mike daga kan musakar kujerar da niyyar
ficewa. Nazifi ya yi farat ya
ce da ita, bakin sa
na rawa.
.
"Ki gafarce ni A'isha,
abin bai kai mu ga haka
ba. In dai don wannan maganar
ce kina
bukatar komawa ki zauna, na
amince zan yi
duk abin da kika ce da ni. Ni
dai a halin yanzu
ko sisi ba ni da shi a
aljihuna, to amma kuma
tunda kin ce da ni rigima ba
ta kashe uban
kowa, to ni ma zan jarraba
yin ta, don na san
ba za ta kashe ni ba. Domin
kuwa ba karamar
rigima ba ce mutum ya tunkari
aure awoyi
ashirin da hudu masu zuwa
sannan ya nemi
gidan haya, da kuma kudaden
limamin daurin
aure duk kwana daya kacal,
amma kuma bai
tanadi ko ahu a aljihunsa ba,
ke ma kin san
wannan katuwar rigima ce,
A'isha."
.
___________
Tab malam Nazifi kwarankwasa
maganarka dutse ce,
Don da rigima na kisa, da
wannan typing din bai zo gareku ba sakamakon rigimar dana jajibo ma kaina
shekaran jiya, sai de dakyar na sha yayin da fuskata ta suntuma suntum, idanuwa
na sukai luhu luhu, sakamakon dukan da na ci wajen .........
Kaga su o'o da o'o an kasa
kunne don jin tsurku to na fasa bada labarin, its shuraih 99%
.
Part 9 is loading
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 9
.
Washegarin ranar tun da
sassafe misalin
karfe bakwai, Nazifi ya fara
zirga-zirga a cikin
garin yana fafutukar nemo
rancen isasssun
kudin da zai rike
,
kafin nan da wadansu awoyi
in dare ya yi, domin kuwa a
yadda suka rabu
da 'yar budurwar ta ce da
daddare za ta zo ta
same shi su wuce wurin daurin
aure.
.
To amma kuma tun a jiya din
bayan sun rabu
yake ta faman cuku-cukun inda
zai sami kudin
da yake bukata, amma kuma shi
dai a iyaka
kokarin sa bai san inda zai
samo wadannan
kudi ba.
.
Sannan kuma bugu da kari ba
shi da wata
tsohuwar ajiya ko kuma
wadansu kadarori
ballantana ya daga su ya
makar don ya sami
kudaden da yake bukata. Ya
san cewa in dai
ba tsohon kekensa ba to da
wahala ya sami
wani abu da zai sayar, wanda
kudinsa za su
kai dubu daya, ko suturunsa
ya daga ya sayar
ya san cewar ba za su samar
masa kudin ba.
.
Don haka ya kasance cikin
rashin kwanciyar
hankali ko wani barcin kirki
bai yi ba.
Duk mutanen da Nazifi yake
tsammanin zai
sami kudi a wurinsu, da kuma
abokansa duk
ya bi su daya bayan daya amma
kuma Allah
bai sa ya dace ba
.
Da rana ta take misalin karfe
sha biyu sai Nazifi ya zauna a makarin
wata kwalbti dake bakin titi,
yana tunanin
inda zai sake dosa kuma gashi
lokaci
kara kurewa yake yi.
.
Nazifi yayi ajiyar zuciya,
sannan ya mayar da hankalin shi kan motocin
da ke wucewa ta gabashi ya
yiwa kansa
murmushi, da ya yi tunanin
cewar wai saura
bai fi awoyi takwas masu zuwa
ba ya zama
ango, amma kuma babu ko ahu a
aljihunsa,
.
gashi kuma wata azababbiyar
yunwa ma yake
ji, ko abin da zai sa a cikin
shi bai mallaka ba
amma kuma wai a yau ne zai
tare da sabuwar
amarya, wacce wani ya kashewa
kusan
miliyan guda don a mallake
ta, lallai wannan
shi ne daukar dala ba gammo.
.
To wai shin me zai sa ma in
dami kaina ne?
Nazifi ya tambayi kanshi
lallai fa bai kamata
ba ma ya tsaya yana damun
kanshi, domin
kuwa ita ta ce ta ji ta gani,
ko ba shi da ko
sisi, ya san cewar za ta san
inda za ta samo
masa kudaden tun da dai ta
riga ta mutu akan
kaunarsa.
.
Ya sake yiwa kansa murmushi
sannan ya ce a bayyane.
"Kada ka damu Nazifi, ko
baka da ko sisi yau
sai ka zama ango a duniyar
nan, kuma sai ka
tare a dakin kyakkyawar
amarya, wacce
farashinta ya zo daidai da
naira miliyan..."
.
Bai gama tunanin ba ya ji dirar
zukekiyar
motar a gabanshi, ya dawo
hayyacinsa cikin
kaduwa a lokacin har gilashin
motar ya sauka
kasa
,
suka dubi juna shi da dogon
saurayin
dake cikin motar, shi kadai
sanye da bakar
kwat, yana murmushi. Da farko
Nazifi bai
gane shi ba, domin kuwa rabon
da a ce sun
hadu da wannan saurayi tun a
makarantar
sakandire, inda suka gama
tare, to amma a
halin yanzu ya kara girma da
kiba da ba don
tun a wancan lokaci sun shaku
ba, to har ga
Allah da Nazifi bai gane
babban abokinsa Gali
ba.
.
"Nazifi me kake yi a nan
zaune, lafiya"
Nazifi ya mike ya dafa tagar
motar ya ce
dashi cikin mamaki "Gali
ashe dama kana
duniyar nan"
Saurayin ya yi dariya.
.
"Ina nan a raye Nazifi,
ina nan a garin
wallahi"
Samarin biyu suka gaisa cikin
farin ciki nan
suka tuna da tsohuwar
abotarsu tun suna
makaranta.
.
"Wallahi Gali na cire
tsammanin za mu sake
haduwa, domin kuwa tun
shekara da shekaru
na neme ka har na gaji."
Amma kuwa har
yanzu tunanin awoyin da suka
rage ta zo ta
same shi ne zuciyarsa.
