RAINA KAMA (BOOK 3) 15
💡HASKE WRITERS ASSO....
♦RAINA
KAMA...!!♦
(Kaga gayya)
Bilyn Abdull ce🤙🏻
__________
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya
Ubangijin Al'arshi kama mahaifin takwara (Bily s Fari) rahama, ka yalwata kabarinsa da Ni'ima, ALLAH ka yafe
masa, harda iyayenmu😭👏🏻.
Takwara ALLAH ya k'ara mana hak'urin
rashinsu, muma ALLAH yasa randa zaka d'auki ranmu muna cikin masu imani da
tsoronka, da soyayyay Manzonmu ANNABI MUHAMMADU S.A.W.😭😭👏🏻
__________
BOOK 3 👉🏻1⃣5⃣
.................Duk
da Munaya a rikice take haka tayi jarumtar danne zuciyarta, cikin hikima ta
dinga bin jama'ar gidan d'ai-d'ai tana tambayar wad'anda tasan Abba zai iya
kira kai tsaye, amma kowa yakance tun daren jiya basuyi wayaba, hankalinta a
tashe ta sulale gidan innaro ba'a saniba, itama dai tace tun bayan sallar asuba
bai sake kiranta ba. Munaya tafito jikinta sai rawa yake, kiran Galadima tayi,
lokacin yana waya, tamkar zata fasa kuka ta cire wayar daga kunnen ta, tana
niyyar sake kiranshi saigashi ya kirata.
Da sauri ta d'aga.
Yace, “yauwa Yayi waya da wani?”.
Muryarta na zuga alamar tahowar kuka
tace, “A'a, innaro kawai ya kira bayan sallar asubahi, amma yau koda su innarmu
baiyi wayaba”. ta k'are maganar hawaye na gangarowa a kumatunta.
Galadima ya furzar da huci daga can, a
hankali yace, “Munaya”.
Muryarta na zuga ta amsa tana share
hawayen da bakin hijjab.
Had'iye abinda ya tsaya masa a mak'oshi
yayi da k'yar, muryarsa takuma komawa can k'asan mak'oshi, cikin sigar
lallashin da Munaya bata ta6a sanin galadima ya iyaba yace, “insha ALLAH babu
abinda zai faru da Abba, kiyi mana addu'a, sanan karki sanarma kowa wani Abu
har inna, wayarki tazama kusa dake, Dan zan dunga kiranki idan buk'atar hakan
ta taso”.
Munaya takuma goge hawayen dasuka gaza
tsayawa, cikin had'iye kukan tace, “ALLAH yabaku nasara, ya tsareku da tsarewarsa”.
“Amin ngd”. Galadima ya fad'a yana yanke
wayar.
A bakin fanfo Munaya ta tsaya ta wanke
fuskarta, akuma lokacinne Zarah da Siyama suka shigo kusan lokaci d'aya.
d'agowa nayi Na kallesu ina k'ak'aro
murmushin da musu sannu da zuwa. Saidai ayanda suka amsamin cikin sanyin jiki
saina tsorata, nabaro bakin fanfon da hanzari zuwa garesu ina fad'in “Kai
lafiyarku kuwa?”.
Duk d'insu murmushi suka k'ak'alo,
Siyama tace, “babu komai fa sis...”.
Dukda ban yardaba haka nayi murmushi,
sannan Na kar6i yaransu duk biyu Na rik'e ina yaba Girman da sukayi, saikace
tagwaye.
Daga Siyama har Zarah basuce dani Uffanba
duk suka shige, kowa tanufi d'akin Uwarta. Duk binsu nayi da kallo, saida suka
shige Na sauke ajiyar ziciya nima Na nufi sashenmu Ina tunanin mike faruwa? Dan
alamu sun nuna akwai dai wani Abu a k'asa.
Saidai bankai ga Shiga d'akinmu ba mamansu
Yaa hameed ta tareni ta kar6i yarinyar Zarah. Ban musaba Na bata tundai ALLAH
yasa Nima Na Haifa balle ace, na shige falonmu da d'an Siyama nima.
Bayan Galadima sun gama waya da Munaya,
number da daddy ya turo masa ya duba, ganin wadda yake da itace saiya gwada
kira, switch up, ya ciza lips yana kallonsu Nuren da suma duk suka zuba masa
idanu.
Muftahu yace, “Ranka ya dad'e mu sanarda
y'an sanda mana?”.
Murmuahi takaici Galadima tayi, ya girgiza
kansa yana fad'in “Hakan zai 6ata aikinmu, duk indama yake a safiyar yaune suka
sameshi, akwai zoben dake hannunsa zamu iya bibiyarsa tanan, saidai matsalar
d'aya dole sai wayarsa Na aiki, gashi number sa kuma switch up”.
