NAJEEB 1
ASSALAMU'ALAIKUM
DA SUNAN
ALLAH MAI RAHMA MAI JIN 'KAI, TSARKI YA TABBATA GA ALLAH UBAN GIJIN TALIKAI
WANDA YA SAKE BANI DAMAN SAKE RUBUTA WANNAN LABARIN, YANDA NA FARA LAFIYA ALLAH
YASA IN GAMA LAFIYA🙏
WARNING
BAN SON
KORAFI, WANDA YAGA BAZAI IYABA YA BARI, SHI RAYUWA BABU DOLE, BAZAN D'AUKI ZAGIN DA AKAMUN AKAN NOVEL DIN
BARIKI NA FITO BA NOVEL D'INA KYAUTA NE, AMMA WLH IDAN AKA ZAGENI ZAI KOMA NA
KUD'I, NASAN REAL FAN'S D'INA WILL COME AND PAY, FAKE ONE KUMA NASAN BAZASU
ZOBA, SO PLZ A KIYAYE, IN KAGA BAI MAKA BA, JUST LEAVE IT, SANNAN WANNAN
LABARIN ZAIZO DA WANI SALO, KAWAI KU BIYONI NA RIGA NA TSARA LABARIN.
LONDON
Airport wani
jirgi ne mai cin mutane 500, ya sauka airport inda mutane suka fara fitowa,
yayin da masu taransu suke tsaye suna jiransu, haka har suka gama fita daka
cikin jirgin.
Wani Guy ne
fari Mai cikar zati ga kyau ga kwarjini ya fito daka cikin jirgin sanye da
farin kaya, wanda zai baka tabbacin cewa shi pilot ne.
Mi'ka yayi
tare da kallon gefenshi inda ya fara tafiya lokaci d'aya, wani d'aki ya nufa
inda Nan ne aka tanadar ma matuka jirgin in sunzo zasu dinga hutawa, d'akuna ne
a jere sunkai guda Goma, shiga yayi yana shiga yayi toilet.
Jim kad'an
sai gashi ya fito alaman yayi wanka yana goge kanshi da towel, wayanshi ne ya
fara ruri d'auka yayi yaga Monica, d'an tsaki yaja tare da danna wayar yace
nazo, just coming, yana fad'in haka ya kashe wayan ba tare da yaji Mai zata
fad'a mishi ba.
Ko 30mnt da
Gama wayan baiyi ba aka fara mishi nocking, daka shi sai boxer a jikinshi, babu
ko riga, haka ya tashi ya bud'e kofar, ganin Monica ce yasa ya kura mata ido
ganin irin shigar da tayi wanda gaba d'aya half naked, d'an tsaki yayi domin
duk da Monica Tana biya mishi bukata baya son tana irin wannan dressing din,
dan yana da kishi, uwa uba bazai so ramin daya shiga ba wani ya shiga, shi kaf
y'an matanshi sun San halinshi, shi zai iyayin komai a gabanki amma ke baki isa
kiyi ba, domin yasha fad'a shi mata bai d'aukesu bakin komai ba, face Abun
hutawa, sannan tunda yana da kud'i zai iya harka dako wace mace, ba tare da
damuwa ba, sai yasa har yau ya kasa aure tunda yana samun abunda namijin auren
ke samu a cewar shi....
Hugging
d'inshi Monica tayi wanda yasa dole ya dawo daka duniyar tunanin daya afka.
D'an tureta
yayi tare da fad'in just go away.
Tsayawa tayi
sororo Tana kallonshi, cikin harshen turanci Wanda bata iya fad'in sunanshi
Sosai ba, tace najub what happen?
Kallonta
yayi shima cikin harshen turancin yake mata magana, yace nace ki tafi
Sanin
halinshi sarai yasa ta juya, domin tasan ko tafi kud'a naci tunda yace mata ta
tafi dagaske yakeyi, komai zatayi bazai saurareta ba, tayi nisa Sosai ta tsaya
tana tunani, lokaci d'aya ta kalli dressing d'inta, kaita dafe alaman ta
kwafsa.
Shiko rufe kofarshi
yayi domin bacci yakeji Sosai, dama yaso tayi massaging d'inshi ne, but ta bata
mishi rai, dole ya kwanta bai dad'e ba bacci yayi gaba dashi.
Waye wannan
guy din?
Ku biyoni
nan gaba kad'an za kuji ko Waye.
NIGERIA
Tafiya take tana
sauri daka ganin alama tana cikin farin ciki Sosai, domin kallo d'aya zaka mata
ka gane irin farin cikin da take ciki, wani Gida ta shiga, cikin sauri, a
tsakar Gida ta iske umminta da kakarta wacce take kira da granny, tace ummi
ummi ko sallama batayi ba, tace ummi kalla naci jamb d'ina, na samu 198 wayyo
dad'i naci jamb.
