RAINA KAMA (BOOK 2) 30 END
~Book 2~ 👉🏻3⃣0⃣
................Galadima
daskarewa yay a zaune, gaba d'aya magudanar jininsa tana neman Gaza aiki,
saboda jininsa a daskare yake, dai-dai da bugun zuciyarsa salon datake bugunta
da banne a yanzu, lallai masu kiran
mata masu k'arancin *TUNANI* a zahiri sune
masu k'arancin tunanin, lallai mata suna suka Tara, akwai mata akwai mata maza,
juye-juye yay tayi a gadon ya kasa ta6ukama kansa komai, barci ya k'auracema
idonsa, d'aya bayan d'aya Brain nasa ke markad'a maganganun Munaya dalla-dalla,
wani murmushi yasaki yayinda yakai hannunsa yana shafo kwantaccen sajensa zuwa
gemu, dukkanin bincikensa akan dai-dai yake, saidai rashin tsoron Munaya da
kaifin basirarta ya matuk'ar k'ayatar dashi, ya tashi zaune yana jawo laptop ya
kunna, saiga su Munaya sun bayyana a itada yara da Samha a kan gado, saidai
yanda ya lura ba barci takeba itama, Dan tana d'an girgiza k'afarta daga
kwancen. tsayin wasu mintuna ya kashe tareda mik'ewa ya d'auro alwala, abin
salla ya shimfid'a ya fara gabatar da nafila kamar yanda ya saba inhar yanada
lafiya.
********************
Yau likitocin Abie dasu Momma suna
cikin farin ciki, saboda k'afarsa ta dama sun wayi gari tana motsawa, bayan
gwaje-gwaje suna tabbatar da canjin da aka kuma samu a dukkan halittun
ga66ansa, yau daga shi har Momma harda kuka, tako rungumeshi cikin tsantsar
farin ciki da godiyar ALLAH, jakadiya sai fita tayi jiki na rawa.....
Galadima na tsaka da salla kira ya shigo
wayarsa, koda ya idar saiya share, har yana masifa a ransa wane ke kiransa a
wannan time d'in bayan yasan shi mai iyaline (🤣 kaga mai iyali😜👍🏻).
Ganin dai baza'a barsa yaji da abinda
ya damesa ba saiya d'auka a masife da nufin kashewa, kad'an ya rage ya aikata
hakan sai yaga Ashe Momma ce, mugun zaro idanu yayi, jikinsa na rawa
yay picking
video call d'in, Momma ce ta bayyana tana sharar kwalla, har taune harshe yake
wajen fad'in “Momma mike faruwa ne?”.
Ganin ya rikice saita hau dariya da share
kwalla tana masa bayani, ta matsa kusada Abie ta had'asu, yaukam dai Galadima
harda k'ananun hawaye yayi Dan dad'i, gashi yau yaji muryar Abie d'insa tafito
sosai ba laifi. Sunja lokaci suna waya, har kud'in wayar Momma ya k'are sannam
suka hak'ura, baibi kiranba yacigaba da mik'a godiyarsa ga ALLAH. ranar dai
zumbur akan abin sallah yayisa, sallar asubahi ma a d'aki yayi sannan ya samu
ya kwanta, barci mai nauyi kuwa ya kwashesa.
Da shirye-shirye Munaya ta tashi, dukkan
abinda zasu buk'ata tagama tanadar musu itada yara, Samha dai tayi tagumi
tamkar zatayi kuka.
Bayan anma yara wanka Munaya ma tayi
sai ta zauna yin break fast, suna d'an hira jefi-jefi da laraba dake ma y'an
uku shiri cikin wasu kayan sanyi masu laushi.
A kullum Munaya kan tsarkake sunan
Ubangiji idan ta kalli yaranta, takanyi mamakin anya kuwa daga jikinta suka
fito? idan ta tuna a yanda mahaifinsu ya Samar dasu takanyi murmushi da cizar
lips (copy copy😜😂).
Duk abinda takeyi laraba na lura da
ita, Munaya na birgeta sosai, Dan idan
tana wani abun takanyi tunani kodai Munaya jinin sarautace? Dan salonta da
takunta tana kamada na mashahuran y'ay'an sarakuna masu aji da Jan aji, cikin
hikima irin tasu ta manya tace, “Ranki ya dad'e ko Baban y'an uku yatashi? Naga
bakije dubashiba, gashi tun d'azun naga ankawo Karin kumallo, kuma since shima
sunkai NASA amma baya falo.
Munaya tad'an Sosa k'eya tana murmushi,
tace, “eh iya, ban saniba koya tashi, amma bara na lek'a na ganni”.
“yauwa ko kefa ranki ya dad'e”.
d'aukar k'aramin mayafi tai ta fita, sanye
take cikin sket da riga na wani yadi mai kama da boyal Orange color, an masa
kwalliyar surfani kad'an da stones da milk . Sai mayafinta siriri ya kasance
milk shima, tayi k'yau sosai gashi tasha d'aurin zarah buhari😜.
Tunda ta fito daga bedroom d'inta idon
Galadima a kanta, fitowarsa kenan daga wanka sanye da bathrobe da k'aramin
towel a hannu yana tsane ruwan kansa zuwa fuska da wuya, daina tsane ruwan yayi
yatsaya kallonta ta cikin Computer d'in, harta shigo falonsa, tad'anyi
kalle-kalle da lakatar center table d'in falon da d'an yatsa, da alama tana
duba ko da dattine, idonsa yad'an lumshe yana lasar lips, yabar gaban Computer
d'in zuwa ga mirror, zamansa babu dad'ewa tayi knocking k'ofar tare da sallama,
kamar bayaso ya amsa mata, ko kad'an bata wani jisaba, Dan haka ta harari k'ofar
sannan ta bud'e ta shigo.
