RAINA KAMA (BOOK 2) 20&21
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
_jinjinar gaisuwa a gareku da fatan
alkairi, Bilyn Abdull ta gaisheku, gaisuwa irin ta musamman d'innan my lovely
sister's🥰🥰🥰🥰🥰🤝🏻_
*_Aysha
Manshart (Ummu zunnur😍), Hafsa abdulaziz, mmn fukaihat,
Hannah A Ali, marnona, Mmn Al'ameen, Sumee waziri, Ummu walid, Yar tulluwa,
Khadija Aliyu Sa'id, Umm Abdul, Umm Yusuf, Mrs Ahmad, zubby abdullahi, Hajara
Ismail shatu, Ummu barakat, maryam haruna, Ummu sulaym, Ummu Ahmad, Haizarana
halliru._*
I love you mazga-mazga😂🤸🏻♀
____________________________
~Book 2~ 👉🏻2⃣0⃣➖2⃣1⃣
................Tafiyar
su Abba dai ta kankama, dan Abba ya matsa ainun, dole Galadima ya musu dukkan
shirin daya kamata, zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu jirginsu zai d'aga.
Da yake yau Saturday ce babu aiki, amma
hakan bai hana zama gidan shiru ba, su Sauban da innarmu sun fitane, nikad'aice
a gidan sai jakadiya, nima barci nake suka gudu suka barni a gidan.
Yunwar dana farka da ita ta tilastamin
sakkowa k'asa neman abinci, dan a 'yan kwanakinnan nazama wata acici, danaci
abinci danaji sabuwar yunwa, narasa wannan dalili.
Bannemi kukun gidanba ma ko cikin
bayi, nahau dafa abinda zaimin saurin dahuwa, kafin ya dahunma saida na d'umama
madara nad'ansha sannan 'yar nutsuwa tazomin. ina sauke abincin kuwa Na juyoshi
a plate na koma sama. tun a hanya naji k'amshin turarensa, ban kawo yashigo
gidan bane nidai na ida hawa. ban tsaya faloba na shige bedroom.
Galadima dake zaune a sofa yana
kwance igiyar takalminsa ya d'ago ido yana kallona da amsamin sallamar danayi.
Sandunan wasan Golf d'insa daya shigo
dasu ya zube a carpet d'in gaban gadon na janye gefe na zauna, dan nafijin
dad'in xaman k'asan yanzu.
Shidai bai fasa kallona ba baikuma bar
cire takalman ba, dan abincin dayaga ta
zubo yakema kallon mamaki, kafinfa yafita harda kukanta ta farka wai yunwa
takeji, haka dole yafita yasaka kuku dafa mata abinci, baibar gidanba saida
taci takoma barci, da fitarsa kuwa baifi 3hours ba, amma jita yanzu dawani
abincin.
Ya janye takalaman daya gama cirewa a gefe
ya zubamin ido kawai, dukda abincin nada zafi haka nakecinsa da sauri-sauri.
Janye plate d'in yayi daga gabana,
fuskarsa babu walwala yace, “waike mike damunki hakane?”.
Idona harya fara tara kwalla cikin
marairaicewa nace, “dan ALLAH kabani, wlhy yunwa nakeji bata wasaba”.
Rasa ma mizaicemin yayi, ya zubamin ido
kawai yana kallona. a mamakinsa saiyaga ma ina hawaye, abincin ya tura min yana
fad'in “wannan cin naki yayi yawa, gama muje wajen Akash ya dubaki”.
Uffan bance masaba, shima bai sake tankawa
ba yanufi bathroom, yaja wasu mintuna saigashi ya fito d'aure da towel, kallo
d'aya namasa na janye idona, wannan abun nasa yafara damuna, yanzu baijin
kunyar yafitomin a duk yanda yaso, ko yana mantawa bashi kad'ai bane a d'akin
oho.
Shima dai kallonta kawai yakeyi, dan
nacinye abincin plate d'in tas, a ransa yace shiyyasa taketa zama k'atuwa, irin
wannan ci haka.
Oho bansan yanayiba, nidai mik'ewa nayi
nashige bathroom abuna, nasamu nai wanka da ruwa mai sanyi dan naji dad'i.
lokacin dana fito yagama shiryawa cikin ainahin kayan malam bahaushe, blue d'in
shaddace akaima d'inkin wando da 'yar shara, saidai tasha aikin sarauta d'an
asali da d'aukar hankali, ya kawo bak'ar hularsa ya d'ora, itama dai irin ta
mutanen dace *dara* (irin wadda su ibro suke sawa), saidai wannan batakai
waccan tsawoba, dai-dai take kamar sauran huluna. harga ALLAH kwalliyar tasa
tamin k'yau, dan yafito a cikakken bahaushensa, turare yake fesawa amma nakasa
d'auke idona daga kansa.
Duk kallon k'urillar datake masa yana
kallonta ta gefen ido, wani miskilin murmushi yayi Na gefen baki, ya juyo muka
had'a ido, saurin janyewa nayi cike da basarwa.