Nuren yace, “to mizai hana mu bincika
kozamu samu daga inda Number tabar aiki”.
Da sauri Galadima yace, “yes, yes Nuren,
shawara mai k'yau.....”
Shiru yay yakasa k'arasawa, saboda tuno da
matsalar da Computers nasu suke ciki kuma, ya dafe kansa.
Daga Muftahu har Nuren duksun fahimceshi,
zuwacan kuma miya tuna saiya mik'e da hanzari zuwa cikin d'akin, babu dad'ewa
yafito dawani k'aramin abu a hannunsa, lap-top yajawo ya manna a jiki, ya had'a
da waya ya Shiga sarrafata cike da kwarewa.
Zuwa can yad'ago yana kallon su Muftahu
da tura musu lap-top d'in gabansu, yana sanar dasu titin da wayarsa ta daina
aiki.
Cikin takaici yace, “Sunriga da sun tsara
komai, mubarma tunanin plan A, muje zuwa plan B kawai”.
Cikin mamaki duk suka kallesa alamar miye
plan B d'i?.
Lips d'insa yad'an ciza yana d'age gira
d'aya da buga yatsan saman bakinsa, Yace “maida hankalinmu a nemansa shine
target d'insu Na farko wajen janye ra'ayinmu, plan d'inmu mukuma anan shine
bazasu ta6a kasheshi ba inhar bai basu Camera d'inba, a yanda Na lura kuma
yanada taurin kai shima, bazai ta6a basuba ko fad'a musu inda take. Sunada
damar yin amfani da surukan senator halluru wajen turasu gida su nema musu
camera d'in, kodai ta hanyar musu barazana da mutuwa, kokuma akan aurensu, ko
kashe mahaifinsu, kodai wani Abu daban, shiyyasa dolene mumaida matsalarsa
cikin plan B d'in”.
Duksun gamsu, dukda sufa har yanzu yak'i
sanar musu miyake shiryawa a plan B d'in.
Cikin damuwa Nuren yace, “Amma nasan zasu
wahalar dashi”.
Galadima baice komaiba dan shikad'ai yasan
azabar da zuciyarsa kemasa, bayason ya nuna karayarsane saboda karsuma su Muftahu su karaya, sannan koda
sanyin jiki yanemi tasiri gareshi sai kalaman Munaya su masa allura, inhar
yarinya k'arama kamarta zata iya tasirantuwa da abinda ta fad'a, mizai hana
shima ya samu jarumta cikin tagomashin fik'irarta.
Mik'ewa yay tsaye yana tattara kayansa da
fad'in “Bara Na wuce, sai kunji yadda zata kaya kawai”.
Basu barshi yatafi shikad'aiba, saida sukai
masa rakkiya har masarauta, koda ya shige sashensa saiya kulle kansa, domin yin
shiri.
Hummm,🤸🏻♀shirya da k'yau Galadiman mu.
★★★★★★★★★★★
Abinda ya faru da Abba shine, bayan
yagama kammala shirinsa domin baro inda sukaje shida S... halluru daya jashi
domin masa rakkiyar tafiyar kwanaki biyu kacal.
Lafiya lau suka shiga mota zasu taho, amma
sai shi S... Halluru ya dakata da cewar Abba yayo gaba, shi anmasa kiran
gaggawa, bai kuma kamata ace ya tsaidashiba shi, tunda ya sanarma iyalansa yau
zai dawo.
Da farko Abba kamar zaice suzauna kawai
harya gama, saikuma tunanin yariga da ya sanarma su innaro zai dawo ya fad'o
masa, shiyyasa kawai yataho, basuyi wani nisa da tafiya ba driver ya tsaya wai
motar Na d'aukar zafi, ALLAH Sarki Abba, sai shima ya fita domin taimaka masa,
suna tsaka da duba motarne garadan samari hud'u suka fito daga ma6oyarsu sukai
ma Abba d'aukar amarya. Duk yanda yaso kare kansa ya gaza.
Driver da dama duk cikin shiri yayi haka
saiya hau tsallen k'arya cikin pretending yana ihun azo a taimakesu, (🤦🏻♀bayan
yasan baza'a samu kowaba a wajen tunda jejine☹).
Abba mutumne mai dagiya akan
ra'ayinsa, hakan yasa duk yanda sukaso yabasu had'inkai akan zancen Camera
yak'i, yama dage shi baisan Cameran da ake magana a kaiba, kuma dayaso basun
tun lokacin da ake bibiyarsa da dukiya mai tsoka daya bada, amma basuda kud'in
dayakai darajar camera d'in, sannan inda zai bada kodan barazana da rayuwarsa
da sukasa aikaitayi tunba yanzuba daya bada, amma yasan ruhinsa Na hannun Wanda
ya halicceshi, shine kuma mai kar6a aduk lokacin da yaso, inma sun kasheshi
dama kwanansa ya k'arene, Dan haka subar wahalar da Kansu kawaima.
