BARIKI NA FITO (BOOK 2) 26
PAGE 26
Yarima Aliyu
sai nishi yake sama sama, mai martaba ya cire mishi rigan jikinshi ya rage daka
shi sai singlet, sai zufa yake ta keto ma Aliyu, duk da kuwa akwai AC a d'akin,
mum shigowa tayi cikin tashi hankali ganin halin da Aliyu ke ciki,
Kuka ta Fara
tana fad'in Aliyu sannu, tare da kallon mijin Nata tace mu maidashi asibiti.
Mai martaba
yace ai kinfi kowa sanin maganinshi, dan haka ki barshi kawai, babu abunda
asibiti zasu iya mishi.
Mum fita
tayi Jim kad'an sai gata da limam, tana fad'in dan Allah kayi mishi addu'a,
nasan wannan Asirin Nata BA'KIN AJANI Ta tura mai, dan Allah mlm dubashi Karta
kashe min yaro, tana maganan tana kuka
Mai martaba
yace Khadija ina tunanin Kece kike bukatar ruki'a bashi ba, kallon limam Mai
martaba yayi tare da fad'in limam kaje abunka.
Limam fita
yayi
Mum tace na
shiga uku, haba Kai baka ga halinda yake ciki ba, yanzu Inba asiri ba taya
danya saki matarshi zai shiga irin wannan halin, wannan wani irin sone haka?
Wannan aikin sihiri ne ba komai ba, ban tunanin koni na mutu Yarima zai shiga
wannan halin, amma akan y'ar iskan karuwar yarinyar can duk ya d'aga hankalinsa
W....
Mai martaba
ya daka mata tsawa tare da fad'in Yimin shuru, Khadija zan saba miki, naga
alaman kina son wuce gona da iri, ki barshi yaji da abunda yake ji, kinsa ya
rabu da matarshi ki barshi haka karki k'arasa shi, komai ya sami Aliyu Kece
sila.
Mai martaba
kallon Aliyu yayi da yake faman jin jiki tare da fad'in Aliyu Ina son kayi
hakuri ka d'auki komai ya faru da bawa kaddara ne, sannan zansa a nemo maka
matarka duk da kun rabu zata zauna a nan har
sai ta haiyu.
Mum dai fita
tayi tana kuka ita an gama da d'anta da mijinta
Koda labari
ya iske gimbiya zinatu da gimbiya Amina, zo kuga murna, inda sukai ta fad'in
Ashe y'ar iska ce amaryan daya aura, nan suka tashi suna cashewa, inda daka nan
magana ta canza ana cikin rawa gimbiya Amina ta kamo kugun gimbiya zinatu tare
da fad'in yau zaki cika min Burina tare da alkawarin da kikamin in Kinyi aure
zamu fara soyayy.....
Gimbiya
zinatu tace dole In cika miki wannan burin naki my love domin Ina cikin
nishad'i, sannan bani da wata fargaba K..... Kafin ta k'arasa magana gimbiya
Amina takai bakinta cikin na gimbiya zinatu ta Fara kissing dinta.....
Washe gari
da safe Bariki ta tashi,kuma Alhmdlh ciwon cikinta ya warke bata jin komai,
direct bank ta nufa inda ta tsaya tana jira 8 tayi, lokaci nayi ta shiga ta
amsa check book ta rubuta adadin kud'in da take bukata, sannan ta bu'kaci a
bata ATM, nan dai ta gama komai cikin awa d'aya, tun tana bank din take jin
kaman hanjin cikinta zai fita, dan haka tana barin bank din taga inda ake siyar
da waina Aiko nan taji ranta ya biya, zuwa tayi ta siya gashi ba'a cikin shago
bane, akan benci kowa yake ci, babu yanda ta iya haka ta zauna tana ci, ita dai
burinta taji wainar cikin bakinta, tana ci tana mamaki Wai itace take cin
abinci a irin wajannan ga maza, gashi akan titi, Yarima ya fad'o mata a rai
tare da tunanin ko wani hali yake ciki yanzu oho, wani hawaye taji ya zubo mata
Mai zafi Sosai, lokaci d'aya taji wainar ya fitan Mata a rai, gashi tana jin
tashin zuciya, da sauri ta tashi taje gefe ta Fara kwarara amai kaman zata
fitar da hanjin cikinta, wani irin jiri taji tana ji, Wanda yasa dole ta zauna
a wajan tare da lumshe ido, tana sauke numfashi dakyar, duk wannan abunda take
ledan kud'in data ciro yana hannunta,
mutanan dake wajan wasu sun tausaya mata, yayin da wasu suke fad'in hala
tayi cikin shege ne aka korota har suke fad'in tir da ita, Bariki dai ita
burinta jiran ya saketa ta tashi ta shiga cikin kaduna.
