RAGGON MIJI 71-75
*Dedicated
to maman nour, soupnass, ikra rukayyat, maman 4H,hauwa lawal,kucigaba da
comments*💓
Jiki a mace
ya shigo dakin tabishi da ido tanata kallonshi mamaki kawai yake bata yasha
jibgarta amma bai taba yi mata wannan jina jinan ba, kenan itama watarana yakan
iya yi mata haka,
Bakin gadon
amira yaje yayi tsaye yanata kallon fuskarta da yadda take nishi zuciyarshi
takara cunkushewa yanajin tsanar kanshi ,ya dade tsaye yana kallon amira Aisha
batace mishi komi ba yajuya yafita daga dakin tabishi da ido,
Office din
doctor ya shiga yaja kujera ya zauna yana yamutsa fuska yace "me ke damun
amira? "
Doctor dake
duba wani buk ya dago face yace "she's very scared and shocked abun ya
girmi brain dinta ,that force her to fainted ,amma she'll be okay, "
Fahad yace
"what about my wife? "
Doctor okato
yakara gyara zama yace " sakamakon dukan da akamata sosai tayi miscarriage
sannan taji ciwuka sosai tana bukatar kulawa da lokaci kafin tasamu lpy "
Fahad ya
daga kai ya hadiyi miyon bakin ciki,
Doctor yace
"as ur family doctor I want to advise you, dukan mata baya taba kawo gyara
sede yabata, mata wani lokaci they're crazy se ana kai zuciya nesa ana
kaucemusu amma duka bedace dasu ba saboda they're weak , ina maka jajen rashi
da kukayi Allah ya bata lpy"
(wani lokaci
sekaga Christian da soft heart kuji yadda yake bawa fahad shawara)
Fahad yace
"thanks you"
yatashi
yafita yanajin duk duniyar tamishi zafi,
omer yakira
abba yafada mashi suna asibity kuma ana bukatar jini ba bata lokaci segashi
asibityn aka dibi nashi dana abul, aka cigaba da sawa faseelat dake kwance tana
nishi,
Duk kansu
hankalinsu tashe abba yakasa yadda da abun da yake gani,
ummi dataci
kuka tagaji tacewa abba "wlh seya saketa yata bazata zauna da meduka ba,
wannan shine karshen zamansu"
abba yace
"kiyi hakuri asiya amma kidena rantsuwa cikin bacin rai, amma ni kaina
bazanso takoma gidan shi ba"
ummi
tace"hmmmmm"!
fahad dakin
da akai admitting faseelat ya nufa ,akunyace ya tura kofar ya shiga wayam ba
faseelat basu ummi yabi gadon da kallo zuwa jinin dake sargafe ,ya karasa ya
tura kofar toilet nanma wayam hankalinshi tashe yakaiwa abunda ake dannawa for
emergency bugu ya dauki kara, duk yaburkice ko 1mnt baaiba doctor yashigo da
nurses biyu, sukaga gadon wayam se fahad dake tsaye kamar mahaukaci,
fahad
jijiyoyi amike yace "where's my wife? Ina matata where do you take her?
"
Doctor da
mamaki yagama cika shi yace "this is unbelievable, how will this happened
in my hospital? "
Ya kalli fahad
yace "I'm sorry sir bansan komai ke faruwa ba amma we have CCTV cameras
all around the hospital zamu gano mike faruwa"
Fahad ya
dafe goshi kanshi na mugun bugawa ,su ummi suka dauketa kokuwa? Yana ta
tambayar kanshi,
Doctor
yadafa shi yace "meet me in my office "
Yajuya
yafita tareda nurses ,hawaye suka zubowa fahad yace "meyasa zaku dauketa?
Ni yadace na kula daita"
Ya fita ya
nufi office na likita,likita yanata duba computer abunda yafaru akofar dakin
faseelat ya juya wa fahad computer yace "take a look at them do you know
them or seen them before? "
fahad ya
kalli computer omer ya fito dauke da faseelat ranshi yakara baci yace
"he's her brother, but saboda me zaabari sufitar min da mata a asibity su
suka kawota ?yama akai suka san we are here? bazan kara kawo patient a asibitin
nan ba tunda it's not safety "
doctor
yajawo computer gabanshi yayi rewinding lokacin da bello yakawosu kofar dakin
ranshi ya baci yaja telephone ya kira number office dinsu bello ba dadewa sega
shi ya shigo yanata hada zufa,
fuska tamke
okato yanunawa bello computer yace "meyasa ka kira wadannan mutanen waya
aike ka? meyasa ?"
bello yace
"I'm sorry nasan yayanta ne banyi tunanin fadamishi ze zama matsala ba
kuma nayi iya kokarina na tsayardasu basu tsaya ba "
fahad jiyake
kamar yakaiwa bello naushi don haka ya tashi yafita ,
okato yace
"meyasa baka fadawa securities ba?
U r suspended kaje sena nemeka "
Bello ya
fara begging "I'm sorry sir it's a mistake wlh danasan haka zata faru da
bazan kira shi ba dan Allah kayi hakuri "
okato ya
nunashi da yatsa cikin nuna gargadi yace "next time idan haka tasake
faruwa zaka bar nan harabada,now leave "
Bello yajuya
yafita yana yamutsa fuska cikin ranshi yanata regretting kiran omer,
Fahad nafita
yashiga mota ya nufi gidan umma don besan ya zaiyi ba, a mota hawaye yake tayi
duk lokacin da ya tuno ihunta da jinin da ya zuba seyaji hawayen tausayinta Sun
zubomishi,
ya samu
yaisa gidan umma suna zaune suna kallon film din su bosho munafikin mata sunata
dariyar yadda yake fadawa hafsa idris cewa jamila nagudu wari take seya toshe
hanci yake bacci saboda tusa, kwasar dariyarsu kawai suke hankali kwance ,ya
shigo main falon wuji wuji dashi riga duk jini, dukkansu faraar dake kan
fuskarsu ta gushe yaje wurin umma ya zauna kasa tana kan kujera yadora fuska
akan cinyar ta yasaki kuka,
Umma tadora
hannu ta tallabo fuskarshi zuciyarta na harbawa dasauri tace "meyafaru
fahad jinin minene ajikin ka haka? "
yana kuka
yace "umma I cheated myself na doki faseelat har tayi miscarriage "
umma dasu
lady suka dau salati "innalillahi wainna ilaihi rajiun!"
Umma kamar
zatai kuka tace "me tamaka da zaka
dauki wannan hukuncin? Faseelat ce fa ur love meyasa zakai haka? "
Muryarshi na
rarrabuwa yace "naga pic dinta da wani awayarta I tried my best nakasa
controlling kaina shine na doketa"
umma tai
shiru hawaye suka zubomata na tausayin baiwar Allah,
ya cigaba da
cewa "na kaita asibity ,wani doctor yakira yayanta yafadamishi ina komawa
nasamu Sun dauketa Sun tafi daita, ya zanyi ne umma? "ya cigaba da kuka,
Su lady suna
hawaye suka tashi sukabar main falon,
Umma tasamu
ta goge hawayen fuskarta tace "sunyi dede kuma Sun kyauta konice abinda
zanyi kenan, banji dadi ba da dana yakasance mahaukaci me dukan mata ba don duk
namiji me hankali bazaya iya daukar hannu ya daki matarshi ba ,bare faseelat
yarinya me ladabi da biyayya me sonka me addini amma har kaiya cutar daita kayiwa kanka ai don bazaka taba samun kamar
ta ba "
yana hawaye
yace "umma Dan Allah ki temakamin kije ki basu hakuri wlh inasonta
kishinta ne yasa nai haka"
umma tace
"yo kishi haukane ko kai kadai ne me kishi aduniya? Saad daya daga
cikin mubashshirina bil janna yace dazan
kama wani akan shimfidar iyali na dazan sare shi da adda kuma ta wurin kaifin
zansa se sahabbai sukaita mamakin kishinsa manzon Allah (S. A. W) yace shin
kuna mamakin kishin saad ne? yace wlh ni nafishi kishi kuma Allah yafimu kishi
gabadaya,bakai kadaine me kishi ba fahad amma ai kishi bekamata ya rabaka da
hankalinka da imaninka ba har kayi kisan kai ko agadon ta kasameshi? kasan yaya
suke daita ne? Shin kai baka daukar pic dasu lady dasu ramlat? , wai duka ne
har ze zubar da ciki wlh fahad bakayi ba ni banda temakon da zan maka sede zan
baka shawara ka koma wurin malamai kakara neman ilimi saboda da kanada ilimi
wadatacce da baka aikata haka ba "
ta dauke
kanshi tatashi zata haye sama ya waiwaya fuskarsa gwanin tausayi yace"
umma tafiya zakiyi? "
Batare da ta
jiyo ba tace"eh tafiya zanyi ko zaunawa zanyi na tayaka kukan katashi
kabarmin gida "ta haye sama ranta bace,
wasu zafafan
hawaye suka zubowa fahad dama anan kadai yake tunanin samun sauki kuma itama ta
hau ya dade zaune sannan ya tashi ya fita ya nufi gida,
Yana zuwa ya
danne horn bako dagawa baba tsoho na toilet yaji odar tayi yawa ko tsarki
besamu yayi ba yafito da gudu yaja gate din dayake sliding ne,
fahad da
kanshi ke jikin sitiyari ya dago yaja motar cikin gida,
Yakai kusan
15mnt zaune sannan yafito yashiga cikin gidan, dakin faseelat ya nufa
zuciyarshi na harbawa tuno jinin dake kwance adakin,
dakin a bude
yake yana zuwa yayi tsaye ya dafe kofa yasa sabon kuka dakin duk jini bakyan
gani, ya karasa ciki yanata kukan yayi zaman dirshan gaban gudan tsokokin dake
a wurin yana ta kallonsu yana kuka, yake tuno maganar faseelat "amma kasani
cikinnan shine farincikina shi nake burin gani ayanzu nabaka amanarshi karka
bari wani abu yasameshi"
da kuma inda
take cewa "zan haifarma baby boy kasamu freind"
Kamar dan
maye yafara magana "meyasa zaka zube?inason naganka araye banyi don na cutar
da kai ba, katafi kabarta she love you ur her happiness and joy why zaka
gujeta? it's just an accident meyasa bazaka hakura ba..." maganganun duk
gasunan yadade yana sambatu, har yakai yayi kwance agun,
can zuwa
yatashi yasamo leda ya sa hannu ya fara kwashe abinda zeiya kwasuwa yagama ya
kulle ya ajiye gefe, ya cire shirt din jikinshi ya gogge abinda yasamu yafita
ya dauko mofa yazo ya goge wurin sosai ya kuma sa fresheners duk da haka seda
dakin yadauki kanni,
yafita yaje
can garden yayi rami ya rufe ledan da rigar yadawo ya shiga toilet yasakarwa
kanshi ruwa yanata meda numfashi, yana cikin cuda jikinshi ya tuno yadda yaja
faseelat daga toilet din tana cikin cuda jikinta yakai wa bango naushi yanajin
haushin kanshi, wayar faseelat ta fado mai arai yayi sauri yafito ya dauketa
duk ta tarwatse baxata kara amfanuwa ba, ya budeta ya cire sim dinta wanda take
chart ya dauko one of his phone yasa sim din, ya sake download wats app yayi
restoring duk messages suka dawo ciki, yakoma cikin chart din ta da baffa beko
bude pic dinba yawuce gaba don kar zuciyarshi ta tarwatse , faseelat da taga
pic din tace "baffa kayi hakuri plss bansan yaakai nai missing contact
dinka ba, ya gida yasu hjya da alhaji? ashe haryanzu kanada wannan pic din yayi
kyau sosai "
Baffa yace
"lpy lau suke ,badole kiyi missing no dina ba tunda kinyi aure 😬 thank God ansamin rana jiya nima zan angwance "
faseelat ta
tura laugh emoji 😁tace "wai dagaske ?yaakai
bansaniba "
Yayi dariya
yace "young girl ,ai ummi dazakiji gunta batanan nasan kuma wannan
miskilin baze kiraki yafada miki ba "
faseelat ta
turamashi smiling face tace "namaka murna wacece ita takaini kyau ? 🤣"
yace
"kedin me kyakkyawa ce ajin karshe"
faseelat
tace "muganta in dagaske ne "
yayi dariya
yace"banda sheri fa "
tace
"Allah aa kawai inason ganinta "
seya
turomata pic din wata black beauty jibgegiya kamata😂 me dogon hanci da wawakeken baki tana da ido she's
cute de 😂🙈,
Faseelat ta
tura mishi "haba baffa wannan doshumar ina zaka ajiyeta 😂"
baffa yace
"kambuuuu matar tawa ce doshuma?"
faseelat
tatura mai "sorry sorry 🤭"
yace
"ke ni banason fararen mata ni fari ita fara abun will waste, nafison
baka me kiba shiyasa seda na darje amma
ai tanada kyau duba sosai inkuma Sheri ne sekitayi "
Faseelat
takara kallon pic din itade awurinta batada kyau abun mamaki ma yabata yadda
yake kyakkyawa amma wagga yakeso lalle so makaho ne,
Tace "
Allah yasa alheri, gaskiya tana da kyau ka gaidata kafin musan juna"
Yace
"wannan is not a villager wayayyace degree gareta akan microbiology awani hospital ma take aiki
kibari gobe innaje wurinta zan kiraki vedio call amma ta wats app seku gaisa
daita ki kara ganinta sosai Allah tahadu kuma tanada hankali"
faseelat
tace "ihmmmmm Allah yakaimu naganta "
Daganan se
chart da yaturo mata yau wanda bata ganiba,
"aljanah
ya kk tashi? gani wurin waseela "
"zan
kiraki yanzu"
Se kiran,
fahad yasa
hannu yaita bugun kanshi yana hawayen danasani "why ban tsaya ida karanta
messages dinba? "
"meyasa
zata dauki pic dashi? don yana cousin dinta ai zeiya aurenta donme zata
sakarmishi jikina "
Yanajin wani
malolon bakin ciki a makoshi yace "ya Allah ka ragemin kishinnan na zauna
lpy kasamin hakuri akan dangin ta, don ban kaunar naga tana muamala da kowane
namiji"niko nace insun barmaka ita ko?
