RAINA KAMA (BOOK 1) 25&26
👉🏻2⃣5⃣
..........Bugu biyu ta d'auka, jinayi
tamkar anmin bishara da aljanna dan dad'i, lokacin danaji muryar innarmu tayi
sallama cikin sanyinta sai kawai na Sanya mata kuka.
Ita kuma daga can batasan wayeba, a
sanyaye tace “baiwar ALLAH ko bawan ALLAH lafiya kuwa?”.
Murmushi nayi, gakuma hawaye na
kwaranya, nace “innarmu nice fa”.
Cikeda d'okantuwa tace, “Munaya kece?
ya kuke?”.
Murmushi nayi mai sauti, nace “innarmu
ina yini? inasu Aryaan? Wlhy ina missing d'inku innarmu, ALLAH kamar na dawo
gida”. na k'are maganar da sakin kuka.
Kallon juna sukayi da Abbanmu, da yake
girkin tane tana d'akinsa, sukama juna murmushi, Abba yace, “haba dai munaya ta
jaruma ce da kuka haka? Ina aka ta6a kai mutum gidan miji yayi sha'awar dawowa
gida inbada yawoba?”.
“wayyo Abbanmu I miss u so much kaima
wlhy”.
Dariya suka sanyamin shida innarmu, Abba
yace, “yo ga sakaran yarinya, miyeto na
kukan hakan? Yaya mijin naki da jama'ar gidan?”.
“komai lafiya lau Abba, sai kewarku,
musamman ma Munubiya, ALLAH ina kewarta Abba, dan ALLAH kace ya kaini na
ganta”.
Yanzu kam dai su Abba sosai sukemin
dariya, saikuma suka shiga tsokanata, tun ina kukan harna ware nima ina dariya,
munyi hira sosai, kafin Abba yace “saida safe hakanan, karda ki k'are masa
kud'in, ki gaidashi”.
Cikeda farinciki namusu sallama, da
cewa zankirama gobe.
Na yanke wayar ina murmushi, Munubiya na
kira itama, cikin sa'a tashiga kuwa. tana kwance jikin yaa Marwan yana d'an
rage zafisa🤫, wayar tafara ring, shine yamik'o
mata, ta amsa tana kallon number, irin Special number d'in Nance, wadda zaka
ganta a tsare. (🤫bara
na Baku, amma banda matan aure 07000000000😝)⛹🏻♀⛹🏻♀.
Saida ta kalli yaa marwan ya d'aga mata
kai alamar tayi picking sannan ta d'aga.
Muryar Munaya dataji yasata mik'ewa zaune
zumbur cikeda d'oki.
Kowa yay kewar d'an uwansa, dan haka ko
gaisuwa bamu tsaya yiba muka shiga fad'ama juna yanda mukai missing. muka 6alle
hira kamar zamu ga juna tacikin wayar..
Mun d'au tsawon lokaci munayi kafin yaa
Marwan yasamu dole yin sallama, wayar ya kar6a ya jawo matarsa ya rungume,
zatayi magana ya d'ora yatsansa a bakinta alamar tayi shiru tareda yanke wayar
ko sallamar arzik'i bamuyiba.
Inajin sukur-sukur d'insu ta wayar, dan haka
na tuntsure da dariya ina fad'in oni su yaa marwan Ashe dai ashe?....😂🤭.
Number Fauziyya na gwada itama akashe,
nace lallai amarci yayi dad'i kenan?, itama Ayusher na kira number busy, 'Yar
tara, nasan tanacan itada khamees ana soyewa.
Feena ma wayarta Switch up, nad'anyi tsok'i
na ajiye wayar Na tashi domin yin shirin barci, dan yau ina cikin farin ciki,
tunda naji muryar families d'ina.
Tun bayan fitar Munaya kam Galadima
yafara jin canji a jikinsa, a hankali yakejin wani feelings na bijiro masa,
kamar wasa abufa yafara tsamari, tun yana basarwa har mamaki yafara kamashi,
shin wai mike faruwa ne dashi haka? bazaice baya sha'awa ba, yanayi sosai, dan
wani time d'inma saiyasha tablets, ko allurar kwantar da sha'awan, amma baita6a
jin irin na yauba, k'arfin sha'awarsa yasashi katange kansa daga dukkan abinda
zai iya zurmasa ga halaka har yazama hanyar tsanin aikata zina. duk da jiya
yad'ansha wahala saboda abinda yafaru tsakaninsa da yarinyar can duk da shi yayine badan yaji
wani abuba, amma Abu yaso zamar masa Matsala a yinin gaba d'aya, sai dai tunda
yaje yay allura sai nutsuwa tazo masa.
Dauriyarsa ce take Neman zuwa k'arshe,
sai kawai jikinsa yafara rawa, da bin bango yashiga bedroom d'insa, drowan gefen
gadomsa yabud'e yad'iba drugs kusan uku ya watsa a baki, ruwa ya d'auka frigate
ya korasu suka wuce.
Humm abanza wai man kare, maimakon yaji
sauk'i saima abin ya k'aru. yadawo falo saman doguwar kujera Yakuma kwanciya
bayan ya kashe AC n gaba d'aya, Dan k'ara dulmiyar dashi yakeyi.
Nima d'in agareni kusan hakane,
kad'an-kad'an nafara jin tsigar jikina Na tashi.
Kamar wasa ina wanka sai Abu yafara
shan kaina, abinda bansan ma'anarsa ba yafara bin jinin jikina da 6argo, na
lumshe idona ina hango abunda yafaru tsakani na d'azun da Galadima, duk dani
wahala ma nasha, wani feelings na tashin hankali yafara bijiromin, idanuna
harsun sauya kamanni, da k'yar nayi wanka nafito, ko towel d'in ban cireba na
saka hijjab Na d'au wayarsa Na fita, koda nayi sallama a k'ofar falonsa banji
ya amsa ba, nayi har sau uku shiru kakeji, shikam yana kwance yana jina, amma
bakinsa yakasa koda motsawa barema ya amsa min, saima muryata dake sakashin jin
wani zirrr, duk sanda nayi sallamar sautin muryata na motsawa da tsigar jikinsa
ne, gaba d'aya gashin jikinsa ya tashi.
Jin shirun yayi yawa natura k'ofar kawai
Na Shiga abuna, azatona ko barci ya d'aukesa kokuma bai jiniba.
