TARAYYA 1-2
TARAYYA HAUSA NOVEL
BISMILLAHIR RAHMANIRRAHEEM
For you my ummu-khulthum.
Page 1
Bayine da kuyangi bila adadin
akowace kusurwa ta cikin babbar masarautar kowanne da aikin daya duqufa yanayi
wasu nsu kuma a qaqqame suna gadin hanyoyin wucewa da kowace qofa ta cikin
masarautar
Dukkaninsu kalar kayansu
dayane mazansu da matansu kalar dark blue Wanda zaa iya kira da uniform.
Ahankali kowannansu yafara
aje aikinda yakeyi yana ra6ewa gefe tareda sunkuyarda kai qasa sbd takun
tahowar sarauniya Wanda sautin anklets din zinarin dake qafarta shine yake
sanarda isowarta ko tahowartar tundaga nesa wanda tunda ta tashi arayuwarta ta
taso agidan sarauta tasaba duk inda take sautin sarqar ke sanarda tahowarta
harzuwa yanxu data manyanta sbd mulki a jininta yake.
Tana qarasowa hanyar dazata
shigarda ita 6angaren mai martaba sarki ta tsaya cak batareda tace qalaba
tareda juyawa ahankali tadan kalli gefenta da dama.
jakadiyarta dake gefenta tayi
saurin matsowa tareda juyawa takalli kuyangin dake take musu baya kusan su
shida kallo daya tayi musu suka ja baya ahankali suka tsaya tareda sunkuyarda
kai.
Boyayyar ajiyar zuciya
tasauke ahankali tareda shiga qofarda aka jima da wangale mata jakadiya tabita
abaya aka rufo qofar. 1
Parlour ne mai wani irin
girma da tsari dayaji adon royal chairs red and golden kamar zinari sai qyalli
suke sai komai daya qawata palon yazamto shima red and golden dinne splits
aircon kusan guda biyar sai aiki suke sanyi yakama palon takoina sbd wata irin
dukiyace ta musamman aka narkar a palon.
15
Babu kowa a palon sbd palon
farkone dazai sadaka da palon sarauta harzuwa turakar sarki
Ta sake tsayawa cak tareda
sake sakin wata sahirtacciyar ajiyar zuciya akaro na uku zuciyarta na harbawa
batareda tajuyo bangaren jakadiyaba murya a karye tace,
Wannan saqon na sultan(sarki)
yana matuqar girgixa zuciyata sbd saqone daya zamto na baqin ciki agaresa,
Duk wani bawa ko bafade yakai
wannan saqon abakacin rayuwarsane shiyasa nazabi nazo na isardashi dakaina,
Ajiyar zuciya mai nauyi
jakadiya ta sauke tareda kallon sarauniya zaarah din cikin tausayawa acikin
aranta afili tace,
Allah yataimaki sultana
yakuma sanyaya ranki badan kinyi rashiba yabaki ikon isarda saqon sarkin
sarakuna....
Katseta sultana zaraah tayi
da cewa,
Haihuwa tazamar mana abar
fargaba maimakon farin ciki.
Uwargijiyata Allah ya
sassauci fargabarki amma dakin sake kin nunawa yarima farin cikinki da qaruwar
dayasamu tunda shi yanaso ahakan kuma yana godiyar Allah da arzikin qaruwa daya
basa
Allah ya raya abinda aka
Haifa din yasa ayi alfahari da hakan gaba.
Ajiyar zuciya sultana tasake
tareda furta amin qasan maqoshinta kafin ta tattaro jarumta da qarfin gwiwa ta
gyara zaman gyalen kanta daya rufo dogon gashinta dake kwance har bayanta Wanda
shima gashin harzuwa goshinta adone na wata kyakkyawar sarkar zinari ta kai sai
aka rufo gyalen doguwar rigarta dark purple dataji adon duwatsu masu shegen
kyau da kyalli gyalen naja har qasa kadan.
STORY CONTINUES BELOW
Ratsa dogon palon tayi
jakadiya na bayanta ta nufi qofarda zata kaita ainihin palonsa na musamman tana
zuwa wanda ke tsaron qofar ya wangale mata qofar ahankali tashiga jakadiya
takoma gefe ta toge itama tana jiran fitowar uwar dakin tata.
