RAINA KAMA (BOOK 2) 16&17
~Book 2~ 👉🏻1⃣6⃣
.................“Kin
shirya taimakon Mijinkine Munaya?”.
A salon da yay maganar saida tsigar
jikina ta tashi, nad'an lumshe idanu sannan na bud'e a kansa, muryata na rawa
nace, “ni bansan komaiba. kuma
ina ganin a wajen Abie yakamata ka k'ara samun
haske ai, tunda yanzu yana magana”.
Murmushin takaici yayi, sannan ya kamo
hannuna cikin nashi, “Kinsan miyasa nabaki dukkan wannan labarin daba kowanne
mahaluki ya sansu baki d'aya ba?”.
Kaina na girgiza masa a sanyaye.
Ya murmusa, tareda d'ora hannunsa saman
cikina, hannun nasa na kalla, shima idonsa na a wajen, yace, “saboda kece wadda
zata zama uwar d'ana ko 'yata, ina fatan koda nabar duniya ban cimma burina ba
kibama duk abinda kika haifa labarinnan domin ya ida cimma manufata, wannan
wasiyyace ga abinda zaki haifamin, dan inaji a jikina komi zaki haifamin insha
ALLAH ba zai zama ragoba, sannan kuma tabbas kin cancanta, domin kece mutum ta
farko dana ta6a yarda bazataci amanata ba bayan Mahaifiyata da kakannina da
yayata da k'anina. daga k'arshe ina rok'onki girman ALLAH ki sanarmin da abinda
kika Sani game dani, dan tabbas nasan kinsan wani Abu, nasha auna fik'irarki a
ma'auni kuma ina samunta dai-dai, dan haka batun 6oyemin ma kibarsa zuwa yanzu, kinga Abba jibine zasu koma, to
lallai rayukansu tana cikin had'ari kuma komai zai iya faruwa, saboda a yanzu
mak'iyansa sunyi shirin dayafi na farko ma, a zatonsu Abbanki yasanar dani
komai ne. ni kuma ban ta6a wannan maganar dashiba, sannan Abie da kike magana
likitoci sunyi gargad'in kar'a tuna masa da abinda ya wuce yanzun, saboda gudun
dawo da hannun agogo baya, kuma kodama na tambayesa zai iya dakatar dani yace
ya yafe, ni kuma nariga nataso da BURIN 'DAUKAR FANSA, a cikin zuciyata da
kwanjina, Ni nasan Yaya nayi jiyana, yau d'ina ma a wahale take kasantuwa, dan
haka nakeson gyara gobena da goben 'ya'yana da dukkan ahalina, inason sanin
dalilinsu nama mahaifina hakan, inba hakaba bazan ta6a samun kwanciyar
hankaliba”.
Nad'an muskuta domin gyara zamana, ina
fad'in “shikenan, amma kabani lokacin please”.
“Nabaki”. yafad'a yana mik'ewa tsaye.
Binsa kawai nayi da kallo, saiya kuma bani
tausayi, dukda kasantuwar rayuwarsa cikin Rud'ani, hakan bai habashi zama
kamilin mutum mai tarin Nutsuwa ba, gashi da sauk'in kai, saidai idan baka
fahimceshi baneba, kamar yanda na kasa fahimtarsa a farko, saika masa kallon
mai girman kai.
A gaba d'aya yinin wannan ranar cikin
nazarin maganganun galadima na yisu, tabbas abotar Alhaji Mamman kurfe da
Senator Halluru da Abbana abin dubawace, na shiga tunano wasu abubuwa danaita
karo dasu a d'akin Abbana ni da Munubiya, a wani time d'in da Innarmu ta sakamu
masa wani gyaran d'aki, Wanda shine sanadin shigowarmu wannan cakwakiyar kuma,
na dafe kaina saboda saramin d'in da yakeyi, motsin da d'an cikina yayine ya
sakani dafe cikin ina lumshe idanu, gaba d'aya kaina yana Neman kullewa, har a
washe garin ranar haka naita fama da tunani, danma yana hanani, amma danaga ya
matsa zan d'ora daga inda na tsaya, yanzu ma dazai fita aiki saida yamin
gargad'i, yace na sauka k'asa wajensu innarmu nayi hira, to kawai nace masa,
amma yana fita ban fasaba, ganin lokaci na k'ara k'urewa saina d'auki waya na
shiga rubuta massage mai tsawo dazan turama Munubiya.
Duk abinda takeyi a idon Galadima ne, tun
d'azun yana lura da dukkan motsita ta camera d'in daya ajiye a d'akin wadda
koda wasa Munaya batasan da zamanta ba, ya murmusa tareda godema ALLAH, dan
yasamu damar kamata a hannu, ta wannan hanyarce kawai zaiyi amfani da ita wajen
samun abinda yake buk'ata ga Abbanta, dan Abba yak'i bashi kowacce k'ofa dazai
san wani abinda ya sakashi shiga wannan halin, alhalin yaga tarin damuwoyi a
idanunsa, masu kuma matuk'ar muhimmanci a aikinsa.
Wayarsa tai 'Yar k'ara alamar Munaya na
sarrafa wayarta, saurin saita abinda ya saka mata a wayarta bata saniba yayi,
harta gama typing ta tura sak'on akan idonsa, shiga yayi ya duba, saiyaga
Munubiya ta turama sak'on, yay hanzarin bud'ewa. (Galadima ya had'a wani tarko a wayar Munaya
batareda ta saniba, dukkan wani Abu dazai shiga wayarta ko fita saiya gansa a
wayarsa, ta wannan hanyarne yaga na yanzu, saimu bishi muga abinda Munayar ta
rubuta to).
_“ ‘Yar uwata, tabbas Allurafa na shirin
to no galma, anzo ga6ar da lallai yakamata mu sanarma Galadima komai akan
abinda muka Sani, danna fahimci lallai zatonmu yazama gaskiya, wannan sunedai
ahalinnan da mukaga bayanai a Kansu, dukda nakula Abbanmu nasan basarwa, saidai
bansan manufarsa tayin hakanba, bayan wannan itace damarsa ta k'arshe dazai
yadda kwallon mangwaro ya huta da k'uda, sweetheart minene shawararki? dan
burina dana haife cikinnan auren contract ya k'are a tsakaninmu, domin babu
alak'a kuma kenan, kinga nima na samu 'yancin kaina, nayin auren din din din
kamar kowacce mace”._
Babu shiri Galadima ya mik'e tsaye,
jikinsa har wani tsuma yakeyi, lallai anzo ga6ar Ashe, hasashensa yazama
gaskiya kenan kokuma zai zama, tomi wad'annan yaran suka sani? kenan Munaya
Nada dalilinta na yarda da auren su na Contract? Mi Muftahu ya Sani gameda
Munaya dahar ya d'anata a gareshi a matsayin tarko?, bayan shi yana nan yana
ik'irarin yima Muftahu tarko da auren Munayar. Lallai kan yakula itama Munaya
da 'Yar uwarta da Muftahu suna Neman zame masa RAINA KAMA.