Tana nan
zaune kaman daga sama taji ana mata magana, da sauri ta bud'e ido, wanda ya sauka a kanshi sukai ido biyu,
gabanta taji ya fad'i, ba kowa bane sai Mai kid'a , duk da tana jin jiri saida
ta tashi tare dayin baya.
Yace Bariki
Kece a yashe a nan haka? Murmushi yayi
tare da fad'in daka gani kina neman taimako, yanzu abunda za'ayi kizo muje
inada d'aki a nan saiki huta.
Bariki ido
ta bishi dashi Wanda jikinshi ga kurajen HIV nan duk sun feso mishi a jiki duk Wanda yasan Kalan kurajen yana kallo zai
gane yana da cutar, mai karya garkuwan jikin d'an Adam.
Yace
taimakon ki zanyi, kin tsaya kin kafeni da ido, naji ance kinyi aure? Ko dama
k'arya ne? Muje in baki masauki ki huta, ko ince Mu huta.
Bariki kai
ta girgiza tare dayin gaba dan bata tunanin zata iya furta wani kalma a yanda
take jin jikinta.
Binta yayi
yana fad'in nan ba maraban jos bane, gwara ki bini in taimaka miki, in bani
bama Waye zai kalleki, kalli yanda duk kayanki suka baci, m.... Motar data tsaya a gaban Bariki ne yasa Mai
kid'a yin shuru
Wata mota ce
'kiran Prado ta tsaya gaban Bariki, da sauri aka bud'e motar hafsat ce ta fito
daga cikin motar tare da ri'ke Bariki tana fad'in Zainab Ina zaki haka? Usman
shima faka tashi motar yayi Bayan ta hafsat, tare da fitowa, tun sanda bariki
take cin waina ya ganta shine ya kira hafsat dama jiya da suke waya da hafsat
take fad'a mishi halinda Yarima yake ciki, da Kuma neman da Mai martaba yasa
ayi mata.
Hafsat tace
Zainab maza kizo muje Gida, Yarima yana bu'katarki.
Bariki tace
a'ah hafsat tare dayin gaba lokaci d'aya jiri ya kwasheta ta Fara k'okarin yin
k'asa hafsat ta kamata tare da sata a mota, suka wuce.
Usman kallon
mai kid'a yayi tare da fad'in mai kake binta kayi Mata?? Mai kake nema wajanta? Bud'e Mai ido usman
yayi
Mai kid'a ya
fara bashi hakuri tare da fad'in taimako nake nema wajanta yana fad'in haka ya
ruga da gudu, dan ya tsorata da usman yana tsoran Kar yasa a kamashi.
Bariki dake
kwance cikin mota bata san inda kanta yake ba, hafsat kiran Mai martaba tayi
tare da shaida mishi Anga Zainab a halin yanzu ga sunan suna tafe, amma kaman
ta suma.
Mai martaba
yace ma Hafsat ta kaita asibiti, shima yanzu zaizo shida Aliyu, domin ga shinan
kwance bai San inda kanshi yake ba.
Hafsat tace
toh Abba.
Asibiti
takai Bariki inda akai emergency da ita domin bata ko motsi, nan aka fara bata
taimakon gaggawa.
Basu dad'e
da zuwa ba saiga Mai martaba da Yarima an kawo an sashi akan Keken d'aukan
marasa lafiya, nan shima aka shigar dashi emergency, likitoci dai suna nan
tsaye kan masoya biyu, suna iya bakin k'okarin su.
Yarima ne ya
fara sauke numfashi sama sama, alaman yana jin jiki Sosai, sannan sanda aka
kawo shi ko numfashin baya iyayi da kyau, irin haka inda an k'ara bata lokaci a
gida, sai mutum ya rasa ranshi gaba d'aya, Yarima yana kwance yana nishi sama
sama, d'aya daka cikin Dr din ya fara
mishi magana tunda yana d'aya daka cikin wanda suka duba Yarima lokacin da abun
Farko ya faru, a kunne tare da fad'in Yarima wake up ga matarka kusa dakai,
kallon abokanan aikinshi yayi tare da fad'in su matso da gadon da bariki take
kusa.
