TARAYYA 31-32
31
Not edited.
Kallon adama
dake qoqarin saukowa gado yayi yaga yanda jikinta ke rawa saidai Sam bata tata
yakeyiba mafarkinsa ya girgiza tunaninsa da zuciyarsa matuqa sbd su mutane ne
dasuka
yarda da mafarki,
Basason
'yaya mata sbd muguwar aqidar dasuke ciki ta wani irin mulki da ake gudanarwa
na tsantsar iko kowa yasan mulkin mace a mineelik masifa ce dabaza'aso
maimaitawaba sbd jinin matansu bazai iya controlling na abinda yake tareda
throne dinba kamar namiji shiyasa mulkinsu yake zama tamkar masifa ko annoba
sbd mulkine na tsantsar zubarda jini Wanda babu yaro ba babba bare mata bare
maza,ba tsoho ba tsohuwa.
Alqawarine
yadauka bazai taba bari mace ta mulki mineelik ba koda zai rasa ransane sbd
yasan duk macen dazata hau zaiyi wuya basuyi ajalin junaba dayaga haka ya roqi
Allah yayi gaggawar daukar ransa.
Cikeda rudu
adama takallesa tana goge fuskarta dahar lokacin take gumi tace,
Sultan nayi
mugun mafarkinda gwara nayi mutuwar qasqanci a hannun 6arayi dana fuskanci irin
abinda Nagani a mafarkin.
Bai
kalletaba bare yatsaya sauraran abinda take fada sbd tunanin daya cika
zuciyarsa akaro na farko arayuwarsa dayaji mulki yafara fita ransa sbd duba da
irin mutuwar da sarakunan mineelik keyi yayi tunanin zai iya tsallakewa ya
sauka mulkin salin alin batareda fuskantar irin qarshen sauran sarakunan ba
shiyasa ya tattara duk dagewarsa akan ganin maheer ya karbi mulkin amma yaqi
gashi matarsama ta haifi namiji arabasa da wannan masifar abu yaqi yiyuwa ta
wani 6angare ga daular shiefffs na jiran rashin magajinsu su zamo bayi a
qarqashinsu Wanda yafison ya sare kansa daga gangar jikinsa dayaga wannan baqar
ranar yanzu kuma ga wata masifar nason 6ullowa sbd baisan me mafarkinsa na
assultana yake nufi ba.
Hannunsa ya
daga ahankali ya shafo fuskarsa cikin mamaki saiyaga zufa ne ke tsatsafo masa,
Rabon da
yayi zufa a rayuwarsa harya manta.
Irin
tarbarda akayiwa isowarsu ta qara sanyaya jikin rumanah sbd tafara fargabar
itama me zata Haifa sbd ganin irin dubban jama'ar dasuka dogara da abinda zata
haifa.
Lokacinda
mamani tayi ido biyu da rumanah da cikin dake jikinta wani mugun jiri mai qarfi
ya 'dibeta nuratu tayi saurin tareta tana kallon idanuwanta dake cikowa da
qwallar baqin ciki tace,
Mamani
lafiya?
Kasa riqe
hawayenta tayi sbd baqin cikin daya rufe zuciyarta tace,
Har abada
bazanyi lafiyar zuciya ba sbd bulama da asma'u har bayan barinsu duniya basu
bar kurwata ta zauna lafiya ba bayan duk balain dasuka sako rayuwata aciki dan
haka wlh bazan zauna nashaqi numfashi mai dadiba sai ranar dana gama lalata
dukkanin zuriar da suka bari aduniya....
Sakinta
nuratu tayi cikeda mamaki da baqin cikin halin mahaifiyar tata muryarta na rawa
tace,
Mamani
dazaki cire abinda yake ranki gameda rumanah dakin cire sbd zai kaikine matakin
halaka sbd yanxu tariga ta taka wani matsayinda duk Wanda yayi mata wani
ganganci zai iya rasa rayuwarsa sbd dukkanin burin daular nan da zagayenta
akanta da cikinta yake dan haka ki nesanta kanki da ita sbd gujewa rasa
rayuwarki..ke mahaifiyatace ina sonki fiyeda komai amma bazan iya kallo ki cuci
rumanah ba dan haka karkiyi abinda zai barni da rashin zabi face na fadi
gaskiyar dazaki rasa rayuwarki.
Tana gama
fadar haka tabar gurin cikeda damuwa
Duk murnarta
da farin cikin ganin rumanah din ya 6aci sbd mamani.
Kukan 6aqin
ciki mamani tasake tana tsinewa bulama da asma'u ta juya ta nufi gurin adama da
sai alokacin zata fito tarbon.
Kallo daya
tayiwa cikin rumanah taji tari mai qarfi ya sarqeta kamar ranta zai fita
take ta
gigice da gudu akaje aka kawo mata ruwa ta karba tasha idanuwanta dasuka firfito
sukai jajir sbd tari numfashinta na fita da sauri ta juya tabar gurin nanma
idonta ya sauka kan na suhailat dake tsaye gefen Maheer ai take taji qaramar
hauka na neman kama zuciyarta tana isa palonta na farko dukkanin bayi da
kuyangin part din suka fice sbd gudun laifi lurada halinda take ciki.