Baifi mintuna 15 ba da tura sak'on da
Munaya tayi, saiga Munubiya ta kirata, duk Galadima yana kallo daga camera
d'insa da kuma saitin wayarsa, dukda kuwa yana office ne, Munaya bata d'aga
kiranba, saida ya katse sannan ita ta kirata, munubiya na d'agawa Munaya race,
“Sweetheart kinga sak'ona kuwa?”.
“Na gansa sweetheart, amma fa ni duk kin
rikitani, kinga wata alamace data tabbatar miki ahalin Galadima ne?”.
“Munu, tabbas alamomi da yawa sun
nunamin hakan, sannanfa shima yasan Alhaji Mamman k'afur fa, kuma kinga ai a
takardarnan munga sunan Alhaji Mamman k'fur d'in, gashi abokin Abbanmu sosai,
nifa yau wlhy abubuwa masu yawa ya fad'amin game da sirrinsa, dukda
kasancewarsa mutum mara yarda, duk dai da inaji a raina kamar ya fad'amin wani
yankin sirrinsane danya bigi cikina be, amma ni wlhy tausayi guy d'innan yake
bani da gaske”.
Munubiya tayi murmushi daga can, cikin
tsokana tace, “to ALLAH yabar k'auna dai, sweetheart”.
“ban ganeba, k'aunar mi zai bari?”.
“keda Galadima mana, ai soyayya kan fara
da tausayine”.
“Mtsoow dan ALLAH muyi magana mai amfani
Munu, yanzu ya kika gani, danya rok'eni ALLAH akan nafad'a masa mina Sani,
nikuma ina tsoron koba akansa d'in baneba Abbanmu yake cikin damuwar, karmuzo
kuma muyi aikin Baban giwa”.
Ajiyar zuciya Munubiya ta sauke, ta gyara
kwanciyarta tana fad'in Munaya kodai mu sanar da innarmu ne kozata bamu
shawara?”.
“kai amma bakida hankali yasin, sokike
innarmu taci k'aniyarmu Ashe, zatace miyasa tun a farkon lamarin bamu sanar
mataba, k'ilama tayi fushi, Dan nima wlhy ayanzu ina ganin munyi wauta fa”.
“to komadai miye munrigada mun aikata.
Yanzu mafita zamu nema, mizai hana ki rok'eshi inhar bashi bane kokin fad'a Dan
girman ALLAH karya tada zancen kawai, yakuma rik'e mana sirrinmu, idan kuma zai
taimakemune akan Wanda kema Abbanmu barazana da mutuwa ai kingani munsamu
madafa muma, kinga dai yanda sukaso cin galaba wajen kashesa, wlhy Munaya
jinake kamar kar Abbanmu su dawo k'asarnan”.
“Ni kaina tsoron dawowar tasa nakeji,
musamman da jiya Yakuma maimaitamin, shiyyasa kawai na Yanke shawarar mu fad'a
masa, idanma ba shi bane saiya taimakemu wajen gano wanene”.
“to shikenan, sai naji yanda kukayi
kenan, Yaya unborn d'inmu?”.
“gashi nan ya isheni da motse-motse wlhy,
na k'agara ma ya fito na huta, kema Yaya namu da lafiyarki?”.
Cikin tsokana Munubiya tayi dariya,
“aikoya fito nanda wata shekarar Munafata wani ya Shiga sweetheart”.
“wlhy na kula bakida man kai Munubiya,
sai anjima”. Munaya tafad'a tana yanke wayar.
Galadima daga can yay wani k'asaitaccen
murmushi yana shafa Kansa da cije lips, ya koma jikin kujera ya lafe yanamai
lumshe idanu.
👭
🤣Galadima Kodai-kodai🤫
************
Muna gama
waya da Munubiya na sakko k'asa, babu kowa gidan dagani sai su innarmu sai
jakadiya, a falon k'asa na iskesu suna hira.
Jakadiya tace, “ranki ya dad'e kin fito?”.
Murmushi namata, ina fad'in “na fito
jakadiya, ya k'ok'ari?”.
Tai 'yar dariya tana cewa “kuke fama da
k'ok'ari ai, ALLAH dai ya raba lafiya”.
Bance komaiba na zauna ina gaida Innarmu ta
amsa tana tambayata ya jikin.
“da sauk'i” na fad'a kaina a k'asa, nace,
“innarmu Abba fa? ko barci yakeyi?”.
“A'a sun fita ai shida Sauban tunda safe,
zasuga likitansa daga nan sud'an zaga gari”.
“Oh ALLAH ya dawo dasu lafiya to, zaisha
yawo kam indai fita da Yaa Sauban ne”.
Dariya jakadiya tayi, tace, “ai mai sunan
manya sai a hankaki, shibama ya gajiya”.
Inna tace, “a baya gajiya kam, ni ai
birgeni yakeyi, babu ruwansa, sai tsokana da barkwanci”.
“Ai tamkar gadone abin nasu, dan mai
martaba lokacin yanada lafiya, dukda kasancewarsa shugaba hakan baya hanashi
barkwanci da mutane lokaci-lokaci, to hakama magajin gari yake, daga bayane shi
sai nasa halayyar suka canja, yazama shiru-shiru, amma shi mai sunan manya
saibai canjaba kuma”.
Ina jinsu nidai bance komaiba, sai murmushi
danake tayasu dashi kawai.
Mun dad'e a falon har su Abba suka dawo,
masaukinsu ya wuce, Sauban kuma ya zauna muka cigaba da hira, tashi innarmu
tayi tabi bayan Abba.
Sauban ya mik'e yana cewa zaije ya
watsa ruwa, itama sai jakadiya tashiga domin nunawa kuku abinda zai dafa, ganin
haka natashi na nufi masaukin su innarmu.
Nakama handle d'in k'ofar zan murd'a
tareda yunk'urin sallana sainaji muryar innarmu kamar tana kuka, “Haba Abbansu
dan ALLAH ka sanarmin damuwarka, Yaya kana cikin matsala amma ka gaza fad'ama
kowa?, tunda tafiyarnan tamu ta gabato ina lura dakai baka ko barcin kirki,
sannan inajinka kana sambatu cikin mafarki jiya da asuba akan kozasu kasheka
bazaka bayarba, shin wai minene? kuma su waye?, nidai tun bayan haihuwar su
Munubiya na fuskanci kana cikin wata damuwa, amma kullum cikin k'ok'arin 6oyewa
kake, bansan minene kake 6oyewarba, haba Auwal, a tunanina yanzu munzama irin
d'ayan da bazaka 6oyemin matsalaba kowacce irice, a nawa tunanin munkai bigiren
raba farinciki ko sa6aninsa, ko kasan ranar da muka fita da dasu Samha naga
lokacin da wani bak'in mutum yazo kuka ke6e gefe, kana kuma magana tsakaninka
dashi cikin fushi”......
