BARIKI NA FITO (BOOK 1) 24
*PAGE 24*
Fita yayi ya
bud'e kofarshi ganin fadawa a wajan yasa yayi tsaki, domin ya tabbata bazasu
Bari ya fita shi d'aya ba and inya fita dasu akwai matsala, dan shuru yayi
sannan ya dake tare da fitowa,
nan suka zube suna gyara kimtsa Allah ya
taimaki Yarima Mai jiran gado takawarka lafiya.....
Dakatar dasu
yayi alaman ya isa, gaba yayi suka tashi suna kokarin binshi ya dakatar dasu
tare da fad'in bana bukatar ku bini.
kansu na
k'asa suka amsa da fad'in komai Yarima yace dole mubi
Murmushi
yayi cikin jin dad'i tare dayin gaba, mota ya shiga kiran VENZA gaba d'aya
motar tinted ne baka ganin wanda ke cikin motar saboda tinted din but na motar
na ganinka, harya tada motar saiga
Usman nan kaman daka sama bud'e motar yayi ya
shiga, tare da fad'in ina zaka? Gimbiya ta karaso kai ake jira
Yarima Aliyu
tsaki tayi tare da kashe motar ya fita cikin takaici
Ganin ya
fita yasa usman binshi a baya
Direct
d'akinshi ya shiga kayan da akace shi zaisa in gimbiya tazo shiya sa, sannan ya
fito a falo yaga usman baiko kulashi ba yayi waje abunshi
Ganin haka
yasa usman ya bishi a baya yana murmushi.
Koda Yarima
ya fito fadawa suka bishi direct wajan motocinshi ya nufa suka bud'e Mai ya
shiga, usman shima da sauri ya shige aka ja dan zuwa gidan sarkin katsina dake
nan domin suje su tawo dasu.
Koda suka
karasa duka mutane suna mota, gimbiya ce ta fito fadawa suka mata Iso har motar
da Yarima Aliyu yake ta shiga ta zauna a baya, usman kuma ya koma wata motar
Gimbiya
zinatu Bayan ta shiga ta kalli Yarima cikin murmushi tare da fad'in wow my
handsome....
Ido ya rufe
cikin takaici, jiba yanda take abu a gaban driver
Jan motar
akayi suka fara tafiya, hannunta tasa cikin na Yarima
Kallon
hannun yayi tare da kallonta ya watsa mata wani irin kallo da sauri ta cire
hannunta ganin irin kallon da yayi mata, ganin yanda ya d'aure fuska yasa taji
ya bata tsoro yasa ta kame bakinta tayi shuru
Bayan sun
karasa masarautar tasu, aka bud'e musu Mota suka fito, su mum ne a tsaye dasu
fadawa domin tarban su, gimbiya da Yarima suka fito tafiya suke a tare har inda
aka ware musu, wajan babba ne gefen gimbiya da kawayenta babba ne sannan gefen
danginta shima daban, Bayan gimbiya zinatu ta shiga ciki zama tayi Yarima fita
yazo....
Tayi caraf
tace Yarima ba yanzu zaka fita ba sai wani ya shigo
Yace Aiba
gadinki aka bani ba yana fad'in haka yasa Kai ya fita a falo yaga su mum suna
kokarin shigowa ciki
Mum ganin ya
fito tamai wani irin kallo alaman ya koma, ranshi a jagule dole ya koma ciki,
tare suka shiga gimbiya zinatu gaida mum tayi cikin girmamawa
Mum amsawa
tayi tare da fad'in tubarkallah, su Hafsat zama sukayi suna dan Jan gimbiya da
fira duk da tana yi tana d'an jin kunya kaman dagaske, mum ita da Yarima suka
fita
Mum d'akin
yarima sukayi tace Yarima Wai mai yake damunka ne? A haka kake son in bari ka
kara aure jiba yanda kakema wannan ma Anya zakai adalci kuwa?..