Wannan maganar Ce ta fusatasu, wani ya
daki Abba a baki harya fashe, dukda yaji zafi saiyayi murmuahi kawai yana kauda
kai gefe.
Wanda sukasa yamusu aikin lalata
documents d'in Galadima Na cikin Computers ne ya ankarar dasu zoben hannun Abba
akwai wata kimiya a cikinsa, wannan ne ya sakasu cire zoben daga yatsansa, shi
Abba saima yanzune yasan manufar zoben, yay murmushi, Dan hakan ya tabbatar
masa cewar Galadima yasan wani Abu game dashi.
Duk yanda suka ringa k'ok'arin yima
Galadima mugunta a sirrinsa Na Computer Abba Na kallonsu, hankalinsa kuma a
tashe yake, amma jarumin namijineshi mai iya sarrafa kai aduk yanayin daya
kasance, ko'a fuska bai nuna musu yana tare da damuwar abinda sukeyinba, saida
Galadima ya kashe komai nasune Abba ya sauke 6oyayyar ajiyar zuciya, dukda
yasan hakan ba shine nasaraba.
Wanda suka saka aiki mai suna William
yashiga rud'anin abinda Galadima yayi, Dan da farko yanata cika baki babu wani
d'an African daya isa ja dashi a fannin ilimin Computer, bak'ak'en fatar ai a
wajen su suke koyan komai, ta Yaya kuma zasu fisu Sani?.
wad'annan kalamai nasa sun Sosa zuciyar
Abba da sakashi cikin takaici, shiyyasa yayta jerama Galadima addu'ar samun
nasara a zuciya.
Yayinda sukuma wad'anda akema aiki suke
kuma hurama William kai da kwanzartashi (ko kishin Kansu basayi😏, a zageku da kuma k'ask'antar daku kuna yabon mai
ganinku marasa daraja🤦🏻♀, wata dai bahaguwar rayuwa sai bak'in fata😏🙄.
Dak'ilesu da Galadima yayi ta hanyar
kashe komai ya fusatasu suda William d'in, suna kuma kunna Computers d'in komai
naciki ya goge, wannan Abu ya rikita William matuk'a, gashidai yagama proud
d'in shi kwarone kuma bak'in fata d'an Africa ya masa kwaf d'aya, dukkan
fushinsu saiya dawo kan Abba.
Ana cikin haka saiga Alhaji halluru
da sauran tawagar y'an group d'in, wad'anda sai yanzune suka samu k'arasowa, da
farko Abba ya zata Alhaji Halluru taimakonsa yazoyi, saida yaji suna masa
izgilanci sannan ya fahimci komai, cikin tsantsar mamaki yace, “Alhaji Halliru
da kanka?”.
Ta6e baki Alhaji Halluru yayi, yace,
“zaka bani takarar Governor ne?”.
Abba yay murmushin takaici yana fad'in
“Tir da kai Halluru, wannan ai jahilcine, ALLAH shikad'aine ke bada mulki ga
Wanda yaso, akuma lokacin dayaso,, yanzu kana nufin duk shekarun daka d'auka a
jikina kai dama da manufa kake tare dani?”.
Alhaji Halluru ya kuma ta6e baki yana
murmushin mugunta, yace, “Alhaji Auwal kenan, ai bama zaka tabbatar da hakanba
sai y'ay'anka da kansu sun d'akko min camera sun kawo, sannan mukuma kasheka a
gabansu babu yanda zasuyi, yanzu haka suna gida, zuwa anjima kad'an kuma camera
zatazo garemu”.
Zufa ta fara karyoma Abba a dukkan
sassan jikinsa, danjin za'ayi amfani da gudan jininsa wajen tarwatsa abinda yad'au
shekaru yana rik'ewa amana, k'ala baice da Alhaji Halluru ba, su kuma sai
kiraye-kirayen waya suke Na had'ama Galadima tarko.🤦🏻♀
Abba ba tausayin kansa yakejiba, tausayin
Galadima yakeji matuk'ar tik'ewa, Dan ganin rai kusan 15 kowa k'iyayyarsa
akansa take da muguntarsa...
★★★★★★★★★★
Tunda Galadima ya shigo bai zaunaba,
saida yagama had'a komai dazai buk'ata, yabama sarkin mota yakai cikin motar
dazaiyi amfani da ita, alwala yay yafita salla massalacin masarautar, bai yarda
sun had'u da Sarki ba, yay fitowarsa, koda ya dawo saiyasha magani ya kwanta,
kaikace bashida wata matsalane, babu dad'ewa kuwa barci yay gaba dashi.
