RAINA KAMA (BOOK 3) 21
BOOK 3 👉🏻2⃣0⃣
.................Galadima
ganima yake kamar Sarkin mota baya Sauri, amma baiyi maganaba, zuciyarsa tamafi
motar gudu, dan bugawa take da sauri-sauri tamkar zata fito.
Suna isowa bai saurari an bud'e masaba ya
bud'e da kansa yay cikin asibitin, dayake k'aramin asibitin ne, na kud'i su
Ahmad suka
kaisu, da sauri Nurses d'in dake reception suka masa sannu, tare da
gaisheshi, dan 6atancin da aka musu Shida sh Munaya a wancan lokacin yakuma
sakawa wad'anda basu sanshiba ma suka sanshi, ga kuma abinda ya faru a
kwanakinnan.
Uffan baice da suba yay gaba abinshi, cikin
takunnan nasa Na k'asaita da izza, Wanda a yanzu yak'ara armashi da 6acin rai.
Su Ahmad da suka hango tahowarsa duk suka
mik'e a tare suma suka nufosa, kallon mamaki yake binsu dashi, suma duksun lura
da hakan.
Gebiral yace, “Uncle!”.
Kallonsa Galadima yayi idonsa sakaye cikin
eyeglasses daya 6oye jajayen idonsa,
kafin wani ya sake rmagana a cikinsu doctor ya iso wajen, duk hankalin
su suka maida ga doctor d'in suna tambayar ya jikin Aunty?.
Doctor yace, “ku kwantar da hankalinku,
insha ALLAH komai zai zama normal, Ranka ya dad'e barka da zuwa”.
Hannu kawai Galadima ya iya d'aga masa, a
lokacinne suma su Abba Hayatudden suka k'araso wajen.
A hankali Galadima ya bud'e baki yace,
“Ina matata da d'an uwana?”.
Cikin girmamawa Doctor yace, “Ranka ya
dad'e inason magana dakai idan babu damuwa”.
Kamar Galadima bazaiyi maganaba saikuma
ya gyara tsayuwa yana fad'in “Inason ganinsu tukunna”.
Doctor yay jimm baice komaiba.
Hakanne ya d'arsa tashin hankali a
zukatan kowa Na wajen, Galadima ya yunk'uro zaiyi magana doctor yay saurin
taresa ta hanyar fad'in “Amma ranka ya dad'e namijin kawai, dan gaskiya ita
ba'ason ayi wani kwakwkwaran motsi a kusa da itane”.
Kowa Na wajen ajiyar zuciya ya sauke,
danjin sunada rai, Galadima daya kasa koda motsi doctor ya kuma kalla, zaiyi
magana ya d'aga masa hannu alamar baison jin komai.
Abba Hayatudden da Baffi da sukasan
halinsa idan yana cikin damuwa suka kalli doctor, baffi yace, “doctor yakamata
ko shi kad'aine ya ganta, mu saimu duba Nuridden d'in”.
A sanyaye doctor ya gyad'a kai, dan
inda sonsamune babu mai shigar.
Nurse ya had'a su da ita takaisu inda
Nuren yake, amma kar ayi hayaniyar dazai farka, dan ana buk'atar yasamu barci
sosai.
Doctor kuma yayma Galadima jagora da
kansa, amma a k'ofar d'akin suka cire takalmansu, dagasu sai sock's d'in
k'afarsu suka shiga.
'Dakine madaidaicine da gad'o d'aya,
asibitin sunada Kayan aiki babu laifi, tamkar an zarema Galadima lakar jiki
haka yake takawa cikin sand'a, doctor ya nuna masa kujera guda d'aya dake kusa
da gadon, idonsa a kanta tunda suka shigo, harya zauba yakasa janyewa, tana
kwance sam6al a gadon tamkar wata gawa, kanta nad'e da bandeji alamar taji ciwo
akan, dan har fuskarta tanuna saboda kumburi da tayi, alik'a mata oxygen a
hanci Wanda da alamar shike taimakawa numfaahinta fita, ya maida kallonsa ga
damtsen hannunta da shima yake anad'e, sannan kuma tafin hannunta ma haka, wasu
hawaye masu zafi suka gangaro tacikin eyeglasses d'in idonsa daya hana ganin
tahowarsu tun daga cikin idon.