Shikuma ya ta6e baki yana takowa inda
nake. tuni zuciyata harta fara tsitstsinkewa, dan ayanzu babu abinda nake gudu
kuma irin yace zai ra6u jikina koya nunan buk'atar wani abu, shima inaga
fahimtar hakanne yasa a kwanakinnan bai cika takurani kamar abaya danake kawo
kaina ba.
Ganin yanda ta tsorata sai abin yabashi
mamaki, waskewa yay yafasa zuwa gareta, ganin ya canja hanya Na sauke ajiyar
zuciya wadda har fitar sautinta saida yaji.
Kansa kawai ya girgiza ya zauna a bakin
gado yana fad'in “kishirya mana”.
Bance komaiba nawuce Na d'auki Arabian
gown da zan saka, dan yanzu sune kawai kayan dakemin dad'in sakawa, bathroom
nakoma Na saka, Na fito Na iskeshi yana waya da Akash dake fad'a masa inda zamu
iskeshi. wucewa nayi nad'an gyara fuskata, inason shafa mai a k'afa amma ina
tunanin yanda zan sunkuya.
Lura da yay da hakan yasashi mik'ewa,
wajen takalmanmu yanufa ya d'aukamin masu taushi cikin wad'anda ya siyamin
saboda naji sauk'in tafiya.
Kafad'una ya kama ya zaunar dani ga stool
d'in mirror, sannan ya d'auki man ya duk'a k'asa a gabana yakamo k'afata yana
shafamin, nidai kallonsa kawai nakeyi, harya gama yasakamin takalman ya d'auran
igiyar yana fad'in “yakamata ma mufara fita kina motsa jiki, dan k'afarnan
kamar tana d'anyi fushi a kwanakin nan”.
Nace, “ai bata ciwo”.
Baice komaiba yamik'e yana kama hannuna ya
mik'ar dani.
A falo muka iske jakadiya tana kallo,
tamin sannu sannan ta gaida Galadima.
yafad'a mata zamu fita, tabimu da
addu'ar dawowa lafiya.
Tafiyar tamu takasance shiru kamar yanda
muka saba inhar ta had'amu mu biyu, maimakon muje asibiti sai gamu awani gida
mai k'yau da tsari, kafin nasamu damar tambayarsa saiga Akash yafito yana zabga
murmushi, rungume juna sukayi da Galadima, kafin ya d'ago yanamin sannu da
zuwa.
Fuskata da murmushi Na amsa masa tareda
gaishesa.
A tsararren falon gidan muka yada zango,
komai ya birgrni dan an tsarashi yanda ya kamata. dandanan Akash ya tara mana
kaya a gaba, sannan ya zauna muka sake sabuwar gaisuwa. Suka d'ora da
barkwancinsu irin Na abokan da suka shak'u. A firar tasune nakejin Auren Akash
d'in ya matso, dan zasuyi baiko next week da wadda zai aura, Na tayashi murna
da fatan kaiwa da rai. ya amsamin bakinsa har kunne.
Bayanin yawan cin abincina Galadima
yamasa, Akash yay dariya, “to inbanda abinka Sameer ai dole taci abinci fiyeda
da, karka manta yanzu ba ita kad'ai bace, kuma saitaci abin cikinta zai samu
shima, kunk'i yarda ayi scanning muga adadin 'ya'yan namu ko jinsun su”.
galadima ya murmusa kawai, karka damu,
miye Na zazzari, kwana nawane insha ALLAH zaizo ko zatazo duniya, yanzu dai
tunda ba Matsala bane cin abincin ai Alhamdllh”.
“no babu wata Matsala, abindama yasa
zakuga yanzu takanyi saurin jin yunwa cikinta ya tsufa, shima yak'ara girma
abin cikin nata, dan zama ta dingajin idan bataciba ana motsi da harbe-harbe a
cikin, idan da zaka kalli cikin a time d'in datakejin yunwar sosai har yanda
yake wuntsilniya saika gani kaima, Madam ko hakan baya faruwa?”.
Nace, “yana faruwa sosai, amma da zaran
naci abincin sai a nutsu”.
Akash yay dariya, “Alamun yana cikin
k'oshin lafiya kenan, abincinne kawai buk'atarsa”.
Galadima ya juyo muka kalli juna, gira ya d'agamin nikuma nayi murmushi
ina kauda idona gefe.
Daga nan wata hirar suka koma, wadda nake
zargin akan Abba nane, dan naji Akash Na fad'in doctor Johnson yabama Abba
glasses d'in amatsayin medical glasses, kuma ya gargad'esa karyayi wasa dashi
saboda jijiyar idonsa nason samun Matsala, to sunason glasses d'in yazama riga
kafine, dayake da turanci suke magana sai yazam inaji nima.
Murmushi Galadima yayi yana jinjina kai.
A raina nace mikuma Galadima ya shiryama
Abban?. banida mai bani amsa, dan haka nayi gum.