A rikice naji Abba ya katseta da
fad'in Ai'sha kenan ido kike sakamin ban saniba?, dan kawai kin ganni da mutum
saiki fassara da wani Abu, Toni banma sanshiba, dan kawai ya ganni bak'in
fatane shine yake tambayata, amma daga hakan babu komai, tunba yanzuba kikemin
tambayar mike faruwa ina baki amsa babu komai, miyasa bazaki yarda babu komai
d'inba, ni nama matso da tafiyar tamu baya, dan doctor yakuma tabbatarmin da
babu wata sauran matsala, ki sanarma Munaya ta sanar da mijinta gobe zamu koma
kawai”.
“gobe kuma Abbansu?”..
A fusace yace “eh!”.
Ni kaina saida na razana da tsawarsa naja
baya daga jikin k'ofar, da sauri nabar wajen jin alamun za'a bud'e k'ofar,
tabbas akwai abinda Abbanmu ke 6oyewa da gaske, to wanene bak'in fatar da
innarmu tagani tare da Abba ranar? a ranar tare dasu muka fita, saidai sun
rigamu tafiya, saboda ni da Galadima mun biya asibiti wajen awo, saida akamin
sannan mukabi bayansu, kenan kafin muje abin ya faru? dan tabbas na tarar Abba
baya cikin walwalarsa, harna tanbayesa ko jikinsa ne? Amma yacemin a'a kansane
kawai ked'an ciwo.
Bansan na iso bedroom d'inmu ba saboda
zirfi danayi a tunani, ko hawan benen ma bansan nayoba, juyowa nayi da sauri
saboda jin an kama hannuna. ganin Galadima saina rajaza zanyi baya, da sauri ya
rik'oni da k'yau yana fad'in “Nutsu mana”.
Da k'yar na tattaro nitsuwa ta, shikuma
ya zaunar dani gefensa, hawayrne suka shiga ziraromin a kumatu, Abbana yana
cikin matsala, amma wani dalili ya hanashi fad'a, takai har inda yake jiyya ana
bibiyar rayuwarsa kenan?.
Ido Galadima shidai ya zubamin, bai
hanani kukanba baikuma tambayeni dalilin yinsa ba, kusan 5minutes sannan ya kwanto
da kaina jikinsa, jina a k'irjinsa saina fashe da sabon kuka, nanma k'ala bai
ceminba, yadai cigaba da bubbuga bayana alamar lallashi, saida nayi mai isata
nayi shiru sannan ya d'agomin kaina, dukkan kumatuna ya rik'e cikin tafin
hannunsa, Kafin yay k'ok'arin saka idanunsa cikin nawa, cikin k'asaitacciyar
muryarnan tasa mai kama da anmasa dole yace, “Haba yalla6iya, sokike ki
haifamin abin cikin kwan mai saurin kuka irinkine wai shin?”.
Bansan Sanda murmushi ya su6ucema fuskata
ba, na lumshe idanuna saboda bana da jimirin jure kallon da yakemin, shima
murmusawa yayi, sannan yakai fuskarsa dab da tawa yana huramin iskar bakinsa a
saman ido.
Ban iya hanashiba kusan mintuna 2 sannan ya
daina, bud'e idona nayi nad'an kallesa, ya d'agamin gira yana fad'in, “ya
dai?”.
Cikin tunzuro baki nace, “babu komai”.
“To miye abin jin haushi daga tambaya”. ‘yay
maganar yana sakin kumatuna’.
Binsa nayi da kallo, ganin zai fara
k'ok'arin cire kaya, na mik'e zan fice, dan yanzu na lura lamarinsa kullum
k'ara girmama yakeyi, baya shakkar cire kaya a gabana ko sakawa, sai dai ni na
fita na bashi waje.
Hannuna ya rik'o, na waro ido waje
cikin mamaki.
“ina zaki?”. ya fad'a cikin tsare gida.
“ba wanka zakayi ba?, idan kagama zan
dawo ai”.
“toni dodone?”.
“A'a na fad'a ina ta6e baki”.
“to koma ki zauna ki kalli sadakinki”.
Idanu na waro masa waje da hangame
baki.
Yiyai kamar bai ganniba ya basar. bai
sakeniba yakuma cigaba da cire kayansa da hannu d'aya. Ni daifa k'in kallonsa
nayi, dan wlhy kunya nakeji sosai, dukda 'yar shak'uwa ta shiga tsakaninmu
hakan bai sa mun saki jiki da junaba, garama shi idan rashin kunyarsa ta motsa
yakanyi abinda ya gadama yana basarwa a dole kar'a kawo masa raini. Yakan bani
dariya sometimes, amma nima saina Basar saboda Jan aji.
Iska kawai naji a cikin kunnena, da
sauri na waigoshi, ganin sa dagashi sai boxer sai na juya fuskata.
Bayana ya koma ya zagayo da hanayensa
duka akan cikina, yayinda kansa ke a kafad'ata, muryarsa can k'asan mak'oshi
yace, “miya sakaki kuka?”.
Salon da yay maganar ya sakani lumshe
idanu saboda tsigar jikina data tashi.
Nace “kabari ka gama zan fad'a maka”.
“miyasa ba yanzu ba?”.
“ka saka riga to”.
Murmushi yayi yana shafa cikina, “my friend
sarkin tsiwa sarkin kuma Kunya, akwaiki da abubuwan bi........”
Saikuma yay shiru yak'i k'arasawa,
hannuna na saka na rik'e hannunsa da ke yawo saman cikina, nace, “ka k'arasa
mana, akwaini da mi?”.
“Humm” kawai ya fad'a yana sakina, yaja
bathrobe d'insa dake jikin hangar ya sanya, saida naga ya fara k'ok'arin d'aure
igiyar sannan na d'ago na kalleshi.
“To mikuma kike kallo?”. Ya fad'a
cikin tsare gida.
Baki na ta6e ina fad'in, “miye abin kallon
to?”.
Ya
d'an fiddo ido sannan ya matsoni, “zona
nuna miki”.
Nasan ko guduwa nayi saiya kamoni dan
haka na duk'e ina fad'in “wash ALLAH cikina”.