Ganinsa kwance saman doguwar kujera yasa
gabana d'an fad'i, gawani iri dana kuma ji jikina yayi, dagashi sai boxer da
vest, hannunsa d'aya dafe da mararsa, d'ayan kuma dafe da kansa, kauda kaina
nayi daga kallonsa saboda tsorata da ganinsa a ainahinsa, gaskiya ba k'aramin
namiji bane guy d'innan, duk kunya ta isheni, ban ta6a ganin namiji ba a haka,
yo samarin gidanmu basa zama haka. duk tunanina barci yakeyi, na ajiye wayar
saman cikinsa a hankali, kamar yanda naga d'ayar a ajiye, caraf ya rik'e
hannuna da hannunsa daya dafe kansa, tsoro yakamani lokacin daya bud'e idonsa yana
kallona, jazur idon yake abin tsoro. Muryarsa a matuk'ar sanyin daban ta6a
Sanin yana da shiba yace “mi zakiyi?”. idanu na nad'an waro waje cikin tsarguwa
nace, “mi zanyi kuma? wayarkace fa na ajiye maka”. ajiyar zuciya yad'an sauke,
ya zuba min idanu batareda yasakimin hannunba. Gaba d'aya jikina yakuma
rikicemin, jima nake tamkar Na fad'a kansa saboda abinda nakeji, ganin karna
aikata abinda zanzo ina nadama saina zare hannuna dad'an k'arfi, jikinshi babu
kuzarin kirki, danhaka yasaki hannun kawai, nikuma na juya nafice daga d'akin
da saurina.
Lips d'insa ya cije da matuk'ar k'arfi
kamar zai huda, Yakuma dafe mararsa datayi tamkar zata fashe masa, kai bazai
iya daurewaba, domin zai iya mutuwa wlhy, ganin yarinyarnan kuma Yakuma birkita
tunaninsa. idonsa yarigada yarufe, ya manta matsayin Auren Nasu, duk da
gargad'in da wani sashen zuciyarsa yake masa akan alk'awarin daya d'auka,
burinsa kawai ya sauke wannan nauyin kozai samu nutsuwa, da k'yar yamik'e ya
fice zuwa d'akina.
Nikam INA zuwa na zube saman gado bayan
Na zare hijjab d'in, dagani sai towel, marata data d'aure tamkar zata fashe na
rik'e da hannu biyu Ina hawaye, wai wannan wace iriyar masiface ne?, nashiga
uku ni Munaya, mike shirin faruwa dani ne?..
“innalillahi” kawai nake iya karantawa
saboda tashin hankali, jikina harwani rawa yakeyi, ko kad'an bansan Galadima ya
shigo d'akinba, dan nafad'a wata duniya ta daban, babu zato kawai naji mutum
yafad'o jikina yana sauke numfashi wani na k'orar wani, wata wawiyar runguma
yamin tareda matseni ajikinsa gam, kai kace cikinsa zai maidani.
Humm maimakon na turesa sai nima nakuma
k'ank'amesa, banyi k'asa a guywaba wajen maida masa murtani abinda yakemin..
Daga ni harshi kowa yafita hankalinsa,
dan idonmu yarufe bamusan mi Muke aikatawa bama.
Hankalina bai nemi dawowa ba saida naji
Galadima na neman kasheni, duk da inajin lokacin dayake jero addu'a amma ban
dawo dai-daiba, nayi nisan da banajin kira kam, saida mai gayya mai aiki ke
shirin faruwane na farga.
Ina yayi Nisan da bazaiji kiranaba balle
kuka da magiyata akan karya cutar dani, yatuna alk'awarin daya d'auka please,
baimasan inayiba, duka, cizo, yakushi, babu kalar da ban masa ba, amma bawan
ALLAH nan saida yamin biji-biji, dukkan fushinsa na shekarun baya saida ya
fanshe a wannan daren.
Nayi kuka harma ba'a jin sautin fitarsa,
a jama'ar gidanmu kuwa ai mutum d'ai-d'aine ban kiraba, duk tsanar innaro
danayi ranar saida nakirata ta taimakeni (🤣Munaya anga idi😝).
★★★*★*★*★★★
A can kuwa muftahu Na fita sukaci karo da
Harun, kallon-kallo akama juna, cikeda tsantsar mamaki Harun yace, “wai Muftahu
mikake shiryawa ne?”.
Kallon rainin hankali muftahun yamasa,
yagyara tsayuwarsa yana wani murmushin da bakowa zai iya fassara Shiba, “ban
fahimci tambayar takaba, amma mikake nufi?”.
Harun ya d'an hararesa, “Muftahu karka
rainamin wayo, tabbas nasan ni da kai duk abokan Galadima ne, bayan zumunta
dake a tsakaninmu, amma shige masan dakake fiye da kowa a wannan tsakanin yana
bani mamaki”.
Muftahu ya ta6e baki yana wani basarwa,
kafin ya kalli Harun a wani yanayi, “Harun kana sakamin idone kenan a
al'amurana? humm bazance ka bariba to, kacigaba, ni da kai d'an halak ka fasa,
idan kaga dama ka kunna wutar jefani bayan kaga abinda zanyin, wannan ba
damuwata baceba, inar Na cimma burina right?”.
yana gama fad'ar haka yabar wajen kawai.
Yayinda Harun yabishi da kallo kawai tamkar wani soko, a zuciyarsa yana tunanin
mi Muftahu ke shiryawa ne akan Galadima? tun kwanaki yakeson fargar da Galadima
illar kusanta Muftahu a jikinsa, amma abin kamar wani tsafi, da Zarar sun
ke6ance da Galadima to saikaga Muftahu a wajen, saikace mai gani har hanji,
kenan yakamata yasake shiri akan Muftahu?.
Da wannan tunanin shima yashige mota yabar
gidan, saikuma Galadima ya fad'o ransa, waya ya d'auka ya kirashi, amma saiyaji
Number busy, hakanne yad'an sakashi nutsuwa, a tunaninsa ko Galadima yana
wayane dasu Momma. (A time d'in Munaya Na waya da phone d'in Galadima).
★★★*“*“★”*”*★★★
Yanda ta tashi a firgice haka shima ya
tashi, jikinsa ya jawota ya rungume saboda waige-waige da takeyi tana kwala
kiran sunan MUNAYA!.
jinta a jikinsa saita d'an sami nutsuwa,
cikin kuka tace, “yaa marwan mike faruwa da 'yar uwata ne?, nayi mafarkinta
cikin mawuyacin hali tana kuka da kiran sunana Nazo Na ceceta”.
“sorry baby, ki kwantar da hankalinki
mafarki ai ba gaskiya baneba, maybe shaid'anune kawai suka taswuranta hakan a
gareki, amma ba d'anzun kuka gama wayaba? kofa awa 5 ma ba'ayiba da gama wayar
taku?”.