Ko motsi baiyiba daga inda yake, saima
cigaba da shafa mansa dayayi, itama batareda ta kallesa ba ta wuce zuwa ga bed
d'insa tana fad'in “yalla6ai barka da asuba”.
Yanda tayi wani masifar basar dashi
saiya d'an waigo ya kalleta, sa6anin da da yake kallonta ta cikin mirror. Zanin
gadon ta cire hankalinta kwance, ta wuce ga wardrobe nashi ta d'akko wani tazo
tana k'ok'arin shinfid'awa.
Mik'ewa yay ya tako gareta.
Jinsa akwai nayi a kaina, amma ban
lura da sanda yabaro gaban mirror d'inba, k'amshin sabulun dayay wanka dashi da
man days shafa duksun addabi hancina, na d'ago gaba d'aya na ina gyara mayafina
domin ya rufemin k'irji da k'yau, saboda kayan babu laifi sun kamani, wajen
yakuma cika sakamakon shayarwa. Dab dani yake a she, koda na mik'e sainayi
kamar zan fad'a masa a jiki, nadai samu nad'an jaa baya ina tunzura baki, taku
d'aya yayi yakuma matsoni, na matsa nima, shima ya matso, hardai muka kai
k'arshen bango, kad'an ya rage na yandda Prime dake saman drowan gefen gadon,
Wanda hoton Y'an uku ne yasa akayi ya ajiyeshi a wajen, na kalla ina gyara masa
zama cikin d'an rankwafawa kad'an, hakkane yabama gyalen damar kuma zamewa,
batareda na luraba na tsaya sosai, nad'an 6ata fusaka ina fad'in “yalla6ai lafiya
kuwa?”.
Luuu yay da idanu saikuma ya bud'e a
kaina yana cizar lips, ganin ya tsurama waje d'aya ido a jikina saina kalli
wajen, baki na bud'e nakama gyalen zan rufe k'irjina da sauri ina tura baki.
Caraf ya rik'e hannun, zan saka d'ayanma
shima ya rik'esa, sosai na had'e fuska idona na tara kwalla, kuma matsoni yayi
sosai, ya rankwafo da kansa saitin k'irjina, rufe idona nayi ina k'ank'amesu
sosai saboda tsoron mizaiyine haka?.........
Bankai k'arshen tunanina ba naji saukar
iska a wajen, a hankali na bud'e idona, sainaga Ashe gyalen yake hurawa da
iskar bakinsa danya bud'e sosai, kunya ta kamani, dan rabin k'irjin duk abid'e
yake, wuyan rigar ya cika girma.
Wata muguwar girgiza nayi, had'eda shock a
lokaci d'aya, saboda saukar nutsatstsiyar Sumbata danaji a wajen, babu shiri na
maida idona na lumshe ina sauke ajiyar zuciya cikin shashsheka da nima bansan
nayiba.
Hakan ba k'aramin yamutsa jinin Galadima
yayiba, ya d'ago yana matsoni jikinsa sosai da maida hannuna duka baya ya rik'e
da hannu d'aya, na manne da jikinsa sosai. K'asa nayi da kaina saboda wata
matsananciyar kunya data ratsani da mamakinsa, murmushi ya saki, Wanda tundaga
zuciyarsa ya taho, Dan naji alamar hakan ta k'irjinsa, ya wani kuma maida
muryarsa very slowly cikeda k'asaita yace, “yalla6iya dama kinada lafiya
haka?”.
Bansan na d'ago kai da idoba na kallesa,
baki bud'e nace, “kamarya? Dama nace maka banida lafiya ne? ni kabarni nayi
aikina inada abunyi”. ta k'are maganar da kauda kai gefe tana tura baki.
Gira d'aya ya d'age sama, cikin ta6e baki
yasa yatsu biyu ya maido fuskata Inda take, yace, “kin tabbatar kinada
lafiya?”. Yay maganar yana d'aura
yatsansa kan la66ana da zagayasu a hankali.
Yanzunma tilas na lumshe ido, jikina harya
fara tauma, zuciyata kam sai fat-fat take tamkar zata faso k'irji ta fito.
Gangaro da yatsansa yafarayi daga saman
bakina zuwa wuyana har yazo k'irijina.
Bansan nafara kamo addu'a inayiba
azuciyata, gashi na kasa bud'e idanu, muryata na rawa nace, “please yalla6ai
k...ka...kabari”.. Uffan bai ceba,
idonsa akan fuskarta yana murmushi da taunar lips, kuma bai bar abinda yakeba
har saida ya dire saitin da zuciyata take, yace “ita wannan miyasata fargaba?”.
Bud'e ido nayi a hankali dan naga miyake
nufi? Na kallesa, ya nunamin k'irjina da ido, a d'arare na kalla inda yatsan
nasa yake, na had'iye wani yawu dak'yar ina fad'in “babu komaifa, kaga yara
zasu iya kuka ina nan fa”.
“Uhmyim” yafad'a yana d'auke yatsansa
daga saman k'irjina yana maidawa kan k'uguna, ya tura hannunsa cikin rigata
cikeda wani salo, hannuna nafara yunk'urin kwacewa, saiya tsaya kawai yana
kallona, saida nayi harna jigata kafin yayi wani munafikin murmushi, ya matso
da k'uguna da k'arfi ya had'e da jikinsa, saida naji zafi na yamutsa fuska da
cewa “Uhchhh! Yalla6ai ciwo”.