Da sauri
yace mum kiyi hakuri, yau raina a bace yake amma ai kin San your son zaiyi
adalci mum
Murmushi mum
tayi tace waya batama Yarima rai?
Dan shuru
yayi Kafin yace mum Zainab taki picking calls dina, wai sai Bayan biki na,
gashi babu inda zani Har sai an d'aura aure
Murmushi mum
tayi danta gane itace wacce d'an nata yake so, tace bani number dinta in kira
maka ita..
Kaman yana
jira da sauri ya karanto ma mum number din, dialing mum tayi ringing biyu
bariki ta d'auka tare dayin sallama dan tunda taga number din take tunani dan
taga special number ne sai yasa tayi sallama
Amsawa mum
tayi tare da fad'in my daughter, Yarima ya kawo karanki kinki d'aukan waya.
Jin haka
yasa ta gane mum dinshi ce, da sauri ta gaida mum cikin girmamawa.
Amsawa mum
tayi tare da bama Yarima wayan sannan ta fita
Yarima yace
my princess do you know how worry I am right now? Wannan wani irin punishment
ne haka? Kin San zan shiga damuwa Sosai na rashin jin muryanki
Bariki tace
shine kasa mum ta kirani koh?
Murmushi
yayi tare da fad'in Aida Nasan hakane dama tun dazu na fad'a mata, Zainab am so
worried about you, harna fito Zanzo aka kirani....
Tace Yarima
amma kace bazaka fita ba sai Bayan aure koka manta kace haka al'adan yake?
Yace ban
manta ba, dama Nasan saboda kina tunanin bazan zoba yasa kika 'ki d'aukan
wayana, ai inda Banyi magana dake ba yau Toh da komin dare sai nazo na ganki
Murmushi
tayi
Yace I miss
you my princess, ya shirye shiryen Walima?
Tace
Alhamdullilah muna tayi, ga Kai yayi zafi, sai naga anyi an gama Kafin in huta.
Yarima yace
Allah ya taimaka, gaskiya Kina bukatar hutu
Tace hakane
idan muka gama zanyi tayin bacci har na sati d'aya in kashe waya na in huta
Yarima Aliyu
yace joking, ban yarda da kashe waya ba
Murmushi
tayi tare da fad'in ina amaryan mu?
Yace Tana
nan yanzu ma zani in ganta.
Bariki tace
uhm toh sai ka dawo Tana kokarin kashe wayan....
Yace karki
kashe min waya ban gama magana dake ba..
Tace Yarima
amarya na jiranka fah
Yace I know
ita da zamu kwana gida d'aya
Bariki wani
abu taji ya tokare mata a rai, amma saita dake tace uhm
Yarima jin
tayi shuru yasa ya canza maganan da fad'in my princess very soon za'a turo
gidanku so plz next ganin da zan miki a gidanku nake son in ganki, tunda har
kin amince min inaga dan nazo babu wani laifi, sannan a ranan da Zanzo Zan nemi
izini wajan baba
Tace Allah
ya kaimu lokacin da zaka zo
Ya amsa da
Ameen tare da fad'in my wife to be insha Allah
Murmushi
tayi cikin jin dad'i
Sun dad'e
suna fira cikin so da k'auna Kafin sukai sallama, tare da fad'in inya kirata ta
d'auka ko ya fad'ama mum, dariya tayi tare da fad'in zan d'auka
********
Hjy habiba
ce zaune daka ita sai rigan bacci haulat kuma na kwance akan cinyarta tana
danna waya
Wayan hjy
habiba dake ajiye kusa da ita ya fara kara, d'auka tayi taga son da sauri ta
d'auka tare da fad'in ya naga number dinka na Nigeria?
Dariya yayi
tare da fad'in mum Ina airport plz turo a d'auko ni.
Hjy habiba
tace what a surprise, Bari in turo yanzu tashi tayi tana fad'in haulat tashi
kisa kayan mutunci d'ana ya dawo yanzu za'a dauko shi a airport.