yatashi
zuciyarshi na ciwo yasaka kaya ya tada salla har anyi laasar yayisu ahade, be
taba adduar Allah yarage masa kishi ba segashi yau shine ke kuka yana rokon
Allah yarage masa kishinsa,
yana gamawa
ya tashi yafita direct gidan su faseelat ya nufa amma gidan akulle don duk suna
asibity,
yadade yana
kallon kofar sannan yajuya ya nufi asibity,
A asibity
amira ta farko a firgice, Aisha ta riketa tana rarrashi amira tana kuka take
cewa "ina anty? Ni kikai ni wurin anty "suna haka fahad ya shigo ya
karasa bakin gadon dasauri yana fadin "sannu princess "
amira
naganinshi ta rumtse ido tai gum zuciyarta na harbawa don matsanancin tsoronshi
takeji,
Aisha dake
hawaye ta kalleshi,
Ya riko
hannun amira yace "princess open ur eyes it's me ur dad "
gaf-gaf
hannun amira ya dauki rawa, takara rumtse idonta yanzu in akwai abinda batasan
gani befi daddinta ba,
Aisha ta
zare hannunshi tana hawaye tace "katashi kafita bata son ganinka tsoron ka
takeji karka karasa rikitamin ita"
Yayi kasake
yana kallonta yace "u r lying "
Ya meda
hannu ya riko amira yace "amira it's me ur beloved dad"
amira tafasa
kara idanunta a kulle wadda tasa seda fahad yasaki hannunta, amira na kuka tace
"I don't want to see you stay away
from me"
ya fiddo ido
waje "amira nine fa dad dinki bakison gani na inyi nesa dake? "
amira tace
"mommy please take me to big mom house I'm scared here,"
Aisha tace
"Dan Allah kafita kabarmu, badole taji tsoronka ba yadda kake dukan mu
tana gani tanaji dan Allah kafita "
Fahad ya
tashi yafita yanata tariyo maganganun umma da amira, wai his daughter da kullum
take cewa she love him itace ke cewa yayi nesa daita ,ya shiga motar shi yayi
zaune yakasa ma hawaye se zuciyarshi dake kuna,
yadade zaune
sannan ya nufi gidan mommy dan yafada mata amira ba lpy,kokadan beda niyyar
fadamata abunda yafaru amma yasan she must heard it,
har lokacin
faseelat bata farfado ba daga baccin da take, dukkansu tun safe har yanzu bayan
laasar ba wanda yakara sawa cikinshi komi,
itako jamila
gidan siyama tawuce tana ta kuka tafadawa siyama abinda tayi tace dan Allah
taje tabata hakuri,bataso su mama suji siyama shiru tayi kawai jin abinda hjy
keyi da tsiyar da jamila tayi,
seda mijinta
yayan mamar jamila yadawo cin abinci sannan siyama tafadamishi abinda jamila
tayi tace anjima ze kaisu su bata hakuri,
Ranshi ya
baci yakira jamila ya rufeta da fada "ke dan uwarki saboda yana kai dare
be dawo ba shine zakije kiwa hjy wulakanci, ke wlh a aljanna kike in kikaji
matsalolin uwayen mazan wasu sakarai shasha hakanan zaki rusa mana zumunci,
kika ma kanki wlh in kuma so kike ki zama karamar jawara to tashi kiban wuri
"jamila ta tashi tana kuka tafita,
Cikin
kwantar da hankali siyama tace "kayi hakuri yarinya ce nangaba ko ance
tayi bazata yi ba,Allah yasa hjyar ta
hakura "
Tai shiru
tana tunani don tasan hjyar ma bata kyauta ba kuma zatai mata magana koba yau
ba ,
Motarsu
khalil tayi nisa da tafiya sunkusa kai batsari tunda yashiga counter dinshi
kawai yake latsawa yana lazimi dede gadar wani kauye kurmiyal wata mota ta
kwacewa wani driver tazo tabanki motar su khalil karfen da yakare gadar ya
balle duka motocin suka afka cikin gadar akife , suna fadawa suka kama da wuta
gabadayansu,
Kafin mutane
su taru mutanen ciki tuni sun kone koda mutane sukazo bakajin sautin komi se
fasss! Dasss!! Tatasss!!! Jikin mutane na fashewa, mutane sunata zuba kasa da
ruwa kafin motar kashe gobara tazo , daga katsina zuwa kurmiyal akwai yar
tafiya don sunfi kusa da batsari,shiyasa abun yadauki mintoci
wutar bata
mutu ba har yan kwana kwana sukazo aka kashe wutar ,
ranar yan
kauyen kurmiyal sunga tashin hankali tsoron Allah yakara shigarsu wadanda suka
manta da Allah ranar Sun tunadashi sun koma agunshi, ga warwakin sunyi baki
kirin wasu Sun fashe wasu Sun kwarkwarje wasu hanji awaje, yara, jarirai, maza,
mata, samari da yanmatasa,
kusan rai 15
don waccan motar j5 ce,
ba jimawa
police suka zo aka daukesu zuwa matuary kafin asamu danginsu dukkansu sun mutu
kurmusss,
dandanan
gidajen radio suka fara baza labarin,
Hjya aminiyar
radio tana zaune tana sauraren radion taji hadarin gabanta yayi mummunar
faduwa, tai sauri takashe radion,
Ba arziki
tana rawar duwawu ta shiga daki tana haki ta dauki waya takira mamar jamila,
Mamar jamila
dabatasan abinda ke faruwa ba ta dauka da sallama hjy batako amsa ba tace
"khalil yaiso nan? "
mamar jamila
tace "a, a khalil bezo ba da yataho.... "bata ida magana ba wayar ta
sullube daga hannun hjy,
Ta zame kasa
zaune saboda kafafunta daketa rawa, ta dora hannu akai tafasa kara
"nashiga ukku nabani na lalace wayyo Allah khalil dina ya mutu ya tafi
yabarni"hawaye kamar famfo suke zubarmata ihun da take ta rafkawa yasa
seda makwabtan ta suka shigo gidan suka rirriketa suna tambayar baasi,
Allah sarki
rayuwa in Allah yaso cikin kiftawar ido se kaga duniyar ta zama empty , mutum
ba abakin komi ba amma munsamu duniya mun shan take ko tunanin mutuwar ma
bamayi kamar anan zamu dawwama,mun manta kiyama munata tsiya,ya Allah ka
kyautata rayuwarmu kasa mucika da imani kasa muyi kyakkyawan karshe amin,
*ya ubangiji
ina rokon ka kajikan dukkan musulmai maza da mata ka musu rahma kajikansu domin
kai mai rahma ne me jinkai*😭😭😭
[8/20, 7:11
PM] SHALELE😍: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*
✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽
We are
bearer's of so golden a pen🖊
We write
assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative
golden pen🖊
Be hold our
words
A product of
our pen🖊
Savour our
words
For it will
cause you no pain.✍🏽
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
7⃣2⃣
*SHAFIN
mommyn mufeeda da me dambu inajin dadi yadda kukasance daga cikin mabiyan buk
dina ina kuma jin dadin comments naku thanks*
*yaruwa
kinayin azkhar din safiya da marece kuwa? Koko aiki da son kwanciya barci ko
saurin kunna data suna hanaki yi? Da kinsan falalar yinsu dako kina gudun ceton
rai zaki rikayin su,in kuma kinsan falalarsu why kike sanya? Ko mantawa dasu?
Azkhar suna haska rayuwa, yana sauya mummunan abu zuwa alheri, kariya ce daga
sharrin kowane abu, yana kawo arziki dajin dadin rayuwa,yana gyara zuciya,yana
kusantar da mutum ga ubangiji, yana kai mutum zuwa aljanna,shin me zesa kiyi
sanya da yinsu? gasunan da yawa masu saukin karantawa se dumbin lada da falala,
Dan Allah murika yin azkhar karmuyi sanya dasu don neman kusanci da kariya
awurin ubangiji, duk abinda mukeyi mu daure murika yin azkhar dinnan koda muna
kitchen ne, ko a mota going to office ko a school ko ina sau da dama Allah ya
janyemiki sharri sanadin azkhar wanda ke baki sani ba, kinemi littafin azkhar a
book shop's ki kara samun wasu ki hardace kitayi insha Allah zakiji dadinsu
kuma zaki samu natsuwa*
*yaruwa
kinada riyadul janna fi azkharul kitabu was sunna kuwa?littafi ne da ya tattara
azkhar da adduoi wanda baakawosu hakanan ba seda akafara rubuto hadissan da aka
samosu da wadanda suka ruwaito, acikinshi akwai adduoi da yawa wadanda wlh
zakiji dadinsu an tattara duk adduoin dake cikin alkurani a littafin da kuma
sunayen Allah kyawawa wadanda idan an rokeshi dasu yana amsawa wanda sukazo a
alkurani me girma wanda suka jerosu tun daga fatiha to nas, ga kuma manyan
adduoi a bayansu wanda Allah yake amsa addua in akayi su , na rungumi riyadul
janna naji dadinshi matuka,idan bakidashi ina me baki/ka shawara ki nemi riyadul
janna zaki samu biyan bukata kuma zakisamu kusanci da Allah (S.W).zaki sameshi
a kasuwanni wurin masu littattafai ko bookshops wallafar yusuf bin Ismael
,bangonshi da hoton lambu da
flowers,nasan beda tsada ada bansaniba yanzu kiyi kokari ki mallakeshi don
bukatarki, bakin cikinki,ko damuwarki zasu yaye,zaki godemin kede kinemi naki
ki runguma*
Cikin
gigicewa Hajiya take ce musu"nabani khalil dina ya mutu yayi accident ya
mutu"
Matan suka
dauki salati jikinsu yayi sanyi domin khalil mutum ne har mutum yana girmama
mutane bazaka ce ga abokin fadanshi ba yana da hakuri uwa uba yawan ibada,
Hjy tace
"hjya rabi Dan Allah kuce be mutu ba, be mutu bako? Nasan baze mutu yabar
niba bandashi cikin motar wlh babu shi"
matar
daakace ma hiya rabi ta kalli abokiyar zamanta tace "hjya zaliha ki kira
alhaji kifada mishi yafada ma manu naji labarin accident din yanzu inajin radio
se suje su dubo indashi se suanso gawar ai mishi sutura "
Zaliha ta
juya dasauri ta shiga gida ta dauki waya ta kira mijinsu tafada mai yayi ta
sallallami yace "yanzunnan naji labarin accident din bari nakira manun
donni ina jibia amma yanzunnan zan kamo hanya "
ya kashe
kiran ya kira manu, kawu manu ya girgiza ba bata lokaci ya tafi gidan kaninshi
suka nufi matuary dauko gawa,
zaliha ba
bata lokaci ta dannawa siyama kira ,siyama na kitchen wayar ta keta kara
yaranta duk sun tafi islamiya jamila ta dauko wayar ta kawomata ta juya ,
siyama ta
dauka takara kunne da sallama a bakinta,
Zaliha tace
"siyama nice hjya zaliha ki taho gida khalil yayi accident ya rasu hjyar
ku kuma bata lpy"diff takashe takoma gidan hjya dasauri,
Siyama
zuciyarta ta rika harbawa dasauri hawaye suka rika zuba a fuskarta masu zafin
gaske,
Tai cikin
daki tana kuka, jamila dake zaune tayi tagumi taga siyamar tashigo tana kuka ta
tashi tabita ciki siyama har tazira hijab jamila tana ta kallonta tace
"anty lpy kike kuka? "
siyama
tafashe da kuka tace "yaya khalil ne yayi accident ya rasu "
kamar saukar
guduma jamila taji maganar ta yanke jiki tafadi,
Siyama tai
kanta tana kuka tana kiran sunanta "jamila! Jamila kitashi Dan Allah
"
Mijinta
babban mutum ne idan ya dawo aiki a kofar gidanshi yake zama wurin har yazama
majalisa cika yake da maza,
siyama ta tashi tafita waje dagudu bata tsaya
koina ba se gaban mazan dake gun ta kalli mijinta tana kuka cikin tashin
hankali tace "baban farida jamila ta fadi "
yace
"subhanallahi ! "ya tashi yayi cikin gidan dasauri, siyama tabi
bayanshi,
Yana shiga
ya samu jamila a sume da sauri ya bude fridge ya dauko ruwa masu sanyi ya sheka
mata su a fuska,
jamila
tasaki ajiyar zuciya ta bude ido wuf
tatashi zaune tafara hawaye" anty yaya na ya rasu? Ya khalil dina
fa"?
siyama
daketa kuka tace "ya rasu jamila "
Marar jamila
da tunda tafarko take murdawa kadan, ta murda
da karfi ,jamila ta dafe ciki da kugu tafara kuka tana nishi zufa tarika
karyomata ta koina,
Baban
farida yace "siyama me kike fada
ne?"
siyama tace
"yanzunnan aka kirani akace yayi accident ya rasu "
Baban farida
yace "innalillahi wainna ilaihi rajiun!!!! ...
karar da
jamila tayi ne ya katseshi,
"wayyo
Allah marata zata balle wayyo kuguna "
dashi da
siyama suka rirriketa baban farida yace ma siyama "dauko min keys dina
mutafi asibity"
Siyama ta
saketa tana kuka tatafi dauko keys, shima idonshi jawur ya dauko jamila suka
fito siyama ta bude mai yasa jamila baya tashiga yajasu suka nufi asibity,
tsakanin jamila da siyama bazaka gane wake nakudar ba don dukkansu kuka suke
riris,
baban farida
har kyarma yake wajen tuki dakyar suka isa Medical Center aka amshi jamila
akashiga daita,
siyama ta
cigaba da kuka zuciyarta kamar zata fito duka yaushe sukai rashin alhaji yanzu
kuma khalil,
baban farida
ya rungumota jikinshi yana rarrashi,
ba jimawa
wata nurse tafito wurinsu tana sauri tace "patient da kuka kawo labour
take ayi sauri akawo kayan haihuwa "tajuya takoma dakin,
baban farida
ya zaunar da siyama akan seat ya fita anan bakin asibitin yasiyi kayan haihuwar
ya koma ciki dasauri,
Ba jimawa
nurse tafito ta amshi kayan hankali tashe yace "ta haihu ne?"