“Da gaske?”. ‘yay maganar cikin matso da
fuskarsa dab da tawa tamkar zai had'e bakinmu, idonsa cikin nawa yace, “kinsan
mizan baki?”.
Kaina Na girgiza masa kamar wata sokuwa.
Hannunsa Yakuma turawa cikin rigata har zuwa
gadon bayana, a hankali yace, “k'yauta”.
“K'yauta kuma? Tami to?”.
K'ala baice daniba ya juyani ta hanyar
murza k'uguna ya maidani saitin gadon yana lankwasani a hankali, yayinda
shikuma yake biyoni idonsa kan lips d'ina danake motsawa amma maganar ta gaza
fita.
Muna gab da kaiwa gadon ya saki hannayena
ya tallafe bayana da hannunsa, d'ayan kuma yana rik'e da k'uguna har
yanzun, ahaka muka fad'a saman gadon,
saidai bai sakemin nauyinsaba sosai, koda ya fad'o jikina banji zafi mai
tsananiba, yay min runfa da faffad'an k'irjinsa yana matso da face nashi daf da
tawa. cikin wata iriyar murya mai sanyi da k'asaita yace, “bud'e ido ki gani”.
Ban musaba na bud'esu, sai cikin mayun
nasa da har yau launinsu yakeda sirkin jaa, duk yanda naso fiddawa na kasa, dan
ya hanani wannan damar, saima wasu abubuwa danaga tamkar yana zubawa cikin
idona, batareda na fargaba na shagala nima nabar yunk'urin janye nawa. Munkai
tsawon mintuna a haka, saida ya tabbatar nagama zuwa hannunsa sannan ya d'ora
tattausan lips d'insa akan nawa ya fara sarrafasu cikin tsantsar nuna yana tare
da kewa da bege.
Ni munaya naga ta kaina, bansan ya
akayi galadima yaci galabar samun kainaba, lallai shid'in yanada wani baiwar
iya sarrafa mace a yanda yaso, ya mantar dake wacece ke balle daga ina kika
fito, yakan basar tamkarma baisan micece wata soyayya ba, duk kuma randa kikazo
hannunsa zaki tabbatar yacika namiji, Dan asalin jinin Malam bahaushen Na yawo
ajikinsa, dukda kasancewar wayayye kuma bai girma cikin k'abilarsa ba, yakan
maida hankali a harkokinsa, randa kuma soyayyar ta motso yabata muhimmanci Na
ban mamaki (Matan hausawa konayi k'ayya ba hakan mazan hausawa sukeba😂?) (Shiyyasa Muke cewa basu iya soyayya ba🤭🤣⛹🏻♀).
Sosai na shiga bashi dukkan goyon baya
harda saka hannayena na zagaye bayansa dasu...........
😨yaukuma su Oga Galadima an tina da sadaki😌🤭😂.
Tafiya tafara nisan da naji yana neman
sakin layi, a kasalance na rik'e hannunsa dake yawo a jikina, sannan na fara
k'ok'arin janye fuskata daya koma bama kisses tako ina, sai gwama numfaahi yake
yana sakin tagwayen ajiyar zuciya. ganin bazai bariba nasakar masa siririn
kuka, ina fad'in, “yalla6ai jegofa m....mu...mukeyi”.
Sai a lokacinne ya tsaya cak, amma
yak'i d'agani, juyo da fuskata nayi na kallesa, ya sake sark'e idonsa da nawa,
idanunsa sunkuma rinewa launin jaa sosai, wani murmushin takaici ya sakarmin,
cikin magana da k'yar yace, “kina kukane danna mori sadakina?”..
Wannan magana tasa tamun nauyi, Dan haka
na gagara bashi amsa, sai janye idona da nayi hawaye masu d'umi suka gangaro ta
gefen kunnena.
Gefena ya koma ya kwanta yana cizar lips
da lumshe ido, yayinda hannunsa ke shafa kaina saboda tuni d'an kwalin ya zame.
A haka yafara magana a hankali, “toke yanzu Yaya kenan? naga alamar auren
Contract yakusa k'arewa, gashi ko rabin sadakina ban Moraba, zaki dawomin da
kayanane ko yaya?”.
Kai wannan Bawa ya shahara a fagen
rainin wayo, nafad'a a zuciyata, a fili kuma sai nace, “nima sai'a biyani
d'aukar ciki da nak'uda, da shayarwa ai, tunda babusu a yarjejeniyar auren”.
Yanda nayi maganar ina yamutse fusaka da
murgud'a baki saiya shagala da kallon la66anta, hannu yasaka ya tallafo
fuskarta yajuyo da ita sosai inda tashi take, dukda idonta a rufe suke,
“kifad'i ko nawane sai a biyaki ai, nikuma ba kud'in Dana bayar nake buk'ata
ba”.
Na bud'e ido baki bud'e, “to mi kake
buk'ata? Naga kud'i ka bada kuma kud'i ya kamata a baka”.
Cikin ta6e baki yace, “farashina ya wuce
haka”.
Nina bakin na ta6e nace, “Niba arhar banza
bace”. Nayi maganar ina yunk'urawa da tashi zaune, da kallo ya bini, saida na
ziro k'afafuna k'asa sannan nakuma fad'in “mun gama sahirinmu”.