Bai tashiba saida aka kira sallar
la'asar, nanma massalacin yaje, bayan ya dawo yay kiran Momma ta video call,
duk suna asibitin hardasu Samha, d'aya bayan d'aya ya gaisa da kowa, Samha
harda kukanta tanason zuwa Nigeria, ita missing nasu takeyi sosai. Galadima
yace a'a ba yanzu ba, tashi tai tabar gaban lap-top d'in tana kuka, Galadima ya
girgiza kai kawai.
Yasha hirarsa da Abie sosai, saboda
Alhamdullah jikinsa saidai godiyar ALLAH, dama ciwo keshiga farat d'aya, sauk'i
kam sai a hankaki. Addu'a kuma takobin muminice ako yaushe.
Bayan ya gama waya dasu Momma Sir Isa ya
kirashi, ya tabbatar masa da komaifa is done, Dan ansami kowanne acikinsu,
yanzu haka wasu sunma iso.
Galadima yay murmushi yana shafa fuskarsa.
Yace, “Nama canja shawara, zamu canja gidan da zamu ajiyesu da, yanzu akwai
wani gida annan kusada plaza d'ina, nagama magana da Saleem komai yayi ready,
Ameer duk yakaisu can, insha ALLAH ana idar da sallar Isha'i zan fito”.
Sir Isa yace, hakan yayi, dan acikin
yaran nasuma za'a iya samun munafukai, tunda duk sunsan gidan daza'a ajiyesun,
yanzu kuwa shi Ameer kad'ai zaisan da wannan.
Galadima ya kira Munaya, dama tun
d'azun kiran nashi take jira, ta d'aga tana shigewa cikin bayin d'akinsu Dan
kar wani yaji.
Galadima yace, “haryanzu kukan?”.
“a'a” ta fad'a cikin share hawaye.
Yad'an murmusa kawai yana fad'in, “Akwai
bak'in da sukazo gidanku?”.
“A'a babu Wanda yazo, sai Siyama da Zarah”.
Galadima yay murmushin gefen baki yana
cigaba da danna lap-top, hasashensa yazama gaskiya kenan, gyaran murya yad'anyi
kad'an yana fad'in, “kina jina?”.
Munaya tace, “eh”.
“Ki saka ido akan d'akin Abba, motsin
kowa yazama akan idonki koda cikin matansane, ko yayyenki maza, Dan za'a iya
yin amfani da kowa, inda da dama ma key d'in d'akin yazama a hannunki”.
Munaya tayi d'an jimm alamar tunani, zuwa
can tace, “babu damuwa, zan gwada hakan insha ALLAH, amma kunji labarin
Abban?”.
“Karki damu, insha ALLAH Abba zai dawo
gida, addu'a muke buk'ata”.
Munaya ta jinjina masa kai tamkar tana
ganinsa, ta share hawayenta dake zubowa.
Yana yanke wayar nafito, cikin dabara
nashiga d'akin innarmu, key d'in d'akin Abba Na d'akko, dukda nasan kowama yana
dashi cikin matansa, fitowa nayi naje cikin dabara da sauri-sauri Na saka key
d'in cikin k'ofa d'in, cikin addu'ar Neman nasarar kozai karye a ciki, amma ko
gezo baiyiba, hannuna sai azabar zogi yake, danma nayi amfani da wani abin
sarrafa k'arfene, cirewa nayi nakoma ciki kozan samo wani k'aramin k'arfe dazai
iya Shiga, saida nasha wahala nanma sosai kafin Na samo, gashi duk a tsorace
nake kar wani ya fahimci abinda nakeyi, cikin kafar makullin Na turashi,
Alhmdllh nasamu ya shige, nagwada saka key amma yak'i Shiga, nasan babu yanda
za'ayi wani key ya sake shiga wajen harsai mai gyara yazo, tunda kuma Abba
bayanan ai babu buk'atar hakan, Dan duk wanda zai buk'aci shiga yanzu lallai
akwai manufa. Dukda haka saida nasamo kwad'o nakuma sakawa sannan hankalina
yad'an kwanta.
**********
9:00pm
Fitowarsa kenan daga wanka baiko tsaya
shafa mai ba ya hau shiri cikin wandon da riga k'ananu, fuskarnan babu alamar
walwala tattare dashi, komai yana yinsane cikin karsashin fushi da damuwa, ya
kammala tsaf yad'an saka turare.
A k'ofar sashensa ya iske Nuren yana jiransa,
sauran Hadeemansa dabasuyi barciba suka shiga masa barka da fitowa, kansa kawai
ya d'aga musu, d'aya daga ciki ya bud'e masa bayan motar, amma sai bai shigaba ya d'aga masa hannu ya
bud'e gaba da kansa ya Shiga, Nuren yay murmushi kawai, yasan yau mazan a wuya
suke.