nurse din
tace "a, a dasauran lokaci kumata addua "takoma ciki dasauri,
wayar baban
farida tadau kara yana dubawa yaga mamar jamila ce, kamar kar yadauka ya dauka
ya kanga akunne ,
acan
bangaren tace "yaya kuna lpy kuwa dazun maman siyama ta kirani tana
tambayar khalil ko yazonan bamu gama waya ba takashe wayar yanzu naji labarin
accident da akayi ahanya shine hankalina ya tashi nace bari nakira "
Murya dishe
yace "harda Khalil acikin accident din, yanzuma muna asibity jamila labour
take "
maman jamila
dake zaune ta mike tsaye tana salati tace "Allah yajikanshi, Allah yabata
lpy nan bada jimawa ba zamu taho "takashe kiran tafara neman layin mijinta
yana dauka tafada mishi ba jimawa yazo gida suka kama hanyar kt,
Shiru shiru
jamila bata haihu ba, hankalinshi duk da baa kwance yake ba yayi ta maza yacewa
siyama tajira zeje yadawo,
yanufi gidan
hjy,
Hjya tabi ta
rude tayi sambatu har muryarta ta shake dole tai shiru tana ta kuka batsayawa,
matan dake wurinta sunata bata hakuri, hjy rabi tafara mata nata waazi
"haba hjy kinaso kinuna Allah be kyauta ba komi? kituna fa Allah ne yabaki
shi kuma ya amshi kayansa meyasa bazaki hakuri ba? Kiyi hakuri kita innalillahi
wainna ilaihi rajiun ki kuma cigaba da mishi addua ita yake bukata a yanzu
,insha Allah yanzu khalil ba abinda yakeso fiyeda akaishi makwancinsa inamishi
kyakkyawan zato kiyi hakuri Allah seyabaki ladar hakurinki, ko kuma kita kuka
da surutan har Allah yayi fushi dake, hjy bayau akafara miki mutuwa ba ina
iyayenki ina mijinki? duk kin hakura donmi yanzu bazaki hakuri ba? kuka dole ne
amma ba irin yadda kike ba kiyi hakuri Allah yamishi rahma "
hjya ta
cigaba da kukanta danbata jin wani waazi yanzu,
kawu manu
sunje matuary mutane da yawa wadanda abun ya rutsa da yanuwansu ,har akazo kan
su kawu manu aka tambayi sunan khalil suka fadi acikin list na fasinja harda
khalil a motar su shidda ne ,
dandanan aka
shiga dasu ciki akafara zaro maza daga lokokinsu ba kyangani abun, basuga
khalil ba, abun yabasu mamaki ga sunanshi amma babushi dan sandan da kenan yace
"to gaskiya kila babushi a motar don motocin duk sunyi ragaraga kaida ka
gansu kasan ba ran daze fita daga ciki
kuma ba gawar da tazama toka donba kasusuwa kuma wurin ba wasu gawarwaki awaje
munyi screening sosai kuje kukara bincikawa ko kafin accident sun saukeshi wani
gari "
su kawu manu
suka fita suka nufi gidan hjya,
hjya na
zaune tayi lakwas ko mutuwar alhaji bata girgizata haka ba, suka shigo suka
zauna,
ta dago tace
"manu ina gawar khalil? Ko gawar tashi ma bazan samu gani ba? "
manu yace
"se hakuri hjy, Allah kadai yasan komi munje acikin gawarwakin ba khalil
kuma dasunanshi acikin list na passengers ,kila babu shi cikin motar"
Hjya tafashe
da kuka da shakakkar muryarta tace "khalil ya zama toka ya zaai aganshi,ashe
kallon bankwana nayi mishi ayau, naso ya mutu yanajin dadi ba cikin kunci ba
"
baban farida
yayi sallama yashiga ciki,
kawu manu
yace "ance ba gawar da ta kone, kode har yaisa batsarin shi?"
baban farida
yace "a, a beje ba saboda yanzu mukayi waya da zulai tace beje ba "
hjya tace
"khalil fa ya rasu shikenan banda kowa yanzu se siyama ba alhaji ba khalil
"
Sukace
"hakuri zakiyi hjya Allah yajikansu ya musu rahma "
Hjy ta kalli
baban farida tace "ina siyamar? "
baban farida
yace "suna asibity da jamila taji mutuwar se labour tataso mata "
hawaye suka
zuboma hjy jin wadda ma yatafi biko tana cikin garin, se tausayin jamilar
yakamata tanason khalil sosai, se hjyar taji yanzu ba abunda takeson gani se
dan ko yar khalil ,
Tana share
hawaye tacewa baban farida "mutafi asibitin "
Ta tashi ta
dauko abayarta, ta fita su kawu manu da baban farida suka biyo bayanta, su hjya
rabi ko suna zaune jingum jingum,
Baban farida
ya budemata mota tashiga suka nufi asibity,
Suna zuwa
siyama ta rungume hjy tana ta kuka se yazama hjyarce ke rarrashin siyamar, suna
tsaye ba abinda sukeji se kukan jamila dake fitowa daga cikin labour room,
Fahad na isa
gidan mommy yashiga jiki sabule ,ya fada kan kujera yayi zaune yanata tunani
yanzu wane hali faseelat take ciki? zuciyarshi zafi kawai take for minutes
sannan mommy tafito taganshi yanayinshi wani iri tace "lpy son naganka
haka? "
yace
"mommy amira bata lpy suna asibity tundazu "
mommy tace
"subhanallahi tun yaushe? "
yace
"tunda safe "
tace
"shine se yanzu zakafadamin? "
Yayi shiru
taja tsoki ta haye sama segata tafito da gyale da car key da jaka tazo zata
wuceshi tafita,
Yace
"mommy kitafin musu da abinci don haryanzu Aisha bataci komi ba "
mommy ta
harareshi tace "tunda safe ace haryanzu bataci komi ba kai miye amfaninka
ne dabazaka zo kafadamin ba in ita hankalinta ya dauku wurin jinya? Mtsswww
"taja tsoki tafara kwadawa jummai kira, jummai tazo dagudu mommy tace
"kingama dinner? "
Jummai tace
"a, a amma akwai abincin rana kuma cikin warmer yake "
Mommy tace
"daukomunshi dasauri"
jummai
takoma tadawo da kula mommy ta amsa ta fita tashiga mota tai asibity,
Fahad nanan
zaune dafe da kai yarasa yazayayi neman mafita yaketayi daga karshe yatashi
yakoma kofar gidansu faseelat har lokacin kulle gidan yake yaja tsoki yanajin
kamar yayi kuka ya bar unguwar,
mommy
nashiga wurinsu Aisha amira ta rungumeta tana hawaye tace "mommy kitafi
dani gidanki banison gidan daddy "
mommy tace
"yi hakuri princess dake zan tafi kinji ko? Ki kwantar da hankalinki
"ta kwantar da amira jikinta,
ta kalli
Aisha dake koje koje tace "meya sameta?"
Aisha ta
girgiza kai tace "zamuyi maganar after"
Mommy tace
"okay kidaure kici abinci ko kadanne fahad yace bakici komi ba "
Aisha tace
"banajin yunwa ruwa kawai nakeso "
Mommy tace
"kibude jug gashinan ki zuba tea kisha amira nasa aka hadomashi itama ki
zubamata "
Aisha tace
"baride na zuba mata kibata ni zanfita nasamo mana drinks a reception
"
Ta zuba
tamikawa mommy ta dauki kudi ajakar mommy tafita,
Mommy tayi
tayi amira tasha amira taki sema tafara rigimar ita anty "mommy ni anty
nakeson gani ki kaini wurin anty"mommy tai shiru tana tunani dan tagano
akwai abinda ke faruwa,
Su hjy na
zaune sukaji kukan jariri yanata inyarrrr inyarrrr, hawaye suka zubowa hjya,
dukda jamila ta haihu bata bar kuka ba nurses sukace ko ciwo takeji wani wuri
batace musu komi ba tacigaba da kuka sunata fada itako bata fasa kukanta ba,
suka shirya baby nurse tafito wurin su hjya dauke dashi,
duk suka
tashi tsaye hjya hannunta har rawa yake wurin son ta amshi yaron, ta amsheshi
ta bude fuskarshi yaron sakkkkk khalil lokacin da yana jariri, hjy se kuka ita
kuka siyama kuka, Allah assamad khalil yatafi khalil yadawo, nurse tai tsaye
tana kallonsu ganin suduka suna kuka ta juya takoma ciki,
Baban farida
na tsaye ya rike hannu,
bayan
mintoci aka fito da jamila aka medata rest room, su hjya sukabi zuwa dakin,
Jamila na
kwance tana ta kuka suka shigo hjya ta mikawa baban farida jaririn ta matsa
tariko hannun jamila tace "kiyi hakuri jamila, Allah yafimu san khalil
shiyasa yadauki abunsa, "
fuska jage
jage da majina da hawaye jamila ta kalli hjya tace "hjy kema kin yarda ya
mutu? Wlh be mutu ba yana raye yananan zuwa baze tafi yabarni ba "
Hjya ta
share hawaye tace "kiyi hakuri jamila kowa seya tafi can"
jamila
takara fashewa da kuka, ko sanin me ta haifa ma batayi ba, hjy tasa hannu tana
share mata hawaye tana rarrashinta,
Baban farida
besan lokacin da hawaye suka zubomishita gefen ido ba, duniya kenan gashide
wanda suke fada kanshi ya rasu dukansu suna kukan rashi yasa hannu ya share,
ana haka
mamanta suka iso ,jamila takara wage baki tana kuka, duk dauriyar zulai seda
tayi kuka,
gaf Maghreb
faseelat ta farfado tana nishi ,idonta arufe ta tuno abinda yafaru tabude ido
dasauri hawaye na zubarmata ta dafa cikinta dake ciwo, hawaye masu zafi suka
kara zubomata,
ummi ta
dafata tace "sannu faseelat ya kikeji?"
Se sannan
faseelat tasan su ummi na wurin ta juyar dakai ga ummi abba,omer abul ishak da
Mubarak harda baaba matar baba babba,
hawaye na
cigaba da zubomata murya dishe tace "ummi cikin ya zube ko? "
ummi tace
"kiyi hakuri haka Allah yakaddara"
Faseelat ta
juyar da kai tana hawaye ,tana tuno yadda fahad ya rikice yarika dukanta kamar
ba mutum ba, yanzu shikenan cikin ya tafi,
Ummi takatse
mata tunani tace "bari na temaka miki kisha tea kokadanne "
faseelat ta
girgiza kai tace "nakoshi ummi bazan iya cin komi ba"
Ummi
tace"kidaure ko kinsamu karfi "
faseelat ta
girgiza kai, dukkansu suka matso suna mata sannu ta rumtse ido bata amsa suba,
she wonder
yaakai takenan ina fahad yaakai baya nan se su ummi kawai mike faruwa ne?
Karde........zuciyarta tabuga da karfi, ta bude ido tace "ummi ina fahad?
"
ya omer dake
gefe zuciyarshi nacigaba da tafasa saboda halin da take ciki jin tana nemenshi
yasa yaja dogon tsoki ya fita daga dakin,
Ummi rai
bace tace"wane fahad kuma ke yanzu
dan kina dakikiya ya nakada maki shegen duka daga farkowarki kifara tambayarshi
wlh sunan fahad yafita daga bakinki ko natashi nai tafiya ta "
faseelat na
hawaye tace "ummi waya kawoni nan?dan Allah kufadamin yana ina "
Ummi taja
tsoki zatai magana abba yace "Dan Allah kibarta zafin ciwo ne bawani abu
ba, kibari tadawo hankalinta sannan "
ummi ta tabe
baki, faseelat ta cigaba da hawaye zuciyarta na harbawa tarasa gane meke
faruwa,
Maghreb tayi
musa da yazo duba gonarshi daga babbar
riga, besamu yaje gonar bama seda aka kusa Maghreb don ya samu hadarin da
yafaru, yagama abunda yake ya na cikin tafiya zuwa wurin da yayi parking
motarshi yaga mutum sheme sanbal straight akwance acikin ciyayi,
Ya matsa
wurin khalil ba alamun ko rauni jikinshi ya zukunna ya fara duba shi,
kamar wanda
yayi bacci khalil ya tashi zaune, yana
salati ya jujjuya kai gabas da yamma kudu da arewa ,sannan yadafe goshi yana jin
kuwwar mutane da salati da mutane sukai tayi lokacin accident din,
musa ya
dafashi yace "bawan Allah mekake anan yanzu da daddare? "
khalil
idanunshi jawur zuciyarshi sanyaye yace "bansan yaakai nazo nan ba, nide
nasan muna cikin mota, wata mota tahawo tamu daganan bazan iya tuna komi
ba"
Musa yaja
kabbara "Allahu akbar ,Allah me yadda yaso dama akwai ran da yafita a
motocin can abun alajabi, bawan Allah lalle Allah nasonka daya barka da rai har
zuwa yanzu domin acikin motocin bawanda ya fita duk sun kone "
khalil ya
dago arazane, mutumen yace "eh duk sun mutu kaima ina mamakin ganin ka
anan tunda yayi nisa da inda hadarin yafaru "
khalil yace
"jinake kamar nayi bacci na farka amma nasan bakomi ne yasa Allah
yatsareni ba se don yawan ambatonshi da nake kuma nakasance me kiyaye
dokokinshi "
Musa yace
"hakika wannan ba abun mamaki bane don ikon Allah yawuce mamaki azamanin
manzon Allah (S. A. W) wata unguwa takama da wuta duk gidajen suka kone daakazo
akafada ma sahabin daya daga cikin mutanen unguwar se ya karyata yace wlh banda
gidana saboda bana fitowa gida harse nayi adduar da manzo ya koyar damu (fans
namanta adduar) kuma ana zuwa akaga gidanshi lpya lau amma duk nakusa dashi
akone,"
Ya cigaba da
cewa" nan kusa akwai wani abokin mahaifina shide yakasance kullum baya
manta karanta ayoyin karshen suratul tauba, lakadjaakum sau 7 koda yana tafiya
yakan karanta ta koda besamu yin kowane azkhar ba yanayin wannan, se wani
amininshi ya kawo mashi ziyara daga sudan shikuma abokin mahaifin nawa yana zaune
a kaduna, bayan ya kwana se suka shirya suka nufi abuja don ziyarar abukkansu,
tareda driver suke amma se abokin mahaifina yaamshi driving, kasancewar beiya
dogon driving yake fara bacci suna cikin tafiya yafara gyangyadi dole yadawo
gidan baya ya kwanta amininshi da driver suna gaba, baadade ba bacci ya
daukeshi,yana bacci sukai accident koda yafarka sede yaganshi yashe a gefen
titi mutane suna zagaye dashi bako kwarzane jikinshi, seyafada musu suna tare
da yanuwanshi a mota, daaka bi daji ashe motar yankar daji tai taita tafiya
tayi raga raga driver ya mutu yana ciki yayi jina jina, hankalinshi yatashi aka
dukufa neman amininshi baagano amininshi ba se da akai tafiyar kilometers 25
sannan akaganshi kwance a mace cikin kungurmin daji, ya kidima sosai abun yabawa
mutane mamaki, a kd akai janaizar amininshi da driver ana zaman gaisuwa wanda
ina daga cikin wadanda ke gun anata jajanta lamarin sewani malami yake tambayar
shi wace addua yayi ayau seyace "wlh ban karanta komi ba se lakadjaakum
kafa 7 wanda kuma a riyadul janna nasamu falalarta hadisin da yakawota a rauda
ta 18 ankarbo hadisin ne daga Muhammad bn abubakar cewa wanda ya lazimci karanta lakadjaakum ila
akirul sura lam ya mut hadman wala garqan wala harkan wala darban hadid,shine
na lazimceta kowane lokaci "
,malamin
yace"hakika karshen suratul tauba kariya ce daga dukkan abun ki, nima
zankara dukufa wurin yinta "
Musa ya
cigaba dacewa daganan sena rike ta inayi danaji falalarta ,ban wata biyu da
riketa ba zanje Lagos motar mu ta kife karamar macapolo ce amma bawanda ya fita
seni nima cikin jini nake domin naji ciwo sosai "ya bude kafarshi zuwa
bakin gwiwa wani katon tabo ya bayyana harda rami ajiki yace "kaga tabon
da yakasa bacewa daga cikin tabunnan danayi a kalla anyi shekara biyar amma har
yanzu be cike ba sede ina tafiya da kafata lpy lau duk dan temakon Allah
"(it's true life story ya faru dagaske)
khalil
yace"ina yawan karantata domin tana daga cikin jerin azkhar dake cikin
littafi na sede bansan falalarta ba, hakika nagode ma Allah daya kareni domin
koda mutuwa hutuce aguna zanso nakara rayuwa dan nakara aikata aikin alheri
,inada mahaifiya ita kadai ta ragemin
inason na rayu har zuwa tsufanta zuwa lokacin da zata kasa yiwa kanta
komi yazama nine me mata hidima don samun rahmar ubangiji da albarkarta dafatan
Allah yabani wanda zemin haka nima"
musa yace
"Allah ya yarda wane gari kake zan
temaka maka nakaika duk da dare yayi "
khalil yace
"cikin katsina nake idan har zaka temaka mun ba gida nakeso kakaini ba,
don ina samun matsala da matata da mahaifiyata nasan in sukaji labarin mutuwa
ta zasu saduda mahaifiyata zata sauko domin tana sona sonda takemin ne yayi
yawa haryake kawo mana matsala take kishi da matata kamar kishiyarta, inso samu
ne zanso na zama bakonka nawani lokaci sannan zan koma garinmu "
Musa yace
"ba matsala nima zanso nasamu ladar bakuntarka, na tausaya maka Allah ya
ganar da mahaifiyarka"
Khalil yace
"amin nagode Allah ya baka ladar "
musa
yace"amin ni sunana musa ina zaune babbar riga da matata da yara na uku
"
khalil yace
"ni sunana khalil ina zaune a layout matata yarinya ce aurenmu beyi
shekara ba"
musa yace
"masha Allah Allah yabada zuria dayyiba zamu iya tafiya "
khalil
yatashi suka nufi motar musa suka shiga suka kama hanyar babbar ruga batareda
kowa yasan khalil na raye ba.