Ya kalli doctor da shima yake tsaye
kansa duk'e a k'asa alamun damuwa, baice komaiba ya mik'e ya fito abinsa,
doctor ya biyoshi a baya shima da hanzari.
Da hannu yamasa alamar ya kaisa inda
Nuren yake.
Nanma shine yamasa jagora, duk inda suka
gitta idanun mutane akansa, oho baimasan sunayiba, abinda ya dameshi shine
gabansa.
Su Abba Hayatudden suna d'akin har
yanzu, shigowarsu Galadima ya sakasu juyowa suna kallonsa gaba d'aya, ya
k'araso gaban gadon idonsa akan Nuren dake barci shima, saidai shi babu bandeji
ko d'aya a jikinsa, dan baiji rauniba, dukansa da sukayi a kai ne ya sakashi
suma, anama zuwa asibitin babu dad'ewa ya farfad'o, shine sukai masa allurar
barci da saka masa k'arin ruwa danya huta, sanda zai farka ya farka da k'arfi a
jikinsa..
Galadima ya durk'usa a gaban gadon ya
kamo hannun Nuren cikin nasa, yana k'aunar Nuren sosai har cikin ransa, danshi
mutumne simple, idan yamaka wani abun bazaka ta6a cewa shi jinin sarauta
baneba, ko kad'an bashida damuwa a rayuwarsa, tunba yanzuba Nuren yake bama rayuwarsa gudunmawa, baita6a k'osawa ko
gundura da halinsaba, balle yace masa bazaiyiba, saidai inhar abin baida
tsarine zai bashi shawaran a canja kokuma ayi haka ko haka..........
Wayarsa datai ring ce ta katse tunaninsa,
yad'an karkata yana cirota a aljihun wandon yadinsa, ring d'in daya sakama papi
shi kad'aine ya sakashi fahimtar waye, ya mik'e daga gaban gadon yana picking
call d'in, saida ya fice a d'akin gaba d'aya sannan ya amsa sallamar da papi
yamasa cikeda girmamawa da tsantsar damuwa.
Daga can ajiyar zuciya papi yayi, dan
baiyi zaton samun Galadima cikin k'oshin lafiya hakaba, cikin tausasa Murya
papi yace, “Muhammad kana inane?”.
Shiru galadima yayi, kamar bazai iya
maganaba, saikuma ya bud'e baki da k'yar yace, “papi asibiti”.
“Asibiti kuma? Wanene babu lafiya?”.
Kasa danne kukan daya taho masa yayi,
ya fice daga cikin asibitin da sauri, mota ya bud'e ya shiga, ya kife kansa a
sitiyari ya fashema papi da kuka mai tsima rai da 6argon jiki, gaba d'aya jikin
papi yay sanyi lakwas, saima ya kasa magana shima, yay shiru kawai yana
sauraren jarumin jikansa mai yawan hak'uri da juriya akan abu, saida yay kusan
mintuna biyu yanayi, papi ya tabbatar nauyin da zuciyar galadima tayi ta ragu
sai yay gyaran murya, cikin tausasa harshe yace, “Muhammad Sameer mike
faruwane? Kokuwa kukan farin cikin cikar burine?”.
Da k'yar Galadima ya iya bud'e baki
yace, “papi yanzunan duk abinda suka aikata a gareni tsawon shekaru bai
ishesuba? Saisunyi yunk'urin kashemin d'an uwana da matata? Papi minayi musu da
zaifi haka? Miye laifin mahaifina danyak'i goyama k'arya da cin amana baya?
Miye laifinsa danya zama shugaba? Bayan hakan ba shirinsa bane tsarin ALLAH ne?
Miyasa suka manta babu abinda ke dawwama sai ALLAH, papi inhar matata ko d'an
uwana suka rasa ransu wlhy bazan hak'uraba, saina kashesu da hannuna nima
s........”
Dakatar dashi papi yay ta hanyar kiran
sunansa.
Galadima ya amsa masa da k'yar.
