BARIKI NA FITO (BOOK 2) 27
Bariki ihu
ta saki cikin tashin hankali, nan mum ta fita da gudu kiran Dr, yayin da
Falmata take ta zunduma ashar kan cewa Bariki zata kashe mata miji, Bariki kam
kuka take tana manne jikin Yarima, Falmata k'okarin cafko Bariki take, Yarima
kaman ya Lura da hakan yasa ya dawo da Bariki baya tare da shiga gaba.
Dr shigowa
yayi inda ya bu'kaci su mum damai martaba da Falmata su fita danya samu ya duba
patient din, nan Dr Ya fara duba sheik musa monguno, cikin ikon Allah ya
Farfado nan ya fara kuka tare da zufa dake faman keto mishi, tashi yayi tare da
nufa wajan da Bariki take inda ya fara kuka yana neman gafaranta akan abunda
yayi mata, wanda yace Wlh bai San ya akai har shida kanshi ya koreta ba,
Dr fita yayi
domin yaga ba wani serious ciwo bane, suma yayi and kuma ya Farfad'o, ganin Dr
Ya fita yasa su mum shigowa.
Falmata
ganin mijinta ya tashi yasa ta Fara rusa kuka lokaci d'aya kuma ta Fara dariya
tare da fad'in Nina sa akama Zainab ciki saboda ka tsaneta Wlh nice nasa aka
mata hahahaha hahahaha sai kuma ta saki kuka lokaci d'aya kuma taci gaba da
fad'in
Nice nasa
mata kwaya cikin juice tasha, tayi bacci Mai nauyi, Nasa driver ya mata ciki,
hahahaha bayan nasashi na koreshi, daka karshe ya faramin barazana nasa aka
kasheshi har lahira, wlh nice nasa aka mata ciki, saboda ta'ki yarda dani, ni
kuma ina sonta Sosai ina son in lashi zumarta, Wlh Ina Sonta Sosai dan Allah ku
bani ita, ko ku aura min ita, sai kuma ta k'ara fashewa da dariya taci gaba da
fad'in abunda yasa nasa aka mata ciki saboda ina son Dad d'inta ya tsaneta,
yace ta d'auko mishi abun kunya, kuma Nayi wannan tunanin ne saboda Kar wata
rana ta tauna min asiri dan yana jin magananta, kuma in ya tabbatar tana da
ciki zai daina yarda da ita, bayan nasa anyi mata ciki, nasa akaje min
maiduguri wajan wani boka inda na amso mugun sihiri Wanda na rufe mishi ido da
baki sai abunda nace, duk da lokacin sihirin baiyi wani tasiri Sosai ba, dan
Bayan ya koreta yaita fama da ciwo tare da damuwa yana mamakin Wai shine ya
Kori y'arshi da kanshi, ganin irin damuwan da yakeyi gashi ana kawo mishi
hotanta da shigar banza, hakan yasa hankalinshi ya tashi Sosai, ganin irin
halin daya shiga yasa na tafi maiduguri dakai na wajan boka, gashi ina takaicin
ban haiyu dashi ba, yau Idan ya mutu ba wani kud'i zan samu Sosai ba, inda Nayi
mishi bayani, tare da cewa Ina son a cire mishi tunanin Zainab harta danginshi
kona mamanta karsu nemeta, boka yace wannan aikin akwai hatsari Sosai sannan
akwai zunubi Sosai, domin raba y'a da iyayenta babban aiki ne, nan nace ma boka
na d'auka, boka yace dad din Zainab yana matukar son y'arshi Sosai koda anyi
aikin muddin ya ganta komai zai lalace, Indai kina son aikin yayi tasiri karki
bari su had'u, nace ma boka babu damuwa
Yace an
gama, za'a tura mishi Aljani, wanda zai dinga juyashi, nan na amince boka ya
k'ara min kashedi Idan na Bari suka had'u komai ya faru dani Kar ince bai
fad'amin ba? Nace na amince domin a lokacin idona ya rufe.
