BARIKI NA FITO (BOOK 1) 21
*PAGE 21*
Bariki ce
zaune idonta duk sun kumbura alaman taci kuka, sannan kallo d'aya zaka mata ka
gane tana bukatar bacci Sosai, amma saboda damuwa yasa
kwata kwata bata ji,
domin burinta shine anjima Yarima yazo, ta fad'a mishi komai taga yanda zasu
kaya, wani hawaye ne ya silalo mata Mai zafi, tunawa da mafarkin da tayi jiya
tayi wanda tsoro ya kamata take ganin kuma kaman hakan ne zai faru inta fad'a
mishi, kaita girgiza alaman bazan iya juran rasaka ba Yarima, tashi tayi dakyar
tayi toilet dan tayi wanka ko zata ji dad'i tun tana toilet take jin nocking
sauri tayi ta gama wankan ta fito daka ita sai towel ta nufi kofar Tana fad'in
Waye ne?
Muryan hjy
babba ne yace nice
Bud'e kofar
bariki tayi tana fad'in hjyta wannan uban nocking haka kaman zaki ballamin
kofar
Hjy babba
yace kedai bariki kin iya iskanci dama kina jin.... Bai karasa ba yayi shuru
yana kallon fuskanta hannu ya fara tafawa tare da fad'in mai zan gani haka?
Tace maika
gani?
Yace kodai
alh madu ne ya kuma marinki? Ji yanda Fuskanki yayi sintin kaman biredi bugun
k'ato.
Bariki tace
Wlh babu abunda ya faru kawai bacci ne da Banyi ba, shi yasa fuskan ta kumbura.
Hjy babba
tabe baki yayi tare da fad'in baki kwana wajan alh madu din ba kenan?
Tace ko
d'aya ban kwana ba, tunda period nake inna zauna uban Mai zan masa....
Hjy babba
yace kyasha masa ayaba mana
Bariki
dariyar da batai niya ba tayi tare da fad'in wace ayaban zansha? Dariya ta kuma
saki tare da fad'in dan Allah hjyta kibar maza suyi magana alh madu ai baida
ayaba sai tsinke Abu yanda kasan ayaban yara, ni Wlh matarshi ma take ban
tausayi, koya take dashi oho.
Hjy babba
yace haka zatai ta cinye kayanta tana jin dad'i AI abincin wani guban wani.
Bariki tace
tab aiko Indai ayaban alh madu ne toh Wlh babu mace Mai lafiya da zata ji
dad'inta hjyta Kinga ayaban ne kuwa? Niko damai zanyi miki kwatance..... Dariya bariki ta saki tace Wlh Kaga karamin
yatsa ta? Toh da kad'an ayaban alh madu
ya fishi.
Dariya Hjy
babba ya saki tare da fad'in na shiga uku Nayi gamo, kice ba banza ba kike
gudunsa?
Bariki tace
Ashe kin gane gashi babu y'an shafe shafe da tsotse tsotse sai dai kawai ya
kamo y'ar ayabarsa yasa yanda kasan ya sami kayan wanki dan iskan tsoho
Dariya Hjy
babba yayi yace ah toh wannan ai iskanci ne, taya yasan sarai abunshi karami
ne,, kuma bazai dinga shafaki da tsotse kiba sai kawai ya Saka miki ayaba gskya
da sake an Kama ango da Uwar amarya.
Bariki
dariya tayi tare da cewa Toh hjyta ai na dad'e Ina fad'a miki ni yanzu aure ma
zanyi in huta
Hjy babba
salati ya saki tare da tafa hannu yace bariki aure dai?
Tace shifa
Yace keda
alh madu din?
Tsaki tayi
tace koma da Waye zaki ji hjyta lokaci nayi
Hjy babba
yace adai gama rufa rufa din zai fito kuma zamu ji.
Bariki tace
toh sai a Bari lokacin yayi......
Habib ne ya
fad'o d'akin ganin hjy babba da bariki suna fira, yace wace wainar kuke toyawa
ne haka kuke k'asa k'asa da murya
Hjy babba ya
kalli habib yace Wlh dad'i na dake habiba kin cika zargi, shikenan babu daman
aga mutane suna fira sai a fara zargin su.