“hakane yaa marwan, amma acikin awa 3
wani Abu bazai iya faruwa ba? ka kiramin ita please naji?”.
“no kiyi hak'uri, dare yayi gaskiya,
babu yanda za'ayi mu kirata a wannan time d'in, k'arfe 1 fa ta wuce, 2 ma
saura, karkuma ki manta tanada miji itama yanzu. Muyi addu'a ALLAH yasa
alkairine, da safe saiki kirata ko?”.
Cikin share kwalla ta d'aga masa kanta,
a hankali ya kwantar da ita a jikinsa bayan shima ya kwanta, yad'an furzo huci
kafin yakai hannu yana shafa kanta tareda sumbatar goshinta yacigaba da bubbuga
bayanta a hankali, kowa yana yin adu'a, ahaka barci ya kwashesu, duk da sun
dad'e basu koma ba, musamman ma Munubiya da mafarkin yak'i barin ranta, Dan
takasa yadda Munaya Na cikin k'oshin lafiya gaskiya, ka wai dai dan batada
yanda zatayine ta hak'ura.
*****★★★*★★★****
Hawaye kawai nake iya zirarwa, amma
kwakwkwaran numfashi bana iyawa saboda jigata, zan iya danganta abinda Galadima
yayimin da fyad'e, dan baya cikin hayyacinsa ko kad'an, kamar yanda nima nawa
ya gushe daga farko nabashi gudunmawa. (Nasan duk mai hankali ya k'iyasta a
yanda Galadima ya zomin zai tabbatar dolene na jigata d'in😭).
Tunda yasamu nutsuwa yana gefena a
kwance kawai, a hankali memory d'in brain nasa ke tariyo masa abinda ya aikata
tamkar a mafarki, ya bud'e idonsa da hanzari akaina, domin kuma gaskata abinda
yafarun, shin da gaskene ya aikata? “innalilahi” yashiga maimaitawa dan ganina
kwance a gefensa ina hawaye, daganin yanda nake a kwancen ina fidda numfashi
d'ai-d'ai kasan nagama jigata, yabi d'akin da kallo cikin tsantsar takaici,
yaushema shikam yazo d'akinnan? “Hasbinallahu wa ni'imal wakil. mike faruwa
danine ni Sameer? wace k'addarace kuma ta kutsoma rayuwata? yanzu nan ni Muhammad
Sameer ne da wannan d'anyan aikin? miya samu tunanina haka?.......”
Tunaninsa ya tsaya cak lokacin daya
jiyo dasashshiyar muryata ina kiran innarmu da Munubiya, muryata a raunane,
runtse idanunsa yayi tareda mik'ewa zaune da k'yar, dan jikinsa gaba d'aya yayi
week, ga wani masifaffen ciwo da kansa keyi. da k'yar ya iya kuma bud'e
idanunsa a kaina, babu shiri yakuma runtsewa saboda tsorata da ganin yanda
yamin, hawaye kawai yaji suna neman zubowa a face nashi saboda shi mutum ne mai
tausayi, bayason yaga ancutar dawani bare kuma shi da Kansa ya aikata, jarumtar
had'iyesu yayi tareda kuma bud'ewa, yazubama fuskata ido batareda ya iya cemin
uffanba, yama rasa ta inane zai fara shikam, mizai fad'amin kuma a yanzu Na
yarda dashi? mizai cemin shikuwa?.
Innarmu dana sake ambata murya a
sark'e yasakashi saurin kallona, baisan yarik'o hannuna ba ya rumtse anasa,
la66ansa sai motsawa suke amma yagaza yin magana, shi yanzu ma baisan wane irin
taimako zai baniba, bai ta6a irin hirarnan dawani abokiba balle yace yasan ya
zaiyi, bai ta6a aikata zinaba, zai iya rantsuwa da Ubangijin daya haliccesa bai
ta6a ta6a jikin wadda ba muharramarsa ba, sai ita Munayar daya d'auketa randa
yasa a sato masa ita. Kuma ko muharramar tasa bazai wuce yarik'e hannun taba
shima ba kowaba wlhy, inhar kacire Samha Momma Aunty Mimi ko Mom, sukad'aine
mata Muharramsa da zaice yanada shak'uwa ta musamman dasu, amma shi ko yaran
masarautar nan bama kowacce zai iya ambatarta da sunanta dai-daiba.....
Rashin ya cika da tashin hankali, kukan
danakeyine yasakashi waigen phone nashi, baiga komaiba, tunawa yayi ba d'akinsa
baneba nan, ya saki hannuna ya sakko agadon bayan ya suturta jikinsa, jikinsa
gaba d'aya ya mutu, ahaka da sand'a yakai falonsa, wayarsa dake a saman kujera ya
d'auka, to inama zai dosa shikam? wazai kira akan wannan abin kunyar daya
aikata? tunanin bincike a network ne ya
fad'o masa a rai, maybe yasamu bakin zaren, Google yashiga yay d'an rubutu
yahau Searching, amamakinsa kam saigashi sun bashi, saiya kuma wata tambayar,
nanma yasamu amsa dai-dai, “Alhmdllh” yafad'a yana mik'ewa rik'e da wayar.
Inda yabarni ya iskeni, Toilet yawuce
kai tsaye, yayinda nabishi da kallon tsana, nikad'ai nasan minakeji akansa,
ayanda nakeji ko wuk'a aka bani zan iya fidda masa hanji waje, tabbas yanzu
nakuma yarda banida wayo, yanda tun farko Na yarda da maganar wai auren
yarjejeniya mukayi da Wanda yafi k'arfin ajina da matsayina, inma banda wauta
irin tawa tayaya mutum kamar Galadima zai nemi kulla aure dani?, Na manta namiji
zai iya komai domin cikar burinsa, k'ilama *AUREN 'DAN'DANE* yayi dani, ai
sainaji wani kuka ya tokaremin mak'oshi, har ina neman shid'ewa.
Kamar yanda yaga sunsa ya had'a ruwa
mai zafi-zafi, sannan yafito, ficewa yakumayi, babu dad'ewa sosai yadawo yakuma
shigewa toilet d'in, ni dai idonama Na rufe gaba d'aya, dan bana k'aunar
ganinsa.
Jinai kawai an kama hannuna ana
k'ok'arin tadani zaune, wata azaba naji har cikin kwalwar kaina, saina fashe
dawani marayan kuka Wanda yasakashi saurin sakina nakoma Na kwanta.