Gali ya ce da Nazifi ya bude
bangaren mai
zaman banza ya zauna suka
sake gaisawa da
Gali babban aminisa. Gali ya
ce da shi.
.
"Na san cewar dole ne ka
yi mamakin
bacewar da na yi shekara da
shekaru Nazifi,
ba na kasar ne domin kuwa tun
bayan gama
makaranta ni ban ci gaba da
karatu ba, sai na
shiga aikin soja, aka turani
kudancin kasar
nan, daga baya kuma da za a
je sasanta
rigimar kasar Saliyo aka diba
har da ni.
.
Tun wancan tsawon lokacin
muna can sai bara aka dawo da mu, shi ne na dawo gida a halin
yanzu don in yi aure, domin
kuwa wallahi
abokina mun sami alheri sosai
a dalilin
wannan yaki da muka je."
.
Nazifi ya ce da shi cikin
yake-yake, dariya-
dariya.
"Ai na ga alama wallahi
mutumina ka sami
hutu, mu muna nan har yanzu a
rabe muna
ta `yan buge-buge, amma ba
wani canzawa
kullum muna guri guda."
.
"Tun bayan gama
makarantarmu me ka yi
Nazifi?"
Ya yi ajiyar zuciya sannan ya
ce da shi.
.
"Ba na aikin komai Gali,
kawai dai ina dan
taba sana'ar kafinta wacce
nake dan samun na
batarwa a cikinta"
.
Gali ya dan nuna damuwarsa a
fuska sannan
ya ce da shi.
.
"Rayuwa kenan Nazifi sai
hakuri, ka san
cewar kowa rabon shi yake
samu a duniya
mutum bai wuce rabon shi
Nazifi."
.
Nazifi ya yi murmushi a
zuciyarsa yace "Ni
kuwa na san haka tunda gashi
ba ni da ko ahu
amma zan auri kyakkyawa wacce
wani
miloniyan ke burin ya aura a
duniya."
.
"Yanzu zaman me kake yi
a nan kai kadai
cikin rana, Nazifi?"
Ya sake yin ajiyar zuciya,
"Wallahi wannan zaman da
ka ga na yi Gali
ina cikin wata katuwar
matsala ce wacce ta fi
karfina."
.
Gali ya yi masa murmushi ya
ce da shi.
"Ni kuwa ban yi tsammani
cewar a wannan
halin da nake ciki har akwai
wanda zai ce ya fi
ni shiga matsala ba,
matsalarka ba ta kai ko
rabin wacce nake ciki
ba"
.
Nazifi ya ce dashi.
"Haka dai ka ce Gali
amma da a ce za ka ji
matsalata, kai da kanka za ka
san cewar ta fi taka matsalar" fada min matsalar taka na ji ni kuma zan
fada maka tawa matsalar." Nazifi ya kurawa gilashin
motar idanu ko kiftawa ba ya
yi sannan ya ce
da abokin nasa
.
"A halin yanzun da ka
ganni a nan Gali, yau
ne za a daura aure na kuma a
yau ne zan
nemi gidan da za mu zauna ni
da amarya,
amma kuma ko sisin kwabo ba
ni da shi a
aljihuna
.
Ka san cewar ina cikin
matsala maigirma, Gali"
Gali ya tuntsire da dariya.
.
"To kai Nazifi ya aka yi
ka daukowa kanka
wannan rigimar, ka san cewa
ba ka da ko sisi?
sai ka ce za ka auro `yar
tsana ba mutum
ba?"
.
Nazifi ya dube shi sosai ya
ce.
"Wallahi rigima ce kawai
Gali, bari ka ji yadda
abin ya faru. Tun farko
yarinyar ce ta like
mini na rasa yadda zan yi da
ita shi ne ta ba
ni zabi ko dai in nemo kudi a
daura auren a
yau din nan ko kuma mu yi
hannun riga
ma'ana mu rabu , to ni kuma
ina bala'in son
yarinyar nan Gali, kullum
tana raina, shi ne
na yi mata karya zan nemi
kudin amma har
yanzu da ka same ni a nan ko
kwabo bai zo
hannuna ba, kuma anjima za a
daura
aurenda daddare"
.
Gali ya yi ajiyar zuciya
sannan ya ce.
"Eh, to kai ma kana
cikin matsala Nazifi, to
amma kuma dai har yanzu ina
jin matsalata
ta fi taka domin kuwa ni ma
gobe ne za a
daura aurena da wata yarinya,
na kashe kudi
sun kusa miliyan daya a kan
wannan yarinya,
.
to amma kuma ba ta kauna ta
ko nan da can.
Ko jiya da na je wurinta da
zage-zage muka
rabu amma kuma gobe ne za a
daura mana
aure domin kuwa tuni har na
gama rarraba
katin gayyata, Nazifi."
.
Nazifi ya ce da shi "Ina
ban da abinka Gali me
ya ja maka yin wannan
tabargaza? Yaya za a yi
bayan kasancewar yarinyar ba
ta kaunar ka
amma kuma ka kashe mata
wadannan uban
kudade sai ka ce za ka auri
`yar zinariya, ba
wacce take da jini irinka
ba?"
.
"Wallahi Nazifi ni ma
dai rigima ce kawai ta
sa ni yin wannan aika-aikar
domin kuwa irin
ciwon son yarinyar nan da
nake shi ya sa na
turawa iyayenta wadannan
makudan kudade,
domin kuwa na san cewar duk
tsiyarsu dai ko
ba sa so dole ne su ba ni
yarinyar, tunda dai
ba za su iya biyana kudin da
na kashe ba."
.
Abokan biyu suka tuntsire da
dariya a lokaci
guda hade da tafa hannuwa.
Nazifi ya ce da
abokin nasa.
.
"Kai rigima dai ba ta
karewa a wannan
duniyar Gali, in kana duniya
ka ga tsiya iri-iri,
wato in da za ka san cewar ni
dan tsiya ne,
bani da kirki abokina, wani
miloniya ne fa ke
son yarinyar nan tawa amma
kada ka ga
yadda take kwabsa shi
.