“Kayi hak'uri Muhammad kaji, ALLAH yana
tare da masu hak'uri, Hayatudden ya sanarmin komai, ALLAH yabasu lafiya, ba
shari'ar duniya bace kawai shari'a, akwai babba wadda babban alk'ali zaima
kowa, koba komai ALLAH ya kunyatasu tun a duniya, kowa yasan misuka aikata,
kuma ka dak'ilesu suda masu burin aikata irin nasu, ka ringa tunawa akwai tonon
asirin dayafi wannan, harma abinda yafi wannan da suka aikata akwai babbar kotu
mai cikeda d'unbin jama'a da babban alk'ali a gaba, banason kabar wannan abin
yayma zuciyarka tasiri haryakai ga kadaka k'asa, sannan karna kumajin kayi
kuka, ka kwantar da hankalinka muci gaba da musu addu'a, insha ALLAH gobe zan
shigo garin”.
Gyad'a kai Galadima yayi tamkar yana
gabansa, papi yakuma kwantar masa da hankali da nasiha mai ratsa jiki, saida ya
tabbatar hankalinsa ya kwanta sannan ya barsa....
Ya jingina da kujerar yanamai lumshe
idanu, wata nutsuwa ta musamman Na ratsa jinin jikinsa da zuciyarsa, knocking
glass d'in da akayi ya sakashi bud'e idanu a hankali, ganin sarkin motane saiya
sauke glass d'in k'asa, cikin girmamawa sarkin mota ya mik'o masa gorar ruwa.
Bai musaba ya kar6a yana gyad'a masa kai
alamar ya gode.
Sosai yasha ruwan kuwa, wata nutsuwa takuma
saukar masa, ya kuma d'aukar kamar 5minutes ya fito daga motar, ya koma cikin
asibitin, yanson ganawa da doctor d'in, idan yaji bai gamsu da aikinsaba dolene
yasan mai yuwuwa.
Yana shigowa su Ahmad suka k'araso
gareshi suna gaidashi da jajanta masa.
Cikin k'arfin hali yace, “baku tafi gida
bane?”.
Sarkin mota dake tsaye kusa dasu yace,
“Ranka ya dad'e ai Ahmad shine ya taimakeni nakawo camera d'in kotu d'azun”.
Da mamaki Galadima ya kalli Ahmad yana
nunashi da d'an yatsa alamar kaid'in?.
Murmushi Ahmad yayi yana gyara tsayuwa.
yace, “Uncle bayan fitowa daga kotune za'a hutunnan sai naji wani yaron su
Abbana yana waya akan atare su Aunty a kar6a Camera d'in, dan basa buk'atar ta
k'araso Court d'in, to hakan danaji shine Na k'arasa garesa Na bigi cikinsa
akan zancen”.
“nake cemasa zamuje ni da su Ahakam muma a
kwato Camera d'in damu, so hakan dayaji saiya d'auka da gaske tare nake dasu,
shine yabani key d'in mashin. Ina ajiye driver d'inka, sai mukazo asibiti ni da
Yassar muka sanarma da Uncle d'ina, shine ya bimu da Ambulance har wajen da
abun ya faru muka d'akkosu”.
Galadima ya kamo hannun Ahmad ya
rungumesa, yayma su Yassar dake kallonsu alamar suma suzo, cike da farin ciki
suma duk sukazo jikinsa.
__________
Hankalin mai martaba a matuk'ar tashe
yake, jin wai dan kawai yayi mulki wasu suka bada gudunmawa domin durk'usar da
d'an uwansa, “hazbinallahu wa ni'imal wakil” wannan wace iriyar masiface
hakan?.
Sai safa da marwa yakeyi a bedroom d'insa,
idanunsa Na kwarar da hawayen tausayin d'an uwansa da Galadima, ALLAH Sarki
mahaifiyarsa, yadad'e yana zarginta akan ciwon d'an uwansa, Ashe babu hannunta
a ciki, son zuciyar mahaifinta ne, Wanda a yanzu haka tsufa ya kamashi sosai.
Waya ya d'auka ya kira Abba hayatuddeen danyaji wane hali d'an d'an uwansa yake
cikine? Dan yayi tsumayen shigowarsu masarautar amma yaji shiru.
Bugu biyu Abba Hayatudden ya d'aga. Mai
martaba ya tambayeshi suna inane?.
Abba hayatudden ya amsa masa da vewar
gasu a cikin asibiti, Dan mutanen su Alhaji Mansur sun saka an tare matar
galadima a hanya itada Nuridden yayin kawo Camera Court.
Kasa magana mai martaba yayi, saboda jin
kuma wani sabon zaluncin, Wanda suka aikata baya baima ishesuba kenan.