Runtse idonsa yayi saboda jin addu'ar
danake jero masa ta neman sakayya ga ALLAH tsakanina dashi, wani bai ta6a masa
makaman ciyar addu'ar nanba, amma gashi matarsa ta sunnah tana masa, duk da
yasan hak'in sane ya k'ar6a agareta hakan bai hanashi jin bak'in cikiba, dan
aganinsa inada hujjar masa addu'ar da tafi wannan muni, tunda Bahaka mukayi
dashiba.
Cikin tsantsar damuwa ya d'aukeni zuwa
bayin, yayinda nikuma nake kuka ina fad'in ya saukeni, duk da a hankali nake
maganar yana jina.
Ba k'aramin daga mukayi dashiba wajen
taimakona, harda cizonsa nayi a damtsen hannunasa, aiko yacizu wlhy, dan
hakwarana saida suka huda lallausar fatarsa, (to dama ba wahala tasaniba fatar)
amma a mamakina sainaga ko gezau baiyiba, kuma Na tabbata yaji zafin cizonnan,
saidai bansan dalilinsa Na daurewaba, da k'yar ya samu nayi wankan tsarki kuwa,
dan saida yakusa makeni ma dan haushi sannan nayi, harya dawo dani d'akin ban
daina jera masa ALLAH ya isaba a fili da kiransa mugu azzalumi.
Duk da kalamaina suna sukar zuciyarsa haka
yadake yanuna tamkarma baya jina.
Bashida maganin dasuka rubuta akan
matsalata, sai dai yanada Wanda zai iya taimaka min kafin zuwa Safiya ya nemo
wancan.
Haka yakawo min maganin da tea wai nasha,
harara kawai Na zuba masa Na maida kaina Na kwanta batareda nako motsaba balle
yayi zaton zan tashi.
Shima baice komaiba yakamani ya tayar,
hannunsa da k'irjinsa nashiga bugu, ina kuma kaimasa cizo, amma k'arfin ba
d'ayaba, bai barniba saida ya tadani, sannan ya wani ci uban Magani fusakarsa
amatuk'ar murtuke, yace “kinsan ALLAH koki kar6a kokuma....humm”.
Yanda yay maganar kuma sai tsoro ya
kamani, Na watsa masa harara kafin nabud'e bakin, da kansa yabani shayin,
sannan yabani magani. mugun Ashe harda Na barci, cikin mintuna k'alilan barci
yay awon gaba dani.
Sai lokacin ya samu damar sauke ajiyar
zuciyarsa tareda dafe kansa dake tsananin sara masa. Duk yanda yaso yayi
tunanin ya akayi hakan tafaru yakasa, saboda matsanancin ciwon da kansa kemasa,
dole yamik'e zuwa d'akinsa, shima ruwan mai zafi yay wanka dashi sannan ya
tsarkake jikinsa ya fito, Magani yasha ya haye gado ya kwanta shima, yasan
bazan farkaba a nan kusa.
Maganin barcin da shima yashane yasaka
barci suresa shima.
★★★★★(())★★★★★
Tun daga shigar Muftahu wajen
Galadima har zuwa sanda ya zuba Abu cikin milk d'in Galadima lokacin daya Shiga
bedroom d'insa d'aukar Abu suna kallo, har ya girgiza ya ajiye kwalin da sauri
inda ya d'auka, fitowar Galadima zamansa
da files d'in daya bama Muftahu Na masu buk'atar taimako a asibiti da aka kawo
masa zai biya, har shigowar Munaya falon Galadima da fitar Muftahu, zamanta da
kar6ar wayarsa zuwa fitarta itama, yanda Galadima yafara fita hayyacinsa har
dawowar Munaya sashen takawo masa wayarsa, fitarta dakuma bin bayanta dayayi,
hankalinsu ne yad'an tashi ganin yadad'e bai dawoba, gakuma a yanayin daya
fita.
Hakanne yasaka aka turo wasu mata biyu
da kayan fruits wai sukawoma Galadima domin suyi CID d'in yana ina?.
Sai dai sarkin k'ofa kuma yace saiya musu
iso, kamar yasani saiya rufe k'ofar ta ciki sannan yanufi sashen Galadima d'in,
yayi sallama tafi sau 15 amma babu amsa, ya tabbata da yana kusa daya amsa,
komawa yayi yace musu ai yamayi barci, su koma dashi kawai, babu magiyar dabasu
masaba yak'i bud'e musu, dan yarigada yasan komai Na kitumurmurar gidan, sannan
yasan Galadima bayacin abincin kowa a masarautar, ko ankawo su yake bamawa,
idan kaga yaci abincin dawani yadafa a masarautar to tabbas aunty Mimi tana
k'asar, sunzo tare kotazo ta iskeshi. dan haka yahanasu shiga, harma yad'an
tsargu da tunanin kawai wani Abu a k'asa ganin sun jajurce dason shigar.
Ransu a 6ace sukabar wajen, inda aka
aikisu suka koma, sun Isar da abinda yafaru.
Hakan kuma yakuma tada hankalin masu Aiken
nasu, domin an ruguza musu plan d'insu kenan...........✍🏼
🤔hummmm.⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀
_ko Yaya
za'a kwashe tsakanin Galadima da Munaya da safe kuma🤣🤭, Munaya team amin afuwa🥳🙏🏻ku kora da wanan🍾🍺🍻🥂🍷🥃🍸🍹😂😝._
🏇🏻
*_Masu
karatu nasan kowa yamatsu yasan tarihin masarautar su Galadima, insha ALLAH
zakuji, inason muzo ga6ar daya kamata kuji d'inne insha ALLAH, saura k'iris😄👌🏻._*
Barkanmu da
dawowa😄✋🏻.
*_ALLAH ka
gafartama iyayenmu_*😭
*_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA
KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
👉🏻2⃣6⃣
..........Da kuka na farka, duk da naji
dad'in jikinna kuwa, dan banajin azabar kamar jiya, tashi nayi zuwa toilet
danna d'auro alwala, na tuna labarin da wata k'awarmu ta ta6a bamu akan yanda
taita ciwon jiki, saida mijinta yata mata ruwan zafi a ranar, ruwan mai d'an
zafi na had'a na shiga ciki, nasha zafi kuma naji dad'i, amma inajina kamar ba
a dai-daiba maganar gaskiya, haka dai nasamu nayi sallar asubahi, ina tsaka da
sallar yashigo da nufin tadani, ganin na tashi ma saiya juya yafice abinsa zuwa
masallaci shima.
Koda na idar kwanciya nayi saman abin
sallar nacigaba da kuka na, ina kuma tunano abinda yafaru a jiya tamkar a films
ko novels ko mafarki, babu abinda zuciyata keyi sai tsinemar, a yau d'inan
dolene saiya bani Sakina natafi gidanmu, nafasa auren Contract d'in ma, da dai
na zauna da mugunnan gwamma nakoma gidanmu nacigaba da rayuwa dasu innaro
yafimin....