An ce wai da motoci yake zuwa
wurin ta zuka-zuka, amma kuma na kwace mishi ita."
Suka sake fashewa da dariya
Gali ya ce
.
"Ai ni har yanzu ban ma
gano nawa abokin
karawar ba, wallahi na rasa
dan iska da ke
hurewa tawa budurwar kunne a
garin nan. To
amma ina nan ina zuba idanu
sai na gano dan
banza."
.
Ya rage fara'a sannan ya ce
da abokin nasa.
"Ka san abin da zan yi
masa kuwa Nazifi?"
Nazifi ya girgiza kai cikin
rashin fahimta. Gali
ya dan yi busasshen murmushin
mugunta
sannan ya ce da shi.
.
"Harbe shi zan yi da
`yar kaunar bindigata."
Suka sake yin dariya a lokaci
guda, amma
shi Nazifi yake-yake yi ba
dariya ba, domin
kuwa bai taba tsammanin irin
wannan tunani
na kashe mutum a zuciyar
abokin nasa ba.
.
To amma kuma abin da bai sani
ba, shi ne
abokin nasa yafi jin tausayin
kashe kiyashi
fiye da kashe mutum. Gali ya tattara
hankalinshi wuri guda sannan
ya ce da Nazifi.
.
"Kada ka damu Nazifi zan
magance maka
matsalarka gaba dayanta, daga
nan kuma sai
mu dawo ni ma ka taya ni don
mu magance
tawa matsalar.
.
Yanzu dai da farko zan ba ka
gida da zaka zauna kai da amaryarka domin
kuwa ina da sababbin gidaje
har guda uku a
garin nan duk gaba daya na
ginasu, sannan
kuma zan ba ka isassun kudin
da za ka yi
hidimar komai da komai na
wannan aure."
.
Nazifi ya ji numfashinsa ya
dauke, don
tsananin murna, "Na gode
sosai Gali, wallahi
ka yi bala'in `yanto ni
mutumina"
.
Gali ya jawo wata bakar jaka
da ke bayan
motar, ya dorata a kan cinyar
Nazifi, sannan
ya danna wani kwado murfin
jakar ya bude.
Nazifi ya some a zaune, jakar
dankare take
da 'yan dari biyar-biyar
sabbi fil da su, suna
ta daukar idanu. Gali ya dafa
kafadarsa cikin
tsokana sannan yace da shi.
.
"Kai banza na ga duk ka
bi ka wani rude sai ka
ce ka ga wasu kudin arziki Ka
da ka damu Nazifi ba su da yawa rabin
miliyan ne, da ma yanzu na je
banki na amso
su, Allah ya sa rabonka ne,
ka je ka yi
hidimar aurenka da su."
.
Nazifi ya dubi abokin nasa a
rude ya ce da shi
cikin kidimawa "Duka ka
bar mini Gali?
Rabin miliyan fa ka
ce...?"
Gali ya daga masa girar
idanunsa sannan ya
ce da shi.
.
"Eh, rabin miliyan ne
Nazifi, ko sun yi maka
kadan ne in kara maka kamarsu
su zama
miliyan guda?"
.
Nazifi bai gasgata kunnuwansa
ba.
________
Hehe Rikici bata kisa amma da
alama zata fara takan Nazifi
SOJA GALI yayi tabargaza,
shin meye tunaninku alokacin daya gano budurwarsa daya rage saura kwana biyu a
daura masu aurene, Nazifi zai aura, kuma zasu zauna cikin gidansa, me zai faru
.
GWARAMA KENAN
Its shuraih 99% ________________
BABI NA HUDU|
.
Dogon malamin wanda ke sanye
da dogayen
kaya farare rike da dogon
carbi a hannunsa
ya gyara zaman katon nadinsa,
wanda ya
mike tsawon bayan sa ya
kwanta, kamar
wutsiyar doki, ya dubi
saurayin da budurwar,
wadanda ke zaune a gaban shi
suna
sauraronsa kamar wadanda ke
daukar darasu
ya ce dasu cikin girmamawa,
.
"Yara me yake tafe
daku?"
Nazifi da A'isha suka dubi
juna a sannan
lokaci guda suka yi ajiyar
zuciya, domin kuwa
shi dai Nazifi tun kafin su
zo wurin malamin
da ma yana shakkar da wahala
idan za su yi
nasara, to amma dai a yadda
ya ji ana kishin-
kishin tabbas ya ji an ce wai
wannan malami
dan tsubbu ne shi ya sa ya
zabi su zo wurin
sa, domin kuwa ya san cewar
zai dan fi saukin
kai in dai suka nuna mishi
makudan da ke
hannusu
.
Nazifi ya dan yi masa
murmushi sannan ya ce da shi.
"Mhm. da ma malam wata
`yar matsala ce
ke tafe da mu zuwa
wurinka."
.
Malamin ya sake gyara zaman a
kan tafkeken
buzu, sannan ya gyara zaman
nadinsa mai
kama da mushen jimina, domin
kuwa tun
zuwan wadannan yara biyu
saurayi da
budurwa, ya ji kansa yana dan
sarawa kamar
zai yi ciwo, domin kuwa duk
ya rasa kansa
kamar ba mutane ba.
.
"Ni fa a gaskiya ban
gane abin da kuke nufi
ba, ban san me yake tafe da
ku ba. Ina jin da
za ku fito fili ku fada mini
matsalarku da zan
fi son haka, amma kuna ta
wasa da hankalina
sai ka ce wani karamin
yaro."
.
Nazifi ya sunkuyar da kan shi
cikin ladabi ya
ce da malamin.
"Ka yi hakuri malam
lamarin ne yana da dan
wahala shi ya sa ka ji muna
fargabar fada
maka."
.
Malamin ya shafi dogon
gemunsa ya ce da su
"Duk da haka dai tun da
kun rigaya kun zo ai
sai ku fada mini in ji domin
kuwa ina da aiki
da yawa a gabana, kun ga
yanzu dare ne
lokaci ne da muke aiki da
rauhanai, ba
lokacin tsayawa wasa ba
ne." Wannan karon
yana magana yayin da yake dan
zazzare ido don
barazana.