Muna niyyar tashi Akash yace bamu
isaba, bazamu tafi bamuci komai a gidansa ba, kodan munga bashida matane.
Badan munsoba mukad'anci abinda zamu iya,
sannan yayo mana rakiya har wajen mota.
Saida munaya tashiga mota sannan Galadima
ke fad'ama Akash yayi mantuwa.
Akash yace “tami?”.
Babu kunya Galadima yad'an ciza lips
yana tambayar Akash wai miyasa yanzu take gudunsa?.
Akash yabashi amsa da maybe salon cikine,
danshi babu yanda baya zuwa ma mace, wani yasata sha'awa wani kuma akasin
hakan, amma idan na haihu zan iya komawa normal. Galadima ya basa hannu sukai
musabaha sannan ya shigo mota yana masa godiya.
Tunda muka fara tafiya saina kasa
jurewa, na jeho masa tambaya muryata a sanyaye.
Kad'an ya juyo ya kalleni ya maida kansa ga
tuk'i, saida yaja wasu mintuna kafin yasaki ajiyar zuciya tareda cizar lips
nashi, batareda Yakuma kallonna ba yace, “Friend! Wani karatun baya buk'atar
fashin bak'i, akan karantashine a barsa
a yanda yazo”.
Murmushi nayi ina maida hankalina
gareshi, nace “yalla6ai koda shi wannan karatun zai iya fita a jarabawa?”.
“Humm” yafad'a yana rage gudun motar,
yanzunma bai kalleniba, yad'an zakud'a jikin sitiyarin sosai, “sometimes akanyi
burin cin jarabawane domin canjin aji ko gama makaranta ko shiga, saidai
awannan karon ni nawa jarabawar da banbance-banbance tazo, dan bana buk'atar
cin jarabawar kai tsaye, har sai harsashina ya isa ga zukatan malaman”.
“to amma yalla6ai karka manta Hasashefa
ba shi bane yak'ini”.
“wannan gaskiyane yalla6iya. Saidai yak'ini kuma baya amsa sunan tabbaci,
daga lokacinda kika shiga fili wasa kika saka aranki bazakiyi nasara ba, to da
kamar wahala kiyi nasarar, duk abinda zanyi nakan rok'i ubangiji nasara Kafin
yinsa, sannan na cika zuciyata da kwad'aituwar samun wannan abin, lokuta da
dama mutane kan Gaza tsarkake zuciya kafin su cikata da buruka, shiyyasa kikaga
duk gudun jirgi a samaniya wataran gaggawa nasakashi tarwatsa a filinda ba
muhallin saukarsaba, kiringa zama mai yak'ini saikiga kin tabbata a jerin masu
samu”.
Murmushi nayi har hak'orana na
bayya, nace, “dakai kanarine danace kafi dukkan halittar kanari iya raira
zance, dakuwa mawak'ine saina saka a jerin masu zak'ak'an murya, inkuwa a
Marubuci kazo to tabbas kai Kanada yawan fik'ira, domin hikayarka zata yawaita
saye zukatan mabiyanka ne”.
Gefen hanya ya gangara, ya kashe
motarma baki d'aya ya maido hankalisa gareni.
“Munaaya!” yakirani cikin wani yanayi
kuma murya ahankali.
nima saina amsa masa a sanyaye.
Hannuna ya kamo cikin nasa yana mirza
yatsun a hankali, yaci gaba da fad'in “A shekarun baya ni mutumne mai ra'ayin
Kansa, ma'ana murd'ad'd'e mai wahalar sha'ani, sannan mai zama a bisa tsarinsa,
kece mutum ta farko dana fara doguwar magana da ita koda bana so, nakanyi
mamaki a duk lokacin da kika taya nazamo mai sallama miki, anya kuwa bakizo da
wani Siddabaru ba?”.
Idanu nad'an fiddo waje, nace “siddabaru
kuma yalla6ai? to ai awajena ni har gobe kana akan wad'annan ra'ayoyin naka,
dan banga canjin dakake hasashen kasamu ba, amma miyasa kace hakan?”.
Numfashi ya sauke ahankali, kafin ya
ciji gefen lips nashi yana Sosa girarsa d'aya da d'an yatsa “wannan sak'on zuciyane,
kibata dama, zata tabbatar miki da cewar wannan Muhammad Sameer d'in yasha
banban dana shekarun baya”.
“sak'on zuciya kuma?”. nafad'a cikin
hasashe, dan nikam Yakuma dilmiyar dani.
Mortar ya tada yana fad'in “well basai kin
zurfafa ba, dan haryanzu akwai sauran dama”.
Baki na d'an ta6e ina gyara zama, “har
walau zancen “dama! dama! dai again?, bana son saka baki a hurumin daba nawaba,
amma abinda nasani dama dai duk damace, sannan mai ita yakan tanadar mata
dukkan muhalin daya tadace da ita, damarmu ce mu damata takowane
hanya mukaso”.
Idanunsa ya lumshe yana sakin wani
k'asaitaccen murmushi daba koyaushe yake irinsaba.