Tsayawa yay cak, saikuma ya tako da
hanzari yana tambayar lafiya?.
cikin marairaice face nace “Motsi yakeyi
ALLAH”.
rankwashina yayi aka yana cewa “ke d'inan
ko”.
Dafe wajen nayi, bai kulani ba ya shige
bathroom, na harari bayansa ina masa gwalo, nasan inda banyi hakaba bakina ne
zaisha wahala.
Ina zaune ya fito, na d'auke kaina
tamkar ban ganshiba, shima hakan yayi, ya wuce wajen frigate ya d'akko ruwa da
Kofi, kujerar dake wajen karatunsa ya jawo ya zauna yana fuskantata, batareda
yayi yunk'urin cire bathrobe d'in jikinsa ba, yanzun kam babu wasa a fuskarsa,
ban damuba dan nasan halin kayana yanzu, yanzu zakiga yasaki jiki yana magana
kamar ba shiba, anjima kad'an saiya koma Asalin Galadimansa dana fara gani a
Hospital, Mara dariya mara later r😏.
K'afarsa d'aya ya d'ora kan d'aya yana
shan ruwa, yasha kusan rabi sannan ya cire, batareda ya ajiye kofinba ya maido
dukkan hankalinsa kaina, “A kwana biyunnan kokin lura Abba yana cikin damuwa?”.
d'ago idanuna nai na kallesa, a sanyaye
nace, “abinda naji innarmu na masa Complain kenan yanzu, amma saiya nuna
fusata”.
“shine kika shigo kina kuka?”.
Na jinjina masa kai batareda nace
komaiba.
Shima bai sake cewa komanba ya kauda
idonsa daga kaina yana kur6ar ruwansa. kusan 2minutes sannan yakuma kallona,
“Munaayaa mukawo k'arshen 6oye-6oye mana”.
Kallonsa nima nayi, nace, “kamar ya?”.
“humm” yafad'a yana cije lips, mik'ewa
yayi tsaye ya ajiye cup d'in hannunsa a gabana, sannan ya shiga zagaye d'akin
hannunsa goye a baya, nikam dai binsa
kawai nakeyi da kallo kamar na samu television, maganarsa ta katsemin tunanina.
“Munaaya! Mikuka ta6a gani a d'akin Abba
ke da 'Yar uwarki?”.
Zumbur na mik'e dan mamaki, “yalla6ai a
ina kasan wannan?”.
batareda ya kalleni ba yace “Munaya Sameer ya wuce dukkan tunaninki, dan
haka fad'amin?”.
Ajiyar zuciya na sauke, wadda ta tilasta
masa juyowa ya kalleni, nace, “yalla6ai ba fad'a maka bane matsalar, kuskuren
muhallin fad'arne da kuma makomata”.
“bakida dukkan Matsala da wad'annan,
idan bai danganceni ba zan d'auki matakin taimakon sirikina, makoma kuwa inada
yak'inin kare martabar matata uwar d'ana ta kowanne hali”.
Furicinsa yaban mamaki, dan haka nace,
“matar Contract ko?”.
“Well Duk yanda kika fassara dai-daine,
abinda na Sani kawai wannan maganar batada nasaba da waccan, dan haka kibar
kowanne a muhallinsa sai lokacin yinsa yayi”.
“humm” kawai na fad'a na koma na zauna inda na tashi.
Idonsa a kaina ko k'yaftawa bayayi.
Na nisa sannan nafara fad'in,
_“Na tabbata tunkan ka k'ulla alak'a
dani saida kasan koni wacece, dan babban mutum irinka bazaiyi Abu babu wani
tanadiba, banida matsala wajen maimaita maka sunana ko tarihin ahalin dana
fito, kamar yanda kasani mu 'yan biyune hakan yasaka ba'a banbancemu ni da 'yar
uwata, sai dai hallaya takan banbantamu ga Wanda ya sanmu, Munubiya mutumce mai
hak'uri da yawan kawaici, a wajen gadon hali tabbas ta biyo mahaifiyarmu ne,
sa6anin ni Munaya mai zafi da yawan tsokana, a lamarina babu ragi ko d'aga
k'afa, inhar kaga nayi dogon zama da mutum babu sa6ani to ka tabbata ya tanaji
matakan iya zama danine, basai amfad'a ba nima kaina nasan halayena na
kamanceceniya dana Mahaifina da kuma kakata innaro, a wata litinin d'in da
bazan ta6a mantawa ba sai mahaifinmu yayi wani bak'o, matsalar da aka samu
shine yazo bai iske Abba a gidaba, a wannan ranar innarmuce da aiki, dan haka
hak'in tarbar wannan bak'o saiya rataya a wuyanta, maimakon tayi da kanta saita
saka cikinmu ni da Munubiya wani yayi”._.......................✍🏼
Mu had'u a
page na gaba🤫
*_ALLAH ya
gafartama iyayenmu🙏🏻😭_*
*_typing📲_*
💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*
*_♦RAINA
KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
~Book 2~ 👉1⃣7⃣
_..................“Da
haushi na d'auki ruwan da innarmu ta bani na fita, saboda muna tsaka da kallon
wani film daneke masifar sone, Munubiya dan kartaje kaiwa saita hau barcin
k'arya. Tunda na shigo shegen mutumin nan ya tsura min idanu yana lasar baki,
kai kace tsohon mayene yaga nama, a zafafe na dire tiren agabansa ko k'ararsa
zatasa ya dawo hayyacinsa, amma wawannan yayi nisa, na buga tsaki a zuciyata
zan fice, caraf ya kamo hannuna, ban dubi girmansa ba na dage na watsa masa
mari, hakan kuma yayi dai-dai da shigowar Abbanmu falon. Amma d'an iskan ganin
Abbanmu da marin danai masa baisashi sakin hannunaba, saida Abba ya daka masa
tsawa da fad'in “SD! wane irin iskancine wannan? a cikin gidana ka kama hannun
'yata?!”. Abba na rufe baki ina kuma bashi mari na biyu, tunda naga alamar shi
bunsurune. a wannan karon ya saki hannun nawa, saboda janyeni da Abba yazo
yayi, Abba ya nunamin k'ofar fita, koda na fita saina la6e a corridor d'in
shiga falon bak'in._
_A zafafe Abbanmu naji yana fad'in “SD
ubanwa yabaka damar shigomin gida ne?”. sautin tafin bak'on na jiyo dan haka
nai saurin lek'awa ta kafar labule, gani nai yana zagaye Abba yana dariya da
tafi, cikin shak'iyanci yake cewa “Alhaji Auwal, Alhaji Auwal! dama kanada
k'yawawan 'yammata haka? Woow nice babie, idan na samu wannan ai ko rana bazata