Mamani data
sake biyota da ruwa ta miqa mata har lokacin itama jitake kamar ta cinnawa
mineelik wuta kowa ya babbake ya mutu ko zataji abinda ya tsaya mata a maqoshi
ya fada.
Karbar ruwan
tayi tasake sha tana cewa,
Burina dana
gina tun ina budurwa bazai taba rushewaba kan baiwa 'yar bayi,
Babu Wanda
bazan iya raba gangar jikinsa da kansaba kan burina sbd burina shine burin
karagar mineelik..
Cikin
tsananin damuwa da baqin cikin mamani daya kasa dannuwa aranta tace,
Duk inda
bulama da asma'u suka sauka saisun bar masifar data addabi kowa awajen
Shiyasa
bazan numfasaba saina tabbarda na tarwatsa rayuwar rumanah da abinda ke
cikinta.
Kallonta
adama tayi da jajayen idanuwanta baqin cikinta na ninkuwa tace,
Ko bulama ne
aduniya bai isa ya shiga tsakanina da hawa throne din mineelik ba bare 'yarsa
dan haka ni adama ayau ina sake daukarwa kaina alqawarin kawarda ko wanene ya
shiga hanyata ta cimma burina
Idan nace ko
wanene ina nufin ko wanene ciki bancire kowaba.
Cikin
takaici mamani tace,
Allah yasa
gurin haihuwa ta mutu daga ita har abinda zata haifa kowama ya huta.
Kobata mutu
gurin haihuwa ba ta haifi namiji saiya mutu kozan rasa
rayuwatane"""adama ta fada tana miqewa tsaye.
Tsayawa tayi
tareda juyowa takalli mamani itama mamani ita takalla sai alokacin kowannensu
yadawo nutsuwarsa jiki na rawa mamani ta zube tana sunkuyar dakai
Adama
fuskewa tayi sbd duk duniya daga ita sai bokanta ne suka San da sirrinta sai
yanzu da 6acin rai yasata fadar abinda ke ranta saidai kuma ga alama tasamu
wadda zata riqa amfani da ita Dan cimma burinta musamman da kusancinsu da
rumanar zasuyi amfani tunda tana yiwa mamani kallon uwa.
Wani irin
babban sabon sashe da aka zubawa tsaro na musamman aka kaita Wanda yake gefen
part din yarima maheer duk wani abin jin dadi da hutawa anxuba mata shi ga
kuyangi na musamman da aka kawo mata.
Bayan duk
wata aladar tarbonsu anyi angama da daddare bayan tayi wanka ta saka kayan
bacci ta kwanta bakin gado tareda lumshe idanuwanta ta bude ahankali tareda
kiran sunansa cikin zuciyarta.
Suhailat
kuwa sbd yanayin jikinta da gajiya yasa tana kwantawa bacci ya dauketa cikin
tsananin gajiya.
Abincin da
aka aikawa kowaccensu daga part din sultana zaarah babu wadda tasamu damar ci
har gwara suhailat tasha madara mai zafi sbd sanyi datakeji kamar zai kamata.
Rumanah kuwa
kwance take tayi lamo cikin zurfi a tunani da tsananin son ganinsa sbd har
lokacin takasa daina tuno yanayin dasuka rabu 'dazun hakan na raunana zuciyarta
da kuzarinta ahaka bacci yadan 'dauketa tanayi tana farkowa hardai akai asuba
tayi sallah takoma ta kwanta nanne tasamu baccin yadauketa sosai.
Qarfe goma
ta fito palonta anan ta tararda dining shaqe da kalolin abinci ta kalli qofa
kamar tana jiran isowar wani hardai tagaji ta nufi dining tana fidda wani irin
qamshi mai dadi.
Fara cin
abincinta kenan taji muryar data sakata dakatawa ta juyo da sauri suka hada ido
da nuratu dake cikin tsananin farin cikin ganin rumanah din.
Miqewa
rumanah tayi zata nufeta Jakadiya data kawo mata nuratu din tayi gyaran murya
dole ta tsaya tana kallon nuratu cikeda farin ciki
Nuratu
'dince taqaraso gaban rumanah tana kallon cikinta tana sake bayyanarda farin
cikinta zata zube qasa rumanah ta riqota tareda Rungumeta duk da tsinin cikinta
baibari sun rungume juna sosaiba.
Cikin
tsananin murna rumanah tace,
Tun jiya
yakamata ace ke nafara gani da mamani amma shine kikaqi zuwa sai yanzu danace
anemoki ina mamani?
Baki washe
tace,
Mamani qila
wani aiki ya hanata zuwa nima sbd tun jiyan nake yawo a hanyar sashen nan sbd
kawai naganki amma bansamu damaba yanxu ana cewa kekenemanmu na aje aikina nazo
bakisan yanda na matsu nagankiba rumanah nayi kewarki sosai kinbarni cikin
kadaicinki...
Hawaye suka
sakata kasa cigaba da maganarta
Rumanah ma
hawayen ne suka ciko mata idanuwa ta riqe hannunta tace,
Nayi kewarki
nima nuratu saidai bayanda zanyine sbd kinsan da zabi ake bawa mutum nafison
zama taredaku duk da ayanxu komai ya canxa arayuwata saidai matsayinku nanan
keda mamani bazan ta6a canzakuba arayuwata.