.
Saurayin da budurwar suka
sake kallon juna.
`Yar budurwar tana sanye da
burmemen
hijabi, tana sauraron diramar
da ake yi
tsakanin saurayinta da kuma
malamin mai
kama da rauhani, domin kuwa
ya mafi kama
da rauhanin fiye da mutane.
Nazifi ya ce da
shi kai tsaye..
.
"Alagafarta malam ka
gafarce mu, ba wani
abu ya sa muka zo wurinka ba
ni da wannan
masoyiya tawa sai kawai don
wata `yar
bukata wacce muke son ka
share mana hawaye a
kan ta."
.
Nazifi ya dan saurara sannan
ya cigaba.
"Alagafarta malam mun zo
gurinka ne don
ka daura mana aure a boye,
ma'ana ba ma
son kowa ya san da faruwar
wannan
al'amari."
,
Dogon malamin ya zaro
idanunsa cikin rudani
kana ya yi saurin dafe kan
shi. A wannan karo
ji yake kamar zai rabe gida
biyu domin kuwa
duk shekarun da ya dauka yana
wannan
sana'a ta tsubbu ya hadu da
attajirai da
talakawa, `yan kasuwa, da
kuma `yan siyasa,
kai har da `yan fashi da
makamai, amma ko
sau daya bai taba jin wani ya
zo masa da
tatsuniya irin wannan ba, sai
a wannan karon.
.
Ya gyara zamansa sannan ya
muskuta baya
kamar yana tsammanin za su
haushi da duka
a cikin dan tsurkun dakin
nasa na ganawa da
baki.
.
"Ku gafarce ni yara a
gaskiya ba ni jin zan iya
wannan aikin, ina jin sai dai
ku lalubi wani
malamin amma dai ni ba na
irin wannnan
aika-aikar."
.
Nazifi ya dubeshi cikin
damuwa.
"Ka taimake mu malam,
wannan ba wai abin
assha ba ne domin kuwa kai ma
za ka samu
lada, tun da dai raya sunnar
fiyayyen halitta
ce."
.
Malamin ya ce "Ba wai
taimakon naku ne
bana son yi ba, to amma shi
aure ba haka
nan ake yin sa kawai ba wani
bincike ba,
domin kuwa ni yanzu ba zan
iya sani ba ko da
aure a tsakaninku ko babu ba,
tunda dai ban
taba ganinku ba. Sannan kuma
ban san da
wacce manufa za ku yi auren
ba."
.
Nazifi ya sake marairaicewa.
"Wallahi malam ba wata
manufa, muna so ne
kawai mu yi aure, wadansu
matsaloli ne suka
sa za mu yi a boye."
.
"To me ya sa ba za ku sa
iyayenku a gaba su
wakilci maganar ba? Ko ba ku
da iyaye ne a
nan garin?"
.
Masoyan biyu suka sake duban
juna, kana
saurayin ya ce, "Muna da
iyaye Malam, to
amma dai wannan wani sirri ne
a tsakaninmu
da kai. Mun wakilta ka ka
zama iyayenmu,
sannan kuma ka zama waliyi a
tsakaninmu
duka, kuma kai ne
shaida."
.
Malam ya tattara carbinsa
wuri guda kamar
`ya`yan goriba sannan ya dubi
masoyan biyu
ya ce da su.
"Aure irin wannan ba shi
da kyau, ko kuma in
ce yana da matsala domin kuwa
babu
mamaki ma kun sha nono
daya."
.
Nazifi ya ce a marairace.
"Wallahi malam ba mu sha
nono daya ba,
masoyiyata ce ba kanwata ba
ce."
Malam ya sake hade fuska duk
ya yi zufa
sharkaf ya ce da su "Kai
ni fa ban taba yin
wannan aika-aikar ba, a
gaskiya sai dai ku
gafarce ni ba zan aikata
wannan tabargazar
ba, domin kuwa shi aure ba
haka kawai
ake..."
.
Maganar ta makale a makogwaronsa,
bai
samu damar karashewa ba
sakamakon
abinda ya hango a hannun
saurayin. Sababbin
`yan dari biyar ne dami guda
suna daukar
idanu. Saurayin ya ajiye
kudin a gaban
malamin sannan ya ce da shi
.
"Amincewarka muke bukata
ba wa'azinka ba
Malam, domin kuwa ba haka nan
za mu barka
ba. Idan ka amince ka dauki
wannan duk naka
ne ladan aiki. Idan kuma ba
ka amince ba shi
kenan sai mu dauke kudinmu
muje gaba wani
malamin ya daura mana auren.
To amma dai
me ka gani?"
.
Malamin ya sake gyara zama
kamar wanda
yake zaune a kan kunama, ya
sake duban
kudin a halin yanzu bayan
ciwon kan da yake
ji har wani abu kuma yake ji
yana tsikarar
hakarkarinsa da cikin
zuciyarsa. Ya yi ajiyar
zuciya sannan ya ce da
saurayin.
.
"Kada ku damu yara zan
dan yi shawara. Mu
gani, ni dai a gaskiya ban
taba irin wannan ba,
to amma dai tunda kun ce a
taimaka muku ai
dole ne a taimaka muku din.
Ina ganin ba
wata matsala ta yanka maka
sadaki ka biya,
yanzu nan ma sai a daura muku
auren, ku yi
tafiyarku."
.
Yana gama fada ya warce damin
kudin, ya
bankada karkashin tafkeken
buzunsa ya watsa
su ciki. Duk fa wa'azin da ya
yi musu a baya
duk ya mance.
.
_____________________________________
Shuraih 99%
.
"Ku yi hakuri Gali,
wallahi ni kaina ban ji
dadin faruwar wannan mummunan
al'amari
ba. To ka san zamani ya
canza. Wallahi ni
kaina ban san lokacin da
yarinyar nan ta
lalace haka ba, ban taba
tsammanin zata iya
guduwa ta bar gida a kan
wannan maganar
ba."
.
Gali da ke sauraron Alhaji
Dage ya hade
fuskar shi.