Jin Sautin murmushin ya sakani juyawa na
kallesa, ya d'agamin gira yana maida hankalinsa ga tuk'insa.
Babu Wanda yasake yin magana har muka Isa gida. har yanzu babu Wanda ya
dawo, dan haka muka haye sama kai tsaye. dama na k'agara na cire rigar jikina
saboda azababbiyar zufar danakeji, danma ya tausaya min yad'an saka AC a mota,
ban iya zama ba saida na watsa ruwa, nifa abubuwan sunmin yawa, nice jin zafi
nice ci kamar gara, harda alwala nayo, Dan magriba tayi.
Ina fitowa shima yashiga yayo alwala.
Koda yafito saiya wuce masallaci.
Ina jiyo hayaniyar su Samha dasuka
dawo amma nakasa sauka, ina kwance abina, hawa da saukarnan bak'aramin wahal
dani yakeba yanzu, ahaka Galadima yadawo ya iskeni, sallamarsa kawai na amsa,
amma ban iya d'agowa na kalleshiba. Saida ya sauya kayan jikinsa zuwa marasa
nauyi kafin yazo ya zauna kan sofa yana fad'in “lafiya dai?”.
d'ago ido nai namasa d'an murmushi,
nace, “babu komai, gajiya ce kawai”.
Shima murmushin yamin, cikin lumshe ido
yace, “Sorry friend, saura k'iris insha ALLAH”.
“Humm” kawai nafad'a batare da nace masa
komaiba.
Daga nan muka d'anyi shiru, kusan mintuna 3 yanata latse-latsen wayarsa,
batareda ya kalleni ba yace, “Abba kuwa yana saka zobe?”.
Kallonsa nayi, amma hakan baisa ya
kalleniba, a d'arare nace, “eh yana sakawa amma miyasa kamin wannan tambayar?”.
Wayar ya ajiye yana sauke ajiyar
zuciya, ya saka d'an yatsansa yana bubbuga la66ansa ahankali, yayinda idonsa
yake a kaina tamkar mai nazari, “kina ganin idan kika bashi zai saka?”.
Yunk'urawa nai na tashi zaune sosai,
“dan sakawa zai saka, amma kana ganin bazai zargi wani abuba kuwa?”.
“miyasa kikace haka?”.
Shiru nad'anyi, dan ganin ina neman
zirma kaina, saina d'an murmusa kawai cikin basarwa, nace, “waynot abashi ba
kai tsayeba”..
Murmushin gefen baki yayi, yace, “y'ar
tsuntsuwata wai mikike tunanine? da har kiketa kwana-kwana haka?”.
Baki na tunzuro gaba, ina fad'in “nidai ba
tsuntsuwa bace ba”.
Dariyace ta kufce masa babu shiri,
yasaka hannu yana rufe bakinsa.
Haushi ya kamani na d'auki filon dana
kwanta na jefa masa. da sauri ya cafe yana cigaba da dariyarsa, hakan yasa
najawo na kujerar ina cigaba da kai masa duka yana karewa da wancan. daga
k'arshe sakkowa yay yahad'a nida filon ya rik'e yana fad'in “sorry sorry na
bari, ba 'yar tsuntsuwa ba giwar mata”.
Hararsa nayi nafara kukan shagwa6a kuma.
dariya Yakuma sakawa yana fad'in “toni
bansan mikikeso nace mikiba kuma?”.
“ni banaso duka”.
“to shikenan nabari, yanzu dai yaza'ayi
Ring yaje yatsan Abbanmu to?”. ‘yay maganar yana d'ora kaina jikin kafad'arsa’.
“saika fad'amin sirrin sannan zan fad'a
nima”.
Ya murmusa yana jan hancina, “kin cika
wayo yarinyarnan wlhy”.
K'aramar dariya nayi nace, “ai awajenka
na koya”.
Murmushi kawai yay baice komaiba, ya jawo
wata 'yar k'aramar bag mai k'yau fara ya mik'omin.
Kar6a nayi ina tashi zaune sosai na bud'e
jakkar ina fiddo kayan ciki, agogone mai masifar k'yau da tsari, na azurfa 'yar
asali mai tsada, sai wani d'an akwati da ring mai k'yau na azurfa shima, an
masa ado da farin stone mai garai-garai tamkar diamond, na jujjuya zoben kafin
na d'ago mu kalli juna ni da Galadima, ido d'aya ya kashemin😉.
Janye idanuna nayi nakuma maidawa ga
zoben ina k'ok'arin sakashi a yatsana, saidai yamin yawa sosai, na cire ina
fad'in “amma gaskiya zobenan ya had'u sosai yalla6ai”.
“duk haduwarsa bai kaikiba ai”. ‘yay
maganar acikin kunnena’.
Kallonsa nayi, amma saiya basar tamkar
bashi yay maganar ba.
Lips na cije na d'an hararesa.
Shikuma ya ta6e baki.
Na maida kayan duk a cikin bag d'in
dad'an hanzari ina rik'e cikina dayay wata wuntsulawa.