Shiga yay shima mazaunin driver yaja suka
fice.
Gidane matsakaici sabo, dagani ko
dad'ewa da gama gininsa ba'ayiba, saidai anzuba komai Na amfanin gida, ahaka
suke buk'atar badashi haya. Dan haka da saleem yanemi hayar suka bashi kai
tsaye.
Suna isowa Muftahu ma ya iso d'auke da su
Harun, Alhj Darma, Farhat d'iyar Minister sai mal. Saminu driver Alhaji balala,
kusan shima yana hannunsu har yanzun.
Ameer ya mik'e da Sauri yana salute d'in
Galadima, hararsa yayi, Ameer yay murmushi yana yin k'asa da kansa. Cikin
girmamawa yace, “Ranka ya dad'e wad'annan sune phones d'in yaran da tarkacen
kayamsu”.
Jinjina kai Galadima yayi, hannunsa duk
biyu goye a bayansa yana zagaya table d'in da aka zube wayoyi, da lap-tops,
iPad's dukna wad'anda aka kawo d'in, ya kalli Ameer cikeda k'asaitarnan tasa
yace, “Suna INA?”.
“Duk suna sama ranka ya dad'e, Dan inaga
yakamata kazauna acan, danka ke ganin motsin kowa daga waje, dukda ansaka cctv
a ko ina na wajen”.
Galadima ya kad'a kai alamar gamsuwa da
bayanin Ameer.
Cikin takunsa na izza da lafiya ya nufi
saman benen dake gidan, Muftahu da Nuren suka kalli Ameer cikin neman k'arin
bayani, murmushi yamusu, yana tattare wayoyin yabi bayan Galadima dasu.
A k'aramin falon k'asan ya iskeshi tsaye
yanabin komai da kallo, Ameer yace, “ranka ya dad'e yazamuyi da wad'annan
phones d'in nasu?”.
Galadima yad'an ciza lips yana kallon
Ameer, yace, “inasu Nuren d'in?”.
“Suna k'asa”.
Galadima
baice komaiba, hakan da yayi ya saka Ameer fahimta su shigo kenan, saiya ajiye
abin hannunsa ya sauka k'asan Dan kiransu.
Saleem yafito daga wani d'aki ya taso
k'eyar wani matashin Saurayi k'yak'yk'yawa, daka gansa kasan hutu yagama
ratsashi, kallo d'aya Galadima yamasa ya d'auke kansa, Saleem yaja kujerar
dining d'aya ya zaunar dashi, sannan yasaka igiyar daya d'auka ya d'auresa
jikin kujerar, saurayin sai zaginsa yakeyi, amma Saleem ko kulashi baiyiba,
saida yagama tsaf sannan ya kalli Galadima, wata alama yamasa da ido.
Sai kawai naga Saleem ya d'auke saurayi da
wani shegen mari, Wanda yasaka su Nuren dake shigowa jan birki suna kallon
Saleem, bakin saurayi bai mutuba, Dan haka Saleem yakuma zuba masa wani har
hancinsa Na fashewa, azaba ta sakashi kama bakinsa yay shiru yana huci da
had'iye hawaye.
Galadima ya ta6e baki yana d'age kafad'a.
Alamar sudai suka sani.
Haka Saleem yayta fiddosu d'aya bayan
d'aya harsu 7, maza 5 mata 2, sai Farhat cikon ta takwas, amma su matan babu
wacce aka d'aure, mazanma idan har bakayi gardama ba ba'a ta6asu.
Saleem yagama jerasu reras gaban Galadima
daya d'ora k'afa d'aya kan d'aya cikin kujera yana danna lap-top hankali
kwance.
Muftahu da Nuren dai sunyi mutuwar zaune,
basu ta6a tunanin Galadima zaibi wannan hanyarba, gashi yak'i basu wata fuska
dazasu masa magana ko tambaya.
Saleem da Ameer suka kamo Harun shima aka
d'aureshi a gefe ba cikin yaranba, shi baima cikin hayyacinsa, Dan su Nuren
saida suka shak'a masa Abu, Alhj Darma da m. Saminu ne kawai ba'a d'aureba,
suma dai aka kawosu gabansa aka zube.
Galadima ya d'ago yana kallon su Muftahu
dasuka Gaza barin kallonsa, cikin ta6e baki yace, “kallonfa?”.
Ajiyar zuciya suka saki a tare, Nuren
yace, “Brother mufa bamu fahimtaba”.
Lips yad'an ciza yana ta6e baki da fad'in
“Duk wannan dalla-dalla d'in da akai muku?”.
