BARIKI NA FITO (BOOK 1) 10
PAGE 10
Driver din
direct wajan habib ya nufa yace bawan Allah Yarima na son ganinka.
Habib waige
ya farayi yaga dawa mutumin yake magana dan yaji yace Kai ba ke ba, habib yace
dawa kake?
Mutumin yace
dakai mana, yarima ke magana,
Habib yace
dakata Aiba namiji ka gani a gabanka ba, mace ce a gabanka kalleni dakyau ko
Kaga na maka kama da namiji?
Driver din
Yarima yace ikon Allah, kai yanzu kana gansamemen kato ka dinga kiran kanka da
mace?
Habib yace
dalla Mlm dakata Wlh sai in rufe idona in sharta maka rashin mutunci.
Ganin haka
driver din yace a'ah Allah ya baki hakuri Hjy, yarima na son ganinki,
Shuru habib
yayi yace wani yarima?
Nuna Mai
motar driver din yayi tare da fad'in yana cikin mota.
Habib yace
oh dama tare kuke Aida kamin bayani tun Farko muje.
Yarima duk
wannan abunda suke yana kallonsu amma baya jin abunda suke fad'a, danko bai
tambaya ba yasan habib dan daudu ne domin yanda yaga yana abu, sannan kan
Yarima ya fara kullewa domin ganin irin mutanan dake sintiri a wajan.,
Toh miye
tsakanin yarinyar daya gani da wannan dan daudu din?
Jin bud'e
motar yasa Yarima ya dawo daka duniyar tunanin daya Fara.
Habib ne ya
shigo motar sanyin AC ya dukeshi ga kamshi na tashi, yace oh aljannar duniya
Mai kud'i bai kwana da haushin kowa ba.
Kallon
Yarima yayi wanda yaga ya mishi kwarjini, yace ranka ya dad'e barka da zuwa,
ina fatan dai lafiya?
Yarima Aliyu
yace lafiya, ina da tambayan da nake son maka ne.
Habib kasa
cewa komai yayi duk da yarima yace mishi Kai ba ke ba, sai fad'i yayi Ina ji.
Yarima Aliyu
yace kwanakin baya nazo wucewa na ganka tsaye kaida wata yarinya tasa hijab a
bakin titi....
Tun Kafin
Yarima ya karasa magana habib yace bariki kake nufi?
Yarima yace
what bariki kaman ya?
Ganin yanda
Yarima ya shiga da yaji yace bariki yasa ya gane badan hannu bane, saiya
wayince yace Ina nufin gidan duniya kaman bariki ne zaka ga mutane da yawa sai
yasa nace bariki kake nufi ina nufin ni inada mutane Kala Kala.
Jin haka
yasa Yarima hankalinshi ya kwanta dan da har yaji kirjinshi ya fara bugawa da
karfi
Yace baiyi
sati biyu ba na ganka kaida wata tasa hijab ta ri'ke akwati daka gani bakuwa
ce.
Habib yace
au kodai Zainab kake nufi? Tasa hijab blue koh?
Yarima yace
eh itace
Habib yace Zainab
baiwar Allah Aiba a nan take ba, gidansu yana cikin gari, tana zuwa wajan y'an
uwanta ne a nan.
Yarima yace
ko zaka iya kaimu gidansu?
Habib yace
Kai Anya zata kulaka kuwa?
Inaga ka
bani number dinka inna mata magana sai in tura maka number dinta, sai ku Fara
magana koh?
Yarima yace
hakan yayi bashi card dinshi yayi tare da dauko kud'i bandir d'aya y'an dubu
d'aya d'aya ya bashi dubu d'ari kenan.
Habib amsa
yayi tare da zabga Mai godiya yace saika jini ranka ya dad'e.
Kai yarima
ya d'aga tare da fad'in ka tsaya a baka babban riga, inka fita kama driver dina
magana.
Habib sai
murna yake tare da godiya.