Tun
d'azun yana tsaye a kaina, tausayina yakamashi, dan yasan shine silar kukan
mawa, bayason zalunci ko kad'an, amma saigashi shine da aikatawa kuma, zama
yayi a bakin gadon, cikin muryar nan tasa mai kama da anmasa tilas yace “tashi
zaune muyi magana”.
“baza na masa, a zuciyata nace bazan
tashiba mugu kawai, bakada abinda zaka fad'amin na yarda, azzalumi, dama abinda
ka shiryawa rayuwata kenan? Dan kaganni d'iyar talakawa banida k'arfin gogayya
da kai, tabbas nayi kuskuren yadda da Wanda shikansa ma bai gama yadda da
kansaba, ALLAH ya Isa wlhy tunda ka ketamin mutunci har abada bazan yafe
makaba, kullum cikin sallata saina sakoka da neman sakkaya ga mahaliccina akan
zalincin dakami.........
A fili kuma nace, “kagama zalintata kazo
kanamin mazurai da mulki, ank'i tashin”. a hankali nake maganar banyi tunanin
yana jinaba, sai tsawa kawai naji ya dakamin
“k!!!!!”.
Yafad'a cikin daka tsawa, Ashe tunda nafara
maganar ya rumtse idanu saboda yanda Kalmar zaluncin suke sukarsa a zicciya,
ban ta6a ganinsa a wannan yanayinba, a cikin fad'a yace, “Niba azzalumi baneba,
zina nayi dakene!? dazaki dunga aibantani damun duk furucin dayazo bakinki? to
bara na tuna miki idan kin manta, SADAKI na biya na auroki! tun jiya kike
fad'an magana amma na shareki, ni sa'an kine? wlhy idan bakiyi wasaba zan koya
miki hankali! danaso muyi magana ki saurareni mana kiji mizance?.........”
Zumbur namik'e zaune, duk da azabar da
k'asana kemin, na kallesa ido cikin ido ina zubda kwalla nace, “bakada abin
fad'a shiyyasa bazan saurarekaba, bar ganina 'Yar talaka bana d'aukar raini
wlhy, mina maka ne? miye had'ina da kai kaketa bibiyar rayuwata da bala'i,
tunda na had'u da kai ban kuma samun nishad'iba, wlhy bazan yafe makab.......
Jikake bamm! ya make bakina da bayan
hannunsa, cikin zazzaromin ido yace bazaki nutsuba Ashe?”.
Naji zafi sosai, dan haka nafashe dawani
marayan kuka mai ban tausayi, ga wani bala'in tsoronsa daya kuma shigata,
maganar ma a tsorace dama nayita, Dan tsabar bala'i na hango cikin idonsa Dana
kallesa.
Kansa ya dafe da hannu, jiyake tamkar ya
tariyo jiya a rayuwarsa ya goge dukkanin abinda yafaru
Ganin bazan sauraresan ba da gaske
saiya tashi ya fice yabarmin d'akin.
Nakuma 6arkewa da kuka.
Koda yafita a falona ya zauna, ya dafe
kansa daya koma masa ciwo k'asa-k'asa yau, tunaninsa yafara komawa baya daga
jiya zuwa yau, shin miya sakashi wannan matsananciyar sha'awar ne wai? dan bai
ta6a jin makamancin feelings irin na jiya ba, da sauri yamik'e yanufi sashensa,
a falo ya tsaya, ya d'auki kwalin hollandia fresh milk d'in jiya yana dubawa,
shi dai yasan shine last abu daya sha a jiya, to kenan koma miye daga cikinsa
yake?. to amma ai ba yaune yafara shan fresh milk ba a gidannan balle yace kuma
shine. kwalin ya ajiye yakuma dafe kansa, gaba d'aya tunaninsa ya kulle, dama
shi indai yana cikin 6acinrai to komai nasa birkicewa yakeyi, dolene saiya
kwantar da hankalinsa zai iya kamo bakin zaren. a kujerar Yakoma ya kwanta, ko
azkar yakasayi yau, babu dad'ewa barci yakuma kwasheshi anan.
Itama Munaya daga kuka barci yay awon gaba
da ita a wajen.
Har Samha suka kawo abinci duk barci suka
Tatar sunayi, tasan halin Uncle Sam shiyasa bata tadasu ba, kad'an daga aikinsa
ya mammaketa a safiyarnan.
Su duka sai wajajen 12 suka farka,
kowanne yatashi da damuwarsa.
Tunda nayi takun farko nakuma tabbatar da
akwai matsala, dan ruwan zafin da yaymin jiya kad'ai ya isa na daina jin
zafinnan irin haka, balle kuma nima nayima kaina da safennan, amma maimakon
k'asana yabar zafin saima zugi yake k'arawa, gashi idan nashiga ruwan, zafi
nakeji sosai.
Yanda nake takawar ina hawayene
yabashi mamaki, dan aganinsa yakamata nasamu sukuni saboda yanda yamin jiya.
bansan yashigoba, maganarsa kawai naji..
“Wai mike faruwane? Ko dai kinji ciwone?”.
Wata uwar harara dataso bashi dariya na
zuba masa, amma saiya danne baiyiba, takowa yayi har inda nake yakama hannuna
na fisge, ya d'aure fuska shima yana hararata, “k! Wlhy kinutsu kafin na canja
miki kamanni”.
“yo kammani na yaushe kuma zaka canja
min? bayan Wanda ka canja min yanzu? dama haka kake? a fuska kamar babu ruwanka
amma sai zalunci taf zuciyarka”.
Idonsa ya runtse dan bayason Kalmar
zaluncin nan danake jifansa dashi, jinai kawai an fusgoni an zaunar a bakin
gadon, nakuwa fashe da kuka ina fad'in “wayyo zafi, munubiya Azalumin nan zai
kashe miki ni”.
Ko kallona baiyiba yafice, ina nan ina
kuka saigashi yadawo da wayarsa a hannu, ya zauna saman sofa batareda ya
kalleninba, bashida mafita saita kiran Akash, dan yanason sanin minene matsalar
datake sakani wannan kukan da complain d'in zafin, yasan koya tambayeni ba
fad'a masa zanyiba..
Da turanci suka gaisa, amma da zaiyi
tambayar saiya canja harshe zuwa yaren daban saniba.
Akash yace saidai idan ciwo taji, dan bai
kamata ace tana Complain zafi irin haka ba, zataji ciwo kam amma bawai yanda
yake nuna masa yanzun ba.