Shiru sukayi Dan inhar a fahimtarsuce
dai yau sunzama Kidnappers Na gaskiya kenan🤭😂.
Galadima yace, “Well, Ku ajiye zancen
fahimta gefe, kuduba phones d'in su Wanda babu charge a saka, Dan zuwa safiya
duk za a fara aiki dasu, daganan mai buk'atar barci yaje ya kwanta kawai,
sauran aiki sai safiyar gobe”.
Babu Wanda ya iya cewa komai, dan sunsan
dai Galadima bazai sakasu a had'ariba saboda son zuciya, Ameer ya fidda
Chargers suka saka dukkan wayoyi ajikin caji, Dan akwai wuta.
A wannan daren Galadima ya tura sak'o ga
dukkan iyayen yaran, lokacin duk sunbar wajen Abba sun koma gida, anbarsa da
garadan samarinnan akan sai washe gari, Dan sun tsarama su Zarah duk yanda
zasuyi.
Babbar magana, Alhaji Mansur habibu Uba yana
shirin kwanciya barci wayarsa tayi tsuwar shigowar sak'o, sharewa yayi, hakan
kuma saiya saka matarsa a zargi, tatashi zata d'auki wayar ya hana, saita kuma
tsarguwa, a zarginta wata shegiyarce ta turo masa, ganin ta fusata saiya bud'e
sak'on.
Babu shiri ya dirgo daga gadon a tsorace
yana tambayarta ina nerh-nerh take?.
Da mamaki race, “batace ta sanar maka
zataje wajen Rahma ta kwanaba?”.
A rikice yace, “Rahmar ubanwa, maza
kiramin ita yanzunnan su Abubakar suje su d'akkota”..
Bata fahimci inda ya dosaba, amma
rikicewarsa saiya sakata d'aukar waya ta kira nerh-nerh d'iyarsu, wayar na
Shiga amma ank'i d'agawa, cikin tsantsar tashin hankali ta sanar masa, ya daka
mata tsawa yana fad'i “ki kira Rahma d'in ko wani d'an gidansu mana!!”.
Maida akalar kiran tayi kan Rahma, itama
dai ank'i a d'aga, bataso kiran Hajiya yalwa ba, dan atunaninta kota kwanta,
amma dole ta kiratan.
Hajiya yalwa Na zaune kusada mijinta Alhaji
Abdul-Naseer Nafi'u kiran ya shigo, tayi mamakin Kiran, Dan hajia Marya bata
kiranta a irin wannan time d'in, saitayi tunanin ko takasa hak'urine da rashin
nerh-nerh abinka ga auta. Cikin raha tayi picking tana nunama mijinta wayar da
baki, yay y'ar dariyarsu ta manya yana kuma kishingid'a da zubama matar tashi
idanu.
Tambayar da Hajiya Marya tama hajiya
yalwa ce ta rikitata, ta mik'e zumbur tana fad'in “bara Na duba to, Dan wajen
3pm suncemin zasuje zaga gari, amma 7 zasu dawo gida, to wlhy bak'i mukayi suka
d'auke hankalina nikuma ban nemi ganinsuba, tunda ina tunanin sundawo suna
sashen Rahma”.
Duk kiranda Alhaji Abdul-Naseer kema hajiya
yalwa batajishiba, hakan ya sakashi biyota.
Kusan atare suka iso sashen Rahma d'iyarsu,
y'an aikinta guda biyu Na zaune a falonta sunata gyangyad'i, kai kace sashen
wata mai aurene ba budurwa y'ar 17years ba, Dan itace autarsu suma.
Hajiya yalwa ta dakama masu aikin tsawa
tana tambayarsu ina su Rahma?.
A rikice sukace suma dawowarta suke jira
tun d'azun (Dan sunsan inhar ta iske sunyi barci zasu yabama aya zak'inta,
maybe ma yazama sanadin barin aikinsu).
Alhaji Abdul-Naseer yana k'ok'arin gwada
kiran Rahma shima irin sak'on Alhaji Mansur ya shigo masa.
Ai sai suka kuma rikicewa, Ashe sak'o dukya
jema sauran abokansu, dan dannan suka Shiga kiran juna kowa yana tabbatarwa
d'an uwansa Galadima ya d'auke masa d'a ko y'a.
A wannan Daren suka sanarma police,
gidajennan 11 babu Wanda ya rintsa barci, dukda yaran 8 ne a hannun Galadima,
biyu basuda sauran yara a gabansu, duk sunyi aure, Galadima kuma yakafa musu
nasu tarkon ne daban, biyu kuma a ciki bamasu ta6a haihuwa ba, biyar sun mutu
yace bashida matsala da matacce, shi wannan saisunje babbar Court ALLAH zaimusu
nasu hisabin. Sauran yaransu irinsu Alh halliru kuma yace nasu mai sauk'ine
tunda manyansa suna hannunsa.