Granny tace
Dallah Rufamin baki, kin shigo ko sallama babu, kina wani fad'in kinci Janus ne
ko me kike fad'a oho.
Dariya
ibtisam ta saki tare da fad'in ba Janus bane jamb nace.
Granny ta
tabe baki tare da fad'in koma dai miye, ni bason wannan karatun nake ba, shima
Umar d'in, na rasa mai yasa yake biye miki, in banda iya shege ace yarinya
takai shekara Goma sha bakwai ace tana gida har yanzu ba'a maganan aure sai
wani karatu, ta k'arasa maganan tare da tsuke baki.
ita dai ummi
bata ce musu komai ba, dan inda sabo ta saba, sannan yanzu inta tofa wani abu,
Indai granny ce da ibtisam ba'a shiga tsakaninsu.
Ibtisam tace
gaskiya granny ki daina min irin haka, yanzu na samu dakyar abba ya yarda amma
kina son rusa mun komai, shi auran ba lokaci bane, rungumo granny d'in tayi
sannan taci gaba da fad'in, Kinga ina gama karatu sai aure, nan da shekara
hud'u.
Granny tace
shekara hud'u? Kuka ta saki tana fad'in Wlh bazan yihu ba, har sai kin k'ara
shekara hud'u a gida, yanzu kina 17, sai kin Kai 21 sannan zaki aure, sai kin
gama tsofewa a gida, bari Umar d'in yazo, shike d'aure miki gindi
Ibtisam tace
wayyo Allah na shiga uku, gaskiya granny kina son samun hawan jini.
Granny Tana
d'an share kwallanta Tana fad'in, Aini kin samun, yanzu ace aure sai nan da
shekara hud'u, inna mutu banga auranki bafa? Shima gashi wannan shegen miskilin
ya'ki aure, shikenan jikokin nawa bazan ga y'ay'an suba, amma Nasan maganin ku
daka ke har shi Wlh.
Ibtisam
tashi tayi domin jin an kira miskili tasan wa granny ke nufi, domin a duniya
babu wanda ta tsana sai shi, dan ita ta tsani mutum Mai girman kai.
Ummi dai
bata tanka musu ba, wani abun ma in sukayi dariya suke bata, granny na matukar
son ibtisam domin sunanta aka saka mata, Amina, kuma wannan fad'an da granny
take tayi koda tayi ma mahaifin ibtisam magana ya hanata, tana ganin ibtisam ta
Fara kuka da fushi zata ce a barta, domin bata san ganin jikar tata kuma
takwarar tata cikin damuwa ko kad'an.
Ibtisam
abinci ta Fara ci tana fad'in, yanzu Idan na zama wata babba a gwamnati inna
Gama karatu, ai sai kinfi kowa jin dad'i.
Granny tsuke
baki tayi tana fad'in Kedai kika Sani, aure dai shine darajan mace.
Ummi tace ni
maza ki gama cin abinci kije min kasuwa.
Granny ta
kalli ummi tace yanzu da tsohon ranan nan zaki aikata kasuwa? Ki bari rana ta
fad'i.
Ummi tace ai
gwara taje ta dawo da wuri, kar muyi daren girki.
Granny tace
koma dai miye sai rana ta fad'i, yanzu inta Fita cikin rana ta kwaso ciwon kai
ai baki da Asara..
Jin haka
yasa ummi ta tsuke bakinta tare dayin shuru, domin tasan halin granny sarai
Indai akan ibtisam ne
Bayan
ibtisam ta kammala cin abinci, ta tashi ta nufi Ummi tare da fad'in mai zan
siyo?
Kafin ummi
tayi magana, caraf granny ta amshe da fad'in, oh Ina cewa ki bari rana ya fad'i
kina fad'in mai zaki siyo koh? Wlh Idan kika dawo kina kanki na ciwo ko kallonki
banyi.
Ibtisam tace
dama zance miki kaina na ciwo ne? Kona
fad'a Aiba ciremin za kiyi ba.
Granny tace
toh shikenan ke kika sani tare da tashi tana fad'in bari in rakaki in wasa
kafa.
Da sauri
ibtisam tace babu inda zaki bini, wajan da zani cikin minti talatin in dawo, in
Naje dake Ai sai nayi awa uku, gwara Kima zauna .
Granny tace
ah, lallai naga dai k'afa tace, bata wata ba, kuma Wlh saina biki, kallon ummi
tayi da take ta faman musu dariya, tace maza ki fad'a mata abunda zata siyo
muje mu dawo.
Nan ummi ta
fad'ama ibtisam abubuwan da take bukata.
Babu yanda
ibtisam batayi ba, amma granny tace Wlh tare zasu, haka suka fita, ibtisam tana
mitar inta fad'in mata a kasuwa bazata iya d'aukanta ba.