Bayan na
dawo Abuja naga aiki yayi, domin a lokacin tunanin Zainab yasa dad d'inta ya
rage ibada, domin yana cikin ciwo, wannan ne yasa nayi nasara akanshi, har
Aljani ya shige shi, saboda ina fargaban karsu had'u nasa muka koma misra gaba
d'aya inda na bu'kaci Nima Ina son inyi karatu a can, wannan ne dalilin
komawarmu k'asar misra yana business dinshi ta Nigeria da kasashen da yake yi,
amma maganan zuwa Nigeria gaba d'aya nasa an cire mishi a rai, kwasam sai gashi
yace min zaizo Nigeria amininshi yana nemanshi zai gabatar mishi da wani lacca,
a lokacin na tsorata domin kuwa harta wa'azin da yake zuwa nasa an hanashi, sai
gashi ya kawo min maganan zuwa Nigeria yayi lacca, da Farko naso in hanashi sai
kuma Nayi tunanin muzo dan Ina son zuwa maiduguri wajan boka inji ya akayi ko
aiki ya fara sanyi ne, ashe asiri ne zai tonu.. Dariya ta saki Tana fad'in Wlh
koda zan mutu saina ciki Zainab Ina sonki.
Kowa dake wajan
salati yake cikin takaici tare da jimami, da Allah wadai da halin Falmata
Dad d'in
Bariki nan take yace Falmata na sakeki saki uku, kuma insha Allah sai Kinga
abunda kika aikata, kin cuceni kin batamin rayuwar y'ata, lallai Falmata sai
nasa an hukunta ki W.....
Mai martaba
yace kayi hakuri, baka ga halinda take ciki ba, Mai martaba ya lura da Falmata
kaman ta haukace.
Falmata tace
saime cikin ihu, ni dama ba Sonka nake ba, saboda kud'i na aureka, da naga
y'arka sai naji Ina Sonta, tunda naga irin suranta kuma Wlh sai na cita,hahahha
Kaga koda ka mutu nida ita zamu zauna muci kud'inka, sannan ta dinga biya min
bukata, Hahahahahaha sai kuma ta saki kuka tare da fara k'okarin cire hijab
d'inta, nan mum ta k'ara fita ta kira Dr.
Koda Dr yazo
dakyar aka ri'keta tana ta fusge fusge, andai samu an d'aureta dakyar inda
sheik musa monguno yace zai sa a maidata maiduguri domin wlh ko sisi bazai bada
ba wajan yi mata magani ba.
An ro'ki Dr
akan su Fara dubata inda Mai martaba ya bada umarni tare da fad'in ba'a saka
sharri da sharri, Dr yace gskiya wannan asibitin mahaukata za'a kaita, mai
martaba yace babu damuwa a kaita, zai biya ko nawa ne, nan akai Gaba da
Falmata. Kai rayuwa kenan wannan shi ake cema sakayya, lallai Allah ba
azzalumin kowa bane, sai wanda ya cuci kanshi, duk irin abunda Falmata tayi
gashi ya koma kanta, kai Mata mata Wlh muji tsoran Allah.
Sheik musa
monguno kuka yake tare da ri'ke hannun Zainab yana tambayanta akan ta yafe
mishi
Cikin kuka
tace babu abunda yayi mata, tace Dad niya kamata in nemi gafaranka, dana biye
ma shairin zuciya, tare da kokarin San in kuntata maka, ta wajan aikata aikin
sabon Allah, Dad na cuci kaina da yawa, dan Allah ka yafe min dad ta k'arasa
maganan cikin kuka
Janyo y'ar
tashi yayi tare da rungumeta su duka suna kuka abun tausayi.
Yarima Aliyu
jin kukan hafsat din yake har cikin ranshi.
Hafsat da
tun ihun da Falmata ke zabgawa yasa ta tashi ta zauna, nan itama ta fad'o daka
kan gadon d'akin ta zube a gaban iyayenta tana kuka akan su taimaka mata su
yafe mata.