ya Allah
kajikan musulmai maza da mata ka musu rahma 👏🏼
*zakuji
inata yiwa mamatanmu addua wata falala naji daga bakin sheikh daurawa cewa duk
wanda ya nemawa muminai gafara zaarubuta masa lada adadin musulman da suka
mutun , dukda de inayi akowace sallata domin nikan tuno da yanuwana da abokaina
da suka rasu, to jiya kuma hatsarin nan yakara tadamin hankali har natuno
garabasar nan shine nace bari nafada maku nasan akwai wadanda basu sani ba se
sufarayi, Allah kakaramana ilimi*
[8/21, 5:33
PM] SHALELE😍: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*
✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽
We are
bearer's of so golden a pen🖊
We write
assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative
golden pen🖊
Be hold our
words
A product of
our pen🖊
Savour our
words
For it will
cause you no pain.✍🏽
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
7⃣3⃣
*shafin
nakine AISHA ALTO writer of SANA'ACE,da begenki arai na nayi typing inafatan zakiji dadin page dinnan
nakine ke kadai uwargidan fahad🤣*
Har suka isa
babbar ruga bawanda yace uffan dukkansu suna tunani daban, a kofar wani karamin
gida suka tsaya duk suka fito waje, musa ya kalli khalil yace "nan shine
gida na,muna zaune ne tareda mahaifiya ta "
Khalil yayi
shiru yana tsaye musa ya shiga gida ba dadewa ya fito bakin gidan akwai kofar
wani daki yasa key ya bude dakin yashiga few minutes yafito yacewa khalil
"bismillah"
Khalil ya
karasa ciki dakine karami da toilet aciki bakomai ciki se katifa da praying mat
musa yace "nan shine masaukinka duk abinda kake bukata kamin magana "
Khalil yace
"nagode sosai Allah yabaka ladar"
Musa yace
"amin "ya juya ya fita,
Da fitarshi
khalil yashiga toilet yayo alwala ya dawo ya shimfida carpet ya tada sallar
laasar da Maghreb ,yana sallar yana hawaye yana tuno mutanen da suke tare a
mota dukda shi yana gaba amma a bayanshi yanajin wata mata na waya tanafadin
Sun kusa karasowa abata minty 10 kawai, da danta ahannu yanata kuka,sanda
yagama sallar addua yayi ta masu akan Allah yajikansu ya musu rahma ,
Aisha ta
dawo da drinks a leda tazauna tabude kwalin happy hour tadansha ta aje sauran,
har lokacin amira tana ta kiran anty,
Mommy ta
kalli Aisha tace "wai ina antin tata ita bazata zo dubata bane? "
Aisha ta
yamutsa fuska tace "itama bata lpy tananan asibitin akwance "
Mommy tace
"mtswww meyasa meta ne ita kuma? "
Aisha tace
"I don't know me tamishi yayita jibgar ta ina shiga dakin na ganta cikin
jini inaga tayi miscarriage abinda ya tsorata amira kenan har ta suma "
Mommy tace
"amma naji dadi shegiya Allah yakara
Aisha ta
girgiza kai ta nunamata amira da ido, mommy tai shiru,
amira tace
"nide kukaini wurin anty inason naganta "
mommy tace
"to zan kaiki wurinta kisha tea nikuma sena kaiki "ta dorawa amira
cup,
Amira ta dan
sha ta janye fuska,
mommy ta
kalli Aisha tace "bari naje naga likitan inda yiwuwa se mukoma gida seya
cigaba da zuwa yana dubata acan kamin ta warware "
Aisha tace
"to "
Mommy ta
dauki amira suka tafi office din doctor, ta zauna ta mishi magana yace ba
matsala zasuiya tafiya mommy tai payment suka koma dakin, Aisha ta tashi suka
shiga mota suka nufi gidan mommy,
Kafin su isa
amira tai bacci suna zuwa mommy ta kwantar daita Aisha kuma tashiga toilet ta
watsa ruwa,
Hawaye
faseelat taketa yi don ma batada karfin yin kuka ,
ummi tagaji tace
"shin ce miki akai ya mutu komi?"
faseelat
tace "toyana ina?"
ummi tace
"yananan zuwa ki kwantar da hankalinki "
Sannan tai
shiru tana ta son taganshi don tsoro take karde sakinta yayi ,
Suna haka
omer yashigo dakin faseelat tai sauri ta kulle ido, badan yadena jin takaici ba
yace "faseelat ya jikinki? "
tai shiru
saboda kunya dama he warned her amma bataji ba ga abinda yake gujewar yazo yana
faruwa,haka akai ga auren khalil bata dauki shawararshi ba abinda yazatan kuma
shi yafaru,
Ummi tace
mishi "jiki kam aiba sauki kana ganin yadda take a kumbure, sonake jinin
nan yakare in kamata in dan gasa mata jikin kotaji dama "
Omer yace
"Allah ya sawwake "
Gidan sabeer
fahad ya nufa yana parking yafito ya nufi gun sabeer dake waya da fatouma,
sabeer naganinshi yace wa fatouma "pretty ga kanenki nan yazo bari nayi
attending dinshi I will call you back"
yakashe
kiran ya kalli fahad da yazauna a seat ya dafe kai ,sabeer yace "lpy de
fahad naganka haka Very tensed? "
Fahad ya
dago fuskarshi da tayi jawur yace "ina cikin tashin hankali sabeer kabani
shawara plss "
sabeer yace
"inajinka"
Fahad ya
furzar da iska shikanshi haushin kanshi yakeji yace "something bad
happened, kishi ya rufemin ido na doki faseelat hartayi miscarriage after I
took her to hospital..."
sabeer
yakatse shi yana fada "kana cikin hankalin ka kuwa? wane irin kishi ne da
zesa ka bugi matarka har tayi bari? haba dude sekace baka waye ba ga hanyoyi
nan birjik da zakai punishing nata seka tsaya ga duka saboda kajawa kanka raini
agunta da iyayenta?"
Fahad ya
dagamai hannu yace "please karka ce zakamin fada banzo wurinka don ka
karamin tension ba nazo ne kafadamin mafita,in kuma fada zakamin sena tashi nai
tafiya ta kobari bakai ba nakai numfashina ba "
sabeer yaja
tsoki yace "badole nai masifa ba karika abu like mad person yanzu inajinka
"
Shima fahad
yaja tsokin bacin yana neman mafita da tafiyarshi zeyi, ya cigaba da cewa
"after na kaita asibity nafita in duba princess dabata lpy se dawowa nai
na tarar batanan yanuwanta sun dauketa naje gidansu many times a kulle "
sabeer
yace"wow sunyi dede dasuka dauke diyarsu, kai kana tunanin kamar Aisha ce
da kake jibga son rai dan tana kanwar ka? to yanzu de kaga da banbanci, seka
jira hukuncin da zasu yanke "
fahad da
tundazu yake kallon sabeer kamar ya kaimishi naushi, ya hadiye miyon bakin ciki
yace "u r very stupid da kake tunanin ina hada Aisha da faseelat kowace da
matsayinta in Kana bani shawara kabani in bazaka bayarba senai tafiya ta "
Sabeer ya
janye hannunshi da yadora kan fuska yarage murya yace "gaskiya baka kyauta
ba duk son da yarinyar nan ta nuna maka amma har kaiya mata haka "
fahad yace
"I known, ya zanyi yanzu they took her bansan ina suka kaita ba nikuma
inason ganinta inason sanin halin da take ciki "
Sabeer yace
"dole kayi hakuri kaita zuwa har kasamu ganin mahaifinta kabashi hakuri
sosai kila su hakura , don inajin tsoron kar su rabaku, saboda diyarsu tana da
komai dahar wanda yafika zata iya aura "
Fahad ya
dafe goshi yace "bazan iya rayuwa babu ita ba, she's my life, I'm
regretting bazan iya bacci ba batare da nasan halinda take ciki ba ,ina son
sanin halin da take ciki "se hawaye sharr sharrr
sabeer ya
dafashi yace "kayi hakuri kabi komai asannu faseelat takace,ka kwantar da
hankalinka kacigaba da zuwa gidannasu har kasamu ganin abban nasu sede sekayi
hakuri bazan boyemaka ba duk mutuncin da suke ganinka dashi yanzu babushi
"
fahad yayi
shiru yana tunanin yadda ze tunkari abban nasu,
sabeer yace
"amma dan Allah ka rika kiyayewa,karage kishinnan karika hadiye shi don
gudun nadama "
Fahad ya
share hawayenshi yace "thank you, nagode "ya tashi ya shiga motarshi
yabar gidan,
Sabeer yabi
bayanshi da kallo ya girgiza kai,
har bayan
isha seda fahad yaje gidan har lokacin yana rufe, yajuya yanufi asibity
yanaganin basanan yayi tunanin an sallame su ya nufi gida,
faseelat na
nan tazuba ido jiran hero shiru babushi,hankalinta duk yatashi ,jinin na karewa
ummi ta jona heater ta kamata suka shiga toilet, ta temaka mata ta tube se
lokacin ummi taga tashin hankali jikinta duk bakin tabo ne ga kumburi da tayi,
ummi takara hawa fiyeda baya, ta gasa ta tai mata wanka ta sauya mata kaya
sannan takamata suka fito,
faseelat ta
kwanta tana meda numfashi, ba dadewa abba yashigo da maltina da madara aka
hadamata ,ummi ta tadata tabata don dole tasha sannan ummi ta kwantar daita ,
ummi ta
kalli su abul da tundazu suna asibitin kamar masu azumi tace "yakamata ku
tafi gida hakanan har tara tawuce"
Suka fita
jikinsu a mace, ya omer ma ya masu seda safe yafita,
Ummi ta
kalli baaba tace "baaba yakamata kitafi gida kihuta kema "
baaba tace
"to Allah yakara lpy bari natafi "
ummi tace
"a, a kijira alhaji ya kaiki "
abba yace
"to inde ana bukatar wani abu ki kirani"
ummi tace
"to insha Allah "
Abba yafita
baaba tabi bayanshi yana cikin tafiya baba babba yakira ya dauka bayan sun
gaisa,baba babba yace"ya me jikin?"