Wani palon ne na alfarma babu
kowa sai qarar ac dake tashi ahankali
10
Zaune yake cikin shiga ta
alfarma
Dattijone sosai da Hutu da
mulki na jinin sarauta daya ratsasa,
Kallo daya yayi mata da
idanuwansa masu tsananin kwarjini da firgitarwa taso rudewa tayi saurin
daidaita kanta ta tattaro nutsuwa da qarfin hali.
Qarasowa tayi cikin sanyin
jiki da fargaba ta kallesa ta rufe idanuwanta dasuka fara canxawa murya na rawa
tace,
Allah yataimakeka saqo daga
GEORGIA.....
Idanuwan daya sake watso
matane yasa taso daburcewa tayi saurin gyara murya cikin nutsuwa ta dauke
idanuwanta daga kallonsa murya na rawa tace,
Yarima yabugo yasanarda saqon
matarsa ta sauka ansamu 'YA MACE.
Sake dauke kai tayi sbd gudun
ganin yanayinsa sbd kodagajin yanda ya dauke wuta tasan ran maza ya baci babu
jin dadi ko alamar farin ciki dagajin saqonta.
Tsawon mintuna ashirin shiru
Kamar daga sama taji
dakakkiyar muryarsa cikin ikon mulki yace,
Kin isarda saqon yarima Dan
haka kisanardashi saqonsa ya iso
Ke kuma tukuicinki na sanarda
saqonsa bazaki sakashi a idoba sai bayan shekara daya,
Karya dawo harsai matarsa
tasake samun wani cikin wannan karon anan zata haihu
Zata haifi yariman da ubansa
yaqi amsa.
Yana gama fadar haka ya miqe
zai shige turakarsa
Dagowa tayi takallesa
idanuwanta na canxawa zuwa kalar tausayin kanta dabazataga 'dantaba ko awannan
shekarar
Tsawon lokaci kenan tunda
yayi aure matarsa tahaifi ya mace suka koma Georgia sarki yace karsu dawo saita
sake samun wani cikin tasamu tasake haihuwar mace yasake korasu yarinyar ta
rasu still yahanasu dawowa harsaita haifi namiji yanxuma gashi macen ta haifa
kuma yanxunma saiwata shekara kenan kusan shekara biyar kenan rabonta da danta
tana tsananin kewarsa dason ganinsa.
Cikin sanyin murya tace,
Allah ya huci zuciyar sarkin
sarakuna
Na karbi hukuncina matuqar
hakan zai faranta ran sarkina
Saqon yarima kuma kamar
yagama isa a kunnensa ne
Nabarka lafiya.
Juyawa tayi ta nufi qofar
tana isa aka bude mata ta fice
Jakadiya tayi saurin Mara
mata baya kanta asunkuye sbd ganin yanayin uwar dakin nata.
Suna isa babbar qofa suka
fice kuyanginta sukai saurin Mara musu baya
Bayi sai zubewa suke suna
sunkuyar dakai yaukam ko kallonsu bata iyayi bare amsa gaisuwarsu dankuwa ranta
amatuqar dagule yake.
Tana isa sashenta cikin
tsananin sauri aka bude mata qofa tashiga
Tana shiga kai tsaye hanyar
bedroom dinta tayi bayan tasake wuce palonta na musamman inda babu mashigowa
duk fadin masarautar daga ita sai danta yarima sai amintacciyar kuyangarta
datake kamar matsayin 'ya agareta saikuwa jakadiya ko matar yarima bata taba
shigowa nan palonba iyakacinta na farko bedroom dinta kuwa ko yarima baitaba shigaba
bare jakadiya kuyangarta mai gyara mata kawai keshiga.
Tana shiga bedroom din
taganta a tsaye jikin wardrobe din lafiyyan dakin tana jera mata sabbin kayanta
dasuka iso.
Daidaita nutsuwarta da
fuskarta tayi tareda gyaran murya batareda takalletaba.
Juyowa tayi da sauri tana
ganin sultana zaarah tasaki wani irin lafiyyan murmushin daya bayyanarda dimple
dinta duka guda biyu cikin tsananin taushin murya da tsantsar ladabi tace,
Ammy barka da dawowa.
Daga mata kai ammyn tayi
batareda sakin fuskaba kamar yanda suka sababa murya a dake tace,
Ina buqatar hutu.