Haulat tace
wow mum kice bros dina, tashi tayi itama ta nufi toilet dan tayi wanka dan basu
dad'e da gama she'ke ayarsu ba suka zauna a nan
Hjy habiba
tasa aje a d'auko mata gudan d'an nata daka airport inda itama tayi wanka tasa
riga da zani na atamfa ya Mata kyau dan dama tana da kyan jiki, zama tayi a
parlour tana jiran zuwan d'an nata...
Haulat ce ta
fito itama cikin wata doguwar rigan less dinkin yayi mata d'as a jiki tayi kyau
Sosai nufan hjy habiba tayi tare da manna mata kiss a baki
Hjy habiba
taja baya tare da fad'in a'ah dakata mubar wannan abun sai a cikin d'aki any
moment d'ana zai iya fad'owa so ya kamata mu dinga taka tsan tsan
Haulat tace
Kai mum naga kin min kyau ne dana ganki harna Fara sha'awanki so nake miyi love
plz mum
Hjy habiba
tace sorry my daughter Bari farhan yazo inya shiga d'akinsa sai muje muyi
abunda za muyi
Haulat tace
ok mum
Suna cikin
fira saiga wani saurayi ya shigo falon
Da sauri hjy
habiba ta tashi ta nufeshi tare da rungume shi tana fad'in welcome son
Yace mum I
really miss you tare da kara rungumeta
Idonshi ya
sauka akan haulat dake tsaye tana ta murmushi, ido ya kura mata na wani lokaci
sannan ya d'an saki mum dinshi tare da fad'in mum Bakuwa kikayi?
Hjy habiba
tace eh sun tare da fad'in haulat ga farhan
Haulat tace
sannu da zuwa
Murmushi ya
sakan mata tare da fad'in yauwa nagode
Hjy habiba
janshi tayi sukai sama direct d'akinshi suka nufa, suna shiga yace Kai mum
wannan yarinyar tana da kyau Sosai
Hjy habiba
bata fuska tayi tare da fad'in toh inma kana tunanin wani abu ka Bari domin
bikinta ya kusa
Dariya kawai
yayi sannan ya shiga toilet dan yayi wanka
Ganin ya
shiga toilet yasa Hjy habiba fita danta jirashi a dinning yazo yaci abinci,
A falo taga
Haulat tana waya tana murmushi tun Kafin ta karasa ta d'aure fuska domin ganin
yanda take wani murmushi, kusa da haulat taje tana fad'in ke dawa kike waya?
Kashe wayan
tayi tare da fad'in mum nida wani guy dina ne
Hjy habiba
tace OK dan a zaton ta haulat na waya da wata mace ne sai yasa take wani kanne
murya
Farhan ne ya
fito cikin Kananan kaya yayi kyau Sosai dan dama babu laifi yana da kyau dogo
ne bashi da jiki Sosai ga idonshi manya......
Kallon
haulat yayi wacce take danna waya yace Mata haulat come let eat together
Tashi tayi
suka nufi dinning din Wanda hjy habiba ke zaune na jiran fitowan nashi
Hjy habiba
ce ta zuba mai abinci, Fara ci yayi yana yi yana kallon haulat duk hjy habiba
na Lura da hakan wanda take ganin ya kamata ta d'auki mataki tun da wuri....
Hmmm muje zuwa dai
*******
Yau ake
shirya mothers day Wanda mum din Yarima ce ta had'a, a cikin masarautar za'ayi,
karfe biyu na rana aka saka mutane har Sun Fara hallara
Amarya ce
cikin wani shegen less Wanda kallo d'aya zaka masa kasan Mai shegen tsada ne,
anyi mata kwalliya na Kece raini babu laifi tayi kyau Sosai, bayan an gama
shiryata da zata fita aka saka mata wata alkyabba akan kayanta nan kawayenta
suka jeru gaba kuyangi baya ma kuyangi har wajan da aka tanada dan zaman
amarya.