abba yace
"dasauki zaace"
baba babba
yace "Allah yabata lpy, da Allah ko mijinta yazo karka saurare shi ,ya
saketa kawai "
abba yace
"to Allah yasa haka shine mafi alheri"
Baba babba
yace "amin"sukai sallama,
abba na
ajiye baaba ya wuce gida,
fahad na
zuwa gida besamu su Aisha ba yajuya ya nufi gidan mommy, yana zuwa ya zauna a
kujera ya kwantar da kai jiki kanshi na mugun ciwo,
mommy tafito
daga kitchen taganshi tabata rai tazo ta zauna, tace "yanzu fahad rayuwar
da kazabar wa kanka kenan? matanka kamedasu kamar jakkai kaita bugunsu kamar
dabbobi? "
Fahad
hannunshi akanshi yace "mommy it's a mistake baason raina nayi ba "
mommy tace
"idan de zakai hankali kayi idan kana dukan Aisha nayi shiru ita wagga
iyayenta ba shiru zasu yi ba "
tatashi zata
haye sama murya sanyaye yace "ina Aisha? "
mommy tace
"tayi bacci katafi kawai gobe kazo ka dauketa, ita kuma amira anan zata
zauna tunda kagama tsorata ta"
Ta juya ta
hayewarta,
Fahad ya
tashi yabar gidan, yakoma gida ruwa kadai ya iya sha ya shiga dakin
faseelat yayi kwance kan bed dinta
yanajin kewarta sosai, ya tashi ya bude wardrobe dinta ya dauko sleeping dress
dinta ya rungume a kirji yana hawaye,
gidansu umma
ma duk basu cikin walwala har 10 tayi umma taji bata iya bacci ta tashi ta nufi
dakin lady, Lady na waya da Hussein dasuke matukar son juna yanzu, umma ta
shigo lady takashe kiran ta meda hankalinta kan umma,
Murya
sanyaye Umma tace"waikinsan gidansu faseelat ne? "
lady tace
"eh nasani"
umma taji
dadi tace "yawwa kitashi kisa hijab can zamuje yanzu bari naje na dauko
mayafi na"
ta juya
tabar dakin, Lady ta tashi ta dora after akan kayan baccinta tafito, umma
tafadawa daddy suka tafi gidansu faseelat,
suna zuwa
sukai parking suka fito suka tsaya bakin kofa sunata knocking, can zuwa
abulkhair ya bude gidan unguwar dun dum dan babu nepa, sede hasken farin
wata,yagade mata ne yayi tunanin kawayen ummi ne,
abul yace
"inawuni "
Umma tace
"lpy lau ya me jiki an sallamosu ne"
yace
"dasauki suna asibity "
umma tace
"wace asibity suke room nawa? "
Yace
"turai, aminity ward room 9"
umma tace
"to nagode sosai "ta kalli lady tace "mutafi asibitin "
suka juya
suka tafi abul yameda gida ya rufe,
akan hanya
suka sai kaza me dawafi da drinks suka tafi asibitin,
Bawani
wahala suka gane dakin suka tura suka shiga da sallama bakinsu, ummi kadaice ta
rage itama tana salla, da lady da umma hankalinsu bakaramin tashi yayi ba ganin
halin da faseelat ke ciki,
idon
faseelat akulle umma takarasa kan bed din dasauri tana kara ganin barnar da
danta yayi,
jin kamshi
na daban faseelat ta bude ido taga umma, tafara hawaye,
Umma tace
"sannu faseelat Allah yabaki lpy"
Faseelat tariko hannun umma murya shake tace "umma!
ya sakeni ko? "
umma
tace"me kike cewa ne? Yazaai fahad ya iya sakinki yana sonki sosai baze
iya rabuwa dake ba "
Tace
"ban ganshi ba har yanzu bezo wurina ba, Dan Allah umma kikiramin shi
inason ganinshi "
Umma tace
"ki kwantar da hankalinki yananan zezo "tasa hannu tana share mata
hawaye,
ummi da
tundazu ta sallame tai shiru tana kallon gadon da faseelat ke kwance tanajin
takaici kamar me,
lady ta
matsa tace "sannu anty "
faseelat ta
daga mata kai tana cigaba da hawaye,
ummi ta
tashi tana linke carpet tace "sannunku da zuwa "
umma ta juya
wurinta tace "ina wuni yame jiki Allah yabata lpy"
ummi tace
"amin "
Itama lady
ta gaida ummi, shiru dakin nawani lokaci sannan umma tace "Dan Allah ummi
kuyi hakuri akan abinda fahad yayi baa cikin hayyacin shi yayi haka ba, shi
kanshi yana cikin tashin hankali don koda yazomun da labarin kuka yakeyi ,nasan
yanacan cikin tashin hankali, kuyi hakuri Dan Allah wlh ni kaina abun yabatamin
rai sosai don faseelat kamar diyata na dauketa, yaran ne ka haifesu baka haifi
halinsu ba"
ummi tace
"ihhhm bakomi"
umma tace
"kuma wlh naji dadi sosai da kuka dauketa, sede ina rokon da kuyi hakuri
kubarmishi ita karku rabasu, don ita haske ce arayuwar dana, tana duk wani
kokari na gyara mishi rayuwarshi badan ita ba da yanzu bama tare dashi, ina
rokon da kuyi hakuri akan abinda yafaru kubarmishi ita Dan Allah "tahade
hannayenta biyu,
umma ta bawa
ummi tausayi tace " da nasa araina dole ya saketa saboda wannan abunda
yayi kuma ba yaune yafara dukanta ba, amma na hakura saboda ke kuma zanyi iya
kokarina naganin takoma dakinta, sede bazan bashi ita hakanan ba se yagane
kuskurenshi "
Umma tace
"nagode sosai ummi kuma naji dadin hakan don ko dauketan da kukayi yau
kadai ma ya razana shi na tabbata wannan zesa yagane kuskurenshi nagode da kika
min wannan alfarmar "
ummi tace
"bakomi "
su faseelat
najin abinda suke fada sede ita abun be mata dadi ba ashe dauketa sukayi, yanzu
se yaushe zata ganshi? jin datayi umma tace yana ta kuka yasa taji tausayin shi
ta riga tasan fahad na sonta sosai wannan dukan da yamata Har cikinta yafita
kokadan besa ta rage digon son da takema shi ba,
Faseelat
tace "umma dan Allah kikiraminshi inason ganinshi "
umma tace "kiyi hakuri kinji ,kibarshi yakara
gane kuranshi, hakan zesa kobaya cikin hankalinshi baze iya dukanki ba, kuma ze
kara sanin darajarki "
faseelat tai
shiru,
ganin har
11:30 yasa umma tacewa ummi zasu tafi ta fiddo kudi boundles na 1k ta aje musu,
Ta shafi
fuskar faseelat tace "kiyi hakuri kinji yata gobe inanan zuwa me kkso nazo
miki dashi? "
faseelat ta
girgizakai,
umma tace
"kifada min me kkson ci ni da kaina zan girka miki "
Faseelat ta
yamutsa fuska ahankali tace "komai inaso "
umma tai
murmushi tace "to ki kwantar da hankalinki kiyi bacci "
taiwa ummmi
bankwana ummi nata godiya suka fita daga dakin,
ummi ta
kalli faseelat tace "shasha ashe duk sunsan kin mutu sonshi,mutum ya
nakada maki duka amma kinata nemanshi har uwarshi taji haushi amma ke ko
ajikinki marar zuciya"
faseelat ta
juyar da fuskarta ummi tace "Allah yakawomaki sauki"
khalil ko
abinci kala kala aka kawomishi wanda sede ya tsakura yabarsu saboda bejin dadin
komi hankalinshi kuma yakoma ga hjya yasan iyanzu tana cikin tashin hankali,
musa yazo sukai ta fira sama sama se 9 sannan ya shiga gida,
suma su hjy
sunanan har 10 ganin ba yau zaa sallamesu ba yasa mamar jamila tace wa su hjya
sutafi gida, hjya tace ita zaabari akai akai tatafi taki dole suka hakura suka
tafi sukabarta rungume da lil khalil ,
da khalil da
fahad da hjya da jamila, duk bawanda ya rumtsa,
Baccin asuba
ne ya dauke fahad sede bewani dade ba yafarka ,
karfe 7 aka
sallami su hjy suka dawo gida,
Karfe takwas
fahad ya fita daga gida wanka kadai yayi ya sauya kaya ya nufi gidan su
faseelat sede ya makara don har sunbar gidan yana kulle kamar jiya, ya bata
fuska yanajin kamar yayi kuka ya cize lips ya juya ya tafi gidan umma,
umma na
kitchen don sotake karfe tara tabar gidan,
ya shiga
yayi kwance kan kujera don gabadaya bejin dadin jikinshi,
umma tagama
komi ta fito da niyyar hawa sama tai wanka ta ganshi kwance hannunshi saman
kai,
ta dawo tai
tsaye kanshi tace "lpy me kazo yimin nan? "
fahad ya
tashi zaune kanshi na sara mishi kamar ze kuka yace "Dan Allah umma kiyi
hakuri wlh nayi nadamar abinda na aikata,"
umma tace
"to ni aiba fushi nai ba, don kai kaiwa kanka ,don haka katashi katafi
wadanda kawa laifi yakamata kabawa hakuri bani ba"
yace
"umma nayi zarya gidansu akulle narasa yadda zanyi "
Ta tabe baki
tace "to dama ya zaai ka iskesu tunda kaja musu jinya hakuri zakai har
tasamu lpy insun barmaka ita to ,katashi katafi fita zanyi akwai inda nikeson
zuwa "ta tafi tabarshi dafe da kai fahad ya rasa yadda zeyi kwana guda
jinshi yayi kamar shekara,
umma nagama
shiryawa ta sa me aikinta ta kaimata girkin da tayi da lemun da tahada a mota
sannan tafita ta nufi asibitin,
abul da omer
basunan suna school ,dakin daga ummi se Mubarak da ishak,
umma ta
shiga tana ta faraa lokacin har ummi takama faseelat tayi wanka ta sauya mata
kaya,
Bayan ta
zauna suka gaisa ,
umma taiwa
faseelat ya jiki sannan ta tambaya kotaci abinci, ummi tafada mata bata ciba,
ta zuba farfesun kayan ciki da tayomata ta tada ta zaune tasa hannu ta rika
bata abaki,
agidan hjy
kau anata zaman gaisuwa dan ta tabbatar khalil ya mutu don beje batsari ba kuma
baya kt hakan ya tabbatar da ya mutu tunda safe su kawu manu sunje inda akai
accident din sunga yadda motocin sukai hakan yasa sukadawo suka zauna ansar
gaisuwa,
mata anata
zuwa yiwa hjya gaisuwa da barka lokaci daya,
Anata kiran
fahad da wayoyin Suka isheshi da kara seya kashesu gabadaya donshi bata wani
aiki yake yanzu ba,
yana zuwa
gidan mommy ya tarar da Aisha main palo tana zaune tana kallo ga amira da tai
kukan anty har tagaji kwance kan cinyarta,
amira na
ganinshi ta tashi ta haye sama da gudu,
Aisha
tabishi da kallo duk ya fita hayacinshi,
Fahad ya
zauna gefen Aisha ya kwantar da kanshi akan cinyarta yasaki kuka me taba
zuciya,
Aisha ta
rungumo kanshi tana share mishi hawaye idonta tafff da kwalla tace "kayi
hakuri yaya kadena kuka "duk atunaninta gudunshi da amira keyi yakewa
kuka,
Yana kuka
yace "meyasa zasumin haka? meyasa zasu dauketa daga gareni ina tsananin
sonta bazan iya jure rashinta akusa gare
niba "
Aisha ta
tsaya da share mai hawayen tace ".....
[8/22, 2:56
PM] SHALELE😍: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*
✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽
We are
bearer's of so golden a pen🖊
We write
assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative
golden pen🖊
Be hold our
words
A product of
our pen🖊
Savour our
words
For it will
cause you no pain.✍🏽
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
7⃣4⃣
*ban manta
daku ba,kuna raina,lady ,maman zainab, Aisha habib, Firdausi,sede kundena comments
why?*😒
*soupnas*
comment dinki nasani farin ciki keda *maman nour* comments dinku yana kayatarwa
kucigaba da gashi 💃🏼, *maman nour* wai ina kawalliyarki
*earmeenatuwa*🤣
Aisha tace
"bangane ba yaya? "
Yana cigaba
da kuka yace "iyayen faseelat Sun daukemun ita sun tafi daita"
Aisha farin
ciki ya mamaye zuciyarta batasan lokacin da tasaki murmushi ba tace "Allah
yasa daga can ai can"
Jin abinda
tace Fahad ya tashi zaune yana mata kallon mamaki yace "me kk cewa ne
Aisha? kina farin ciki da abinda yafaru ko? "
Aisha ta
zumburo baki tace "to da so kake nace Allah yasa su medo maka ita? Saboda
ita kamanta duk wata soyayyata idonka ya rufe akanta se kuma nakijin dadin
tafiyarta, wlh naji dadi Allah yasa susa dole ka saketa ,hakanan batasan ya
zaman mu yake ba tayi duk yadda tayi taja hankalinka har ka aurota ni ba abinda
zance sede nace Allah yaraka taki gona "
Ranshi ya
baci sosai da dane da seya mazge bakin amma ya dau alwashin barin dukan
matanshi ya ciza lips yace "toko Allah baze amshi adduar ki ba saboda bame
kyau bace, faseelat tananan dawowa gareni nida ita mutu karaba, don we love
each other insha Allah we will die together"
Aisha dake
jin haushin maganar shi kamar me ta turo baki gaba ,
Yaja tsoki
yace "stupid bansan time din da zaki dena kishin hauka akan faseelat ba,
ita kullum tana girmamaki tana sonki ke kuma ba wacce kika tsana kamarta"
ya tashi
tsaye ze fita Aisha tace "bazaka jira ni mutafi tare ba? "
Beko waigo
ba yace "batare mukazo ba kinsan hanyar gidan inkinso zuwa "
Yajuya ya
bar gidan,
Aisha taja
tsoki tace "so yake nayi addua sumedota kome?wlh yaya ya raina ni da yawa
wai yagama cemin yanason ta har kuma yayi tunanin zanyi wata kyakkyawar addua
can"
Mommy da
tundazu tana kan dining tana jinsu tafito da cup ahannu tana kyalkyata dariya,
Tace
"ke kuma dan ubanki waya ce kice mishi haka keda yazo ki rarrasheshi
"
Aisha tace
"mommy ba abin dariya bane wannan yazaai yazo yana fadamin wai he love her
inba raini ba"
Mommy tace
"to seme dan yace yanason ta tuntuni ina fadamiki kidena fiddo mai kiyyyar ta a fili kirika nuna
kinasonta"
Aisha ta
mike kafarta akan kujera tace"bazan iyaba niba wacce natsana kamarta Allah
nagani da nasota kafin nagane hainta ta take ita ,ni wlh har mamakin zuciya ta
nayi duk yadda natsaneta ranar da ya nakada mata duka seda naji tausayinta
"
Mommy ta
zauna ta kurbi tea tana murmushi tace "kin shirya zaman gida ko? Tunda
kinsan ba zuwa zeyi daukar ki ba "
Aisha tace
"hmm zezo ai Wadda ake makalewar batanan kinanan zaki ganshi "
mommy tai
dariyar manya tace "amma kinyi kuskure karki kara irin wannan "
Aisha tace
"to"
Fahad gida
yakoma yayi kwance zuciyar shi na kuna yarasa ina zesa kanshi ba arziki da
yunwa ta cishi ya tashi ya hada tea yasha,
akai akai
yakan leka unguwarsu faseelat amma gida kulle, har dare yagaji yakoma gida,
Aisha taci
wanka tana jiran yazo daukarta har 9:30 shiru bezo ba ta tashi ta dauko gyale
mommy ta kalleta tace "ina zaki? Bakince ze dawo ba kijira shi "
Aisha ta
yafa gyale akafada tace "mommy baze zo ba tunda har aka kai wannan time
din bezo ba tafiya zanyi maybe yanacan ko abinci beci ba "
mommy tace
"aiko baki isa ba ki samu wuri ki zauna, har se randa yaga dama yazo da
kanshi daukarki "
Aisha ta
turo baki gaba tace "Dan Allah mommy kibarni in tafi wlh hankalina duk baa
kwance yake ba, yaya yana bukata ta yanzu "
mommy tace
"yanzu kikasan haka ai, kicire gyalen nan "
Aisha ta
turo baki ta tafita daga dakin mommy nata kiranta taki amsawa, daga karshe
mommy tace "zakizo kisameni ne "
Aisha ta
fita tasamu napep ta haye yakaita bakin gidansu, ta kwanwasa baba tsoho ya bude
ta shiga ciki,
Ta kitchen
tabiyo ta shigo gidan, fahad na kwance akan gadon faseelat rungume da kayanta
ta shigo dakin,
Dukda yaji
kamshinta amma be nuna ba, tana sanye da riga da wando na Sari ta haye gadon
idanunshi a lumshe ta riko hannunshi tana cewa "yaya kaci abinci kau?