Nan aka
matso da gadon sauran Dr din suna son suga Mai d'ayan Dr din zaiyi, idan kuka
duba in za'a ma mutum operation tiyata, za kuga likitoci fiye da d'aya ne suke
aikin, domin ko wanne zai bada nashi gudun mawan, wani yana da experience fiye
da wani, so wannan shine dalilin da yasa suke kallon d'ayan Dr din suga Mai
zaiyi.
Kamo hannun
Yarima yayi dana Bariki ya had'a waje d'aya, tare da k'ara yima Yarima Aliyu
magana a kunne ka tashi matarka na bukatar taimakon ka, Plz wake up.
Yarima tun
sanda aka sa mishi hannun Zainab a nashi, zuciyarshi ta Fara harbawa da sauri,
suda kansu sauran Dr din sunyi mamaki, lallai soyayya ba k'arya bane and basu
taba ganin irin wannan son ba, ashe hakan na faruwa, ikon Allah.
Yarima Aliyu
a hankali ya fara bud'e ido, wanda suka sauka akan selling d'in d'akin, lokaci
d'aya ya waiga ganin Zainab kwance kusa dashi ya fara k'okarin tashi, da sauri
Dr ya rik'eshi tare da fad'in plz Aliyu ka kwanta matarka Tana kusa dakai babu
inda zata.
Yarima Aliyu
hannun Dr yake k'okarin cirewa daka jikinshi amma ya kasa saboda jiki babu
'kwari.
A hankali
yace plz leave me, I want to see my wife.
D'aya daka
cikin Dr din yace ka d'agashi ya ganta.
D'ago Yarima
Aliyu yayi tare da matso dashi gadon da Zainab take, k'ara matse hannunta yayi
yana hawaye tare da fad'in my princess I will never ever let you go from me
again, I can't live without you, my princess why r you go far away from
me?..... Lokaci d'aya kuma yayi shuru komai ya tuna kuma oho, yayi wajan minti
biyu yana kallon Zainab, lokaci d'aya kuma ya rungumeta duk da tana kwance, sun
dad'e a haka Kafin Bariki ta farka tare da bud'e idonta itama kukan ta Fara,
tare da matse mijinta a jikinta tana fadin Yarima zan mutu , mai yasa mum
bazata duba irin sonda nake maka ba, Yarima plz kaba mum hakuri ta hakura ta barmu
tare, bazan iya rayuwa ba tare dakai ba, plz Yarima kazo mu gudu muyi rayuwa a
wani waje wanda babu wanda zai gammu....
Muryan mum
sukaji Tana fad'in Sai dai ke ki gudu ba d'ana ba, y'ar iska, har abada d'ana
bazai taba barin iyayenshi ba, kaman yanda ke kika bar naki, y'ar iska karuwa
hafsat dake Bayan mum tana takaicin abunda mum din ke fad'a tare da tausaya ma
d'an uwan nata da matarshi, k'okarin fita tayi domin kiran Mai martaba dake
waya a waje Aiko jiri ya d'ibeta lokaci d'aya tayi k'asa, nan mum ta waiga jin
kaman mutum ya fad'i, ganin hafsat ce yasa ta saki ihu tare da fad'in na shiga
uku, da gudu ta fita ta kira Dr inda aka fara duba hafsat din itama.
Nan mum ta
fita ta kira Mai martaba take fad'a mishi hafsat ta fad'i Tana ciki ana dubata,
hankalin Mai martaba ya tashi Sosai, yara uku ba lafiya, Yarima da matarshi ga
hafsat, mai martaba ko zama ya kasayi saboda tashin hankalin da yake ciki, tare
da fargaban maike damun hafsat itama
Sunyi wajan
30mnt suna jira Dr ya fito wanda tun a ciki Dr ya fad'ama Yarima Aliyu abunda
ke damun hafsat, ya shiga mugun damuwa wanda ko magana ya kasayi, Bariki ce
tayi karfin halin ro'kan Dr akan karya gayama mum da Abba a waje saboda Akwai
fadawa, ya shigo dasu nan ne Kafin ya Sanar musu, hakan ko akayi aka kira mum
da Mai martaba, inda Mum ta Fara fad'in Dr dan Allah fad'amin abunda ke
damunta?