Shiru yamin tamkar bazai tankaba, harma
na juyo na kallesa, idonsa a rufe suke yayi filo da hannayensa, d'auke idona
nayi ina gyara rigata.
Yace, “zuwa ina kenan?”.
Nace, “gidanmu”.
Tashi yay ya sauka daga gadon duka yana
nufar wardrobe, saida ya bud'e yana kallon kayansa sannan yace, “mizai hana
kibari ki k'arasa aikinki kawai saiki tafi gaba d'aya”.
Na murmusa ina mik'ewa tsaye nima, na
koma jikin mirror na jingina ina hard'e hannayena a k'irji, idona akansa nace,
“aini nagama aikina, Dan nabaka dukkan sirrin dake raina”.
Yana ciro wasu bak'ak'en wando da Riga
yace, “zadai ki gamane yarinya, Abin cikin kwan bazasu gusa a kusa daniba”.
“Humm” nafad'a cikin takaici, nace, “mizai hana ka yanke dukkan alak'a,
Dan nima iyayena na buk'atar ganina a kusa dasu”.
Murmushi yayi yana juyowa hannunsa
d'auke da kayan daya za6o, kallo d'aya yamin ya janye ido, “mikikeci na baka na
zuba babie, indai an gama yak'in ai zata yanke”.
“nikuma bana buk'atar ganin k'arshen,
in ank'i cikin sauk'i zan bud'e komai kowa ya sani”.
Murmushi yay mai sauti, har fararen
hak'oransa na bayyana, ya kwance igiyar rigar wankar babu kunya ko shakkar
ganina, kauda idona nayi daga inda yake, yafara saka kayansa, cikeda izza yace,
“wace k'arfin gwiwa gareki na samun wannan damar?”.
“Court, tabbas zan maka ka a Court, sai a
kar6a min ai”.
“kinada abin dariya kwarai da gaske, a
mutum dubbunai dasuka shaida na biya sadaki sannan na d'auka, mutum d'ayane
yasan sirrin ba haka bane, bayan wannan hujjar kinada watane?”.
Dariya nayi irinta tsantsar rainin
hankali, harya d'ago daga d'aura belt d'in da yakeyi ya kalleni sannan ya
janye, zama nayi a stool mirror, na d'ora k'afa d'aya kan d'aya ina girgizawa,
“yalla6ai kenan, a tunaninka zaka iya cin bulus ne?”.
Murmushi kawai yayi bai sake tankawa ba,
Dan ya kula ciwon kai take Neman saka masa, ya zauna bakin gadon yana saka
sock's da takalmi, yayinda Munaya taketa cika da batsewar sharetan da yayi.
rigar jacket d'insa milk color ya d'ora bisa bak'ak'en kayan, komai nasa ya
kasance bak'i, jacket d'ince kawai milk, ya matsa gaban mirror kusada ita yana
gyara sajensa da fesa mayen turarensa. Saida ya gama dukkan uzirinsa kafin yazo
gabana ya tsaya hannayesa duka zube a cikin aljihu.
Dan k'yau yayi k'yau kam, amma saina kauda
kai gefe ina ta6e baki, irin bakayi d'innanba.
Shima bakin ya ta6e yana rankwafowa kaina
har inajin hucin numfaahinsa, “karki damu mai yabawar tana nan tafe lokaci
kusa, matar Sameer sarauniyarsa kinji yalla6iya”.
Cikin azama na mik'e, yay saurin ja da
baya, Dan daya tsaya saina buga masa kaina wlhy.
Hanyar fita na nufa ina fad'in “idan kana
buk'atar y'ay'anka zaka iya bina gidanmu ka kar6o abinka”.
Da kallo yabi bayanta kawai yana ta6e
baki, akan la66ansa yace “iya tsiwa”.
Agogonsa ya d'auka bak'i ya d'aura,
sannan yazuba wayoyinsa a aljihu tareda saka eyeglasses mai duhu a idonsa, ya
6oye tsananin jaa da sukayi, a falo ya iske tea a cup an had'a yanata turiri,
zama yay yana lumshe idanu, yakan rasa Munaya wace irin macece ita? So salon
nata akwai tsagwaron k'ayatarwa, Crossing k'afarsa yayi yana shan tea d'in a
hankali, yasha kusan rabin cup ya ajiye yana mik'ewa da kallon agogonsa yanajan
k'aramin tsaki.
sashen Munaya ya nufa, bayin daketa
gyare-gyare suka zube suna gaidashi, hannu ya d'aga musu kawai batare da yace
k'ala ba, cikin takunnan nasa na k'asaita da izza yake tafiya, bayinnan sai
satar kallonsa suke, da sallama ciki-ciki ya shigo d'aki, Laraba tai saurin
risinawa tana gaisheni, ya amsa batareda yako kalleta ba, ficewa tayi da
hanzarinta, Samha ma ta gaidashi.
Zama yay a bakin gadon idonsa akan
akwatina da Munaya ta had'a, ya janye ya maida kan yaran yana fad'in “ku shirya
gobe zaku koma?”.
Cikin d'oki Samha tace, “Uncle Sam harda
Aunty gimbiya?”..
Cire glasses d'insa yayi ya maka mata wani
kallon daya saka hanjin cikinta mitsawa, yace “tare kuka zone?”.
Da k'yar ta had'iye yawu tana girgiza masa
kai.
Da yatsa ya nuna mata k'ofar fita, jiki na
rawa ta ajiye Amaturrahman tafice tana tuttura baki da share kwallan shagwa6a.