"
yayi banza
ya kyaleta tace "yaya kayi hakuri da abunda yafaru plsss katashi kaci
abinci kar ciwo yakama munkai"
Fahad ya
bude ido yana kallonta ,ta langabe kai tace "plsss katashi kaci abinci?
"
ya yamutsa
fuska yace "Aisha plss leave me alone ba ruwanki da naci abinci ko banci
ba just go to ur room "
kamar zatai
kuka tace "yaya da ruwana mana yanzu in wani abu yasameka fa?bansan
ganinka cikin wannan halin na damuwa kayi hakuri katashi kaci wani abu "
Yace
"bazan ci ba ko dole ne, kitashi kibani wuri, damuwa kuma zan cigaba da
zama acikinta har lokacin da farin cikin rayuwata zata dawo gareni "
Aisha ta
tashi tafita daga dakin tana kuka, fahad yaja tsoki yace "u don't love me
da kina sona da kinso faseelat"
Aisha tafada
kan bed ta cigaba da rusar kuka, ita ba maganganun nashi ba suka fi kona mata
rai aa yadda yabi ya rude harda sukin cin abinci saboda mace, ta sha kuka har
tagaji, har 2 takasa yin bacci shima ba baccin yake ba idonshi biyu,
Kanta na
ciwo Ta tashi ta shiga kitchen ta hado mishi tea me kauri ta dawo dakinshi,
yana kwance yanata kallon silin tazo ta zauna akan gadon murya dishe tace
"Dan Allah yaya katashi kasha ko da tea ne ba don ni ba "
yayi mata
banza tai ta magiya hardasu kuka sannan ya tashi zaune ko kallon fuskarta be ba
ya mika hannu ze amshi cup din, taki bashi ta kai cup din bakinshi seda
yashanye shi tasss sanan ta dauke cup din,
Tai murmushi
ta share hawayenta tace "nagode da ka daure kasha "ta ajiye cup din a
bedside table ta tashi zata bar dakin ya riko hannunta yace "anan zamu
kwana"
Ta dawo ta
kwanta gefenshi ta rungumeshi ba dadewa bacci ya dauketa,shiko yakasa koda
rumtsawa sema kukan faseelat da yayita masa yawo akunne kamar lokacin yake
dukanta duk da AC dake dakin yayita zufa,
Da safe,
tun 7 ya isa
kofar gidansu faseelat lokacin har abba yafita yana tsaye bakin kofa omer
yafito cikin shirin shi ze tafi school, fahad ya mika mai hannu ya mishi
sallama fuska murtuke omer ya mika mai hannu ya amsa gaisuwar, ya zare
hannunshi tun kafin fahad yace komi omer yawuce ya shiga mota yayi tafiyarshi,
fahad yayi
tsaye zuciyarshi na kara zafi,can sega abul yafito shima ze tafi school ko
kallon fahad beba yawuce warshi, sega su ishak da Mubarak sunfito suma zasu
tafi school kasancewar yau Monday abun yabashi mamaki suma basuko kalleshiba
ishak ya garkame gida suka juya suka tafi abun su,
dana sani
yakara cika zuciyar fahad yara kananu ma Sun dena ganin girmanshi ,ya dade
tsaye sannan ya shiga mota ya nufi gida time to time seya share hawaye bakin
ciki da suke fitowa ta gefen idonshi,
Ya koma gida
yayi kwance, Aisha tayi rarrashin yakasa
koda shan ruwa ne har tagaji se yanzu takara gane faseelat ta mata nisa
azuciyar fahad gatade zaune dashi amma zuciyarshi tana wurin faseelat seta
karajin tsanar ta aranta ,damuwar shi yasa itama tashiga damuwa, yakasa komi se
aikin tunani, itama faseelat na can tana fama da ciwo da damuwa amira ma nacan
tana kukan anty, fahad akewa punishment amma su duka suke azabtuwa, har Aisha
taji gwara faseelat din ta dawo kota samu fahad dinta yasamu natsuwa,
Wansafe
tunda asuba fahad yafita da mota a masallacin unguwarsu faseelat yayi salla ana
sallamewa yafito yakoma bakin kofar gidansu ya tsaya yasan de dole abba yafita
sallar asuba, yana nan tsaye yara yaran sukai tawuceshi suna shiga gida, can
zuwa sega yaya omer yana zuwa ya daga mishi hannu yace "assalamu
alaikum" yawuce abunshi, fahad
bewani damu sosai ba shide burinshi yaga abba, yana tsaye sega abba yazo ze
wuce yashiga gida, yayi sauri ya duka yafara gaishe shi memakon ya amsa seya
mika masa hannu suka gaisa fahad na zukunne be tashi ba,cikin ladabi yace
"abba Dan Allah ina neman yafiyarku kuyi hakuri akan abinda na aikata,
nasan ban kyauta ba kuma nayi nadama Dan Allah kuyi hakuri "
abba yace
"banji dadi ba yadda ka wulakanta min diya raina ya baci amma ni na yafe
maka sede ina bukatar ka rubuta mata takardarta saboda zamanku atare akwai
cutarwa "
Fahad da
kanshi ke Duke ya dago arazane besan lokacin da ya mike tsaye ba, sannan yakoma
kasan yana magiya "Dan Allah abba kuyi hakuri inason ta sosai bazan iya
rayuwa batare daita ba, wlh nayi alkawari bazan kara dukanta ba Dan Allah kuyi
hakuri wlh itace rayuwa ta zan kiyaye duk wani abunda ze bata mata rai koya
taba lpyarta"
Jin abinda
yake cewa cikin ran abba yace "nan wurin ba lpy "🤣
Yace
"nide nafada maka Dan Allah kakawomin takardanta in kuma bahaka ba zamu
shiga kotu "yana gama fadar haka ya shige gida,
fahad yaida
yin zaman dirshan awurin yana hawaye da kukan zuci seda gari yayi fayau sanann
yatashi ya nufi gidan umma,
umma ko
kullum setaje asibity suna zaune a dining sun hallara don yin breakfast yashigo
gidan duk sukabishi da kallo umma ko kallonshi batai ba bare ma yabata tausayi,
yazo yaja
kujera ta kusa da daddy ya zauna murya na rawa yabawa daddy labarin abinda
abban faseelat yace,
yace
"Dan Allah daddy kaje kabashi hakuri wlh nayi nadamar dukanta tun daga
lokacin da abun yafaru "
umma tai
karaf tace "alhaji dan Allah ka kyaleshi karka shiga wannan maganar kaje
kaji kunya kaima kasan sunada gaskiya gwara ya saketan yafi tunda beda hali
"
Fahad
idonshi cike da hawaye yake kallonta,
daddy yace
"a, a bahaka yakamata ba, zanje nasamu abban nasu in roki yafiyarsu, ka
kwantar da hankalinka kaji "
fahad de
bece komi ba ya tashi yafita tun kafin yakai gida zazzabi ya rufeshi yana zuwa
ya shiga wurin Aisha ya kwanta ya kudundune jikinshi na mazari, Aisha ta rude
tai ta kuka ta kira doctor ba dadewa okaton yazo ya dubashi jinin shi yahau
yabashi drugs da shawarwari ya fita, dakyar Aisha tasamu yasha maganin da aka
rubuta mishi badadewa bacci ya dauke shi dan cikin magungunan akwai na bacci
acikinsu kwananshi ukku ba bacci saboda rashin faseelat, Aisha na zaune
gefenshi tai tagumi tana kallon fuskarshi duk yabi ya rame har baki ma yayi ba
wata kwanciyar hankali duk harijan cin nan ya tafi 🤣yau kwana ukku ba tabi 😅,
awurin
aikinshi anyi neman wayoyinshi amma switch off ba karamar asara suke yiba
mutane sunyi zarya gidanshi sede baba
tsoho yace bayanan, don fahad yabashi umarnin fadin hakan,
Yau akayi
sadakar ukkun khalil su hjya suna cikin tashin hankali har yau, jamila duk tabi
ta zube ta rame duk kibarnan ta tafi hartafi lokacin da take budurwa rama, hjy
ma ta kanjame don bata bacci rashin ganin gawar nema yakara tada mata hankali,
zakuyi mamaki innacemaku hjy ce kebawa jamila abinci abaki don mugun tausayinta
takeji tana ganin kamar itace takashe mata miji, kullum lil khalil yana
hannunta ,
bayan yan
gaisuwa Sun wuce da marece sosai mamar jamila sun hadu falon hjy tafadawa hjy
yau zasu koma gida kuma tareda jamila zasu tafi,
Hjya tafashe
da kuka tace"dan Allah zulai kubarmin yarinyar nan awurina wlh yanzu ba
abunda nake kallo naji dadi se ita da danta, ina rokon kubarmin ita tazauna
anan nawani lokaci ,zuwa lokacin da zansamu natsuwa nida kaina zan medo muku
ita na rokeku "
Maman jamila
tace "hjy zamu tafi daita ne don amata wanka, kuma anan zata karamiki
damuwa tunda har yanzu taki dena kuka ga danta dabata damu dashiba,dawainiya
zata miki yawa ki kula daita ki kula da danta, gwara mutafi daita can "
hjy tace
"wlh bata karamun damuwa, wanka kuma zansamu unguwar zoman da zata mata
wanka, kula daita da danta bawani abu bane wurina, nide ina rokonku wannan
alfarmar"
dakin yayi
shiru na wani lokaci jamila na kuryan hjy kan dadduma tanajin komai hawaye suka
kara zubomata wai hjy ce kuka tana rokon abar mata ita inama ace lokacin da
khalil yana raye ta nuna mata wannan soyayyar ba yanzu ba,
Baban jamila
yace "toshikenan hjy ga jamila nan zata cigaba da zama anan kamar yadda
kika bukata, Allah yakara mamu hakurin rashin khalil "
Maman jamila
tai shiru dan taso tatafi da yarta takula daita sosai ,
hjy tafara
godiya "nagode sosai Allah yabar zumunci"
sukace
"amin "
Maman jamila
ta tashi tashiga ciki tasamu jamila dake zaune ta zauna tace "jamila zaki
zauna nan din? "
jamila ta
daga kai tana matse baki,itakanta jamilar tausayin hjy takeji saboda Halinda
tashiga, lalle mutuwa waazi ce gasu ba sulhu sun dedeta,
maman jamila
tace "to amma ki kula da kanki sosai don dinkin jikinki ya warke kuma ki
daure kiyi hakuri jamila khalil de yatafi baze dawo ba addua kawai zaki rika
masa "
jamila tace
"to mama"
maman jamila
ta tashi tafita hjya nata godiya suka tafi garinsu,
Unguwar
zomar dake dora musu ruwa itace ta cigaba da yiwa jamila wanka kuma tana bakin
kokarinta,
Khalil ko
yanacan yana daukar darasi musa ya girme shi dan yayi 45 amma yanayin yadda
yake tafiyar da rayuwa ya burge khalil, yana aiki ne a babbar ruga shima
likitan fata ne, bayada wani hali sosai amma kullum dasafe se anfita da Kula da
bokitai na kunu wanda ake kaiwa asibity ana rabawa patients marassashi, da
yadawo daga asibity yake sauya kaya bayasa kananan kaya, kuma kayansa duk ba
tazarce suna da dan shape Iya gwiwa yaiya dressing sosai anan khalil yakara
daukar cause din saka hula ashe ba bakin ido ake kaita ba 😬tsakiyar goshi ake dedeta ta,
Shima musa
ya karu da khalil dan yalura khalil kosu na magana yana dannar counter dinshi
in suka tsagaita wani lokaci yana ganin bakinshi na motsi ,shima yanzu ya dage
rikon counter yana tasbihi kuma yakara kula da mahifiyarshi akan baya don yayi
mamakin dukda khalil bejin dadin mahaifiyarsa amma burinshi ya rayu dan ya kara
kyautata mata bare shi tashi da yakejin dadinta ,
da drugs
suka saki fahad ya farka tsakar dare dakyar Aisha tasamu yasha tea tayi
iyayinta yakara shan magani yaki wai beso yayi bacci ,idanshi biyu har asuba
yakara komawa gun abba,
abba beji
wani tausayin shi ba yakara memeta mishi abinda yafada jiya don umarnin alhaji
babba ne kuma shi bemasan su ummi sunyi wata magana da mahaifiyar fahad ba yade
san tana zuwa amma besan komi daganan ba,
fahad ya
koma gida ya dukunkune dan zazzabin da yakara rufeshi fiyeda jiya,
sabeer ya
kira wayar fahad many times besameshi ba, tun karfe 7 yayi parking kofar
gidanshi yafara knocking gate, baba tsoho ya bude mishi yaganshi tsaye baba
tsoho da yasaba ganin shi yana faraa yace "barka da zuwa alhaji "
Sabeer yace
"ina kwana baba, mutumen yana ciki kau? "
baba tsoho
yace "eh yana ciki sede yace duk wanda yazo ace bayanan"
Sabeer ya
girgiza kai yace "OK Allah yasa lpy nizanshiga naganshi"
baba tsoho
yace "afito lpy "
sabeer
yawuce ciki yatsaya bakin kofa ya danna door bell shiru yadade tsaye yanata
dannawa sannan Aisha taji tazo tabude mishi,
idanunta
jawur dan tana shan kuka akai akai ta yadda fahad be damu daita ba, ga kuma
damuwa da halin da yake ciki "tana ganin sabeer taji dadi ,
sabeer ya
kalleta tayi wani kala abun tausayi yace "Aisha lpy kuke "?