Cikin nutsuwa tayi saurin aje
kayan ta nufi qofa zata fice jiki asanyaye sbd ganin yaudai ammyn bata cikin
kwanciyar hankali dankuwa tunda safe take lureda ita bata cikin kwanciyar
hankali.
UMMU-RUMANA....cak ta tsaya
jin ammyn takirata tareda juyawa cikin ladabi tace,
Allah yataimaki ammy.
Bana buqatar damuwa takomai
da kowa ko dogon motsi banaso kowa yafice daga nan shashen zuwa anjima saiku
dawo ina buqatar Hutu.
Ahuta lafiya
ammy"""tace cikin sanyi tareda ficewa jiki ba dadi sbd damuwar
ammy na matuqar ta6ata sbd akoyaushe idan takalleta cikin annushuwa ganin take
tamkar mahaifiyartace cikin annashuwar kasancewar mahaifiyarta babbar
amintacciyar baiwar ammyn kuma jakadiyarda kafin tarasu.
Tana fitowa bban palon ammyn
duk ta sallami sauran kuyangi da bayin sashen itama ta fita masu tsaron qofar
shiga sashen kawai aka bari tareda nufar hanyarda zata sadata da bangarensu na
bayi inda kowa keda daki mutum uku daki daya.
#mamuhgeee.
Page 2
Babban sashensu na bayi da
bororin masarautar ta nufa tana isa kai tsaye dakinsu ta nufa tana ganin qofar
abude tasan nuratu naciki tashiga bakinta daukeda siririyar sallama.
Zaune bakin katifa taga
nuratun tana qoqarin zare wandon uniform dinta zata shiga wanka ta nufi bakin
tata yar katifar ta zauna tana cewa,
Yau kingamo da wuri Nima
nasamu dan qaramin hutu daga ammy yanxu kiyi sauri kiyi wankan sai kiyimin koda
kalbane sbd inason zanyi wankan tsarki banasan nayi da kaina a tsefe zai dameni
tunda ba iska zaishaba koyaushe muna cikin uniform. 5
Kallonta nuratu tayi jin
yanayin data qarasa zancen dashi kamar koyaushe tun tasowarsu sun bude ido sun
tsinci Kansu a bayi kuma yayan bayi Wanda har gwara ita tanada mahaifiya rumana
din batada uwa batada uba.
Fasa shiga wankan tayi ta
qarasa katifar rumana din ta zauna tareda zame mata dankwali tace zonayi miki
daga baya nayi wankan sbd nima aikine dani matuqa zanje karbo sabbin furannin
dazaa jera a kwalbar ruwan dake girke palon sarauniya adama na farko gakuma aikin
chanxa
Gyara zama tayi cikin
tausayawa rayuwarsu tace,
Mamani tasha saqe saqin
maganinta kuwa kafin tafita aiki?
Girgiza kai nuratu tayi cikin
tausayin mahaifiyarta dakuma na rumana din datake qaunar mamani da zuciya daya
duk da kyararta datakeyi.
Kamar rumana tasan me take
tunani cikin sanyin murya tace,
RUMANA INA MAI HORAR DAKE KI
RIQE ALLAH AKO WANE HALI KO YANAYI KIKA TSINCI KANKI DA RAYUWARKI,
IDAN KIKA RIQESA KIKA ZAMA
MAI HAKURI DA DANGANA DA DAUKAR QADDARAR DAYA DORA MIKI MAI KYAWU DA MARAR
KYAWU TO KODA KIKE BAIWA RAYUWA BAZATAYI MIKI TSANANIBA HAKAMA IDAN KIKA ZAMO
BAIWA MAI BIN UMARNIN UWAYEN GIDANKI TO HAKAMA RAYUWA BAZATAYI MIKI
TSANANIBA...
Nuratu wainnan sune kalaman
ummana da ako yaushe suke shawagi cikin zuciya da kunnuwana wainda sune nake
kallo amatsayin wasiyyarta gareni,
Ni baiwa ce uwata da ubana
bayine harsuka rasu,
Banida wani gata ko
martabarda zan kalli kaina amatsayin wata mace ko 'ya mai qima sbd nima
zanqarasa rayuwatane amatsayin baiwa kamar iyayena,
Tun lokacinda nayi wayo
cikakkiyar mai yanci ta
hanyar 'yantawa
Allah yakarbi adduata amma
adaidai lokacinda yantawar batada amfani sbd tana kwance ciwon ajali Wanda yasa
na yanke rai daga samun ingantacciyar rayuwa.....