Abba Hayatudden ma bai kuma cewa komaiba
saboda yasan ran yayan nasa ya 6aci.
Mama Fulani kanta yau cikin damuwa
take, bata ta6a tunanin mahaifinta zai iya aikata hakanba, dukda tsantsar son
datake da burin y'ay'anta suyi mulki bazataso duk'usar da Saifudden akan
hakanba, shekaru 26 bawan ALLAH Na kwance yana jiyya tamkar gawa, banbancinsa
da gawar fitar numfashi, wannan wane irin son zuciyane su jinin sarauta sukeyi?
Shikenan saboda sarauta sai aita halaka juna? “Ni Marawuyya wannan wane irin
burine mai cutar da imani.......”
Lallai zato zunubine koda ya zama gaskiya😢, kiyi hak'uri mama Fulani munata zarginki Ashe ba
haka bane🤔🤦🏻♀.
.............................★
A gidansu Munaya ma hankalinsu a matuk'ar
tashe yake, gasu Abdurraheem nata kuka, dan tunda Munaya tabar gidan suke kuka,
kukansu ya tada hankalin Munubiya dasu Inna sosai, lokacin da aka harbi Munaya
bak'aramar fad'uwa gaban Munubiya tayiba, ta mik'e a zabure tana dafe k'irji,
number Munaya tashiga nema, dan taji a jikinta wani mummunan abu ya faru da
y'ar uwarta.
Lokacin da labarin abinda ya faru da
Munayar ya iso garesu mafi yawan jama'ar gidan saida suka koka, Dady kuma ya
hana kowa zuwa asibitin, saisu mazan kawai sukai shirin zuwa, gashi basusan
wane asibitin bane.
__________
Iyalan su waziri hankalinsu a matuk'ar
tashe yake, hakama su Alhaji Sageer, ga duniya tanata ALLAH wadai dasu, gaba
d'aya yau kowacce kafar yad'a labarai da social media maganar kenan, su kansu
sauran manyan kowa ya shiga hankalinsa, dan lamarin yayi matuk'ar girgozasu,
suna yabama basirar Galadima matuk'a, gashi yabi ta hanyar da babu Wanda yata6a
zaton zata 6ille masa yayi nasara, inhar za'a iya samun irinsa a yau, to lallai
wataran za'a samo Wanda ya fisa ma.
....................★
Yanda masarautar su Galadima take a
harmutse gameda wannan lamari haka tasu papi ma ta gama harmutsewa, dan lamarin
ba'a cewa komai, cin amanar da waziransu sukayi yayi matuk'ar girgiza
masarautun, bakajin komai sai gutsiri tsomar bayi da dogarai, harma da manyan gidan
ba'a barsu a bayaba.
Tashin hankalin da papi da inno suke
ciki ba'a magana, ga Sauban ya tasasu gaba yanata kukan son zuwa yaga halin da
Munaya da Nuren suke ciki, harma da yayansa.
Dukda an hana fad'ama Su Momma amma saida labarin yakai musu, aranar aka
nemama Aunty Mimi ticket d'in tahowa Nigeria, Samha nata kuka itada Khaleel
zasu biyota, amma bata sauraresuba, dan hankalinta a matuk'ar tashe yake.
............................★
Doctor da kansa ya fito yayma Galadima
iso cikin office nashi, bayan sun zauna doctor ya kalli Galadima cikin alamun
damuwa, yace, “ranka ya dad'e da farko dai ina mai baka hak'uri akan zaluncinsu
mijin y'ar uwata, ALLAH yay maka babban samako da sayya agaresu”.
Murmuahi kawai Galadima yayi amma baice
komaiba.
Doctor ya kuma gyara zama yana fad'in
“Alhmdllh jikin namijin babu wata babbar matsala, yanzuma mun saka masa alurar
barcine cikin ruwan danya huta sosai yasamu nutsuwa, daya farka Normal zaku
gansa. Ita kuma akwai harbi da akai mata a hannu, amma Alhadullh mun samu
nasarar cire harsashin, tafin hannunta kuma shima anji mata ciwo, dan yatsunta
Na tsakkiyama duk sun samu karaya, amma shima an gyarashi, maganar gaskiya
ranka ya dad'e bazan 6oye makaba, tasamu buguwa akai, dan ALLAH ne ya tak'aita
batasamu wata babbar Matsala a brain ba, saidai ahalin yanzu dukkan wani motsi
mai k'arar sauti bama buk'atarsa kusa da ita, insha ALLAH inhar za'a kiyaye
cikin kwanaki kad'an komai zai iya dai-daita, takuma dawo normal kamarma komai
bai faruba, zamu bata dukkan kulawar daya dace da izinin Ubangiji. daganan har
kwanaki uku zuwa hud'u zata kasance a halin barci, dan hakanne kawai zai
girmama nutsuwar da muke buk'atar ta samu d'in, kai kad'aine kuma zaka ringa
shiga d'akin”.