Murmushin
qarfin hali nuratu tayi tace,
Mamani
bazata taba daukarki ayanda kika dauketaba.
Ni zan
cigaba da daukarta matsayin yayar mahaifiyata har qarshen rayuwata bazan taba
duba abinda takeminba tunda na saba.
Karkice haka
rumanah sbd yanxu akwai banbanci bazanzo na rasataba sbd yi miki wani abu yanxu
daidai yakeda rasa rayuwarta.
Karki damu
da wannan yanxu zo muci abinci tare nayi kewar hakan sbd bansaniba kozan sake
samun irin wannan damar tacin abinci tare dake.
Zama sukayi
a babban dining din mai kujeru goma sha biyu nuratu na 'dar 'dar rumanah
najanta da magana sbd tasaki jikinta ahaka sukaci abinci nuratu taci abinda
takeso ta qoshi suka nufi palonta na qurya nan suka fara fira
Nuratu
takalli cikin rumanah dayayi mata kyau matuqa musamman sbd bai sakata qiba ba
tsawo yayi sosai.
Murmushi
tayi cikin kulawa tace,
Nayi farin
cikin ganin rayuwarki ta canxa rumanah gashi zaki haifar mana 'yaya jinin
sarauta.
Kallonta
rumanah tayi tasaki murmushi kawai sbd tunaninta ba akan firar tasu yakeba.
Agurinta
nuratu ta wuni sai tsakar dare ta tafi koshi da sharadin gobe Jakadiya zata
saka acanza mata aiki adawo da ita gurinta.
Mamani kuwa
sunyi jiran zuwanta harsun gaji bata zoba gashi dokace akan rumanah bazata fita
koinaba idanba da qwaqwaran daliliba harsaita haihu.
Washe gari
aka dawo da nuratu aiki gurinta duk yanda taso hanata aiki tabarwa sauran
kuyangin qi tayi saidatayi.
Kowace
safiya da maraice sai Ammy ta Aiko mata da madara mai zafi itada suhailat
harsukai kwana uku inda tun tana dannewa harsaida damuwarta ta daqushe
kuzarinta matuqa dan ita kadai tasan halinda zuciyarta take ciki na rashin
ganinsa gashi da alama bazata sake ganinsa ba saita haihu qila hakan ke sata
kwantawa tayi kukanta sbd ji take nutsuwarta na neman gagararta abincima tun
nuratu na iya yinta dan ganin taci har abin yafi qarfinta ta sanarda Jakadiya
rashin cin isashen abincinda rumanar keyi.
Lokacinda
Jakadiya taje ta sanarda ammy hakan yarima na tareda ita bai 'dagoba amma ammy
kallo 'daya tayi masa tagano halinda yake ciki musamman dama tana lureda
shikansa miskilanci da mulkine yahana agano halinda yake ciki na rashinta.
Jakadiya
tayiwa wani irin kallo nan take tagano me take nufi ta gyada kai ta wuce
zuciyarta fal tsoro da mamakin irin sonda yarima kewa rumanah haka ta wuce taje
kitchen ta bada umarnin ayi dukkanin girkinda akasan yarima maheer naso a
shirya a palonsa na musamman zaici abincin daren tareda matansa.
Da daddare
koda Jakadiya tazo kiranta cin abinci cikin yanayi na rashin walwala tace
batajin dadin cikinta bazata iyacin abinciba yanzu sai zuwa anjima.
Ba musu
Jakadiya ta tafi
Koda yafito
cin abincin cikin wata irin shiga ta musamman ta kayan shan iska qamshinsa na fita
ahankali.
Suhailat
dake zaune da cikinta ya kalla cikeda kewarta da tausayinta ya ware mata hannu
ta taso ahankali tashige jikinsa ta rungumesa tareda sakin ajiyar zuciya.
Cikin kulawa
ya dagota tareda kallon fuskarta da cikinta ya shafi fuskarta ahankali yace,
Hey hw are
you?
Murmushin
mai ciwo tasaki na qarfin hali tace,
Lafiya klau
I missed you""ya fada tana zamewa daga jikinsa ta zauna kan dining
sbd ita kadai tasan me ta hango a cikin idanuwansa.
Zama yayi
yana sake kallonta ganin jikinta yayi sanyi lokaci 'daya duk saiyaji lissafinsa
na sake kwancewa abincin gabaki daya yafita ransa.
Itama
abincin fita ranta yayi saidai hakanan ta tsakuri kadan taci ta miqe tazo tayi
kissing forehead dinsa tace,
Gud
night""ta fice tana mayarda hawayen idonta.
Harta fice
bai motsaba sbd damuwa da takaicin kansa dayaji akaro na farko.
Saqone
yazowa Jakadiya daga yarima maheer cikin gaggawa ta nufi sashen rumanah ta bada
umarnin duk wata baiwa dake sashen rabarshi cikin mintuna biyu kacal.
Babu 6ata
lokaci dukkaninsu suka watse bayan koina yadauki sabon qamshi sai masu tsaron
qofar shigowa ne kawai.