sake ganina ba, wlhy nasan zan kwashi rom........., mari Abba ya zuba masa a
kumatu, yana nunashi da yatsa, a matuk'ar fusace yace, “wlhy idan ka kuma
furtawa saina datse kazamin harshenka a falonnan, wawa kawai”. SD ya shafa
kumatunsa sannan ya sumbaci hannun yana hurama Abba, “Kafa birgeni Alhaji
Auwal, kai jarumi, 'yarkama jaruma, kai inason irin haka mutumina uhhhhhhm
mutccch”. ya k'are maganar da kuma kissing hannunsa. Banza Abba yamasa ya
d'auke kai daga kallonsa yana fad'in “miya kawoka gidana?”._
_Alhaji Auwal kenan, kaima kasan dakaga
SD kasan zancen, a wannan karon da albishir d'in k'arin farashi akan tayin baya
nazo maka, sannan kuma damace a gareka ta k'arshe hakan, mun yanke shawarar
baka naira milyan 500”. Abba yaja tsaki yana hararsa, “ka koma ka sanar ma
iyayen gidan naka ina kan bakana, sannan Ku farka daga barcin da kukeyi, dan
bazan ta6a badawa ba, kamar yanda ban ba da jiya ba, bazan bayar yauba, sannan
gobe ma bazaku samuba, wannan kuma yazama first and last dazaka shigomin gida,
inba haka ba ina mai tabbatar maka zaka aikata kuskuren da bayan bayanka ma
saisunyi takaicin jin yanda zaka k'are”. “kwantar da hankalinka sarkin jarumai,
tabbas zan tafi, bakuma zan sake dawowa ba balle nayi nadama Oga, ammafa bazan
6oye makaba, kana bani mamaki, kak'i bama Wanda akace ka bamawa, sannan kak'i
saida mana mu masu buk'ata, shikuma wannan Abu ba tuwoba balle muyi tunanin
zakacine, waikai mike damun kankane haka? ka zauna kanata rik'ema Wanda
yarigada ya mutum amana, shikuma Wanda kakema tanadin bashida maraba da gawa,
koda yake ashefa ga Galadiman Ku nan, koshi kakema tanadi?”. “wannan ba
matsalarka bace”. Abba yafad'a cikin karsashi. “kumafa gaskiyarka wannan ba
matsalata baceba, amma tabbas inada yak'inin kai zata zama taka matsalar maybe
ma harda santaleliyar budurwar 'yarka, lallai labarin k'yak'yk'yawa da ahalinta
zai Shiga duniya kwanannan, nabarka lafiya, ka huta”._
Da sauri nabar wajen gudun karya fito ya
ganni, nakoma cikin gida ina juya wad'annan zantuka na abbamu da bak'onsa, masu
tsananin wahalar fassara, mi bak'on yake nema a wajen Abba dahar yake ik'irarin
sun basa zunzurutun kud'i naira na gugar naira, d'ai-d'ai har miliyan d'ari
biyar? Amma dukda yawansu Abba bai firgitaba balle mik'a wuya?, sannan wanene Galadima
kuma? Miyake nufi da labarina zai shiga duniya? Na shiga uku ALLAH karka bama
bawannan damar cutar da rayuwata ko ahalina gaba d'aya.
Munubiya data lura da halin danake cikin
ta sakani gaba da tambayar, tun ina k'ok'arin 6oye mata Dan kar hankalinta
itama ya tashi, harna fito fili na sanar da ita gaskiyar abinda naji da kuma
gani, harma Wanda na aikata.
Hankalin Munubiya ya tashi sosai itama,
nanfa muka Shiga kullawa da kwancewa Munason gani gaskiyar lamarin, amma mun
kasa kama bak'in zaren, fita kuwa mun koma yintane a d'arare saboda tsoron
furucin mutuminnan.
a wata ranar talata da Abba zai dawo
daga tafiya sai innarmu ta sakamu gyaran d'akinsa saboda kanta namata ciwo.
muna tsaka da aikin sai muka tsinci wani file da yasha k'yak'yk'yawar adana a
awani akwati dake cikin wardrobe d'in Abba, to dama da biyu muke aikin, harda
bincike akan Neman hasken maganganun da mukaji ranar, jikinmu har rawa yake
muka bud'e wannan file, a shafin farko mukaci karo da wani Abun daya kuma
rikita tunaninmu”.
👇🏻
*_Tabbataciyar
wasiyya ga ahalina, koda ace na kwanta dama kafin cimma burina ko mik'a wannan
sak'on amana ga Wanda ya cancanta, to na
shaida muku da cika umarnina na ida nufina a garesu 'ya'yana ko 'yan uwana,
inason Ku isar da wannan amana da aka bani ga ahalin wannan
masarauta............”._*
“iya nan rubutun ya tsaya, muka bud'e
shafin na biyu kozamuga sunan masaurar da Abba ke magana da k'arashen zancensa,
amma sai sunayen mutane muka gani a k'alla sunkai goma. Wucewa mukayi shafi na
uku, a dai-dai wannan lokacin Abbanmu ya shigo d'akin batare da mun Ankara ba,
wata hargitsatstsiyar tsawa mai tsinka hanji ciki da zukata ya daka mana yana
fad'in “ku harkunkai girman da zakumin bincike a d'aki a matsayina na mahaifinku?
mi kuka sani akan wannan takardar dahar kuke binciken abinda ke cikinta? Yaushe
kuka koma la6e?”. haka Abba ya rikice gaba d'aya muma ya rikita mu, ya dinga
zabga masifar dahar tajawo hankalin jama'ar gidanmu, indai tak'aice maka bayani
har innarmu saida fushin Abba ya shafa ranar, hakanne yasani fahimtar Abba ya
gane naji komai a ranar. munshiga damuwa a time d'in matuk'a, dukda hak'urin da
muka bashi yak'i saurarenmu, ya d'au tsawon lokaci yana fushi damu kafin ya
daina. bayan komai ya daidaitane kuma wani yammaci mun fito daga school saiga
motocika a jere suna tsula uban gudu a titi, wucewarsu tamkar iska yasakani
fad'ar bak'ar magana ga manyan k'asarnan har 'yan uwana na tayani. Sai kuma
mukaji sunanka a bakin wani saurayi da 'yammata biyu. Wannan ganinaka ne
yasakani dawoma Munubiya da abinda ya wuce, saboda sunan Galadima da mukaji
saurayinnan ya ambata, sai muka dinga tunanin kokaine Wanda muka ta6aji a
furucin bak'on Abba?. ga kuma sunan masarauta da muka gani a rubutunsa, dukda
bamuji sunan ainahin masarautarba kuma, balle mu tabbatar da kaid'inne..