Galadima ya lumshe idonsa tausayin Munaya
da yaransu Na kuma mamaye jinin jikinsa da kowanne ga6a, da k'yar ya iya bud'e
baki yace, “Doctor! Kana ganin zaku bata dukkan kulawa?. Sannan tanada yara
jinjirai, yaya kenan za'ayi?”.
Insha ALLAH ALLAH ranka ya dad'e, dan
munada kayan aiki a asibitin mu, dakuma kwararrun likitocin da zasu iya aiki a
kowacce k'asa, maganar yara inaga inhar akwai mai kulawa dasu acigaba da basu
madara har ALLAH yasa ta farfad'o, saboda mu yanzu matsalarmu kawai shine
motsin dazai iya farkar da ita ko wanda zaiyi tasiri cikin brain nata”.
Gyad'a kai kawai Galadima yayi, yabama
doctor hannu sukayi musabaha, daganan ya fito.
Kuma ficewa yayi daga cikin
asibitin, Sarkin mota yay saurin biyo bayansa, da hannu yamasa alamar yashiga
mota suje.
Dukda sarkin mota baisan inda suka nufaba
haka ya amsa cikin girmamawa.
Saida suka fara tafiya ya sanar masa inda
zasuje.
yana nufi gidansu Munaya dan yaga halin
da yaransa suke ciki.
Munubiya da kanta ta fito masa dasu
itada Ayusher, tausayin su ya kamashi matuk'a, musamman ma Munubiya, dan tayi
wujiga-wujiga.
Cikin k'arfin hali yace, “kiyi hak'uri
Sister, muyi musu addu'a ita kad'ai suke buk'ata a wajenmu, yanzu yaza'ayi dasu
Amaturrahman? Dan nakula kamarma yunwa sukeji?”. ‘yay maganar yana kallon yaran
da sukayi barcin wahala bayan sun gama shan kuka’.
Share hawaye Munubiya tayi. tace,
“Yakamata a nemo musu madara, idan kuma Na shayar dasu to shikenan”.
Galadima ya jinjina kansa yana fad'in
“Bamusan hikimar da ALLAH ya 6oyeba a gaba, karmuyi ganganci, bara kawai a nemo
madarar, dan dolene su kwana anan, ita ba'ason mata hayaniya yanzun, maybe ma
harnan da wasu kwanaki, saboda ta bugu a kanta, kuskuren kwakwkwaran motsi zai
iya shafar brain nata”.
Munubiya takuma fashewa da kukan
tausayin y'ar uwarta, hakama Ayusher, shi kansa Galadima dauriya kawai yakeyi,
danma ya 6oye idanunsa cikin eyeglasses shiyyasa basa ganin nasa tsantsar
damuwar.
Muftahu ya kira ya sanar masa a samoma su
Abdurraheem Madarar da zasu ringa sha.
Daga nan gidan yabaro akan cewar Muftahu
zai kawo, yakuma rok'esu akan Abdurraheem, dan ba'ason yacika yawan kuka.
A gurguje
please😏😜
_________
BAYAN KWANAKI UKU
A kwanaki ukunnan fad'ar tashin
hankalin da bayin ALLAH suke ciki 6ata lokacine, musamman ma Galadima da har
wata uwar rama yayi lokaci d'aya, hakama Munubiya da innarsu, Nuren dai ya
farka tun washe garin faruwar lamarin, kuma jikinsa Alhmdllh yanata murmurewa,
saidai tausayin d'an uwansa daya addabi ransa.
Ko abinci Galadima bayasonci, sai Aunty
Mimi ta turkesa tana bashi abaki, shima baifi yay lauma biyarba yace ya k'oshi.
tayi-tayi kuma ya kafe, garama idan tea ne, shima sai an had'a da lallashi,
babu abinda ke addabar ransa irin damuwar Munaya da yaransa, sukansu duksun
rame, danma suna samun tsantsar kulawane ta kowanne fanni.