Yarima Aliyu
kam yana gefenshi cikin bedroom dinshi shida usman falon abokananshi ne, Usman
dake zaune a gefe yace plz Yarima ka tashi ka shirya mana kasan zamu je muyi
mata koda 5mnt ne sai mubar wajan plz ka tashi ka shirya K...... Kiran mum din Yarima cikin wayar usman shine
ya Katse Mai magana tare da fad'in Kaga mum ce ka tashi muje
D'auka usman
yayi ban San mai mum tace ba naji yana fad'in ga munan ranki ya dad'e
Usman kallon
Yarima yayi yace mum tace maza maza muzo yanzu
Tashi yayi
rai a jagule ganin ya tashi yasa usman fita danya bashi waje ya shirya
Yayi wajan
30mnt sannan ya fito cikin wata Shegiyar shadda tare da malin malin ba karamin
kyau Yarima Aliyu yayi ba kamshi kawai ke tashi ganin fitowanshi yasa
abokananshi suka tashi dan tafiya wajan mothers day din tun a nan wasu suka
fara d'aukanshi hoto, suna fita fadawa suka fara kirari har wajan mothers day
din suka je, inda Yarima ya zauna kusa da amarya wato gimbiya zinatu, sunyi
matukar kyau Sosai ana ta d'aukansu hoto
Nan aka saka
wa'ka inda aka bu'kaci amarya da ango su fito, Yarima tashi yayi inda suka jero
tare gimbiya ta sa'kale hannunta cikin na Yarima har filin inda za suyi ranan
inda suka fara rawa tana manne a jikinsa, duk da Yarima yana dan basarwa baya
son yi, nan abokananshi suka fito suna musu spraying, kawayenta ma Suma suka
fito suna musu liki, abun dai gwanin sha'awa ana ta d'auka a hoto har y'an
gidan tv Suma sun zo suna d'auka, Anata watsi da naira kaman ba gobe
Yarima ko 1hr
baiyi ba yabar wajan ya samu ya silale ango ya gudu sai a bokanan ango kawai,
ganin Yarima baya wajan yasa Suma suka bar wajan
Yarima
d'akinshi ya shiga inda ya kira bariki har sau uku batai picking ba, yace where
did she keep her phone ?
K'ara kira yayi
amma still batai picking ba jin karan bud'e kofarshi yasa bai kara kira ba
friends dinshi ne suka shigo suna fad'in saika tafi babu wanda ya Sani
Shuru yayi
ba tare daya tanka musu ba danshi rashin d'aukan wayan zainab yana sashi cikin
wani hali
Bariki kam
tana kallon kiranshi taki d'auka domin wani irin azabban kishi take ji, danya
fad'a mata yau za suyi mothers day tasan muddin ta d'auka sai taji wani abun ta
rasa mai yasa ta kasa controlling kanta tana matukar kishin Yarima, wani hawaye
ne ya zubo mata tare da fargaban duk ranan da Yarima yasan tana bin maza ta
shiga uku, kirgawa ta farayi rabonta dana miji tace dole ina gama istabra 'I
muyi aure karya ja wani lokaci Kafin a sami masu bakin jaba su fad'a ma Yarima
ya fasa auranta, tunawa tayi sanda yake fad'a mata zina kawai zaki aikata in
fasa auranki.... Lallai Yarima in yasan
nabi maza bazai aureni ba, dole insa Ayi bikin da wuri in yaso Bayan bikin zan
fad'a mishi komai da baki na tabbas dole auran ya zama na sirri ba kowa zai san
da auran ba sai an d'aura a hankali ta
furta karuwanci baiyi ba yaune rana ta farko da tayi data Sani tare da biye ma
zuciyarta data ingizata tace mai yasa na yanke hukunci cikin fushi kuka ta saki
mai taba zuciya .....
~MARYAM
OBAM~
No comments