Kwance take
lamo bakin gado idanuwanta a rufe tayi nisa cikin tunani.
Ahankali
taji qamshinsa yana shiga hancinta ta bude ido tareda lumshewa zuciyarta na
sake shiga damuwa sbd tasan har abada bazaizo sashentaba sbd atarihin sarautar
mineelik ba'a taba yin sarki ko yariman dayaje 'dakin matarsaba saidai ita taje
to mezaisa shi yazo gurinta.
Shafo
fuskarta yayi ahankali cikeda kulawa yana kallon kyakkyawar fuskarta tayi
saurin bude idanuwanta dasuka ciko da hawayen ganinsa saita samu kanta da
mayarda idanuwanta ta rufe.
Rintse ido
yayi cikeda mamakin kansa ya kamo hannunta ya riqe cikin nasa murya qasa qasa
yace,
Are you
angry?
Bude ido
tayi takallesa sbd bata taba tunanin zai kulaba harya tambaya.
Idonta dake
kansa yakalla yana sake matse hannunta cikin nasa yace,
Tashi zaune.
Ba musu ta
tashi zaune ya saki hannunta ya fito palo tabisa da kallo zuciyarta na qara mutuwa
a sonsa,
Jin
soyayyarsa takeyi har cikin jini da ruwan jikinta kowane bugawar zuciyarta da
sonsa take fita tana fata da roqon Allah yasa kar soyayyarsa tasakata kaucewa
hanya takoina koda kuwa sonsa da kishinsa zasu kasheta.
Jakadiya na
ganin fitowarsa tayi saurin qarasowa tace,
Allah
yataimaki uban magajin mineelik akwai abinda ake buqatane?
Hannayensa
ya zuba cikin aljihun wandonsa cikin wani irin miskilanci yace,
Ahado
abincin cin mutum biyu.
Cikin
qanqanin lokaci ta dibi abincin cin mutum biyo ta jero a tray takawo masa ga
mamakinta hannu yasa yakarba ya juya dakin yabarta da baki sake sbd tsananin
mamaki.
Duk yanda
yaso tasakar masa fuska qi tayi yasamu ya lalla6ata taci abincin ganin shi
baici ba yasata daukar abincin itama ta basa babu musu yaringa ci harsaidata
kwatanci ya qoshi ta ajiye tana kallonsa da mamaki yadauki tray din yamiqawa
Jakadiya dake palo ta fice da kayan.
Brush
yakaita har toilet tayo suka dawo ta zauna bakin gado ya zauna kusada ita
tareda kallon fuskarta dahar lokacin take kadaran kadahan duk saiya rasa me ke
masa dadi baimasan mezaice mataba sbd baisan menene yake faruwaba gabaki daya
ta qarasa dame masa lissafi ya dafe goshinsa tareda rintse ido ya bude ya miqe
zai tafi kawai yadawo yajawota jikinsa ya rungumeta batareda yace komaiba.
Rungumesa
itama tayi tareda barin hawayenta datake riqewa suka gangaro tana sake
qanqamesa.
Tun jekadiya
na jiran fitowarsa harta gane ba fitowar zaiyiba tabar palon takoma palon farko
ta dasa sabon jira.
Tunda tabaro
gurinsa mararta tafara ciwo ahankali tana shiga bedroom dinta takwanta tana
qoqarin danne ciwon datake ji amma alamarin yafara qarfafa kafin tayi wani
yunquri ciwon mara ya taso mata gaba 'daya gashi cikinta yanxune yashiga cikin
wata na bakwai.,
Cikin
qanqanin lokaci ta tabbarda naquda ce ta taso mata mai tsananin azaba sbd bata
taba jin irin wannan ba a duk haihuwarta tun tana boyewa tuni yaci qarfinta
koda Carolina taji kamar nishinta a dakin da sauri ta fita zuwa neman mutane
duk da dare ya tsala sosai har anyi kiran farko.
Asubar farin
yabaro part din yakoma nasa ita kuwa zazzabi ne mai qarfi ya rufeta bayan
wankan datayi da asubar amma bata nuna masaba saida ya fice takwanta tana rawar
sanyi mararta na mata ciwo ahankali.
Qarfe takwas
na safe ta shirya daqyar tana daddaurewa sbd ta masa alqawarin zuwa gurin ammy
yin breakfast su hadu acan.
Nuratu na
lureda kamar batajin dadi amma tayi shiru sbd ganin kamar batason yin ko magana
suka fito suka nufi sashen sultana ana biyeda ita bayi kuwa sai zubewa sukeyi
suna bata hanya cikin tsananin girmamawa.
Jakadiya
nacan tareda masu karbar haihuwa sashen suhailat hankulansu duk atashe sbd
haihuwar tazo mata da gardama matuqa
Shikansa
lokacinda labarin ya iso masa hankalinsa ya tashi dan haka ko gurin ammy bai
nufaba ya kira doctors din dake karbar haihuwar kasancewar yasansu duka matane
suke karbar haihuwa a masarautar in brief sukai masa bayanin haihuwa ce zatayi
ta wata bakwai kuma tazo da gardama sosai.