Aisha tace
"sabeer yaya yadena kula dani baya bacci baya cin abinci baya zuwa aiki
baya komi se tunanin faseelat, tun jiya baya lpy har yau nayi iya kokarina yaki
shan magani doctor ma yace jinin shi ya hau sosai, yarage damuwa amma yaki,dan
Allah kaje kamishi magana koyaji ya rage yiwa kanshi wannan horon"
ta matukar
bashi tausayi yace "kiyi hakuri insha Allah ze dawo dede muje naganshi
"
Aisha tawuce
tahaye step sabeer na bayanta har cikin dakin faseelat da fahad ke kwance cikin
duvet,
Aisha na
tsaye sabeer yaje ya zauna kan bedside ya dan yaye duvet zuwa kan fuskar fahad
yaganshi duk yayi wani wuriwuri dashi,
be wani
mamaki ba don yasan yana matukar son faseelat ,sede yaji haushi yadda ita Aisha
ke azabtuwa saboda da damuwarshi
Fahad ya
bude ido ya kalli sabeer, sabeer yace"yanzu fahad dan an dauke faseelat
shikenan Kagama rayuwa, kazauna kana wahalar da kanka da matarka, ka ki yin
aiki kaki zuwa office kasan asarar da akeyi kuwa kuma kasan kamfani baze dauki
asara ba "?
Fahad da
muryarshi ta Marassa lpy yace "I know and I don't care ,idan har basu
barmin faseelat ba mutuwa zanyi she's my life bazan iya dena tunaninta ba kona
second "
sabeer yadan
saci kallon Aisha don shi kanshi yaji haushin maganar yaga tana ta kallon fahad
tana hawaye,
Yace ma
fahad "to cewa sukai bazasu baka itaba kome? "
fahad yace
"naje 2times wurin mahaifinta he's
asking for her divorce later nabashi hakuri amma beyiba "
Sabeer yace
"Dan Allah friend karika hakuri da yadda rayuwa tazo maka, yanzu kaga
Aisha daita dakai bazaa gane marar lpyar ba, ka daure karika shan magani ko
kasamu lpy "
"yanzu
ka kwantar da hankalinka kabani address na gidansu zanje nasamu mahaifinta
nakara bashi hakuri zan kuma nemi alfarmar yafadamin asibitin da suka kaita,
kaje kadubota koka dawo dede "
fahad yafada
mishi adress din ,
sabeer yace
"zanje nasameshi insha Allah zanyi bakin kokarina wurin shawo kanshi amma
katashi kasha magani"
fahad yace
"magani baze yimin wani amfani ba faseelat itace maganin rashin lpy ta
"
Sabeer ya
tabe baki yace "Allah yasawwake to, bari natafi gidan nasu "ya mike
tsaye,
fahad ya
meda kanshi cikin duvet, da hannu sabeer yayiwa Aisha dake tsaye tana hadiyar
zuciya magana akan ta biyoshi, ta bishi suna fita kofar dakin, sabeer ya juyo
yace "kiyi hakuri Aisha da yanayin shi, karki bari suratan shi su dameki
naga kamar baya cikin hayyacin shi, kiyi hakuri ki sa masa ido "
Aisha tai
murmushin da yafi kuka ciwo aranta tace aiba yanxu nafara jin irin wadannan
daga bakinshi ba, afili tace "Tom nagode Dan Allah kayi bakin kokarinka
wurin samo mishi address na gidan nima zanso yaganta koya dan samu sauki "
sabeer ya
lumshe ido ya bude yanajin matsanancin tausayinta yace "I will do my best
"
ya juya
yatafi ita kuma takoma dakin ta kwanta gefen fahad don hakanan take kokari amma
zuciyarta matsanancin ciwo take,
sabeer na
cikin mota yana tuki hannunshi daya akan bakinshi yana tunanin maganganun
fahad,yace"kammmm amma wlh Aisha na hakuri, wannan irin so haka to ko ya
zaman nasu yake? nide insha Allah bazan bari matana sugane wacce nafiso
ba,"
har yaisa
unguwarsu faseelat gidannasu a kulle dayake komi acikin natsuwa yafi hankali
seya nufi wasu samari dake zaune can gaba da gidan bayan ya musu sallama
yatambaye su kosun san inda zesa mu alhaji maaruf,suka fada mishi ai shagon shi
nanan kofar keke, ya musu godiya ya kama hanyar kofar keke don ganawa da abba,
gaskiya duk
group din da baa comments zandena turawa aciki kunsamu awani wuri, yan groups
dina kuma zanfara removing marassa magana wasu ma tunda suka shigo basuyi
magana ba kar in cire mutum yaji badadi shiyasa nafada kurika comments please,
shalele
novels group
Shalele
value group
shalele
boost group
raggon miji
fans 123
duk wace
batason ganinta awaje tarika comment.
[8/23, 2:42
PM] SHALELE😍: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*
✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽
We are
bearer's of so golden a pen🖊
We write
assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative
golden pen🖊
Be hold our
words
A product of
our pen🖊
Savour our
words
For it will
cause you no pain.✍🏽
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
7⃣5⃣
*page
dinkune yan group dina shalele novels group, kai jiya kun matukar burgeni
wannan ruwan comments haka, naji dadi sosai Allah yasa ku dore 😍*
Ba wuya ya
gane shagon shi ya shiga ciki da sallama bakinshi,
Shagon ba
kowa ciki don safiya ce mutane basu fito ba, abba ya amsa sallamar yana kallon
sabeer,
Sabeeer yaja
bench ya zauna acikin ladabi yace
"abba ina kwana ya mejiki? "
Se sannan
abba ya gane ba siyayya yazo ba yace " lpy lau dasauki "
Sabeer ya
kara sunkuyar da kai yace "abba ni abokin fahad ne aminina ne sosai, nazo
ne nakara baku hakuri akan abinda yayi wlh yayi nadama sosai yana cikin tashin
hankali yanzu haka ma baya lafiya, Dan Allah abba amishi hakuri kar a rabasu
domin yana sonta sosai kishi ne ya rufe mai ido har ya mata haka "
Abba yayi
murmushinsu na manya yace "u only know about ur friend, yayanta da
kannenta suna nan suma duk basajin dadi atare suke jinyar, kishi ai bahauka
bane daze mata irin wannan dukan haka, don kishin ma nada kyau manzon Allah (S.
A. W)cewa yayi wanda baya kishin matar sa baze shiga aljanna ba, amma shi nashi
yawuce akira shi kishi gaskiya "
Sabeer yace
"Dan Allah abba kuyi hakuri kudauki wannan abunda yafaru a matsayin
kaddara "
Abba yace
"mun dauki kaddara kam amma seya saketa "
Sabeer yace
"kuyi hakuri dan Allah wlh duk gidannashi ya birkice rashin faseelat,
shiba lpy matarshi ma yarshi ma, Dan Allah kuyi hakuri tunda yagane kuransa
nasan nan gaba baze sake ba "
Abba yayi
shiru sabeer ya cigaba da bada hakuri,
Jim kadan
abba yace "nifa nadade da yafemasa tunda ya sameni batun saki kuma bani
zebawa hakuri ba seyabari idan alhaji yadawo daga Niger yaje yasameshi idan ya
yafemishi shikenan danni haifuwar yara na kawai nayi amma alhaji yafini son su
yafini kula dasu danhaka nabar masa ragamarsu seyajira shi har yadawo nanda
kwana goma "
Cikin ran
sabeer yace "tirkashi yo shi yana kai kwana goman ma "
Afili yace
"to nagode sosai abba Dan Allah ina rokon alfarma abani address na
asibitin da faseelat take ,wlh yar shi ma kullum kuka takeyi tanason ganin
antin ta atemaka Dan Allah "yayi kamar maroki,
Abba ya
yamutsa fuska yace "nan ne asibitin turai room 9"
sabeer yace
" nagode sosai abba ina kuma kara baku hakuri akan abinda abokina yayi
"
abba yace
"bakomi "
Sabeer ya
mishi bankwana ya tafi,
direct gidan
fahad yawuce, Aisha ta budemai yashiga yana shiga dakin da fahad yake ya zauna
gefen shi ya furzar da iska ya dan bugi fahad yace "katashi muyi magana
"
fahad ya
yamutsa fuska jikinshi na fidda wani irin suraci yace "komi zaka fada
kafada inajinka kaje baka samesu ba ko? Bashi ne maganar ba "
Sabeer yaja
tsoki yace "to wlh zanyi tafiya ta in baka tashi ba nasameshi har
shagonshi nabishi amma zan tafiya ta "
fahad ya
tashi yana yamutsa fuska yace "inajin ka "
sabeer ya
kalleshi duk yadda ya koma yace "look at you hmm, na sameshi nabashi
hakuri sosai yace shide ya yafe amma seka saketa da nai ta bashi hakuri yace
shi yahakura sede kajira yayanshi da yatafi Niger har yadawo kabashi hakuri in ya hakura
shikenan yacemin nanda kwana goma ze dawo "
fahad ya
tabe baki yace "kafin kwana goman na mutu ai ,wlh ina cikin hali zuciyata
ciwo takemin kamar zata buga"
sabeer yace
"kai kasani ai kana mutuwa ni kuma nasamu mata "
fahad ya
wurga mai harara sabeer yayi karamin murmushi yace "eh mana ko haramunne?"
fahad ya
koma ze kwanta sabeer yace "jira mana inada good news bayan bad one's
nasamo maka asibitin da take da room number "
fahad yafasa
kwanciyar yace "wace asibity room nawa? "
sabeer
yace"turai room 9"
fahad naji
ya yaye duvet din yatashi tsaye Aisha na gefe na kallon ikon Allah,
ba bata
lokaci ya bude wardrobe ya dauko jallabiya ya zira ya dauki key din mota yayi
hanyar fita ,
sabeer yace
" kai malam bazaka tsaya muida maganar ba? ko godiya aikatsaya kamin
"
fahad ya
juyo yace "thanks ,kuma kafitomin daga dakin mata "ya juya ya bude
kofa yafita yana sauri,
Sabeer yayi
murmushi ya girgiza kai ya tashi tsaye, ya kalli Aisha yace "Allah yabashi
lpy ni natafi aita hakuri lokacine "
Aisha batace
komi ba, ya fita,
Koda yafita
har fahad yabar gidan ya shiga motarshi ya nufi office,
fahad yayi
ta sharara gudu cikin mintuna kalilan yaisa turai yana tafiya ahankali jikinshi
ba kwari har yaisa kofar dakin,
nan kuma
gabanshi yarika faduwa yayi knocking so biyu omer da tunda yazo duba faseelat
yakasa tafiya saboda yadda ya ganta yana zaune yana bata abinci yace "turo
"
Jiki mace
fahad ya tura kofar dakin yana shiga yaga faseelat jikin omer ,zuciyarshi tayi
mummunar bugawa, (ana nanfa me hali.....) dasauri yafara a'uziya yana korar
shedan aranshi
Faseelat
idonta a lumshe suke itakadai tasan yadda takeji abubuwa Sun jagule mata ba
ciki ba fahad ga ciwo, kamshin fahad daya kewaye dakin yasa faseelat ta bude
ido ta ganshi tsaye kamar bashi ba duk ya rame ya jeme yayi wani iri, tausayin
kansu yakamata ta meda ido ta lumshe,
kallo daya
omer ya mishi ya daure fuska tamau,
fahad yasamu
yakara dedeta kanshi ya karasa ciki,
Ya mikawa
omer hannu, omer yabashi sukai musabaha kowa ya zare nashi,
Omer ya
dauki spoon yakara kaiwa setin bakin faseelat
,ta kauda kai idonta lumshe,
Omer ya
kwantar da ita ya ajiye cup din yafita don in yatsaya bazaa kwashe lpy ba,
Bakowa dakin
domin ummi tafita,
fahad
yakarasa bakin gadon da faseelat take kwance yana kallonta tayi muguwar rama
tayi fayau,
Faseelat kam
taji dama da taganshi amma bataji dadin yadda taganshi duk yafita hayyacin shi
ba,
Fahad Ya
zauna kan bed din yanajin matsanancin tausayin ta ya dora hannu akan cikinta ,
yace "I'm sorry honey I hurt you, na rabaki da farin cikin ki I'm very
sorry kiyafemin " hawaye suka zubomai ,
faseelat
bata bude ido ba tai shiru se takara jin kewar cikinta don tunda yana 3wks
yafara mata motsi,
Fahad ya
riko hannunta ya rungume a kirji ya saki kuka, tabude ido tana kallonshi ba
tayi shiru dan tanajin haushin shiba ne tayi shiru ne don kartai magana tayi
kuka don inde tabude baki kuka zatai, ganin yana kuka yasa tafara hawaye,
irin muryar
marassa lpy tana hadiye kukanta tace "hero kadena kuka,bakamin komi ba,
nasani acikin tunaninka bazaka yimin haka ba,kayi hakuri kashare hawayenka
banajin dadin ganinsu"
fahad yanata
kallonta da jikakkun eye lashes dinsa tunda tafara magana ,yace "we lose
our baby "
faseelat ta
lumshe ido ta bude tace "Allah ze bamu wani, kadena damuwa "
Fahad be
dena hawaye ba na tausayi da kaunar faseelat yariga yasan tana sonshi sosai
yanzu dabata yi fushi dashi ba sonta yakara ninkuwa a ruhinshi,
faseelat
tace "stop shedding ur tears pls, har yanzu inasonka mijina nayi kewar ka
sosai, kewarka tafi ciwon jikina zafi amma na samu lpya da naganka
"tasakar mishi murmushi,
Ya share
hawayenshi ya duka ya mata kiss a wuya yace "I miss you too kidubeni yadda
sonki ya medani ina wahala honey "
faseelat tai
murmushi tace "I'm very sorry ina Princess?ina anty I hope suna lpy "
Yakai hannunta
dayake rungume dashi abaki ya mishi kisss yana karajin sonta yace "Aisha
tana nan lpy, princess bata lpy, yanzu haka bata gida don tsoro na takeji
saboda halin da ta ganki aciki, kiyi hakuri honey wlh bansan nayi ba bansan
meke faruwa ba sede naganki cikin jini "
faseelat ta
lumshe ido tana tunanin yadda yashigo toilet din ya fincikota, tace"i
known kadena damuwa na yafe maka since,yakamata ka kawomin amira naganta kona
ida warwarewa ina kewarta da surutun ta "
Yace
"zan kawomiki ita meyasa baki fushi dani ba ?"