Tabe baki
habib yayi tare da gwale kafa ya zauna yana fad'in kwaji dashi, kallon bariki
yayi wacce fuska take a kumbure ga ido yayi ja, yace Mai zan gani dambe kikayi
da wani?
Tace Ya'ki
Nayi ba dambe ba.
Habib yace
ah daka tambaya? Ke kika sani ina Fata dai kin San yau kina da ba'ko saiki
tashi ki shirya muje inda zamu tun Kafin lokaci ya kure, ni Mai kika dafa ne
yunwa nake ji wlh.
Tace ban
dafa komai ba, nima saida kayi m.....
Yace dakata
Mlm ban son iskanci miye wani kayi? Mai ya had'ani da wannan Kalman ina mace
Bariki tace
Kai Allah ya kyauta
Habib da hjy
babba suka amsa da Ameen
Habib yace
dan Allah tashi kisa kaya mu fita daka nan maci abinci dan y'ay'an hanjina har
kugi suke
Kaya ta
d'auka tayi toilet tasa sannan ta d'auki Wanda zata canza anjima tasa a akwati
karami suka fita
Bayan sun
fita Hjy babba yaga mota sabuwa fil tana walkiya yace oh ji wannan motar Mai
Kyau
Bariki
kallon motar tayi ita harga Allah ma ta manta da ita.... Tace Alh madu ya bani
ita jiya.....
Hjy babba
yace shine baki fad'a mana ba amma dai baki da hali
Tace ni nama
manta da ita Wlh sai yanzu dana ganta na tuna
Habib yace
bariki Anya Kema baki Fara d'an taba shaye shayen nan ba? Taya zaki ce kin
manta da motar da aka baki?
Tabe baki
tayi tare da fad'in saboda ban d'auki kyautar da wani muhimmanci ba S.......
Hjy babba ne
ya Katseta da fad'in amma dai gaskiya bariki baki da mutunci, wannan motar Mai
Kyau matrix cefa, gata Sabuwa fil da ita, mutumin nan yana sonki amma kina
mishi tsiya....
Tace hjyta
yanzu saboda yaban mota kike wannan abun? Bayan kin San matsalan.
Tabe baki
hjy babba yayi tare da fad'in Indai da kud'i ai sai Ayi hakuri haka....
Bariki tace
bashi bane damuwa ta, hjyta inna dawo za muyi magana...... Gaba sukayi ita da habib
Habib yace
bariki Wai wani tsohon ne ya baki mota kike kushewa?
Tace wani
Sanata ne, mai karamin ayaba kaman na jarirai yaban.
Habib yace
na shiga uku Nayi gamo karamin ayaba? Kuma kaman na jarirai Toh ya yake cinki
da ita?oh ni habiba
Bariki tace
ci kodai gogawa dan banjinta ako ina
Habib yace
tunda ya baki mota ai Kinji dad'i yanzu dai kin San yakamata kiyi taka tsan
tsan dan Kar Yarima ya gane wani abu, in kuma sanatan zaki aura Toh yana kaiwa
nan ya sake shewa tare da fad'in sai kuje kuyi ta goge juna, tunda baida abun
kwarai
Bariki duka
takai ma habib tare da fad'in Rufamin asiri, in aureshi ince ma mutane Nayi me?
Wai dana bani miji babu kayan harka
Habib ya
saki shewa tare da fad'in shi Yarima yana dashi?
Duka takai
ma habib tare da fad'in ban son iskanci
Habib yace
karki kassarani, ai gaskiya ne shi yana dashi Mai girma ko ya Kar sai Kinje
kiga wacce bata Kai ta jarirai ba
D'aure fuska
tayi tare da fad'in habib Wlh ka daina dan ban son ana kushe min Yarima
I.......