“lafiya?”. ya fad'a yana rik'o hannuna.
'Dagowa nayi na kallesa da k'yar, da
hannu na nuna masa cikina dake juyamin, jinake kamar numfashine zai bar jikina.
Babu shiri ya dire wayar hannunsa ya
rik'oni jikinsa da k'yau.
Sosai na fara murk'ususu ina kuka da
k'ank'amesa, dukya rikice, yama rasa mi zaiyi?.
Ana cikin haka saiga sallamar Aunty Mimi
dataga shirun yayi yawa sun dawo ban sakkoba, saitai tunanin kobana jin
dad'ine, sallama tayi Galadima ya amsa murya a rikice, hakanne yasakata shigowa
batareda jiran isoba.
Da hanzarinta ta k'araso tana tambayar
miya faru?. nidai kuka kawai nake ina kuma k'ank'ame Galadima.
Shine yasamu damar mata bayani
sama-sama, yak'are maganar da fad'in “Aunty mutafi asibiti please, maybe
haihuwa Ce?”.
Da sauri tace, “badai haihuwaba
Sameer, cikin dake wata takwas, kaga ina zuwa”. Ta fita a hanzarce.
Babu dad'ewa sai gata tadawo da innarmu da
jakadiya, dak'yar innarmu ta amince ta hawo, danma taga tsantsar rikicewar da
aunty Mimi tayine. har yanzu dai kukan nake ina jikin Galadima dashima dukya
koma kalar tausayi kamar zaiyi kukan.
Ganinsu a haka yasaka innarsu munaya
k'ok'arin komawa da baya, dan saitaji kunya ta kamata, dukda tasan suma bada
son ransuba ne. ita kanta jakadiya taji kunya. ganin innarsu munaya zata gudu
Aunty Mimi tayi azamar rik'o hannunta. “please inna karki duba ta kunya, halen
datake cikine abin dubawa, kowa yasan dai ba haihuwa baceba tunda da saura”.
Ajiyar zuciya inna ta sauke, batare da
ta motsa daga inda takeba takuma musu kallo d'aya ta d'auke kanta, tace, “inaga
juyine ai, zai lafa insha ALLAH”. ‘tana gama fad'a ta fice abinta’.
Jakadiya da aunty Mimi suka kalli juna,
murmushi jakadiya tayi, tace, “gaskiya ta fad'a, juyine, amma nadad'e banga uwa
mai kawaiciba irinta a wannan zamanin”.
Murmushin itama aunty Mimi tayi, ta
maida kalonta kansu, yafara lafawa sosai, dan haka munaya tafara tsagaitawa da
kukan.
Galadima yakuma k'ank'ameni a jikinsa
sosai yana shafa kaina, nikam sai ajiyar zuciya nake saukewa tareda shashshekar
kuka, ya manna min kisses a kaina idonsa a lumshe, danshi yama manta dasu Aunty
Mimi a d'akin.
Jakadiya ma dai lalla6awa tai ta gudu, dan
taga magajin gari yau sai a hankali.
Aunty Mimi ta tako inda suke ta zauna a
sofa tana fad'in “sannu Munaya”.
Bud'e ido Galadima yayi, harsun kad'a
zuwa launin jaa, yad'an furzar da iska yana lek'a fuskarta, barci ya d'auketa.
ido ya d'ago yana kallon aunty Mimi dake kallonsu cike da sha'awa, tamasa
murmushin kwantar da hankali, ajiyar zuciya ya sauke yana cije lips da jinjina
mata kai.
Tace, “tayi barcine?”.
Nanma kansa ya jinjina mata, yana
gyarama Munaya kwanciya a k'irjinsa yanda zataji dad'i, yace, “Aunty Mimi amma
yakamata muje asibiti aga miye matsalar?”.
“karka damu my k'ani, juyine kawai,
insha ALLAH babu wata damuwa. bara inje nima saida safe, idan kuma kaga dawata
matsala saika kirani muje asibitin tunkan dare ya kumayi”.
Bayan fitar aunty Mimi kuma k'ank'ameta
yayi yanamai jin tausayinta na ratsashi, ya sumbaci goshinta, kafin ya d'auketa
dukda nauyin datayi ya maidata saman gadon, yanzunma a jikinsa ya sakata, yaja
bargo ya lullu6esu tareda musu addu'ar kwanciya.
Cikin barci ta farka da wata
matsananciyar yunwa, k'irjin Galadima na shiga girgizawa ina kuka.
Galadima ya farka a firgice yana rik'e
hannunna, ya yunk'ura da k'yar ya tashi zaune, “miya faru?”. ‘yafad'a cikin
muryar barci’.
“yunwa yalla6ai, abinci xanci, kafad'a masa magana yabar
halbina”.
Dukda tabashi tausayi saida ya murmusa,
sauka yay yafita, k'asa ya sauka zuwa kitchen, yau saiga Galadima a kitchen🤣, rasa mizaimayi yayi, ganin yana 6ata lokacine kawai dan ba
iya uwar komai yayiba saiya fice, dole yaje ya tado kukunsu.