Galadima ya gyara zamansa sosai yace “to
ai na sanar maka fyad'e akama yarinyar fa”.
Akash yace “zata iya kai shekara nawa
yarinyar?”.
'Dago ido yayi ya kalleni kafin ya janye
yana fad'in “Maybe 19years ko 20 kawai”.
“ai bama yarinya baceba can sosai, inaga
taji ciwone gaskiya, yakamata doctor ya dubata gudun samun matsala, amma kabada gudunmawa a hukunta Wanda yay abunnan
my man, please ka kwatarma yarinyar hak'k'inta wajen azzalumin nan”.
lips d'insa kawai ya cije maganar Akash na sukar zuciyarsa, da Akash yasan
shine yay aika-aikar dabai ce hakaba. sallama sukayi ya yanke wayar, saikuma
yafara tunanin doctor d'in dazai nemo ya dubani, dan bashida damar fita dani a
gidan yanzun.
Can doctor Hafsat ta fad'o masa a rai,
ita kad'ai zai iya aminta tasan matsalarsa, dan ya yarda da ita sosai, yasan
zata masa k'yak'yk'yawar fahimta.
Kiranta yayi bayan sun gaisa cikin mutunci
ya fad'a mata matsalar ta yanda zai iya, dukda ya 6oye mata wacece keda
matsalar ta fahimcesa, d'an murmushi kawai tayi tana girgiza kai da tausayin
yarinyarnan data shiga hannun Galadima, duk abinda zata buk'ata tagama had'ashi
sannan ta fito, matsalar gidansu data Sani yasakata yin shiri tamkar ba doctor
ba.
Shiru d'akin yayi, sai kukana dayake
fita a hankali, shikam ya zubamin idanu yana kallona k'asan ido, zaune yake
k'afa d'aya akan d'aya, ya jingina da kujera, saika rantse idonsa a rufe yake,
amma yana kallonane ahaka.
Bayan doctor Hafsat tazo k'ofar fada
saita kirashi, dan baza'a barta kai tsaye tashigaba.
Ina kallonsa ya fice bayan ya yanke wayar
daban San dawa yakeyinta ba.
Kusan mintun 20 saigasu sunshigo dawata
mace, ba yarinya baceba can gaskiya, zasu iya zama sa'anni da Galadima d'in,
dan haka na tashi zaune na gaidata cikin girmamawa.
Ita kuma ta amsa cikeda fara'a.
Kallon Galadima tayi dayake tsaye yana
kallonmu, “ranka ya dad'a kozaka bamu wajene”.
Murmushi yad'anyi yana fad'in babu
damuwa.
Yana fita matar ta zauna kusa dani a
bakin gadon, fuskarta d'auke da murmushi tace, “sunana doctor Hafsat Abu,
friend d'in Galadima ce tun a primary school”.
Murmushi nayi mata na yak'e kawai.
Takuma gyara zamanta tana kallona, please
dear karkiji nauyina, ki fad'amin matsalarki kai tsaye, dan ba'a wasa da wannan
matsalar, takan zama babban Abu anan gaba ga d'iya mace”.
Kai na jinjina mata ina hawaye, sannan
nace “inajin zafin wajen sosai”.
“ok kozaki iya kwanciya nagani”.
Ido na waro waje a tsorace, sai kuma nayi
k'asa da kaina saboda kunya.
Tayi murmushi tana kama hannuna, “karkiji
kunya akan lafiyarki dear, please ki daure kinji”.
Kai kawai na gyad'a mata sannan na
kwanta, babu yanda zanyi dole na yarda ta duba, kanta kawai ta girgiza da
mamakin Galadima, saikace Wanda ya kusanceni da k'arfin tuwo?, ai wannan kam da
wani doctor d'inne saiya yima Galadima fad'ama wlhy, dan ko kad'an bai bini a
hankaliba, amma ciwon daya jimin bazai zama mai cutarwa ba insha ALLAH.
da kanta yanzu ta had'amin ruwan zafi
tazuba wasu magani, sannan ta taimakamin har zuwa bayin ta nunamin yanda zanyi.
ban cutar da kainaba na nutsu nayi komai yanda tace, dukda inajin zafi kuwa,
bayan nafito saina sameta zaune ta gyara gadon tsaf, gakuma abinci a ajiye, da
alama Galadima ne ya kawo, tsareni tayi da lallashi naci abincin ma yanzun,
sannan tabani magunguna nasha, ta kalleni da murmushi, “ALLAH yak'ara lafiya
gimbiyarmu, indai zaki cigaba da kulawa kamar yanda na nuna miki insha ALLAH
nan da 2days zaki dawo normal, ga drugs d'inan saikina sha, shima wannan cream
d'in kina matsi dashi awajen a koda yaushe”.
Kaina na jinjina mata sannan nace “ nagode
Aunty”.
Sallama tamin tafice.
A falo ta iske Galadima, bayan tamasa
bayanin yanda yakamata a kula dani saita kallesa cikin tsokana, “ranka ya dad'e
kafayi 6arna gaskiya, Shifa wajenan ba a nuna masa k'arfi, please a kiyaye”.
Murmushi kawai yayi baice mata komaiba.
rakiya yamata tareda mata alkairi sannan
yadawo.
A kwancen data barni ya iskeni, zama yayi
gefen gadon yad'an kalleni ya janye idonsa “yaya kikeji yanzun?”.
Baki na turo masa, amma ban tankaba.
shima bai damu da amsawar tawaba, ya basar kawai ya d'akko wata maganar.
“nasan babu abinda zan fad'a ki yarda
dani tabbas, sai dai zankuma maimaita miki SAMEER BAYA ZALUNCI, koda wasa ban
ta6a kawo zan aikata hakan agarekiba har kibar k'ark'ashin kulawata, bansan
miya shiga kainaba a jiya”.
Kallonsa nayi ina hawaye da takaicin
maganarsa, nace “bakasan miya Shiga kankaba ka d'auki fresh milk kabani? bayan
kasan mika zuba”.
Shima kansa ya d'ago yana kallona,
cikeda k'asaitarsa yace “ban fahinceki ba, mikike nufi? dan ina son na kusance
ki sainayi amfani da wani abu? da hakan naso daret zanzo gareki tunda nasan
nabiya sadaki ai, tunda ba tsoranki zanjiba ko?”.
“dama ai bazaka fahimceni ba tunda
Kasan ka aikata ai, kuma ai alk'awarin zama tamkar abokai kamin ba irin wannan
ba”, na had'e hannuna alamar roko🙏🏻 ina
kuka nace “dan girman ALLAH ina rok'onka kabani Sakina a yau natafi gidanmu,
wlhy nafasa auren Contract d'in, koma waye yayi abun ni na yafe masama, kawai
ka sallameni”.