''Agaskiya Alhaji ba zan
yarda da duk abinda
za ka fada mini a kan wannan
al`amari ba.
Ta yaya ma za a ce in gama
raba katin
gayyata, anjima nan jama`a fa
za su fara
zuwa kofar gidan nan don
daurin aurena da
yarinyar nan, amma ka ce da
ni wai tun
daren jiya ba a san ma inda
take ba
.
Dole ne a nemo mini matata,
in dai ana son zaman lafiya.''
Alhaji Dage ya gyara zaman
faskeken
tabaronsa, wanda ya fi
fuskarsa sai ka ce
wazirin akun magana jari.
"Bai kamata a ce ka yi
saurin fushi haka ba
Gali, domin kuwa wannan
yarinyar dai ba za
ta bata ba a garin nan. Koda
bayan an daura
auren dole ne a nemo ta, dole
ne a gano
inda ta shiga."
.
"Haba Alhaji, to amma
saboda Allah yaya za a
ce an daura mana aure ba
amarya? Kai ma ka
san cewa wannan ba karamin
tonon asiri ba
ne a gare ni. Ya kamata dai a
san abinda ake
ciki kawai."
.
Siririn mutumin ya share zufa
de ke kan
dokin wuyansa. "Wallah
ni kaina ban san me
yake damun wannan yarinyar
ba. To ka san
bai yiwuwa ka haifi yaro
sannan kuma ka haifi
halinsa, wannan hali nata ni
ban san inda ta
samo shi ba, domin kuwa daga
ni har uwarta
duk mutanen kirki ne
wallahi."
.
Gali ya harari mutumin a
fakaice, a zuciyarsa
ya ce "Kana matsayin
mutumin kirki amma
ka damfare ni kusan miliyan
guda, don kawai
za ka ba ni 'yarka?" To
amma dai a zahiri
cewa ya yi da shi, "Ni
dai ka ji bayanina
Alhaji, in dai har ba a gano
mini amaryata ba,
to ina jin mu duka sai kawai
mu yi hakuri da
maganar. Domin kuwa jiya aka
daura auren
abokina, muna so ne mu hada
bukukuwanmu
rana daya da aurenmu, amma
kuma ni a ce
wai ba a ga tawa amaryar ba.
Wannan ai
tonon silili ne ake nema
kawai a yi mini."
.
dan motsattsen mutumin ya yi
ajiyar zuciya,
jikinshi ya soma kyarma domin
kuwa a yadda
ya lura da kwayoyin idanun
saurayin ya san
cewar abubuwan da yake fada
har cikin
zuciyarsa abinda yake nufi
kenan.
.
"To ni yanzu don Allah
me kake son in yi
maka? Ai'sha dai ni na haife
ta, kuma ta
kwashe kayanta ta gudu ta bar
gidan nan, me
kake so yanzun in yi maka,
tunda ka ce ba ka
yarda ba?"
.
Saurayin ya sake hade fuska
sannan ya ce da
shi.
"Ai ba wani abu ba ne
mai wahala, ina ganin
Alhaji, in dai ban takura
maka ba, ai ina gani
ban yi laifi ba idan na ce ka
shiga cikin gida ka
tattaro min kudadena da na
kashe tun farkon
soyayyata da 'yarka A'isha.
Domin kuwa idan
har za ka iya tunawa ka amshi
manyan
kudade a wajena, kuma kai ma
ka san dai ai
ba kyauta na ba ka su ba,
domin kuwa inda a
ce ni talaka ne ba ni da
kumbar susa, na
tabbata daidai da rana daya
ba za ka taba
barina in zo kofar gidanka
har in furta ina
neman 'yarka ba
.
Don haka ni ma na rika ba ka kudaden da kake
bukata, na san dai ba ka mance ba da su ba."
Saurayin ya dan yi murmushin
takaici sannan
ya ci gaba da shaidawa
ramammen tsohon
.
"Tun fara neman auren
A'isha na fara lissafin
abubuwan da nake kashewa a
dalilinta, kai
hatta man da nake zubawa a motata
in zo
wurinta, da kuma kudin da
nake baiwa yara
su kira min ita, duk ina
rubutawa. A halin
yanzu lissafi ya yi kauri,
domin kuwa kullum
sai na ciro doguwar takardata
ta lissafi, na yi
bitar kudaden da ke cikin
akawun dina da
wurinka
.
Don haka na ba ka awowi goma
ka
tattaro min kudadena. In ba
haka ba, ka ji na
rantse maka da Allah, sai na
dankara ma ka harsashin bindiga,
tsohon banza makwadaici kawai
macuci!"
.
Gali ya bude kofar motar a
fusace ya shiga ya
tashe ta. Ya juyo ya dubi
motsattsen
mutumin, wanda a halin yanzu
ko'ina a
jikinsa kyarma yake yi hatta
fuskarsa da ke dakon faskeken tabaron
ita ma kyarma take yi, duk da
uban kayan da
aka jibga mata,
.
"Kada ka damu Baba, na
ga ka rude, ai kudin
ba wasu masu yawa ba ne,
miliyan daya da
dubu dari bakwai da hamsin
kawai, sai naira
dari uku da talatin da
biyar." Ya fizgi motar ya
fice a guje daga kofar gidan
.
Motsattsen mutumin ya bi
kurar motar da kallo. A daidai
lokacin ne faskeken tabaron
ya kubuce daga
'yar mitsitsiyar fuskar tasa,
ya fadi kasa. Tuni
har ya fara tsammanin hawan
jini.
.
___________
Shuraih 99%
Iyaye ayi hattara da amsar
kudi ko wani abu a hannun siriki kafin Aure
.
Duniya ta lalace da cin hanci
wai har MALAMAN ADDINI suna RASHAWA
._____________
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 11
.
____________
Tsawon mintuna biyar
mafadaciyar matar na
ta faman yiwa mijin nata
banbami. Yana
tsaye kawai yana duban ta,
sai zufa ke ta
faman kwararo masa, tana wanke
masa
fuska, kamar ana yi masa
sakiya
.