Mai martaba
yace duka su tashi suyi gida, acan za'ayi magana, hafsat jikinta yayi sanyi
ganin mahaifin nata ko kallonta baiyi ba, lallai ta aikata babban kuskure na
yarda da Umar wajan bashi jikinta, kuka take Sosai, inda gaba d'aya suka fita
Bayan an tambayi Dr ko akwai wani damuwa, Dr yasa anba ma Hafsat magani sannan
yace Bariki tana bukatar hutu Sosai, inda so samu ne ma a bata bed rest, da
Farko Yarima Aliyu yace ta koma a bata gado, amma tace a'a a gida zata fi samun
hutu, babu yanda ya iya dole ya biye mata itama aka bata maganin suka nufi
Gida, duka a babban falon Mai martaba suka zauna inda Mai martaba ya kira
waziri akan yazo, domin yana son yin magana yau wanda tun tuni yake son yi.
Kowa ya hallara,
inda Mum tace ina zinatu ya kamata tazo itama, mai martaba yace Aliyu yaje ya
kirata.
Yarima Aliyu
fita yayi amma bai soba, domin duk zuwa asibiti da yayi bata tako k'afa tazo
ba, and yanzu kuma maganan daya shafi Zainab za'ayi sai yake ganin kaman bai
kamata tazo wajan ba, tunda kishiyar Zainab dince ita.
Direct
gefenta ya shiga tun Kafin ya k'arasa d'akinta yake jiyo maganansu ita da
gimbiya Amina, wanda yama manta tazo, gimbiya zinatu tana fad'in ai Wlh inda
badan wannan maganin dana sama Yarima yayi mishi karfi ba, toh da Wlh zai gane
niba virgin bace, ki duba fah ki gani baya cikin hayyacinshi har Ya iya gane
niba virgin bace, dariya gimbiya Amina ta saki tare da fad'in hmmm ai tunda
yaga wannan jinin na tabbata dole ya yarda ke budurwa ce.
Gimbiya
zinatu tace yauwa wai jinin miye kika Aiko min dashi?
Gimbiya
Amina tace Wlh fadawa naba kud'i suka kawo min, nace musu kona dabba ne kona
mutum suje asibiti su siya, bayan sun dawo suka cemin Sun yanka raguna uku,
shine suka kawo min jinin
Dariya
gimbiya zinatu ta saki tare da fad'in ashe jinin rago ne, Yarima ya d'auka jini
nane, kai gskya anyi bidiri, dariya suka saki.
Gimbiya
Amina tace shidai duka baiyi dace ba, ita wancan amaryan tashi ba budurwa ba,
Kema gaki, yatsa da ayabar roba yasa kin rasa budurci.
Gimbiya
zinatu tace uhm Kedai bari, ni bada sanin namiji ba budurci ya gudu, hmm inda
Yarima bai saki matarshi ba Aida tasha gori wajena Wlh da habaici
Gimbiya
Amina tace toh Kema dai Kibi sannu a hankali, domin wlh idan Yarima ya gane kin
mishi wannan yaudaran kashinki ya bushe, shi yanzu yana miki kallon budurwa ne
Yarima Aliyu
dake tsaye yana jinsu cikin tashin hankali, gaba d'aya jikinshi yayi sanyi, ji
yayi kaman ya juya amma wata zuciyar tace ka shiga ka nuna musu kaji komai, dan
haka ya kutsa Kai kalman Innalillahi'wa inna ilaihirajiun ya iya furtawa, ganin
gimbiya zinatu da gimbiya Amina zindir haiyuwar uwarsu jikinsu manne dana juna.