Hafsat na
kwance tana bacci abunta, ansa Mata drive.
Dr yace hjy
tana d'auke da ciki na wata uku, abunda yasa ta fad'i saboda jikinta yayi weak,
is lyk Tana cikin damuwa so..... AI tuni
mum tayi k'asa sumamma, shiko Mai martaba kasa magana yayi sai Innalillahi'wa
inna ilaihirajiun da yake ta faman furtawa cikin ranshi, ganin mum tayi k'asa
yasa ya d'agota da sauri inda Dr ya d'auko ruwa aka yayyafa Mata ta Farko .
Kuka tasa
tare da fad'in Hafsat kin cuceni, kin gama dani, yanzu irin tarbiyan dana baki
kenan? Kin d'auko mana Abun kunyar da ban taba jiba ko a zamanin baya ba, ace
y'ar gidan sarauta tayi cikin shege, kuka Mum take Sosai cikin 'kunan rai, tare
da ba'kin cikin abunda y'arta ta d'auko, shiko Mai martaba kukan zuci yake
lallai basai kayi abuba Allah yake jarabtanka, koda baka kasance mazinaci ba, Allah
yakan jarabceka da samun mata mazinaciya ko kuma cikin y'ay'anka, lallai babu
yanda Allah bayayi akan wannan al'amarin, Allah yakan jarabci bayinshi tako
Ina, yaga ya za suyi.
Zainab dai
itama tana zaune tana hawaye, lallai abunda ciwo, ganin yanda mum take kuka
saita tuna da dad d'inta, irin halin daya shiga sanda yace tana da ciki, Wanda
ita bata san Wanda yayi mata ba, sai yanzu Bariki take k'ara ganin laifin kanta
wanda komai dad d'inta zai Mata bai kamata ta fad'a Bariki ba, danta kuntata ma
mahaifinta ba, gashi yanzu abunda tayi shi take girba,tayi aure amma saboda
rayuwar da tayi baya ya bata mata rayuwar auranta, kuka ta saki mai sauti wanda
hankalin kowa yayi kanta.
Mum kallon
Bariki take irin yanda take kuka, jikin mum yayi sanyi, lallai abunda mijinta
yake fad'a mata gaskiya ne, kaddara tana kan kowa, gashi yanzu ya fad'a kan
y'arta, Innalillahi'wa inna ilaihirajiun. Hmmmm Allah sarki rayuwa kenan, kowa
baya yarda da kaddara saiya fad'a kanshi, sannan zai san kaddara ne, Abu Indai
ba'a kanka ya fad'a ba to wajan kowa ba kaddara bane wasu sai su dinga fad'in
dagangan mutum yayi ko kuma ace shiya sa kanshi, Hmmm mutane suna bani mamaki,
wlh baki shi yake Kai mutum ga halaka, sai kuji mutum yana fad'in Wlh ni ai duk
wacce take karuwanci ita taso maganganu dai irin haka, toh Wlh y'an uwa ku iya
bakinku, Domin kuwa Allah zai iya jarabtanku ku fad'a cikin harkan karuwancin
sai yaga yanda za kuyi, sai yasa a kullum ake son mutum ya dinga fad'in Alheri,
kaman dai irin abunda mum ta dinga fad'i akan Bariki ita bata haifi karuwa ba,
sai gashi y'arta da cikin shege, lallai dubaranka ko wayanka bashi bane zai sa
Allah ya'ki jarabtanka, Allah yana jarabtan bayinshi ta hanyoyi da dama domin
ya gwada imaninsu, wasu ta dukiya, wasu ta ciwo, wasu na talauci babu yanda
Allah bayayi, sai dai muyi fatan Allah yasa mu cinye ko wace jarabawa da zata
zo mana a rayuwa.