Ya lumahe ido yana jan tsaki, Munaya dai
na zaune tana had'a wasu y'an kaya da suka rage a k'aramar bag, ko kallo basu
isheta ba.
Rankwafawa yay duk ya sumbaci kumatun
yaran, sannan ya kalleta fuska babu alamun yasan dariya yace, “wannan
kayanfa?”.
Duk da na tsorata da yanayinsa, hakan
bai hanani dakewa ba, cike da jan aji nace, “Na tafiya”.
Uffan baice daniba ya mik'e, kansa
tsaye ya nufi k'ofa, nikuma nabisa da kallo harya fice.
Wasu hawaye danake rik'ewa tun lokacin dana
baro d'akinsa suka samu damar zirarowa, hannu nasaka na sharesu ina zuge zip
d'in bag d'in.
Waya na d'auka na kira Momma, na
gaisheta cikeda ladabi, albishird'in cigaban jikin Abie da aka samu ta
sanarmin, tsantsar farinciki ya sake kamani, nace insha ALLAH su Samha ma zasu
taho da wasu magungunan. godiya tamin da sake sakamin albarka, ta tambayeni ya
mukayi dashi?.
Na sanar mata yace baza'a jemai ko ina da
yaraba.
Murmushi tayi mai sauti har ina jiyota.
“karki damu d'iyata. Da Kansa ma zai kaiku”.
Na amsa mata da to kawai, Dan banga alamar
Galadima zai tankwaru ta cikin sauk'iba akan tafiya wanka d'innan.
***********
Tunda ya fito hadimansa keta kwasar
gaisuwa damasa Yaya jiki, hannu kawai yake iya d'aga musu fuskarsa babu
walwala, sarkin mota da dogaran dakan bisa yayin fita suka taso da hanzarinsu,
bud'e masa mota akayi ya shiga.
Saida Sarkin Mota ya tada motar sannan
yace, “ranka ya dad'e ina muka nufa?”.
Banza ya masa kamar bazai tankaba, sai
zuwa can yad'an nisa yana bud'e ido, “mu fara Shiga wajen mai martaba”.
“Angama ranka ya dad'e”. Sarkin mota ya
fad'a cikeda girmamawa.
Bai fita a motarba, sarkin mota ne yafita
domin nema masa iso, amma sai jakadiya tace, “ai takawa tunda safe suka fita
shida su Masu da baraya.
Sarkin mota yazo ya sanarma Galadima,
baice komaiba sai kansa daya jinjina kawai.
Daga
nan basu zame ko inaba sai gidanda su Muftahu suka kai yarannan. Muftahu da
kansa ya bud'e musu k'ofa suka shiga, aka bud'ema Galadima ya fito, tafiya yake
a nutse cikeda k'asaitar masu mulki da tashen k'uruciya, Muftahu ya tako a
hanzarce garesa, hannu yabasa sukayi musabaha, sannan suka cigaba da tafiya
cikin gidan a jere, fuskarnan babu walwala yace, “ya kuke ciki dasu?”..
Muftahu yad'an nisa yana bud'e masa
k'ofar shiga falon dansun k'araso, “Ranka ya dad'e bamu tambayesu komaiba, Dan
wannan ba Hurumin mu baneba ai”.
Galadima baice komaiba, ya zauna kujera
mai zaman mutum d'aga yana d'ora k'afa d'aya kan d'aya.
Muftahu bai zauna ba saida ya d'akko glass
cup da kwalin Hollandia ya ajiye gaban Galadima.
Galadima dake danna waya yad'an d'ago ido
ya kallesa ta cikin glasses, kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru ya maida
kansa ga wayar.
Girgiza kai kawai Muftahu yayi, Dan yasan
magana yakesonyi amma yaza6i yayi shiru daya bud'e bakin. yana tausayama Munaya
wlhy, “Ranka ya dad'e su zone?”. dan yasan bai wuce abinda yake son cewa
kenanba.
Ilai kuwa sai Galadima ya jinjina kai
yana nuna yatsansa d'aya alamar mutum 1 yakeso.
Nanma dai Muftahu kan ya girgiza kawai
sannan ya mik'e. Mintuna uku kacal saigashi da mutum d'aya a cikinsu. har yanzu
kuma idon Galadima nakan phone nashi.
Saurayi da bazai wuce shekaru 30 zuwa
sama a duniya ya durk'usa gaban Galadima kamar yanda Muftahu ya umarcesa,
kwarjinin Galadima da cikar haibarsa da tsare gida duksun rikita gayen, bakinsa
na rawa yace, “barka da safiya ranka ya dad'e”.
K'ala baice dashiba, kusan mintuna
biyu ya ajiye wayar yamasa kallon tsaf sannan ya janye idonsa, kansa ya jingina
da kujera ya lumshe idanu, hannayensa duk suna bisa hannun kujerar, cikin
maganar nan tasa mai kama da anmasa dole yace, “wanene kai? miya kaika
gangancin shiga hurumina?”.
Ba k'aramin tsuma da birkita muryar
Galadima ta saka guy d'inba, haka kawai sautin muryar Galadima dabata da r a
cikin kalami ya rikita guy d'in, murya na rawa yace, “Ranka ya dad'e sunana
Shazali, kuma wlhy bansan komaiba, nidai kawai anzo an bamu aikine”.
Halbi Muftahu yakai masa yana fad'in
“k'arya kakeyi”.