Habib yace
ke zance ma ki daina miye kuma wani habib Toh Waye habib din? Taya zaki dinga
kirana da Sunan maza Ina mace karki kuma in ba zaki cemin habiba Toh ki bari
ban son iskanci yana maganan ne yana bud'e hanci alaman yayi fushi
Bariki gaba
tayi tana fad'in ni Nayi gaba in Kaga dama ka zauna a nan
Binta yayi
yana fad'in Wai bariki Mai kike nufi dani ne wai? Kalleni sama da k'asa miye a
jikin ki wanda babu a nawa?
Dariyan da
bariki batai niya ba ta saki tare da fad'in taya zan sani tunda kaya Sun boye
muje kowa yayi tsirara sai a gani
Habib yace
Aini ba y'ar iska bace in zaki zo muje kizo muje dan zaki iya ganin yarima ya
fad'o koda yaushe
Gaba sukayi
Dan zuwa gidan y'an uwan bariki na karya😹
********
Karfe hudu
da wasu mintinoni motocin Yarima suka tsaya a kofar gidan su zainab wato
bariki, message ya Mata tare da fad'in ina kofar gida
Bariki dake
kwance akan tabarma taji wayanta yayi kara, d'auka tayi ta duba ganin sa'kon
Wanda tun dazu take jira yasa ta tashi da sauri ta kara feshe jikinta da turare
tare da shafa powder, fita tayi
Tunda ta
fito idonshi ke kanta harta karaso matsowa yayi ya bud'e Mata kofar ta ciki
Tana kokarin
bud'ewa taga an bud'e murmushi tayi sannan ta shiga da sallama tare da rufo
kofar dan AC a kunne yake
Amsawa
Yarima yayi tare da fad'in maiya sameki? Kina ciwon ido ne?
Kai ta
girgiza alaman a'a
Yace Toh
maiya sami idonki naga kaman sun kumbura? Ko kuma kikayi?
Tace Yarima
wani mafarki nayi Wanda Yaban tsoro cikin mafarkin Wai nida kai muna fad'a har
kace bazaka aureni ba saboda an fad'a maka mugayen Abu a Kai na kum........
Hannunta ya
ri'ke Wanda yasa tayi shuru daka abunda tayi niyan fad'a, yace my princess bana
tunanin akwai abunda wani zaice a kanki in fasa auranki Abu d'aya za kiyi wanda
ko a masarautar mu babban laifi ne kuma yana d'aya daka cikin laifin Wanda Idan
ka aikata dole kabar masarautar shine zina, wannan abun ne kad'ai zaki aikata
na fasa auranki domin ni namiji ne mai kishi Sosai ina da kishin abunda nake
so, wanda na tabbata ke bakya d'aya daka cikin masu aikata alfasha sai yasa a
kullum nake kara sonki, ban kasance mazina ciba sai yasa a kullum nake ro'kan
Allah ya bani mace tagari wacce ta tsare kanta daka rudin zamani
Wani hawaye
ne ya silalo daka fuskan bariki wanda bata san sun zubo ba .....
Jin hannun
Yarima tayi akan fuskanta yana share mata hawayen tare da fad'in baby maiya
faru?? Ki daina wani tunani ina tare dake
nazo jin amsa kona karbu Ashe an dad'e dayin accepting dina.
Murmushi
tayi cikin sanyin jiki ba tare da tace komai ba, domin gaba d'aya maganan
Yarima yasa ta fita hayyacinta tare da neman hanyan mafita, tabbas Idan Yarima
yasan ita wacece bazai taba auranta ba, kenan mafarkinta gaskiya ne?.....
Katse mata
tunani yayi da fad'in my princess tell me Mai kike ji a kaina?
Murmushi
tayi tare da fad'in ai kace ka sami amsa
Yace eh but
Ina son in kara tabbatarwa
Tace Yarima
tabbatarwa ya wuce yardan da nayi za muyi aure Tana maganan ne tana rufe fuska
alaman kunya take ji
Matsawa yayi
kusa da kunnenta ya fara mata magana cikin rad 'a tare da fad'in I need my
kiss...
Tana jin
haka tayi saurin matsar da kunnenta Tana fad'in zan koma Gida
Murmushi yayi
tare da fad'in yau babu inda zani har sai anyi min abunda nake so, sannan kema
kina nan babu inda zaki
Tace Yarima
ko gaisawa ba muyi ba.