Ya rasa da me zai ji tsakanin masifar da kuma
gargadin da surukinsa ya zo ya yi masa. Ya san cewar
wannan saurayin dan
bindiga-dadi ba hankali
ya cika ba, kamar yadda da ma
ya dade yana
jin ana cewa ba duk soja ne
ke da cikakken
hankali ba
.
Hakika yana iya aikata duk
abubuwan da ya fada, ga shi
kuma yanzu
Juma ta tuso shi a gaba da
tata masifar.
.
Duk ya rasa abinda ke masa
dadi a duniya.
"Kawai aikin banza
Malam, ka jawo min 'yata
kwalli kwal da nake alfahari
da ita a duniya ta
tattara kayanta ta gudu, da
ma haka kake so
sai ka zuba ruwa a kasa ka
sha, burinka ya
cika."
.
Alhaji Dage ya yi shiru, bai
ce da ita kala ba,
domin kuwa ya san cewa yanzu
ba lokacin
tankawarsa ba ce, don kuwa
har ga Allah
matar tasa ta tunzura. Ya san
cewa idan ya
biye mata, tana iya kama shi
da kokawa,
kuma ba ya kokwanto ya san
cewa shi za ta
kayar
.
Shi ya sa ya rufawa kansa
asiri ya rabu
da ita, in ta yi ta gaji dai
ai dole ne ta bari.
Juma ta sake cewa da
motsattsen mutumin
cikin kwarmato kamar za ta
hadiye shi.
.
"Wai me kake nufi ne
Alhaji, ba ka ce komai
ba. Ko kuwa kana nufin shi
kenan, kai ka
cinyewa mutane kudi, ni kuma
ka bar ni da
asarar 'yata. To ai sai ka
sake tunani, don
kuwa ba kyale ka zan yi ba,
duk inda 'yata ta
shiga sai ka je ka kwakulo
min ita, in dai kana
son zaman lafiya a duniyar
nan, to wallahi ka
nemo min A'isha domin kuwa
duk kai ka
jawo mana wannan
masifar."
.
Ramammen mutumin ya yi ajiyar
zuciya, a
karo na farko ya ga cewar ya
kamata dai ya
dan ce wani abu. Don kada ta ga ya ki tabuka
komai, ta sake haye masa
yadda ta ga dama.
.
"Ba na son rashin
albarka, Juma." Ya ce da
ita, "Ni kike yi wa
wannan tsagerancin ko
kuwa kin fi ni son 'yar tawa
ce, da kike fada
min wadannan maganganun? Ko
kuwa ni ne
zance ta gudu ta bar gidan?
Wannan
tsinanniyar yarinya ina
amafaninta, duk ba
halinki ta kwaso ba? Ke din a
da can me ye ba
ki yi ba? Ba don yanzu an
mance, ba a tone-
tone, shi ne har kin samu
bakin magana.
Kada in sake jin muryarki a
kan maganar nan
Juma."
.
Ya zazzaro mata idanunsa da
ke cikin
fasasshen tabarau, a
tsammaninsa watakila ta
dan ji tsoro ta lafa. To amma
kuma cikin
rashin sa'a sai ya ga ta yi
shewa, sannan ta yi
tafi ji kake fas, ta ce da
shi.
.
"Lallai yau da tone-tone
a gidan nan. Au kai
nan har gori zaka yi min? Ka
mance da
abubuwan tsiyar da ka kuntuka
a baya? Haka
fa kawai nake zaman hakuri da
kai.
.
Shi ne yanzu har ka samu
bakin da za ka yi tonon
silili. To ai sai mu fara a
ji ni da kai wa ya fi
wani mugun tabo, ba tsoron ka
nake ji ba
Alhaji, mu yiyar tonon
asiri."
.
Alhaji Dage yayi saurin
tsayar da ita, da ya ga
ta sake hayewa.
"Duk wannan ba ta taso
ba, ni dai gaya miki
na yi dama don maganar da ya dace ki rika
fada, ai ba cewa na yi za mu
yi wani tone-
tone ba, don kuwa mu dai ba
yara ba ne, ya
isa a ce mun mallaki
hankalinmu a halin
yanzu."
.
Juma ta yi guda sannan ta ce
da shi.
"Ashe ka ji tsoro mai
gida. Ai na so mu
jarraba tonon silili da kai
wallahi da ka ga dan
biki da cika yau a gidan nan.
In ana fadin abin
kunya kai har ma ka sa baki a
gidan nan. In
ba abin kunya ba mene ne
amfanin karbarwa
mutane dukiya don za su auri
yarka? Haka
fa ka yi ta yi wa ragowar
yayan danginka da
ka rika a gidan nan. Ka aurar
da yan mata
sama da biyar duk a bisa
zalunci. Yanzu suna
can dakunan mazajensu suna
shan wahala ana
yi musu gori da wulakanci,
tunda dai ka
saida musu da mutunci. To ni
ba mai yi wa
yata A'isha wannan mulkin
mallakar, mu
zuba ni da kai a gidan nan
tun da kai ba ka
gudun abin kunya."
.
Mutumin ya yi ajiyar zuciya,
ba shi da ta cewa
domin kuwa duk abin da matar
ta fada
gaskiya ne duk ya aikata.
Yana jin ta ta ci gaba
da cewa da shi.
.
"Duk wanda ya sa ranshi
a kwadayin abin
duniya dole ne ya ga
wulakanci mai gida,
amma ina amfanin a ce a
matsayinka na
babban mutum wanda zai yiwa
wani nasiha a
ce kana rigima kai da
surukanka kana amsar
musu dukiya? Yanzu ga abin da
ka jawo
mana, wannan mutunci
ne?"
.
Ramammen mutumin ya girgiza
kan shi
kamar uwa na wa danta fada
"To ai laifin
yarinyar ne ni wannan tsinaniyar yarinyar
wallahi ta cuce ni.."
.