Tun a wannan daren manyan police suka
Shiga Neman ina Galadima yake, tunda kai tsaye yasaka sunansa a sak'on messages
d'in daya turama iyayen yaran.
Galadima yarigada ya tsara komai yanda ya
dace, duk wata waya dazata fita a wayarsu saiya ganta yakumayi recoding d'in
maganar, wannan yasa duk abinda suka fad'ama police yaji, murmushi kawai
yaytayi, yayinda su Nuren sudai hankalinsu bai wani kwantaba, dukda sunji
dad'in rikicewar da mak'iyar Galadima sukayi.
Abinka ga manya, tun a labaran 12am Na
daren ranar aka fara saka maganar, labari yafara shiga kunnuwan wad'anda basuyi
barciba.
Ciki kuwa harda y'an masarautar gagara
badau.
Hankalin mai martaba ya tashi, a Daren ya
aika jakadiya data rako matarsa turakarsa kiran Galadima, danya kira wayarsa
switch up.
Lokacin da jakadiya taje sark'in k'ofa ya
tabbatar mata Galadima ya fita tun farkon dare.
Komawa jakadiya tayi ta sanarma mai
martaba, aiko yakuma shiga tashin hankali, minene haka Sameer dayake kallo mai
nutsuwa da hankali ya aikata?.
Yana cikin wannan damuwa Waziri ya kirashi,
ya tabbatarmasa Sameer ya turo masa sak'o shima Harun yana hannunsa.
Zuface ta shiga jik'a mai martaba, yanzunan
duk jajen da akeyi Na 6atan Harun d'an waziri dama Sameer yasani amma yay
kunnen uwar shegu da kowa, hazbinallahu wa ni'imal wakil, shikam baya fata
wannan mummunan labarin yaje kunnen 'Dan uwansa dake kwance cikin halin
matsananciyar jiyya (kunsanfa har yanzu babu Wanda yasan samun sauk'i da Abie
yakeyi, bayan ahalinsa dasu papi) a gagara badau babu Wanda yasani.
Su Galadima duk suna ganin abinda ke
faruwa a TV suma, amma ko'a kwalar rigarsa, damuwa d'aya kecin ransa halinda
Abban Munaya ya tsinci kansa a ciki, amma sauran matsalolin dama dukya dad'e da
shirya abinsa, komi zai biyo baya dama zuciyarsa ta shirya d'auka.
Yau dai kam kusan a zaune suka kwana, abin
tausayi saiga Galadima da kwannan kujera, aiko yasha wahala, Dan tashi yayi
jikinsa Na matuk'ar masa ciwo, d'akin da aka saka masa kayansa yashiga, yasamu
yay wanka sannan yayo alwala sukayi salla a jam'i, Dan har yaran duk kwancesu
akayi, wad'anda kuma basayi suna zaune daga gefe.
Galadima yace Ameer yaje da y'ammatan su
had'a musu breakfast, cikin cika umarni yatasasu gaba suka fice, saidai kuma
Farhat ce kawai ta iya girkin a cikinsu, gashi tanada Asthma, bakomai take iya
sakewa wajen yiba, haka dai Ameer ya saka Nerh-nerh da Rahma suka taimaka mata
da Abu mai sauk'i, dayake a tsorace suke, komai aka saka su yi sukeyi, sunga
zuk'ek'iyar bindiga ahannun Ameer yo🤭😂.
Koda aka kawo abincin dukda tashin k'amshi
da yakeyi Galadima cayay bazai ciba, sudai su Muftahu kam ci sukayi, shikuwa
yak'are dacin cake da tea, Wanda dama da kayayyakinsa yazo caf (Galadima fa da
shirin zama yazo🤣
fans).
Tun'a daren jiya gidan da su Galadima suke
aka zagayeshi da y'an sanda, yasan kuma da hakan Dan CCTV Na nuna masa komai,
amma saiyayi tamkar baima San da zuwansuba.
Harun dai yak'i ci shima, hasalima sai
yankama Galadima magana yake, wai inhar ya isa shid'in shegene ya kwanceshi
mana, Ashe shid'in matsoracine ma, Dan ba'a sake d'aure kowaba bayan sunyi
salla saishi Harun d'in daya nemi yin gardamar k'in nutsuwa waje d'aya.
Ko inda yake Galadima bai kallaba.
Nuren yay gyaran murya, duk suka maida
attentions d'insu garesa. Yace, “inhar kun shirya bamu had'inkai kowa zai fita
a gidannan lafiya babu ko kwarzane a jikinsa, Dan bamuda matsala daku, da
iyayenku mukeyi, Wanda yaza6i kuma tafiya barzahu babu shiri saiya nuna
jarumtarsa ko rashin kunya, wannan wawanma ya isheku izna”. Yay maganar yana
nuna Harun daketa bige-bige yana kumfar baki masifa.