Tai murmushi
tce"yazaai na iya fushi dakai, kaine rayuwata hero ina tsananin sonka
bazan iya rayuwa in babu kai ba "
Yana
tausayin kansu yace "gashi zasu rabamu abba is asking for ur divorce paper
,yan uwanki duk basu son kici gaba da zama dani "
faseelat ta
dan bata fuska jin abinda ke faruwa tace"bazasu rabamu ba don inasonka
sosai ka kwantar da hankalin ka ni takace, taka kai kadai my hero,u r my
everything we will be together forever "
fahad yayi
shiru yana aika mata da wani kallo me kashe jiki, itama ta rika aika masa da
nata sihirtaccen kallon da murmushi kan fuskarta dukkansu Sun manta aina suke,
ahankali
fahad yake kasa da fuskarshi zuwa tata, har fuskokin su suka hade suka rika
kissing juna passionately, dukansu sunajin matsanancin dadi,
Ummi da taje
dubo diyar wata kawarta data haihu ta dawo omer har ya tafiyarshi yabar
asibitin gabadaya, batare da tasan abinda ke faruwa ba ta tura kofar dakin
tashiga, abinda tagani ne yasa ta fiddo ido waje, faseelat na kwance fahad
agefenta azaune ya sunkuya har yadan danne ta sunata kissing bakunan juna a
dimauce faseelat hardasa hannu tarike mai kai don duk sunyi kewar juna,
ummi batasan
lokacin da bakinta yafara hailala ba "Lailaha illal lah Muhammadur
rasulillah (S. A. W)
tun kan
takarasa faseelat ta Saki kan fahad, ya tashi zaune ya sadda kai yana sosa
keya, itako faseelat ta rumtse ido,
kafin ummi
tai magana umma ta turo dakin da faraa da sallama bakinta,
Taga fahad
zaune gefen faseelat ga ummi tsaye hannunta kan bakinta da alama yanzu tashigo,
Umma tabata
fuska tace "kai me kakeyi a nan?
"
fahad ya
dago ya kalli umma ya kara sadda kai kasa,
tace
"tambayarka nake me kk anan da ba kasheta kaso kayi ba "
fahad yayi
fuskar tausayi yace "umma nazo dubata ne, bawani abu ba "
tace "to
tashi kafita tunda kagantan"
Fahad ya
kalli faseelat da har lokacin idonta ke kulle tanajin matsanan ciyar kunya ya
tashi ya fita yanajin kamar yayi kuka, faseelat jitayi kamar tajawo shi ya dawo
ya zauna dan zamannan nashi setaji har karfin jiki tasamu,
yana fita
umma taja tsoki, har lokacin ummi na tsaye da hannu abaki, umma ta kalleta tace
"se hakuri yaran zamani basu da kunya kokadan"batasan ma abinda
sukayiba zaman shin agadon kadai ma taga bedace ba,
Aran ummi
tace "aini naga dahirrr"
umma takarasa
ta ajiye kulas dake hannunta da ledoji ta zauna gefen faseelat tana kallon
fuskarta, datake kamar meyin bacci,
ta juya ta
kalli ummi tace "bacci ma take ko? "
ummi tace
"ihmmm idonta biyu "
umma ta riko
hannunta tace "daughter yau bakison ganina ne? "
Faseelat ta
bude ido badan taso ba, bata kalli gun ummi ba tace "sannu da zuwa umma
"
Umma tace
"yawwa ya jikin? "
faseelat
tace "naji sauki"
ummi tace
"kwarai kau taji sauki azoma a sallame mu mutafi gida haka ta karasa
warwarewa acan"
Umma tai
dariya tace "zaman asibiti akwai cin rai dama amma tunda ta samu lpy gwara
ku koma gidan "
ummi tace
"ai dole saboda banga amfanin zaman da muke ba "
umma tai
dariya ta meda hankalinta gun faseelat tace "yau tuwon shinkafa miyar
shuwaka na miki danta temaka jinin da yarage ya ida wankowa, inafatan zakiiya
ci? "
faseelat ta
daga kai, umma tafara zuba abincin faseelat ta saci kallon ummi taga har
lokacin ita take kallo takara lumshe ido sosai,
Umma nagama
zubawa ta tadata zaune ta rika bata batajin yunwa bataci sosai ba tace takoshi,
Umma na nan
zaune zuwa sha biyu da 30 lady da safiyya suka zo sannan suka tafi tare,
Suna fita
kamar ummi najira tace "kede anyi jarababbar banza daga zuwanshi kin sakar
mai jiki yakara dura miki wani cikin yakara zubardashi shasha wadda batasan
ciwon kanta ba"
maganar ummi
tabawa faseelat dariya aiko tadora hannu abaki tafara dariya ummi tace
"dariya nabaki ko zata koma maki kuka don alhaji babba yace dole seya
sakeki bazaki komaba kuma kinsan shi in abu yabata mai rai yana dadewa be sauko
ba "
faseelat ta
tashi zaune idonta taff da hawaye tace "ummi dan Allah kuyi hakuri
kutemaka mana wlh kuskurene kuma bazaya kara faruwa ba "
ummi tace
"seki bari seyazo seki fadamai nide ba ruwana aciki"
faseelat ta
koma ta langwabe,ciwo yadawo ummi tace "kima tashi alhaji kawai nake jira
yazo a sallame mu nagama wahala dake kuma "
Faseelat Tai
shiru gabanta nata faduwa,
Tunda fahad
yafita Aisha take kuka, tayi danasani tayi danasanin sanin faseelat a rayuwarta
tanata karajin mugun tsanarta a ranta,
fahad ya
nemi fever din jikinshi ya rasa yana cikin mota se lasar lips yake yana sakin
murmushi shikadai, gsskiya he's missing he's messing soft and sweet hq na
faseelat
yana zuwa
gida ya shiga yasamu Aisha kwance taci kuka tagaji, yaje wurinta ya zauna ya
medo kanta jikinshi yace "meke damunki ne Aisha?"
Aisha ta
kalleshi cikin ranta tace shifa har ya warke, tace "zuciyata ke ciwo
sosai"
Ya bata
fuska yanajin tausayinta yace "sannu heart beat bari nakawo miki abinci da
magani dan Allah kikara hakuri dani "ya aje kanta ya nufi kitchen,
Aisha tabi
bayanshi da kallo tanajin takaici tace "ga heart beat dinka can ni I'm
only a sister kuma kasan baka kyautamin kenan har kake bani hakuri"
shima yunwa
yakeji ya dafa musu indomi da kwai yadauko mata magungunanta itama yunwa takeji
ta bude baki tadanci yabata magani sannan yaci nashi yana gamawa ya dauketa
yanata mata sannu taita kallonshi kawai,
ya sakarmata
murmushi yace "I love you heart beat ina tsananin sonki"
aisha tai
murmushi me ciwo tace "I love you yaya more than everything in this world
"
Yace
"thanks you so much dear ya kaimata kisss a head"
Akan bed
yaajeta yashiga toilet ya watsa ruwan dumi don yakara jin karfin jikinshi
yadawo har lokacin bacci be dauketa ba tana ta kallon shi kamar bashi ne ke
kwance dazun ba, yazo ya haye bisa gadon ya matseta yafara aika mata da kisses,
Bata hana
shi ba don itama tayi kewar dumin jikinshi sambatunshi and his sweet words
after sex,
bayan komi
yagama wakana ya rungumeta yana fada mata sweet words da kullum yake fadin
sabbi kuma tanajin dadinsu ,har bacci ya dauketa yana rungume daita ya dade
yana kallon fuskarta duk ta rame ya shafi gashinta ya tashi yayo wanka yasaka
kaya ya nufi gidan mommy dauko amira yakaita wurin faseelat,
koda yaje
yasamu amira kwance tana bacci ya Daukota beko gaisa da mommy ba ya nufi
asibity,
Tun kafin
yakai amira tafarka tana ganinshi tafara kuka yace "princess wurin anty
zan kaiki kiyi shiru kinji "
amira tace
"aika kasheta ni kamedani wurin mommy "
yanajin
zafin maganganunta yace "antinki bata mutu ba kiyi hakuri mutafi wurinta
tanason ganinki, kinji?"
Tai ta kuka
yanata rarrashi har suka isa ya fito ya dauketa suna Zuwa bakin kofar dakin ya
tura yace tashiga, amira tashiga dakin wayam bakowa don an sallamesu,
yana tsaye
bakin kofa tafito tana kuka, ya riketa yace "me akamiki? "
tace "u
lied to me bata ciki "
Ya tashi ya
tura kofar wayam ba kowa, ya dafe kai yace "nashiga ukku"
amira ta
kama hanya zatai tafiyarta yabita ya dauketa tana ta harbe harbe, har suka isa
bakin mota ya dorata saman motar ya zaro mata ido rai bace yace "Dan
ubanki natsu kimun gumm wlh kona zane ki "
amira tai
gum tana ta hadiyar kukan, don betaba mata haka ba
Idonshi
jawur yace "in kara jin kin min kuka sena miki dan banzan duka "
ya dauketa
yasata motar suka tafi gidansu faseelat gidan kau a bude yake,
Ya fito ya
dauketa yakaita har bakin kofa yace "she's inside enter "
a tsorace ta
shiga cikin gidan, ummi nata yan aikace aikace amira ta shigo tana share hawaye
Ummi tace
"a, a amira kedawa? "
amira tace
"daddy ne yace anty tananan in shigo "
ummi tajawo
hannunta tace "antinki nanan kuwa"ta shigar daita dakin faseelat
faseelat na
kwance bacci ya dauketa, amira ta tafi ta rungumeta tana kuka,
faseelat ta
bude ido taga amira ta riko fuskarta tace "princess yaakai me kikewa kuka?
"
amira tace
"inata nemanki banganki ba anty karki dawo gidanmu daddy yakara
dukanki"
ummi tace
"kwarai ko fadamata gaskiya tunda ita kwakwalwarta ta toshe"tajuya
tafita tana surutai
Faseelat ta
sa hannu tana sharewa faseelat hawaye tace"bakiso na dawo mu cigaba da cin
abinci tare, karatu, wasa, bakiso? "
Amira tace
"inaso amma daddy na dukanki bana so ya cigaba da dukanki"
Faseelat
tajawota ta rungumeta tace "baze kara ba it was a mistake kuma it won't
happen again kinji? Kidena jin tsoron daddynki he loves you baze miki komai
ba"
Amira
tace"he don't love me anymore, yanzu ma yafadamin ze zane ni"
faseelat
tace "kidena tsoronshi baze miki komai ba, kinji ko maybe kin bata masa
rai kuma I have told you baa batawa iyaye rai "
amira ta
daga kai, sunanan kwance sunata dan labari amira nabata labarin abinda yafaru
bayan batanan,
fahad yana
cikin mota zaune se tunani yake shifa he want to see her me yasa aka sallamesu
acan zesamu damar ganinta anan ko baze samu ba "
omer yadawo
daga aiki har yazo yashiga gida fahad be lura dashi ba yanata tunani,
omer nashiga
ummi na tsakar gida yace "lpy ummi naje asibitin naga bakwanan kuma naga
har yanzu dasauran jikinta "
ummi tace
"kai ke ganin haka amma ita ta samu
sauki ,ina dawowa dakin nasamu mijinta yazo ya danneta sunata tsotsar juna,
shiyasa nace a sallame mu takarasa warware wa anan karma yadura mata wani cikin
tun muna asibitin tunda de ita sakarai ce"
Omer ranshi
ya baci yaja tsoki yace "yanzu ma nabaro shi kofar gida kome yake anan
shima yasan baze samu ganin taba "
Ummi tace
"yarshi yakawo tana ciki wurin ta"
omer yaja
tsoki ya nufi dakin faseelat suna kwance ya janye amira, yace "kede anyi
wawuya wadda batasan ciwon kanta ba, wato wannan karan ma bakiga laifinshi ba
ko? To inke bakisan ciwon kanki ba mu munsan ciwon kanmu"
Yaja amira
suka fita waje har bakin motar fahad da kofar ke bude ya tafi dogon tunani gwam
gwam omer ya kwankwasa motar, fahad ya dago yana kallonshi,
Omer ya tura
amira wurinshi yace "take ur daughter and go karka sake dawowa kofar
gidannan, I warned you kar nakara ganin ka anan idan kuma kazo to zaka sha
mamaki"
Fuuuu yajuya
cikin gida,
Fahad yayi
kasake yana ta kallon bayan shi, ya girmi omer amma gashi yanata datsa mishi
magana, amira dake ta kuka tace "daddy ni awurin anty zan zauna"
Zuciyarshi
na zafi ya dauketa yasata cikin motar suka nufi gida ita tana ta kuka shi kuma
yanata tunani tunkafin suyi nisa zazzabin yadawo mishi,
Itama
faseelat tana can tana kuka.
comments,
comment's nikuma in rika antayo maku long page ko mungama.
No comments