Kafin su isa
sashen ammy ta lurada akwai abinda yake faruwa a masarautar sbd koina yayi tsit
babu dogon motsi nuratu ce ta sanarda ita suhailat ce ke naquda.
Faduwa
gabanta yayi zuciyarta na cikeda mamaki da tausayin suhailar da ita kanta
batace komaiba sai sanyi da jikinta yayi tana mata fatan haihuwa lafiya.
Cikeda
kaduwa da rashin sukuni ammy ta kalli Jakadiya tace,
Ya Allah
karabasu lafiya saidai ina cikin damuwa da fargabar yaya haihuwar rumanah zata
zo itama Allah kadai yasan mezata haifa.
Numfashi mai
qarfi da sanyin jiki Jakadiya tasaki cikin rashin sanin abinyi itama tace,
Mafita
'dayace itace idan har anason sirrin mutuwar iyayen rumanah yazamo sirri daga
gareta muyi adduar kar asamu namiji daga gareta idanma ansamu namijin mutuwarsa
itace mafita.
Kallonta
sultana tayi da sauri tana sake shiga rudu tace,
Mutuwarsa na
nufin qarasa bankado komai Wanda kinsan hukuncinda zamu fuskaanta agun sultan
zaifi musan hanyarda zamubi musan wannan sirrin yacigaba da zama sirri kamar
yanda sultan yafada tun farko...
Saidai kuma
zuciyata na quna da fargabar yanda zan fuskanci rumanah ranarda tasan mune
sanadin mutwar iyayenta....
Da qarfi
ruwan haihuwa suka 6alle mata lokaci 'daya sbd masifa da tashin hankalinda
tashiga lokaci 'daya
Cikin tashin
hankali suka juyo cikeda mamaki da tashin hankalin abinda taji kafin suyo kanta
ta durqushe agurin cikin tsananin azabar ciwon mara nan take naquda mai qarfi
ta taso mata.
#mamuhgee.
[12:36 AM,
7/30/2019] +218 94-4138736: TARAYYA
wattpad @mamuhgee
Haske writers association💡
32
Not edited
A gagguce
Dafe cikinta
tayi cikeda tsananin azaba da wani irin juyi da cikin keyi mata.
Arikice
Nuratu ta riqota tana kiran sunanta cikin tsoro da tashin hankali
Su ammy
atare sukayo kanta cikin sobon tashin hankali da fargaba
Ammy ta
riqota tana kiran sunanta cikin damuwa take kiran sunanta.
A gaggauce
suka kamata sukai sashenta da ita inda tun kafin su isa ta qarasa rikicewa sbd
azabar naqudar.
Cikin
gaggawa Jakadiya ta isa gaban sultan dake zaune cikin royalhall suna jiran
haihuwar suhailat ta zube qasa kanta qasa ta sanarda shi ummu-rumanah ta shiga
naquda yanxunan.
Da wani irin
kallo ya dubeta zuciyarsa na shiga wani sabon farin cikin sbd yasan cikinsu
biyun dole asamu namiji insha Allah.
Wani
murmushi yasaki na qasaita cikin nuna isa yace,
Kije idan
akasamu namiji a mineelik yau namiki na miki alqawarin dukiyarda bazaki iya
qirgata da kankiba sai antayaki.
Cikin
fargaba tayi godia ta fice hankalinta tashe sbd daga ita har sultana a gigice
suke basa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali sbd fargabar haihuwar rumanah
dakuma babban sirrin dataji Wanda basusan ta yaya zasu fara fuskartartaba
saidai abinda suka sani kome zatayi wannan sirrin bazai fadu garetaba babban
tsoronsu da tashin hankalinsu kar Maheer yaji wannan alamari.
Kai tsaye
sashen yarima ta nufa lokacin yana zaune palonsa na farko zaune ya dora
qafafunsa kan table din dake gabansa ya rufe idanuwansa kallo daya zaka masa
kasan kadaici yake buqata baya buqatar hayaniya sbd yanayin naqudar suhailat
dayake cinsa musamman yanda yasan ta wahala haihuwarta ta qarshe gashi yanxu
har lokacin bata haihuba yana iya sensing azabar datake ciki.
Gabansa
Jakadiya ta tsaya tareda rusunawa cikin jimami tace,
Allah yataimaki
uban magajin mineelik uwardakina ummu-rumanah ta shiga naquda yanxunan..
Idanuwansa
dake rufe ya bude ahankali ya zuba mata suna sake canxawa sbd dama tuni suka
canxa sbd zaman jiran na kashesa.,
Miqewa tayi
ta fice jikinta a sanyaye sbd gabaki daya ta rasa nutsuwarta jitake kamar zata
zauce sbd fargabar tashin hankalinda zai biyo baya idan rumanah ta haihu ta
tambayi abinda taji ayau din.
Wayarsa daya
kashe ya dauka ya kunna tareda kiran Dr ammenen muryarsa na bayyanarda tsananin
damuwarsa da tashin hankalinsa yace mata tabar Dr noorah da nurse agurin
suhailat taje gurin rumanah takuma babbatarda tana basa bayanin komai harta
haihu idan kuma taga da damuwa takirasa kawai zaizo yakarbi haihuwar da kansa
duk abinda zai faru yafaru.