Yama rasa mizai cemin shi, ajiyar
zuciya yad'an sauke, kafin ya cije lips nashi, “shikenan, zan miki yanda
kikeso, amma kibari ki warke, bai kamata ki koma gida ahakaba”. ‘yana gama
fad'ar haka yatashi yafice batareda yaji amsa taba.
Duk da naso yabani sakina a yau, amma
zanyi hak'uri na warke d'in kwana nawane.
******
Yinin yau
haka mukayishi duk zukatanmu babu dad'i, Galadima kam ai ciwon mara saiya nemi
dawo masa sabo, jiyayi kawai yana sake buk'atar kasancewa dani, haka yayta
dannewa har zuwa dare, dan bazai kuma yarda yin gangancin nanba. ganin yana
neman mutuwa yay shiri a gaggauce yafito domin zuwa hospital.
Tunda yafito suke zubewa gaisheshi,
hannuna kawai yake iya d'aga musu, dan kallo d'aya zaka masa ka tabbatar yanada
damuwa, da sauri sarkin mota yazo yabud'e masa ya shiga, suma dogaran dakan
bisa idan zai fita sai duk suka taso.
Tundaga fitarsu gidan Muftahu na
kallonsu, yad'an murmusa kawai abinsa. (🙄wlhy Reader's suka kamaka zaka gane bakada wayo😡)
Shi kad'ai yasan azabar dayakeji a
jikinsa, yana kwance cikin kujerar ne sai faman cije lips yakeyi.
Tunkan sarkin mota ya tambayama ya sanar
masa asibitin da zasuje.
Sarkin mota ya amsa cike da girmamawa da
tausayin shugabansa, dama shi tunda yaga yafito ya fahimci akwai matsala.
Tun amota yakira wata number yana
tambayarsa ko yana asibiti?. Dr Jalal ya amsa da eh yana nan.
Yanke wayar yayi kawai baisake cewa
komaiba. Dr jalal yabi wayar da kallo yana mamakin Galadima da halinsa, kiransa
yakuma yi shi dan bai fahimci inda maganar tasa ta dosaba. sai dai harta yanke
bai d'aukaba, yana k'ok'arin sake kira yaji ana Knocking d'in k'ofar.
Amsawa yay da yes tareda izinin shigowa.
Wani dogari ya bud'ema Galadima k'ofar
yashiga, da hanzari Dr Jalal yamik'e yana murmushi da masa welcome.
Hannu kawai ya iya d'aga masa ya zauna
kujerar gaban decks d'in.
Shima Dr jalal saiya zauna, “ranka ya
dad'e lafiya dai ko?”.
Saida yaja wasu Seconds sannan yafara
ma Dr jalal bayanin damuwarsa, ya sanar masa mararsa namasa ciwo tun jiya, kuma
ada bata masa kamar hakan.
Shiru Dr jalal yay yana nazarin maganar
tasa, saida yakai aya sannan yace “ranka yadad'e kokasha pills ne?”.
Kallonsa Galadima yayi, “pills kuma?
wane irin tambaya kakemin haka?”.
“afuwa ranka ya dad'e, matsalar taka
tayi kama da wanda yasha tablet ne, mikaci na k'arshe jiya?”.
cikeda nazarin maganar Jalal yace
“fresh milk ne last abinda nasha jiya da daddare”.
“to amma bayan shi kafara jin
matsalar?”.
“kusan haka gaskiya”.
Dr jalal dai shiru yayi, dan ya
tabbatar wannan aikin desire tablets ne, amma koya fad'a dawuya Galadima ya
yarda, sai kawai yashare ya had'a masa drugs da injection yamasa, yace yad'an
kwanta na kamar 20 minutes a office d'in. bai musa masaba ya shiga inda jalal
kan huta idan yaso, saiya kwanta kawai, dan shima bazai iya tafiyarba, d'akin
ma da taimakon jalal d'in yashigo.
Ni bansan hidimar da akeyiba, dan rabona
dashi tun bayan munyi maganar saki, abinci ma tun Wanda doctor tabanine a
cikina, sai kusan 8 Samha takawo min kayan fruits dawani Abu mai dad'i daban
san mineneba😝.
Ta zauna mund'anyi hira kafin tafice. a
bakin ta nakejin wai jibi Friday zasu koma India.
Na danci abinda takawo nasha magani
nayi kwanciyata cikeda kewar 'Yar uwata dana kanyi akowanne dare.
Galadima kam bai dawo ba sai kusan 1pm,
yana shigowa sashensa yawuce yay shirin barci ya kwanta, Alhmdllh zuwa yanzu
yaji k'arfin jikinsa, sai dai zuciyarsa nata cud'a masa tunanin ina yasamo
pills? dan shima yafara yarda da maganar jalal, musamman idan ya tuno furucin
Munaya na d'azun da safe.
To kenan wani ya zuba masa bai saniba?
to amma wazai zarga shikam? duk wad'anda suka shigo wajensa a jiya amintattun
sane, Sauban, Samha, Harun, Muftahu, duk sun shigo wajensa a jiya, amma Muftahu
shine last shigowa, shiru yay yana nazari, can kuma saiya cije lips d'insa ya
lumshe idanu yana shafa gurin Dana cijesa.
A haka barci ya kwasheshi.
★★★★
Munubiya tashiga damuwa sosai akan rashin
jina a waya, takira number ta yafi sau goma amma switch up, gashi yaa Marwan ya
hanata kiran number dana kirasu a ranar, yace wai number Galadima ce bai kamata
su damesa ba.
Haka taci kukanta a yinin ranar, saikace
mara lafiya haka ta yini, zuwan su Ayusher ne ma yad'an sanyaya ranta har suka
janye mata hankali da yawan tunani, a ranar gidan suka yini cir, sunsha hira da
labarina, kowacce tana missing d'ina.
Sunce suna son zuwa amma an hanasu, wai
gidan danake ba gidan da ake zuwa any how bane ba, babu yanda suka iya haka
suka hak'ura.
*********
A gidanmu ma yau sukayi niyyar kawo min
akwatinana da abinda ba'a rasaba, amma ankira wayata akashe, wannan yasa Abba
yace abarni akaima su fauziyya nasu. ni daga baya idan an sameni akai min nawa
d'in.
Duk inda akaje da innaro ake zuwa,
kowacce ta taima gidanta kallon kwaf kenan, sotake taga gidan wacce tafi acikin
sauran 'yan uwana.