Habib fita
yayi ya Kalli driver din Yarima, tare da Galla Mai harara yace ana magana
dakai.
Driver din
bud'e motar yayi
Ban San mai
yarima yace Mai ba sai gashi ya rufe motar tare da bud'e booth din motar da
wasu fadawa ke ciki ya d'auko kaya a Leda ya mi'ka ma habib tare da fad'in
gashi Hjy.
Habib amsa
yayi tare da fad'in dan rainin wayau.
Murmushi
driver din yayi tare da fad'in Allah ya shirya, mota ya shiga suka wuce.
Shiko habib
gidan ya koma, cikin murna, direct d'akin bariki ya nufa.
Nocking yayi
tace Waye?
Yace bud'e
mana.
Jin muryan
habib yasa ta bud'e kofar.
Shiga yayi
yana fad'in bariki bariki gskya inda ban sanki ba, da Nayi Asara.
Kallonshi
tayi tace maiya faru haka? Wannan ledan fah?
Dariya yayi
tare da fad'in kyauta aka ban duk saboda ke.
Tace ni?
Waya baka?
Zama yayi
tare da ajiye ledar yace d'an Sarkin Zazzau Yarima, shida kanshi yazo nemanki.
Tace kaman
ya?
Labarin
abunda ya faru ya bata, tare da fad'in Kinga kyautar da yamin ya nuna mata
kud'in da Yarima ya bashi, tare da bud'e ledar shadda ce dinkakku har Kala biyu
kuma duka gezna, habib yace oh Kinga Abun arziki, ni Ina mace anban kayan y'an
maza.
Bariki dariya
tayi tare da fad'in wato shi ustaziya yake so? Dariya ta kuma saki oh hijab ya
gani shi'a dole yaga Kamila matar aure, dariya take Sosai harda hawaye lallai
sai yanzu na gane maganan nan da ake
cewa karka taba shaidan mutum domin baka san maike zuciyarsa ba, lallai inda
yasan wacece ni da bai kawo kanshi ba.
Habib yace
Kedai kina da matsala kin ganshi ne? Wlh ya had'u na tabbata irin mijin da zaki
burin aure bee, sai dai gskya ina tsoran Idan yasan koke wacece ban tunanin zai
aureki.
Bariki dan shuru
tayi can tace, toh ai nima ba aure nace ina so ba, bariki na fito, .
Habib yace
oh ni habiba rabo na kiran mutum yana gudu, wlh zaki ci dukiya iya dukiya ga
sarauta, ga guy din ya had'u, amma naga akwai miskilanci.
Bariki tabe
baki tayi, tace habib kasan n........
Dakata Mlm
habib ya Katseta, wlh zan miki bura uba, wai mai yasa kike min haka y'ar A
dince kike kyashin karasawa, gaskiya banso yana maganan yana wani daure fuska
tare da hararan bariki shi'a dole ranshi ya baci.
Bariki tace
yakuri kawata
Tabe baki
yayi tare da fad'in hakuri kaya ne.
Bariki tace
kawata babu abunda na tsana kaman in yaudari mutanan kirki, kince wannan badan
hannu bane, aurena yake son yi?
Habib yace
kwarai dagaske.
Bariki tace
bazan iya soyayya dashi ba, yafi karfina.
Habib ya
tabe baki, tare da fad'in kaman ya yafi karfin ki? Haba bariki ai babu namijin
da yafi karfin ki, kalli madubi ki gani mana kina da kyau na bugawa a jarida.
Bariki tace
hakane, niba mutuniyar kirki bace, bazan yaudari mutanan kirki ba, hawaye ne ya
zubo mata a ido, da sauri ta goge dan Kar habib ya gani, but is too late dan ya
riga da ya gani.
Yace Mai zan
gani haka? Bariki Kece kike hawaye? Babban magana, toh amma miye dalilin ki na
cewa ba zaki yaudari mutanan kirki ba, aiba ke kika ce kina sonshi ba.