Papi yazo ya dubasu, hakama su mom da
iyayen su Nuren d'in da y'an uwansa, mai martaba ma da daddare yazo cikin 6adda
kama ya dubasu.
Mama Fulani ma kullum saitazo, a matan
Sarki gimbiya Zulfah Ce kawai batazoba, Dan kunyama ta hanata walwala gaba
d'aya a masarautar, Mai martaba kuwa ya hanata hanyar ganinsa gaba d'aya itada
y'ay'anta, sai matawalle kawai daya nuna damuwa akan abinda kakansu da
mahaifiyarsu suka bada gudunmawa wajen aikatawa wan mahaifinsa, sanan yay ALLAH
wadai akan son zuciyarsu, koda yaushe yana tare da Galadima da Muftahu a
asibitin, da wata buk'ata ta taso kafin Galadima yayi shi yayita.
A koda yaushe Momma cikin kira take taji
yaya jikinsu Munaya, koda wasa ba'a sanarma Abie komaiba, Dan ana ganin cigaba
da haske game da jikinsa sosai, ba'a fatan wani abinda zai maido da hannun
agogo baya game da ciwon nasa.
Addu'oi kam sosai aka duk'ufa yinsu game
da Munaya, wadda har yanzu Galadima ne kawai keda alhakin shiga ya dubata,
shima sau d'aya a rana kawai, yau dai duk ake saka ran farkowarta, Dan an
dakata damata dukkan wata allura dake sakata barci, saidai kuma har dare babu
wani bayani.
Zasu tayar da hankalinsu doctor yace suyi
hak'uri, maybe zuwa dare ko safiyar gobe ta farka d'in, danba a sume takeba,
barcine kawai da sune suka sakata ta hanyar mata allurar.
Badan hankalin nasu ya kwantaba sukai
shirun, har lokacin barinsu asibitin yayi babu wani bayani game da farkawar
tata.
Washe gari.
Duk dai yanda akaso farkawar Munaya a ranar
sai a washe garine ALLAH ya amince da hakan, Alhmdllh anci nasarar farkawar
tata yanda ake buk'ata, saidai ciwukan jikinta a halin yanzu.
Saida doctors suka gama dukkan kai
kawonsu naganin komai ya ida daidaita sannan aka bama Galadima damar shiga.
Tamkar mai sand'a haka ya shiga d'akin,
tana kwance amma idonta biyu, sai dai a lumshe suke, an kuma cire mata bandejin
da aka zagaye mata fuska, sai kad'an aka bari inda ciwon yake.
Durk'usawa yay a gaban gadon, ya kamo
hannunta Na haggu dakeda lafiya ya saka nashi ciki, a hankali ta bud'e idanunta
saboda jin tattausan hannunsa cikin nata, ga k'amshin turarensa daya mamaye
d'akin Wanda ya tabbatar mata da shid'inne, tana shak'a a hankali.
Idonta ta saka cikin nasa, kowanne
yakasa koda kwakwkwaran motsi tsawon mintuna 2, a hankali Galadima ya bud'e
baki tamkar mai rad'a ko gudun wani ya jisu yace, “Munaayaa I love you, I
really love you, I love you more and more my Heartbeat..”
Lumshe idanu Munaya tayi, wasu hawaye
suka gangaro daga cikin idanu zuwa gefen kunnuwanta, zuciyarta sai wani irin
bugawa take da sauri-sauri, ta kuma damk'e hannunsa cikin nata tana maijin
tsigar jikinta Na tashi, jininta sai yamutsawa yake a kowanne 6angare. Kuma
bud'e idon tayi a kansa, suka sakarma juna lallausan murmushi ga hawaye Na zuba
a idonta har yanzu, shima kwalla sun tarar masa a cikin ido sun saka idon wani
k'yalli Na musamman daya kuma sakama munaya wata kasala da tsantsar k'aunarsa,
ya lumshe idanunsa alamar tabbatar da abinda ya fad'a mata har cikin ransane ba
iya fatar bakiba.
Itama hawayen ta kuma matsowa, ta bud'e
baki da k'yar tana cigaba da kwararo hawaye. Tace, “i love you too yalla6ai, I
love you so much...”. ‘takai k'arshen maganar wani kukan Na kwace mata.