Ganinmu dakai na biyu kuma saika bani haushi, dan ganinka mutum mai yawan izza,
sainaga bebekin Abba daya saka kansa had'ari akan Wanda shi baima damu da
damuwar kowaba sai tasa gakuma tarin girman kai Dana hango tartare dakai”.
(Kafayi hak'uri, gaskiyata nake fad'a, guntun murmushi kawai Galadima yamata
baice uffanba) taci gaba da fad'in “Wannan ne dalilin yimaka tsak'i a asibiti,
idan har baka mantaba, har dogarinka d'aya yataho da zummar d'aukar mataki amma
ka dakatar dashi da fad'in ya barni”.
Galadima ya murmusa alamar bai mantaba.
Nace, “ka tuna kenan?”.
“Na tuna kwarai da gaske, dan bancika
manta abuba saidai idan na d'aukeshi mara muhimmanci, amma a time d'in ai banga
face nakiba, shiyyasa banida tabbacin kece, saidai na muku kallo d'aya a lab da
muka iskeku keda sisters d'inki, ni nama zata Ku 'yan uku ne ai”.
“Umyim, amma a time d'in babuma Wanda zai
d'auka Kasan da zamanmu a lab d'in, dan gaisuwar da ake maka ma, kamak'i amsawa
sai d'aga hannu, hakanne ya tunzurani na fito daga lab d'in, dasu munu sukace
kainema kabada jinin da za'a sakama feena ban yardaba”.
Baki Galadima ya d'an ta6e yana shafa
kwantaccen sajensa, ya d'agamin gira d'aya yana fad'in “bazaki fahimta bane
yalla6iya. yanzu labarin da kika bani ya farune duk a wace shekara?”.
Na d'an ya mutsa fuska ina fad'in bamai
nisa bace, dan ko 2years cikakku baza'a k'ulla ba, Muna Exam d'in NECO nema,
dan har results d'inmu suka fito aka fara biyan JAM Abbanmu ya biyama sauran
'yan uwanmu amma banda ni da Munubiya, sai baba k'aramine ya biya namu, so
munfara karatu dai babu dad'ewa muka shirya da Abbanmu saboda magana da dad
d'insu Ayusher yamasa Yakuma sake bashi hak'uri. tundaga nan komai yazama Normal.
Amma kaikanka yakamata kayi mamakin yanda a kwanaki kad'an na amince da tayin
auren Contract d'in da kukaimin, dukda ba waccan binciken namu kawaine keda
alak'a da amintar tawaba, akwai wani dalili daya shafi ahalina”.
Mik'ewa Galadima yayi yana salute d'ina,
yace, “kin cancanci yabo my friend, dukda tabbas a farkon aurenmu kema kina
cikin zargina akan turoki akai gareni tun farko, amma yanda kike halayyarki da
d'abi'unki sai kika kauda hankalina, a tunani na dukkan mutum dazai kwantarmin
dakai yaringa nuna tsorona to tabbas wannan mutumin sunamsa *MAGE MAI KWANCIYAR
'DAUKAR RAI* a wajena, amma kece mutum ta farko kuma mace data iya mayarmin
murtanin magana kai tsaye, batare da shakka ba, sai dai inason Sanin minene
alak'arku da Muftahu to?”.
“muftahu kuma? babu wata alak'a bayan
wadda kasani, dan tare Na fara ganinku ai”.
Takowa yay zuwa inda yake zaune a da,
ya koma saman kujerar ya zauna, “kin tabbatar babu alak'a ta kowane fanni?”.
“miyasa kake kokwanto? inhar zaka kasa
gaskatani a nan bai kamata ka aminta da zancena Na farkoba kenan?”.
Ya murmusa yana fad'in “kozaki gaji Abba
ne?”.
Nace, “akan me?”.
“jaridanci mana, naga kin shahara wajen
iya bincike”.
Mik'ewa nayi saboda k'afata tafara yaamm alamar
jinina yana buk'atar motsawa, nafara d'an takawa. hannaye kawai ya hard'e a
k'irji yana bina da kallo, saida nad'an zagaya d'akin kafin nabashi amsa da
fad'in “yalla6ai kasan wani Abu kuwa?”.
Kansa ya girgizamin kawai.
Nace, “humm nifa nan daka gani,
kwakwalwata tana aiki fiyeda yanda kake aiki da agogo”.
“really?”.
“baka buk'atar jayayya”.
Ya d'aga kafad'a yana ta6e baki, “hakane
kuma”.
Sharesa nayi na zauna a bakin gadon danna
d'an mik'e, a haka najawo filo na kwanta k'afafuna a k'asa.
Tasowa yayi ya dawo ya zauna saman
k'aramin table d'in gaban sofa, jinai kawai ya kama k'afata ya d'ora saman
cinyarsa yana matsamin a hankali.
Da mamaki na d'ago kai na kallesa.
Ido d'aya ya kannemin yana d'an ta6e gefen
bakinsa, ya maida kallonsa ga k'afar.
Sabon salo, na fad'a a raina. a fili kuma
nace, “yalla6ai kaine......”
Bai bari na k'arasa ba yay saurin fad'in,
“ba dole na taimaki lafiyar abin cikin kwan ba”.
Harara na dalla masa ina janye k'afata,
ya kalleni da mamaki, “ya haka? ko haushi kikajine?”.
“miye zai Sani jin haushin? saika bari
idan yafito duniya ka matsa tashi k'afar”.
“oh ni Sameer naga ta kaina”.
“zama kaga ta k'afa bata kaiba, Sunan
nakama bazaka iya fad'arshi da r ba”.
“oh nan kuma kika dawo?”.
Matsawa nayi baya saman gadon sosai
batareda na bashi amsaba. shima saiya taso ya hawo gadon, hakan yasani
yunk'urawa zan sauka na bar masa, fan nasan hawan nasa bazai haifar da d'a mai
ido ba, yasa hannu ya rik'eni, “yalla6iya ai saikin maimaita mikika fad'a
dalla-dalla”.
“lah wasafa nake maka, kaga rigar
wankace a jikinka kaje ka cire kar mura ta kama ka”.
“Ai kinga dai-dai kenan”. Yay maganar
yana k'ok'arin kwance igiyar rigar.
Hannunsa nayi azamar rik'ewa ina marairaice
face alamar yaji tausayina.
Baki ya ta6e yana ture hannuna, na kuma
k'ank'ame nasa nak'i bari. Murmusawa yayi, ya kwanto gefena tareda sakani
jikinsa ya rungume.
“Nace please wankama zanyifa, zafi nakeji”.
Maidani yayi ya kwantar, cikin kunnena
yace, “kedai fad'i gaskiya, ko kina son a.......”.