Mai aiki da aikinsa dannan saigashi ya
had'a mata Abu mai sauk'i, Galadima ya kar6a da kansa Yakoma saman.
Isketa yayi zaune tsakkiyar gado tana
kuma rurus, saita k'ara bashi tausayi, ya haye gadon da abincin, da kansa
yabata yana lallashi. saida tayi nak sannan ya sauka da tiren yana sauke
tagwayen ajiyar zuciya.
Nikam hankalinna kwance nazame na kwanta,
barci ya sake kwasheni.
Mamaki yasakashi tasata gaba yana kallo,
saikace wata mai aljanu, lallai duk namijin daya kasa tausayawa matarsa lokacin
da ciki yake jikinta yacika mara tausayi number d'aya, babu abinda miji zai iya
biyan matarsa dashi akan rainon cikinsa datayi da tarbiyyar 'ya'yansa, amma a
wannan time d'in wani namijinma rashin tausayinsa ke tashi akan matar, ALLAH ya
ganar dasu to.
Amin galadima🙁😔.
**********************
Washe gari
A safiyar yau su Abba suka tashi da
shirin komawa Nigeria, gaba d'aya saina tashi duk babu dad'i, jinake kamar
karsu tafi, dana tuna yaune zasu barmu sai hawaye ya zubomin, inama zai amince
nidai nabisu mu tafi tare?.
Agogo da zoben jiya na d'auka nafita
masaukin su Abba, dan Galadima ya fita tunda sasaafe, bansan ina yajeba.
Saida nayi sallama aka bani izinin Shiga
sannan na shiga, Abba na zaune a bakin
gado agogo rik'e a hannunsa suna magana da innarmu dake tsaye ita kuma tana
zuba sauran kayansu a k'aramin akwati.
Abba yay murmushi yana fad'in “sannu
munaya kinji”.
Murmushi nayi a kunyace, na dafa gadon zan
durk'usa k'asa na gaidasu amma saiya dakatar dani ta hanyar rik'e hannuna,
“kinga zauna, inake ina durk'uso yanzu”. da taimakon Abba na zauna a kujerar
dake kusada gadon, sai faman jeran sannu yakeyi, nikuma ina amsawa cikeda jin
kunya. gaishesu nayi, suka tambayeni yaya jikin? na amsa da “Alhmdllh”.
Jakar hannuna na mik'ama Abba, ya amsa
yana fad'in “minene kuma?”.
“Abba ka bud'e to”. ‘nayi maganar a
shagwa6e’.
Dariya yayi yana k'ok'arin bud'ewa,
“yanzu dai fitinarki k'aruwa ma tayi Munaya”.
Innarmu dake ta6e baki tace, “ai bamaka
san fitinarta ta zarce tadaba sai jiya, juyi kawai ta zauna tana rusama mutane
kuka a gidannan, yo ke aibama asan abin fad'in dazaki bariba ranar
haihuwar?”..
“babu abin fad'in dazata bari insha
ALLAHU”. cewar Abba yana juya agogon fuskarsa d'auke da murmushi.
Nima sai ban kula zancen Innarmu ba nace,
“Abba yayi k'yau?”.
“sosai kuwa Munaya”.
“Abba kawo na saka maka to”.
“to amma kekuwa ina kika samu kud'in
sayen wannan agogon da zoben mai tsada haka?”.
Murmushin nayi, nace, “Abba awani shago
mukaje sayen kaya tun kwanaki dashi, daga nace agogon yamin k'yau shinefa yace
na d'auka to”.
“Amma munaya yayi tsada da yawa, karna
sakejin irin haka, dan takurawace ai, idan kuma bashida k'arfin siyen abunfa?
Karki sake kinji ko?”.
“inasha ALLAHU Abba bazan sakeba, amma
dan ALLAH karkace bazaka kar6i wannanba, dan shima bazaiji dad'iba”.
Murmushin Abba yayi, yashiga sanya
albarka a garemu da abinda ke cikina, hardama addu'ar d'orewar lafiya ga Abie
shima. cikeda d'oki naita amsawa da amin, da kaina na saka masa agogon da
zoben.
Daga nan muka d'an ta6a hira. Dan akwai
sauran time sosai na tafiyarsu. Mun dad'e muna hira, dan ko break fast yau tare
dasu na sakeyi, dama tun asuba ni yanzu nakeyin nawa🤭, sanda kowa zai k'ara sainayi na
biyu.😂
Galadima ma daya dawo ya kimtsa nan
yazo ya samemu, yanda suke sakin jiki da
juna shida Abba abin na bani mamaki, Galadima yakuma yima Abba bayani sosai
akan yanda zaicigaba da tattalin lafiyarsa da kulawa da dukkan dokokin da sukai
masa, daga nan muka cigaba dad'an ta6a hira, itadai Innarmu duk adabaibaye
take, danma taga yau zasu wuce da bazata zaunaba.