Hannunta dake rik'e cikin nasa ya sumbata
yanamai jin farin ciki, yace, “ki kasance dani Munaya, ki kasance dani har
k'arshen rayuwata, ke Katanga tace, haskena ce, farinciki nace, duniyata ce,
duk duniya kece mace ta farko bayan mahaifiyata da y'ar uwata danakema so Na
musamman, please karki barni uwar y'ay'ana, karki gujeni komai rintsi, nima
namiki alk'awarin kasantuwar mu tare har k'arshen numfashi, ki rayu dani, ki
mutu dani bugun zuciyata, kamar yanda nima burina kenan a gareki tsawon
lokaci”.
Lallai yau daba'a halin ciwo takeba har
rawa sai tayi, Wanda bata ta6a tsammani ko tunanin zaisotaba shine yake furta
wad'annan dad'ad'an kalamin agareta, shine yake rok'onta ta kasance dashi har
k'arshen rayuwarsa?, shine yake kiranta katangarsa?, harskensa, bugun
zuciyarsa? Koda a yau tabar duniya ta ribantu da nasarorin masu yawan da
wahalar k'ididdiga wajen lissafi.
Galadima dake share mata hawaye da
hannayensa ya duk'a ya manna mata kiss a goshi da saman la66a.
Ta kuma bud'e idonta da suke jajur akansa,
murmushi suka kuma sakarma juna, ya girgiza mata kansa alamar tabar kukan,
idanunta ta lumshe alamar amsawa.
Shikam ya tsura mata idanu ko k'yaftawa
bayayi, y'ar ramar da tayi saiya k'ara mata k'yau da k'uruciya, ya shafa
k'ananun kitson dake kanta ta kuma bud'e ido tana kallonsa.
Cikin d'age gira d'aya yace, “baki
tambayi ina yaraba?”.
Lallausan murmushi ta kuma sakar masa, ta
kwanto hannunsa dake sark'e da nata saitin bakinta ta sumbata, sannan ta
d'orasa a saman k'irjinta.
Tausayinta ya kamashi sosai, domin jikinta
akwai zafi har yanzu, ga abincinsu sunyi matuk'ar cika, Wanda zazza6in nata
yanada nasaba da rashinsu gareta, dukda akwai Na zafin ciwo.
Hakan da tayi shima saiya fahimci mitake
nufi, kuma duk'owa yay ya sumbaci goshinta, zaiyi magana doctor ya shigo.
Shiru Galadima yay ya juyo yana kallonsa,
itama Munaya daga kwancen take kallon doctor ta k'asan ido.
Doctor dake gulma da zuciyarsa yana fad'in
lallai ya yarda, duk sarautar Sarki a gaban matarsa bawane, matarce ke zama sarauniya.....
(Ga naku Matan kwarai sarakin duniya👍🏻👌🏻😜)
Galadima ya katse tunaninsa ta hanyar buga
yatsunsa biyu suka bada sautin d'as-d'as.
Doctor ya dawo hayyacinsa a kunyace.
Yace, “sorry ranka ya dad'e, dama Nurse zata goge mata jikine da kuma gasa
mata, Dan tasamu sauk'in nauyin da yay mata”.
Murmusawa Galadima yay, ya zare
hannunsa daga cikin Na Munaya yana mik'ewa tsaye, hannayensa ya hard'e a k'irji
yana kallon doctor da fad'in “Doctor da raina zan bar wasu ganarmin sirrina? Ku
kawo kayan buk'ata kawai”.
Doctor daya fahimci Inda zancen Galadima
ya nufa saiya murmusa yana cewa “Afuwan ranka ya dad'e”.
Hannu kawai Galadima ya d'aga masa, ya
juyo suka had'a ido da Munaya ya d'aga mata gira da cizar lips d'insa.
Baki ta tunzuro masa tana yamutse fuska.
Ya d'aga kafad'a da ta6e baki alamar
bashida matsala🤷🏿♂🤣.
Nurses biyu suka shigo da dukkan abinda
ake buk'ata, Galadima Na tsaye ko kallon inda suke baiyiba, idonsa nakan
matarsa k'yam, sukam sai satar kallonsa sukeyi, suka ajiye suna fad'in “Gashi
Ranka ya dad'e”.
hannu kawai ya d'aga musu amma ko tari
baiyiba.