"Ka da ka tsinewa yata a
banza domin kuwa
ba ta da laifi, kai ka jawo
mana wannan
rigimar muna zaman zamanmu
lafiya. Ka san
cewar A'isha ba ta kaunar
yaron nan ka nace
a kan maganar nan don ka gan
shi da kumbar
susa, ga shi yanzu kana jin
tsoron fita waje ka
da surukinka ya harbe ka
.
Ina na taba jin irin
wannan abin tsiya ma a
duniya, ni Juma."
Alhaji Dage cikin nadama ya
ce.
.
"Kin ga laifina ne a
banza Juma, amma a
matsayina na magidanci saboda
Allah ba ni
da yanci zabarwa yata mijin
da na ga ya fi
dacewa da ita? Wani zamani
dai Allah ya kawo
mu inda yara ke kangarewa su
fi karfin
iyayensu.
.
Mu a zamaninmu wane yaro ya
isa
ya ce shi zai yiwa kansa zabi
sai wanda ya ke
so, mu kuma mutane sai mu bar
abu ya
lalace da kanmu, mu ce ai
zamani ne, da
gangan ake kyale yara suna
wannan iya
shegen da fitsarar ana kallon
su."
.
"Ba haka ba ne
maigida" Juma ta ce da shi
"Ko ka ki ko ka so
al'amura suna canzawa,
kuma zamani ya kan zo da
abubuwa iri-iri
dole kuma mutum ya bi abinda
zamani ya zo
da shi matsawar bai sabawa
shari'a ba. Ai ba
haramun ba ne don yaro ya
zabi wanda ya ce
yana so ya aura. Kuma da ka
ce a naka
zamanin ba haka ake yi ba,
kai zamaninka ka
sani, ba ka damu da zamanin
yayanka ba. A
zamanin naka ai bante ake
daurawa ba sutura
ba, me ya sa ba za ka cigaba
da daura bante a
wannan zamanin ba, tun da ka
ce ba ka
amince da canjin zamani ba,
sai ka koma
tafiya tsirara da bante, don
kuwa shi ake
daurawa zamaninka na
baya."
.
"Yanzu dai mu bar wannan
maganar" ya ce da
ita abin da ya faru dai ya
riga ya faru, dole ne
in sanar da jami'an tsaro su
shiga cikin
maganar don a kawo karshen
wannan rigima,
kafin abin ya kai mu ga
kashe-kashe don na
ga alamar abin da wannan
mahaukacin sojan
ke nufi kenan, in ya so daga
baya sai in sayar
da gidana na sabuwar unguwa
in biya shi
kudadensa, ita kuma A'isha
sai a nemo ta a
bata wanda take so."
.
Juma ta dan saki ranta ta ce
da shi.
"To yanzu da ka yi haka
kai kanka ba ka fi jin
dadi a ranka ba? Ai wannan
shi ne datattako
maigida, yanzu to ka nemi a
zauna lafiya."
Kamar aikin budar idanu cikin
yan tsararun
mintuna mafadanta ma'auratan
biyu suka
dawo cikin raha kamar ba su
ba. Shekaru
sama da talatin kenan, suna
wannan halayya,
an ce a cikin minti daya sai
su hautsine da
fada, kafin kiftawa da
bismillah sai kuma a ga
sun dawo suna dariya.
.
To sai dai kuma a wannan karon da sun san
cewar akwai wani
shu'umin saurayin da ya cika
bindigarsa da
harsashi, sannan kuma ya saya
musu likkafani
jana'iza da ba su sake yin
wata raha ko dariya
ba.
_____________
A'isha ta dubi angonta Nazifi
cikin farin ciki
sannan ta ce da shi
"Nazifi 'darling' yau dai
Allah ya cika mana burinmu,
mun zama mata
da miji. Duk duniya babu mai
raba mu ni da
kai masoyina."
.
Nazifi ya dube ta shi ma duba
na so da kauna
yana kwance a kan doguwar
kujerun da ke
cikin tsararren dakin da suke
ciki, ya ce.
"Ai ni A'isha ba ma
abinda zan iya cewa sai
dai kawai in godewa Allah da
kuma wannan
abokin nawa domin kuwa
wallahi ni dai ya
gama yanto ni, ya yi min
komai na alheri."
A'isha da ke zaune a kusa da
shi ta ce cikin
mamaki "Wai da gaske
bayan ya ba ka rabin
miliyan har kuma wannan gidan
duk shi ya ba
ka, Nazifi?"
.
"To ga zahiri ma kin
gani A'isha tun da har ga
shi kuma na shigo da ke kin
tare a ciki, ko
kuwa ke a da kin ga na yi
miki kama da
wanda zai iya mallakar wannan
tsantsareren
gidan?"
.
A'isha ta yi dariya farin
ciki.
"Mun gode masa wallahi.
Don Allah sai
yaushe zai zo don in gan shi
mu yi masa
godiya ta musamman akan
wannan abin
alheri da ya yi mana?"
.
Nazifi yace da ita "An
jima nan kadan za ki ji
ya zo ya kwankwasa mana kofa
domin
kuwa shi ma yau ake daura
aurensa da wata
yarinya a nan garin kuma mun
yi da shi zai
biyo min ya dauke ni mu wuce
wurin daurin
aure tare."
.
A'isha ta sake lumshe idanu
cikin murna ta
ce.
"Mun gode wallahi, Allah
ya bar zumunci
tsakanin mu da shi. Yaya
sunan tasa amaryar
Nazifi?"
.
Nazifi yayi farat ya ce.
"Ai abin namu ni da shi
ya zo daya domin
kuwa saboda tsabar shakuwa da
muka yi da
shi, har ankon sunan amare
muka yi, cikin sa'a
ita matar tasa sunanta
A'isha."
.
Suka yi dariya, A'isha ta ce.
"Lallai abin yayi min
dadi Nazifi, ka ce kun
samar min kawa kenan ni
ma" Suka ci gaba
da dariya abin gwanin ban
sha'awa. Suka fito
da naman kaza suka tasa a
gaba, dama tun
tarewa su gidan a daren jiya
Nazifi ya sawo
dakwalen kaji soyayyu har
guda uku. Tun a
jiya suka cikye biyu saura
ragowar daya wacce
suka baje a halin yanzu.