Wajen 12pm mukabar gidan zuwa asibiti, a
asibitine akayi dogon zama, dan godiya ta musammance tashiga tsakanin surukan
guda biyu, Abba kuma yay alk'awarin kuma tsayawa wajen dagewa da addu'oi na
musaman ga jikin Abie da alk'awarin kawo wasu taimakon na tsarin jiki, dan
sunga fa'idar addu'a sosai.
Kowa jiyake tamkar karsu tafi, saboda
shak'uwace ta musamman tashiga tsakanin wad'annan families guda biyu, zaman
mutunta juna ya gudana sosai a tsakani.
Kuka na shiga rairawa lokacin danaga
tafiyarfa da gaske yinta za'ayi, sai alokacin muka san ashe wai harda Sauban,
zai rakasu saudiyya suyi umrah ta kwana 10, daga nan saisu wuce shikuma yadawo.
na kama hannun Abba na rik'e gam nak'i saki zai hau jirgi, su Sauban suka
tasani da dariya kuwa, oho ban kulasu ba, Galadima ya girgiza kaiwai yana
murmushi, yarinyarnan ta6ararta tayi yawa, yafad'a yana takowa inda muke da
Abba yana lallashina.
A Kallonsa Abba yayi sukayi murmushi, Abba
ya zame hannunsa a hankali yajuya zuwa ga jirgi, yunk'urin binsa nayi Galadima
yay azamar rik'o min hannu batareda yayi magana ba, juyowa nayi na fad'a
k'irjinsa ina kuma sakin sabon kuka.
Hannu biyu ya saka ya rungumoni yana guntun
murmushi.
Innarmu dake hangenmu ta cikin jirgi ta
share hawayenta itama tana murmushi, banda aure waya isa ya rabaka da
'ya'yanka. Abba daya zauna kusada ita ya saka hannunta cikin nasa yana murzawa,
juyowa tayi ta kallesa, yamata murmushi yana share mata hawayen da har yanzu
sun kasa tsayawa, jikin kafad'arsa ta d'ora kanta kawai.
Sauban dake kallonsu yay murmushi,
lallai Aunty gimbiya 'yar gatace a gidansu.
Saida naji alamun jirgi zai tashi sannan na
d'ago kaina, inaji ina gani jirgin yafara shawagi a samaniya harya shilla da
iyayena.
A motama haka naita sharar hawaye, dayake
dagani sai shi da Samha a motar, cankuma Aunty Mimi da Khaleel da jakadiya.
Samha tana ta bani hak'uri, amma tamkar tana zuganine, saida Galadima ya
harareta yana mata alamar tamasa shiru sannan tayi shiru, shikam ko sau d'aya
baicemin uffanba..
Asibiti muka koma, tunda muka shigo Momma
ta taso ta rungumeni a jikinta tana lallashi.
Galadima ya jingina da bango ya hard'e
hannayensa yana kallonmu, a haka sauran suka shigo suka iskemu, Abie ma
kallonmu yakeyi cike da tausayina.
Saida nasamu na tsagaita da kukan sannan
nacema Momma zanci abinci.
Galadima yaje kusada Abie ya zauna yana
k'aramar dariya, “dama kice yunwa kikeji kika zauna kinama mutane ta6ara?”.
Hararsa Momma tayi tana masa dak'uwa,
hakama Abie, aunty Mimi kam saida ta rankwasheshi akai.
Gurin ya dafe yana fad'in “a'a yazaku tararmin
ne kuma?, gaskiyafa na fad'a ko Samha?”.
Samha tace, “Uncle nima dai ina bayan
aunty gimbiya”.
Idanu ya kwalalo alamar tak'aremin.
Muka had'a ido na hararaesa.
Lips d'insa ya ciza yanamin alamar zan
kamakine da ido.
Na ta6e bakina nikuma. Dolenesa yatashi
yanemomin abinda zanci.
★★★★★★★★★★
Tunda su Abba suka tafi lafiya tamin
k'aranci, bana iya tsinanama kaina komai sai kwanciya, dukna fita hayyacina na
canja kamanni, ga cikifa sai kuma bud'ewa yake yana k'ara girma. Kai kace ba
halitta d'aya bane a cikinsa.
Galadima dole ya d'auki hutu a office,
idan abinda yazama dolene saiyaje Office kam yakanyi shine ta yanar gizo.
Gakuma nasarar jikin Abie daketa k'ara
k'yau, dan wasu sassan jikinsa suna nuna alamun fara aiki kamar yanda doctors
d'insa suka sanar mana.
A kwana na 8 da tafiyarsu Innarmu ranar a
asibiti na kwana, saboda jiki dai yak'i dad'i, ga masifaffen cin abinci abin
babu arzik'i.
★★★★★★★
Su Abba sun gudanar da ibadar Umrah
cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, ga Sauban dake nuna musu komai yanda bazasu
wahala ba.
Suna cika kwanaki goma yasakasu a jirgi
suka nufi k'asar haihuwa Nigeria kenan, sun rabu cikeda kewar juna suna saka
masa albarka.