“Wlhy da gaske nakeyi”. Shazali yafad'a
cikin mak'yark'yata.
d'agowa Galadima yayi zaune sosai, yace,
“kozan iya sanin wanene yabaku aikin?”.
“Bansan sunanta ba Ranka ya dad'e, amma
zan iya ganeta”.
Kallon Muftahu Galadima yayi, Muftahu
daya san abinda yake nufi ya jawo laptop yana ajiyewa gaban Galadima.
Zama ya gyara, cikin kwarewa yafara
sarrafa System d'in yana cizar lips kad'an-kad'an, wannan salo na yarima yana
burge Shazali, aransa yana jinjina mulki mai dad'i kenan, haka kawai k'aunar
Galadima ta shigesa, kuma yayi alk'awarin taimakonsa cikin sauk'i insha
ALLAH.......
Tunaninsa ya katse lokacin da Galadima ya
turo masa laptop d'in.
Kallonsa yad'anyi Dan baisan mizaiyi da
itaba. d'auke kai Galadima yayi alamar bazai yi magana ba.
Muftahu yace, “ka duba idan akwaita
anan”.
Laptop d'in Shazali ya ida jawowa gabansa,
hotunane suka bayyana da yawa. Muftahu yamatso yana masa zooming nasu one by
one.
Nuren yafito daga wani d'aki yana
mik'a, da mamaki yake kallon Galadima dashima shi yake kallo, “brother kaine?”.
Kai Galadima ya girgiza masa alamar a'a.
Nuren ya murmusa yana tahowa cikin
falon, hannu yabama Galadima sukayi musabaha, yana tambayarsa yaya jiki?.
Akan la66a ya amsa da “Alhmdllh”.
Nuren yace, “ina yarana?”.
Da hannu yamasa nuni da lfy.
Kular da Nuren yayi yau k'asaitar a kusa
take saiya barsa ya mik'e, Coffee ya had'o yadawo ya zauna yana kallon abinda
su Muftahu sukeji.
Shikam Galadima yayi shiru yana tunano
yanayinsu da Munaya na d'azun, yana da buk'ata mai tsanani, saidai yakan danne
saboda jarumta, musamman idan ya tuna matsayin auren nasu, ko a baya saboda
yanayin data shigane ya sakashi yin yadda yaso da ita, Dan hak'k'insa ne ya
taimaketa a lokacin kodan buk'atar tazame mata lalurar cikinsa, yanzu kam
dolene yanemo mafita ko matar aur..........
Tunaninsa ya katse lokacin da Shazali ke
fad'in “itace wannan yalla6ai”.
Daga Muftahu har Nuren kallon picture
d'in suka tsaya yi, sannan duk suka kalli Galadima da shima idonsa ke Kansu.
Nuren ya d'auki laptop d'in ya mik'a
masa, shiru Galadima yay yana kallon hoton, Matar Abie ce ta biyu, wadda yata6a
gani a wayar Harun, yay wani miskilin murmushi yana yana kallon Shazali,
saikuma ya janye idonsa batare da yace uffanba.
Shazali ya gyara zama yana fad'in “bayan
ita kuma sai aka had'amu da wannan matan daga masarauta, sukuma sunce Uwar
gidan sarkice ta sakasu”.
Nuren yace, “uwargidan Sarki kuma? to
tayaya tasan kud'in ga abinda zakuyi?”.
“wlhy ban saniba nima ranka ya dad'e,
abinda na Sani kawai a ranar wlimar kafin mu shigo hall d'in aka taremu a
hanya, shine wani dogari ya shigo
motarmu, da farko mun taso masa harda fiddo wuk'ak'e, saishi kuma ya nuna mana
bindiga, hakanne ya sakamu nutsuwa, yace, yasan abinda zamujeyi ai, dan haka
idan munason mu tsira da ranmu mu sauraresa da k'yau, shima aiki zai bamu. Zai
had'amu da bayi biyu mata dazasu taimakemu mu sace yaran, bayan mun gama akwai
kaso mai tsoka, sannan zai fad'a mana wani sirri, mahaifin yaran yayi shirin
canjasu da y'ay'an babyn roba dan haka karmu sake mu d'auki yaran da za'a bama
wasu yara, mu d'auki na cikin gado daza'a sakasu a wajen taron, sune zasu zamo
na gaskiya, mak'udan kud'in daya bamune suka samu amincewa da gaggawa, Yakuma
sanar mana aikin uwargidan sarkine, idan har mukayi kuskuren wani yasani dagamu
har ahalinmu sai sun shafe labarinmu a doron k'asa”.
Daga Muftahu har Nuren kallon Galadima
suke da mamakin Brain nashi, hakan suka shirya, amma daga baya sai sukaga ya
canja yabada yaran da gaske, sunyi mamaki sosai, amma bai basu fuskar
tambayarsa ba a time d'in.
Yay musu alamar miye suke wani
kallonsa.
Salute d'insa sukayi su duka, ya kauda
kansa kawai yana ta6e baki.
Sun kuma tabbatar da akwai sirrika da
yawa da Galadima ya Sani, akwai yana basarwane saboda jiran lokaci.
Da hannu yamasu Nunin Shazali yatashi yaje.