Aje wayar
yayi zuciyarsa kamar zata buga,
Yanxune yake
sake takaicin haihuwarsu anan sbd acan shine zai karbi haihuwar kowaccensu da
kansa musamman ita datake ta farkonta tana tsananin buqatarsa.
Dafe
goshinsa yayi ya miqe yayi ciki ganin kamar zai iya rasa hakurinsa yaje
musamman dayaga anfara jan lokaci babu wadda ta haihu.
Duk iya
galabaituwa kowaccensu ta galabaitu sbd kowacce gadan gadan naqudar ta taso
mata babu sauqi,
Duk Wanda ke
cikin mineelik hankalinta a tashe yake tsit koina ana jiran tsammani
Sultan ma
wannan karon saida hankalinsa yatashi shi fargabarsa kar doguwar naqudar tasa a
rasa 'yayan dake cikin.
Ammy duk
inda nutsuwa da kwanciyar hankali suke basa tareda ita ko zama takasayi addua
tajeyi tana qarawa musamman datake jiyo irin azabarda rumanar ke ciki sbd tana
palo suna ciki tareda masu karbar haihuwar.
Zufa mai
zafi Jakadiya ta sharce lokacinda Dr ammenen takalli nurse tace,
Get ready ga
babyn nan fitowa yanzu Ku kawo komai kusa.
Zufa
Jakadiya ta gogewa rumanah data fice hayyacinta cikin tsananin tausayi da
tashin hankali take mata sannu.
Cikin wata
irin rikitacciyar azaba tayi wani irin nishi mai qara Atake baby ya fado Dr
ammenen ta qarasa jawosa tareda yanke uwa ta 'dagasa sama ya buga wani irin
kukan jarirai babu qaqqautawa.
Kadan yarage
Jakadiya bata fadawa rumanah ba sbd rudewa da ganin abinda aka haifa.
Miqa mata
shi Dr tayi jikinta na matuqar tsuma ta karbesa aka nado cikin farin zanin
auduga mai tsananin laushi ta qura masa ido tana jera ajiyar zuciya ba
qaqqautawa.
Wata sabuwar
azaba ta tasowa rumanah cikin tashin hankali Dr takalli cikinta tana cewa nurse
wani babyn na zuwa.
Jiki na rawa
Jakadiya ta fito ammy data jiyo kukan jariri ta matso bakin qofar jikinta na
'dan rawa zuciyarta kamar zata fado sbd bugawar datakeyi a qofar sukayi karo da
jakadiya hannunta na rawa ta karbi jaririn tana qoqarin budewa taga menene
cikin rawar murya Jakadiya tace,
NAMIJI NE.
Da sauri
ammy ta dago ta kalleta tareda hadiye yawu ta qurawa yaron ido jajir dashi babu
inda ya dauko rumanah Sak maheer ne saitaji bazata iya cutatar dashiba.
Nurse ce
tazo ta karbesa sbd aankeshi dazasuyi su kintsashi kafin dayan babyn yafado sbd
naqudar takoma qasa tsananin wahala take sha ko ayanxun.
Jiki na
matuqar 6ari Jakadiya ta isa qofar sashen maheer tun a qofar ta zube tareda
'daga murya tace,
Allah
yataimaki uban magajin mineelik ummu-rumanah tasauka lafiya ansamu magajin
mineelik da yardar Allah.
Zabura yayi
daga kishingiden dayake yana sakin ajiyar zuciya da qarfi yana rufe ido sbd
zaman jiran dayake shine abu mafi azabtuwa a tsawon rayuwarsa ayau ya raina
zamtaowarsa likita tunda bai taimaki matarsaba lokacinda takeda tsananin
buqarsa.
Fitowa yayi
cikin wata irin qasaita hannuwansa zube a aljihunsa ya tsaya nesa da jakadiyar
yana kallonta kamar tana daukeda abinda aka haifar yace,
Kije ina
miki albishir da zama jakadiyar magajin mineelik tareda kyautar werik'i(gold)
Murna fal
cikin ranta tace,
Ameseginalehu(godiya)
Miqewa tayi
zata fita abakin qofa taci karo da 'yar saqo daga sashen suhailat ta durqusa
qasa cikin girmamawa da rawar jiki tace,
Gimbiyar
yarima ta sauka ansamu NAMIJI saidai likita tace sanarda yarima bazata sake
haihuwaba mmahaifarta tasamu matsala wannan itace haihuwarta ta qarshe.
Zaro ido
Jakadiya tayi cikeda tsananin mamaki da farin ciki tareda tausayin suhailat
tajuya takoma gurin maheer tasanar dashi atake ya sake lafta mata wata kyautar
zuciyarsa na harbawa da qarfi
Ya zauna
ahankali tareda lumshe ido yana yiwa Allah godia.
Koda
Jakadiya takoma sashen rumanah haihuwar tazo gadan gadan nan wani babyn ya fado
Dr ta ciresa nanma sukaga namiji atake aka shiryasu jikin Jakadiya babu inda
baya rawa ta zube gaban sultan kanta qasa cikin tsananin farin ciki tace,
Allah
yataimaki kakan magajin mineelik ummu-rumanah ta sauka lafiya ansamu 'yan biyu
duka MAZA sai gimbiyar yarima itama ta samu 'da namiji
Ina yiwa
sultan farin cikin ganin wannan rana mai tarin cikar buri da biyan buqata,
Ayau
mineelik ta samu qaruwar 'yaya uku uku duka maza ina sake taya sultan murnar
ganin wannan rana.