Sun isa Nigeria batareda sanin kowa
namuba sai Yaa marwan da Galadima yakira ya sanarma yaje ya d'aukesu a airport.
Isowarsu gidanmu tazama a bazata, hakan
yasaka gidan rikicewa da murna, dukda kishin daya cika matan gidan ganin
innarsu munaya takoma wata d'anya shakaf saboda Hutu da canji wajen zama data
samu, dandanan 'yan anguwa suka shiga shigowa taya murna dama Abba jajen ALLAH
ya kiyaye gaba.
Innaro babu kunya taketa haba-haba da
d'anta, kota innarsu munaya batayi, dan haushinta takeji taje ta zauna a India
itako an maidota gida. (Babu mai iyama Innaro dai sai ALLAH🤦🏻♀🤣).
Su Ayusher da sukazo suka zage suka
gyarama inna d'akinta, komai ya koma need, tamkar ba shineba ya had'a uban
datti na tashin hankali.
Tafiyarsu Abba Nigeria da kwana 5 Sauban
ma ya dawo India, ya iske ina asibiti, dan gado suka bani dole, babu ranar
sallama ma, k'ila saina haihu.
Saidai randa mukayi waya da Munubiya
nake fad'a mata tace ai gidama yakamata na dawo na haihu, itama batada lafiyar
sosai.
Da to na amsa mata kawai, amma ina
tunanin yanda Galadima da ahalinsa zasu amince da zuwana haihuwa Nigeria, kuma
tunda 'Yar uwata ta ambata dolene hakan za'ayi,
kona so koban soba kuwa.
___________________________
*_Two months ogo_*😬🤭
Watanni biyu kenan da tafiyarsu Abba,
tunda sukatafi kuma babu wani Abu mara k'yau kona Sosa zuciya dayay gamo dashi,
harma ya koma wajen aikinsa hankali kwance.
Jama'ar gidansu Munaya kuwa sunyi haushin
da nuna hassadar ga inna harsun gaji sun bari, dan sudai san ba kulasu
zatayiba, ita yanzu babbar damuwarta ma 'ya'yanta su sauka lafiya, dansu
Safara'u duksun haihu sukam, kuma dab da dab sukaita kancamo 'ya'yan, ayanzu
haka sunan d'an Fauziyyane kawai yarage gobe idan ALLAH ya kaimu, dan itace
k'arshen haihuwa..
Su fiddausi duk suna gida sunzo wanka,
iyayensu kowa ta zuba k'arya a hidimar sunan 'yarta, yanzu maman Fauziyya da
innarsu munaya kawai aka zubama ido aga yanda zasuyi nasu.
Inna dai bata d'ad'ara kanta da k'asaba,
iya abinda ALLAH ya hore mata iya shine tai k'udiri yi a hidamar sunansu
Munubiya idan sun haihu. Fatantama su sauka lafiyar, dan gasu suna neman share
watanni na goma haihuwa babu amo babu labari.
Mama Rabi'a cema kawai keta k'ok'arin ta
na ganin sun tanadi dukkan abin fita kunya, sai Aunty Salamah dake taimaka
musu, wadda a yanzu tazama 'Yar uwa agaresu makusanciya, dan komai nasu tana
tsaye a akai tsakaninta ga ALLAH.
WASHE GARI akasha sunan d'an Fauziyya.
Wanda mijinta da mamarta suka bada mamaki, masu shirin asha kunya sai aka barsu
su dajin kunyar da shak'ar bak'inciki irinna masu hassada.
Itama tamkar su Haleematu gida ta taho
wankan jego.
**************************
A wata ranar talata datai dai-dai da
cikar cikunanmu wata goma da sati biyu natashi da matsanancin ciwo, Wanda ya
rikita Galadima da ahalinsa, nan take doctors sukace haihuwace, aka fara shirin
kar6arta amma ina, gadai haihuwar gadan-gadan da gaske amma kuma nagagara
haihuwar har washe garin laraba.
Nayi masifar galabaita, Galadima yace
sumin cs idan bazan iya haihuwa da kaina ba.
Amma sukace zan iya haihuwa.
Ranar laraba da daddare Galadima da Momma
na kusadani suna ta tofamin addu'a saboda zufar danakeyi, nace su kiramin
munubiya, babu musu Galadima ya kira Yaa marwan.
Shima dakaji muryarsa zakasan a rikice
yake, hakan yasaka Galadima tambayarsa ko lafiya?.
Yaa Marwan yace, “dadai sauki ranka ya
dad'e, tun daren jiya Munubiya ke nak'uda amma haihuwa shiru, sai sunan Munaya
kawai taketa kira”.
Mik'ewa Galadima yayi tsaye, yace, “muma
ai halin da ake ciki kenan, yanzuma itace tace akira mata ita, please kakai
mata wayar”.
“ok”. Yaa marwan ya amsa yana nufar
d'akinda Munubiya take...............✍🏻
Barkanmu da
dawowa.🤩✋🏻
*_ALLAH ya
gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
No comments