Bayan tafiyar Shazali ya kallesu yana
sauke ajiyar zuciya da gyara zamansa, ya d'auki kwalin hollandia yazuba a cup,
Muftahu da Nuren dai na kallonsa, saida yafara sha da kallon agogon hannunsa
sannan yace, “Zanje India gobe idan ALLAH ya kaimu, akwai ayyukan dazan tattara
na kwanaki uku, sannan na d'auki Hutu a wajen aiki, dukda muna shirye-shiryen
fidda kaya na shekara mai zuwa, a Daren yau Harun zaisan matsayinsa, Dan tuni
nagama da matsalarsa dama, wannan ranar nake jira, so Nuren ka bincikamin inda
matarnan take zaune a yanzu, Dan ina dawowa zan shiga aikine sosai, matsalar
Harun da ita da Sarauniya kowanne akwai manufa, su nasu wasan yarane a wajena.
Erfan shine yajema Munaya a matsayin Fu'aad, yanzu na fahimci sune suka saka
aka buga waccan jaridar, amma da saka hannun wasu a gefe........”
Muftahu yay saurin cewa “yi hak'uri
ranka ya dad'e zan katseka, sai yanzu wani Abu yazomin a rai, wato ranar salla
a filin idi, kasan Erfaan yana tare damu, anya kuwa ba a wannan time d'in ya
ganku kaida gimbiya ba, lokacin da kukayi karo, wata k'il shikuma yayi tunanin
alak'a Ce a tsakaninku?”.
Murmushi Galadima yayi yana lumshe ido,
“ni kaina ina tunanin haka, saidai akwai wani Abu bayan wanna, dan haka
sarakuna uku sun shigo cikin aikina”.
Da mamaki Muftahu da Nuren sukace
sarakuna kuma?.
K'ala baice da suba ya mik'e tsaye, ya
kalli agogon dake tsintsiyar hannunsa sannan ya kallesu, “gobe da safe Alhaji
Shehu Darma zaije taron k'arama juna sani a jihar Katsina, lallai bana buk'atar
yama k'arasa”.
Kusan a tare sukace Alhaji Shehu Darma
kuma?.
Ficewarsa yayi batareda yabasu amsaba
balle su sami k'arin bayani. baki bud'e Nuren da Muftahu suka kalli juna,
Muftahu yace, “shikuma miye nasa to?”.
Cikin jimami Nuren yace, “nima abinda
nake son Sani kenan, mutumin da tunda mijin aunty Mimi ya rasu yake fad'i tashi
a kanta da yaranta, danma tak'i amincewa ne da aurenta zaiyi, anya kuwa shi
yake nufi kodai wanine mai irin sunansa?”.
Jiki a sanyaye Muftahu ya yarfar da
hannu alamar bai saniba shima. danshi lamarin Galadima yafara bashi tsoro,
mutum kamar wani tsohon aljani.
Shikam koda yabar wajensu wani office yace
Sarkin mota ya kaisa, yakai tsawon lokacin a wajen tareda wani mutum dabazai
gaza shekaru 56 ba a duniya, bansan mi suka tattauna ba, dan ba'a bani damar
jinba.
A wajen yay sallar azhur har la'asar
sannan yayo masa rakkiya wajen Motocinsa, saida yaga fitarsu sannan yakoma Office
d'in.
Daga nan masarauta suka nufa, dan Galadima
a matuk'ar gajiye yake,
Ya iske sashensa fes an gyara, ko ina
yana tashin k'amshi tamkar yadda yake buk'ata, kayansa yacire ya watso ruwa,
bai nemi kowa baya ya zauna a falo yana aiki a System, dukda yaga abincin da
aka ajiye masa baiko bud'eba balle tunanin cinsa, Yakuma san Aunty Mimi ce zata
saka a kawo.
Yana tsaka da aikin Sauban ya shigo, bai
kallesaba koda ya gaidashi, yadai Amsa.
Sauban yace, “yaa Sam tafiyar safe zamuyine
goben?”..
Ido Galadima yad'an d'ago ya kallesa,
ya maida kansa ga laptop d'in yana fad'in, “Kwana 3 zamuyi ni da kai mu dawo,
komanka na gameda bautar k'asa yagama kammaluwa”.
Kamar Sauban zai sanya kuka yace, “Amma
Yaa Sam su Momma sai abarsu babu kowa?”.
“kafin ka girma dawa suke zaune?, Sauban
ka kiyayeni, karka bari na fusata akanka, tashi bani waje”.
Sauban ya mik'e zuciyarsa na zafi, harzai
fita Galadima yace, “zonan”.
Dawowa yay yana mirgina kai, batareda
Galadima ya kallesa ba yace, kar6a wannan, kaje ka sakashi jikin rigar
Abdurrahman ko Amaturrahman ka d'auki Wanda ka samawa d'in kaje sashen Ummu
Amaan (gimbiya Zulfa) dashi”.
Sauban baice komaiba ya kar6a abinda
yabashi mai kama da ma6alli ya fita, ya iske Munaya na barci, yaran kuma na
tare da Khaleel dake ta fama jagwalgwalasu, Abdurrahman ya d'auka ya sakamawa
ya nad'eshi a showal ya fita......
Nikam wannan gangancin na Galadima ya
isheni😨🙆🏽.
Bansake jin miya faruba dan banbi Sauban
ba nikam, ina tsoron ganin abinda zai hanani barci😌.
__________________________
Misalin 8:30 na dare Galadima ke shiri
bayan ya dawo daga sallar isha'i, yagama tsaf cikin k'ananun kaya da jacket
d'insa wadda takai masa har gwiwa, ya saka safa har a hannunsa, cikin takunnan
nasa na gwarzantaka ya fito, sashen Munaya ya nufa, sukaci karo a k'ofar d'aki
zata fito a rikice, sauri tareta yayi ta fad'o jikinsa saboda kad'an yarage ta
fad'i, k'amshin turarensa ya sakata shaida shine, ta share hawayenta tana
kallonsa a rikice, shima kallonta yakeyi, Muryarta na rawa saboda kuka tace,
“yalla6ai Abdurrahman sai kuka yakeyi, jikinsa ya d'auki zafi”.