ALLAH ya taimaki munubiya lokacin dasukaje
gidanta yaa Marwan yana gidan, hakama su Ayusher.
Fita yayi yasiyo musu abubuwa yakawo,
sannan suka zuba musu girkin da sukayi, babu ko kunya suka mik'e kafafu suka ci
abinsu, to dama gidan Fauziyya ne kawai suka samu sukaci abinci, su Safara'u
kam casukai basu fara girkiba, dan ita haleematu ma ruwa wannan bata basuba,
banda innarmu akaje, dayake kowacce idan za'aje gidan 'yarta banda ita ake zuwa.
Zasu taho kuma yaa Marwan yabasu kud'in
mota, dukda kuwa a mortar Dady yaa Anas ya kaisu.
Tunda suka dawo gida aka shiga labarin
yanda aka iske gidan kowa, nanfa wad'anda gidan 'ya'yansu ba'a samu wani abun
kuzo aganiba sai suka fusata, kunsan dai halin jama'ar gidan namu🤣, wannan Abu saida yakawo rikici,
fad'a sosai sukasha abinsu, itadai innarmu k'ala bata ceba, saima ta maida
hankalinta ga girkin dare datakeyi, ga innaro sai habaici takeyi, saida gwaggo
Safiyya tazo da k'yar ta lalla6ata tafita.
Matan anguwa makwafta kam sun masa kunne
suna saurare da kwasar dariya, dan lamarin gidanmu yazama kamar na 'yan wasan
kwaikwayo.
Duk tsiyar dasukeyi dady yana gidan yana
jinsu, amma ko lek'owa bai yiba, danshi bashida hayaniya ko kad'an, balle daya
fahimci abin yashafi 'yan bani na iya d'in gidan ne, dariya kawai yayi yace
ALLAH ya k'yauta. kad'anma kenan ai, bakuga komaiba tunda yanzu kuka fara
aurarwar, kuma har yanzu da sauran 6ur6ushin amarci ga yaran harsu Aunty
khaleesa kam dake cikin watanni na hud'u da auren.
★★★★★
Alhmdllh yanzu kam naji dad'in jikina,
dan ko ciwonma banaji, sai shirye-shiyen kayana nakeyi dan yau nakeson tuna
masa batun sakina, tun shekaran jiya rabona da ganinsa, harma na d'auka baya
gidan sai d'azun da safe Samha take cemin ai tare suka fita itada Uncle Sam da
Sauban birnin gayu da asibiti zagayen marasa lafiya, sune har Asibitin
mahaukata, tace duk atsorace take ALLAH yasa kartayi mafarki.
Ni dariya ma tabani yanda take bani
labarin kamar a firgice take.
Komai nagama had'ashi tsaf, Galadima kawai
nake jira, amma abin haushin har kusan 4pm babu labarinsa, gani nayi zan zauna
jiran gawon shanu, dan haka na mik'e zuwa sashensa.
Nayi sallama yafi 7 amma babu amsa, sai
kawai natura na shiga, a zatona rainin wayonsane da mulkin ya motsa, babu kowa
a falon sai wani k'amshi dake tashi na musamman, ko ina kuma need a gyare,, a
yanda naga yanayin falon kamar babu kowa a sashen gaskiya, dan komai akashe
yake har AC, dawuya kuma yana nan kaga AC n sa a kashe, duk da haka saina d'an
zauna ina k'arema ko ina kallo, kai kace yau nafara shigowa, hotunansa da bana
gajiya da kallo naketa kallo yanzun ma, idona nacikin zageye-zagaye saina hango
wani k'aramin frame na photo, bana ganin mutanen jiki sosai dan haka namik'e
tsaye, ga hoton na isa, yana a kusurwar d'akinne ta gabas, saman wani d'an
katako da aka k'awata wajen, bayan foton akwai flower babba mai k'yau, sai aka
jigina hoton jikin flower d'in.
K'yak'yk'yawan mutum ne ajiki Wanda
kallo d'aya zaka masa ka hango tsantsar kamaninsa da Galadima, saikuma mace a
gefensa itama masha ALLAH, Galadima kuma yana satar kamanninsa da ita, musamman
idonsa ha6arsa dawasu abubuwa, saikuma wadda nake k'yautatama zaton aunty Mimi
Ce kusada matar, shima namijin ina tunanin Galadima ne, yana cinyar mutumin,
bazai wuce 5 to 6 years ba a picture d'in, Anty Mimi kuma bata wuce 10 ba, sai
tsohon ciki ajikin matar, dukda ban saniba sainayi tunanin iyayensane, duk
cikin kayan sarauta suke.
Samha ta fad'amin iyayensa suna india,
Abbansa bashida lafiya, ban wani tambayeta komaiba, iyanan naji kawai.
Hoton na maida na ijiye ina murmushi, sun
birgeni gaskiya sosai, flower d'in nabi da kallo, itama tamin k'au, gawani
k'amshi mai dad'i datakeyi, kuma nalura da dare kamar tana wuta haka. Hannuna
na kai na ta6a ganye d'aya ajiki, sainaji Ashe ta roba Ce ma, mamaki ya kamani,
banyi zaton ta roba bace wlhy, dan tayi k'yau.
Har zan bar wajen, kamar ance na d'aga
kaina saman p.o.p d'in ta jikin kusurwar sainaga tamkar CCTV camera, amma
bakowa zai iya fahimtar hakanba, domin ansata cikin tsantsar kulawa, gabanane
yafad'i, nayi azamar kauda idona tamkar ba ita nake kalloba, saina d'an gyara
zaman flower d'in kawai nabar wajen zuciyata na tsitstsinkewa, toshi miye nawani
saka CCTV camera a falonsa?, komawa nayi na zauna, zuciyata nawasu
tunane-tunane daban.
Sai lokacin tunanin koma bayanan yazomin,
abinda Nagano ya hanani lek'a bedroom d'insa, dan nasan zai iya ganin komai ta
CCTV camera d'insa.
Sai kawai natashi na fice nakoma nawa
d'akin.............✍🏼
Hum masu
karatu kuna zaton Galadima bai fahimci Muftahu namasa zagon k'asaba kuwa🤔?. kuduba yanda ya shashantar da
binciken ya akayi yasha desire tabs a fresh milk🤔.
To koma dai miye kumuje zuwa, ai masu iya
magana kance *Karshen alewa k'asa*🙄👎🏻.
Humm ya kuke
ganin sakin da Munaya ta nema? Shin zata samu? kokuwa zai bita bazai bayarba🤔?.
Kumuje zuwa dai a page nagaba my guys🥳⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀
No comments