Yarima Aliyu
tunda ya furta wannan Kalman na Innalillahi wa inna'ilaihira jiun bai k'ara
cewa komai ba, sai hawayen dake idonshi dake zuba, tare da fad'in wannan wace
irin jarabawa ce cikin ranshi, juyawa yayi ya fita jim kad'an sai gashi da mum
d'inshi itama Abun ya bata mamaki, gimbiya zinatu da gimbiya Amina, Sun kasa
koda motsi ne
Yarima Aliyu
kuka yake yana fad'ama mum dinshi abunda yaji, suna fad'a tare da fad'in mum
ban kasance mazinaci ba, amma Allah ya bani Mata fasikai,mum.. Kuka ya hanashi
k'arasa abunda yayi niyan fad'a.
Mum
rarrashinshi take tare da fad'in yayi hakuri ya d'auka wannan shine
jarabawanshi na rayuwa, uhm su mum kenan yanzu an gane kaddara da jarabawa uhm.
Yarima yace
mum bazan zauna da macen dana Kama tana aikata mad'igo ba, na tabbata duk macen
dake aikata lesbians kallon hoto take ma mijinta, tana mishi kallon sakarai,
mum bazan iya zama da itaba, lallai laifinta yafi na kowa muni, mum kice ta
tafi bana son ganinta,
Zinatu da
sauri ta taso tana kuka tare da ri'ke kafan Yarima tana bashi hakuri akan bata
dad'e da fara aikata wannan aikin ba, dan Allah Yarima ka yafe min Wlh yi kawai
nakeyi, amma bawai Ina jin dad'inshi ba, kuka take Sosai tana bashi hakuri
Mum tace
tashi kisa kaya ki samemu falon Mai martaba, tare da kallon gimbiya Amina tace
ke kuma ki shirya ki koma Gida, abunda kuka aikata dakai na zan fad'ama
iyayenku, tana fad'in haka taja Yarima suka fita, tana fad'a mishi karya sake
yace zai rabu da matarshi, tare da fad'in a farko tayi kuskuren raba shi da
wacce yake mutuwar so, bazan k'ara Bari ka saki matarka ba, itama Zainab Ina
neman hanyar da zaku dawo tare ne.
Koda suka je
cikin falon idon Yarima Mai martaba ya kalla, yace maiya faru? Mum shuru tayi
haka shima, yarima, muryan Gimbiya zinatu suka ji Tana fad'in dan Allah Abba
kuyi min rai Nasan na aikata mummunan laifi, wlh shairin shaidan ne, dan Allah
Abba kaba Yarima hakuri karya rabu dani Ina sonshi, wlh ban taba aikata mad'igo
ba sai shekaran jiya, duka salati suka saki kowa kallonta yake cikin jimami da
Tashin hankali .
Jin kowa na
salati yasa gimbiya zinatu kallon mutanan dake d'akin, wanda idonta ya rufe
bata ko Lura dasu ba, sai yanzu cikin jin kunya tare da tsanar kanta da kuma
gimbiya Amina da tasa ta Fara aikata wannan abun.
Mai martaba
ne yayi gyaran murya tare da fad'in Innalillahi'wa inna ilaihirajiun, kai
duniya kai duniya Mai take son zama ne, da farko dai zan fara da Zainab yanzu
Zainab zaki bi dad d'inki ne ko zaki zauna a nan har sai kin haiyu?
Bariki cikin
sanyin jiki tare da zubar da hawaye tasan ta rasa Yarima har abada tace Abba
zanbi Dad Dina
Da sauri
Yarima yace ban amince ba, wanda bai San maganan ta fito ba
Kowa
kallonshi yayi,
Mum kam kuka
take k'asa k'asa domin tasan d'anta bazai jure rashin Zainab ba, kai ta cuci
d'anta, ta rabashi da farin cikin shi
Mai martaba
yace Aliyu karka manta yanzu Zainab ba matarka bace.
Yace Abba
Zainab har gobe tana matsayin matata
Mum da sauri
ta d'ago tana kallonshi, bama mum ba duk wa inda ke falon, yace Abba sanda mum
tace in saketa na rubuta mata saki biyu Naji bazan iyayi mata uku ba, bayan na
bata takardan naga mum bata damu data duba takardan ba hakan yayi min dad'i
amma ganin yanda mum ta korata yasa naji a jikina kaman mum bazata taba Bari in
dawo da ita ba, lokacin dana Fara ciwo nan take na dawo da ita, Zainab yanzu
tana matsayin matata, takardan dana bata yana hannunta
Mum wani
irin ajiyan zuciya ta sauke tare da furta Alhmdlh, Allah na godema.