Baice komaiba ya kama hannunta suka koma
cikin d'akin, laraba da aunty Mimi na zaune, aunty Mimi tana zarema Abdurrahman
kayan jikinsa za'a watsa masa ruwan d'umi kozaiyi shiru.
Zama yayi ya kar6e sa daga hannun Aunty
mimi, ya fiddo wani kwali k'arami daga aljihun jacket d'insa ya bud'e, k'aramar
kwalbar dake cikeda magani ya fiddo, ya d'iba maganin cikin tsinken da ake bama
yara magani ya zubama yaran a bak'i, dak'yar ya shanyeshi.
Sudai sunyi jugum-jugum suna kallonsa.
Yunk'urin amai da yaron keyi yasaka
Galadima d'agashi daga jikinsa dan kar yay masa, baimayi amanba, hakanne yasaka
Galadima sauke ajiyar zuciya ya mannashi da k'irjinsa yana hura cikin kunnen
yaron a hankali.
Tun yana kukan kad'an-kad'an ya koma
ajiyar zuciya, sai gashi yayi barci. Kwantar dashi yayi kusada y'an uwansa ya
lullu6esa.
Ya kalli aunty Mimi yana mik'ewa, “insha
ALLAH zai sauka zaza6in”..
Yanda Aunty Mimi kebinsa da kallon
tuhuma saiya janye idonsa yakama hanyar fita, da sauri tamik'e tabi bayansa a
fusace. Dan Sauban ya sanar mata Galadima ya sashi kai yaron sashen mai martaba
d'azun.
“Dakata Sameer”.
Cak ya tsaya yanajan hular rigar bisa
kansa, amma bai juyoba.
“Sameer wai mike damun kankane haka? da
zaka ringa wasa da rayuwar yaranka da kanka?”.
Lips d'insa ya ciza, ya juyo yana
kallonta, amma ita bata ganin idanunsa saboda hular ta rufe, murmushin takaici
yayi, yace, “Ni ba wasa da rayuwarsu nakeba aunty Mimi, komai kikaga nayi nasan
abinda nakeyi, zuwa nangaba kad'an kuma zaku fahimci komai”.
“ALLAH yasa to, amma ni yanzu na zone
muyi maganar komawar Munaya gida kafin mu wuce goben, tunda jirgin rana
zamubi”.
Agogon hannunsa ya kalla, yace, “yanzu
kam inada uzirin fita?”.
“fita? Inakuma zakaje a wannan daren?”.
Batareda ya tanka mataba yajuya yakama
hanyar fita, saida yaje bakin k'ofa sannan yace, “Farauta”. yay ficewarsa.
Kasa motsi aunty Mimi tayi a wajen, sai
maimaita Sunan Galadima kawai takeyi akan la66anta.
******
Tacan baya yabi shikam, hanyar akwai
k'arancin mutane sosai, yana zuwa ta wani waje yagamu da wani Wanda ke sanye da
irin kayan hadiman masarautar, rissinawa yay yabashi keys d'in mota. ya kar6a
batareda sunma juna maganaba ya wuce.
Can sashen su Harun naga ya nufa, dukda
tazarar dake tsakaninsu baiji tafiyarba, motar dake fake a wajen ya bud'e ya
shiga ya zauna, zamansa da mintuna uku Harun yafito ad'an hanzarce, motar
yabud'e seat d'in baya ya shiga ya zauna, cikin bada Umarni yace, lawandi muje,
kasan d'an bala'innan yanada securitys dake kaimasa rahoto”.
Murmuahin gefen baki Galadima yayi yatada
motar yafice daga masarautar................✍🏻
“Hummmm!
Reader's harna sauke numfashi, babbar magana, yau dai ga Galadima ga Harun,
sauran abinda zai faru kuma sai a buk 3 na raina kama”.
Miya faru da Abdurrahman lokacin da Sauban
ya kaisa sashen gimbiya zulfah ne🤔? Yaya batun kama SD?, wad'anne sarakuna ne Galadima yake
zargi? Kodai dama can Galadima yasan wanene Harun yabashi damane kawai?🤔, Yaya batun warkewar Abie da Auren
Contract tsakanin Galadima da Munaya?, mi suke shiryawa itada Momma da suka damu
da zuwanta wankan gida? Ko Galadima zai amince?”.
Yaya batun gano asalin innarsu Munaya? Da
ita Munayar ta d'auki alwashi?.
Tofa wannan amsar dai duk zatazo a littafi na
3 kuma na k'arshe da izinin ubangiji, dukkan wasu tambayoyinku amsarku na cikinsa, zan had'a muku da albishirin zan dingayi a
weekend rana 1, kodai asabar ko lahadi, kowacce rana nasamu dama aciki, dan buk
3 inason kammalashi ne a gaggauce saboda uzirin danake dashi insha ALLAH.
Ngd sosai da had'in kan da kuke bani, muje
zuwa my guys⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀🥰🥰🥰🥰🥰🥰😍😍😍😍😍😍❤❤❤.
Barkanku da
juma'a🙋🏻.
Musha weekend lafiya⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀
*_ALLAH ya
gafartama iyayenmu_*😭🙏🏼
No comments