Bariki tace
kawata mutanan kirki suna da kyakyawan zuciya, suna saurin yarda da Abu, in
zaki fad'i gskya kawata keda kanki kin San mutumin kirki kamili bai dace dani
ba.
Habib yace
a'ah Wlh.
Bariki tace
nidai yanzu bazan ganshi ba dan ban shirya aure ba.
Habib yace
ban son bariki Mlm, Kar kisa ya maidani karamar mace, mai magana biyu, dan
kawai nace miki kamili ne, Aiba daka nan yake ba, ki bari ki had'u dashi sai ki
gane ko Waye shi.
Bariki shuru
tayi tana nazari, can tace hakane zan had'u dashi, ka bashi number dina zan
gane koshi Waye.
Habib yace
yanzu naji Batu.
Bariki tace
yau wani mai kid'a ne zaiyi wasa?
Yace masu
kid'an kwarya yau muka gayyato.
Bariki tace
Kai yau zamu ra'kashe.
*****
Yarima ya
koma Gida, koda ya isa gefenshi ya shiga domin yayi matukar gajiya, yana shiga
bedroom dinshi kwanciya yayi akan gadon d'akin tare da lumshe ido, yau yana
cikin farin ciki domin nan bada dad'ewa ba zaiga yarinyar da yake burin gani
wajan shekara da shekaru.
Ya dad'e
yana kwance yana tunanin bariki, son yarinyar yana kara shiganshi koda yaushe,
d'auko drawing dinshi yayi yana ta kallon fuskanta yanda take murmushi saiya
kara mata kyau, jin karan wayanshi yasa ya ajiye hotan tare da d'aukan wayan,
limam ya gani da sauri ya danna tare da d'auka, ban San mai limam yace mishi ba
naji yace OK gani nan zuwa, tashi yayi tare da shiga toilet yayi wanka Jim
kad'an sai gashi ya fito, shiryawa yayi cikin wata shadda Mai ruwan sky blue ba
karamin kyau yayi yasa hula ya fita domin gidan sarauta Indai zaka wajan Mai
martaba ko Yarima dondole sai mutum yasa hula, fita yayi dan zuwa wajan limam.
Koda Yarima
ya karasa suka gaisa da limam cikin girmamawa.
Limam gyaran
murya yayi tare da fad'in Nakira ka kaman yanda nace zan nemeka.
Yarima yace
hakane Allah gafarta Malam.
Limam yace
akan maganan da mukayi dakai kwanaki akan yarinyar daka fad'amin, Nayi istahara
naga akwai alherai da dama a tare da ita, sai dai abunda ban gane ba shine
akwai wani boyayyan abu a tare da ita wanda in ba'ai wasa ba zai iya hana ka
samunta, inaso ka dage da addu'a akan zabi mafi alkhairi.
Yarima shuru
yayi yana nazari, can yace nagode Mlm tare da tashi yabar wajan.
Direct gefen
mum dinshi ya nufa inda ya sami Mai martaba yana nan, zama yayi sannan ya gaida
iyayen nashi,
mai martaba
yace ya hanya?
Yace lafiya kalau Abba
Mum tace
ansha hanya ya sirikar tawa?
Kai ya dan
Sosa cikin jin kunya yace tana lafiya.
Tambayan mum
yayi tare da fad'in ina Hafsat?
Mum tace
Tana d'akinta.
Tashi yayi
ya fita, d'akin lil sis din nashi ya shiga inda ya ganta tana karanta wani
novel, fisgewa yayi da sauri ta d'ago ganin dan uwan nata yasa ta saki kara
tare dayin hugging dinshi
Tace saukan
yaushe?
Yace ban
dad'e da dawowa ba, inata magana kinyi shuru kinyi nisa wajan karanta littafi.
Tace bros
Littafin ne akwai dad'i.
Murmushi
yayi tare da zama inda suka fara fira cikin so da kauna.
Hafsat tace
ya sister dina hope Tana lafiya?
Jan Hancin
Hafsat yayi tare da fad'in kije katsina saiki tambaye ta.