Bariki tace
Yarima Wlh sanda kaban takardan ban duba ba, harna yaga shi saboda ba Abun
kallo bane, ashe saki biyu ne sai kuma ta saki kuka.
Mum ta tashi
taje kusa da ita tana fad'in kiyi shuru zainab, wlh nafi kowa murna, inda Yarima
saki uku yayi miki, dana shiga uku, kai Allah na gode ma, naso in aikata
kuskure a rayuwa, naso bata rayuwar d'ana da kaina, sai yasa akace ba'a yanke
hukunci cikin fushi, yau gashi naga yanda naso jefa yarana halaka sai kuma
itama ta saki kuka, Bariki ganin haka sai ta dena Nata kukan ta Fara rarrashin
mum.
Mai martaba
yace yanke hukunci cikin fushi babu abunda yake haifar wa, sai dana sani, A
kullum ana son Kafin ka yanke hukunci ka Fara bincike inka tabbatar, saika
zauna kayi tunani akan maiya kamata, inko kace zaka yanke hukunci cikin fushi
lallai zakai dana sani, Allan yasa kun fahimta.
Mai martaba
ya kalli sheik musa monguno, ya fara bashi irin rayuwar da y'arshi ta shiga,
bayan ya koreta har zuwa auran Yarima da tayi.
Sheik musa
monguno kuka ya fara tare da fad'in Falmata ta cuceni, ta batamin rayuwa data
y'ata, kallon Zainab yayi tare da fad'in ki yafe min inda ban aureta da hakan
bai faru ba.
Mai martaba
yace ka daina fad'in haka, sheik ko ka manta Idan Allah yasa abu zai zo gareka
dole sai yazo, sannan sheik asiri yana bin hali ne, na tabbata koda Falmata
bata maka asiri ba, zaka iya Koran Zainab, domin lokacin kana cikin fushi, zaka
yanke hukunci cikin fushi, domin zaka ga a matsayinka na babban Malami y'arka
ta kwaso cikin shege na tabbata koda babu asiri zaka iya koranta, daka baya
kayi dana sani, sai yasa akace ba'a yanke hukunci cikin fushi, a lokacin duk da
akwai sihiri a kanka Bayan ta tafi aika
nuna kayi nadama, tare dason ganinta.
Sheik musa
monguno yace hakane, tabbas asiri yana bin hali, asiri yana tafiya ne da halin
mutum, Allah ka k'ara tsare mana imanin mu, kallon Yarima yayi tare da fad'in
lallai Aliyu ban San da wani baki zan gode maka ba, domin kayi babban jahadi na
ceto rayuwar Zainab, duk da kasan irin rayuwar da tayi daka baya, bayan tayi
maka k'arya kaci gaba da zama da ita, lallai ban tunanin duk irin sonda nake
mata cewa nawa yafi maka, lallai ka fini son Zainab, tunda harka iya zama da
ita, sa'banin nida nake mahaifinta sanda take bukatar kulawata Sosai lokacin na
juya mata baya, duk saboda fushi tare da kunyar duniya, kai kaico na, Yarima
Allah yayi maka albarka.
Yarima ya
amsa da Ameen tare da kallon zainab wacce itama shi take kallo, Yarima ido ya
kashe mata, da sauri tayi k'asa dakai tana murmushi tare da tsoran Allah yasa
wani baiga sanda ya kashe mata idon ba.