.
Ba abin da ya dame su, kudine
dai sun samu abin kamar daga sama, dole ne su godewa wannan abokinsu
mai farar aniya.
A daidai wannan lokaci ne
Gali ya karaso
kofar gidan fuskarsa a
murtuke kamar wanda
aka yiwa albishir da mutuwa.
Lokaci-lokaci
yakan kai hannusa cikin
aljihu ya shafi
bindigarsa. Kamar yadda ya
tsara a ransa,
.
daga nan idan ya gama gaisawa
da ango da
amarya, to farauta zai wuce
abinsa. Ba
farautar namun daji zai fita
ba, farautar
amaryarsa A'isha zai fita da
kuma saurayin da
aka ce ya sace masa ita sun
gudu. Kuma ya
sha alwashin muddin ya yi ido
biyu da A'isha
da wannan saurayi da ya sace
ta, to ba wani
bata lokaci duk aikawa da su
zai yi barzahu
.
Gali ya yi murmushin mugunta
sannan ya
sake mika hannu ya shafo
bindigarsa wacce
ke boye a cikin aljihu. Ya
daga hannu ya
kwankwasa kofar gidan a
sanyaye. A'isha da
Nazifi da ke cikin gidan suna
baiwa juna
naman kaza a baki, suka dubi
juna cikin farin
ciki a dai dai lokacin da
suka jiyo sautin
bugun kofar "Kin ji dan
halak!"
.
Nazifi ya ce
"Shi ne yake kwankwasa
kofa, Gali ne
abokina. Je maza ki bude masa
kofa ki rako
shi, A'isha."
.
Amayar ta ce da angonta a
sanyaye.
"Wata kila ma wasu
miliyoyin kudin ya sake
kawo mana 'darling'."
Nazifi ya ce "Babu
mamaki, A'isha ai na fada
miki abokin nan nawa yana
bala'in sona, ke
dai je ki bude masa kofa, ki
tarbo shi ya
shigo."
.
___________
YAU KAM RIGIMA ZATaYI KISA
.
Ya kuke ganin zata kaya
Ku biyoni Shuraih 99% a littafin
AJALI
Nazifi ya ce "Babu
mamaki, A'isha ai na fada miki abokin nan nawa yana bala'in sona, ke dai je ki
bude masa kofa, ki tarbo shi ya shigo."
.
A'isha ta mike cikin farin
cikin tana rangwada ta nufi kofar gidan.
Hakika sun yi dace ita da angonta
Nazifi, Allah ya hada ta da mai sonta kuma ita ma take kaunarsa. Ya raba ta da wannan
wahalallen da a da ya nace mata, A'isha ta ce a zuciyarta tana murmushin farin ciki.
.
Ta kama kofar gidan da
hannayenta biyu, ba tare da wani fargaba ko zullumi ba TA BUDE MASA kOFAR!
****====******
Dankareren kayataccen gidan
ne da ya kai matuka wajen tsaruwa. Jama'a da dama kan dakata don yiwa
kyakkyawan gidan kallon tsaf! saboda ginuwarsa.
Mutane da dama kan tuna da kayataccen
gidan saurauniyar ingila
dake "BUCKINGHAM
PALACE" a duk lokacin da suka dubi tsararren gidan. Wani dadin abin da ke
matukar jan hankalin jama'a ga hadadden gidan shi ne daddadan kamshin furanni
dake gewaye da gidan.
dan tsamurmurin dattijon
maigadin da ke zaune akan bencin a gefen katotuwar kullalliyar kofar gidan mai
fasalin fuka-fukan dawisu, ya dan yamutsa fuska gami da gyara rikon jaridar da
ke hannusa tamkar mai tsammanin shekowar wani a guje ya wafce ta, cikin zakuwa
ya soma bude shafukan cikin ta, a shafi na biyar ya yi ido hudu da labarin da
yayi matukar jan hankalinsa mai taken KADDARA KO FANSA!
.
A hanzarce ya muskuta gami da
gyara zama, kana ya sake kafa kwala- kwalan idanunsa akan hotunan gawarwakin wasu
mutane biyu mace da namiji da ke gefen rubutun, cikin zakuwa ya soma karantawa.
.
A safiyar jiya ne yan sanda
suka tsinci gawar
wani saurayi Nazifi tare da
masoyiyarsa A'isha.
.
An tsinci gawarwakin ne yashe
a cikin wani sabon gida bayan an harbe su da bindiga har lahira.
Tuni jami'an tsaro sun cafke wanda
ake zargi da aiwatar da kisan gillar wanda ya kasance wani matashin soja wanda shima
yake kaunar budurwar, wanda kuma har an sa ranar bikin su da ita amma kuma ita
ba ta kaunarsa.
.
Mahaifin yarinyar mai suna
Alhaji Dage ya yi
nadamar afkuwar mummunan
al'amarin sannan kuma ya tabbatarwa da wakilinmu cewar dukkan wannan al'amari
da ya afku laifinsa ne sakamakon tilastawa diyar tasa da ya yi a kan sai ta
auri wanda ita ba shi take so ba. A karshe ya yi kira ga iyaye a kan su dinga mayar
da hankali a kan dukkan abin da `ya`yansu ke bukata matsawar dai hakan bai sabawa
addini ba.
.
Sannan kuma ya yi doguwar addu'a gami da bayyana
matukar alhininsa ga mamatan
.
Don jin yadda zata kaya mu hadu
a cigaban littafin nan mai suna A’ISHA don
jin karshen sarkakiyar sarkakakken
labarin.
Na gode, naku Shafi’u
Dauda Giwa.
.........................
Anan kuma ayau muka kawo
karashen littafin AJALI amma da yardar Allah daga nan zuwa wani lokaci zan saka
maku cigabansa
.
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing Shuraih Usman 99%
....
JINJINA GA
Shafukan
Shuraih 99%
Zauran labarai
Home of Littatafan yaki and Hausa
novels
.
Ina mika sakon gaisuwata ga
ahalin kungiyar
TSANGAYAR MARUBUTA
TASKAR GIDAN LITTAFI
No comments