Dariya
Hafsat tayi Sosai sannan tace bros sai dai muje tare kafata kafar ka.
Tashi yayi
tare da fad'in inna zauna dake saiki samin ciwon kai bye.
Dariya tayi
shiko fita yayi ya nufi gefenshi koda ya shiga sintiri ya dingayi a d'aki yana
tuna abunda limam yace, toh miye boyayyan abun? Ya kamata in sani, tunawa yayi
da gidan da yaga habib ya fito ko bai tambaya ba yasan gidan karuwai ne, Toh
miye dangartakar yarinyar da wannan dan daudu din? Kai something is fishy I
have to find out. Wata zuciyar tace karka manta ance gidan y'an uwanta tazo Kar
kayi Mata mummunan zato, ka had'u da yarinyar farko Kaga yana yinta Kafin ka
zurfafa tunani, wannan tunanin da yayi shine yasa yaji duk wani tantama da
yakeyi ya kawar, yace bana tunanin zaki Aikata hakan domin Fuskanki ta mutanan
kirki ce.
****
Bariki ce
cikin wani crazy jeans da wata Shegiyar top Wanda saman ya kama kasan kuma ya
bude, gaba d'aya duk wata sura dake jikinta kayan Ya bayyana su, tayi mugun
kyau duk da batai makeup ba, kanta ko d'ankwali babu, fita tayi zuwa wajan da
ake kid'a karuwan gidan suna ta rawa, ita kam tsayawa tayi tana kallo, habib ne
yazo inda take tare da fad'in bariki ya naga baki shiga cikin rawan ba?
Bariki tace
kid'an ne bai tsuma ni ba. Suna tsaye suka hango khairat ita da mutumin da suka
gama fad'a jiya sukai ma juna zagin kare dangi sai gasu yanzu suna tare suna ta
dariya.
Habib yace
oh in kana bariki zaka ga Abu iri iri Kinga y'an iska jiya Sun gama kwasan y'an
kallo yau kuma gasu can suna soyewa oh ni habiba.
Bariki tace
toh yana zuwa ana bashi gindi yana ci ai dole ya manne Mata.
Habib yace
ah naga alama hala ta wanke mai ne yasha wannan rashin mutunci da suka tsunduma
jiya amma har ya dawo yau, yana maganan ne yana kama kugu.
Ya kalli
bariki yace na turama Yarima number dinki dazu, Nasan koda yaushe zai iya
kiranki inya kira saiki nuna mishi keta Allah ce, mi'ka mata card din Yarima
yayi yace ga Katin shi numbers dinshi suna ciki duka, dan karya kiraki ki
d'auka ki kwafsa, amsan card din tayi Mai kyau taga an rubuta Yarima Aliyu ga
tambarin sarauta ansa a card din ga numbers dinshi guda uku da email dinshi a
jiki, murmushi ta saki tare da tsintar kanta da son ganin wannan Yarima din,
taga Ya yake domin yanda habib yake kozan tashi abun yayi yawa, suna nan tsaye
saiga Hjy babba shida Haulat Sun zo. Hjy babba yace wace wainar kuke toyawa ne?
Haulat tace
tambayesu dai, ni naga kwana biyu suna makale ita da habiba,
Hjy babba ya
tabe baki tare da kallon habib yace wani dadiron kika had'a mata da taji
dadinsa yasa ta manne miki ?
Habib yace
ah yau naga idi zindir, wannan tambaya sai kace ina zaune gidan Radio ana
interview dani, gaskiya bana so ance damai dami tayi sata.
Haulat tace
in tayi wari maji ai.
Habib yace
Toh Uwar kini bibi aiko fasa gurbi yayi baki ji.