Katseta nuratu tayi da cewa,
Ba'a cire rai daga rahamar
uban giji rumana,
Ki zamto mai gode masa da
kowace irin niima,
Ke mai saa ce sbd koda
kasancewarki baiwa kinfita dabam acikin bayi sbd ke abar qaunace ga sarauniyar
datafi kowace mace matsayi acikin masarautarnan sultana zaarah kasancewarki 'ya
ga amintacciyar baiwarta
Ko ahaka kika duba zaki
godewa Allah da wannan ni'imar.
Ajiyar zuciya tasauke
ahankali tareda zare kanta ta juyo ta kalli nuratun tana tattare dogon gashinta
tace,
Kibar kitson kiyi wanka
kikoma bakin aikinki da wuri sbd gudun kwana gidan kason masarauta.
Tashi nuratun tayi tana jawo
kayanda tafara maidawa tana cewa,
Bazan samu yin wankaba kuma
sbd lokaci yashiga kuma wlh tsananin aikine asashen sarauniya adama sbd komai
na sashen zaa canza har sitirunta kaf ko tsokalinda aka siyo jiya bazai shiga
sashentaba sai sabo dal sbd kwanaki uku zuwa hudune suka rage ta kammala
hukuncinta na sultan daya bata na ko qofar palonta na farko karta fito sai
bayan shekara guda iyakacinta palonta na qurya zuwa bedroom dinta ko 'yayanta
anhana shiga gurinta bare kuyangi iyakacinsu palonta na farko jekadiyarta kawai
keda izinin shiga sbd kamata da laifin sa likita yaje gidan 'yarta gimbiya
amatullah yayi mata allurar tsarin haihuwa suda ake fatar samun 'da namiji a
zuria sbd.....
STORY CONTINUES BELOW
Rufe mata baki rumana tayi
tana kallon qofa tace,
Ya isa idan wani yajimu
kinsan rayuwarmuce zamu qarasa a kurkuku.
Saurin kallon qofa nuratu
tayi ido a firgice zufa na karyo mata sbd shaf idan tafara barin baki mantawa
takeda abinda zaibiyo baya sbd masarautar takasance maitsananin hukunci babu
sauqi ko bata lokaci sbd tsagwaron mulki da iko ke yawo a jinin masarautar
kasancewar sarkin masarautar mai tsananin zafine da zallar mulki babu sauki
gurin daidaitawa kowa kansa,
Kwarjininsa ikonsa kesa ko
matansa da 'yanyansa ke matuwar shakkar hukuncinsa shiyasa kowa a kiyaye yakeda
umarninsa bare 'yan fada da sauran hakiman sarki.
Kusan atare suka fito daga
dakinsu suka jawo dakin suka kowa yanufi gurin aikinsa
Kai tsaye rumana sashen
sultana zaarah takoma inda ta tararda dukkanin wasu kuyangin sashen a qofar
sashen sun jeru zai zufa suke sbd tsayuwa gashi babu ikon zaunawa haka itama
tabi layinsu suka cigaba da tsayin jiran lokacinda uwar dakinsu zata gama
hutawa sukoma ciki domin hidimarta.
Saida rana tafadi lis kafin
ta matsa sbd lokacinda ake diba nabawa sarauniya Hutu yayi idan bata fitoba ana
shiga aga lafiyarta
Matsu tsaron bakin qofar
sashen sukayi saurin bude mata tashiga
tana goge zufanta ta tsaya a palon farko saidatayi mintuna kusan shida atsaye
AC ya butsarda ita kafin ta nufi palon gaba tashiga da sallama Mara qarfi sbd
gudun yin hayaniyar da ammyn bataso.
Shigarta yayi daidai da
fitowar sultana din daga bedroom dinta cikin doguwar riga maroon dataji adon
sequence stones masu masifar kyau sai qyalli suke wannan karon babu adon sarqar
zinari a gashinta da wuyanta kamar koyaushe saidai wasu awarwaron zinari masu
kauri da girma sosai hakama babu kwalliya afuskarta kamar koyaushe sbd sultana
zaarah takasance yar sarautar qasar Morocco koyaushe cikin tsananin ado da
kwalliya take musamman gwalagwalai naban mamaki hakama bazaka gantaba kace
tanada babban jarumin 'da sbd zamanta kyakkyawar mace mai kyawun jiki.