Wani irin
murmushi yake fitarwa mai bayyanarda farin cikin da zuciyarsa ke ciki bamai
misaltuwa bane
Dukkanin
Wanda ke royalhall din farin cikine mai tsanani a fuskarsa nan take aka buga
bell din mineelik aka sanarda haihuwar magajin mineelik atake labarin farin
cikin ya bazu koina Ethiopia ta dauka kowa farin ciki yake da wannan burin na
qasar daya cika.
Dayake ba
qaramar wuya dukkaninsu suka sha ba ana kimtsasu sai bacci banda rumanah data
rufe idone kawai zuciyarta cikeda tashin hankali da fargaba tareda baqin cikin
abinda kunnuwanta sukaji mata ammy na fada da bakinta.
Hawayen
idonta suka gangaro batareda tadamu da gogesuba ta bude idanuwanta dasukai ja
hawayen nacigaba da 6alle mata.,
Idan
kunnuwanta sun jimata daidai ammynta ke fadar sune suka kashe mata iyaye kenan
ba mutuwar Allah sukayiba qarfi da yaji aka rabasu da rayuwarsa,aka rabasu da
'yarsu,Ashe shiyasa aka 'yantasu???
Girgiza
kanta tayi hawayenta na tsananta tace,
Ammy
bazatayi hakaba nice banji daidaiba,ammy bazata iya kashe kowaba bare iyayena.
Sakin
siririn kuka tayi tareda kifa kanta a pillow.
Suhailat
kuwa bacci tayi sosai sbd ta galabaita fiyeda yanda ta tsammata saidai tana
haihuwar taji batajin komai.
Lokacinda
aka kaiwa maheer yaran duka yana tareda khaleefa daya iso ranar khaleefa ne
yakarbi sauran biyun maheer kuwa Wanda aka fara haihuwa ya karba akaro na farko
dayaji jikinsa yayi sanyi sbd soyayyar yaron dayaji shima yau yahaifi magajin
kansa bama na mineelik kawaiba.
Qura masa
idanuwansa yayi ganin yaron shine Zak sai lips din mahaifiyarsa daya dauko ya
sa hannu ahankali ya shafo lips din tareda sakin wani irin murmushi qasa qasa
yayiwa yaron addua kafin ya furta,
ABEEL
HASSAN.
Kallonsa
khaleefa yayi cikeda farin ciki ya maimaita sunan yana jinjina kai kafi ya
karbesa ya miqa masa babyn suhailat da ba'ason motsasa sosai.
Qura masa
ido yayi cikeda tausayinsa da qaunarsa mai qarfi shima shiya dauko Zak saidai
zamansa qarami sosai yasa yafisu haske.
Addua yamasa
sosai cikin rada rada ya furta,
Jemaal.
Koda ya
karbi Hussain din abeel abrar bayan yamasa addua ya rada masa,
ABEEL
HUSSAIN
Koda aka
kaisu gurin sultan kowa saida yatabbatarda yau ranar daban take arayuwarsa ya
'dagasu daya bayan daya yayi musu addua kafin aka sanar dashi sunayen da yarima
maheer ya rada musu sultan mai damuba sbd ayau angama masa komai arayuwa ya
'daga abeel cikin babbar murya yace asanarda kowa ga magajin mineelik ABEEL
HASSAN.
Atake akaje
dakin tarihi aka saka sunansa da sunan mahaifiyarsa nan aka fara shagulgulan
haihuwar.
Har dare
ammy bata samu ganin rumanah ba sbd tunda tayi wanka take rufe a dakinta tace
bata buqatar kowa Hutu take buqata.
Lokacinda
aka kawo mata yaranta qura musu ido tayi hawaye na gangaro mata sbd idan bar
aka iya raba iyayenta da ita za'a iya rabata da 'yayanta saidai batajin hakan
zata iya yiwuwa koda zata rasa rantane.
Rungumesu
tayi tareda rufe ido qaunarsu data mahaifinsu na shigarta tako ina.
Da daddare
lafiyyan abinci kala kala aka aika gefen kowaccensu aka jera.
Duk yanda
Jakadiya da ammy sukaso ganinta qin bari tayi ta dasun shigo zata rufe ido tana
bacci idan sun fita zata cigaba da kukanta.
Kukane
takeyi na rashin Sanin abinyi sbd ko ganin kowa batason yi.
Lokacinda
labarin haihuwar tasamu adama da 'yar dakinta mamani kadan yarage adama bata
yanke jikiba mamani kuwa kasa daurewa tayi saidatayi kuka taji sauki sauqi
cikin ranta.
Koda aka
kawo mata yaran saka musu albarka saidata kai zuciyarta qololuwa gurin bugawa
kafin ta iya kallonsu idanuwanta na cikowa da hawayen baqin ciki tasaka musu
albarkar dole.