Bariki tace
kanku ake ji shiga filin rawa tayi ta Fara kad'a duwawu Tana juyashi ganin haka
yasa Haulat itama ta shiga nan Suka fara li'ka ma masu kid'an kud'i Anata ma
bariki kirari, bariki na rawa Hjy babba yazo yaja hannunta tare da fad'in tawo
akwai magana, bayan sunje wajan da babu hayaniya ya kalleta tare da fad'in alh
madu yanzu Ya kirani yace in fad'a miki ki d'auki wayarsa yana son magana dake.
Bariki tace
in dauka inyi mishi Uwar me? Wlh Hjy
babba kibar wannan dan iskan mutumin babu ni babu shi kuma Wlh saina rama
abunda yayi min, shi ayabarsa karama ba dadinta nake jiba, gashi babu y'an
wasanni balle in rage zafi sai dai kawai ya saka maka ayaba cikin gindi yanda
kasan ana Wasan yara, ni Wlh babu abunda zai kara had'ani dashi tsohon banza
yana gaf da rami amma yana bin jikokin sa, matsiyaci.
Hjy babba
yace ah Abun har yakai haka? Toh fah Tashin hankali, nidai ki dubi mutunci na
kiyi hakuri Wlh mutumin nan sonki yake duk yabi ya damu.
Bariki tace
yana dai son kayan dad'i
Hjy babba
shewa ya saki tare da fad'in kaji tsohon banza har yasan dad'i, au Ashe sulhu
nake, nidai bariki kiyi hakuri yace ran Friday zai shigo kaduna kuma danke zai
zo, ki daure ki d'auki wayarsa.
Bariki tace
shikenan zan d'auka tunda kince amma fah saina rama abunda yamin dan sai na
nuna mishi niba Kalan karuwan da ake duka bane inyi shuru.
Hjy babba
yace oh waike bariki Abu bai wuce wane a Wajanki ,ki duba fah kiga wannan
mutumin da girmansa yake lallabaki aiko darajan girman nashi kya hakura.
Tace wani
girma? Ai tunda ya tube tsirara a gabana naga komai kallonshi nake kaman Sa'a
na, ni a wajena bashi da girma dan ya zubar dashi.
Hjy babba
yasa hannu a baki tare da fad'in ah yau Ina ganin sabon salo, nima kam bari in
fara rufe nawa jikin Kafin ki gane min komai.
Dariya
bariki tayi tare da fad'in hjyta Aini dake duk abu d'aya garemu inna gani ma ai
babu damuwa.
Hjy babba
yayi gaba yana botsare duwawu tare da fad'in karki lalata ni.
Tana tsaye
tana dariya taga ansa Mata wani abu a hanci tun daka lokacin bata san inda
kanta yake ba.
Koda ta
farka ta ganta cikin wani d'aki Mai datti duk yayi kura waige waige ta farayi
tare da fad'in inane nan? Jin karan kaman za'a bude kofar yasa ta tashi mai
kid'an nan taga ya shigo, tace dama kaine ka kawo ni nan?
Yace kwarai
kuwa, dama na fad'a miki, Kinga nan babu kowa, zanyi abunda nake so inyi dake
kuma Bari kiji bazanyi amfani dake da condom ba saboda ina son in saka miki
cutar dake jikina wato HIV.
Bariki tace
karka fara yin wannan kuskuren, kai baka isa ka taba koda yatsa na bane balle
gindina.
Dariya yayi
tare da fad'in bari in nuna miki, matsowa kusa da ita yayi tare da cafko ta,
yace gashi na taba ki, tureshi ta farayi amma ina taga ya Mata ri'kon gaske,
kokarin cire mata riganta yake yana fad'in ai koda mutuwa za kiyi yau sai naji
irin naki zumar Wlh tunda na ganki na mutu da sha'awar ki, cire mata rigan yayi
daka ita sai brezia da jeans din dake jikinta yace Kai kalli nono masu kyau yau
zansha dad'i bariki tace kana aikata kuskure wani Wawan Mari ya sakar mata
Wanda saida taga stars yace kuskuren uwarki ai Wlh yau saina ciki tunda na kawo
ki nan gwara ma ki bani hadin kai tun Kafin in illataki......
No comments