Durqusawa tayi cikin tsananin
ladabi tace,
Barkada fitowa ammy da fatar
kinhuta lafiya.
Zama ammyn tayi kan 'daya
daga cikin royal chairs din palon batareda takalli rumanarba ta 'daga kai kafin
tace,
Rumana 'yau banason dogon
motsi bare hayaniya Dan haka kisanarda sauran ayi komai cikin qanqanin lokaci
kowa ya fice kema ki kammala kije kihuta bana buqatar kowa.
Angama ammy.
Miqewa tayi taje tasanarda
sauran kuyangin tadawo ta nufi bedroom din ammyn tafara gyara ta canza zanin
gado sbd kwana daya 'daya yakeyi acire asaka sabo tana gama gyara koina ta
sassaita AC daidai yanda ammy keso sanyinsa ya kasance takunna burners qamshi
yafara tashi ta shiga toilet tayi gyaran dazatayi ta fito taje takarbo
abincinta a manya manyan tururuwa ta jera a makeken royal dining din dake palon
ta dawo gabanta ta durqusa a ladafce tace,
Allah yasa ahuta lfy yakuma
tasheki lfy.
Ficewa tayi lokacin tuni aka
fara kiran magriba daidai zata fito dake jakadiya dake qoqarin daidaita
nutsuwarta tashigo.
Tsayawa jakadiya tayi a palon
farko tafitarda numfashi mai zafi sbd sotake ta daidaita kanta sbd da
rayuwartace amatuqar tsaka mai wuya duk tabari fargabarta tasa sultana tagano
hukuncin da sultan ya yanke akan alamarin dake damun masarautar shekara da
shekaru.
Tunda suka baro gurin sultan
dazu tasake komawa sbd kai saqon banhakuri da tubar uwargijiyarta bisaga saqo
Mara dadi data kaimasa na haihuwar mace da matar yarima tayi.
Abakin qofar fadar ta wuni
tsaye cikin rana Dan nuna banhakurin uwargijiyarta Wanda saida rana ta fadi lis
sarki ya aikoda izinin shigowarta.
Jiki na rawa ta zube gabansa
cikin tsananin girmamawa tace,
Allah ya huci zuciyar sarkin
sarakuna,
Sarkinda yafi kowane sarki
adalci,
Da yardar Allah sai anmaka
takwara harsai andarje a jininka,
Ba 'daya za'a samuba ba
biyuba dozin ne da yardar ubangiji saika gansu saika aurensu
Allah ya sake hutar zuciyarka.
7
Gyara murya yayi cikin wani
irin iko da umarni dake nuni magana daya yakeyi yace,
Jakadiya aje aciro 'yan mata
biyar dasukafi kowa kyawu acikin kuyangun masarautarnan a killacesu afara
kintsasu daga yanxu harzuwa nanda shekara daya lokacinda yarima zai dawo
Za'a kaisu sassansa amatsayin
sa dakokinsa duk wadda ta haifi namiji ayimata albishirda tazama uwar sarkin
wata rana.
Amatuqar kidime jakadiya zufa
ya keto mata murya na rawa tace,
Angama sarki mai adalci,
Cika umarninka zaifara ne
daga yanxu,
Allah dai yaqara hutar
zuciyarka
Nabarka lafiya.
Fitowa tayi saida ta
tabbatarda tayi nisa da sassasansa ta tsaya gefe tareda sharshe zufar daketa
faman karyo mata tayi shiru tsawon mintuna zuciyarta na tumamin hukuncinda
sarki ya yanke dakuma sanin waye yarima akan tsantseni matarsama da yaya
akasamu yayi auren bare sa 'daka har biyar...
Sake sharce zufa tayi cikin
tsananin fargaba gashi abakacin ranka matuqar sarki ya yanke umarni katsaya
sanarda wani batareda ka cika umarninba Dan haka batada ikon fadawa kowa saidai
kawai aiwatarwa.
Nufar sassan sultana tayi
cikeda fargaba da tausayinta ta yanda hankalinta zai matuqar tashi duk randa
taji zata fara shirin tarbon jikokinta na sa'dakoki.
#mamuhgee
No comments