Murmushi
yayi dan yasan Tana son su canza zancen ne sai yasa tace basu gaisa ba , yace
oh hakane fah bamu gaisa ba
Tace eh Ina
wuni? Da fatan kazo lafiya
Murmushi
yayi tare da fad'in lafiya qalau, toh mun gaisa yanzu koh?
Tace eh
cikin murmushi
Yace Toh am
waiting for it
Tace what???
Yace kiss
Ido ta
lumshe ba tare da tace komai ba, wani irin son Yarima yake fusganta sai yau ta
kara tabbatarwa da tana sonshi tunda ta ganshi taji wani irin sonshi na
fusganta
Shima haka
ta gefenshi wani irin sonta yake ji har cikin ranshi ji yake kaman ya tafi da
ita ace yau mallakinshi ce da yafi kowa murna, daya nuna mata so Wanda bazata
taba samun wanda zai Mata shiba, amma dai a kwana a tashi burinshi insha Allah
zai ciki, ya tsara musu abubuwa da dama shida ita ya tanadar mata soyayya
tsantsa Wanda zai nuna mata inya mallaketa
Bariki ido
ta bud'e ta kalleshi ta gefen ido taga ita yake kallo, da sauri ta kara lumshe
ido, tare da tunanin abubuwa da dama, lallai Idan Yarima yasan wacece ni Toh
daka ranan na rasa shi, maiya kamata inyi? Hawaye ne ya silalo mata a
fuska......
Janyota yayi
jikinsa tare da share mata hawayen yace mai yake damunki ne yau my princess?
Tunda ya
janyota jikinshi ya saka mata kanta a kirjinshi ta lumshe ido domin gaba d'aya
jikinta ya mutu ga kamshin turarenshi dake dad'a tayar mata da hankali, yau ce
rana ta farko da namiji ya Mata haka taji har tana sha'awa da sauri ta Fara
kokarin Jan jikinta daka nashi amma saiya kara manneta dakyau
Ta gefen
Yarima kam shima jinshi yake wani iri, ya rasa wani irin so yake mata, kwata
kwata baya son ganinta cikin damuwa ko kad'an baya son yin nesa da ita akan
dole yake tafiya ya barta, yau ne rana na farko daya kosa ayi bakinshi da
gimbiya zinatu dan Ayi maganan auranshi da zainab dinshi....
Bariki ce ta
katse shi da fad'in Yarima wayanka na wuta kaman ana kira.
D'aukan
wayan yayi yaga gimbiya zinatu ce, murmushi yayi tare da d'auka har yanzu
bariki na manne dashi yaki sakinta. Yace gimbiya Barka da yamma... Yana maganan
ne yana Satan kallon bariki dake manne a jikinsa ban San mai gimbiya tace mishi
ba naji yana fad'in saura kwana nawa a kawo ki kaman jibi ne koh? Tunda anan
za'ayi komai.....
Bariki dake
kwance a kirjinshi taja jikinta da karfi har wayan tayi kasa ta silale daka
hannunshi, kallonta yake tayi yanda yaga ta murtuke fuska abun yaso ya bashi
dariya amma saiya dake dama da biyu yayi hakan, wayan yake kokarin d'auka
bariki kuma tana kokarin bud'e kofar, hannunta ya ri'ke Bayan ya d'auko wayan
kashe wayan yayi gaba d'aya, ya kalli zainab dinshi yace Ina zaki?
Tace zani
gida in d'auko Abu ne tunda naga kana waya
Yace Toh
yanzu na gama
Tace ina
zuwa yanzu zan dawo
Yace OK tare
da sakar mata hannu,
Fita tayi
tana shiga cikin gidan ta fashe da kuka, yanzu dan wacce zai aura ta kirashi
nake wannan kishin shifa Idan yaji na bayar da mutunci na ga wasu mazan ya
zaiyi? Kuka ta kuma saki Sosai tare da fargaban abunda zai faru in Yarima yaji
wannan zancen.......
~MARYAM
OBAM~
No comments