Mum tashi
tayi tare da nufa inda Yarima da Bariki suke ta Fara bashi hakuri tare da
fad'in lallai ni uwa ce, wacce ban kasance mai fahimtar abunda d'ana yake soba,
ni uwa ce Mai son kanta, tunda na nuna nafi son y'ay'ana akan na wasu, na kasa
amsar kaddaran data fad'a ma matarka, Ina gudun kaci gaba da zama da ita, yau
gashi nima Allah ya jarabceni y'ata d'auke da ciki ba tare da aure ba, ciki
harna wata uku, lallai Allah ya nunamin ishara, kamo hannun Bariki tayi tana
fad'in dan Allah ki yafemin Wlh Ina jin kunyar kaina irin munanan kalaman dana
dinga fad'a miki, gashi nasa d'ana ya miki saki har uku, banyi la'akari da cewa
Kece rayuwarshi, ba idona ya rufe Ina ganin kaman kin mallake min d'ana kuka
yaci karfinta Sosai.
Bariki cikin
kuka tace mum kiyi hakuri, nayi imani da kaddara, lallai na yarda sakin da
Yarima yayi min yana cikin kaddara na, ban taba ganin laifinki ba, abunda kika
aikata ko wace uwa abunda za tayi kenan,
babu wata Uwar da zata so d'anta ya zauna da macen da tayi rayuwar
Bariki, lallai nima na cuci kaina kuka ta saki mai sauti wanda duk wannan
abunda suke idon hafsat biyu tana ji itama hawaye take, lallai tayi kuskuren
mallaka ma Umar jikinta gashi yanzu baya Raye.
Mai martaba
daya kasa magana sai yanzu ya iya bud'e baki, yace Zainab daka ina kika fito,
Ina son ki fad'amin koke wacece dan a nemi iyayenki mu samman yanzu da kike da
juna biyu ya kamata musan iyayenki
Bariki taba cikinta tayi tana mamaki dama ciki
gareta? Wani hawaye mai zafi ya fito mata nan ta Fara bama Mai martaba Labarin
irin abunda ya faru da ita harda irin rayuwar da tayi a bariki, ta k'arasa
maganan cikin kuka mai ban tausayi .
Kowa ya
tausaya mata,ciki harda hafsat dake kwance tana jinsu, jikin mum ya k'ara sanyi
Sosai, tare dayin nadaman abunda ta aikata ma Bariki, lallai tayi kuskure
babba, ashe itama babban kaddara ne ya fad'a mata, had'e da Sharrin matar uba,
lallai wasu matan bazasu ga annabi ba, tayi sanadin lalacewan yarinya danta k'i
yarda da kudirinta na aikata mad'igo, Mum jikinta yayi sanyi Sosai, gashi ta
raba d'anta da ita, koya rayuwarshi zata kaya?
Mai martaba
yace dama ke yarinyar Sheikh musa monguno ce?
Ikon Allah, d'azu dashi muke waya kan cewa yazo Nigeria nace mishi muna
asibiti, nasa aje a d'aukoshi daka airport Wanda na tabba sun kusa zuwa nan
bada dad'ewa ba, Abokina ne tare mukai karatu a k'asar misra, lallai abun yaban
mamaki, Yarima yasa in gayyato shi akan yana son ya gabatar da lacca, Amma
Zainab kinyi kuskure babba, iyaye ai iyaye ne, komai suka miki bai kamata ki
k'ara bata rayuwarki ba danki kuntata ma mahaifinki, haba zainab ina iliminki?
Kin aikata babban kuskure a rayuwa.
Kallon
Yarima Mai martaba yayi tare da fad'in ko kasan shine mahaifinta dama??
Yarima yace
eh Abba, ranan da aka d'aura mana aure na gane tamin k'arya, inda daka baya ta
fadamin gaskiya, shine na bukaci ka gayyatoshi dan nasan inka kirashi zai zo,
kayi hakuri Abba Nayi maka k'arya akan ina son yazo yayi lacca, Nayi hakan ne
danka kirashi yazo in dai daitashi da y'arshi, ni bamma san abokinka bane, dani
dakai na zani wajansa har misra din.
Mai martaba
yace lallai Aliyu kayi jahadi, Allah yayi maka albarka, karan wayar Mai martaba
ne yasa ya d'auka tare da fita waje, Jim kad'an sai gashi ya shigo da sheik
musa monguno da matarsa Falmata wacce tasha hijab har k'asa kamar wata
mutuniyar kwarai, idon sheik musa monguno ya sauka akan na gudan y'ar tasa Aiko
yana ganinta ya fara nunata da hannu lokaci d'aya kuma ya fad'i k'asa.......
Hmmm muje zuwa muji maike faruwa?
No comments