Mai martaba
kallon waziri yayi tare da fad'in, Ina son aje a sauke sarkin u/k daka kan
kujeranshi, domin bai kamata a barshi yana shugabantan al'umma ba, a sami wani
kamili Dattijon arziki a saka, amma yau nake son a bashi takardan murabus,
domin duk mutumin da zaiyi Abu saboda kud'i ciki harda yaudara ba mutumin
arziki bane, bai kamata ya dinga shugabantan al'umma ba, nan take waziri yace
an gama ranka ya dad'e
Mai martaba
kallon hafsat yayi tare da kiran sunanta da sauri ta d'ago cikin faduwan gaba
tace na'am Abba, tana hawaye
Yace hafsat
Mai kika rasa? Mai kika nema kika rasa? Hafsat wani irin tarbiya ne bamu baki
ba? Dama kin San kina da ciki shine kike k'okarin yin aure da cikin wani?
Hafsat kin bani mamaki matuka.
Cikin kuka
tace Abba ka yafemin Wlh cikin Umar ne
Mai martaba
shuru yayi cikin jimami da takaici, Amma babu yanda ya iya, wannan abunda ya
sameshi kaddara ce.
Yace hafsat
gashi Umar ya rasu, yanzu kina tunanin zaki sami wanda zai aureki, Bayan kin
bata rayuwarki?
Sheik musa
monguno yace mai martaba, yanzu ka gama bayani akan hakuri da dangana, da kuma
d'aukan kaddara, kayi hakuri, ka cinye wannan kaddaran taka kaima.
Mai martaba
yace hakane, Allah yasa mu dace, zan nemi iyayen umar din muyi magana dasu
Kallon
gimbiya zinatu yayi sannan yace zinatu kinyi matukar bani mamaki, kin San
bala'in dake cikin aikata mad'igo kuwa?
Bariki kiji daka aikata mad'igo gara kayi zina duk da shima babban
bala'i har gwara mai aikata zina akan mad'igo Bari kiji illar dake cikin zina
kawai Kafin muzo wajan mad'igo
Mai zina
mace da namiji akace ayi musu bulala d'ari, kuma kada aji tausayinsu akan bin
hukuncin Allah, Indai kayi imani da Allah da Ranar lahira, sannan ana son
jama'a mumunai su halarci azabar da za'ayi musu, wannan in saurayi da budurwa
ne wanda basu da aure.
Masu aure
kuma mace kona miji jifa ne.
Manzon Allah
(S A W) Yace:
Mai zina ba
zaiyi zina ba, yayin da yake zina sai an cire mishi imani... Wa'iyazubillah yanzu Idan kana aikatawa Allah ya d'auki
rayuwar mutum kunga ya mutu a kafiri Innalillahi'wa inna ilaihirajiun, yarima
yasa mu dace .
Yace zina ta
had'a dukkan sharri gaba d'aya, zina bala'i ce babba, tana haifar da bala'i Mai
girma, Tana sa rashin tsoran Allah, tare da haifar da cututtuka da mutuwar
zuciya, Tana sa zuciyar mutum tayi ba'ki da tsatsa ,tana sa mutum kullum ya
jishi cikin damuwa da rashin kwanciyan hankali, sannan tana haifar da talauci, da
zubewar mutunci, mazinaci dukiyarshi bata albarka, saboda kullum yana neman
mata yana basu, Suma matan basa iya tara dukiyar saboda suna ganin wani zai
basu, a haka za suyi ta zama har su daina samu, kowa ya'ki taimakon su.
Manzon Allah
( S A W) Yace mutum bakwai Allah ya
tsine musu, kuma bazai kallesu da rahma ba ranan Al'Qiyama zaice musu ku shiga
wuta Innalillahi'wa inna ilaihirajiun..