Rufe bakinsa nayi da tafin hannuna ina
kukan shagwa6a, ya shiga k'ok'arin cirewa amma nak'i bari, shi dariyama na
bashi, irin wannan hak'ilo haka. duk yanda yaso na barsa k'i nayi, saida barci
yafara fisgata hannun ya zame.
Kansa ya girgiza kawai yana murmushi, a
fili ya furta “mai bakin tsiwa”. Ya k'are maganar da sumbatar goshinta yana
gyaramata kwanciya a jikinsa.
Ya tsira mata idanu yana kallon yanda
take fidda numfashi a hankali, a zahiri idonsa a kanta, amma zuciyarsa
maganganunta taketa cud'awa, shi baima ta6a ganin mace yarinya k'arama mara
tsoro da shiga rikita-rikita irinta ba, bata gudunma shiga had'ari? ya sauke
ajiyar zuciya yana tashi zaune, k'afafunta yashiga mammatsa mata a hankali,
aikam harda gyara kwanciya su madam munaya, yad'an murmusa, yasan ko'a d'azun
tanaso fa, amma iyayi yasata hanashi ya mata. Ya d'auki tsawon lokaci yana
mammatsa mata jikinma gaba d'aya, yayinda zuciyarsa kuma ke tattance bayananta
dalla-dalla, daga k'arshe sauka yay daga gadon ya fice zuwa d'akin sirrinsa,
duk abinda tafad'a yasamu sabon file ya bud'e masa, baya wasa da evidence komai
k'ank'artarsa, balle ma nata ya wuce Na wasa, ya dad'e yana rubuce-rubucensa
kafin ya koma kan Computers, sunan SD kawai ta ambata masa, dan haka yafara
searching gameda SD d'in kawai, babu abinda ya fahimta akan hakan, dama baiyi
tunanin fahimtarba, waya ya d'auka ya kira Nuren, bayan sun gaisa yace,
“Nureddin acikin yaransu Tanderu kasan SD?”.
“SD! SD! kai anya kuwa? amma dai ina
zuwa bani mintuna 30”.
“ok saina jika”.
Galadima Na yanke wayar ya nemo number d'in
Abba da bakowa ya sani d'innanba yafara aiki a kansa, dukkan Contact d'in ciki
suka bayyana, d'aya bayan d'aya ya dinga binsu yana nazarin adadin kiran da aka
ta6ayi, sau nawa aka kira Abba sau nawa ya kira shima? Mafi yawa ma kiransu
yafi yawa, yad'an murmusa yana wasa da tsinken hannunsa a kan la66a da nazarin
yanda zai 6ullo musu, dan duk hanyar daya kamata yayi bincike an d'auki mataki
a kanta, tsawon lokaci bai fahimci komaiba, sai zuwacan wata dabara tafad'o
masa, nutsuwa yay yana sarrafa Computer's d'in cikin tsantsar kwarewa da
gwaninta, ya kafa musu tarko ne a wayar innarsu Munaya, dan ya tabbata watan
watarana zasu iya kira ko sak'o, amma abinma haushin saiya iske wayar inna a
kashe, ya dafe kansa, saifa da yacema dady aringa barin wayar a kunne.
Babu shiri ya d'auki waya ya kira daddy,
bayan sun gaisa yaymasa maganar kunna wayar innar. cikin mamaki Dady yace, “ai
a kunne take koda yaushe, Change ma baya k'arewa nake kuma sakata, idankuma zan
zo nan nakan sanarma Jafar shima ya kula, amma ina zuwa dai”.
Galadima ya amsa da to, amma k'asan
zuciyarsa tana mamaki. babu dad'ewa Abba ya sake kiransa, “Ashe Change ne ya
k'are babu dad'ewarnan ban lura ba, amma gashinan Na sakata”.
“to Dady, Na gode sosai”.
Sunayin sallama da Dady Kiran Nuren Na
shigowa, d'agawa yayi, Nuren yace, “inagafa brother hanya d'ayace dazata saka
musan shi wanene SD d'in, dan abinda Na lura dashi baya amfani da hakan ta
kowanne fanin yanar gizo, maybe da full name yake amfani. yanzu zan sayi ticket
insha ALLAH zanje domin bincika a wajen Malam Saminu, nasan ya magantu yanzu,
zai amsa mana dukkan tambayarmu”.
“ok hakan yayi, idan ka fahimci bai saniba
karka takurashi, ka binciki yarinyarnan itama, koma ka fara bincikarta dan ita
bama wayo ta cikaba sosai, k'ila kafi samu cikin sauk'i a wajenta, abinda yasa
Malam saminu baison fad'ar komai, babbar
'yarsa cikin 'ya'yan Alhaji balala wani ya mata ciki, kuma sun dai-daita akan
idan ta haihu za'ama yaran aure, wannanne yasakashi tsoron fad'ar komai, dan
karya lalata waccan alak'ar, dan tabbas yasan yana fad'a auren bazai yuwuba, to
nima banason shiga hak'in kowanne ahali akan aikina, shiyyasa nabashi dama kaga
bankuma waiwayarsa ba, yanzu haka yarinyar ta haihu kwana hud'u kenan, amma shi
yaron ya kawota nan Dubai ta haihu ne, a nufinsu bayan haihuwar da sati d'aya
zasu dawo Nigeria a d'aura musu aure sannan su dawo Dubai d'in, dan Alhaji
balala baya son abinda zai 6ata record d'insa, kuma mamar yaronce ta Dage sai
anyi auren dan ita mutuniyar kirkice, dan haka mu bama Malam Saminu wannan
damar”.
Ajiyar zuciya Nuren ya sauke, cikin
mamaki yace, “duk ya akayi kasan wannan brother? ”.
galadima ya murmusa, yana fadin “Nuren
kenan, to bara nayi copy d'in my mata, kwakwalwata tana aiki fiyeda yanda kake
aiki da agogo, nasha fad'a maka bada kwanji kawai ake yak'i ba, sai anhad'a da
dabarun tunani dana nazari, so kad'an nafad'a maka daga abinda ya shafi Malam
Saminu, kaidai saina jika kawai, a time d'in da zakuyi maganar ka tabbatar ka
had'a Communication dani ok?”.
“babu damuwa aljanin munaya”.
Dariya sosai Galadima ya shiga tuntsurawa
da iskancin Nuren, wato shima ya maida Aljani yau, wlhy yaronnan yagama
rainashi, wai Aljanin Munaya, d'an iska zan kamaka ai.
Kashe komai yayi ya fito daga d'akin,
bai koma cikiba saiya sakko k'asa, ya iske Sauban kad'ai a falo, shima shigowarsa
kenan daga asibiti yake.