Suna fita ta
miqe batareda takalli mamani dake matsar hawayeba cikin tsananin tashin hankali
tace,
Duk yanda
za'ayi ayi yaran nan bazasukai ranar sunansuba batareda sunbar duniyaba kije
yanxu ina buqatar kadaici gobe zan fada miki abinda zakiyi sbd inason alhakin
mutuwarsu ya rataya akan kakarsu da jakadiya sbd inason qulla gaba mai tsanani
tsakaninsu da yarima tareda matansa kuma inason sultan ne da kansa zai yankewa
sultana hukuncin kisa ta yanda abin zai riqa bibiyarsa yana damunsa da haka
zansamu sauqin aikina akansa.
Acikin daren
yakira suhailat yaji yajikinta tareda jemaal duk da khaleefa yadubasa sosai
yafadi dokokin daza'abi kafin suna shi dole za'a koma Georgia dashi sbd
yanayinsa acan za'a fara kula dashi.
Duk yanda
yaso ganinta yasan abune mai wuya saidai kuma bayajin zai iya bacci bai
dubotaba bayan baqar wahalar dayasan tashiga yau gurin haihuwa saidai koda ya
aika asanarda Jakadiya taje tayi ma sashen isonsa ta sanardashi har lokacin
bata fitoba taji jiki sosai hutawa takeyi haka ya hakura saidai asubar fari ya
isa dakinta lokacin tana zaune bakin gado tasaka yaran agaba hawaye nabin
fuskarta.
Qamshinsa
yasata rintse idanuwanta hawayenta na sake gudu.
Zama yayi
kusada ita tareda riqo hannunta baice komaiba ya kwantarda kanta jikinsa sai
kawai tasaki kukan datake ruqewa ahankali
Cikeda
mamaki da damuwa ya kalleta zaiyi magana ta zame daga jikinsa tana tsaida
hawayenta cikin dasashiyar murya tace,
Kaina na
ciwo ina buqatar hutawa.
Da mamaki
yakalleta saidai baice komaiba ya miqe ya fice
Ta saki
sabon kuka cikin rashin Sanin abinyi.
Duk inda
hankalinsu ammy yake yatashi dashi kansa maheer din sbd kwana uku da haihuwar
ko kadan rumanah takasa bari ko 'dayansu ya ganta duk wani tashin hankali suna
ciki
Ta hargitse
tarasa abinyi gabaki daya ta birkice shikansa ta hanasa ganin kanta bare yasan
meke faruwa babban tashin hankalin daya riskesu shine sanarwar da akayi za'a
bawa uwar magajin mineelik kujerarta ta uwar sultan.
Sam ammy ta
rasa ina zata saka kanta shikansa baya cikin nutsuwa sbd bazai taba bari ta
karbi sunan uwar sultan ba gashi dole
zata karba itace zata bawa duk Wanda takeso riqon kwarya.
Yau kwanansu
biyar da haihuwar dukkanin yaran suna sashen ammy tun safe.
Tunda sukazo
abeel hassan ke kuka sosai anmayardashi gurin hamaifiyarsa saima qara birkicewa
da yayi nan hankula suka tashi tuni sultan yasa atara duk masu magani da
likitocin mineelik amma sai qara rikicewa yakeyi nan hankalin rumanah itama
yayi masifar tashi ta rikice.
Cikin tashin
hankali suka dunguma zuwa royalhall inda ake duba yaron kowa hankalinsa atashe
yake.
Kallo daya
yayiwa rumanah yaji lissafinsa yasake kwancewa kafin yayi wani yunquri sarkin
gida yossouf Kaleb yashigo jikinsa na matuqar rawa ya zube gaban jakadiya yayi
mata magana qasa qasa hankali tashe jikinsa na wani irin mazari.
Zaro ido
Jakadiya tayi cikin sabon tashin hankali jikinta yadauki muguwar rawa kowa
hankalinsa nakanta anajiran jin saqon menene
Ta zube
gaban sultan tareda sauke kanta jikinta na tsananta rawa cikin muryar tashin
hankali da tsananin fargabar rasa rayuwarta tace,
Allah
yataimaki sultan ina cikin baqin cikin sanardakai ankama baiwa mamani da dafin
baqin maciji tabawa abeel Hussain da jemaal antabbatarda sun rasu saidai
ankamata.
Rumanah dake
zaune ta miqe a firgice jikinta na rawa saidai ko daga qafa batayiba ta yanke
jiki ta fadi agurin.
Cikin tashin
hankali yayi kanta kai tsaye yadauketa yabar palon su ammy na mara masa baya
hankali tashe musamman sultana da a sashenta suke shaf tashin hankalin abeel
hassan yasa suka mantasu acan.
Sultan kuwa
numfashi ya sauke cikin wani irin yanayi ya miqe tsaye idanuwansa na canzawa.
Suhailat na
zaune tana shan magani daqyar sbd ciwon ciki da jirin datake fama dashi tun
safiyar yau din
Jakadiya ta
shigo mata.
Murya na rawa tace,
Ina neman
afuwar saqon baqin cikin danazo dashi Allah yakarbi ran jemaal........
Bata
qarasaba suhailat ta miqe tsaye atake jini ya 6alle mata ta yanke jiki ta fadi.
#mamuhgee
No comments