Mai yin zina
da dabbobi
Mai yin
luwadi da mad'igo
Wanda akeyi
dashi
Mai yin zina
da uwa
Sannan kuma
yayi da y'arta
Mai yin wasa
da al'aurarta
Ko maiyin
wasa da gabansa
Masturbation
kenan
Zinatu cikin
kuka ta Fara fad'in Wlh shekaran jiya na fara wannan mummunan abun, da
masturbation nakeyi Ashe shima babban laifi ne, wayyo Allah na tuba
Mai martaba
yace
Yana d'aya
daka cikin laifukan da mutanan Annabi LUD suka aikata, sannan an ruwaita duk
maiyin haka Indai harya mutu bai tuba ba zai tashi ranan alkiyama hannayenshi
d'auke da ciki
Yarima Aliyu
yace Abba sannan duk maniyin da aka fitar dashi da gangan baya fita gaba d'aya
wanda ya rage saiya daskare ma mutum cikin mara, sannan yana sa rashin haiyuwa wannan
daskareren maniyin yana kashe kwayoyin hallita daga jikin namiji ko mace,
sannan likitoci sun k'ara fadada bincike akan hakan yana haifar da mugayen cutuka
kamar haka
Saurin yin
realising mutum nan da nan yaji ya Kawo, Yana saka raunin ido, mutum Idan
yanayi zai iya rasa idonshi har abada, yana sa mutum yawan mantuwa, raunin
al'aura, wannan y'ana d'aya daka cikin abunda masu wasa da yatsa ko masu aikata
mad'igo yake haifar wa, bance duka ba sai yasa yanzu mata yawanci suke fama da
rashin haiyuwa, wata ita lokaci ne baiyi ba, wata kuma tana aikata mad'igo
Wanda maniyin daya fita sauran ya daskare mata a jiki, Abba tunda na Fara aiki
a asibiti Ina had'uwa da abubuwan al'ajabi da dama sai dai muce Allah ya shirya
ya ganar damu hanyar gaskiya.
Mai martaba
yace zinatu ana son bawa koda yace ya tuba, yayi tuba na tsakani da Allah yanda
bazai K'ara aikata wannan mummunan aikin ba
Allah
gafurul rahim ne, Allah mai yafiya ne ga bayinsa, Allah yana son bayinsa masu
tuba.
Zinatu ta
kalli Yarima tace dan Allah Yarima kamin rai karka ce zaka rabu dani, wlh Ina
Sonka, dan Allah ka yafemin Wlh na tuba, Yarima Ina Sonka dan Allah kayi
hakuri.
Yarima Aliyu
shuru yayi yana nazari, can yace zinatu Allah ya sani bazan iya zama ina
kallonki da wannan abun ba, domin duk macen da zatai sha'awar mace y'ar uwarta,
Toh kallon hoto take ma mijinta
Da sauri mum
tace Aliyu kayi hakuri ka d'auki komai yazo maka a matsayin kaddara, lallai
Kaga jarabawa, Allah yasa daka wannan sai jin dad'i,.
Yarima Aliyu
wani hawaye ne mai zafi ya fito mishi tare da fad'in ya zanyi mum? Babu yanda
zanyi tawa kaddaran kenan sai hakuri, Allah ya bani ikon cinyewa, zan zauna da
Mata na zan basu dama na biyu, Indai zan yafe ma d'aya dole In yafe ma d'aya,
amma daka ranan da suka k'ara aikata wani aiki irin wanda sukayi, bazan iya
d'auka ba, amma d.....
Shuru yayi
yana kallon Bariki yace mum dole In k'ara aure,
Da sauri
Bariki ta taso ta nufeshi tare da fad'in Wlh ban yarda ba, tama manta suwaye a
falon saida taji dariyan su sannan taji kunya tare da barin falon da sauri,
ganin harda gudu takeyi yasa Yarima yabi bayanta da sauri Karta illata mishi
unborn child dinshi, dan yaga kaman ta manta tana da ciki, kuma ance tana
bukatan bed rest, shine take wannan gudun.
Bata tsaya
ba sai cikin gefenta, a bedroom ya sameta ta kwanta akan gado tana sauke nishi,
d'agota yayi tare da fara fad'a kin manta bake d'aya bace Zainab har kike
wannan gudun.
Kuka ta
sakar mishi da karfi tare da ihu Tana fad'in na shiga uku.....
MARYAM OBAM
No comments