Galadima ya zauna yana fad'in “jirgi
sarkin tashi daga ina?”.
Dariya sauban yayi, yace, “kai Yaya,
nine kuma jirgin?”.
“Kamafi jirgi ai. Wane shiri kakeyi
gameda zuwa bautar k'asarka Nigeria”.
Sauban ya 6ata fuska kamar zai fasa ihu
“yaya yanzu fa ca za'ayi saina koma 9ja har zaman 1year?”.
Hararsa Galadima yayi, “to zakayi anan
k'asar ne?”.
“Ni Yaya ALLAH da anayi da nayi, a
manta da bautar k'asar kawai mana, nayi joining masters d'ina”.
K'aramin tsaki Galadima yayi, yay
crossing k'afarsa yanama Sauban wani kallon bammasan amsar dazan bakaba, saida
ya d'auki wasu mintuna sannan yace, “rashin yin ai bazai zama matsalar kowaba
sai taka, bakuma zaka gane hakanba sai nan gaba idan ALLAH ya kaika inda bakayi
zatoba, idan kace bazakayiba it's better, nidai ai nayi nawa ko. tashi kabani
waje”.
Ganin ransa ya 6aci Sauban ya marairaice
fuska zaiyi magana, amma sai Galadima ya d'aga masa hannu, sannan yamasa nuni
da k'ofa alamar ya fice masa.
Fita Sauban yayi yabarsa, shifa tsakani da
ALLAH zaman masarautar ne baya son yi shi kad'ai.
Galadima ya girgiza kai kawai yana
fad'in “ALLAH ya shiryeka, gata kasamu tunda katashi kaga komai basai ka nema
ba”.
Jakadiya data fito ta rissina tana
fad'in “Ashe ka shigo magajin gari, barka da dawowa”.
Murmushi Galadima yayi, yanason matarnan
saboda halaccin datake wa rayuwarsu, “yauwa jakadiya, ya gidan?”.
“lafiya lau Ranka ya dad'e, a shirya
abinci ko?”.
Agogon dake tsintsiyar hannunsa ya kalla, sai
kuma ya maida ga jakadiya, “bar abincinan jakadiya, akwai Inda zanje”.
“to ALLAH ya dawo dakai lafiya”.
Hannu ya d'aga mata kawai sannan ya tashi
ya fice. mashin ya hau yafita.
Abba dake can gefe a harabar gidan
tsakanin wasu flowers yana hutawa ya sauke ajiyar zuciya, tundaga fitowar
Galadima har hawansa mashin da fitarsa akan idonsane, rufe idanunsa yayi
yacigaba da tunaninsa da tun d'azun yake zaune a wajen yanayi.
Asibiti Galadima ya nufa, yay kici6us
da Aunty Mimi Na shirin tahowa gida ta huta, ta kalleshi da mamaki, “my k'ani
dawowa kayi?”.
Gefen girarsa yad'an shafa da d'an yatsa
d'aya, “eh , ina zakije k?”.
“gida zanje nad'anyi wasu abubuwa”.
“ok sai kin dawo”. yafad'a yana ida
shigewa, ita kuma ta fice.
Momma Na zaune tana waya da papi, ya zauna
d'aya a kujerun yana kallonta cikeda sha'awa, uba da 'Yar sun birgeshi, juyawa
yay ya kalli gadon Abie, barci yakeyi, har Momma ta gama wayar ison Galadima Na
kan Abiensa ko k'yaftawa bayayi, shi kad'ai yasan mi zuciyarsa take sak'awa.
“Muh'd daga ina haka?”. Maganar Momma
ta katse masa tunani.
Janye idonsa yayi daga kan abie ya maido
ga Momma, “Daga gida Momma, har yanzu barcin Abie yakeyi?”.
“eh tunda ka Fita bai farkaba, mike
faruwa naganka cikin damuwa?”.
Huci ya furzo daga bakinsa, zaiyi magana
sai kuma yayi shiru.
“Nifa tsiyata dakai kenan Muh'd, Yaya
Abu nacin ran mutum bazai iya fad'ama kowa a taimakeshi da shawara ko addu'a
ba, kaga yanda jijiyar kanka ta tashi kuwa? Haba Muh'd Sameer d'ina, kaifa
yanzu ubane, girmanka ya k'aru, aringa rage damuwarnan da miskilanci mana, ni
ALLAH ma yasa ba haka kakema d'iyar tawaba?”.
“kai Momma”. ya fad'a amarairaice
cikin 'Yar shagwa6a.
Murmushi tayi tace “to fad'amin mike
faruwa?”.
Yay d'an tsaki, “Ni ai Momma bammasan
ta ina zan fara baneba”.
“kafara ta sama kawai”. Momma ta fad'a
tana dariya.
Shima dariyar yayi kad'an sannan ya gyara
zama, kuma maida muryarsa k'asa-k'asa yayi yana maganar ahankali, tsaf ya
zayyanema Momma yanda sukayi da Munaya, ya d'ora da fad'in “Amma kinsan wani
Abu kuwa Momma?”.
“a'a saina fad'a dear”.
“uhm gani nake kamar bakomai ta fad'a
minba, ta 6oye wasu abubuwan dai kamar, saidai bansan dalilinta ba.
Momma ta jinjina kai tana murmushi, “To
Muh'd mizai hana kacigaba da binta a hankali, nasan zata fad'ama sauranma, ni
aganina kamar tana ganin kaima ka kasa yarda da itane shiyyasa tafad'i wasu
tak'i fad'in wani, idan har ka yaba da hankalin matarka yakamata ka fara sakin
jiki da ita wajen Neman shawararta da sakata cikin wasu al'amura naka Na
tabbata itama zata fara fad'a maka nata”.
“gaskiya kika fad'a Momma, dan naga
fa'idar hakan kwarai da gaske, zan kula insha ALLAH. ya addu'oin Abie akwai
saura?”.
“saura kad'an, gashi bakuyi wasuba”.
“mai k'arfin yince tazama sai a hankali,
daga barci sai barci take yini”.
“ALLAH Sarki d'iyata, ai tanama k'ok'ari,
dama idan ciki ya fara tsufa hakane, ALLAH dai ya sauketa lafiya”.
“To amin Momma”.
Sun cigaba da 'yan hirarrakinsu har zuwa
lokacin da Abie ya farka..................✍🏻
*_inata
gaisheku da yawa da yawa, comments naku Na sakani nishad'i over🥰🥰🥰🥰🥰😍😍😍😘😘😘_*.
I love you
wijiga-wijiga sister's🥰🥰🥰🥰
*_ALLAH ya
gafartama iyayenmu_*😭🤚🏻✋🏻
No comments