Granny tace
ke kika sani, in Kinga dama inna fad'i ki wuce ki barni a nan, a haka kike son
zuwa karatu, a gaban mu, Ina fad'a kina fad'a, ni Wlh kunya nake ji, sai inga
kaman ana nunani ace muna da katuwar budurwa y'ar shekara Goma sha bakwai a
matsayinmu na Fulani ace ba muyi mata aure ba.
Ibtisam
dariya ta saki tare da fad'in, ai sai kiyi tajin kunyar, ai bance ki fito tare
dani ba.
Granny tace
ah lallai, ni Kinga yi gaba inyi baya, dan gaskiya ji nake kaman ana nunani
Ibtisam tace
Aiko tare zamu jera Wlh,wa yace ki biyoni?
Ai ban saki ba.
Granny tamke
fuska tayi, ita a dole ranta ya baci, Hhhhh kunji tsohuwa da karfin hali.
Tafiya suke
har suka k'arasa kasuwa, ibtisam tayi siyayya, granny ta amshi wasu kayan, suka
juyo, har sunyi nisa da kasuwa Granny ta tsaya.
Ibtisam tace
miye kuma?
Granny tace
goro na ya k'are, na manta ban siya ba, gaskiya sai mun koma na siya
Ibtisam tace
Kai Kai na shiga uku, yanzu mun kusa zuwa Gida, shine zaki Mai damu kasuwa,
gaskiya hakuri za kiyi da wannan goron yau, ni bama uncle yace ki daina ciba,
yana da illah .
Granny tace
Dallah rabu dashi, inda yana da illah da tuni ya fito min, muje ni ki rakani in
siya goro, su y'an boko sai iyayi da shegen k'arya, Abu kad'an suce anyi
bincike babu kyau, tsaki taja ta juya ta Fara tafiya.
Ibtisam babu
yanda ta iya dole ta bita.
Sunje ta
siya goron, ibtisam tace gaskiya muhau machine, na gaji.
Granny tsaki
taja tare da fad'in in zaki biyoni ki biyoni, yara sai son jiki
Granny na
gaba ibtisam na baya, wani mai mota ne tun daka nesa ya hango ibtisam tana
tafiya, yanda take tafiyan zai nuna maka cewa lallai ta gaji da tafiyan, harya
wuce ya dawo baya, tare da fita daka motar, ya nufi ibtisam
Sallama yayi
mata, amsawa tayi dan ita a tunaninta zai tambaye tane.
Sai taji
sabanin haka, Tana k'okarin yin gaba, sai ganin Granny tayi a wajan, tana
fad'in sannu yaro, ya akayi?
Har katsa ya
tsugunna ya gaida Granny, domin kobai tambaya ba yasan kakarta ce
Granny
amsawa tayi cikin sakin fuska tare da fad'in tashi yaro, ya sunanka?
Yace kabir
Itbtisam kam
ranta ya baci, Sosai domin ganin yanda ta biye mishi
Yace mama
muje in kaiku Gida.
Granny tace
toh d'ana muje, amma grandi suke cemin ita da miskili.
Dariya kabir
yayi tare da fad'in kodai Granny?..
Da sauri
tace eh grandi hakane
Kabir dariya
yayi Sosai
Kallon
ibtisam tayi da bata da niyan tafiya, tace muje.
Ibtisam babu
yanda ta iya tunda Granny ta bishi haka itama dole taje, bud'e ma Granny gidan
gaba yayi ta shiga cikin motarshi Mai k'iran COROLLA, ita kam Itbtisam baya ta
shiga, sai fira Kabir da granny suke kaman Sun saba, gaba d'aya ma kaman sun
manta da ibtisam a motar, wacce ta gama kulewa da granny.
Granny taita
nuna mishi hanya har suka isa kofar gidan, inda ya faka, Granny tace fito jika
na, ai baka tsaya nan ba,.
Kabir yace
Granny Zanzo gobe yanzu ana jirana.
Kallon
ibtisam tayi tace amsan min number d'inshi
Ibtisam ji
tayi kaman tayi ihu saboda takaici, wato a amsan Mata number dinshi, shiko Fara
gaya ma ibtisam yayi dole ta Fara rubutawa, Bayan ta gama yace ta kira yaga
number din, kaman tace zata kirashi da wayan granny d'in inta shiga gida, amma
ganin irin kallon da Granny tayi mata tasan zata iya tsinkata yasa ta kira.
kabir yace
ngd saina kira, ko amsa bata bashi ba ta shige cikin gida, cikin takaici
Granny tace
toh saina ganka, yace toh Granny tare da bata dubu goma yace asai goro.
Dakyar
Granny ta amsa, saboda yace shima jikanta ne.
Tafiya Kabir
yayi yana tuki yana nishad'i, lallai ya samu matar aure, ya samu irin choice
din macen da yake so, domin yana son mace Mai nutsuwa da kamun kai, yau kad'ai
daya taba ganin ibtisam yaga nutsuwarta da kamun kanta....... Uhm muje zuwa
No comments