Fita saukai cikin takaici, dan sunso yayi
musu magana koda sau d'aya ne.
Takawa yay a hankali jikin k'ofar ya
Mirza key, sannan ya dawo yana cire link d'in hannun rigar farar shaddarsa da
tattarewa zuwa sama.
Suka had'a ido da Munaya tai azamar
janyewa cike da kunya.
Murmushin gefen baki yayi yana zama
bakin gadon kusa da k'ugumta.
Bottoms d'in jikin green d'in rigar
asibitin yafara cirewa a hankali, itadai kunya ta hanata bud'e ido, gashi ya
tsareta da idanu, Dan tanajin yanda idanunsa ke yawo cikin jininta, salon daya
koma wajen cire bottoms d'in ya sakata dafe hannunsa da hannun haggunta, ta
bud'e ido tana kwa6e fuska.
Gira ya d'aga mata, da wani mata salo da
kwayar ido.
Babu shiri ta maida idonta ta rufe ruf,
tsigar jikinta Na tashi.
A haka dai aka gama cire rigar, yaja
bedsheet d'in da ake lullu6a mata a k'afafu ya rufa mata a jiki, sannan ya kuma
gyara hannun rigarsa yana tsoma madaidaicin towel d'in cikin ruwan d'umin dake
a boket, ya matsa dukda akwai d'an zafi ruwan haka yafara danna mata jiki
dashi.
Tanajin zafi, amma kuma tanajin dad'in
d'umin ruwan sosai, k'in yarda tayi su had'a ido har aka gama, ya d'auki wani
d'an kwalba da mai ke ciki tamkar zaitun, karantawa yay yaga amfaninsa sannan
ya zuba a tafin hannunsa yana murzawa, kumajin tattausan hannunsa daya had'u da
sul6in mai tayi a k'afafunta, tad'an kuma bud'e ido tana kallonsa. Ganin ba ita
yake kalloba saita shagala da kallonsa, babban mutum mai daraja jinin mulki yau
shine ke mata hidima irin haka, itako badan kar ace tayi alfahari ba da cika
baki da yawa da tace ta more fiye da kowacce mace (🙄nidai fa bandani, reader's Ku kun
yarda harda Ku🤷🏻♀)?.
Sosai tafara jin dad'in tausar, Dan da
salon nutsuwa yake mata, tuni tafara lumshe idanu, hardai barcin yaci galaba a
kanta. Sai dai saukar numfashinta yaji a hankali.
Ya kalleta yana murmushi da lumshe idanu,
bai bartaba saida ya tabbatar barcin yayi nisa, cikin dabara ya canja mata
rigar da suka sakko a kayan domin canji. Ya duk'o ya sumbaci goshinta da
bakinta yanajan bedsheets d'in sosai ya kuma lullu6a mata.
Kayan ya maida gefe, ya koma saman
kujerar dake gefem gadon ya zauna ya zuba mata idanu, kai kace yaune ya fara
ganinta, ya dad'e a haka kafin ya d'auka wayarsa yana dannawa.
A haka Nurses d'in suka masa Knocking,
izinin shigowa yabasu, amma sai suka murd'a k'ofar a rufe.
K'aramin tsaki yaja yana muk'ewa, shi yama
manta ya rufe. Bud'ewa yay yadawo ya zauna yana d'ora k'afa d'aga kan d'aya da
kuma d'aure fuska.
Tuni Nurses d'in suka shiga hankalinsu,
cikin risinawa d'aya tamasa bayanin zasu canjama Munaya bandejin jikinta ne.
Batareda ya kallesuba yace, “kuyi a
hankali, Dan barci takeyi, idan kuma kunsan zata iya farkawa kubarsa saita
tashi ”.
Kallon juna suka, kowacce tad'an ta6e
baki, d'ayar tace, “insha ALLAHU bazata tashiba ranka ya dad'e”.
Nanma Kansa kawai ya jinjina musu yacigaba
da latsa wayarsa.
Haka sukai wannan aiki a gabansa Dan
yak'i fita, data motsa ya zuba musu uwar harara mai rikita hanjin ciki.
Dolensu suka bita a sannu har suka samu
kammalawa lafiya, kowacce ta fice a tsorace.............✍🏻
ALLAH ya
gafartama iyayenmu😭👏🏻
No comments