Duk suka amsa da zasu bada had'inkai.
Yau dai Darma kam shima yashiga
hankalinsa, Dan yaga lamarin yafi k'arfinsa.
Galadima ya d'auki k'aramar wata waya dake
kusa dashi yafara dannawa yana shan tea d'insa hankali kwance, yayinda k'afarsa
ke hard'e d'aya kan d'aya.
Munaya ya kira, wadda itama batayi isashen
barciba, gashi suna a yanayin rashin tsarki balle ta duk'ufa gayama ubangiji
itama, amma dukda hakan bata fasaba, zuwa dare kuma kowa ya ankara da rashin
dawowar Abba akwai matsala, dan around 7:30pm Baba k'arami ya dawo gida, babu
dad'ewa kuma saiga Dady shima, dawowarsu yasaka kowa Sanin mi ake ciki, innaro
ce kawai aka hana kowa ya sanar mata.
Babu Wanda yay barcin kwanciyar hankali a
gidan su Munaya, saidai yaran k'anana dabasu San dawan garinba, irinsu Inna ma
ai akan sallaya suka kwana suna gayama ALLAH kukansu😭.
Basuda wuta a daren jiya, shiyyasa basuga
abinda yake faruwaba, rashin kwanciyar hankali ya hana a kunna musu gen...,
Gasu Abdurraheem kwana sukayi kuka.🤦🏻♀
Cikin sanyin jiki Munaya ta d'aga
kiran, muryarta ta dushe saboda kuka, ahaka ta gaisheshi.
Ya amsa a sanyaye shima yana tambayar
yaranshi, tace, barci sukeyi.
Cikin lumshe ido yace, “karki damu daduk
abinda zaki gani, sannan karki kirani, dan duk kiran dazakiyi nasan baizama
lallai nikad'aine zan jishiba, zan dinga kiranki dakaina insha ALLAH. Please
take care of yourself”. Kitt ya yanke wayar batare da yajira cewarta ba.
Kanta ta cusa cikin k'afafu ta fashe da
kuka, yayinda Munubiya ma ke gefenta tana nata da shayar da Ameen daya tashi
barci.
Galadima kuwa yana yanke wayar ya mik'e
cikin takun izza da k'asaita ya k'arasa gaban Harun da bakinsa yakasa yin
shiru.
Izzarsa da k'asaitarsa Na burge matasan
samarin nan, hakan yasa duk suka bishi da idanu har y'ammatan, ga fuska a
cakud'e babu alamar yasan minenema dariya.
Gaban Harun ya tsaya hannayensa duka a
cikin aljihun wandonsa, babu Wanda yakula da lokacinda Galadima yaciro hannunsa
d'aya a aljihu, saidai k'arar mazgar Harun dayayi abaki sukaji kawai, kafin
Harun ya farfad'o Galadima yakuma k'ara masa ta d'ayan gefen.
Sannan ya d'an risuno yanama bakinsa
alamar zip da yatsunsa biyu🤐,
Harun yamasa shiru kenan🤣.
Kutt, gaskiyafa Harun ya mazgu babu k'arya🤭🤣.
Amma d'an bala'in naku bakinsa bai mutuba,
bayan ya farfad'o daga azabar dukan saiya cigaba da magana cikin haki da huci.
Sharesa Galadima yayi yakoma ya zauna dan
fuskantar abinda ke a gabansa, a fusace ya d'auki k'aramar bindigar daya fiddo
yanzu yafara Harbin inda Harun yake, ta saitin k'afafunsa. Rikicewa kowa yayi,
Harun yashiga mutsu-mutsu da k'afafu yanasan d'agewa Dan kar Harbin ya sameshi.
K'aramin d'an iska Ashe kanajin tsoron
mutuwa🤣?.
Wannan harbi ya kid'ima police d'in dake a
wajen gidan, akuma dai-dai lokacinne manyansu suna iso suma, kuma duk sunji
harbin.............✍🏻
Humm babbar magana, komiye shirin Galadima
Na zama kidnapper?.🤦🏻♀
Wane ahiri kuma su Zarah sukazo dashi
gida🙆🏽?.
Sannan wane shiri Galadima yake akan
ku6tar Abba? tunda yace plan B😔☹.
Ina baba mai kanwa? Wane taimako
zaibamu shima😭.
Kumuje zuwa
my guys karku k'osa dai, sannu-sannu bata hana zuwa, saidai a dad'e ba'a zoba😏🐢.
ALLAH ya
gafartama mahaifanmu😭👏🏻
No comments